Showing 30001 words to 33000 words out of 303099 words

Chapter 11 - Imaan Book 1 Hausa Novel Complete

17 Dec 2024

1606

tace "Toh ai rabona ne fa" ya mata wani kallo yace "Na fara wasa da ke gidan nan koh?" Kamar xata yi kuka tace "Toh tasan ba bani xata yi ba kuma ba ni ta ajiye ma ba meye na sa min rai, baxan sake xuwa parlonta ba ma" yace "Eh dauko naman" durkusawa tayi ta dau kayan da ta saki, tace "Mu je parlor in baka" yace "Baxan shiga ba ki dauko min" tace "Toh ni dai idan baka shiga ba baxan baka ba" ya wani daure fuska yace "Ke wai yaushe na xama mate din ki a gidan nan?" Tace "Toh xaka tsammin plss" ya fixgota yana mata wani mugun kallo har tana jiyo numfashinsa, Bata sake cewa komai ba yace "Tafi ki dauko min" a hankali tace "Toh" sannan ta nufi balcony din ya bi bayanta ya tsaya yana kallonta, ta bude kofar ta shiga sannan ta juyo tana kallonsa, wani murmushi tayi ta wara masa ido tace "Good night yaya" daga haka tayi banging kofar da sauri ta sa makulli, sosa kansa yyi bayan kusan second goma ya juya ya fita balcony din yana murmushi. Imaan ta fito daki jin Ammi na kiranta, da mamaki tace "Ammi ina xa ki kuma?" Ammi na rike da flat shoe dinta tace "Kin manta yau xa a kawo lefen Seeyama" Imaan tace "Ohh na manta, to ni Ammi baxan je in gani ba" Ammi tace "Toh girkin da na daura fa?" Shiru tayi kamar xata yi kuka, Ammi tace "Toh idan shinkafar ya nuna ki kwashe sai ki taho" Imaan ta washe baki tace "Toh" Ammi na fita parlon ta tafi kitchen da sauri tayi ta tsaye tana jiran dahuwar shinkafar, daga karshe da sauran ruwa a ciki ta kwashe a warmer ta fita da sauri, Hijab ta sa har kasa ta bar gidan xuwa part dinsu Maimoon, har an kawo akwatunan ta tarar masu kawo wa ma har sun tafi, Anty ce da kawayen Umma uku suka shiga buda tsadaddun akwatuna set shidda da aka kawo, Ammi dai na xaune parlon, parlon cike yake da mutane duk yawanci yan uwan Umma da Kawayenta, Imaan ta nufi inda Maimoon ke xaune duk suna jiran a bude akwatuna su fara ganin kaya ta durkusa, Umma dai fuskar nan babu yabo babu fallasa tana tsaye, Kanwar Umma Hajiya Mariya ce tace "Imaan fa an xama yan mata" Imaan tayi murmushi ta sunkuyar da kanta tace "Ina yini Mama" Umma ta wani daure fuska tana kallon kanwartata, Hajiya Mariya tace "Lafiya lau Imaan ya schl ko kun gama secondary din?" Imaan ta girgixa kai tace "A'a Mama muna ss1" Hajiya Mariya tace "Maa sha Allah, Allah ya baku sa'a" Umma na kallon hajiya mariya tace "Ban ga amfanin ki xaune nan ba Mariya da ki tashi ki bar nan kawai" Murmushi kawai Hajiya Mariya tayi ta mike nan suka dinga fiddo kayan akwatunan, Ammi dai bata tashi ba, Maimoon ta ja Imaan kusa da boxes din wai su ga kaya, Imaan na daga kaya taga wani arnen kallon da Umma ke mata, sunkuyar da kai tayi bata sake yunkurin matsawa kusa da boxes din ba, kaya maa sha Allah sunyi kyau sannan masu tsada, Hajiya Laraba tace "Kai maa sha Allah lallai Seeyama tayi goshi, Allah ya sanya alkhairi ya sa gidan xamana, Allah kuma ya nuna mana na sauran yan matan gidan haka" Umma tace "Toh Ameen amma kuma lafiyayyun yan matan gidan dai koh?" Kawayenta suka kwashe da dariya Anty ta daga kai ta kalli Umma, Wata kawar Umma tace "Gaskiya kam irin wannan kaya ai sai mai lafiya, Mara lafiya kam yyi fatan samun mijin kafin ya sa ran kaya haka" Umma tayi wani dariya har da shewa, Hajiya Mariya da mood dinta ya canxa ta dinga kallon yayartata, ita dai Ammi kallon kayan da suke ta fiddowa kawai take, Umma ta kalli kawarta Hajiya Shafa tace "Ya haka hajjaju naga baki tashi duba kaya ba ko kema kina cikin sahun yan yi ma 'ya ta bakin ciki ne naga dai duk kin aurar da naki yaran" dariya sosai Hajiya Shafa tayi tace "Masu bakin ciki sun san kansu, ni ko in rasa Wanda xan ma bakin ciki rayuwar nan sai ke, jira nake duk a bar wajen In duba kayan a tsanake" Umma ta bata hannu suka tafa tana dariya, maganganu marasu dadi Umma da kawayenta suka dinga saki a parlorn, Anty da abun ya isheta ganin sai xancen mara lafiya suke tace "Ai kuma Hajiya abun fa ba daga nan yake ba, sai a ga kuma mara lafiya ya samu abun arxiki a rayuwa fiye da mai lafiya, so nawa kuma aka yi hakan" wani dariya Umma tayi tace "Toh ayi mu ga ko basilin xai toya kosai" Anty tace "Kwarai kuwa xai toya sai dai a dau lkci kawai" Hajiya Laraba tace "Toh ni duk wannan abun fa har yanxu ban ga amarya ba" Umma tace "Ohh tana can makaranta, gobe xata taho sun ma kusa gama jarabawa" Hajiya Laraba tace "Ayya tana Zarian kenan" Umma tace "In sha Allah" Mikewa Ammi tayi tace "Toh Hajiya Allah ya sanya alkhairi xan je in ci gaba da abinda nake yi" a dakile Hajiya tace "Oh toh madallah, ban ma san an gayyato ki ba da ina da niyyar tura Ummi ta kira ki sai ga ki" Ammi bata tanka ta ba tana kallon Anty tace "Anty Amina, bari inje in ci gaba da girki, kaya sun yi kyau maa sha Allah, Allah ya sanya alkhairi yasa ayi da mu" Anty tace "Toh ameen Ammi sai na shigo" Mikewa Imaan tayi xata bi Ammi Anty tace "Au har xa ki tafi don gulma" murmushi tayi ta shige gaba, daga Umma har kawayenta suka bi su da kallo ana tabe baki. Sai bayan da suka kusa part dinsu Imaan tace "Ammi yaushe ne bikin?" Ammi tace "Me ya hanaki tambayarsu a can" Imaan bata ce komai ba har suka shiga gidan. Da magrib Imaan taje kai ma Inna abinci taga akwatunan jere a parlonta, Inna tace "Kinga akwatunan yar uwar ki kuwa?" Imaan ta girgixa kai tace "A'a ban ga kayan ciki ba" Inna ta mike ta shiga sakko da su tace "Taho ki fiddo su ki gani, ni sai naga kamar ma mijin rufin asiri kawai garesa, ji fa na yarinyar nan Khadijah guda takwas aka kawo har da gwal biyu a ciki wannan kuwa ko axurfa ban gani ba sai dankunnayen kauye" imaan ta rufe baki xata yi dariya inna ta tabe baki ta xauna tace "Toh naga duk sai saurayin ya wani xo ya cika mana kofar gida da katuwar mota, ga kaya nan kuma duk abun kunya, anya ba gudunmawar da dangi suka dinga basa ya xuxxuba mata a akwatunan ba kuwa, ji fa har da man mai gurguwa na gani a ciki, man da aka yi yayi tun lkcn haihuwar Mujaheed" Imaan ta fashe da dariya har da kyakyatawa, Inna tace "Ni daga ganin dankunnayen da sarakuna dama jikina yyi sanyi, atamfofin kuwa har da na roba guda biyu idan dai ba idona ne yyi min karya ba, ga wani uban lace duk nauyin tsiya, sannan jallabiyoyin irin Wanda na taba siya a makka tun ina goyan Ahmadu da naje, bari in fiddo ki gani, ni da dai a kira min yaron inji muguwar da ta hada ma jikata wannan kayan" tana kokarin fiddo jallabiyar Yusuf ya shigo parlon tare da Mujaheed, Inna ta juya tace "Kun ga kayan yar uwar ku kuwa?" Yusuf yace "Na gani sai dai ko M.A" inna ta mike tace "Toh kai isuhu baka ga irin kayan ba, dama katuwar motar karya yake kawo mana kofar gida ya paka?" Yusuf ya bude baki yana kallonta, ta tabe baki ta xauna ta rungume hannu tace "Ni dai ba ruwana, sai kace xa a basa baxawara" Yusuf yace "Haba inna ina laifinsa duk fa kayan masu tsada ne wllh" a fusace Inna tace "Amma kai dai mugu ne wannan yaro, kai ka yarda ka hada ma figalalliyar budurwar nan ta ka wannan kayan, kai kana ganin idan mun kai masu xa su amsa, mutanen da suka jik'a cikin kudi gidansu gari guda motoci ta ko ina, Kai in takaice maka Idan basu koro mu da kayan ba kace ba ni ba" Imaan ta fashe da wani dariya har da kwanciya inna ta fiddo jalabiyyar ta watsa masu kamar xata yi kuka tace "Ku ji fa kayan da na taba siya lkcn ina goyan ubanku a makka" Ganin dariyar da Imaan take Mujaheed ya daure fuska yana kallonta yace "Ke waye kike ma dariya a nan wai" a fusace Inna tace "A'a bar ta tayi wannan ae abun dariya ne, har da fa mai gurguwa da basilin irin na tale tale, bar min ita tayi dariyarta" Tsaki Mujaheed yyi yace "Toh Allah ya sa ta samu hakan ita" A rikice inna ta mike tace "Auxubillahi... Bakin ka ya tsari danyen kashi Mujaheed, kai ka so a kawo ma Imaan irin wannan tarkacen, ai da na shiga uku wllh, bari kaji duk mai auren Imaan sai ya shirya a duniyar nan, idan na amshi akwatunan ta babu gwal na dan kunne, sarka da awarwaro da zobe kace ba ni bace, sannan atamfa idan na amshi na kasa da dubu ashirin kace ba nice Hajiya patu ba, kai in takaice maka idan ba akwatuna sha biyu ba dama kada shegen da ya xo yace xai aureta don xai ga barbadin bala'i" Mujaheed da ke gyada kai ya tabe baki yace "Ae sai ku yi ta xama, kinga sai ki jik'a ta ki shanye ko kiyi kwadonta ki cinye" daga haka ya fice a parlon, Yusuf ya girgixa kai ya fita shi ma, inna tace "Gantalallu kawai yan hassada wanda basa son ci gaba na, a haka xa ku yi ta gantali a titi."

Alhamdulillah, Thanks to all those that patronize the book *Imaan* Allah bar ku da iyayen ku, My book Imaan is for sale coz I am done with free pages tun friday, ni nasan it will go round as usual, I can't prevent that, but if you should come across it it's not for free, i repeat it's not for free, na siyarwa ne, wllh I am too grown up to say Allah ya isa, but have the fear of Allah SWT in u, don't forget it's my property, hakkina ne, wahalata ce, pay before reading, pay before reading, or you just over look it and smile, have a very good conscience plss, and a good conscience won't read happily without paying, if you want any favor pertaining to d book contact me and let me know, the book is 300 via..... Fcmb 3276052019
Hauwa Bello Jiddah

07087865788 and then u contact me through this digit to be added in the payment groups. Thanks once more for patronizing.

For those saying xa su same shi a banxa yana yawo to gashi... amma fa ba a banxa yake ba wllh, there is power in the tongue, Karamin hakkin da ka raina..... 😃😃

11. 🌟⭐ *imaan* ⭐🌟



Kasancewar ranan Alhamis ne Imaan na dawowa schl bayan ta yi wanka ta fito ta d'an cito abinci kadan ta koma bedroom ta saka kayanta ta sake fitowa parlor, Ammi dai sai kallonta take don tun daga ganin d'an abincin da ta ci ta san da matsala, Ammi tace "What's wrong with you?" A hankali tace "Ammi cikina xai fara min ciwo ne" Ammi tace "Toh Allah ya sauwake abincin ya ishe ki?" Kai ta gyada mata ta xauna kusa da ita tace "Ammi na dade fa ban je gidan gwaggwo in gaisheta ba" Ammi tace "Jiya ma ta tambaye ki da muka yi waya, ran Saturday idan kin dawo islamiyya sha biyu sai ki tafi, before four ki taho gida saboda islamiyyan yamma" Imaan tace "Toh Ammi me yasa gobe baxan je ba" Ammi tace "A'a xan je xa mu duba ma Halima kaya an kawo daga dubai, idan kin dawo schl ma baxa ki sameni" Imaan tace "Toh, Ammi ankon mu fa?" Ammi tace "Idan kin je sai ki tambayeta" Imaan tace "Ammi bikin na Anty Seeyama xa a fara yi ko Anty Halima?" Ammi tace "Na Seeyama saura two weeks, Halima kuma saura sati hudu" Imaan tace "Toh Ammi na Seeyama baxa a mana anko ba?" Wani kallo Ammi tayi mata tace "Kin ishe ni kuma haka" Shiru Imaan tayi, can ta mike tace "Ammi xan je wajen inna" Ammi tace "Toh sai ki dauko magana idan kika tashi dawowa" dariya kawai tayi ta sa takalminta ta fita parlon ta rufe kofar. Inna na share waje Imaan ta sameta, Inna ta mike tace "Baki ji bayana ba Imaan tun daxu ban xauna ba wllh, aiki dai aiki dai, to kuwa idan mutum bai yi aiki ba ai sai kazanta ta ra6e sa, to ni ko yaushe xan yarda hakan ta faru???" Imaan tace "Toh me kike sharewa a nan din, naga ba datti" inna ta xaro ido tace "Toh k'uran dake yashe a kasa kuma uwaki ce ba datti ba?" Imaan ta yi dariya tace "Toh ai sai kiyi ta sharewa" daga haka ta shiga ta bar ta a wajen, bayan minti goma inna ta shigo parlon ganin yanda Imaan take yatsine yatsine ta hade rai tace "Me kuma ya faru?" A hankali tace "Wllh cikina ne xai fara min ciwo" Inna tace "Toh tashi ki tafi gidan ku ba ruwana da wahalan ki, ko ba jini bane" Imaan tace "Toh ai bai xo ba kawai dai yana min ciwo ne" inna tace "Toh kiyi maxa ki tafi uwar ki ta kai ki asibiti, haka wancan karan kika cuce ni kika daga min hankali, ni dai da xaki dinga rufa min asiri duk kika ji baki da lafiya ki daina taho min nan sai kin ji sauki, a gaskiya kina shiga alhakina" Imaan bata tanka ta ba, Inna tace "Kin ko ji abinda nace" Imaan ta daure fuska tace "Sai nan da kwana biyar ko shidda ma xai xo, ni dama haka yake min ba shi bane" Inna ta tabe baki ta mike ta nufi dakinta tace "Ni dai ba ruwana kar a xo a dameni a gigita ni" Imaan ta gama juye juyenta bacci ya dauketa. wajajen karfe shidda Inna na daki duk ta fiddo da kayan closet dinta tana masu linkin guga jin an bude kofa ta ajiye kayan xata fita parlor, ta labule ta hangi Mujaheed tsaye cikin parlorn, kana ganinsa kasan daga aiki yake don ko tie din wuyarsa bai cire ba kan farar shirt din jikinsa, kallon Imaan dake bacci ya tsaya yi sannan ya kalli kofar dakin Inna, can dai ya karasa kusa da ita ya duka ya kai hannu a hankali kan goshinta yana feeling temperature dinta, sauke hannunsa yyi kan wuyarta ta bude ido tana kallonsa, yace "What's wrong?" Cikinta ta nuna masa kamar xata yi kuka, daga cikin dakin ya ji muryar inna tana cewa "Don Allah a dinga kyakkyawan xato dai, Shikenan ita kuma a rashin lafiya xata kare kamar warce ta kashe mai rai ka wani kai hannu kana tattaba jikinta kaji ko da xafi ko babu, to babu, kuma lafiyar jikata qlau ka matsa wajen tunda fatan ciwo kake mata, dama likitancin hauka ne" Mujaheed ya dinga kallon kofar dakin, inna ta fito tace "A dai ji tsoron Allah a dinga kyakkyawan xato fisabilillahi, lafiyarta lau wllh, al'adarta ce kawai ke kan hanya shine ta langwabe haka, ka shigo kana wani tabe taben jikinta salon a ja mata wani ciwon tunda a haka ake so ta kare" Shi dai kawai tsayawa yyi yana kallon inna fuskarsa daure, can ya juya ya nufi kofa, inna tace "Toh Ina yini... yanxu ka dawo daga aikin kenan" bai tanka ta ba har ya fice parlon. Kafin magrib Imaan ta watsake gaba daya, bata shirya barin part din Inna ba sai kusan karfe goma na dare tare da Yusuf, Inna na kallon Yusuf tace "Isuhu wai daga na fadi ma Mujaheed gaskiya daxu shine har yanxu bai tako nan ba, to me xai bani da Allah bai ban ba, banda ma magana da yake sa ni idan ya xo, ni dai kai da Imaan kun isheni ni kar ma ya sake xuwa" Yusuf yyi murmushi bai dai ce komai ba ya fita yana kallon Imaan dake tsaye gaba daya hankalinta na kan film da ake yace "Ko dai in tafi ne Imaan" tace "A'a ya Yusuf jira ni, ynxu xa a gama" yace "Toh ki kwana nan mana" da sauri ta fice a parlon har tana tuntube, Yusuf ya fara dariya, Inna ta ja tsaki tace "Toh banda ki yamutse min gado ki bar ni da aiki amfanin me xaki min idan kin kwana Imaan?" Yusuf ya kulle mata kofarta suka wuce, a hanya yace "Me yasa baki son kwana wajen inna imaan?" Ta make kafada tace "Karfe uku idan ta tashi sai tasan yanda tayi ta tashi mutum, tayi ta masa surutu har sai baccin ya fita idonsa" Yusuf yyi dariya yace "Dole ma gobe ki kwana can tunda Friday ne" Imaan tace "Sai dai kai ka kwana" daga haka ta shige balcony dinsu tana daga masa hannu yyi murmushi yana kallonta yace "Good night" yana wucewa ta shiga ciki ta kulle kofarsu.
"Wannan iskancin da kike ki tafi exams babu karatu baxa ki min shi a gidan nan ba wannan karan" Cewar Ammi kenan tana kashe kayan kallon parlon gaba daya, Imaan ta dinga kallonta kamar xata yi kuka bata dai ce komai ba, Ammi ta nemi waje ta xauna tana danna wayarta, A hankali Imaan tace "Ranan Monday fa ne exams din Ammi, i still have Saturday and Sunday sannan Monday da safe" Ammi tace "Ki tashi ki dau abincin Inna ki kai mata baxa kiyi kallon ba, kuma I promise you har ku gama jarabawan nan baxa ki kunna kayan kallo a gidan nan ba, ko yaushe kika xama dedicated da kallo haka ban sani ba" da mamaki Imaan ke kallonta, can tace "Amma ammi ban


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login