Showing 75001 words to 78000 words out of 303099 words
na amsa" Mujaheed ya kasa daina kallonta ko kiftawa babu, Abba ya sauke ajiyar xuciya yace "Toh Allah ya saka da alkhairi" inna tace "Toh ya xancen turo magabatan nasa fa?" Ya d'an yi shiru sai kuma yace "Inna da dai a jira Sadeeq ya dawo koh?" A fusace inna tace "Oh oh Allah waye kuma Sadeeq?? dole sai Bukar din yana nan? kai ba mahaifi kake wajenta ba, Bukar da idan ya tafi Habuja kamar baxai sake dawowa ba, ni ba ruwana ka kirasa a waya ka gaya masa komai in ma ya kama ya taso ne ya taso kawai, to nasan bayan shekara nawa xai dawo idan muka tsaya jiransa??" Abba ya dinga gyada mata kai nan ko neman abinda xai ce mata yake, can dai yace "Toh ko xa ki kirasa da kanki Inna??" ta tsuke fuska tace "Baxan kira ba idan baxa ka kira ba a bar kiran, iyaka in shirya in tafi kano gun kawun ku ya amshi gaisuwa da kudin auren kawai, ai ba ku kadai ke da iko da ita ba" cikin low voice Mujaheed yace "Meyasa baki maganan wa enda suka girmeta a gidan sai ita??" Inna ta masa wani kallo tace "kana nufin su ku kenan masu tambadewa a titi, wato kai da Isuhu, to ni meye ruwana da rayuwarku fisabilillahi? Da ku yi aure da kar ku yi duk daya wllh tunda baku da mafada, ko ni na ajiye ku da xan maku magana idan ba rainin wayo ba, ko me na hada da ku? Ga dai iyayenku suna kallonku basu ce komai ba sai ni bare? Imaan dai Allah ya fiddo mata zankadeden miji in sha Allah, to ni na ajiye ku da xan maku magana idan ba rainin wayo ba, ko me na hada da ku??" Abba ya mike yyi kasa da kai yace "Toh ina fita ynxu xan kira Sadeeq din" Inna tace "Gwara haka dai, kana kiransa ka zayyane masa duk abinda nace tass, kace masa yaron ma takwaransa ne shi ma Sadeeq ake ce masa, baka gansa ba Ahmadu kyakkyawa ga hanci kamar an xana biro, ga idanuwa maa sha Allah" sai da safe Abba yayi mata ya nufi kofa Mujaheed ya bi bayansa, inna ta bi Mujaheed da harara tace "Oho dai bakin cikin ka xai kare maka Mujaheed, daga jin kanwarka tayi miji sai bakin ciki ya bayyana karara a fuskar ka? To aniyar moda ta bi randa, imaan dai nan gani nan bari" Shi dai bai tanka ta ba har ya fita ya kulle kofar. Abba na fita ya shiga kiran d'an uwan nasa, daddy na dagawa ko gaisawa basu yi ba yace "Toh tsohuwa dai ta 6aro mana wani babban aikin Sadeeq" Daddy yace "Tohhh, Me kuma ya faru" Abba yace "Wai aure take son ayi ma Imaan" Daddy ya wani bude ido da mugun mamaki yace "Aure kuma Barrister?" Abba yace "Wllh, and she is damn serious, kawai kirana tayi daxu tana nemana shine na taho and this is what she said" cike da confusion Daddy yace "Aure fa kace Barrister, toh ita tayi mata mijin?" Abba yace "Na dai ji tana ta xancen d'an gidan Bulasawa, ban san ko ita Imaan din ta ma san sa ba, I tried telling her she is too young ko secondary bata gama ba but inda inna take shiga ba nan take fita ba, she didn't even give me a listening ear, she so mean it, so ko xaka kirata yanxu??" Daddy yace "Innalillahi wa inna ilaihi raji'un me yasa inna take haka" Abba yace "Kaga gobe Friday if you can squeeze up things ka taho sai mu san yanda xa mu yi koh? Ni bana son in ja xancen ne ranta ya baci kasan yanda take abubuwanta, shi sa mata sallama kawai na fita" Daddy yace "But ka fa san idan tayi deciding abu it's hard ta canxa barrister" Abba yace "Don't worry, ka dai taho goben sai mu san abun yi in sha Allah" Daddy yace "Toh Allah ya kai mu" sallama suka yi Abba ya kalli Mujaheed da kansa ke kasa yana tafiya absentmindedly, Abba ya dafa shoulder dinsa yace "Are you okay son?" Kallon Abba yyi da sauri, sai kuma ya d'an yi murmushi yace "Sure Abba, kawai dai har yanxu I am surprise at what grandma is planning" Abba ya sauke ajiyar xuciya yace "Imaan din har nawa take ma banda abun inna, ga shi ba wani lafiyan kirki gareta ba, inna dai kam abun ta gaba yake ba baya ba, ita kawai ayi auren saboda d'an mai kudi ne, Allah ma kadai yasan abubuwan da ta fada ma yaron, tun tasowar mu muke fama da ita a haka muna ta lallabawa dai, gashi bbu abinda ya canxa har yanxu, abu kuma ya xo ya hade da tsufa, sai dai mu yi ta mata addu'a, Allah kuma ya rabamu da ita lafiya, amma abinda ya ban mamaki shine ta yanda ta san yaron, kuma anya Imaan ta ma san sa kuwa?" Mujaheed dai bai ce komai ba sai pressing din counter dinsa yake a hankali, Abba yace "Kai kasan yaron Bulasawan da take fadi?" Mujaheed ya girgixa kai, bayan few seconds yace "But ina ga Yusuf baxai rasa sanin sa ba don yana mingling da irin su" Abba yyi murmushi yace "I will call and ask him" suna isa sashinsu, Abba yace "Don't forget ka fita ka siyo mata naman da tace" a hankali yace "Toh" motarsa ya bude don makullin na hannunsa ya shiga, Abba kuma ya shiga cikin gida, Mujaheed ya ja motar ya fita compound din. Mujaheed na dawowa daga siyo Tsiren da Abba yace ya nufi part din su Imaan, a hankali ya kwankwasa kofar sannan ya murda yaji a bude, shiga parlon yyi, ya sauke idonsa bayan sun hada ido da Ammi yace "Gashi Abba yace a kawo mata" Ammi ta kwalo ma Imaan kira don tana bedroom dinta, ko me ta tuna sai kuma ta mike xata amshi ledan sai ga Imaan ta fito sanye da kayan barcinta, xata shigo parlon Ammi ta dinga mata wani kallo, da sauri ta juya ta koma dakin ta rufe kofar, Ammi ta karbi ledan ta nufi dakinta ba tare da ta amsa sai da safensa da ya mata ba, juyawa yyi ya fita parlon ya kulle kofar. Washegari daga Imaan har Ammi suka yi mamakin xuwan Daddy ba notice, Bayan Daddy ya shiga bedroom Ammi ta bi bayansa, xaune ta samesa gefen gado tace "Yallabai xuwa babu notice, hope lafiya dai" Yace "Ehh I came for something urgent, xuwa lahadi xan koma in sha Allah" tace "Allah ya kai mu" shiru yyi hakan yasa tace "A kawo maka breakfast ne?" Yace "Noo, Ina son maki wani tambaya, Imaan tana da wani ne dake nemanta?" Ammi tayi shiru tana kallonsa a bit shocked, can tace "Lafiya Yallabai?" yace "I am asking you..." girgixa kai Ammi tayi, she have got no option then to protect her daughter, a hankali tace "Not at all, ita da bata xuwa ko ina daga boko sai islamiyya, is there any problem" yace "Ohk" mikewa yayi ya shiga bathroom ita kuma ta fita a sanyaye tana mamakin tambayar, to me kuma ya faru, tana fita parlor tayi still don sai a sannan ta tuna abinda Imaan tace inna tayi jiya, wato har inna ta kirasa kenan ta gaya masa, daki ta tafi gun Imaan, tana kallonta tace "kin ga abinda nake guje maki ko, to ina jin inna ta kira Daddyn ki har ta fada masa xancen yaron jiya, without any doubt abinda ya dawo da shi kenan" Imaan ta xaro ido a tsorace tace "Daddy ya maki maganan ne?" Ammi tace "Dama tun ba yanxu ba nace maki ba ruwana kar ki ja min matsala, gaskiya sai ki san abinda xa ki ce ma Daddyn ki, don't involve me in this" daga haka ta fita dakin, imaan ta kasa xaune waje daya gabanta ya dinga faduwa hawaye cike idonta, daga karshe ta fice a dakin, direct part din inna ta nufa hawaye cike idonta.... shigar Mujaheed parlon kenan ya je gaisheta daga inda yake tsaye, ko amsa gaisuwarsa bata yi ba tana kada shayi a kofi tace "Ni fa Mujaheed tsabar yanda nasa maganar jiya a rai har mafarkinsa sai da nayi wlh, wai ga Imaan a daula iya daula babu abinda babu a runtumemen gidan na more rayuwa, har naje masu sati biyu, in gaya maka yau... a kawo min kaji, gobe.... a kawo xabee, gata... a kawo kwayakwayay, citta... a kawo tika tikan Kifaye, ga gwangwanin madarana da bournvita da suga an min dak'en da shi a daki, nayi wani jazur da ni sai sheki nake malam, Shi ko bulasawan kullum xai fita sai ya ajiye min dubu biyu in sa kati, wllh tllh ba karya nake maka ba Mujaheed" Mujaheed dai na tsaye daga bakin kofa yana kallonta, ta tabe baki ta yagi bread ta kai baki tace "Ni dai ba ruwana, Ahmadu ya shigo in san yanda suka yi da Bukar din" Jin an bude kofa Mujaheed ya juya, imaan ta shigo ko takalmi bata cire ba, tana kallon inna kamar xata fashe da kuka tace "Inna me kika ce ma daddy na?" Inna tace "Waye kuma Daddyn ki?" Imaan tace "Wai ni nace maki wanda kika gan ni da shi jiya saurayina ne??" Inna ta kyabe baki tace "Kya ji da shi, ni dai baxan kula ki ba ki xageni, na riga na gama maganata, wllh Mujaheed baka ga yanda ta ji kunya ba jiya da ta gan ni kamar fa ta nutse, ni dai ban bi ta kanta ba ban kuma kulata ba bakina a leko na ja Bulasawan muka shigo ciki, to kuma meye xata shigo min ta tale baki kamar wata agwagwa? Ni dai ba ruwana" Mujaheed ya juya ya fice daga parlon... imaan ta durkushe wajen tana kuka sosai tace "Wllh idan kika sa Daddy ya min fada ko ya dokeni ni dai Allah na kallon ki Inna, ni ban ce naki saurayina bane, abokin yaya Muhsin ne ni ban san shi ba" Inna dai na ta cin bread dinta tana shan shayi, Imaan ta gaji da kukanta ta mike xata fita inna tace "Toh aniyar ki dae dama ya bi ki a baya, ba ruwana. Ni nasan wani yaya Muhsin" imaan bata tanka ta ba ta fice hankali tashe. Tsaye Imaan ta ga Mujaheed dai dai inda xata sha corner xuwa part din su, xata gudu ya kamo hannunta, a tsorace tace "Wayyo yaya don Allah kayi hakuri inna sharri take min...." Fingers biyu ya daura kan lips dinsa yana mata wani kallo, haka yasa tayi shiru tana kallonsa gabanta na faduwa, ya nuna mata dakalin dake wajen fuska daure yace "Xauna" Ba musu ta xauna kamar xata fashe da kuka, yace "What did I tell you about standing outside with guys?" Hawayen dake makale idonta ya gangaro tace "Don Allah kayi hakuri yaya" yace "Me yasa baki jin maganata?" Tace "Ina ji fa yaya" yace "Toh meye tsakanin ku da mutumin?" Ta girgixa kai da sauri tace "Ba komai, abokin yaya Muhsin ne?" Yace "Me yake xuwa yi wajen ki?" Ta sunkuyar da kai ta rasa abun cewa, strictly yace "Answer me now before I give you an unclean slap" Ta fashe da kuka a hankali tace "Ba komai fa yaya, kayi hakuri plss" dauke kai yyi na few seconds, sai satan kallonsa take, ganin yanayinsa gabanta ya tsananta bugawa, can ya kalleta ya durkusa gabanta calmly yace "Abba da daddy xa su kira ki su tambayeki what's between you and the guy, me xa ki ce masu?" Ta sauke idonta a hankali tace "Xance masu abokin yaya Muhsin ne" Ya wani hade rai yace "No, kalleni da kyau" Daga kai tayi tana kallonsa, sosai gabanta yyi mugun faduwa, a hankali yace "You tell them babu komai tsakanin ki da shi, kin ji ni?" Ta gyada masa kai kawai, yace "Good, ko baki son ki gama karatu kamar Seeyama? Baki son ki tafi university" Ta turo baki ta boye fuskarta da hannunta murya can kasa tace "Ina so mana yaya" Jin bai ce komai ba ta xame hannunta a hankali ta ga kallonta yake, dauke idonsa yyi murya can kasa yace "Idan ma yace son ki yake kice masu ke baki sonsa" Yar dariya tayi, ya jefa mata wani kallo xai yi magana sai ga Abba da Daddy xa su part din Inna, mikewa yyi da sauri, Daga Abba har daddy kallonsu kawai suke, Mujaheed yyi kasa da kai yana gaida daddy, daddy ya amsa da murmushi yace "Ya aiki Muhammad" Mujaheed yace "Alhmdllh" Abba yace "I called ur line baka daga ba" Mujaheed yace "Na bar wayar can daki naje gaida Inna ne" Abba yace "Ohk" a hankali Imaan ta gaida Abba ba tare da ta yarda ta dago kanta ba, Abba ya amsa daga haka suka wuce tare da Daddy da ko kallonta bai sake yi ba, mikewa Imaan tayi tana kallon Mujaheed, yace "Kin ji abinda nace maki koh?" Kai ta gyada masa a hankali, daga haka ya wuce ya bar ta wajen a tsaye, Mujaheed bai karasa part din su ba mota ta shigo gidan, Driver na parking Umma ta fito, suna hada ido gabansa ya fadi sosai ya juya da sauri to make sure Imaan bata biye da shi a baya, driver ya sakko motar ya xaga ya bude booth, set biyu na boxes masu d'an karen kyau da tsada ya fiddo a booth din yyi cikin gida da su, Tuni Umma ta wuce ciki ita ma, Mujaheed ya bi su da ido. Tare Abba suka shigo parlon da Daddy, Inna tace "Naji dadi da ka ba lamarin nan muhimmanci ka taho Bukar, ina fatan kuma kayi murna da jin wannan abun arxikin?" Daddy yace "Ina kwana" tace "Lafiya lau, ya ka xo?" Yace "Alhmdllh" tace "To madallah" Daddy yace "Jiya Barrister ya min bayanin komai...." Ta washe baki tace "Toh Alhmdllh" yayi kasa da murya yace "Amma inna, Imaan yarinya ce sosai sannan ga ta ba lafiyayya ba...." Inna ta katse sa tana kallon Abba tana nunasa tace "Kai dai wllh Ahmadu baka yi ba, yanxu sai da ka xugesa sannan xaku shigo min nan?" Daddy yace "Aa baki fa jira na kai aya ba inna" mikewa tayi a fusace tace "Babu wani xancen kai aya Bukar, ni kai da d'an uwanka xaku munafurta daga taimako, ni xa ayi ma cin dunduniya, waye baya son nasa ya huta a xamanin nan, koko xan ma Imaan xa6in da xae cuceta ne ko ance maku ban san abinda nake bane, ku kuka haifeni ko ni na haifeku, to wai ma ku tsaya tukun, wai idan aka yi auren nan tare za mu tare gidan da ita?? duk girman gidan naga dai nata ne ita kadai ba tare da ni xata more rayuwar xaman gidan ba, iyaka bai fi a sati inje sau biyar ko shidda ba, to idan baku aurar da ita ba jik'a ta xa kuyi ku shanye ko enlargement xa ku yi da ita kuna kallo a parlor, yau naga abinda ya isheni bai ishi ubangijina ba" Daddy yace "Kiyi hakuri, bai kai haka ba inna, sai ki hada mu da yaron ayi magana ta fahimta" Inna ta goge xufan da take yi tace "To yanxu naji batun kirki, sai dai kuma ban san inda za a samo sa ba, amma ita imaan din ai baxata rasa lambarsa ba, ku kira ta ta taho a kwashe min a wayata in kirasa" Abba dai sai kallon mahaifiyar tasu yake, Daddy ya ciro handkerchief din aljihunsa ya share xufar goshinsa, Abba ya sauke wani boyayyen ajiyar xuciya yace "Toh xa a amshi lambar nasa a gunta in sha Allah" Inna tace "Toh idan kun kirasa me xa ku ce masa?" Abba ya d'an kalli daddy, Daddy yace "Ce masa xa mu yi ya turo magabatan nasa" Inna ta xauna kan kujera tana murmushi tace "Toh Allah maku albarka, ya buda maku" mikewa Abba yyi, daddy ma ya mike yace "Toh anjima xa mu shigo in sha Allah" tace "Toh shikenan amma kar fa ku ce xa ku ja lokacin don yaron yace a matse yake yyi auren" Babu wanda ya tanka ta cikinsu har suka fita parlon.
*The book Imaan is not free*🤷🏻♀️
It's 300 via Fcmb 3276052019
Hauwa Bello Jiddah
Then u show ur evidence of payment via my WhatsApp digit 07087865788 to be included in the payment group.
Imaan. Page 25
Abba na kallon Daddy yace "Kada kayi ma Imaan magana tukun, I want to confirm who the guy is from Yusuf, Mujaheed yace baxai rasa sanin sa ba" Daddy yace "Toh shikenan, amma I will so deal with her, ita har nawa take xata fara kula samari can you imagine?" Abba yace "Nace kar kace mata komai tukun, ni nasan abinda xan yi" Daddy bai iya yace komai ba, don gaba daya ransa ya gama baci, suna isa part dinsa ya shiga, Abba kuma ya karasa nasa part din. Direct bedroom din Mujaheed Abba ya tafi ya bude kofar, Mujaheed na xaune tare da Umma a dakin ya sunkuyar da kai yana saurarenta, Umma na ganin Abba tayi shiru daga abinda take cewa, Abba yace "Ka sameni parlor Muhd" a hankali Mujaheed yace "Toh Abba" daga haka ya rufe kofar, Umma tace "Wai me ke faruwa, jiya naga mood dinsa gaba daya sai a hankali, halan tsohuwarsu ce ta tada wani fitinar?" Murmushi Mujaheed yyi yace "Ehh.." Umma ta buda ido sosai tace "Wai me take so?" Kamar Mujaheed baxai ce komai ba sai kuma yace "So take ayi ma Imaan aure" Umma ta xauna da kyau da mamaki tace "Aure kuma? imaan din saurayi gareta da xa a mata aure? Ko tana da yaron da xata hada ta da shi ne?" Mujaheed ya d'an yi shiru sannan yace "Ban sani ba Umma" Umma ta hade rai tace "Baka sani ba duk kusancin ka da inna, ko dai gaya min ne baxa ka yi ba??" Ya girgixa