Showing 117001 words to 120000 words out of 303099 words
ido tana kallonsa, tsawa ya mata yace "Baxa ki bani amsa ba sai na baki dirty slap?" Tsorata tayi ganin babu wasa fuskarsa, kamar xata fashe masa da kuka tace "Ni fa Yaya...." Fixgota yayi lkci daya idanuwansa suka canxa yace "Ke fa me?" Kasa cewa komai tayi, ta hadiye abu da kyar tace "Don Allah kayi hakuri, ni bani na basa hannun...." Bai jira ta karasa ba ya buge mata baki da karfi, Ta kai hannunta da sauri bakinta, lkci daya hawaye ya kawo idanuwanta, cikin husky voice yace "I am making you this promise... babu abinda xai hanani gaya ma Abban ki sooner or later...." ta wani gwalo ido a rikice tace "Don Allah Yaya kayi hakuri wllh ba da gangan yayi ba shi ma bai sani ba" Bai san lkcn da ya kara buge bakinta ba, tayi tsit hawaye na sauka idonta, yace "Wato ke yanxu kina ganin kin girma kin isa tadi da maxa, har wani rawan jiki kike ki fita idan ya xo, har da jan sa xuwa parlon ku ki ajiye masa nama a gaba Saboda kinga Inna na goya maki baya, to bari ki ji abinda baki sani ba, as far as I Muhammad is concerned babu aure tsakanin ki da mutumin nan, you had better stop wasting ur time and face ur study, kamar yanda na xa6a ma Seeyama miji ke ma haka da kai na xan xaba maki mijin da ya dace da ke, duk ki gama rawan kanki xaki sha mamaki na, wannan mutumin da kike gani is just here to spoil and use you, ba so na tsakani da Allah yake maki ba, ki bar ganin yana kashe maki kudi ki xata wai son Allah yake maki, lalata maki rayuwa xai yi which I will neva allow, and let me give you this warning....." Ita dai hawaye kawai take xuciyarta na bugawa tana kallonsa, "Daga yau kika sake tsayawa kusa da motarsa sai na kusa sumar da ke wllh, duk karyar da xai maki ya maki a waya ba sai ya sake xuwa kofar gida ba, idan kuwa ba haka ba a gaban daddyn ki xan xane ki sai dai duk abinda Inna xata yi tayi..." Kuka kawai imaan take bata ce masa komai ba, strictly yace "Am I clear?" Ta gyada masa kai da sauri, muryar Inna suka ji tana cewa "Naga abinda ya isheni ni patuu na 6ata a gidan Mujaheed" sai kuma ta kwalo masa kira, bude kofar Mujaheed yyi ya fita ya jawo kofar, Imaan ta durkushe a dakin tana kuka a hankali, Inna na ganin Mujaheed tace "Alhmdllh, ni na xata 6ata nayi, Toh ita kuma matar ina ta shiga, har kasa fa na sauka ban ganta ba, kada ta shiga wani waje in shiga uku dama ga Bukar ya xama abun tsoro, ba da xuciya daya ya yarda ta biyo mu ba" Mujaheed yace "Tana waje, muje ki ga dakin dake kasa" Inna tace "Na waye dakin?" Yace "Baki" inna tace "Irin su Hansai da 'ya yanta knn idan sun xo" murmushi yyi ya bude kofar parlon yace "Har ke ai" Bai jira cewarta ba ya fice. Har garden sai da Mujaheed ya kai Inna ya xaga duk gidan da ita, tana kallonsa tace "Toh ai tun yanxu ya kamata mu shiga gun makota a san juna kafin mu tare, ko ya kaga?" Kallonta yyi ya dauke kai, tace "A'a ba xancen dauke kai ba yana da kyau in san su su san ni, ko haka mutum xai ta xama ba jama'ah a gida, ai mutane Rahama ne" Mujaheed yace "Sai ki jira idan kin ga dawowarki gidan" Inna tace "Wannan gaskiya ne, to ni na shiga uku ban fa yi la'asar ba Mujaheed" yace "Toh mu je ciki kiyi" parlon suka koma ya nuna mata dakin dake downstairs yace "Sai kiyi alwala a bayin ciki kiyi sllhn" tace "Toh dakin su Hansai kenan" shi dai bai ce mata komai ba ta wuce ciki, kallon agogo yyi sannan ya wuce sama, parlonsa ya shiga ya bude kofar dakin, durkushe ya ganta inda ya bar ta har sannan tana kuka, tana ganinsa ta mike tsaye, karasawa cikin dakin yyi, ta hadiye kukan da take ta sunkuyar da kanta, takawa yayi har gabanta ya tsaya ta ki yarda ta daga kai balle ta kallesa, ya dago kanta a hankali, ta kallesa sai kuma ta fashe da kuka ta juya masa baya, xagawa yayi gabanta ta rufe fuskarta tana shessheka, d'an murmushi yyi, kamar baxai ce komai ba sai kuma yace "ki dinga jin magana ta idan baki son na dinga sa ki kuka" ta kara juya masa baya cikin kuka tace "Ni bana soo" xagawa ya kara yi gabanta ya jawo ta kusa da shi, ta kuma fashewa da kuka, ya d'an hade rai yace "Toh baxa ki yi shiru ba" kin cewa komai tayi, ya ja ta xuwa bathroom, ruwa ya bude yana kallonta ta madubi a hankali yace "Wash ur face now" ta turo baki ta ki cewa komai, tara hannunsa yayi ya debi ruwan ya dukar da ita ya shiga wanke mata fuskar, yana gamawa ya ciro handkerchief dake aljihunsa ya fara goge mata ruwan fuskar, yana kallonta ta madubi yace "Promise me xaki fara jin magana ta daga yanxu...." Kin cewa komai tayi ya hade rai yace "I am talking to you" da kyar tace "Na ji" yace "Kin ji me?" A hankali tace "Abinda ka ce" mayar da handkerchief din yyi aljihunsa ya juya ya fita bathroom din, murguda baki tayi ta juya tana kallon kofar bayin. Parlor Mujaheed ya xauna yana danna wayarsa har Inna ta fito dakin da ta shiga yin sllh, tace "Wai Mujaheed ni fa ban ji motsin Imaan ba.... A rufa min asiri mu dubota" Mujaheed yace "Tana sama ai" Inna tace "Toh ni dai mu je in ganta" bata jira cewarsa ba ta nufi stairs ya mike ya bi bayanta, dakinsa ya shiga da ita suka ganta tsaye jikin window waya kare a kunnenta, tana jin an bude kofa tayi saurin dauke wayar daga kunnenta tayi tsuru tsuru, kallonta Mujaheed ya dinga yi, Inna tace "Toh ke daga ganin gida sai ki shige dakin matar mutane ki xauna, jira xa ki yi Allah ya kawo lkcn naki da Bulasawa ae" Juyawa Mujaheed yyi ya bar bakin kofar, Inna tace "Toh fito masu a daki yi hakuri haka" imaan bata tanka ta ba ta nufi kofa gabanta na faduwa ta fita, Inna ta bi bayanta, balcony suka tadda Mujaheed suna fitowa ya kulle gidan da makulli ya tafi gun motarsa, imaan bata yrda ta kallesa ba ta bude front seat ta shiga kamar munafuka Bayan Inna ta shiga baya, ya ja motar ya fita compound din yyi ma Mai gadi sallama. Suna hawa saman titi Inna tace "Ni dai Mujaheed da dai in samu kaza in siya, naji raina na so sosai" Mujaheed yayi parking dai dai gun masu gashin kazan da ta gani ya sa tayi magana, tana washe baki tace "Allah dai ya maka albarka" Bai ce komai ba sai ma jinginar da kai da yayi da kujeran motar ya lumshe ido, Inna tace "Toh ko ta fita ta amso?" Ba tare da ya bude idon ba yace "Ehh" inna tace "Toh guda nawa?" Jin bai ce komai ba Inna ta gyara xama tace "Ko guda uku ai yyi, Ni daya ita daya, yan sa ido kuma sai in kacalcala masu daya" Mujaheed yace "Ohkk" Inna tace "Yi maxa ki sauka imaan, kice masu su xabo manya don Allah na tsohuwa ce kuma ba miji gareni ba" Imaan ta bata fuska ta juya tana kallon Inna, inna tace "Naga Ikon Allah, ko in sauka da kaina ne? Me mutanen xa su maki ko ina ruwanki da su" bude motar Imaan tayi ta fita ta tafi gun masu gashin, Mujaheed ya bude ido ya bi ta da kallo daga cikin motar, ba laifi akwai maxa a gun, imaan na sunkuyar da kai ta amsa tambayar da masu wajen ke mata tace "Guda uku" tana ta tsaye har aka gama packaging kajin a leda daban daban ta amsa ta nufi gun mota ta bude back seat tana kallon Inna tace "Wai dubu hudu da dari biyar" Inna tace "Toh ni xa ki gaya ma? sai ki gaya ma me siyan ai" Ta madubi Mujaheed ya kalleta yace "Waye me siyan ban da ke?" Inna ta gwalo ido tace "Ban gane ba" ya buda ido sosai yace "Ko sisi bani da shi, ban fito da kudi ba" Inna ta saki salati mai tsayi tana xaro ido tace "Nima ko sile ban fito da ba Mujaheed" Mujaheed ya daga kafada yace "Sai ki san abinda xaki ce masu" Inna ta kara sakin salati tace "Yau babu lafiya ni patuu an kacalcala kaji uku ba kudi" shi dai Mujaheed bai sake ce mata komai ba, ta kalli Imaan da xaro ido tana kallonsu, Inna tace "Maxa maida masu tsiyar su kice basu da girma an fasa siya, maxa koma" Imaan ta wani xaro ido tace "Iyyee, bayan an yanyanka wllh ni ba inda xan je" a fusace Inna tace "Da aka yanka ci muka yi? Ni naga abinda ya isheni, ki juya ki mayar masu kayansu ba mu da halin biya" Imaan duk ta rikice barin yanda taga duk mutan wajen na kallonsu tace "Na shiga uku, wllh Inna baxan iya komawa dubi fa maxa a wajen da yawa" jaraba Inna ta dinga yi inda take shiga ba nan take fita ba tace "Mazan banxa maxan hofi ina ruwanmu da su bamu da kudin biyan kaji..." wani gentleman dake xaune wajen ne ya taso ya iso gun motar yana kallon Imaan yace "Lafiya kuwa?" Inna tace "Ina fa lafiya yaro an kacalcala kaji uku ba kudin da xa mu biya, nace ta mayar masu tsiyar su shine take kokarin tara min jama'ah wllh ko amsar ledan ma ni ban yi ba balle inji kamshin naman ciki, Toh a kan meye baxa su amsa ba? Dama haka ake yi?" Murmushi kawai mutumin yake yana kallon Imaan yace "Kazan guda nawa ne?" Da sauri Inna tace "Gudu uku ne wllh, daya nata daya nawa, daya na yan sa ido a gida..." Hannu ya sa a aljihu yana kallon Imaan, Mujaheed ya bude motar ya fita gun masu gashin kajin ya fiddo dubu biyar ya mika masu, daga Inna har mutumin da imaan bin sa da kallo suka yi, Inna tace "Kaga katon banxa ko? Ce mana yyi ba shi da kudi fa har sai da ya bari duniya ta gama sanin abinda muke ciki sannan ya fita wani zokai zokai da shi xai bada kudi, Toh Allah ya saka min kunyata ni da ya so yi gaban masu kaji da tona min asiri da yyi a gabanka" Dariya mutumin ya dinga yi yana kallon Inna da ta tsuke fuska tana kallon Mujaheed, imaan ta kalli mutumin gabanta ta mayar masa da kudin da ya mika mata tace "Mun gode" Yana murmushi yace "Don't worry...." Dawowa Mujaheed dake kallonsu yyi ya amshi kudin hannun imaan ya kamo hannun mutumin ya saka masa a ciki yace "Thanks for ur concern" daga haka ya bude mata front seat yana kallonta, ta sunkuyar da kanta ta shiga ya rufe motar, ya xaga ya shiga motar ya tada ya bar wajen. Inna tace "Ni dai duk wanda niyyarsa ya kunyata ni a duniya Allah ya min kantangar karfe da shi, kuma ya saka min" Shi dai Mujaheed bai tanka ta ba har suka isa gida. Shirye shiryen biki aka shiga yi a gidan ba kama kafar yaro barin bangaren Umma da kawayenta, ji take kamar an mata albishir da aljanna xata aurar da first and only son dinta xuwa ga 'yar masu kudi ba na wasa ba, shi ko gogan kamar ba shi xai yi aure ba babu Shirin da yake, idan ya fita aiki tun safe dama sai dare xai dawo don kawai bai son participating a shirin da ake a gidan, shi gaba daya bai fi sau uku suka hadu da Safeenar ba ma, kuma duk Umma ke tilasta sa sai yaje, ko da wasa bai taba dialing lambar Safeenah don kansa ba sai idan yayi missing call dinta, a rana kuwa tana kiransa fiye da sau goma, shi kansa mamakin irin son da take masa yake duk da yasan dole ta fahimci fa baya yinta amma duk class dinta bata nuna ta damu ba sai kara shige masa take. Tun ranan da Mujaheed yyi ma Imaan warning ko da wasa bata son Sadeeq ya xo kofar gidansu sai dai waya amma abinda ke bata mamaki yanda taga shi ma bai damu ya xo ba kamar da, da kusan kullum sai ya xo, sai dai suna kusan raba dare suna waya da shi cikin duvet yanda Ammi baxata ji ba, Duk Friday day kuma sai ya aiko wani worker din gidansu gun Inna ya kawo mata sako, Imaan dai ta tasan soon Mujaheed xai yi aurensa ya kara gaba sai taga ta yanda xai hanata tsayawa da Sadeeq kuma. Yau Friday da ya kama saura sati daya bikin Mujaheed da Safeenah Imaan ta fito daga dakinta ta shiga na Ammi, durkusawa tayi kusa da gado tana kallon Ammi tace "Ammi xan wuce yanxu" Ammi tace "Toh na dai gaya maki kar ki dade imaan" tace "Wallahi baxan dade ba Ammi" Ammi tace "Toh ki gaisheta Ina mata ya jiki" Imaan tace "Toh xata ji" mikewa tayi ta fita daga dakin ta shiga kitchen ta dauko wani leda mai dauke da can malt ta fito parlor ta dau jakarta sannan ta fita gidan, kamar mai tausayin kasa ta isa bakin titi bayan few minutes ta samu adaidaitan da xai kai ta GRA, tafiyar kusan minti ashirin suka yi, suka shigo gate din layin as usual ko ina tsit sai haushin karnuka, dai dai gate din kantamemen gidan Imaan ta sa mai adai daitan ya tsaya ta sauka ta basa kudin tana kallon masu gadi dake xaune bakin gate din gidan, gaishesu tayi daya daga cikinsu yace "Wa kike nema?" Tace "Mariya" Mai gadin yace "Toh ki kirata" shiru tayi tana kallonsa don kwanaki da dadewa da ta xo ae basu mata tambayar komai ba, ba musu ta fiddo wayarta a jaka ta shiga Kiran Mariya, Ba a dau lkci ba sai ga Mariya ta fito gidan, Rungume imaan tayi tace "Welcome frnd" tana kallon masu gadin tace "Kawata ce duk ranan da ta xo ku bar ta shigo babu interrogation" bata jira cewarsu ba ta ja hannun Imaan cike da farin cikin ganinta suka wuce ciki, Imaan tace "Dama kin ma ji sauki koh?" Mariya ta marairaice tace "Yau fa nayi getting self dina" Imaan na murmushi tace "Toh Allah ya kara lafiya" sai da ta fara kai Imaan dakin Mahaifiyar ta ta gaisheta sannan ta ja ta xuwa makeken bedroom dinta, imaan ta xauna tace "Siblings din ki fa?" Tana fiddo ruwa da lemo a fridge dinta tace "Sun fita da Yaya Annur shan ice-cream kinsan yau Friday" murmushi kawai Imaan tayi, Mariya ta ajiye mata drinks din tace "Me xa ki ci, akwai yam with sauce, cous cous with sauce, or kin fi son snacks?" Imaan ta girgixa kai tace "A'a na ci abinci a gida" Mariya ta harareta tace "A'a ni dai sai kin ci wllh" Imaan tayi dariya tace "Bayan nace maki na koshi, Ni la'asar kawai xan yi" Mariya ta nuna mata bathroom dinta tace "Kiyi alwala ga bathroom kafin ki fito xan kawo maki abincin" bata jira cewar Imaan ba ta fita da sauri, Murmushi imaan tayi ta mike ta cire Hijab din jikinta ta ajiye ta shiga bathroom din, tana gama alwala ta fito dai dai nan aka bude kofar dakin, still tayi tana kallonsa, kamar yanda shi ma ya tsaya yana kallonta, juya masa baya tayi da sauri tana xaro ido....
*Imaan isn't for free* it's 300 via
Fcmb 3276052019 Hauwa Bello Jiddah
Then u show ur evidence of payment via my WhatsApp number
07087865788
41.....
Sadeeq yayi murmushi a hankali yace "But you didn't tell me you where coming here da muka yi waya daxu" Ta dau hijab dinta ta saka still bata juyo ba tace "Ae ba wajen ka na xo ba" murmushi kawai yake yana kallonta, Mariya ta iso bakin kofar rike da tray din abinci tace "Ya Sadeeq Aunty na neman ka fa" ya kalleta yace "Har kin ji sauki kenan" dariya tayi tace "Ehh mana bayan alluran da ka sa aka min, Kuma ga kawata ta xo, Hope yau dai ka tuna ta" Ya langwabar da kai yace "Bayan ta ki juyowa ma in ga fuskarta balle in san wacece" Mariya ta wara ido ta kalli Imaan da ta ki juyowa da gaske, ta yi dariya ta karasa cikin dakin ta ajiye abincin hannunta ta isa kusa da Imaan ta juyota suna facing Sadeeq tace "Toh ka gane ta yanxu?" Shafa kai yayi yana cute smile dinsa yace "Anya.. wani anguwar take? Na taba ganinta ma kuwa?" Imaan bata san lkcn da tayi murmushi ba ta sunkuyar da kanta, Mariya ta bata fuska tana kallonsa don da gaske bata ji dadi ba, Sadeeq ya wara manyan idonsa yace "Toh Sannu da xuwa kawar Mariya, duk da dai ni ban gane ki ba" daga haka ya juya ya rufe masu kofar, duk yanda Mariya tayi forcing din Imaan ta ci abincin da ta kawo mata kin ci tayi wai ta koshi, ruwa kawai ta sha shi ma sip daya, Mariya da gaba daya bata ji dadin kin cin abincin da Imaan tayi ba tace "Dama ki dau drinks dinki ki koma da su bana so da gaske" dariya kawai Imaan tayi ta mike tace "Sai ki ba su Hafsat idan sun dawo, ni dai tashi ki rakani" Mariya tace "Bayan kin walakanta ni xa ki ce in raka ki" Imaan na murmushi ta nufi kofa tace "Toh ni fa na ci abinci a gida nace maki Mariya" Mariya ta mike ta bi bayanta suka fita