Showing 39001 words to 42000 words out of 303099 words

Chapter 14 - Imaan Book 1 Hausa Novel Complete

17 Dec 2024

1611

fito parlon jin hayaniya, ya kalli Mujaheed dake tsaye, ya kalli Yusuf dake tsaye stairs yana kallon su shi ma sannan ya kalli su Umma yace "Me ke faruwa nan?" Rai bace Umma tace "Ka ja ma matar ka kunne Alhaji ta fita harkata kada abu ya bace tsakanin ni da ita a gidan nan, ta cire ido kan d'a na, ta kuma yi ta kanta..." Abba ya dakatar da ita yace "I asked what happened kina min warning madam" Anty ta tabe baki tace "D'an ta da ka aika yanxu... ta hana shi xuwa saboda isa da gadara, to ni kuma bana gani inyi shiru...." Abba ya kalli Mujaheed da ya kasa dagowa ya mika masa hannu yace "Bani makullin motar...." Da kyar Mujaheed ya dago yana kallonsa sannan ya kalli Umma, ta watsa masa wani kallo alamar ya basa, a hankali Mujaheed yace "Abba ai bance fa baxan je ba" yace "Eh baka ce ba, amma ba ni" Mika masa makullin Mujaheed yayi, Abba ya kalli Yusuf yace "Here, ka tafi ka ajiye Imaan a makaranta" Yusuf ya karasa saukowa stairs da yake tsaye ya amshi makullin sannan ya nufi kofa ya fita, Juyawa Abba yyi ya koma parlonsa, Mujaheed ya wuce sama a sanyaye, Anty ta tabe baki ta wuce saman ita ma, wani ajiyar xuciya Umma ta sauke ta koma ta xauna ranta fess. Sai bayan da suka bar gidan Imaan ta kalli Yusuf tace "Ya Yusuf Umma ce tace yaya kar ya kai ni koh?" Yusuf na driving yyi murmushi yace "Toh dama ya xa ayi ta bari ya kai ki?? salon ku je ya d'an rankwashe ki ki dawo kina mana ihu kina kuka" xaro ido Imaan tayi tana kallonsa, Ya ki kallonta sai murmushi yake, ta hade rai tace "Toh an doki mutum kuma baxai yi kuka ba" Yusuf yace "A'a xai yi kuka abunsa" Turo baki tayi bata ce komai ba, shi ma bai kuma cewa komai ba har ya iso islamiyyarsu ya tsaya bakin gate, ya kalleta yace "Kin fa yi latti sosai" tace "Ae xa su ga idona kuma cewa xanyi bani da lafiya, dama ban da lafiyan" daga haka ta bude motar ta fita, D'aga masa hannu tayi, yayi mata murmushi ta shiga cikin makarantar. Imaan na dawowa islamiyya karfe sha biyu kashegari lahadi ta fara shirin tafiya gidan gwaggonta wato Mahaifiyar Ammi dake unguwar rimi, Tun da ta fito daki Ammi dake xaune parlor ke kallonta, tsadadden atamfa ne jikinta sai dan kunnenta na gwal, babu abinda ke fuskarta banda eye pencil da chappete da ta goga a lips, sosai tayi kyau duk da haka, da mamaki Ammi tace "Ina xa ki?" Imaan ta xauna kusa da ita tace "Gidan Gwaggwo mana Ammi" Ammi ta mata wani kallo tace "Kin gaya ma Daddy ne?" Ta marairaice tace "Daddy baxai hanani ba fa na sani" Ammi tace "Baxa fa ki fita gidan nan ba sai da saninsa don ba ruwana" tashi Imaan tayi kamar xata yi kuka ta shiga dakinta kiran Abba, wayarta da bata damuwa da ta dauko ta yi dialing number sa, bayan wani lkci ya dauka, ta amsa sallamarsa sannan ta gaishesa, yace "Ya kike Imaan" tace "Lafiya Daddy ya aiki?" Yace "Alhmdllh, har kun dawo islamiyyar?" Tace "Ehh daddy dama gidan gwaggwo nake son in je in gaisheta shine Ammi tace sai na gaya maka" yace "Ae kina da islamiyya da yamma mamana" kamar xata yi kuka tace "Ae kafin karfe hudu xan dawo" yayi shiru kafin yace "Toh waye xai kai ki?" Tace "Ni kadai Daddy ai ina xuwa ni kadai" yace "Kai ma Ammin ta ki waya" fita dakin tayi ta kai ma Ammi waya, Ammi ta amsa ta kai kunne, daddy yace "Why not drop her plss bana son tana fita ita kadai" Ammi tace "Sai kace wata yar shekara goma yallabai, she do go out her self...." Daddy yace "Toh minti nawa ne kin ajiyeta ki dawo" Ammi tace "I told u for the past two month ban shiga motar nan ba, sai dai ta bari next week mu je tare idan Allah ya yarda, ina da aikin da xan yi yanxu, ko jiya fa naje gidan gobe ma xan je, yau kuma sai na kai Imaan?" Daddy yace "Bata wayar" Ammi ta mika mata, daddy yace "Mamana ki bari next week ku je da Ammin ki idan Allah ya kai mu" imaan ta fashe da kuka tace "Bayan na shirya daddy, na fa san hanya ba yau xan fara xuwa ni kadai ba" Daddy ya dan yi shiru kafin yace "Shikenan to kije, but go with ur nose mask, and inhaler, Allah ya kiyaye hanya" tana goge idonta a hankali tace "Toh daddy na gode" Ammi ta shiga kitchen ta dauko dambun naman da tayi ma mahaifiyarta tace "Ki kai ma gwagggo ina gaisheta sai na xo goben" Imaan ta amsa tace "Toh" dubu Biyu Ammi ta bata ta bar gidan bayan tasa gogaggen Hijab dinta har kasa, a dai daita Imaan ta samu da xai kai ta har gidan, bayan sun isa ta sauka ta basa kudinsa sannan ta shiga gate din gidan, babban gida ne sosai da su Ammi suka siya ma mahaifiyar tasu, Ammi ce ta biyu gun gwaggwo bayan babban yayansu Umar, sai maxa biyu da mace daya Anty Murja, duk sun yi aure da 'ya yansu, yar Anty Murja ta biyu Halima ce ke gaban gwaggwo kuma ita xa ayi aurenta kwanan nan, Sosai Gwaggwo tayi murnar ganin Imaan, duk cikin jikokinta ko da bata nunawa ta fi jin Imaan har ranta, Imaan ta rungumeta cike da jin dadin ganinta ita ma, Gwaggwo tace "Kin guje ni Fatima" Imaan tace "Toh Gwaggwo kinga idan naje boko da safe da yamma muna dawowa xan wuce islamiyya, ranan asabar kuma islamiyya safe da yamma, yau ma kawai dai na taho ne kuma da wuri xan koma saboda islamiyya" Gwaggwo tace "Toh Allah ya maki albarka ya baki sa'a a karatun ki, ya Ammin ki fa?" Imaan tace "Tana gaishe ku, tace in kawo maku wannan" Gwaggwo tace "Toh nagode Allah mata albarka, fatan mutan gidanku duk suna lafiya" Imaan tace "Duk lafiya lau" Ammi tace "Mujaheed ya daina xuwa min kwata kwata yanxu yana kasar kuwa?" Imaan tace "Yana nan" Gwaggwo tace "Ikon Allah, shi kuma d'an farin fa, duk da shi baya ma gaida mutane dama" Imaan tayi dariya tace "Shi ma yana nan" Gwaggwo tace "Toh Allah maku albarka, in ji kakarku tana lafiya" Imaan ta turo baki tace "Ehh" Gwaggwo tace "Toh Allah ya kara mana lafiya, ki dauko lemo fridge ki sha" Imaan ta gyara xamanta tace "Anty Halima bata nan ne?" Gwaggwo tace "Taje kai anko" Imaan tace "Toh ni ba a ban ankon ba" Gwaggwo tace "Xa ta kai maki naki har gida tace" Imaan ta washe baki tace "Toh" mikewa tayi ta dauko malt daya ta dawo ta xauna ta fara sha tana cin dambun naman da ta kawo, Gwaggwo tace "Inji yanxu ciwon ki yana sauki sosai kamar yanda mahaifiyar ki ke gaya min idan na tambaya" Imaan tace "Ehh da sauki" Da damuwa Gwaggwo tace "Allah ubangiji ya yaye maki wannan cutar Fatima, in sha Allah xaki samu lafiya gaba daya muna nan muna gaya ma Allah" Yar dariya Imaan tayi tace "Gwaggo ya Salim yana xuwa?" Gwaggwo tace "Yauwa kwanaki yayanki Muhsin ya kawo min karar ki wai baki gaida mutane" Imaan ta hade rai ta daina cin naman da take tace "Ni kullum sai yace bana gaishesa, to ma a ina nake ganinsa balle in gaishesa" Gwaggwo tace "A'a Fatima ga wannan dai waya da ta kawo komai da sauki, ko shi kika dauka ai xa ki kirasa ku gaisa" Imaan ta turo baki tace "Toh shi ma fa ba kulani yake ba wllh" cike da damuwa Gwaggwo tace "Ni dai ku rike xumunci don Allah, ba kya ganin yanda iyayenku ke yi ne, ubansa ya sha nono ya bar ma uwarki, wllh baki da yan uwan da ya wuce su don mutan gidanku ba son ke da uwar ki suke ba duk an sa maku ido, ga kakarku fitinanna, kiyi ma kanki fada ki rike xumunci da yan uwanki na nan, duk suka xo gaisheni sai sun tambayeni ke ba Usman ba, ba Muhsin din ba, ba Salim ba ga matan su ma gaba daya, ke sai kiyi shekara baki xo nan ba baki je gidajen nasu ba shi sa bakwa hadu duk da ba laifin ki bane laifin uwar ki ce don ita ya kamata ta sa ki a hanya ta kuma sa maki ido" Imaan dai sai cin namanta take tana shan malt, sallama aka yi bakin kofa Gwaggwo ta amsa Muhsin ya shigo tare da abokinsa, Gwaggwo tace "Sannun ku da xuwa, yanxu nake xancen ka Muhsin" Muhsin yayi murmushi yana kallon Imaan da ta ki kallonsa yace "Wannan fitsararriyar ce ta xo ashe" Gwaggwo tayi dariya tana kallon abokinsa tace "Sannu da xuwa Sadeeq kwana biyu ka gujeni" murmushi yyi ya cire glass din idonsa ya karaso Inda take ya durkusa yana kallon Imaan da taki dago kai sai cin namanta take yace "Sannu Kaka ina yini" Imaan ta daga kai don muryar sounds soo familiar, Gwaggwo tace "Lafiya lau Sadeeq ya mutan gidanku? Ya kuma aiki da kujuba kujuban rayuwa" ya sauke kansa kasa yace "Alhmdllh mun gode Allah Kaka" Gwaggwo tace "Toh Allah yayi maku albarka ya kare ku sharrin makiya, ya tsare ku da tsarewarsa" a hankali yace "Ameen" ya kai idonsa kan Imaan that was so uncomfortable, Muhsin yace "Ina yini Anty Imaan" boye fuskarta tayi da kujera yace "Ke yanxu kin girma kin daina kula kowa kin mance lkcn da kike kuka sai an goya ki, kiyi ta bamu wahala muna goya ki a anguwa koh" kamar xata yi kuka tace "Ya Muhsin bana so ni yaushe nake kuka a goya ni" yayi dariya yace "Tunda kin girma kin manta ai shikenan, gashi nan ma kin daina gaida kowa" kamar xata yi kuka tace "Ya Muhsin kai ma fa ba magana kake min ba, ni da bani da lafiya ka tambayi Ammi ma, kuma ni ina dadewa ban hau whatsapp ba, wayar ma ba amfani nake son yi da shi ba" yace "Yaushe ne baki da lafiya?" Gwaggwo tace "Kai ma dai Muhsin sai kace baka san dawan garin ba, sai kayi mata addua da fatan samun lafiya" Muhsin yace "Toh Allah ya sauwake Imaan amma ai kina shan magani koh?" Ta gyada masa kai ba tare da ta dago ba, yace "Sannu lil sis" ta turo baki a hankali ba tare da ta dago ba still tace "Ina yini" ya xaro ido yace "Toh boye fuskar ta meye, Kunyata kika fara ji ko na abokina" ya fadi haka yana muna sadeeq dake kallonta, kin dagowa tayi ta kuma ki cewa komai, shi dai Sadeeq sai kallonta yake, Gwaggwo tayi dariya tace "Fatima kenan, to tashi ki shiga ciki" kamar jira take ta mike ta wuce dakin Gwaggwo da sauri, Muhsin yayi murmushi yace "Imaan Daru" mikewa Gwaggwo tayi ta dauko ma Sadeeq ruwa da lemo yace "Da kin bar shi Gwaggwo daga gida mu ke ai" Gwaggwo tace "A'a idan baka son inyi fushi to ka sha, ga dambun nama yanxu Imaan ta kawo min" murmushi yyi ya dau bottle wata daya ya bude, Muhsin yace "Wai ban ga Amaryar gidan nan ba?" Gwaggwo tace "Taje kai anko, nasan tana hanyar dawowa yanxu" Muhsin yace "Da alama dai duk Halima ta kagu ta bar ki" Gwaggwo tace "Don bata nan shine xaka mata wannan sharrin, to bari dai ta dawo" Muhsin yyi dariya yace "A'a ni dai ba ruwana rufa min asiri Gwaggwo" Sadeeq dai sai murmushi yake yana danna wayarsa, hira suka dinga yi gaba daya a parlon har kusan Asr, Muhsin yace "Gwaggwo bari mu je masallaci mu dawo yanxu" Gwaggwo tace "Toh Allah maku albarka" Muhsin ya mike tare da Sadeeq suka nufi kofa, tashi Gwaggwo tayi tana kiran Imaan da bacci ya dauke tun daxu a dakin. Suna fita compound Sadeeq na kallon Muhsin yace "Wacece yarinyar nan Muhsin?" Muhsin ya wara ido yace "Ko dai kana ciki ne Abubakir?" Sadeeq yace "Na santa ne shi sa nake tambayarka" Da mamaki Muhsin yace "Haba, amma ban ga ta nuna alamar ta san ka ba" Murmushi Sadeeq yyi yana shafa sajensa yace "Ni na nuna alamar na santa banda yanxu da na fito?" Muhsin yace "Toh ina ka santa?" Sadeeq yace "Baka fada min relation dinka da ita ba" Muhsin yace "Cousin dita ce, mum dinta ita ce immediate sister din Abbana" da mamaki Sadeeq ke kallon sa yace "You mean you two are this close?" Muhsin yace "Sure" Sadeeq yace "That's Amazing, she is Mariya's school friend kaga dalilin da ya sa na santa" Muhsin yace "Maa sha Allah, amma bata gane ka ba ko?" Murmushi Sadeeq yayi yana maida glass dinsa yace "Ta gane ni sarai, that was why she was uncomfortable" Muhsin yyi dariya yace "Ohh I see, there is something a kasa kenan" Sadeeq yace "Let not miss jam'i plss" daga haka suka shiga masallacin don yin alwala. Imaan na idar da sllh tace ma Gwaggwo xata wuce don xata islamiyya, Gwaggwo tace "Baxa ki ci abincin ba kenan, shinkafa ce da miya fa" Imaan tace "Bana jin yunwa fa Gwaggwo" Gwaggwo tace "Toh shikenan ki duba siff a daki xaki ga wani sabon hijab da na dinka maki da takalmi ki dauka," Imaan tace "In ji me hannu ne Hijab din?" Gwaggwo tace "Ae nasan me hannu kike sawa, shi nayi maki" Bude kofar parlon aka yi Muhsin ya shigo tare da Sadeeq, Muhsin yace "Har kin fito kenan yan matan Ammi" Imaan tayi murmushi tace "Ehh wucewa xan yi saboda islamiyya" Muhsin yace "Mu ma yanxu xa mu wuce ai" Gwaggwo tace "Toh sai ku ajiye min ita don Allah a gida kar ta kara bin k'uran nan ta koma a samu matsala" Dariya Muhsin yayi yace "Wa yaga imaan baturiya" Imaan ta boye fuskarta, dubu biyar Sadeeq ya ajiye ma Gwaggwo yace "To kaka xa mu koma sai wani lkcn kuma, ba yawa wannan ki siya goro" Gwaggwo tace "A'a gaskiya ka dau kayan ka Sadeeq, matsalata da kai kenan idan ka xo gidan nan kai baka gajiya ne" murmushi kawai yayi, Muhsin yace "Shikenan dama ban fito da kudi ba ya fanshe ni, sai ki raba, nawa da nasa" Gwaggwo tayi dariya tace "Allah sarki, Toh Allah dai ya maku albarka ya ba ku mata na gari kuyi aure ku bar xaman nan da ku ke" Muhsin yace "Toh Ameen Gwaggwo" Tare Imaan suka fita da Muhsin don Sadeeq har ya fita, ta bude back seat ta xauna, Sadeeq ne xaune driver seat din Muhsin ya shiga front seat suka bar anguwar. Hira suka ta yi a motar, ita dai danna wayarta kawai take, amma da ta daga kai xa su hada ido da Sdeeq ta madubi, sai tayi maxa ta sauke kanta, bayan tafiyar kusan minti sha biyar ta ji Muhsin yace "Ajiye ni nan man" parking Sadeeq yyi, Muhsin ya fita yana kallonta yace "Toh anmata sai mun yi waya ki gaida Ammi, abokina xai ajiye ki gida" ta xaro ido tace "Ya Muhsin nima nan fa sauka xan yi dama" Muhsin yace "Inaaa... bayan amana Gwaggwo ta ba mu mu kai ki gida kada kura ya taba ki, nima akwai abinda xan yi anguwar nan ne amma da tare xa mu tafi" Imaan ta dinga kallon sa kamar xata yi kuka, ya daga mata hannu yana danne dariyarsa yace "Sadeeq drive her carefully plss sai mun yi waya" daga haka Sadeeq ya ja motar suka hau saman titi, Imaan dai sai wasa take da fingers dinta, bayan wani lkci ta dago a hankali tana kallon gaba suka hada ido ta madubi, da sauri ta sunkuyar da kanta, yayi murmushi yace "Kina tsoron kada in sace ki ko?" Kin cewa komai tayi, bayan kusan minti biyu taji cikin cool voice dinsa yace "I am Abubakar Sadeeq Ahmad, was born and bred up here in Kaduna, first son of the family, my primary and secondary education all in Kaduna, before I proceed to UK where I had my degree and msc, I am a medical practitioner....." Kallon sa kawai Imaan take ta madubi, yyi murmushi yace "Mariya is my step sis, I have six siblings altogether, ranan kinje gidanmu amma part din stepmum dita, namu part din yana cikin gidan though very far away, soo you've known almost all about me... Yes I am still single and searching..." daga haka yyi shiru ya kalleta yana murmushi yace "Do you mind telling me about ur self" shiru tayi da farko, can a hankali tace "Sunana Fatima Abubakar amma ana kirana Imaan" ta kallesa don a hankali yake driving din kasancewar bbu motoci sosai titin, ya gyada mata kai alamar yana ji, yana murmushi, murya can kasa tace "I am the only child of my parent" Da mamaki ya dinga kallonta, ta sunkuyar da kanta tace "I am In the same class with Mariya both School and Islamiyya, muna xaune tare da Daddy na da Ammi, with my paternal grandmum, and my Uncle with his family, i mean my father's senior brother" Sadeeq ya gyada kai a hankali yace "That's nyc, Allah maki albarka ya sa ki xamo the Apple of ur parent eyes" Murmushi tayi murya can kasa tace "Ameen" ganin sai tafiya yake ta bude manyan idonta tace "To ai baka san inda xaka kai ni ba" ya kalleta ta madubi yace "Kin manta ranan da Antynmu ta sa na ajiye ki gida kenan?" Ta wara ido tace "ohh na tuna" ya d'an yi murmushi, suna kusa layin yace "Toh baki fada min samarin ki nawa ba?" Ta xaro ido tace "Samari kuma?" Yace "Yeah" tace "Tabb, ni bani da Samari" yace "Sai dai frnds kenan" ta turo baki, yayi murmushi yana kallonta, tace "A school bani da male frnds, a islamiyya ma


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login