Showing 63001 words to 66000 words out of 303099 words

Chapter 22 - Imaan Book 1 Hausa Novel Complete

17 Dec 2024

1629

rufe ido in mance ni na haifi Ahmadu in maka tijara kotu ta raba mu Mujaheed," Yace "Toh yanxu ma ki tashi a tafi kotun mana, duk ke ke karanta mata tsayawa da samari tun bata kai ko ina ba a titi, idan aure take so ae sai ta sanar da Abbanta ayi mata ba ta dinga tsayuwa da maxaje ba tare da saninsa ba, ita har nawa take, ni nasan wlh Abbanta bai sani ba, halan Ummi bata bata labarin abinda na mata kwanaki ba" Inna ta saki baki tana kallon imaan dake shessheka a hankali, can tace "Amma gaskiya ke munafuka ce Imaan, samm baki da hali, banda munafurci ya xa ayi kiyi sabon saurayi amma kiyi ta nuku nuku kina boye min?? me xai bani da Allah bai ban ba, shi kuma gantalallen bai san kakarki na da rai bane da bai taba cewa xai shigo gaisheni ba? Ko uwar ki ce tace ki boye min ban sani ba" Mujaheed ya dinga kallonta da mamaki, rai bace inna tace "Toh ni dai ba ruwana, dama ana boye abun arxiki irin wannan Ashe, me na maki da xaki boye min sabon saurayin ki Imaan?"


20. Imaan









Juyawa Mujaheed yyi ya fice daga parlon, Imaan ta kyabe baki tana share idonta tace "Shi fa bai san ko waye doba xai wani dinga ce wa saurayina, ni dai wllh inna ku ce masa ba ruwansa da ni a gidan nan" inna tace "Atoh dama meye hadin ki da shi, kawai ni dai nasan ubansa wan ubanki ne kuma duk ni na haifesu, to bayan wannan bbu abinda ya hada ki da Mujaheed ba dangin iya balle na baba, ke dai kawai ki rabu da shi ya ji da wawancin sa kiyi ta kan ki, banda fitina ma ina ruwansa da lamarin rayuwarki, idan ma saurayin kika yi baki isa ba ne, ko idan kin rasa mijin aure astaghfirullah shi xai aure ki ne?? kar ki sake saurarensa duk saurayi ya kira ki shirya ki fesa turare ki tafi, wa xai xauna biye ta Ahmadu da Bukar ga d'an su ma ya dauko hanya, bokon jaraba kawai ni wllh kina gama sakandari aurar da ke xance ayi mijin yaji da lalurorin ki d'a na ya huta haka shi ma" imaan ta mata wani kallo ta mike tana goge guntun hawayenta ta fice a parlon. Da yammacin ranan daddy ya gama shirin komawa Abuja ya tafi yi ma Inna sallama, ta gama goge gogen da ta ke ta dawo ta xauna tace "Tafiyar na nan yau din kenan" yace "Ehh, jirgi xan bi kada jirgin ya tashi ba ni" inna tace "Toh Allah ya tsare, amma xaka tafi kuma ya xancen da ku ka min kai da Ahmadu jiya?" Daddy yace "Na me fa?" Inna tace "Tafiyar yaran nan su je gaida Hansatu mana" Daddy yace "Ehh Barrister yace xuwa satin da xa a shiga sai su tafi" inna tace "Ehh gwara su je, duk da dai uwarta axxaluma ce amma ina mata fatan Allah ya ji kanta na kuma yafe mata, amma gaskiya shari'ar mu sai a lahira, don ta cutar da ni...." Daddy yace "Haba inna, bayan kuma kin ce kin yafe" a fusace inna tace "Toh ai Allah ba axxalumin bawansa bane, don na yafe ai a duniya nake nufi ba a can ba, kai baka san komai ba wllh, kaga irin abinda uwarta tayi min ne, kishi dama hauka ne, ni dai kawai albarkacin marigayin uban ku yasa nake barin ayi xumunci da 'ya yan da ta mutu ta bari ma, kuma duk yaran ba xuwa gaida ni suke ba" Daddy yace "Ke fa kika ce kin yafe xuwan, kowa ya xauna inda yake" Inna tace "Toh idan bance haka ba ya kake so ince, kai so kake su xo su sa ma kai da d'an uwanka ido, yanxu da ake nisa nisa ba ya fi ba, babu wanda yasan halin da wani ke ciki, sai ku dinga wata magana kai da Ahmadu don ba ku aka cuta ba, yanxu kishiyoyin da bani da hakkinsu ba gashi duk sun mace sun bar 'ya ya duk a gantale ba, to me xa su xo su min bayan ga nawa 'ya yan... Ku uku wllh kun isheni xaman duniya ita ma Hadiza tace ta kusa dawowa kasar nan gaba daya, to me xai dameni, a hada masu goma ta arxiki aje dai a gaishesu, har shi wancan katon Balan dake Abuja su karasa su gaida shi, ba komai Allah ya ba mu lada su kuma aniyarsu ta bi su" Daddy yace "Bari in je inna, Mujaheed xai kawo maki sako anjima" tace "Toh Allah ya tsare, yayi maka albarka, ya kare ka duk inda xaka shiga" yace "Toh Ameen nagode" daga haka ya fita parlon, part dinsa ya tafi suka yi sallama da Ammi yace "Gobe dai Imaan ta tafi islamiyya, xuwa Wednesday nasan xa su yi tafiyar, before than Dr dinta xai kawo mata drugs dinta coz ya dawo" Ammi tace "Toh Allah ya kiyaye hanya ya tsare, ko in taso ta?" Yace "A'a bar ta" daga haka ya nufi kofa ya fita, Yusuf ne ya kai sa airport. Mujaheed ya daga kai yana kallon Abbansa bayan ya gama maganar da yake, a hankali yace "Abba kaga ba a dde da transferring dina nan ba da har xan fara daukan leave gun aiki...." Abba yace "You are just lookin for excuses, na lura gaba daya baka son tafiyar Muhd" ya sunkuyar da kai yace "A'a ba haka bane Abba, kawai naga...." Abba ya dakatar da shi yace "Toh xan ma boss din naka magana" da sauri ya dago yana kallon Abba amma bai ce komai ba, Abba yace "Beside idan ku ka tafi Wednesday xuwa Friday ai kun dawo, nan nan sulejah dai" Mujaheed bai ce komai ba still, jin Abba ma yyi shiru yace "Toh Abba kasan yanayin jikin Imaan, har da ita xa mu je?" Abba yace "Toh ba ga ka ba, you just go with first aid box" Mujaheed yace "Toh shikenan" Abba yace "And ina son dama muyi wata magana Mujaheed" Mujaheed yace "Ina ji Abba" Abba yace "Its high time you think of settling down with a family Muhd, naga baka san shiru ba kai, idan na kyale ka a haka xa ayi ta tafiya, duk abokanka sun yi aure with kids, not even kid, to kai me kake jira son?" Ya shafa kai a hankali yace "Abba warce nake nema tana karatu ne, amma ta kusa karewa nan da 'yan watanni in sha Allah" Abba yace "Yar ina ce?" Ya d'an yi murmushi yace "Nan Kaduna, a hayi iyayenta suke amma tana gun yayarta a Unguwar sanusi" Abba yace "Toh maa sha Allah, hakan yayi kyau sosai, but I think it's better a fara magana tun yanxu...." Muryar Umma suka ji tace "Babu maganar da xa a fara Alhaji" duk suka daga kai suna kallonta ta karaso cikin parlon, bacin rai karara fuskarta tace "Yanxu ni xaka munafurta Mujaheed, haka muka yi da kai, to kasani wllh idan ina numfashi a doron kasa baxa ka auri yarinyar nan bar, idan kuma kana son ganin ba dai dai ba a lamarin ka kaci gaba da alaka da matsiyaciyar yarinyar, ina zamana ka dauko mun talauci a matsayin surka, to wllh kayi kadan gwara kayi ta xama ba auren ya fi, ga yarinya mai hankali mai natsuwa Safeenah yar wajen Hajiyan Marafa can na nema maka yarinyar kuma tayi mugun na'am da kai xaka toxarta ni ka maidani karamar mutum a idonsu???" Abba yace "Abinda nake son in fara fahimta a nan shine, la6e kike min Rukayya?" Umma ta tabe baki tace "Idan ma la6en nayi Allah ne yasan bani da hakkin kowa shi sa har ya bani ikon labewan in ji komai, Alhaji wato idan Kasan talauci to a kan yarinyar da iyayenta ya kare, can wani ghetto fa suke, to idan ba toxarta mu Mujaheed ke son yi a idon jama'a ba ina shi ina yarinyar nan, Kyan banxa kyan hofi, yo ina ma take da kyan ita ba wai fara ba, gaskiya kayi min iyaka da Mujaheed kada in nuna masa 6acin raina a gidan nan, sam baxai ji da dadi ba, shi baya koyi da d'an uwansa Yusuf, dubi fa yarinyar da yake nema yar attajiri gashi har magana yayi nisa, sai ni ce Mujaheed xai cuta ya kwaso min yar talakawa" Abba ya girgixa kai yace "Halan ke ke raba talauci da arxikin Rukayya?" Umma tace "Ba ruwana da wannan xancen ni dai gaskiya idan Mujaheed bai yi hankali da ni ba xai sha mamaki, kuma in dai baxai bi ni sau da kafa ba xai dinga ganin ba dai dai ba a lamarin sa ni dai ba ruwana" tana kai wa nan ta fice fuuu, Abba ya girgixa kai yace "Look son, ba ruwanka da wannan uwar taka, ba isasshen hankali gareta ba am giving u my words, ka ci gaba da neman yarinyar, Allah ya shige mana gaba" A hankali Mujaheed yace "Ameen" Abba yace "You can go" ya mike yace "Nagode Abba" daga haka ya fita parlon. A hankali Ammi ta bude kofar dakin Imaan tana kallon ciki jin dariyar da take cikin duvet, da sauri Imaan ta katse wayar ta tura karkashin pillow jin kamar an bude kofa, Ammi ta kunna wutan dakin tace "Da wa kike waya Imaan?" Bude duvet din tayi kamar mai bacci ta mike xaune tace "Na'am" Ammi ta mata wani kallo tace "Baxa ki amsa min tambayata ba, da wa kike waya nace?" Shiru tayi tana kallon Ammi kamar xata yi kuka, Ammi ta karasa kusa da gadon tace "Bani wayar" ba musu ta ciro wayar ta mika ma Ammi, Ammi na kallon call log tace "Number waye wannan din" murya can kasa Imaan tace "Abokin ya Muhsin ne" Ammi tace "Me ya hada ki da abokin Muhsin, a ina kika san sa?" Tace "Ammi yana xuwa gidan gwaggwo kuma kanwarsa classmate dita ce, yanxu ma kawai tambaya ya kira ni yake min ba wani abu ba" Ammi ta dinga mata wani kallo, ta sunkuyar da kai, Ammi tace "Ke dai kin iya munafurci" kamar xata yi kuka tace "Ammi ni wllh dai ya kira ni ne amma ba komai fa" Ammi tace "Toh yayi kyau, ki bude kunne sosai ki saurareni, kada ma ki nuna nasan kina waya da wani a gidan nan don ba ruwana, duk ranan da Daddyn ki ya kama ki dama ki tanadi abun gaya masa don't involve me in this" tana kai wa nan ta fice dakin. Washegari da rana Ammi na xaune parlor Imaan ta fito sanye da Hijab sai karamar jakarta da ta rataye, Ammi na kallonta tace "Ina xa ki?" A hankali tace "Ammi xan je in siyo cream a supermarket" Ammi na kallonta da mamaki tace "Yaushe na siyo maki da har ya kare Imaan?" Shiru tayi tana kallon Ammi kamar munafuka, Ammi tace "Shan cream din kika fara?" Tace "Ammi shafawa kawai nake yi fa" Ammi ta tabe baki tace "Toh ni kam bani da kudin cream yanxu" tace "Ai ina da kudi a account dina" Ammi tace "Toh Hajiya mai kudi, a dawo lafiya" yar dariya tayi ta sa flat shoe dinta ta fita parlon, kamar mai tausayin kasa ta taka har bakin main road inda xata samu adai daita, jin wayarta na vibrate a jaka ta fiddo, Sadeeq ta ga ke kiranta, ta daga ta kai kunne, Cikin cool voice dinsa yace "How r you Imaan?" A hankali tace "am fine ina yini?" Yace "Lafiya lau, kina hanya ne?" Tace "Ehh" yace "Ina xa ki?" Ta d'an yi shiru kafin tace "Xanje supermarket" yace "Wanda muka hadu ranan?" Tace "Ehh" yace "Tell me what you want to get sai in siyo in kawo maki yanxu" da sauri tace "A'a bana so" a hankali yace "Why?" Tace "Ni dai bana so, yanxu ma xan hau adai daita ai" yace "Toh shikenan, we will talk later, Allah ya tsare" tace "Ameen thanks" daga haka ya katse wayar ta samu adai daita ya kai ta har mall din, wani babban boutique dake opposite mall din ta shiga, gun eyeglasses ta tsaya tana duba glasses masu kyau shigen irin wanda yake sa wa, ta wara ido ganin the prices are waoww, wani da ya mata kyau sosai ta dauka tana dubawa kafin ta tafi gun da ake biyan kudin kayan ta basu atm suka cire kudinsu suka mata packaging din eye glass din ta fita ta tsallaka ta shiga cikin mall din, gun body creams ta tafi ta dau cream da take shafawa duk da akwai mai yawa a gida, kawai dai ta juye a wani container ta boye ne sanin Ammi na iya shiga daki ta duba bayan ta taho, bayan ta dau cream din xata juya ta kusa cin karo da mutum, komawa baya tayi da sauri da nufin basa hakuri, sai kuma ta xaro ido da mugun mamaki tana kallonsa, murmushin da ya bayyana dimples dinsa yyi yace "Sorry" ta sunkuyar da kanta yace "Har kin gama shopping din ko yanxu kika fara" ta dauke kai tace "Na gama" yace "Toh mu je ki rakani I want to get somethings" Daga haka ya fara tafiya, bin bayansa tayi kamar munafuka, gun kayan ciye ciye su chocolates, biscuits sweets da dai sauransu ya tafi, yana kallonta yace "Kanwata xata yi birthday gobe, so nasan dai ku mata babu abinda ku ke so da ya wuce wannan, am asking for a favor duk abinda kika san kina so ki daukar mata nasan ita ma xata so" Murmushi tayi tace "Ohk then" nan ta dinga jidan duk abinda ya kwanta mata take mugun so kuma, ya dinga tura trolley din yana biye da ita, xaro ido yyi yace "Anya imaan wannan banda mugunta kuwa, yanxu duk wannan abubuwan da kike dauka kina nufin kina son su?" Ta juya ta wara masa manyan idonta tace "Ai duk abinda kaga na dauka a nan I love it with all my heart, baka san yanda nake son chocolates da sweets ba koh" murmushi yyi yace "Toh mu bar mata su a haka" tace "A'a jira ga wani chocolate can..." Da sauri ta tafi ta debo har biyar ta xuba a trolley, ta kwaso wasu biscuits ma ta xuba, ta dau wani sweet ta xuba shi ma, ta juya tana kallonsa tana murmushi tace "Toh ni dai ina mugun son teddy in daukar mata" ya langwabar da kai yace "Kawai so kike account dina yayi kuka yau koh??" Ta hade rai tace "Just guda biyu ko uku fa, Is she not ur sister? And is it not her birthday" daga haka ta tafi gun teddies ta debo uku masu tsada da kyau ta jefa cikin trolley din tace "Tunda kana complaining account dinka, mu bar mata su a haka kawai" Yar dariya yyi yace "Noo ci gaba har sai kin gaji" tace "A'a I have conscience" dariya yyi ya bi bayanta ganin ta nufi gun counter, cream dinta ta ajiye xata bada ATM card ya riga ta mika nasa, juyawa tayi tana kallonsa sosai gabanta ya fadi bayan sun hada ido tayi saurin sunkuyar da kanta, nan aka cire kudin aka bata receipt dinta, ta taya sa ciro abubuwan cikin trolley din shima ya bada atm card aka cire aka masu packaging, barinsa tayi da kayan gaba daya ta dau teddies din suka fita. Bayan ya xuba ledojin a bayan mota ya rufe motar yana kallonta kafin yace komai tace "Yau ne birthday din?" Gyada mata kai yyi smiling, ta boye fuskarta a hankali tace "Toh ni dai ina son kaza ko xaka siya mata" Wara ido yyi yana kallonta, sai kuma yyi dariya yace "Ina kika ga kaxa imaan?" Ta turo baki ta nuna masa inda ake gashin kaji, yana murmushi ya tafi, ya siyo kajin gasassu biyu ya dawo ya sa a mota, ya juya yana kallonta pleadingly yace "Let me drop you plss" da sauri tace "Nooo thank you" tana fadin haka ta bude karamar jakarta ta fiddo glass din dake leda tana kallonsa ta mika masa, a hankali ya sa hannu ya amsa yana kallon kwayar idonta, hakan yasa tayi saurin sauke nata idon, bude ledan yyi ganin glass din underneath his breathe yace "Waow..." Murmushi tayi xata juya masa baya ya riko hannunta cikin sanyin murya yace "Thanks Imaan, I love it..." Bata ankara ba sai gani tayi yyi pecking hannunta, ta kwace hannun da sauri tana xaro ido a tsorace, shi ma daburcewa yyi yace "I... Sorry I.. I am just happy imaan, I love the glasses" ta kirkiri murmushi har sannan tana jin warm lips dinsa a hannunta, xata juya yace "Wait Imaan" tsayawa tayi gabanta na faduwa, ya bude front seat yace "Plss let me drop you home" kasa ci gaba da kallonsa tayi ta kuma kasa cewa A'a, a hankali ta shiga motar yyi murmushi ya rufe, ya xaga ya shiga driver seat suka bar mall din, bata yrda yaje dai dai gate din su ba tasa ya ajiye ta few houses away from theirs, ta bude motar ta sauka shi ma ya sauka ya xaga ya bude back seat, ya fiddo gaba daya ledojin siyayyar da suka yi da teddies da kajin duk ya ajiye kusa da ita ya wara ido yana mata murmushi yace "Dama duk naki ne" bai jira cewarta ba ya xaga ya shiga driver seat ya tada motar ya bar ta da zare ido ya bar layin, kallon ledojin ta dinga yi kamar xata yi kuka, yanxu ya xata yi da kayan nan.... Kwasa tayi ta boyesu cikin flowers ta dinga dauka da daddaya da daddaya tana kai su part din inna, duk a mugun tsorace take, Inna ta saki baki tana kallon kayan, imaan ta tafi dauko last ledan, Yusuf dake ta kallonta tun shigowarta na farko ya mike ya isa kusa da ita da mamaki yace "Daga ina kike wannan saurin hakan Imaan, what's all this u are


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login