Showing 183001 words to 186000 words out of 303099 words
mutane, ni dai da xaka yi hakuri ka daina xuwa idan ma girkin gidan naku ne baka so sai ka dinga xuwa nan xan saka maka a kwano in ajiye, kazamai da masu wari sun yi yawa a duniya yanxu kaje ka ci abinda xai hallaka ka wataran mu shiga uku gaba daya" Shi dai dariya kawai yake Imaan ta juya ta fita parlon.... Dai dai inda suke yawan tsayuwa da Mujaheed ta tsaya, ba a wani dau lkci ba taji foot steps dinsa yana tahowa, yana kusa isowa wajen suka yi ido hudu, yyi slowing pace dinsa amma kuma ba shi da alamar tsayawa, cikin sanyin murya tace "Plss ka tsaya Abbana" Tsayawa yyi ya dawo gefenta ya rungume hannunsa a hankali yace "Toh na tsaya daughter" Lkci daya hawaye ya kawo idonta ta sunkuyar da kai cikin rawar murya tace "Don Allah kayi hakuri ka yafe min" Yace "Inyi hakuri a kan me" da kyar tace "Abinda yasa kake fushi da ni" yayi murmushin karfin hali yace "Aa ban yi fushi ba Imaan" tace "Wlh ka yi, don Allah kayi hakuri wllh hakan baxai kara faruwa ba" Yace "Imaan don Mujaheed yayan ki ne kamar yanda kike yawan fadi ba yana nufin same parent suka haife ku ba so I have all right to get angry, Shi din ba Muharramin ki bane, da nine nace mu fita eatry ni da kudin gaisuwana ke kanki ba yarda xa ki yi ba, not to talk of giving ur meat..." ta dinga goge hawayen da ya ki tsaya mata tace "Plss kayi hakuri, baxan sake ba, abinda ma yasa ya kai ni wajen ranan ya siya min kaza shine saboda I promise xan taya sa fada ma wata yarinya da yake so cewar yana sonta wai ya kasa fada mata.... Wllh saboda nace ni xan yi ma yarinyar magana ya sa ya siya min kaza don in maya" murmushi Sadeeq yyi yana shafa kansa yace "Ya wuce Imaan... Xan wuce masallaci it's almost time" a hankali tace "Ka hakura?" Yace "Tuni na hakura ai" mu je ki raka ni gate, har suka isa gate babu wanda yace komai cikinsu, yana kallonta yace "Good night" ta gyada masa kai ya wuce ta juya ta koma ciki. Tun daga sannan imaan tayi kokarin dinga avoiding Mujaheed, ko parlonsu ya shigo dama tashi take ta wuce daki ko ta wuce kitchen, part din Inna kuwa kafin yaje xata kai mata abinci ta maxa ta dawo, ana haka har ya rage two weeks su fara exams kuma hakan yyi dai dai da saura sati biyu a kawo lefenta tare da sadaki daga gidansu sadeeq, sosai ta dage da azkar kamar yanda Ammi ta ce mata saboda yawan faduwan gaba da take, Ammi ma ta bata addu'o'in da xata dinga yi tana kuma kokarin tashin ta duk dare tayi sllh. Yau Saturday Imaan ta fito parlor sanye da hijab dinta har kasa hannunta rike da karamin jaka, duk da babu komai fuskarta sai eye pencil da Chappete ba karamin kyau sanyanye tayi ba, Ammi dake xaune parlor ta bi ta da kallo har ta durkusa kusa da ita tace "Ammi xa mu wuce" Ammi ta d'an yi shiru kafin tace "Kar ki dade Imaan, ko minti goma plss kar ki yi ba mutuncin ki bane, kina yin abinda ya kai ki ki juyo" Imaan ta d'an yi murmushi tace "Toh Ammi in sha Allah" Ammi tace "Ko xa ku dawo napep xa ku hau kin ji abinda nace koh?" Imaan tace "Toh Ammi" daga haka ta fita parlon, ta nufi part din su Maimoon, a hankali ta bude kofar ta shiga da sallama murya can kasa, Umma ce xaune parlon, sai Mujaheed dake xaune shi ma ya jinginar da kansa da kujera idonsa lumshe, Safeenah ma na xaune parlon tana taunar cingam, Umma tace "Toh ni na ta6a jin rashin lafiya haka, bari Abbansa ya shigo kila idan yyi masa magana xai yarda a dubasa, su dama likitocin nan haka suke da shegen taurin kai sai dai su duba wasu ba dai a duba su ba" Safeenah ta tabe baki tace "Wllh kuwa Hajiya, har ce min yake ba ruwana in daina sa masa ido, Toh ya baxan sa ido ba mijina ba lafiya, ko abinci bai ci fa Umma sai dai coffee da tea mun fi sati a haka" Umma ta rike ha6a tace "Ba lafiya kuwa, bari Abba ya shigo wannan ai ba yi bane" Imaan da ta sunkuyar da kanta ta nufi stairs tace "Ina yinin ku" babu wanda ya tanka ta a parlon har ta wuce sama, Umma ta kalli Safeenah, Safeenah tayi wani murmushi tana kas kas da cingam, Mujaheed tunda ya ji muryarta ya bude ido, ba a dau lkci ba Imaan ta sakko tare da Maimoon dake sanye da hijab ita ma har kasa, suna shigowa parlor Umma ta bi su da kallo, Maimoon tace "Sai mun dawo Umma" Umma tace "Yauwa" Imaan dai bata juyo ba har ta fita, Maimoon ma ta fita, Mikewa Mujaheed yyi yana kallon Umma yace "Bari in je in gaida Inna in dawo yanxu" Safeenah ta mike tace "Ehh bari mu je Umma yanxu xan dawo sai mu fita kasuwan" wani kallo Mujaheed ya dinga mata fuska daure yace "Da can baki san xa ki part din Inna ba sai da nace xan je??" Safeenah ta tabe baki ta nufi kofa tana gyara mayafin jikinta ya bi ta da kallo, imaan da Maimoon na isa bakin titi suka tsayar da adaidaita, Imaan na kallon Maimoon tace "Wllh ban san me yasa gabana ke faduwa ba tun daxu Maimoon" Maimoon tace "Haba dai, to ki dinga addu'a" Imaan tace "Ehh Ina yi" daga haka ta kalli mai adaidaitan da suka tsayar....
*Imaan isn't for free* it's 300 via
Fcmb 3276052019 Hauwa Bello Jiddah
Then u show ur evidence of payment via my WhatsApp number
07087865788
66.....
A hanya imaan ta sa mai adaidaitan ya tsaya gun masu fruits ta siya fruits kusan kala hudu sannan suka koma adaidaitan, Tafiyar kusan minti ashirin suka yi suka isa wani babban hospital wanda kai kana gani kasan na masu hali ne, sauka suka yi a adaidaitan kafin Imaan ta basa kudi daga cikin jakarta Maimoon ta basa, hakan yasa Imaan ta ciro wayarta kawai ta shiga kiran layin Mariya, ba a dau lkci ba Mariya ta daga, Imaan tace "Muna waje" Mariya tace "Ohk to gani xan fito yanxu" Imaan ta mayar da wayar jakarta suka shiga haraban hospital din, ba a dau lkci ba Mariya ta fito ta nufo su tana murmushi suka gaisa da fara'a suna tambayarta me jiki, Mariya tace "Da sauki sosai, mu shiga ciki" bin bayanta suka yi har xuwa special ward din da aka kwantar da step sis din nata, da sallama suka shiga cikin babban ward din mai dauke da gado daya sai kujeru da karamin Tv na bango, ga labulaye a duk windows din, gadon ma kadai dake dakin ya isa ya bayyana cewa ward din na special people ne, Mahaifiyar Sadeeq Hajiya Khadijah ce xaune saman kujera, sai Aunty da frnd din Mum din Sadeeq da kanwarta, Aisha kanwar Sadeeq na kwance saman gadon tana bacci an sa mata drip, sai autar su Sadeeq din dake tsaye hannunta rike da incense da ashana, Imaan ta sunkuyar da kai ta karasa cikin dakin da ladabi ta gaida su, Hajiya Khadijah ta amsa tana kallonta, Aunty da sauran mutanen ward din ma duk suka amsa, Aunty na nuna masu kujera tace "Toh ku xauna" Maimoon ce ya fara xama, Imaan kuwa sai da sister din mahaifiyar sadeeq ta sake maimaita mata ta xauna sannan ta xauna har sannan kanta na kasa, Mariya na murmushi tana kallon stepmother dinta tace "Mummy ita ce budurwar ya sadeeq warce xai aura fa...." Mummy na kallon Imaan da kyau tace "Wannan ba warce ku ka yi sauka tare bane kwanaki har muka yi hotuna" Mariya tayi dariya tace "Ita ce Mummy ashe dai xa ki gane ta" Aunty dai sai murmushi take tana kallon Imaan da ta kasa dago kai gaba daya she was uncomfortable ba kadan ba, Mummy ta d'an yi murmushi tace "Toh Maa sha Allah, Allah ya sanya albarka..." Mariya tace "Ameen, amma fa tun kafin saukan suke tare Mummy" Mummy tace "Toh maa sha Allah, hakan yyi kyau" Aunty na kallon Imaan tace "Ya su mamanku" a hankali tace "Tana gaishe ku" Aunty tace "Toh mun gode Allah maku albarka" duk suka amsa da "Ameen" a hankali Imaan ta dago kai tana bin ward din da kallo jin numfashinta na d'an tsarkewa, kanwar Sadeeq ta gani xaune chair din dake kusa da wanda ta xauna hannunta rike da incense har stick biyu ta kunna, Imaan ta kauda kai, sai kuma cikin dubara ta dan rufe hancinta da hijab din jikinta, Lkci daya Maimoon ta lura da hakan, ta taba ta murya can kasa tace "kiyi masu sallama mu wuce kawai" kasa cewa komai Imaan tayi, su Aunty dai hiransu kawai suka ci gaba da yi, Maimoon ta mike tana kallonsu tace "Toh mummy xa mu koma, ga wannan a ba mara lafiya, Allah ya bata lafiya" tana magana tana ajiye ledan hannunta a table, Aunty tace "Har xa ku tafi, to mun gode Allah ya saka da alkhairi" Mummy tace "Toh mun gode, ku gaida gida da mutanen gida" tuni Maimoon ta kama hannun Imaan tana amsa masu da Ameen, Mummy na kallon Imaan da murmushi tace "Toh ya sunan naki?" Maimoon tace "Fatima Imaan" Imaan ta warce hannunta daga rikon da Maimoon ta yi mata ta nufi kofa da sauri dai dai lkcn da aka bude kofar ward din Sadeeq ya shigo, bata kai ga fita ba ta durkushe bakin kofa ta fara gasping for air tana tari, Mariya da Maimoon suka nufeta da sauri, Su Aunty da Mummy ma duk suka mike suna salati suka nufeta, Sadeeq ya xura wayarsa aljihu ya durkusa kusa da ita ya dagota yana kallonta yace "Subhanallah, Imaan are you okay..." Mariya ta kashe incense din hannun Step sis dinta, a nan kuma duk suka dago musabbabin tashin Asthma din nata, ba karamin tausayi Imaan xata baka ba ganin yanda take struggling da numfashin nata a kasa, gaba daya su Mummy da Aunty da mutanen dake ward din duk suka rikice, Maimoon ta durkusa ta cire jakarta dake rataye shoulder dinta ta bude da sauri tana bincika ciki ko akwai inhaler amma taga babu, ganin haka Sadeeq ya daga ta ya fitar da ita daga ward din, Aunty ta bi bayansa ita ma hankali tashe Maimoon da Mariya ma suka fita, cike da damuwa Mummy tace "Ai ba a san she is asthmatic ba, da Suhaila bata kunna turaren ba, kuma duk sai suka yi shiru basu ce komai ba" Kanwar Mummy tace "Wllh kuwa, irin haka ai magana xa su yi, gashi an ja mata wahala yanxu" Kawar Mummy tace "Ikon Allah shi kuma Sadeeq ana neman mai lafiya ya jajibo ma kansa ciwo Allah na tuba, dubi fa d'an hayakin da ya tada Asthma ni fatima Allah na tuba, kenan wannan dai ko shara bata yi balle aje ga soye soye a kitchen, don in dai wannan hayakin xai iya tada Asthma to fa babu abinda baxai tayar ba, Toh Allah dai ya kyauta, Allah kuma ya bata lafiya" Mummy dai bata ce komai ba haka kanwarta da ta mike ta bi bayansu Aunty. Sadeeq na xaune gefen Imaan dake kwance daya daga ward din hospital din, ban da juye juye babu abinda take yi har sannan da kyar take numfashi, Aunty sai sannu take mata tana kallonta cike da tausayinta, Mummy dai na tsaye jikin window ta rungume hannu tana kallonta ita ma, Mariya har da d'an hawayenta, Maimoon na kusa da sadeeq ta kama hannunta tana tofa mata addu'a a hankali, wani likita ne ya shigo ward din yana kallon Imaan yace "Sit upright now" Sadeeq ya mike don ta samu ta tashi xaune, da taimakon Maimoon ta xauna, likitan yace "How are you feeling now" Bata iya tace komai ba, A hankali Sadeeq yace "She said her chest..." Murmushi likitan yyi ya dafa Sadeeq yace "Anya kuwa Dr idan emergency ya tashi gidan ku cikin dare xaka iya ta6uka abun kirki?" Aunty ta ta6e baki tace "Haka nan yake wllh Dr, ni ban ta6a ganin likita haka ba, gaba daya mance cewa shi likita ne yake in a situation like this" Dr din ya d'an yi dariya yace "Gaskiya ne..." Ya maida dubansa gun Imaan da ta hade kanta da pillow yace "Amma an ta6a maki allura idan Asthma din ki ya tashi ba inhaler a kusa?" Bata tare da ta dago ba ta gyada masa kai da kyar, Yace "Toh Allah ya sauke, xai daina in sha Allah mun baki magani ai... Allah ya baki lafiya" Ita dai bata ce komai ba, likitan na kallon Sadeeq yace "Nan da few hours xa a sake shigowa duba ta Dr... Allah ya tsare, sai a dinga kiyayewa" Sadeeq ya d'an yi murmushi yace "In sha Allah" daga haka likitan ya fita yana kara gaida su Mummy, Sadeeq ya duka yana kallon Imaan, murya can kasa yace "Sorry dear" ita dai bata ce komai ba, yace "Toh kwanta da kyau" sai a sannan ta dago kanta a hankali ta kwanta tana sauke numfashi a hankali, Mummy dai sai kallonta take haka ma Aunty, can Mummy tace "Toh Allah ya sauke, bari in koma daya ward din" daga haka ta fita, Aunty ta ja kujera ta xauna, nan da nan bacci ya dauke Imaan. Maimoon dake xaune kan kujera tare da Mariya suna kallon Imaan ta fiddo wayar Imaan dake ring a jaka, number Ammi ta gani a screen, ta daga ta kai kunne tayi sallama murya can kasa, a hankali Ammi tace "Imaan din fa Maimoon?" Maimoon tace "Wlh Ammi ta sami attack ne a hospital din, amma da sauki yanxu tana bacci ma" Mahaifiyar Mariya dake ward din har sannan tana duban Maimoon tace "Kawo wayar" Mikewa Maimoon tayi ta tafi ta kai mata wayar, bayan sun gaisa Aunty tayi mata bayanin abinda ake ciki tace "Amma da sauki Alhmdllh don har tayi bacci, xuwa anjima in sha Allah xa a taho da su gida" Ammi tace "Toh maa sha Allah, an gode sosai, Allah ya saka da alkhairi" Aunty tace "A'a ba godiya Hajiya, mu ma mun gode" daga haka suka yi sallama Aunty ta mika ma Maimoon wayar, kusan la'asar Sadeeq ya shigo ward din rike da ledan drugs, Maimoon da Mariya ne kadai dakin Aunty ta tafi gun su Mummy, Har ya karasa gun Imaan kallonta yake ganin yanda ta takure waje daya, ya kai hannunsa forehead dinta, sosai ya ji jikinta da xafi, ta bude idonta da suka kada tana kallonsa, lips dinta ma yyi ja sosai, dukawa yyi da damuwa yace "Are you okay imaan, har yanxu kirjin na maki ciwo ne" kokarin tashi xaune ta shiga yi da kyar tana dafa bayanta, ya kama hannunta ya taimaka mata ta tashi, ganin yanda ta rufe ido yace "Ina ke maki ciwo??" Murya can kasa tace "I am feeling internal heat, kuma Ina jin sanyi, my back is aching" Shiru yyi yana kallonta cike da tausayi, can ya juya ya fita suka dawo tare da likita, a dakin ya tadda Mummy xata wuce gida ta dawo anjima shine ta shigo yi masu sallama, tana tsaye kan Imaan ganin yanayinta tana kallonta tace "Wani abun na damun ki ne kuma? Ko kina jin ciwo a wani waje ne?" Imaan ta girgixa mata kai da kyar bata ce komai ba, likitan ya karasa ya kai hannu jikinta yana kallonta yace "Me kike ji a jikin ki?" Imaan ta girgixa masa kai a hankali hawaye cike idonta tace "Kawai ina son xan wuce gida" Sadeeq yace "Noo ki fada masa inda ke maki ciwo" da kyar tace "Joint pain, kuma Ina jin xafi a jikina...." Likitan ya kai hannu forehead dinta yana kallonta, yace "Yana maki haka ne?" Kai ta gyada masa, yana kallon kwayar idonta ya d'an yi shiru sai kuma ya kalli Sadeeq yace "Is she a sickled cell patient?" A hankali Sadeeq ya girgixa masa kai yace "She is only carrying the trait" Likitan yace "Wani drugs kike sha a gida?" Cike da karfin hali tace "Suna da yawa" likitan yace "Did you know their names?" Sadeeq yace "I will get drugs for her now, amma ayi mata allura" daga haka ya juya ya fita ward din. Aunty ce ta sakko parlor sanye da hijab hannunta rike da purse, ta kalli Mujaheed tana amsa gaisuwar da yake mata a parlorn sannan ta kalli Umma tace "Xan fita sai na dawo Hajiya" Umma tace "Ina kuma xa ki da magariba" Aunty tace "Xan je dubiya asibiti ne" da mamaki Umma tace "Waye ba lafiya?" Aunty tace "Baki san su ba" Dai dai nan Abba ya shigo parlon yana kallon Aunty yace "Ba ku tafi ba kenan" Aunty tace "Ehh yanxu xa mu fita" Abba yace "Xuwa anjima idan anyi isha xan leka asibitin" Umma na kallon Abba tace "Wai waye ba lafiya" Abba ya kalli Aunty yace "Bata sani ba ne dama?" Aunty bata tanka sa ba ta nufi kofa, Abba ya girgixa kai yace "Imaan ce suka je duba kanwar yaron nan dake nemanta a asibiti shine Asthma dinta ya tashi, ita ma dai tana asibitin yanxu" Kallonsa kawai Mujaheed yake ko kiftawa babu, Umma ta saki salati tana tafe hannu tace "Shine ake boye min, shi ciwon Amina ke boye min fisabilillahi? Meye amfanin xaman munafurci Alhaji, wato ita ta ji xata tafi dubata a asibitin ni kuma sai uwar yarinyar da Inna su kullace ni su xata naji xuwa ne bana son yi, toh xuciyata bai kai haka lalacewa ba, kuma nima yanxu xan shirya mu tafi, sai dai ita ta ji kunya, ban taba ganin munafuka irin Amina ba wllh, duk ita ke hada ni da Aisha na lura" Shi dai Abba ko tanka ta bai