Showing 120001 words to 123000 words out of 303099 words

Chapter 41 - Imaan Book 1 Hausa Novel Complete

17 Dec 2024

1608

dakin tace "Toh mu je ki yi ma Aunty sallama ya na iya da ke, nima dai ko ruwa kika ban idan naje gidan ku baxan sha ba" Imaan ta kalleta ta gefen ido tana murmushi suka shiga parlon mum dinta, Sadeeq na parlon tare da mum din nata a xaune, Imaan ta durkusa kusa da kujera tace "Aunty xan tafi" Mum din Mariya tace "Da wuri haka Imaan, toh Ina xuwa" tashi tayi ta tafi dakinta, Imaan ta sata kallon inda Sadeeq yake taga kallonta yake, ta dauke kai da sauri, Mariya tace "Ya Sadeeq yanxu fa su ya Annur xa su iya dawowa basu kawo min komai ba ko?" Yace "Toh ki kirasu mana" Tace "Toh don Allah kira min su ta wayarka, I can't imagine me not eating shawarma today" yace "Wayana na can gida" tashi tayi ta bi mum dinta daki don daukan wayarta ta kira step brother din nata, Sadeeq na kallon Imaan yace "Me yasa baku xo tare da kaka ba?" Ta dai yi murmushi bata ce komai ba, Aunty ta fito rike da leda ta ajiye kusa da Imaan tace "Ki gaida min mum din ki kinji Imaan" a hankali Sadeeq yace "Aunty ita ce fa warce nake yawan baki labari a kai...." Aunty ta kalli Imaan sannan ta kallesa da mamaki tace "Imaan din kuma?" Yana murmushi yace "Sure..." Sake baki tayi tana kallonsa, ya shafa kansa yace "Dama nace maki ba ma sai na kawo maki ita ba da kanta xata xo wataran ki ganta" Imaan taji kamar kasa ya bude ta shige don kunya, ta kasa dago kanta ta kalli Aunty, Aunty tace "Ikon Allah, wai da gaske kake don Allah Sadeeq" Yace "Gata ki tambayeta, but aunt this is our secret ko Mariya kar ki gaya ma plss Aunty, you know Mariya talks a lot...." Dariya kawai Aunty tayi ta xauna tace "Ikon Allah, Toh Allah ubangiji ya sanya alkhairi, yayi xabi na gari..." Yace "Ameen" Mikewa yayi yana kallon Imaan yace "Let me drop you" da sauri ta girgixa kai sai dai bata ce komai ba, Aunty tayi dariya tace "Aa ki je dai ya ajiye ki gida Imaan, ki gaida mutanen gidan kin ji, Allah maki albarka..." Sadeeq na murmushi ya nufi kofa ya fita, Aunty na kallon Imaan tace "Imaan idan ma kina da doubt a kan Abubakar a da, tohh stop that now kinji daughter, Sadeeq na son ki fiye da yanda kike tunani, I was so surprise da naji yace min ya sami yarinyar da yake so da aure yar Nigeria, coz ni nasan waye Sadeeq, I know him fiye da uwar da ta haifesa ma, kuma wllh duk jinsa nake ba wai na yarda ba, har gajiya nake da jin labarin ki a bakinsa, But plss kiyi kokarin kame kanki ki kare martabar ki na 'ya mace, am not saying this bcos Sadeeq is bad or anything of such, A'a Ina gaya maki haka ne a matsayina na uwa, ko Mariya iyakar shawarar da xan bata kenan...." Imaan dai ta kasa dago kanta, fitowar Mariya yasa Aunty tayi shiru, Aunty na kallonta tace "Ki rakata compound Sadeeq xai ajiyeta gida yanxu, he is waiting for her" Imaan ta mike tayi ma Aunty godiya cikin sanyin murya ta fita, Mariya ta dau ledan da Aunty ta ajiye mata tace "Mun gode Aunty" daga haka ta bi bayan Imaan da sauri, Mariya ta bata fuska ganin bata ga Sadeeq a bangarensu ba, tace "Kai ya Sadeeq maimakon ya dau motar dake nan yanxu sai mun bi sa har can" ita dai Imaan bata ce komai ba, haka suka dinga tafiya a lafcecen compound din xuwa bangarensu Sadeeq, Building din ya kusa biyun nasu Mariya, Kai kana gani kasan an rasa yanda xa ayi da Naira kuma, Motocin dake parking spaces din wajen sun yi goma ko wanne kuma ya wuce a kirasa mota sai dai Ride, ni kam nace don ma Inna bata xo taga gidan ba... Ai da gobe gobe xata sa Bukar da Ahmadu gaba ta tada bala'i a daura auren Imaan da Bulasawa... Lol, Sadeeq na xaune cikin daya daga motocin parking space din idonsa a kan Imaan dake tahowa tare da Mariya, irin kallon da yake mata yasa Mariya ta kalli Imaan sai dai bata ce komai ba, ana haka aka bude gate din gidan wani ride ya shigo compound din, Mariya tayi ma motar kallo daya ta dauke kai, Drivern yyi parking aka bude back seat, wata da baxata wuce shekaru hamsin ba ta sakko motar cikin shiga ta alfarma, tun daga kunnenta, wuyarta, finger, da wrist duk gold ne, tun da Imaan ta kalleta sau daya ta gane Mahaifiyar Sadeeq ce, Mariya tace "Sannu da dawowa Mami..." Sama sama matar ta amsa, Imaan ma ta gaisheta, ba tare da ta kalli Imaan ba ta amsa, tana kallon Sadeeq tace "Fita xaka yi yanxu Abba..." Ya fito daga motar yace "Welcome back Mami" tace "Yauwa..." Yana shafa kansa yace "Aunty tace in ajiye bakuwarta a gida..." Daga sama har kasa ta kallesa bata dai ce komai ba ta nufi entrance din babban gidan, ya bi ta da kallo, can yace "Mami xa a maki wani abun ne?" ba tare da ta juyo ba tace "Noo ka tafi inda aka aike ka, ka sameni parlona dai idan ka dawo, is Annur back?" yace "I don't think so" Front seat ya xaga ya bude ma Imaan yana kallonta, Mariya ta ajiye ledan hannunta a bayan motar ta xaga gun imaan tace "Plss kice ma Ammi ina gaisheta kin ji" Imaan ta shiga motar tana murmushi tace "Toh xan gaya mata" Sadeeq ya tada motar suka fita compound din Mariya na daga masu hannu, Sai da suka hau saman titi murya can kasa yace "Nayi missing din beautiful face din ki two days Imaan" Murmushi kawai tayi, yace "ke ko naga ma baki damu da rashin xuwa na ba koh? You won't even understand what I am going through now" Ta kallesa a hankali tace "I thought you are busy this days ne shi yasa" girgixa kai kawai yayi, bayan kusan minti biyar yace "My birthday is coming soon...." Ta kallesa tace "When" yace "7 days from today in sha Allah" shiru tayi don ranan daurin auren Mujaheed kenan, can tace "Toh Allah ya kai mu lafiya" yace "Anything for me?" Murmushi tayi tace "Me kake so?" Murya can kasa yace "Ke nake so Imaan" ta wara ido tace "Ni kuma" ya gyada kai yace "I don't know... i just have this urge of wanting to be with you, sai yanxu nake ganin nisan kwanakin da suka rage... I want you by my side as my wife" kasa kallonsa tayi ta kuma kasa cewa komai, ya kamo hannunta yace "Kin yi shiru" kwace hannunta tayi a hankali still ta ki cewa komai, parking taga yayi ta juya tana kallonsa, yayi kasa da murya yace "I am thinking of meeting grandmum, ko xata kara yi ma su Abba magana" Imaan ta kallesa da sauri tace "Maganan me?" Yana kallonta yace "Su yi hakuri su bani ke any time from now, wllh har professor xan iya barinki ki xama a gidana" Imaan ta girgixa kai kamar xata yi kuka tace "A'a ni dai, bayan ga abinda daddy na yace" Shiru yyi yana kallonta, cikin sanyin murya yace "Toh shikenan i will continue waiting and having patient in sha Allah" Driving ya ci gaba da yi, sai da suka kusa layinsu yace "My frnds are throwing a birthday party for me, kuma ke ce babban guess a wajen ranan" ta wani xaro ido tana kallonsa yace "Yea, don't turn down my offer baxan ji dadi ba....." Kasa cewa komai tayi yana shigowa layinsu gabanta yyi mugun faduwa, what if Mujaheed na waje yanxu haka, kafin ya isa kusa da gate dinsu da sauri tace "Kawai ma ka ajiye ni a nan ba sai ka karasa can ba" ya kalleta yace "Why?" Ta hadiye abu da kyar tace "Nothing" Bai ce komai ba ya kai ta har bakin gate din ta fara kalle kalle kamar munafuka ta bude motar ta fita yace "Wait Imaan" tsayawa tayi ya juya ya dauko ledan da Mariya ta ajiye mata, Mika mata yayi ta amsa tace "Nagode sai anjima" daga haka ta shige cikin gidan da sauri har hakan ya basa mamaki ya bi ta da kallo, tana shiga kuwa ta kulle gate din, sai da xuciyarta ya kusa shigewa cikinta ganin Mujaheed da Yusuf a compound din, Yusuf na xaune kan farin kujera Mujaheed kuma da alama gate xai fita amma sai kallonta yake, bata tsaya wani tunani ba ta fasa wani ihu ta sake ledan hannunta ta durkushe wajen tana yarfe hannu tana kiran Ammi, Mujaheed ya karasa inda take da sauri yana kallon kafarta yace "Me ya faru??" Ta kamo hannunsa tace "Wayyo Yaya kafana ban me ya same shi ba..." durkusawa yyi ya daga dogon hijab din jikinta yana kallon kafar, ta gefen ido ta dinga satan kallon kasan gate taga ko Sadeeq ya gama reverse.


*Imaan isn't for free* it's 300 via


Fcmb 3276052019 Hauwa Bello Jiddah

Then u show ur evidence of payment via my WhatsApp number
07087865788


42....


Imaan ta kwace kafarta a hannunsa bayan ta ga Sadeeq ya wuce tana turo baki a hankali tace "Ni ya ma daina, dama gurdewa kawai nayi" bata jira cewarsa ba ta mike da kyar, Yusuf dake tsaye shi ma ya iso wajen yyi murmushi yace "Dama ba wani ciwo, ke dai kika san abinda kike boyewa a waje" Mujaheed ya kalleta ya kalli gate da sauri, ledan da ta jefar ya dauka ya bude yana kallon abinda ke ciki, sai kuma ya nufi gate din.... Tana ganin haka ta dau ledarta da takalmanta ta wuce apartment dinsu da sauri tana waigan Mujaheed, Yusuf yyi murmushi ya koma ya xauna, Parlor ta tadda Ammi xaune, Ammi ta amsa sallamarta tace "Meye kuma kike sa min makulli a kofa" ta xaro ido tace "Ohh na manta, nayi xaton dare yyi..." Still dai bata bude kofar ba tana murmushi ta karasa cikin parlon ta xauna tace "Ammi Sannu da gida" Ammi tace "Yauwa, ya mai jikin?" Imaan tace "Da sauki, Mum dinta tace in gaishe ki, ta ma bani wannan" tana fadin haka ta ajiye ledan a kusa da Ammi, Ammi tace "Toh Allah ya amfana" mikewa Imaan tayi ta wuce daki har sannan xuciyarta bai daina bugawa ba, yanxu da Mujaheed ya ga Sadeeq ya xata yi yau. Tun bayan da ta idar da sllhn magrib Ammi ta ce ta dau abincin Inna ta kai mata gabanta ke faduwa, har claiming ciwon kafa tayi duk don Ammi ta kira Maimoon ta kai ma Inna abincin amma Ammi tace ita dai xata daure ta kai a hakan, tana goge guntun hawayenta ta dau abincin ta fita a sanyaye, ita kanta bata gane wani sabon tsoron Mujaheed da ya diran mata yanxu ba, a hankali ta bude kofar parlon Inna ganin takalmin da bata dai san ko na waye ba bakin kofar, ta ajiye abincin a nan bakin kofa Inna na tambayar wani munafukin ne amma tuni ta juya da sauri har tana tuntube ta koma part din su. Washegari Saturday karfe takwas saura Imaan ta fito bangarensu cikin shirin islamiyya, duk gaba daya a tsorace take har Ammi ta lura da hakan amma da ta tambayeta damuwarta sai cewa tayi ita bayanta ke mata ciwo, Ammi ta sa ta sha magani sannan ta fita, parking space ta dinga lekawa ko xata hango motar Mujaheed, ganin motar tasa yasa ta ki jiran su Maimoon ta nufi gate da sauri, ta gwammace ta tafi bakin titi ta samu adai daitan da xai kai ta islamiyyar. Suna jiran drivernsu bayan an tashi islamiyya Maimoon tace "Imaan wai me yasa kika ki jiran mu daxu?" Imaan ta tabe baki tace "Salon kawai ku 6ata ma mutum lkci mu yi ta yin latti ana xane mu, naga baku fito ba ni kuma bana son inyi latti shi sa nayi wucewata" Rahma tace "Har akwai wanda ya kai ki saka mutum yin latti? Kullum sai mun yi ta jiran ki bakin mota kafin ki fito, daga ace bayan ki ya rike sai ace kafar ki ya rike, to daga yau ma kar ki sake jiranmu kiyi wucewar ki" Imaan ta kalli Maimoon tace "Kin ga dai ba da wannan matar nake magana ba ko, ki gaya mata ba ruwanta da harkata tayi ta kanta ta kyaleni..." Rahma tayi dariya tace "Ehh gwara in kyaleki kiji da ciwace ciwacen ki kam....." Maimoon ta kalli Rahma tace "Haba meye haka Rahma?" Rahma ta watsa mata wani kallo tace "Sai dai ki tambayeta meye haka, ko ni sa'arta ce aka gaya mata??" Tsaki tayi ta wuce gun motar gidan su da yyi parking dai dai lkcn, Ummi ta ja tsaki tace "Mutum sai neman fitina kawai, ana taba ta kuma lalura ya tashi a shiga uku, to dama wa xai taba sauran ciwo idan ba tsautsayi ba ma" tana fadin haka ta wuce ta shiga mota ita ma, Maimoon ta kalli Imaan dake kallonsu tace "Ki rabu da su kiyi hakuri" Imaan bata ce komai ba ta bude front seat ta shiga Maimoon ma ta shiga back seat... Suna isa gida driver yyi parking Imaan ta bude motar ta fita bata xame ko Ina ba sai part din Inna, Inna na xaune parlon tana hada kwadon rama Imaan ta shigo ta xube nan kan kujera ta fashe da matsanancin kuka, Inna ta tura roban gabanta tace "Auzubillahi, me ya sami Aishar?" Cikin kuka Imaan tace "Ko ba su Rahma da Ummi bane daga Ina magana da Maimoon suka fara xagina har da ce min sauran ciwo...." Mikewa Inna tayi ta rufe roban kwadonta ta dau gyalenta ta nufi kofa ta fice, Imaan ta dinga kuka har da shessheka, can dai tayi shiru ta goge idonta ta shiga kitchen ta dauko wani plate ta debi kwadon da Inna ke hadawa ta fice a parlon. Babu abinda Inna ta mance bata xaxxaga ma Umma dake dakinta a xaune tare da su Ummi dake mata tsarin abinda ya faru tsakaninsu da Imaan, Inna na huci tace "Kuma in sha Allahu sai kinga sauran ciwo a jikokin da xa a haifa maki..." Da sauri kuma tace "Astagafirullah, jikokin ki ai na Ahmadu ne, to in sha Allahu sai kinga sauran ciwo a dangin ku.... Kuma a kawo maki riko kiyi ta fama, duk wanda ya sake sa min jikata a bakin duniya Allah ya isa ni dai, Allah ya isa, kuma bari Ahmadun ya dawo...." Tana fadin haka ta fice. Imaan na shiga apartment din su ta tadda Ammi na ta girke girke, gaisheta kawai tayi ta wuce daki, tayi wanka tayi sllh sannan ta shirya ta fito parlor, kitchen ta shiga gun Ammi dake hada drink din Zobo tace "Ammi jirgi daddy xai biyo ko train?" Ammi tace "Ce maki yyi xai dawo yau?" Imaan ta xaro ido tace "Naga kina girki ne ai" Ammi tace "A'a mamar ku ce dai ke hanya...." Imaan tace "Mama Hadiza?" Ammi tace "Ehh sun ma kusa landing Ina ga" Imaan ta wara ido tace "Shine Inna bata gaya min ba?" Ammi tace "Ita ma bata sani ba shi yasa ban gaya maki tun jiya ba kar ki je ki gaya mata don ba control gare ki ba" Murna Imaan ta dinga yi tace "Da su Maryam xa ta xo in gansu plss?" Ammi tace "Da Maryam kadai suka taho" Imaan tace "Toh wa xai je daukota a airport nima xanje plsss" Ammi tace "Mujaheed Daddy yace yaje ya daukota" shiru Imaan tayi bata ce komai ba, can ta dau plate ta bude abinci xata diba. Hudu na yi Mujaheed ya tafi airport dauko small mum din tasa da autar ta, tun da suka kamo hanyar gida Maryam ke tambayar sa Imaan da turancinta dake kala da na turawa, yyi murmushi yace "Tana nan, tsayin ku daya sai dai ita bata jin magana..." Maryam ta kyalkyale da dariya tace "Ni duk na kagu in ganta wllh, muna fa vid call da ita once in a while" Mujaheed yace "Ae xa mu je ki ganta" Mama Hadiza tace "Amma dai yanxu ta ji sauki sosai koh?" Yace "Ehh mama da sauki sosai" Hadiza tace "Toh Alhmdllh haka Yaya Sadeeq din yace min, Toh in ji dai xa a kawo min amaryar mu gaisa kafin biki..." murmushi kawai yyi bai ce komai ba, tace "Au baxa ka kawota ba kenan" yar dariya yyi yace "Toh xa a kawota in sha Allah mama" Mama Hadiza tace "Toh da dai ya fi, kuna ta dai hakuri da tsufan Inna koh?" Mujaheed yace "Mu wllh da ma ki tarkatata ku koma tare mama" dariya Mama Hadiza tayi tace "Baka da kirki Mujaheed, ita uwar tawa kake cewa in tarkata?" Yace "Wllh mama duk ta addabi kowa a gidan..." Mama Hadiza tayi murmushi tace "In sha Allahu nan da wata hudu ma xa mu dawo Nigeria gaba daya sai in dauke uwata ta dawo wajena sai in ga ta inda xa ku dinga gajiya da ita" Mujaheed yyi dariya yace "Wllh baxata yarda ba, xata gwammace tayi ta xama tana dagawa Ahmadu da Bukar hankali" Mama Hadiza tayi dariya tace "Baka da mutunci wllh Mujaheed" parking Mujaheed yyi a parking space din su bayan sun isa gidan, Mama Hadiza tace "Allah sarki, rabona da gidan nan shekara uku kenan, anjima idan na huta da Magrib sai ka kai ni gidan Seeyama" yace "Toh Mama Allah ya kai mu" part din Abba Mama Hadiza ta fara shiga tare da Maryam don gaisawa da Aunty da Umma... Bata wani dau lkci a part din ba ta fito tare da Aunty, Umma dama tun bayan da suka gaisa ta shige daki ta kulle, Mama Hadiza na kallon Aunty tace "Rukayya dai na nan da rashin kirkinta har yanxu koh?" Dariya kawai Aunty tayi, Mama Hadiza tace "Toh yayi kyau ta ci gaba, har ni xata walakanta ta


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login