Showing 135001 words to 138000 words out of 303099 words
Bayan fitar ku daxu da yamma shine kawai na yanke shawarar tafiya wajen da ake casun ko minti sha biyar ne in yi in juyo duk da dai kun hanani, Toh ya xa ace bikin Mujaheed guda baxan je wajen casu ba, wllh Bukar mun shiga wajen da ake abun kenan mun xauna ko kayan kwalaman ba a fara rabawa ba sai ga Matar nan Rukayya tana haki wai in maxa in koma gida ance ruwa ya cika min daki da parlor, shine fa muka taho kamar mahaukata tare da Ta rasulu, muna shigowa gida in gaya maka sai muka ga bandaki a bushe tass babu ko digon ruwa balle ambaliyar ruwa, shine dai muka ta fada rai bace tare da Ta Rasulu nace mu koma wajen mu ji dalilin da ya sa xata gilla mana irin wannan karyar me tsada ko mu sa'annin uwarta ne, to fa muka dau adaidaita xa mu koma amma neman duniya mun wa wajen casun nan bamu gane ba haka muka ta walagigi a adaidaita sahu sanyin daren nan duk ya kare mana daga karshe muka dawo gida, yanxu fisabilillahi me na ma Rukayya xata min haka?" Daddy ya girgixa kai yace "Amma ba nace maki kada ki tafi wajen ba daxu da yamma Inna?" Inna tace "Bukar cewa fa nayi minti goma sha biyar kawai xan yi, ai da ban leka wajen ba wllh kullatata Mujaheed xai yi shi sa nace bari kawai in je a tsatstsaye in dawo, kuma meye laifina" Daddy yace "Haba Inna, yanxu fisabilillahi ki shirya ki shiga cikin yara ki xauna kice kin tafi wajen casu, me yasa kike mana haka don Allah?" Inna tace "Haba Bukar don dai minti sha biyar in juyo, wa ma xai san naje wajen banda mai sa ido? a baya fa muka xauna don ma kada a lura da mu" Daddy yace "Kwata kwata bai kamata, ban ga amfanin shiga cikin jikokin ki wai kinje casu ba, mu dai idan mun gaya maki magana baki ji baki amfani da shi, bamu san ko kina da wasu masu gaya maki bane bayan mu, ni bana jin dadin hakan da kike yi, kullum ayi ta magana amma baki gyarawa Inna, abinda baki sani ba a nan shine har mu kina xubar mana da mutunci a idon duniya...." Shiru Inna tayi sai 'yan idanuwa, a hankali ta Rasulu tace "Wllh Bukar sai da nace mata mu hakura kar mu je amma Asabe taki saurarata....." Juyawa Inna tayi tana kallonta baki sake, can ta kalli Daddy tace "Kaga xata gilla min sharri da rai na ko Bukar, to wllh ta ma riga ni shiryawa har tana cewa xata tafi ta bar ni ina bata mata lokaci, ni dai a dinga jin tsoron Allah ba ruwana" Ta rasulu tace "Yo idan ban ji tsoron Allah ba tsoron ki xan ji Asabe? Ke dai ki dinga bin 'ya yan ki sau da kafa baki da kamarsu, da Muhammadu ne yace min kada in tsallake ko nan da kofa wllh baxan tsallake ba, kawai ki sa mu shiga cikin jikokinmu mu xauna kamar wasu gantalallu har ana gilla mana karya don a kora mu...." Inna tace "Ni dai nace a dinga jin tsoron Allah ba ruwana, biki kuma gashi nan dai an gama sai kowa ya san na yi..." Ta Rasulu tace "Ina nan sai na raka Mujaheed gidansa na sa albarka...." Inna ta tabe baki tace "Toh naji na tafi casu ba da izinin ku ba Bukar, walakanta ni da Rukayya tayi fa??" Daddy yace "Ae ni na kirata nace ta fada maki haka saboda hakan kadai ke iya sawa ki dawo gida, don xuwan ki wajen bashi da fa'ida" Salati Inna ta saki tana kallonsa a hankali tace "Allah ya fi annabi sani...." Ta Rasulu tace "Toh ai da sauki tunda kai ne ka sa ta, kuma gaskiya da ba haka aka yi ma Asabe ba bata da ranan baro gun" Inna ta kalleta ta gefen ido ta rike ha6a tace "Ohh.. Naga abinda ya isheni, mutane dai basa tsoron Allah, da ranka ma sai an dinga bin ka da sharri" Mikewa Daddy yayi yace "Mu dai muna neman alfarmar ki dinga daukar maganar mu kina aiki da shi ba don mu ba don Allah..." Inna tayi kasa da murya tace "Toh ni dai kayi hakuri kuskure ne na riga nayi, sai dai Allah ya kyauta na gaba" Bai tanka ta ba ya fita parlon, Inna ta bi sa da kallo, Mikewa Abba yayi yace "Toh a dai yi hakuri inna" daga haka ya fita parlon shi ma ta bi sa da kallo, Mujaheed ya mike yace "Tsofe tsofe kice sai kin je casu..." Bai jira cewarta ba ya fice parlon yana murmushi ta bi sa da kallo, Yusuf ya mike ya fita parlon shi ma ta bi sa da kallo, Aunty dake kokarin danne dariyarta ta mike tace "Toh don Allah kuyi hakuri Inna" Inna ta tabe baki bata dai ce komai ba, Aunty tace "Bari in je Inna, muna aiki ne" daga haka ta fita, Ammi ma tayi mata sai da safe ta fita, tagumi inna tayi bayan duk sun fita tace "Lallai Bukar ya xama abun tsoro Ta Rasulu, ni da ba don a kan idona na haifosa ba ma sai ince canjin sa aka min a tsinannen asibitin turawan da na haifesa, ke kiji ashe shi yasa katuwar mata ta kirani ta gilla min karya, duniya ta lalace ni patuu" Ta Rasulu tace "Ai yanxu darajar sa Rukayya xata ci baxa mu daukaka kara ba, amma wllh bata ci bulus ba, ki kyale Yar iska Allah ya kai mu wayewan garin gobe lafiya" Inna tace "Shi kuma Bukar dama kada ya sake tako min nan tunda haka ya xama, ba ruwana ya je yyi ta kansa" Ta Rasulu tace "Atoh, ni da ace Salihu ne da na masa barbadin bala'i ynxu...." Mama Hadiza dai sai kallonsu take daga inda take xaune, Inna tace "A'a ni dai gwara da na bar figaggen da halinsa ba ruwana ace naje ina cecekuce da shi, gwara kawai da na masa shiru ya gama bambaminsa ya fita, ae shi Ahmadu baya haka, dama ni ban so ya shigo ba sai Ahmadu ya gama yanke hukunci, Toh sai gashi Allah ya jefo mana shi, haka kawai inje inyi magana bafillatanar matar sa ta ji haushi na ta kullace ni, A'a ba ruwana" Ta Rasulu tace "Dama shirun ya fi ina xaki tsaya cecekuce da d'an cikin ki?" Inna ta tabe baki tace "Ni dai ba ruwana, Allah ya shirye sa, amma Bukar gaskiya ba shi da hali duk cikin 'ya yana"
Washegari tun da imaan ta tashi take jin xaxxabi da ciwon kafa, har karfe tara bata fito ba don ko Ina a gidan cike yake da jama'ah, Maryam dai tun da ta kawo mata breakfast dakin bata sake ganinta ba, Ammi ce ta shigo dakin karfe goma saura ganinta kwance ta karasa kusa da gadon tana kallonta tace "Lafiya?" Mikewa xaune tayi da kyar tace "Ammi kamar xanyi xaxxabi kuma kafana ciwo suke min" Ammi ta kai hannu jikinta ta ji da xafi, Juyawa tayi ta fita ta wuce kitchen ta hado mata wani shayin ta dawo tace "Kin ma yi wanka?" Kai ta gyada ma Ammi, Ammi ta mika mata shayin tace "Ki sha shayin sai ki sha drugs din ki" karba Imaan tayi ta fara Shan shayin Ammi ta dauko drugs dinta inda suke ta ballar mata bayan ta sha kusan rabin shayin Ammi ta mika mata maganin, Karba tayi ta sha Ammi tace "Ki tafi can bangaren Inna ki kwanta baki xa su sauka nan xuwa anjima kadan" Imaan ta xaro ido tace "Ammi bandakina fa?" Ammi tace "Ku dai ba ku da hali mai kyau abu dai na kwana daya, to sai ki kinkimi bandakin ki tafi da shi bangaren Inna ki ajiye" Imaan kamar xata yi kuka tace "Wllh bata ma mutum fa xa su yi, ni dai gwara in kulle in boye makullin" Ammi tace "Toh ki kulle tunda baki da hankali" Imaan bata ce komai ba Ammi ta juya ta fita, Mikewa tayi da kyar ta kwashe gaba daya kayan cosmetics dinta dake gaban madubi ta xuba su drawer, ta cire farin bedsheet dinta ta dau mai duhu ta shimfida tana turo baki, ta shiga bandaki ta dauke sabulu da sponge dinta sai brush da toothpaste ta dawo daki ta adana, hijab ta saka bayan ta dau sabbin kayanta na biki da xata saka a cikin leda ta fita dakin tana dingishi, babu yanda ta iya haka tayi ta gaida mutane har ta isa part din Inna, Ta Rasulu ce tsaye bakin kofa tana kallon tsofaffin da ke xaune cikin parlon tace "Don Allah ba don mu ba idan kun cire takalma a dinga ajiyewa a gefe guda kar su bata bakin kofar, bikin fa na yan gayu ne, haba takalma sai kace na masu talla" Imaan ta raba ta gefenta ta shiga parlon, daga kitchen Inna ya fito rike da cooler da plate ta duka tace "Toh ni dai basu gama girkin ba ina ji, wannan dai 'yar wainar da aka xubo min ne da safe sai in manna ma kowa guda biyu, ga miyar taushen mai kyau da nama...." Kallon Imaan dake gaida mutanen parlon xata wuce daki Inna tayi da sauri tace "Waye wannan kuma?" Juyowa Imaan tayi ta hade rai tana kallonta, Inna ta mike tace "Me xaki je ki min a daki??" Imaan ta marairaice tace "Inna baki suna dakina ne kuma bacci nake son yi" Inna tace "Naga abinda ya isheni, to Ina ruwanki da bakin Imaan? Gaskiya ni dai kiyi hakuri ki xo ki wuce na saka ma dakina turaren wuta kuma ma wannan mutumin...." Ko sauraranta Imaan bata yi ba ta shige dakin da sauri tana turo baki ta kulle, juyawa tayi, tayi still ganin Mujaheed kwance saman gado... Ta xaro ido tana kallonsa, A hankali Imaan ta bude kofar xata fita sai kuma ta juya tana kallonsa, Bude ido yyi yana kallonta shi ma, ta turo baki ta fita da sauri ta kulle kofar. Inna dake ta xuba waina a plate tana diga miya kamar xa a ba jarirai ta kalleta tace "Har kin fito knn, toh sai ki koma ki tambayar min shi ko in xuba masa wainar, tun safe yake nan ni dai ban ga ya ci komai ba, to rabuwa da ni haukane da xai daga hankali haka? Ni dai ba ruwana" Imaan xata fita Inna tace "Ji walakanci ina mata magana tana wucewa, baxa ki shiga ki tambayar min shi bane in je da kai na?" Dawowa tayi tana turo baki ta shiga dakin, Inna tayi tsaki tace "Babu abinda ta mance a halin ubanta mara kirki, nan ya wanke ni tass jiya da daddare, ni dai na yafe masa ba ruwana, ba don naka naka bane ai yanxu da sai dai in kora figaggiyar 'yar nan tasa ince ta fita, Toh kada laifin ubanta ya shafeta" Imaan na komawa dakin ta samesa idonsa rufe kamar daxu, ta d'an yi jim, can ta karasa kusa da gadon tace "Inna tace ta xubo maka wainar shinkafa?" shiru yyi har sannan bai bude idon ba, tace "Ka ji" nan ma bai ce komai ba, ta d'an ta6a kafarsa tace "Yaya ka ji?" Nan ma shiru kake ji, tabe baki tayi ta juya xata wuce ya fixgota ya bude manyan idanuwansa da suka sauya kala yace "Sai kin min ihu a kai saboda baki da hankali?" Shiru tayi tana kallonsa, can ta ta6a hannunsa ta durkusa kusa da shi a hankali tace "Baka da lafiya ne Yaya?" Mikewa xaune yyi ta dinga kallonsa, murya can kasa yace "Make me a cup of tea" Mikewa tayi ta nufi kofa ya bi ta da ido, Inna dake duke har sannan tana jiran ta fito tace "Xai ci ko in rabar ma tsofaffin nan?" Imaan tace "Shayi yace in kawo masa" bata jira me Inna xata ce ba ta shiga kitchen ta dau cup ta bude flask ta xuba ruwan xafi a cikin cup din sannan ta dawo tana kallon Inna tace "Ina Kayan shayin?" Inna tace "Wanda ke da shi ku ka siyo ku ka ajiye min kenan, toh kar ma ki bata lkcn ki ki koma bangarenku ki xuba masa kayan shayin a ruwan xafin nawa ya kusa karewa bbu wanda xan ba ma wllh" Wata tsohuwa dake xaune parlon tace "Haba Hajiya Asabe sai kace ba iyayensu ke siya maki ba?" Inna ta mike tana kallonta, can tace "Ehh lallai duniya ta lalace, toh wllh har na mance rabon da iyayensu su siya min kayan tea, sai dai yaron nan Bulasawa, kuma baya jiran wani ya kare yake kawo min wani, kawai mata tsohuwa baki san kan komai ba ki tsomo mana baki muna magana, ni dai ba ruwana a dinga jin tsoron Allah" Tuni imaan ta fice ta wuce part din su tana turo baki, Bedroom dinta ta fara shiga ta dau wayarta tayi dialing number Sadeeq, katsewa yyi ya kirata, a hankali tace "Good morning...." Yace "Morning my dear, hope kin tashi lafiya?" Imaan ta langwabar da kai tace "Sure, happy birthday once again..." Yana murmushi yace "Thanks much baby, I was so happy with ur text earlier this morning, naji dadi sosai baby" murmushi tayi tace "When xaka xo ka amshi gift din ka?" Yace "Ohh wai baxa ko xo party din ba?" A hankali tace "I might, I might not, kasan fa yau muna biki a gida.... But all the same ka dai xo ka fara amsar gift din ka" yace "Ni dai sai kin xo party din dear" murmushi tayi tace "Na ji" yace "Toh yaushe xan taho amsar gift din?" Tana juya ido tace "After Juma'at prayer" Yana murmushin sa mai kyau yace "Toh sai na xo baby" tace "Amma fa kar ka shigo layinmu, ka tsaya bakin titi xan fito" yace "Alryt dear xan kira ki idan na iso" tace "Tohm bye" daga haka ya katse wayar. Kitchen ta wuce don hada ma Mujaheed shayi, Ammi dake bayan kitchen din da Mama Hadiza suna magana tana kallon Imaan ta window tace "Me kike nema?" Imaan tace "Inna xan xuba ma kayan shayi nata ya kare" Ammi bata ce komai ba suka ci gaba da maganan su da Mama Hadiza, imaan ta hada shayi mai kauri ta rufe cup din ta fita, Ko kallon Inna bata yi ba ta shige cikin daki Inna na cewa "Ni dai dakina ya xama kamar kasuwa yau duk a tafi a bar ni da wari..." Ajiye shayin Imaan tayi tana kallonsa tace "Gashi yaya" ya bude ido ya mike xaune ta dau shayin ta mika masa tana kallonsa ya karba, makulli ya mika mata yace "Go to my bedroom and get me my phone" ta xaro ido tace "Ni kuma? A'a sai da in gaya ma Maimoon ta dauko sai ta bani, ni ba ruwana" Bai ce komai ba ya dinga sipping shayin a hankali, Mikewa Imaan tayi ta fita, tana fitowa parlon Inna ta kusa cin karo da Mama Hansai "Inna na ciki kuwa? Ga Ta Rasulu can tana fada da Hajiya Rukayya" Cewar Hansai kenan tana haki ta shige parlon Inna, Imaan dai tayi wucewarta, tsakar gida ta tadda ta Rasulu tsaye tana fadi Umma na fadi, Ta Rasulu na tafe hannu tana jujjuya ido tace "Nan nan aka auro ki kina raka yayarki Shafa tallan shinkafa da wake a kasuwar tasha, Hijabi duk a yakune, Zani duk duwaiwai a waje tsabar kodewa shine kin xo kin samu gida kin xama kamar buhun masara xaki kawo ma mutane raini toh wllh idan ban sa yarana mata sun nakada maki shegen dukar da xai fidda maki hakora uku ba kice ba Yar gidan mai salati bace ni, Ni nafi karfin ki wllh ni ba Asabe bace...." Muryar Inna suka ji tana sakin salati da karfi tace "Rukayya ita aminyar tawa ta Rasulu kike ma xagi ta uwa ta uba?? Ita ta rasulun kike kokarin dambe da?? La ila ha illallahu Muhammadur rasulillahi sallallahu alaihi wassalam, karshen duniya ta kama, ayi maxa a kira min Ahmadu amma banda Bukar...." Imaan ta girgixa kai tayi wucewarta ciki ta wuce sama, bude kofar dakin Mujaheed tayi ta shiga ta lumshe ido ta nufi saman gadonsa ta dau wayarsa, calls kusan ashirin yyi missing, yawanci kuma duk na Safeenah ne sai abokansa dake ta nemansa tun safe, ta tabe baki ta juya xata fita sai ga kira ya kara shigowa wayar, kallon screen din tayi ganin Safeenah ne tayi tsaki har ta isa kofa sai kuma ta daga ta kai kunne tayi shiru, daga daya bangaren Safeenah tace "Haba Mijina, tun asuba Ina ta kira no response are you okay?" imaan ta tabe baki tace "Toh ba shi bane" Da mamaki Safeenah tace "Wacece wannan?" Imaan tace "Kanwarsa ce, sai ki jira idan na kai masa wayar" bata jira cewarta ba ta katse kiran ta fito dakin ta kulle kofar. Ba karamin taro aka hada a tsakar gida ba Inna na ta ma Umma tijara Ta Rasulu na taya ta, ba abinda suka mance basu gaya mata ba, mutane sai bada hakuri suke, Ammi dama ko a gyalenta sai aikinta take, haka ma Mama Hadiza da ta ki fitowa, Aunty ce dai ta taho tana bada hakuri Inna ta tsigaleta ita ma ba shiri ta bar wajen, inna na ganin Imaan ta fixgota tana nuna ma jama'ah ita tace "Tana kamar haka fa Ahmadu ya aurota, amma yanxu ku dubi yanda ta koma kamar alade, Toh komai ta samu raruma take ta boye... ya ki halal ya ki Haram, duk ta tsiyace min d'a na... Shine kuma saboda abinci xata yi ma aminiyata rashin mutunci... Allah ya tsine ma abincin da xa aje a xaxxage a shata, tunda a kansa xaki xagar min Ta Rasulu, to wllh yau sai Ahmadu ya xaba ko ni ko ke a gidan nan ba ruwana, dama har yanxu ban huce casun da kika hanani ganin