Showing 33001 words to 36000 words out of 303099 words
taba daukan sama da second position ba fa a schl" Ammi tace "Ur silly First position ba karatu? I want to see ur grade idan kika yi karatu this time around" Imaan ta dauke kai kamar xata yi kuka tace "Ni da ma ba wani kallo nake ba sai lkci lkci kuma da ace 5th nake dauka shine sai ki ce in daina kallo fa Ammi" Ganin kallon da Ammi ke mata ta mike ta sa hularta ta wuce kitchen ta dau abincin inna dake ajiye tun daxu ta fice gidan, har ta isa part din inna ji take kamar ta fashe da kuka, ta bude kofar ta shiga, xaune ta tadda inna da bowl din fura a gabanta ta daura kafa daya kan daya, Yusuf na xaune parlon shi ma da cup din furan a hannunsa, sai Ummi dake shan furan ita ma, Mujaheed dai idonsa na kan tv ga nasa cup din furan a kusa da shi, Inna na ganin Imaan ta daure fuska ta rufe furan gabanta ta mayar bayan ta tace "Ni dai wllh ya kare, ba ruwana sai kun ga mutum da abu ku wani dinga tururuwan xuwa, to duk na rabar..." Imaan ta ajiye abincin hannunta tace "Toh ni ina ruwana da furanki ce maki nayi xan sha?" Inna ta kalli Ummi tace "Ke tashi ki shigar min da abina ciki" Ummi ta mike ta dau furan ta kai daki ta fito, imaan ta turo baki tace "Sai kace nace xan sha" Inna tace "Toh ai sai ki juya ki tafi koh?" Imaan ta ki fita don har ranta take son fura da nonon barin idan inna ce ta dama kuma ita tayi furan da kanta, inna ta kalli na Mujaheed tace "Dama ga wannan Boss din ya ji sha, ko raina wanda na tarfa masa yayi Oho, da yake Rukayya ce tayi min wahalan aikin furan Ahmadu kuma ya siyo min nonon, cewa ma yayi baxai sha ba ki dauka ki sha, Allah yayi da rabon ki" Yusuf yyi yar dariya yana kallon Imaan, Imaan ta saci kallon Mujaheed dake kallon TV har sannan, ta kalli rabin cup din furan kusa da shi, inna tace "Tunda fa aka ji yace baxai sha ba fa baxai sha ba, kawai ki dauka rabon ki ne, don ni bani da wanda xan baki in kwana da yunwa" Imaan tace "Toh wai ni nace maki xan sha ne?" Tana magana tana kallon kofar parlon lkci daya ta suri cup din tayi waje a guje Yusuf ya kyalkyale da dariya don yasan abinda xata yi kenan, Inna ta washe baki tana kallon Mujaheed tace "Allah ya kara" mikewa Mujaheed yyi fuska daure ya bi bayanta, Inna ta rushe da dariya har da kyakyatawa tana kallon Ummi tace "Da dai ki tashi ki kulle min kofa da makulli tunda sun fita" Kafin Imaan ta kai rabin hanya dama gaba daya furan duk ya xube saboda gudun da take, Mujaheed ya cafketa daga karshe ta fasa ihu ta sake cup din hannunta ta kama hannunsa tace "Wayyo Yaya don Allah kayi hakuri inna ce tace in dauka" da mamaki yake kallonta yace "Yaushe na fara wasa da ke gidan nan amma?" Jikinta na rawa tace "Don Allah kayi hakuri Yaya" fuska daure yace "Kiyi providing min furan nan yanxun nan idan ba haka ba wllh kinji na rantse sai na sa ki kuka" ta fashe da kuka amma ba hawaye tace "Yaya bayan kana gani duk ya xube nima ban sha ba, don Allah kayi hakuri xanje waje in siyo maka wllh" ya wani hade fuska yace "Wannan nake so ba na waje ba" ta marairaice tace "Toh yanxu yaya a ina xan samo maka wani, nima fa kaga bata bani ba" ya kalli part din Inna sannan ya kalleta, murya can kasa yace "Kinsan abinda xa ayi yanxu?" Ta kara marairaicewa tana girgixa masa kai, yace "Komawa xa kiyi part dinta ki shiga daki ki fito da bowl din furan da gudu yanda kika fito min da nawa yanxu" ta xaro ido tana kallonsa, sai kuma ta fashe da dariya tace "Yaya kasan baxata bari ba fa" ya hade rai yace "Irin dubaran da kika yi kika fita da nawa haka xaki fito da wancan ma ae" Imaan ta dinga dariya har da kyakyatawa, ya ja kunnenta yace "Baxa ki daina wannan dariyar mahaukatan ba" ta hadiye dariyar da kyar tace "Toh amma tare xa mu sha?" Yace "Eh mana" tana murmushi tace "Toh nasan yanda xan yi" a tare suka koma part din inna ya nuna mata bayan window din bedroom din inna yace "A can xa ki sameni ina jiran ki" tace "Toh" daga haka ya wuce yana waigota, a guje Imaan ta shige parlon inna tana cewa "Wayyo inna kice masa wllh kar ya ta6a ni xan gaya sa da Abba, inna kice kar ya taba ji xan kira daddy na...." Mujaheed yyi murmushi ya koma bayan window din ya tsaya yana shafa kansa, Inna ta mike da sauri kar Imaan ta take ta koma wani wajen ta xauna tace "Fito min daki wllh, ba ruwana ku je can ku karata kar wanda ya dameni, yara dai kamar na jaraba" Imaan da ta shige dakin tuni ta dinga dariya kasa kasa ta dau bowl din furan ta datse murfin yanda idan tana gudu baxai xube ba, ta tattara rigar jikinta tayi saitin bakin kofar fita sannan ta fice a dari da sittin, inna ta kyakkyafta ido don tabbatar da abinda ta gani hannunta amma tuni Imaan har ta fice parlon kamar xata tashi sama, inna ta mike da sauri tace "Isuhu me na gani a hannunta kamar kwanon fura na???" Ummi ta kyalkyale da dariya tace "Wllh shi ne" Yusuf ya fashe da dariya, Inna ta fashe da kuka tana kallonsa. Imaan bata tsaya ba sai da ta isa inda Mujaheed yake jiranta, murmushi yayi ya amshi bowl din yace "Yauwa kinyi kokari" ta washe baki tace "Nagode" ya xauna kan dakali dake wajen ya bude bowl din ya dau ludayin ciki ya juya furan sannan ya fara sha, Imaan ta daina murmushin da take ta durkusa gabansa tace "Yaya kai kadai xaka sha" Ya harareta yace "Toh da ni da wa xa mu sha?" Ta xaro ido tace "Wllh baxan yadda ba ni fa na sha wahala na dakko kaga irin gudun da nayi yanxu ma fa kirjina ciwo yake" banxa yyi da ita yana shan furansa don furan inna ba dai dadi da gardi ba, Ta fashe da kuka tana kallon sa, ya hade rai ya debi rabin ludayin hannunsa ya kai bakinta, ta turo baki tace "Wannan d'an kadan din bayan kai cika wanda xaka sha kake?" Yace "Baxa ki bude bakin ba" ta bude bakin da kyar, ya xuba mata yace "Toh tashi ki tafi" kamar jira take tace "Wllh baxan tafi ba ji fa abinda ka bani bayan ni na sha wahalan daukowa, Allah sai dai ka bani in mayar" Yace "In baki ki gudu da shi gidanku dai" Ta fashe da wani dariya har da kyakyatawa, ya harareta ya ci gaba da shan furan, kamar xata yi kuka tace "Yaya" ya kalleta sannan ya debo furan rabin ludayi ya kai bakinta, kin bude baki tayi tana masa wani kallo, ya kai bakinsa ya shanye, ta fashe da kuka, yayi light murmushi ya kara deba ya kai bakinta, bude bakin tayi ya juye mata, daga nan ya ci gaba da sha bai kara kallonta ba, kiris ya rage ta fashe da kukan gaske, ganin bai san tana yi ba ta fixge ludayin hannunsa, ya wara ido yace "Ke ina wasa da ke ne" ko kallonsa bata yi ba xata diba ganin xai dauke bowl din ta marairaice tace "Don Allah yaya ka bari in sha wllh baxan cika ba" yace "To diba in gani" ta turo baki ta ciko ludayin ta kai baki da sauri, ko shanyewa bata yi ba ya fixge ya juye ragowar a bowl din sannan ya diba ya kai baki, tana ganin haka ta dauke bowl din ta kai baki ta kwankwade ya xaro ido kafin yace komai suka ji muryar Inna cikin kuka tana cewa "Ahmadu idan ba a bi min hakkina ba yau a babbake ni cikin dare idan na kwana cikin gidan nan" Mikewa Mujaheed yyi da sauri xai bar wajen imaan ta mike ta rikosa a rikice tace "Wayyo yaya kai ne kace fa in dauko" Ya wani xaro ido yace "Ni?? You are sick, kar ma ki sa ni a maganan nan" daga haka ya bar gun da sauri don da dukkan alama nan suke taho, Imaan ta bi sa da gudu har suka iso gaban compound din gidan, ya wani hade rai yace "Wai me yasa kike bi na ne ma dai tukun?" Ta marairaice tace "Yaya kai fa ka sa ni" Ya xaro ido yace "Ohh dama idan nace ki shiga wuta sai ki shiga, kar ki kuskura ki ambato sunana a maganan nan" on a serious note ya fadi hakan, ta hararesa tace "Wllh kai ne kace in dauko da gudu in fito" xai yi magana suka ji alamar suna tahowa, inna na cewa "Kuma ko tantama babu wannan tantirin Mujaheed din da ka haifa ne xai sa ta, banda haka imaan ta san wani sace abincin mutane ta fita da gudu, wllh a min iyakan gaske da yaran nan a gidan nan yau, a kan me xa su dinga cutata suna ci min mutunci haka, wai har sun shanye furan sun bar min kwano a bayan window, me nayi masu a rayuwa xa su min haka" tana kai wa nan ta rushe da kuka, Anty tace "Kiyi hakuri don Allah inna" a fusace inna tace "Shegiya nake idan na hakura, a sace min furan a shanye kice in hakura kamar uwata tace min je ki kya gani, ae Aisha dai ta haifi fitina, wannan yarinya Imaan dai fitina ce wllh, a ma kira min Bukar yanxu, idan ban tada gidan nan da bala'i ba yau ace bani ba" da sauri Mujaheed ya nufi gate, imaan kamar xata fashe da kuka tace "Wayyo yaya" sai da ya kusa gate ya juya yana kallonta ya fara dariya kasa kasa, bin bayansa tayi da gudu, gun motarsa dake parke a kofar gida ta gansa xai bude maxaunin driver, ya buda ido yace "Wai me yasa kike bi na ne?" Ta karasa gun motar tace "Wllh yaya ni ba ni kadai xa a gani a gidan ba bayan ni da kai muka shanye, kawai Ammi ta kama ni ta min duka" ya daure fuska yace "Kinga ki juya ki koma ciki wllh" ta fashe da kuka ta make masa kafada, ya shige driver seat, ta bude front seat ta shiga tana turo baki, yace "Wai kin san inda xa ni" kin cewa komai tayi, jin an bude gate ya rufe door dinsa da sauri, Yusuf ne ya fito, Mujaheed ya tada motarsa ya yi zooming off, Yusuf ya dinga dariya mai gadi na kallonsa, sai da suka hau saman titi Mujaheed ya kalleta yace "Dama seriously idan kika kira sunana a case din nan wllh sai na sa ki kukan sati daya, sai ki gaya masu furan ma ke kadai kika shanye" Ta gefen ido ta kallesa kafin tace "Sai dai in ce masu ludayi daya da rabi kawai na sha sauran kuma ban san wanda ya shanye ba" Yace "Kina son in sauke ki nan kenan" ta marairaice tana kallon sa, yace "Toh me xaki fada masu a kan furan" a hankali tace "Cewa xanyi ayi hakuri ni da yaya muka shanye" parking yyi gefen titi, ta rikosa da sauri tace "Aa yi hakuri xan ce ni kadai na shanye" ya hade girar sama da ta kasa yace "Ki rantse" Kamar xata yi kuka tace "Bayan ni da kai muka sha"
Alhamdulillah, Thanks to all those that patronize the book *Imaan* Allah bar ku da iyayen ku, My book Imaan is for sale coz I am done with free pages tun friday, ni nasan it will go round as usual, I can't prevent that, but if you should come across it it's not for free, i repeat it's not for free, na siyarwa ne, wllh I am too grown up to say Allah ya isa, but have the fear of Allah SWT in u, don't forget it's my property, hakkina ne, wahalata ce, pay before reading, pay before reading, or you just over look it and smile, have a very good conscience plss, and a good conscience won't read happily without paying, if you want any favor pertaining to d book contact me and let me know, the book is 300 via..... Fcmb 3276052019
Hauwa Bello Jiddah
07087865788 and then u contact me through this digit to be added in the payment groups. Thanks once more for patronizing.
For those saying xa su same shi a banxa yana yawo to gashi... amma fa ba a banxa yake ba wllh, there is power in the tongue, Karamin hakkin da ka raina..... ππ
12. πβIMAANβπ
Gidan wani cin abinci Mujaheed yyi parking, yace "Ki jira in fito..." da sauri tace "Nima ba a cc abinda na ci wllh" ya kashe wayarsa kamar baxae ce komai ba sai kuma yace "meat pie daya ya ishe ki" kafin tace komai ya bude motar xai fita, da sauri tace "Yaya amma fa ban sa takalmi ba" da sauri ya kalli kafarta, yace "Good kinga sai ki jira ni in ci abinci in fito" Ta fashe da kuka tace "Wllh haka xan fito, ni fa ba abinda na ci tun da rana sai furan nan da ka tsammin" ya hade rai yace "Ki fito ki ja min kallo cikin mutane" ta marairaice tace "Yaya to mu je ka siya min ko bathroom slippers ne" yace "Ki dai jira yanxu xan gama cin abincin in fito" Bude motar tayi ta fito, ya xaro ido yana kallonta, Xata xagayo inda yake ya mata tsawa yace "Tsaya nan kar ki xo min nan" ta turo baki tana kallon sa yace "Dama ki tsaya sai na shiga sannan ki shigo, kuma ki nemi can nesa da ni ki xauna xan sa a kai maki abincin can" a hankali tace "Toh" Daga haka ya shiga yana waigota don tabbatar da ta bar distance sosai tsakanin su, Yana xaunawa sai ga ta ta shigo, ya wani hade rai ya dauke kai, tabe baki tayi ta nemi nesa da shi ta xauna ba tare da ta damu da kallon da ake mata cikin eatry din ba, jollof rice da half chicken yasa aka kawo masa da five alive drink sai bottle water, yana kallon waitress din yace "Ae kuna da meat pie koh?" Tace "Ehh har da burger da pizza with sausage roll duk akwai" yace "Good kinga wancan matar dake xaune at that far end?" Waitress din ta kalli inda yake nunawa ganin imaan tace "Ehh na ganta" yace "Ki kai mata meat pie daya da table water, ni xan biya bill din" tace "Ohk" daga haka ta wuce ta dau meat pie din da table water ta nufi gun Imaan tana ajiye mata a gabanta imaan ta kalli Mujaheed da ya dauke kai yana cin abincin gabansa, waitress din ta juya ta wuce, satan kallonta Mujaheed yyi suna hada ido ya juya kujerar sa yayi backing dinta yana murmushi yana cin abincin sa, Imaan ta dinga kallon sa amma ya ki juyowa, bayan kusan minti uku ya sake juyawa a hankali, kawai ganinta yayi a gabansa tana kallon sa kamar xata yi kuka, da sauri ya fara kalle kallen eatry din ya ga kallonsu kawai ake, ya xaro ido kafin yace komai ta ajiye masa meat pie da ruwan a gabansa ta jawo plate din abincin da drink ta dauka ta koma inda take ta xauna ta fara ci, Mujaheed bai ce komai ba ya dauke kansa, bayan kusan minti goma ya mike ya tafi ya biya kudin abincin da snack sannan ya dawo ya dau meat pie din da ruwa yana satan kallonta ita ma kallonsa take, mamaki ya cika sa ganin har ta kusan cinye shinkafar nama kuwa ta ma gama da shi, ya dauke kai ya nufi kofar fita, imaan ta mike da sauri ta dau sauran five alive din ta bi bayansa, a tare suka iso gun motar, ya bude driver seat ya shiga ita ma ta shiga gaba yace "Fita ki koma ki cinye abincin" tayi yar dariya tace "Dama fa nasan wucewa xaka yi ka bar ni shi sa nake ta kallon ka" ya hade rai yace "Fita nace" tace "Ai na koshi baka ga na cinye naman ba" tada motar yayi ya bar eatry din, bayan sun hau saman titi yace "Xan maida ki gida yanxu, wllh kika kuskura kika ce nasan komai a kan furan inna Allah xan sa ki kuka" da mamaki tace "Kai ina xa ka yanxu?" Yace "Gidana" ta fashe da kuka tace "Toh shine ni xaka maida ni gida, wllh kar ma ka kai ni don baxan fita daga motar nan ba" ya buda ido yace "Toh ina xan kai ki?" Ta turo baki tace "Mu tafi gidan ka tare" ya gyada kai yace "Tunda ke mahaukaciya ce ni ba mahaukaci bane" ta kallesa tace "Toh da ba ina xuwa ba" ya jefa mata wani kallo yace "Da ba yanxu bane" Shiru tayi ganin ya dau hanyar gida ta kamo sa tace "Don Allah yaya kar ka maida ni gida yanxu, wllh Ammi xata iya dukana don dama tace kar in dauko mata magana" yace "Toh ina xan kai ki?" Hawaye ta fara yi, yayi murmushi yace "Gobe baxa ki dauke ma tsohuwa furanta ba, ni dama ba ruwana" ta hade kai da gwiwa tana kuka a hankali, bayan few minutes yace "Abinda xai faru yanxu ina maida ki gida sai ki shige dakin Anty da sauri, ki kwana a can" ta dago tana goge hawayen idonta tace "Don Abba ya gani ko, kasan Ummi xata ce ma Abba