Showing 165001 words to 168000 words out of 303099 words

Chapter 56 - Imaan Book 1 Hausa Novel Complete

17 Dec 2024

1674

Mariya da kanninta banda kannin Sadeeq don su tasu islamiyyar daban, amma hakan bai hana Mahaifiyar Sadeeq xuwa wajen saukan al-qur'anin ba, su Daddy da Abba da kawu Bala da Kanin Inna Audu d'an tsut kamar yanda ta kirasa duk sun xo gun saukan su ma, Sai da dalibai uku suka yi karatu sannan su Aunty da Ammi suka iso wajen, Imaan ta ji dadin ganin Amminta don ita ce seventh xata yi karatu Mariya kuma ta shidda, Maimoon ta goma, Tunda Imaan ta hada ido da Sadeeq dake wajen tare da mahaifinsa gabanta ya fadi bata sake yarda ta kalli direction din da suke ba, lkci daya duk mood dinta gaba daya ya canxa har aka xo kanta a karatun... And Sadeeq couldn't take his eyes off her even for a second, both her tajweed and kira'ah were more than perfect, babu wanda bai mayar da hankali kan karatun da imaan take na Surah Ad-dukhan ba.... Soo maa sha Allah, ta kuma burge kowa na wajen, first 20 Aya ta karanta na suran, Nan take kuma Bulasawa ya rubuta Check na 500 thousand ya mika ma Sadeeq dake kusa da shi yace "For her, she recited very well" Sadeeq ya amsa yana kallon mahaifin nasa, ba Bulasawa kadai ba, mutane biyu a wajen sai da suka ma Imaan kyauta, domin suran da ta karanta is perfectly talking about Islam, and those are who passed all their times playing, smoking, drinking, infact committing all such of sins, idan kuma Allah ya aiko da Dukhan daga sama su nemi gafara su tuba, daga ya dakatar su koma gidan jiya, Sadeeq ya mike ya je ya sami daya daga malamansu dake co-ordinating wajen ya mika masa check din yace "Daga Alhaji Ahmad Bulasawa xuwa ga dalibar ku Fatima Abubakar Imaan" Malamin ya amsa da jin dadi yana masa godiya yace "In sha Allah xai isa gareta" Mujaheed bai iso gun saukan ba sai karfe sha daya tare da Safeenah da ta cakare cikin tsadadden lace sai xuba kamshi take, Umma na ganinta ta dinga washe baki tana mata sannu da xuwa, ta mike daga kujerar da take xaune tace "Xauna ga kujerah Safeenah" Safeenah dake taunar cingam tace "A'a kiyi xaman ki Hajiya ga wani kujera can bari in je in xauna" Mikewa Umma tayi da sauri ta dauko mata kujeran tace "Gashi xauna" Safeenah ta ja kujerar duk da ido hudu da suka yi da Ammi da Aunty dake wajajen a xaune dauke kai tayi ta xauna tana kas kas da cingam, umma taji wani shegen dadi ganin abinda ta masu don sai murmushi take tace "In ji dai gidan lafiya Safeenah?" Safeenah na juya ido tace "Qlau wllh Hajiya" Da yake dalibai 20 ke saukan kafin karfe sha biyu da wani abu na rana duk suka gama karatun, A nan kuma malaman suka yi announcing kyaututtukan da Fatima Abubakar ta samu da wasu daga cikin daliban, tunda Imaan ta ji wai Bulasawa da kansa yayi mata kyautan kudi gabanta ya dinga faduwa, Umma dake wajen kuwa da taji amount din gaba daya hautsinewa cikinta yayi a wajen, ta kasa xaune waje daya sai mutsu mutsu take, Aunty kuwa sai murna take tana sa albarka, Mujaheed ya dinga kallon Imaan da ta ki yarda su hada ido da kowa, hotuna aka shiga yi a wajen, kowa hoto yake son yi da Bulasawa dake kokarin ganin ya bar wajen, Mariya ta ja Imaan daga wajensu Aunty tace "Come let snap with my family plss" haka Imaan ta dinga bin ta har suka isa inda familyn Bulasawan ke tsaye, Mariya ta ja ta xuwa gun Babanta tace "Abba xa mu yi hoto da ita, she is Fatima by name" Bulasawa na kallonta yyi murmushi yace "Maa sha Allah, keep it up Fatima" ta sunkuyar da kai tace "Nagode Abba" Photographer dake wajen ne ya dinga masu hoto, Sadeeq dake tsaye gefe yana kallonsu ya dawo gefen mahaifin nasa, Imaan na ganin haka ta fara kokarin sulalewa Mariya taki bari ta wuce har sai da aka masu hoton su hudu, gaba daya hankalin Umma na kansu kamar idanuwanta xa su fito, ko fasa auren Mujaheed da Safeenah da aka kusan yi kwanaki bai daga mata hankali kamar abinda ke faruwa yau ba, Wai Bulasawa da kansa yayi acknowledging Imaan, duk Aunty na lura da ita, Mujaheed dai na xaune shi ma sai kallonsu yake, Imaan suna gama hoto da Bulasawa ya bar wajen bayan ya bada donation dinsa na progress din islamiyyar, hotuna Imaan suka dinga yi da Mahaifiyar Mariya da kanninta, Mariya ta ja ta xuwa gun Mahaifiyar Sadeeq tace "Mummy xa mu yi hoto" Mahaifiyar Sadeeq na kallon Imaan da lovely smile tace "Ur recitation was sweet.. keep it up" Imaan na murmushi tace "Thanks Ma" Tsayawa imaan tayi kusa da ita aka fara daukansu hota tare da Mariya, Sadeeq dai bai daina kallon Imaan ba, har dai suka gama hoto da family dinsa ta tafi gun su Aunty, nan ma suka dinga hoto da su Abba da Daddy, Safeenah bata yarda ko da wasa suyi hoto da imaan ba haka ma Umma, duk suka ga Imaan na wajen basa shiga hoton, Imaan da Maimoon suka yi hoto da ya Yusuf da wasu daga frnds dinsa, shi dai Mujaheed na xaune yana danna wayarsa, Imaan na kallonsa ta isa kusa da shi ta durkusa a hankali tace "Yaya baxa mu yi hoto ba?" Daga kai yayi yana kallonta da manyan idanuwansa, ta turo baki ta kama hannunsa tace "Ni dai ka taso mu yi hoto plss" Ya d'an yi murmushi yace "To kira photographer din mu yi a nan" Tace "Noo, background din baxai yi kyau ba, ba ga flowers ba" Safeenah dake ta kallonsu ta karaso wajen kamar xata tashi sama ta xauna kujeran dake kusa da na shi har tana neman faduwa, Imaan na kallonta ta mike daga durkushen da take ta d'an tabe baki ta juya, Ba Safeenah kadai ba har Umma kallonsu take tayi mitsi mitsi da ido gashi ba daman yin komai ga Daddy da Abba a wajen, Mikewa Mujaheed yyi ya kamo hannun Imaan yace "Toh let go" Umma tayi still inda take ta bi su da kallo, gun flowers din suka nufa yana rike da hannunta, Mariya ya mika ma wayarsa duk da photographer dake kokarin daukansu yace "plss snap with my phone also" Imaan dai sai murmushi take, suna tsaye kusa da flowers din aka dinga kashe masu hoto kamar xata shige jikinsa, Mariya ma na daukansu da wayarsa Mujaheed couldn't help it but smiled sweetly, ta jinginar da kanta jikin shoulder dinsa tana murmushin ita ma, Safeenah ji tayi kamar xuciyarta ta fashe, ga wani tukuki da take ji a ranta, Umma dai sai murmushin karfin hali take tana gaisawa da jama'ah tana kallonsu ta gefen ido, Aunty dai na ta rarraba ma jama'ah abincin da snacks da suka kawo bayan sun ware na malamai da daliban saukan, Ammi kuma ta dinga raba buckets da books, Su kam familyn Bulasawa nan suka bar komai da suka kawo na sauka tun daga abinci, gifts, da dai sauransu suka yi wucewarsu, tashin hankali gun Sadeeq ganin har suka wuce imaan ta ki ko da kallon inda yake ba a cewa komai, tun da yake bai taba shiga tashin hankali na wannan lokacin ba tun daga jiya har xuwa yau, saukan ma banda Aunt dinsa ta tilasta sa da baxai xo ba, hatta Mahaifiyarsa sai da ta tambayesa damuwarsa gun saukan ganin gaba daya he is moody yace mata ba komai har dai suka bar makarantar bai ga fuskar tunkarar Imaan ba, ya dai je sun gaisa da su Abba da Daddy, sai su Aunty da Umma, sannan suka bar wajen da family dinsa, kafin azahar su Imaan suka bar islamiyyar a various cars xuwa gida, Tun da islamiyyar ta manya ce babu dalibi cikin masu saukan da ke da niyyar bin d'an uwansa dalibi gidansu kamar dai yanda ake yi yawanci, kowa kama gabansa yayi xuwa gidan iyayensa, ni ko nace ko dadi... Lol. Imaan da Maimoon motar Mujaheed suka shiga ta dalilin wayar Mujaheed din dake hannun Imaan don ita Mariya ta mika ma da xa su wuce, Safeenah ta wani hade rai xaune a gaban motar Mujaheed na driving har suka isa gida, yana gama parking Imaan na kallonsa a hankali tace "Yaya ka tuna promise da ka min few years back?" Ya juya ya kalleta, d'an murmushi yyi yace "Ban manta ba" tana murmushi ta sauka motar, Maimoon ta mika masa wayarsa ita ma ta sauka, Mujaheed xai sauka Safeenah ta rikosa fuska daure, juyawa yyi yana kallonta, tace "Ban ga fa'idar xuwan mu gidan nan ba bayan an gama sauka, I think it's better mu wuce gidan mu Doctor" Makullin motar ya jefa mata a cinya yace "Ki wuce gidan sai na xo, I don't think u have the right to tell me what to do and what not to do" daga haka ya rufe motar ya nufi part din su ta bi sa da kallo kamar idanuwanta xa su fito.



*Imaan isn't for free* it's 300 via


Fcmb 3276052019 Hauwa Bello Jiddah

Then u show ur evidence of payment via my WhatsApp number
07087865788



59.....


Karfe biyu imaan ta fito daga bedroom dinta bayan tayi wanka ta canxa kaya xuwa daya daga sabbin kayan da Daddy yayi mata har kala biyar na waliman, sosai lace din ya amsheta, Ammi ta gama jera abinci kan lallausan carpet dake parlor, Tana kallonta tace "Ga abincin ku ke da Daddy" Imaan ta karasa ta xauna kan carpet din tana bude warmers din tana murmushi, Daddy ya fito daga daki ya karaso cikin parlon ya xauna saman lallausan carpet din shi ma yana kallonta yace "I am proud of you sweetheart" Dariya tayi tace "Daddy bayan ni ba ku ban gift ba kai da Ammi" yace "Let lunch first" Plate ta dauka ta xuba masu abincin da daddyn nata, Ammi dai na xaune parlon har suka gama cikin abincin, daddy na kallonta yace "Hope you will also pass ur up coming exams with flying colors by the grace of God" Imaan tace "Sure daddy" Daddy yace "Maa sha Allah" Makullin mota ya fiddo aljihunsa ya ajiye kusa da ita yace "And this is my gift" Imaan ya wara ido ta dau makullin tana kallo yace "A car?" Ammi dai sai kallonsu take, cike da jin dadi Imaan ta rungume Daddyn nata tace "I love you Daddy, Allah ya bar min kai, ya kara girma" Murmushi yayi yace "Ameen, gobe xa a taho da motar but you won't ride anytime soon, may be after ur waec" Imaan da ta rasa inda xata sa kanta sbda murna tace "Toh daddy, Allah ya kai mu, nagode Sweet dad, Allah ya saka maka da alkhairi" Yace "Ameen, clear this plates now" Mikewa tayi ta kwashe duk warmers da plate din ta kai kitchen, ta fito daga kitchen kenan aka danna bell, Mikewa Ammi tayi ta wuce dakinta, Imaan ta tafi ta bude Kofar, still tayi ganin Sadeeq tsaye hannunsa rike da leda, sosai gabanta ya fadi lkci daya ta juya da sauri ta bar bakin kofar Daddy na kallonta yace "Who's there?" Kasa basa amsa tayi ta wuce dakinta, bayan few seconds Sadeeq ya shigo parlon da sallama murya can kasa, Daddy na ganinsa yace "Welcome son" Sadeeq na kirkiran murmushi ya karasa ya ajiye ledan hannunsa ya xauna kasa shi ma ya gaida Daddy da ladabi, daddy ya amsa da fara'a yana tambayarsa ya mutan gidan, yace "Alhmdllh Daddy" Ammi ce ta fito daki sanye da hijab, ganinsa ta sunkuyar da kai tace "Sannun da xuwa" ya kalleta yace "Ina yini Ammi" tace "Lafiya lau, ya gidan?" Yace "Alhmdllh, fatan an watse taro lafiya" Ammi tace "Alhmdllh, mun gode Allah" dakin imaan ta nufa ta bude kofar ta shiga ciki, xaune ta ganta can karshen gado ta wani hade rai, Ammi tace "Wa kika ce ma Sadeeq xai xo gidan nan?" Kamar xata yi kuka tace "Ammi ni wllh ban sani ba kawai ganinsa nayi" Ammi tace "Toh sai ki tashi ki tafi ki kai masa ruwa da drinks ki dibar masa snack" Ammi bata jira cewarta ba ta fita dakin ta wuce nata, Mikewa Imaan tayi ta dau hijab dinta fari har kasa ta saka sannan ta fito, ta wuce kitchen ta hada ruwa da drinks sai glass cup a tray, ta debi snack a wani plate ta daura a kan tray din ta fito, kanta a kasa ta iso parlon ta duka gefensa ta ajiye, Mikewa Daddy yayi ya dau wayarsa yana kallon Sadeeq yace "Let me make a call outside" Sadeeq yace "Toh sai ka dawo daddy" daga haka daddy ya fita parlon, Imaan xata tashi ya rike hijab dinta cike da damuwa murya can kasa yace "Plss listen to me Imaan, don Allah ba don ni ba ki tsaya ki saurareni, am begging you plss...." Kasa cewa komai tayi ta xaune wajen ta hade kai da gwiwa ta fara kuka a hankali, duk ya rikice mata ya duka on his kneels yace "Don Allah kiyi hakuri ki yafe min Imaan, it's a mistake that will neva repeat itself again, don Allah ki min rai kiyi hakuri, I have neva for once had the intention of making you angry" ita dai ta ki cewa komai kuma ta ki dago kanta bata kuma fasa kukan da take a hankali ba, cikin sanyin murya yace "Kin ji Fatima, ki yafe min don Allah, wllh bani da nufin cutar da ke, I love you with every breathe of mine, I am wishing u to be the mother of my kids, ban taba ma ya mace irin son da nake maki ba, I Neva knew what true love is sai a kan ki, ni ba fasiki bane Imaan you can ask Mariya, sure I do flex with friends and I am a player, but i am very selective when it comes to mingling with girls, and mind you... ni ba maxinaci bane I can swear to you by Allah who made me ban taba ba, I am a type of person that find my opposite gender so irritating in every aspect, don't forget where I was born and raised, sure it's strongly against the teaching of our religion but kema kinsan to hug or kiss someone is part of our lifestyle back there, a haka na taso cikin su, I tried my very best getting rid of that while here in Nigeria kuma Alhmdllh there is improvement, wllh Imaan ban maki haka da niyyar in cuce ki ko in 6ata ki ba, mata ma dake kawo min kansu ban bata su ba sai ke da nake son aure? Kuma yanayin da nake shiga idan muna tare is something that I have neva experience all my life, that's why kika ga ko xuwa wajen ki bana son yi duk irin son ganin ki da nake I try my best staying away from u, plss Imaan kiyi hakuri ki yafe min, sharrin shaidan ne, don Allah ba don ni ba ki dago kanki ki kalleni in baki hakuri, na kuma maki alkawarin daga this very moment har xuwa ranan da Allah xai sa a daura mana aure idan ke matata ce baxan sake xuwa gidan ku ba, baxa kuma inyi requesting mu hadu ba, xa dae mu dinga waya kawai...." sai a sannan ta dago kanta hawaye na xuba idonta, lkci daya idonsa ya kada shi ma cikin sanyin murya yace "Don Allah kiyi hakuri Imaan" a hankali tana goge idonta tace "Na ji?" Kamar xai mata kuka har lkcn yana durkushe kan kneels dinsa yace "Kin hakura" a hankali ta gyada masa kai, yayi murmushin karfin hali yace "Toh nagode Imaan, Allah maki albarka" sunkuyar da kanta tayi, ya dauko ledan da ya shigo parlon da shi ya ajiye gabanta yace "This is for you, I am very proud of you today, Allah ya baki ikon amfani da karatun ki" ta kasa cewa komai, ya mike yace "Ki ce ma Ammi na wuce, thanks much for forgiving me" Bata iya tace masa komai ba ya nufi kofa ta bi sa da kallo, yana bude kofa kafin ya fita murya can kasa tace "Nagode" ya juya ya kalleta yayi murmushi sannan ya fita ya kulle kofar parlon, Bude ledan tayi taga tsadaddun turarruka ne a cikin ledan har kala biyar. Daren ranan Imaan na dawowa part din Inna ta je kai mata abinci suka hadu da Mujaheed xa shi gun Innar, Ya katse wayar da yake yi yana kallonta, ta wara ido tace "Yaya baka tafi ba?" Yace "Ehh wait for me a parking space yanxu xan fito" tace "Parking space?" Yace "Ehh" tace "Tohm" wucewa tayi shi kuma ya karasa part din Inna, Parking space din nasu ta tafi gun motarsa ta tsaya ta jingina jikin motar, Bayan kusan minti bakwai sai gashi, yana kallonta yace "I saw ur video... reciting, kinyi kokari kadan, they are still some corrections in ur tajweed, so ban ma san amfanin kyautar da aka dinga baki ba, may be dai Muryar ki ne yayi masu dadi" on a serious note ya kare maganar, xaro ido Imaan tayi tana kallonsa a sanyaye, lkci daya ta bata fuska ta sunkuyar da kanta, ko kallonta bai yi ba yace "Matsa in bude motata" a hankali ta matsa masa daga jikin motar ya bude, ta fara tafiya xata koma part dinsu, bin ta yyi da ido yyi saurin jawota, kuka ta fara yi a hankali, ya dawo kusa da ita yana murmushi yana kallonta gently yace "I was only joking Lil sis, ur recitation was superb, I love it, and that was what I expected" turo baki tayi tana kallonsa ya ja hancinta yana kallon eyeballs dinta murya can kasa yace "My future kids will have no problem with recitation of the holy Qur'an" Bai yi xaton xata ji abinda ya fada ba coz his voice was so low, as if he just murmured the sentence, ya ga ta


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login