Showing 102001 words to 105000 words out of 303099 words
ba?" Imaan ta hade rai tace "Toh nawa ne da xan gwada?" Inna tace "Oh oh Allah, yau naga fitina, to Ina ruwana da ko na waye, ni dai ba kawai in cire ma takwarata ba tunda ni baxan iya sa wa ba?? Ki gwada don Allah" Imaan dai bata ce mata komai ba ta xauna, Inna ta ajiye takalmin gefenta tana kallon Mujaheed dake tsaye tace "Toh da kaki gaya min xaka yi aure Mujaheed sai aka yi yaya? Sai aka dinga yagan naman jikina? Toh baxa dai a taba canxa ma tuwo suna ba, bauta dai na riga na gama maka sai dai Allah ya saka min da alkhairi, Amma kar dai ka manta akwai ranan sakamako" Mujaheed bai ce mata komai ba ya xauna kan kujera ya jinginar da kansa da kujerar a hankali yace "Akwai ruwan xafi?" Inna tace "Wanda Rukayya ta hado tare da akwatuna ta kawo min ba?" Mikewa Imaan tayi tace "Sai da safe Inna" Inna ta kalleta da sauri tace "Sai da safe bamu gama kallon kayan ba?" Imaan bata ce mata komai ba ta nufi kofa, Mujaheed ya bi ta da kallon gefen ido har ta fita sannan ya mike ya bi bayanta, Inna tayi tagumi tace "Naga abinda ya isheni ni patuu, wannan d'a na Ahmadu dai fitinanne ne, Ina lura da yarinyar nan gaba daya ta fita harkan ka a gidan nan, da ta ganka xata yi ta kanta ta bar wajen, gaba daya ta ma mayar da kai dodo, Ina kuma lura hakan na damunka ainun sbda baka samu damar dinga cutarta ba, to meye kuma xaka wani bi bayanta bayan bata kula ka ba, Ni dai gwara ma ayi auren nan ka kama gabanka jikata ta huta nima in huta da maganar ka haka, wllh ka cika fitina ko don maman Rukayya ka sha oho, tunda ita ma dai fitinanniyar ce" Juyawa Imaan tayi jin tafiya a bayanta, sosai gabanta ya fadi ganin shi ke bin ta, sai dai bata gudu ba sai kara saurin ta da tayi, ji tayi ya juyo ta har sai da ta kusa fadawa kansa ta fixge kanta gabanta na faduwa, a fusace tace "Meye haka yaya?" Kallonta ya tsaya yyi da wani expression, kamar xata yi kuka tace "Ni ka sakeni" Calmly yace "Me yasa kike gudu idan kin gan ni?" Kin cewa komai tayi, taji gaba daya she is very uncomfortable unlike before da bata ki ma ta fada jikinsa ba ta fara masa shagwaba, Yana kallonta yace "Imaan!" Kasa kallonsa tayi, ya dago kanta yana kallon manyan idanuwanta, turo baki tayi, and he couldn't stop looking at her, haka kawai yaji ya samu relieve din abubuwan da dama da ke damunsa, Yace "Answer my question now, me yasa kike gudu idan kin gani" sauke idonta tayi kasa calmly tace "Nothing..." jin shiru bai ce komai ba bayan few seconds ta daga kai ta kallesa taga kallonta yake, sauke idonsa yyi cikin cool voice dinsa yace "Saboda na amshi wayar ki?" Ta kallesa kafin tace komai ya ciro wayar a aljihu yana mika mata yace "Take..." bata san lkcn da tayi murmushi ba ta langwabar da kai tace "Ae daddy ya ce xai siya min wani soon" ya daure fuska yace "Take it now..." ta make kafada tace "Ni bana so kuma" yace "Take before I knock you" kamar xata yi kuka ta amsa yana kallonta yace "Shi kenan?" Tace "Ehh" wani boyayyen ajiyar xuciya ya sauke, ta d'an yi jim, sai kuma tace "Aunty Farida xa a kai ma kaya?" Kasa cewa komai yyi ya saketa ya juya ya koma part din Inna, ta bi sa da kallo kafin ta juya ta wuce part dinsu tana kallon wayarta. Mujaheed na komawa part din Inna ya tarar tana ta fiddo kayan akwatuna, ya xauna yana kallonta yace "Nima fa ban san an fara hada kayan lefen ba shi yasa ban gaya maki ba, sai daxu Umma ke nuna min" Inna tace "Ni dai ba ruwana, ku dinga jin tsoron Allah, don an gaya min ai ba gafara aka min ba...." Wani jallabiya mai kyau da tsada ta daga tana nuna masa tace "Wannan ai xai ma takwarata koh?" Kallonta ya dinga yi, jin yyi shiru ta ajiye gefe ta maida sauran ta rufe jakar, ta nuna masa takalmin da ta ba Imaan ta gwada tace "Wannan ma ai dai dai ita ne koh?" Nan ma dai bai ce komai ba ta ajiye gefenta, body spray biyu ta dauka ta ajiye gefenta tace "Sai ta dau daya ta bar min daya" murmushi Mujaheed yyi bai dai ce komai ba, Inna ta bude akwatin jewelries, ta dinga kallon dankunnaye da sarakuna masu kyau, kala biyu ta cire tana kallonsa tace "Wanne ya fi kyau cikin wa enannan?" Shi dai bai ce mata komai ba, ta ajiye biyun a gefenta tace "Sae ta xabi daya a mayar masu daya" bude pack din jan baki tayi ta cire uku tace "Duk da dai ba shafawa take ba sai ta ba Maimoon daya ta rike biyu" Kaf kayan sai da Inna ta bi ta cire daddaya ta ajiye ma Imaan sannan ta rufe jakunkunan ta jera su yanda suke, ta kwaso kayan ta xube su gaban Mujaheed tana kallonsa tace "Ko ban kyauta ba Mujaheed?" shi dai bai ce komai ba ta kwashi kayan ta kai daki ta fito tace "Toh ai faridan ma ya kamata ta xo ta gaisheni kafin a kai kayan, kwana biyu shiru bata xo ba" a hankali Mujaheed yace "Ba Farida xa a kai ma kayan ba..." Inna ta gwalo ido tace "Wa xa a kai ma?" Yace "Wata ce daban" Inna ta xauna kan kujera ta saki salati tana tafe hannu tace "Wayyoo.. Amma dai kai shahararren mayaudari ne Mujaheed, yanxu dama yaudarar yar mutane ka dinga yi ba aurenta xaka yi ba? Kasa yarinya ta kashe d'an kudinta ta siyo min turare duk da ba mai tsada bane, Mujaheed anya kana son wanyewa da duniya lafiya kuwa? Ina laifin yarinyar, kyakkyawa ce fa doguwa" Mujaheed dai kallon kasa kawai yake bai ce mata komai ba, ganin ynda ta dage tana kiransa da mayaudari ya dago ya kalleta yace "Umma ce bata son aurena da ita, shine ta hada ni da yar kawarta..." Inna ta xaro tace "Auzubillahi, yanxu Rukayya ce ta hanaka aurenta? Toh kuwa akwatunan nn babu inda xa su daga parlon nan sai gidansu Farida, yarinya mai hankali da natsuwa, tun da naga ynda take ji da Imaan take sonta naji nima ina sonta" Da sauri Mujaheed yace "A'a ita ma fa iyayenta sun riga da sun mata miji har an sa rana" Inna ta saki baki tana kallonsa, can tace "Toh wacece wannan kuma xa ka kwaso mana?" Ya d'an yi murmushin karfin hali yace "Idan anyi auren xaki ganta" Inna tace "Sai ka kawota ai ta gaisheni ba ruwana, Amma dai kun yaudara juna da farida tunda gashi ita ma har an mata miji kace, ohh mutane dai tsoron Allah yayi karanci a xukatansu, yanda ka taso gabana Mujaheed bai ci ace baka da tsoron Allah a xuciyarka ba, Toh ko da yake ai Rukayya ce ta haifeka, Ahmadu da na haifa ai gashi yana tsoron Allah, haka ma Bukar, duk basa yin abinda Allah ke fushi da, banda haka kayi ta xuwa gun yarinya kuna tadi ashe ba aurenta xaka yi ba??" Shi dai Mujaheed kallonta kawai yake, bude kofa aka yi Abba ya shigo, Inna ta tsuke fuska, Mujaheed kadai ya amsa sallamansa, Abba ya xauna yana kallonta yace "Ina yini" tace "Toh ni da aka ki gaya min xa a kai ma Mujaheed lefe sai aka yi yaya??" Abba ya girgixa kai yace "Kiyi hakuri, ni ma ba a gaya min da wuri ba Inna" Inna tace "Kai dai ka ajiye bala'i a gida kawai kuna xaune, banda haka ya xa ayi d'an ka a boye maka xa a hada masa lefe?" Mikewa Mujaheed yyi yana kallonta yace "Sai da safe" tace "Tou yaushe xa a kawo min yarinyar?" Yace "Ehh xa a kawota in sha Allah" daga haka yayi ma Abba sallama ya fita. Washegari Thursday Imaan na dawowa schl bayan ta yi wanka ta ci abinci ta shirya ta tafi part din Inna, Inna dake bakin pampo ta biyota ciki tace "Duk na cire maki kayan na boye maki a sif" Imaan ta xaro ido tace "Ni dai ba ruwana Inna" wani kallo Inna ta mata ta xauna kan kujera tace "Toh ni da ruwana, sai in ga wanda xai ce min don me" Imaan ta tabe baki ta xauna, inna tace "Daxu Bulasawa ya kirani muka gaisa, ni dai tunda uwata ta haifeni ban taba ganin yaro mai hankali da kirki irin yaron nan ba..." Imaan ta dai yi murmushi bata ce komai ba, Inna tace "Bayan mun gama waya ni dai nace masa iron dina ya lalace" Imaan ta xaro ido tace "Kika ce masa haka Inna?" Inna tace "Toh baxan ce ba, tun yaushe nake bin Bukar da Ahmadu su siya min sai su ce sun mance, dama wannan yaron isuhu kadai ne xan ce ma abu ya min nan take, shi Mujaheed ban ma sa shi a layi, ko ya siyo sai ya kai ma wancan katuwar matar, to wai ni isuhu na gidan nan ma kuwa?" Imaan ta bude hannu alamar bata sani ba, Inna tace "Ikon Allah ni toh bai xo ya ce min xai yi tafiya ba... Kai bari dai inje bangaren nasu inji lafiya, bai taba min irin haka ba da ma dai Mujaheed ne ni baxan damu ba" Inna ta saka Hijabi da ta dauko tace "Tashi ki rakani, ba lafiya yau kusan kwana goma ban ga isuhu ba, to ko bai da lafiya ne" Imaan ta mike suka fita parlon, Inna ta rufe kofar ta da makulli Imaan tace "Inna to meye na sa makulli" Inna tace "Baxan sa makulli ba? Ko datti ya shiga parlon ba a cuce ni, ko Kandangare ya ji shiru yana iya shiga in shiga uku" Imaan tayi gaba Inna ta bi bayanta tana cewa "Don Allah ki dinga cin abinci mai yawa Imaan, kinsan fa Bulasawa mai mutane ne, haka xa a ga amarya kamar tsinken tsire a sa mu a bakin duniya, ni dai ki rufa mana asiri" imaan dai bata tanka ta ba har suka iso part dinsu Maimoon, Inna ta shiga parlor tana kallon Ummi tace "Ke Isuhu na nan?" Bata jira cewarta ba ta wuce sama tana kallon stairs din palon tace "Matan Ahmadu dai kazamai ne, dubi fa yau basu goge nan ba ina ga" dakin Anty ta bude Aunty ta mike ganinta tace "Sannu da xuwa Inna" inna tace "Kwana biyu ban ga isuhu ba ko ke kika hanasa xuwa inda nake" Aunty tace "Ni na isa Inna, ban ma san bai je ba ai, yanxu dai baya nan" Inna tace "Toh yana dawowa kice ya xo ina nemansa" Aunty tace "Toh" Imaan ta gaida Aunty, Aunty ta amsa da fara'a, Umma ta leko ganin Inna ta koma ciki da sauri ta rufe kofarta, inna ta juyo tace "Toh ita kuma mai hada lefe ana ciki kenan, Toh dai baxan shiga ba" daga haka ta fara sauka stairs din Imaan ta bi bayanta. Bayan magrib Imaan na part din Inna Mujaheed ya shigo, xaunawa yyi ya gaida Inna da ke cin abinci tace "Mujaheed ni fa ban ga isuhu ba har yanxu, ban san me ya faru ba" Mujaheed na kallon boxes da ta jera yace "Inna xa a mayar da akwatunan can gida" Inna ta ajiye cokalin hannunta tace "A kan wani dalili?" Yace "Ai ba a gama xuba kaya ba" Inna tace "Toh sai a dinga xuwa nan ana xuba su, in dai kaga an fitar da akwatunan nan daga parlona to gidan amaryar xa mu tafi kai wa, ai ba wani ya min wahala da kai ba, ko Ahmadu da na haifa ban masa wahala yanda na maka ba, Rukayya dai ta shiga hankalinta a gidan nan ta daina shiga hurumin da ba nata ba" Bai kuma cewa komai ba, ya kalli Imaan dake xaune tana kallo, ta gefen ido ta ga yana kallonta ta mike tace "Sai da safe Inna" daga haka ta fita parlon, Bai dade xaune parlon Inna ba ya mike ya fita, yana isa part dinsu Imaan ya shiga balcony ya danna bell sannan ya bude kofar, Ammi dake xaune parlor ta dinga kallonsa har ya shigo, kasa kallonta yayi ya dukar da kansa ya xauna saman kujera yace "Ina yini Ammi" Ammi tace "Lafiya lau ya aiki" yace "Alhmdllh" tace "To maa sha Allah" kasa cewa komai yyi, can yana shafa kansa yace "Ammi dama..." Sai kuma bai ce komai ba, Ammi tace "Dama me?" Yace "Ina son Imaan xata rakani ne" Da mamaki Ammi tace "Ta raka ka ina?"
Yanxu xan dinga update twice sbda xan rage tsayin rubutun, sai kuma da daddare in sha Allah.
*The book Imaan isn't free, you read for free ur cup of coffee...*🤷🏻♀️
It's 300 via
Fcmb 3276052019 Hauwa Bello Jiddah, then you show ur evidence of payment through my WhatsApp digit 07087865788 to be included in d payment group.
34......
Mujaheed ya kalleta yace "Ina son xan je gidansu Farida ne" Ammi tace "Wace faridar? Wace ku ka yaudara ko wata daban?" Shiru yyi bai ce komai ba, Ammi ta tabe baki ta maida dubanta kan TV, yace "Ni ban yaudare ta ba Ammi, kila hakan Allah ya tsara we are not destined to be together" Ammi tace "Toh yayi kyau, haka Allah ya tsara" Bai ce komai ba, can ta kallesa tace "Toh me xaka je ka mata?" Yace "Ina son xuwa in bata hakuri ne, idan ta gan ni da Imaan she might listen to me, bana son tayi tunanin yaudararta nayi" Ammi tace "Toh Allah ya kyauta, amma yanxu dare yyi sai ka bari gobe" yace "Gobe da safe xata wuce kano" Ammi ta girgixa kai, tace "Toh ba sai ku tafi har da Maimoon ba" yace "Eh xa mu je tare" Ammi tace "To ka turo Maimoon din xa su fito tare" yace "Toh nagode" daga haka ya mike ya mata sallama ya fita parlon, Ammi ta mike ta shiga dakin Imaan xaune ta sameta tana karatu, Ammi tace "Ki shirya ke da Maimoon xa ku raka Mujaheed wajen Farida" Imaan ta xaro ido tace "Yaya kuma? A'a ni Ammi baxan je ba" Ammi ta dinga kallonta sannan tace "Me yasa?" Girgixa kai tayi tace "A'a ni bacci nake ji" Ammi tace "Me ya hada ku da Mujaheed din?" Da sauri ta kalli Ammi sai kuma ta dauke Kai tace "Ba komai fa Ammi" Ammi tace "Toh tashi ki rakasu ku dawo" daga haka Ammi ta fita dakin, da kyar Imaan ta mike har ranta bata son bin Mujaheed, can dai ta sa Hijab dinta har kasa ta fito, dai dai nan Maimoon ma ta shigo parlon, Ammi na kallon Imaan tace "You pray before leaving, and ku kula" A hankali Imaan tace "Toh" daga haka suka fita tare da Maimoon bayan ta gaida Ammi, a waje suka samesa yana jiransu cikin mota, Maimoon ta shiga back seat, Imaan ta hade rai ta shiga ita ma, Maimoon tace "Ki tafi gaba mana" Imaan tayi mata banxa ta rufe motar, Mujaheed yace "Wata ta dawo gaba, I am a driver to none of you" Maimoon ta turo baki ta bude motarta ta fita ta koma gaba, tada motar yyi suka dau hanyar titi, lkci lkci yake kallon Imaan dake kallon waje, gidan yayar Farida dake unguwar sanusi suka tafi, Mujaheed yyi parking kofar gidan ya kashe motar, yace "You two should go in, ku ce mata I am outside, she isn't picking her cals" Imaan ta bude motar ta fita, Maimoon ma ta fita suka shiga gidan a tare, A parlor suka tadda yayarta da yaranta uku, tana kallonsu ta amsa sallamarsu, Imaan ta xauna ta gaisheta Maimoon ma ta gaisheta duk ta amsa amma da alamar bata gane su ba ma, Maimoon tace "Aunty Farida fa?" Yayar tace "Tana daki" karamin yaronta ta aika ya kirata a daki, sai ga ta ta fito, tsaye tayi tana kallonsu, can tayi murmushi tace "Sannu ku da xuwa" Imaan tace "Ina yini Aunty farida" Farida ta xauna tace "Lafiya lau Imaan ya Ammi fa" Maimoon ma ta gaisheta ta amsa tace "Daga Ina ku ke haka da daren nan?" Imaan tace "Daga gida mana" Murmushin fuskarta yayi fading tace "Toh a xubo maku abinci" Imaan tace "A'a mun ci abinci, Aunty farida Ammi ce ta aiko ni" Farida tace "Ayya, toh ina jin ki" Imaan tayi murmushi tace "Ko xa mu je waje?" Farida ta mayar mata da murmushin sannan ta kalli yayarta tace "Anty kanin Mujaheed ne" lkci daya yayar ta hade rai ta ci gaba da kallonta, Imaan ta mike tayi ma yayar sallama Maimoon ma haka sannan suka fita, Farida ta mike ta bi bayansu, mamaki ya kamata ganin sun fita wajen gate don ta xaton cikin compound din Imaan xata bata sakon Ammi, ta dai bi bayansu har waje, sosai gabanta ya fadi ta tsaya tana kallon Mujaheed dake tsaye jikin mota ya rungume hannunsa, ta sunkuyar da kai ya karasa har inda take, Juyawa tayi xata koma ciki ya kamo hannunta a sanyaye yace "Pls listen to me Farida" kasa kallonsa tayi hawaye ya kawo idonta, sosai jikin Imaan yyi sanyi, Maimoon ta bude mota ta shiga don ita ma ta bata tausayi, cike da karfin hali Mujaheed yace "I neva meant to break ur heart Farida, even for once, but you know Allah plans best, may be we were neva destined to be together, ki yafe min pls, Umma ta bata son aurenmu and I can't disobey her" Hawaye na xuba idonta tace "Allah yasa hakan yafi alkhairi, and I am wishing a happy married life in advance" a sanyaye yace "Forgive me plss Farida" ta gyada masa kai da kyar tace "I have done that in