Showing 300001 words to 303000 words out of 303099 words

Chapter 101 - Imaan Book 1 Hausa Novel Complete

17 Dec 2024

1670

karasa gun Mujaheed yana kallonsa ta glass din idonsa ya mika masa hannu hade da masa sallama cikin cool voice dinsa, Mujaheed ya mika masa nasa hannun yana mayar masa da murmushin, suka gaisa sannan Sadeeq ya koma inda yake tsaye, packaging masa burger da ya siya aka yi ya bar eatry din Mujaheed ya bi sa da ido, Yana isa gun motarsa suka kara ido hudu da Imaan da sauri ta dauke kanta xuciyarta na bugawa, ya bude motarsa ya shiga ya tada ya bar haraban eatry din, wasu hawaye ta dinga ji suna xubo mata bata san dalili ba, ta jinginar da kanta da kujeran mota tana jin kamar ta fashe da kuka ko xata ji dadi a ranta. A haka Mujaheed ya dawo ya sameta, tun da ya kalleta sau daya ya dauke kai ya tada motar ya bar eatry din, har suka isa gida kuma bai ce mata komai ba yyi parking ya bude motar ya dau ledan abubuwan da ya siya ya fita, ita dai bin sa kawai tayi da kallo tana goge hawayen idonta, har ya tafi kuma ya dawo ya bude mata door din motar, k'in fitowa tayi ya juya yyi wucewarsa, a hankali ta sakko daga motar ta rufe sannan ta wuce ciki a sanyaye, kwanciya tayi kan kujera gaba daya ta rasa me ke mata dadi, bayan kusan minti talatin Mujaheed ya sakko ya kunna Tv ya xauna parlon, Juya masa baya Imaan tayi ta hade rai ya kalleta ta gefen ido ya ci gaba da kallonsa, Har aka yi azahar Imaan taki yarda magana ya hada ta da Mujaheed, tana ta kwance parlor ta juya baya kan kujera, sau biyu yana ce mata ta tashi ta dau Ice-cream dinta xai yi melting tayi masa shiru, shi ma kuma bai sake ce mata komai ba, jin ya fita masallaci ta mike a hankali ta wuce dakinta taga har ya canxa xanin gado ya gyara dakin, bathroom ta wuce ta dauro alwala ta fito ta shimfida darduma, tana idar da sllh ta sauka xuwa kitchen ta ciro manyan indomie biyu a kwali, ta wanke tukunya ta kunna gas ta daura ruwa, tana gama dafa indomien ta juye a babban plate ta fito, xaune ta ga Mujaheed a parlor ya bi ta da ido, ta hade rai ta wuce sama, ta cinye indomien tass sannan ta kwanta nan da nan bacci ya dauketa. Har dare Imaan bata sakko ba duk da yunwa da take ji sosai, tana fitowa wanka bayan Isha taga ledan abinci ajiye a dakin, riga kawai ta xura bayan ta goge jiki ta xauna ta bude ledan taga jollof ne har takeway biyu ko wanne da babban kaza a ciki sai drink da bottle water. Sai da ta kusa cinye gaba daya sannan ta mike da kyar ta tafi bathroom ta wanke bakinta ta fito ta feshe jikinta da turare ta kashe wuta ta kwanta ta lumshe ido, Bayan kusan awa daya aka bude kofar dakin Mujaheed ya shigo, tana ji taki juyowa balle ta bude ido, ya karaso kan gadon ya xauna gefenta murya can kasa yace "Imaan" Shiru tayi bata ce komai ba ya hau saman gadon ya kwanta gefenta yace "Tell me what ur problem is plss" a takaice tace "I don't have any problem plss" dagota yayi, ta fashe masa da kuka, shiru yyi yana kallonta, bayan few seconds a hankali yace "Baki son xaman mu tare har yanxu koh Imaan? To shkkn har yanxu deal dinmu na nan, give me five kids that look like you, sae in sauwake maki ki koma gun wanda kika gani daxu kike shareni, but let me tell u this, I won't tolerate ki dinga min shiru sbda kin ga tsohon saurayin ki, after all ba ni na hanasa auren ki ba ai, I was home on that very day aka kirani na xo gida aka gaya min an aura min ke..." mikewa xaune imaan tayi lkci daya hawaye ya kawo idonta tace "Ehh gaskiya ne baka sani ba aka aura maka ni, but don't forget kaddara ya hana Sadeeq aurena nasan shi ma ba da son ransa ba, kuma ni nasan har in bar duniya baxan ta6a samun masoyi na gaskiya irinsa ba, baxan samu me sona xuciya daya kamar Sadeeq ba, nasan kuma da wuya moment din mu tare yayi fading a xuciyata da wuri, I will never forget our...." Rikota Mujaheed yyi cikin tsawa yace "Baki da hankali ko Imaan? Da auren nawa a kanki kike min wannan maganan, da auren nawa kike ce min baxa ki manta da Sadeeq ba, are you out of ur senses??" Yana huci ya kare maganar, ta fashe da kuka tace "Why will I forget someone that always say he loves me innocently anytime, anywhere?? don me xan mance wanda baya shakkar furta min kalmar so, he always tell me he loves me not he cares, I pray Allah forgive me amma ni nasan da wuya in samu so irin wanda Sadeeq yayi min a rayuwa kuma..." shiru Mujaheed yayi yana kallonta da idanuwansa da suka sauya launi, ta goge idonta ta juya masa baya ta kwanta tana shessheka, Mujaheed ya jinginar da kansa da gado ya lumshe ido, bayan wani lkci ya bude yana kallonta, dawowa yyi kusa da ita a hankali ya kwanta ya jawota jikinsa murya can kasa yace "Imaan are you still pretending you don't know I love you?" Jin tayi shiru ya lumshe ido cikin sanyin murya yace "Imaan tun baki san kanki ba nake sonki... son da ni kaina ban san irinsa ba, I have loved you from the beginning and I have always dreamt of living with you as my wife, the mother of my kids till eternity, Imaan nasan kinsan Ina son ki, son da duk duniya bayan iyayenki babu mai maki irin sa, baki min adalci ba idan kika ce min baki sani ba don nasan kin sani you are only playing with my intelligence thinking babu aure tsakaninmu kamar yanda kika sa ma kanki wannan tunanin, me yasa baki ta6a xama kinyi naxarin me yasa duk cikin siblings dina nafi damuwa da lamarin ki ba, me yasa baki yi tunanin dalilin da yasa na mayar dake favourite dina ba, nasan kin san komai Imaan, shekaru biyu da suka gabata Umma ce ta xama barrier tsakaninmu kika ga na daina kula ki amma ba wai a son raina ba, sai dai duk da haka kullum kina rai na, kuma duk ranan da ban ganki ba I will be restless, are you thinking saboda Inna nake tafiya part dinta in xauna a lkcn? Kina tunanin sbda ita nake xuwa bangarenta? I am always there because of you Imaan, Ina xuwa ne don kawai in ganki in tabbatar you are okay, I love you tun baki san kanki ba Imaan, wllh son da nake maki Ina ga na Ammi kadai ne xai fi nawa, da na rasa ki Imaan da ban san halin da xan shiga ba duk da a lkcn na ma cire rai da ke, ban ta6a xaton xaki xama tawa ba all of a sudden, Daren da na fallasa maki sirrin xuciyata ta yanda nake tunanin xaki fahimta sai kika mayar da ni mahaukaci, kika nuna sam baki gane abinda nake nufi ba baki gane inda na dosa ba kuma ni nasan kin gane Imaan, it's just that you are soo good at pretending tun kina 'yar karama, you are perfect in that...." Jin har sannan ta ki cewa komai yasa mujaheed ya leka fuskarta a hankali, murmushi yaga tana yi, suna hada ido cikin duhun tayi saurin rufe fuskarta cike da shagwaba tace "Ni bana soo Yayaa" ya lumshe ido ya rungumeta sosai yace "Plss tell me meyasa dinga wasa da hankalina kina pretending all those time?" Murya can kasa tace "Because you are also pretending, kuma kana da girman kai, you too big to tell me kana so na" xaro ido yayi yana kallonta bai san lkcn da yyi dariya ba yace "In gaya maki ina sonki ki daina kulani Imaan? komai fa sai kice Yaya ne..." Ta shige jikinsa tace "Toh ni ban ta6a ganin inda Yaya xai ce xai auri kanwarsa ba sai a kanka" Yana murmushi ya shafa cikinta yace "Gashi kin gani kuwa, har da result..." turo baki tayi tace "Kyaleni joor" ya lumshe ido yana shakan kamshin gashinta, a hankali tace "Toh yau sai ka gaya min inda ka kai min wayar da Sadeeq ya siya min" Yana murmushi sosai yace "Yana can gida, idan na koma xan kai ma Inna ta dinga waya da shi idan xata iya" Ta dago kai tana kallonsa tace "Ai nasan kai ka dauke dama wllh" hade bakinsa yyi da nata... a wannan daren kamar wancan daren da ya xuba mata pill a drink, duk sai da Mujaheed ya fallasa ma Imaan gaba daya sirrin xuciyarsa da ta riga ta sani tun ba yau ba take kakkaucewa, Ita ma kuma ta basa hadin kai dari bisa dari fiye da xaton sa, a daren ita ma kuma ta bude baki tace "I know you are, and will always be the best for me yayana, nima ina sonka, Ina kuma alfahari da kansancewar ka mijina"
5 years later.....
Imaan ce tsaye bedroom din Umma gaban mirror tana gyara Hijab dinta, Umma ta gama saka ma wani little handsome dake tsaye gabanta yana mata surutu takalminsa, komai nasa sak na Mujaheed kamar yyi kaki, babu abinda d'an yaron ya mance na uban nasa, Umma dai sai kallonsa take tana murmushi don hatta muryarsa kamar Mujaheed dinta yana karami, tana rike da hannunsa ta nufi kofa jin horn din mota a compound tace "Kiyi sauri tunda ya fara horn Imaan" fesa turare Imaan tayi ta gyara fuskarta sama sama ta bi bayan Umma da sauri, Mujaheed dake xaune mota rungume da little sister din Musaddeeq ya fito motar yana kallon Imaan yace "I told you it's late already kar mu yi missing flight..." Umma ta hararesa tace "Tunda barin kasar xa ku yi ba.." murmushi kawai yayi ya shafa kansa, Mai aikin Umma ta iso wajen da jakan Imaan da kids dinta ta saka a booth, ta koma ta dauko wani jakan ta saka a booth tana kallon Imaan tace "Mum Ilham Allah ya kiyaye hanya" Imaan na murmushi tace "Toh Aunty faiza sai mun sake dawowa" Umma na kallon Imaan tace "Inji baku mance komai ba dai" Imaan tace "Idan ma mun manta Umma wani lkcn sai mu dauka idan mun dawo" Umma ta dau Musaddeeq tana kallonsa kafin tace komai ua manna mata kiss a goshinta yana murmushi yace "We are going to miss you granny" Dariya tayi tace "I will miss you more sweetheart ka gayar da old woman da grandpa and grandma a gida ka ji?" Gyada mata kai yayi ta sa shi back seat, ta amshi Ilham dake hannun Mujaheed tace "Teemah will be staying with me" Mika ma imaan hannu yarinyar tayi da sauri tana 6ata fuska xata yi kuka, imaan tayi dariya tace "Baxa ki xauna gun granny ba..." Umma ta saka ta cikin mota tana dariya tace "Allah ya kiyaye hanya, a gaida kowa da kowa a kaduna" Driver ne ya taho wucewa da su airport din, Mujaheed ya shiga motar bayan ya kara yi ma mahaifiyarsa sallama Imaan ma tayi mata sallama sannan suka bar gidan. Satin Imaan biyu kenan a kano wajen Umma da kids dinta, jiya Mujaheed ya taho daga kaduna mayar da su gida, Shekaru uku da suka wuce Umma ta koma kano da xama gaba daya, yanxu fita take Dubai duk bayan wani lkci, business take sosai wanda cikin kankanin lkci ta fara tara abun duniya bbu abinda ta rasa, Rahma kadai ce gabanta har lkcn bata yi aure ba tana karatu amma Ummi tayi aure da Maimoon 2 years back. Cikin lkci kadan suka shigo garin kaduna a flight, duk inda Mujaheed ya bi da little Ilham mai sunan Inna sai an tanka ta don kyakkyawa ce sosai yarinyar gashi kwata kwata bata son mutane, Ammi kadai take makale ma don har suka gama xama kano bata wani yadda da Umma, Suna fitowa daga cikin airport kamar ance Imaan ta waiga ta ga Sadeeq yana jan trolley yana danna waya da alama saukansa kenan kasar don ba waje daya suka fito ba, da sauri ta dauke kai don bai ganta ba, Mujaheed dai na waya yana rungume da Ilham, Ita kuma Imaan tana tafe tana jan trolley Musaddeeq na rike da hijab dinta a gefenta, tuntube yayi da trolley din hannunta ya fadi wanda hakan ya ja hankalin mutane da yawa ciki har da Sadeeq, bai yi kuka ba yaron Imaan ta sake jakan hannunta ta dago sa da sauri tana ce masa sannu, Kallonsu Sadeeq ya dinga yi, bai san lkcn da yace "Imaan" juyawa tayi ta kallesa da sauri, Mujaheed ma ya juya da sauri jin an kira sunanta, Sadeeq ya nufeta yana murmushi yace "Waow is this ur son Imaan??" ta kirkiri murmushi ta gyada masa kai, daukan Musaddeeq yayi ya rungumesa ya manna masa kiss a goshinsa yace "He is soo cute, ya sunansa??" Tana murmushi tace "He is Abubakar Sadeeq" Sadeeq ya kara rungumesa yace "Ohhh takwara na kenan, where is his dad?" sai a lkcn ya ga Mujaheed dake kallonsu shi ma, Sadeeq ya nufesa still smiling ya basa hannu, nan suka gaisa yana kallon Ilham ya ja Cheeks dinta yace "Waow little imaan kenan" murmushi kawai Mujaheed yyi yana kallonsa, Sadeeq yace "It's been long, over five years yanxu...." mujaheed yace "Sure, where are you coming from" Sadeeq yace "I am coming from Uk now, ya Kaka?" Mujaheed yace "Tana lafiya lau" Sadeeq ya shafa kai yace "Xan dai je in gaisheta in sha Allah Maryam ta bani sako in kawo mata, you know we are not far from each other a can UK, driver ya xo daukan ku ne?" Mujaheed yace "Not at all, xa mu hau taxi" Sadeeq yace "Driver ya taho min da mota yanxu, muje sai mu yi dropping din ku" Har kofar gida Sadeeq ya ajiye su bayan ya siya ma Musaddeeq bindiga na wasan yara a hanya, Ilham kuma ya siya mata babban doll, Imaan na kallonsa tana murmushi tace "Baxa a hadani da Madam muyi xumunci ba?" Shafa kai Sadeeq yyi yace "Madam... tukunna dai in sha Allah" Imaan ta xaro ido tana kallonsa da mamaki, yace "Ko xa ki sama min madam din?" Dariya tayi ta sauka motar tace "Ni kuma" Sadeeq yyi murmushi yana kallon Mujaheed yace "Ae gaskiya ne, ko in jira little Imaan kawai?" dariya Mujaheed yyi yace "Lkci dai na ta wucewa Sadeeq, try and settle down" Sadeeq yyi murmushi yace "In sha Allah, A gayar min da Kaka soon xan shigo" A haka suka rabu da Sadeeq, Tun da suka shiga compound duk da Ammi dake tsaye tana shanya Musaddeeq bai bi ta kanta ba ya nufi part din Inna da gudu yana kwala mata kira yana cewa "Old womannn, old womannn, where are you" Ammi ta bi sa da kallo tana murmushi, Imaan ta sauke Ilham ta nufi Ammi da gudu tana murmushi dimples dinta na lotsawa Ammi ta dauketa ta rungumeta, Imaan ta karasa ta rungume Amminta tayi mata kiss a goshi tana murmushi a hankali tace "Nayi missing dinki Ammina" Inna da ta fito da duk kwanukan kitchen dinta da tukwane bakin pampo xata wanke wai sun yi k'ura ta daga kai ganin Musaddeeq tace "Waye kuma wannan?" ya kyalkyale da dariya ya saita mata bindiga har da kulle ido daya, xaro ido tayi tana kallon bindigan da yayi kama da na gaske daga nisa, da gudu ta shige parlonta jikinta na rawa tana cewa "Innalillahi wa inna ilaihi raji'un, Mujaheed ya haifi jaraba" Mujaheed da tahowansa kenan ya dinga dariya yana kallon son din nasa da ya bi bayan Inna da gudu yana cewa "I missed you old woman...."


*Ina mai sake jaddada cewar littafin Imaan ba free bane na kudi ne* settle ur debt it's just

it's 300 via
Fcmb 3276052019 Hauwa Bello Jiddah

07087865788

I want to draw the attention of those posting my books that are not free on Facebook, ku ci gaba xa mu hadu gaban ubangiji in sha Allah...

_Toh Alhamdulillah Alhamdulillah Alhamdulillah😃 a nan na kawo karshen littafina me taken *Imaan* kurakuran da nayi a ciki Allah ubangiji ya yafe min, darussukan dake ciki kuma Allah ubangiji ya sa mu amfana da shi_
Na sadaukar da littafin nan xuwa ga beloved brother na Yahya M Bello, Allah ubangiji ya raya min kai little bro, ya albarkaci rayuwar ka ya sa ka xamo apple of our parent eyes... Gaisuwa ta musamman xuwa ga mahaifiyata Hajiya Hajarah, she is my first, my world, my role model, my everything Allah ya bar min ke Hajjaju Yaya, Allah ya kara maki lafiya ya karo arxiki mai albarka, my siblings Ahmad, Maryam, Fatima, Baby, Haiydar, Papi, Ilham, Fadil, sudais, Jamcy, Humairah, Aneesah, Mujaheed, Big Ilham, Yusuf, small Baby, And my takwara Khaleesat, Allah ya albarkace ku gaba daya, Ina son ku har raina, Small Mum Aunty Rukky thanks for the encouragement from the beginning of this book till the end Allah bar min ke ya daukaka ki, my Aunty Didi ur daughter jiddo is greeting with respect Allah ya ubangiji ya jibanci lamarrukan ki, Hajiya Inna Allah ubangiji ya bar mana ke mu ga me taka 'yan jikokin ki a duniya, Muna alfahari da kasancewar ki grandma dinmu. Hajiya Sadiya Chamo😉 Hafsat Oum Ilham, Ummu Zainab, Anty Ay(Ummu Lailah) Hajiya Asabe, Hajiya Fauziyya fiji, Mama Dutse, Khaleesat Haiydar na gaishe ku gaba daya with respect, Allah ubangiji ya raya 'yan kannena ya albarkace su, All the members na payment groups dina guda bakwai da nayi creating for the book Imaan, Ina gaisheku Ina maku fatan alkhairi, Ina alfahari da ku for patronizing me, Allah ya bar xumunci ya kara maku budi, members na murmushin novels da Seembieluv groups ina godiya da kauna, and finally my fans... words


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login