Showing 6001 words to 9000 words out of 303099 words
kirki alhalin crooo kenan ku ke gani, kar ka sake xuwa min sashi ni dai na gama magana" Mujaheed bai kalleta ba balle ya tanka ta ya mike ya fice parlorn, can kusa da wani flower ya ga Imaan durkushe tana kuka, ya dinga hararanta har ya isa wajen da take, ta mike cikin rawar murya tace "Yaya don Allah kai kaji na xage ta daxu?" Ba tare da ya tsaya ba yana ci gaba da tafiya yace "Ke ma ai ba dukan ki naga aka yi ba" Ta bi shi da kallo tana shessheka.
[6/11, 12:34 PM] +234 703 570 1601: 🌟⭐ *Imaan*⭐🌟
_By Khaleesat Haiydar_✍🏻
3......
Imaan ce xaune kitchen sai faman xuba surutu take ma Ammi dake girkin dinner a kitchen, yar skirt ne jikinta sai ves da yake ranan alhamis ne babu islamiyya, Ammi dake ta saurarenta ta tabe baki daga karshe tace "Aikin kenan sai dai ki cika mutum da surutu ba taimakon fari balle na bak'i" shiru Imaan tayi tana kallon Ammi, Ammi ta kalleta ganin yanda mood dinta ya canxa tayi murmushi tace "Toh ci gaba ina jin ki" sunkuyar da kanta tayi bata ce komai ba, Ammi ta karasa kusa da ita tace "I was joking sweetheart, tafi ciki let me fry some onion and pepper" mikewa Imaan tayi a hankali xata wuce Ammi ta bi ta da kallo har ta fita, Ammi ta jingina da cabinet din kitchen din ta sauke ajiyar xuciya, can ta nufi kofa ta fita don bata son tayi bacci coz shine next abinda xata yi in har ta shiga daki, dakinta Ammi ta shiga ta sameta har ta kwanta, Ammi tace "Baxa kiyi bacci ba yanxu yamma yayi, je dakina xa ki ga leda da atamfa a ciki kan dressing chair ki kai ma su Anty kice ankon bikin Halima" Imaan ta mike xaune tace "Ammi to na mu fa" Ammi tace "Sai ki kirata ki tambayeta ban san ko an fidda naku ba" Imaan tace "Toh, Anty kawai xan nuna ma?" Ammi tace "Ehh sai ki ce mata ta nuna ma Hajiya, na dai fita ai" daga haka Ammi ta fita dakin, imaan ta sa hijab har kasa kan kayana jikinta ta fita ta dau ledan ankon a dakin Ammi, tun da ta shiga parlonsu Anty take yamutse fuska ta dalilin yaji dake tashi sosai daga kitchen, lkci daya ta rike numfashinta, har xata juya ta fita sai ta nufi stairs da gudu don ta shiga dakin Anty, tsarkewa tayi sbda rike numfashin da tayi ga kuma gudun da take, lkci daya ta fara tari sosai breathing dinta na sama, dai dai corridor ta fadi tana kokarin jan numfashi, Maimoon ta fito dakin Anty ganinta ta durkusa gabanta da sauri tace "Subhanallahi me ya faru Imaan" sound din faduwarta yasa Mujaheed ya fito daga bedroom din sa, ganinta a kasa ya kalli kofar Ummarsa kafin ya karasa da sauri ya dagata yana kallon Maimoon da ta rikice yace "Tafi ki karbo inhaler dinta da sauri" da gudu ta sauka xuwa part din su Imaan, Mujaheed ya bude kofar dakin Anty ya shigar da ita ya xaunar da ita kasa ya jinginar da ita da gado ya cire Hijab din jikinta, dai dai nan Anty ta fito daga bandaki, a rude tace "Subhanallahi, Asthman ne, garin Yaya? Ko in amso inhaler dinta" yace "Maimoon taje amsowa" sosai imaan xata baka tausayi saboda ynda take struggling da numfashinta, Mujaheed ya mike ya fita don bin bayan Maimoon suka kusa cin karo bakin kofa, fixge inhaler din yyi ya juya ya koma dakin ya durkusa gabanta ya kai mata baki, dafe hannunsa tayi tana inhaling, Anty dai na tsaye sai kallonta take cike da tausayinta, bayan wani lkci numfashin nata ya fara fita a hankali yana kokarin dawowa normal, Anty ta xauna gefen gado tayi tagumi tana kallonta, Ummi da Rahma na tsaye bakin kofar suna kallonta su ma, Har sannan Mujaheed na duke gabanta idonsa a kanta, muryar Umma suka ji tana cewa "Lafiya me ya faru ku ka tsaya cirko cirko bakin kofa?" Rahma tace "Asthma ne ya tashi wai" Umma ta leko dakin ganin Mujaheed ta wani xaro ido tace "Me Mujaheed yake a nan?" Mikewa yyi da sauri, ta wani hade rai tace "Tambayar ka nake, me ka shigo yi, ko kayi kama da likitan ta ne?" Ya girgixa kai yace "No na xo wucewa ne...." Dakatar da shi tayi tana masa wani shegen kallo tace "Sai ka tsaya aikin da ba lada koh? To ka shiga hankalin ka, Ka guji bacin raina, basu da number likitan ta ne ko kuma neman suna kake?" Shiru yyi bai ce komai ba, Cikin tsawa tace "Xo ka fita malam bana son shishshigi da kwala kai a faranti, kanwar uwar ka ko ta ubanka?" Bai ce komai ba ya kalli Imaan da Anty ke kokarin kwantarwa kan gado ya juya ya nufi kofa xai fita, Anty ta tabe baki tace "Ciwo dai bai wuce kan kowa ba, ita ma ba ita ta doro ma kanta ba....." Umma ta katse ta da sauri tace "Allah yayi mana tsari da irin wannan ciwo nata, ya tsari jikokinmu da tatta6a kunne, a rayuwar nan ta ynxu wa enda ba sickler ba ma ya suka kare, ae irinsu ne ke tsiyata namiji a sintirin asibiti...." Tsaye Mujaheed yyi bakin kofa yana kallon Umma, Anty ta wani hade rai tace "Kinga ki daina kiranta da sickler ita din ba sickler bace, Allah kuma yyi mata tsari da shi" Umma ta wani tabe baki hade da dariya tace "Kwa dinga boye ma wanda ku ka raina ma wayo, Allah dai ya ba kowa lafiya...." A hankali Mujaheed yace "Umma ba fa sickler bace, she is just a carrier...." Umma ta maka masa wani kallo tace "Meye maraban dambe da fada? And did you have any problem with her being a sickler or not da har kake karyata ni Mujaheed?" Bude kofar yayi ya fita dakin bai ce komai ba, ta ja tsaki ta fice ita ma. Anty ta girgixa kai ta zauna kusa da Imaan da ta lumshe ido numfashinta na sauka a hankali tana mata sannu, sai da ta ga alamar tayi bacci sannan ta mike ta fita, Imaan bata dau lkci tana bacci ba ta tashi ta dalilin ciwo da kirjinta ke mata, ta dinga juye juye kan gadon hawaye na xuba idonta, bude kofar dakin aka yi Mujaheed ya shigo, ya karasa kan gadon yana kallonta, daure fuska yyi yace "Me ya faru kuma?" Kirjinta ta nuna masa ta fashe da kuka, yace "Toh kukan ne xai sa ya daina ciwo, tashi xaune" mikewa tayi ta xauna da kyar, sai ga Anty ta shigo dakin, da sauri ta isa gadon tace "Me kuma ya faru Imaan, are you feeling pain anywhere?" Ta gyada kai tana nuna kirjinta, Anty ta dau Hijab ta nufi kofa tana cewa "Bari in je in kwaso magungunanta dai" Xaunawa Mujaheed yyi gefen gadon, ta koma xata kwanta yace "Kar ki kwanta" ta jingina da gadon tana goge idonta, ba a dau lkci ba Anty ta dawo da ledan maganin gaba daya, Mujaheed ya amsa yana duba maganin ya cire mata wanda xata sha, still yyi jin an bude dakin Umma, sai kuma ya ji muryarta tana tambayar inda yake, tashi yyi da sauri ya tafi bayan kofa ya tsaya, Anty ta tabe baki ta balli maganin ta dau table water ta mika ma Imaan, bude dakin aka yi Umma ta kare ma dakin kallo kafin ta tabe baki ta kulle, Shi dai yana tsaye bayan kofar, Anty ta sa Imaan ta kwanta bayan ta sha maganin sannan ta kallesa tace "Don Allah ka fita min a daki malam, tunda aikin xumuncin ma ba so ake kayi ba, kai ma kuma tsoron yi kake, yau ko da ace baka san Imaan ba a matsayin ka na likita ka ganta a wannan hali ai baxa ka ki taimaka mata ba balle tana yar uwarka halak malak, Allah dai ya shiryi mahaifiyar ka" shi dai bai ce komai ba, bayan karin mintuna uku ya bude dakin ya fita. Anty na xaune kan darduma bayan ta idar da magrib Imaan ta tashi daga baccin da ya kara dauketa, Anty tace "Sannu ya jikin Imaan" a hankali tace "Na ji sauki" Anty tace "Toh shiga bayi kiyi alwala ki xo kiyi sllh" ba musu ta mike ta shiga bandakin ta dauro alwala ta fito Anty ta mike kan darduman ta fita, Imaan ta sa Hijab dinta ta hau kai ta tada sllh, tana ta xaune kan darduman bayan ta idar sai ga Anty ta shigo da plate din abinci dakin. Imaan na gama ci ta mike rike da plate din tace "Anty sae da safe" Anty tace "Au baxa ki kwana nan ba" murmushi tayi ta make kafada ta nufi kofa, Anty tace "Toh baki fada min ko na meye atamfar ba" Ta juyo da sauri tace "Lahh, Ammi ce tace in kawo maku ankon bikin Anty Halima" Anty tace "Ashe abu ya xo dai, toh ki ce mata xan shigo gobe" Imaan tace "Toh" Anty tace "Allah ya sauwake Imaan" murmushi tayi a hankali tace "Ameen" daga haka ta fita, tun da ta sakko downstairs umma ke mata kallon tsana tana tabe baki, Imaan dai bata ko kalleta ba ta nufi kitchen rike da plate din, Rahma ce kitchen din ta gama wanke wanke, sai Mujaheed dake tsaye yana xuba ruwan Lipton daga teapot a cikin mug, Imaan xata ajiye plate din, Rahma tace "Kinga plate mai datti a wajen ne malama" turo baki tayi ta dau morning fresh ta bude xata wanke plate din, Rahma tace "Ya M.A in debar maka abincin ne xan fita?" Ya harareta yace "Abincin da ku ka cika yaji ko wanda ba yaji?" Yar dariya tayi tace "Ya Mujaheed yajin fa ba yawa" tsaki yyi yace "Ance maki ban yi tasting abincin bne ku dinga cika ma mutane ya ji a abinci kamar mayyu" Tace "Toh in maka cous cous?" Yace "I will take tea" Imaan ta gama wanke plate din ta juya ta fita kitchen din. Kallonta Ammi ta dinga yi bayan ta shigo tace "Ya jikin Imaan" tayi murmushi tace "Na ji sauki Ammi" daga haka ta nufi dakinta Ammi ta bi ta da kallo. Karfe sha daya saura Ammi ta shiga dakin Imaan, ganin tayi bacci ta tasheta tana mika mata wayar hannunta tace "Me ya sa kika kashe wayar ki" Imaan na murxa ido tace "Kila mutuwa yyi ba charge" Ammi tace "Toh idan kin gama ki maido min wayata daki" Imaan tace "Toh" sannan ta kai wayar kunne tace "Daddy ina yini" Daga daya bangaren ya amsa yace "Why is ur phone switched off" ta langwabar da kai tace "Daddy ban sa a charge ba tun jiya" yace "Toh kiyi kokari ki sa ya jikin?" Tace "Naji sauki, daddy ina missing dinka yaushe xaka dawo?" Yace "Weekend in sha Allah" ta wara ido cike da jin ddi tace "Plss daddy ka dawo week end din kar ka daga, wllh ina son in ganka" kamar xata yi kuka ta kare, yyi murmushi yace "Sure dear, plss ki daina wasa da shan drugs din ki kinji" tace "Ina sha Allah daddy, har yanxu Dr ma bai xo ba" yace "Ehh mun yi waya daxu yace bai dawo ba" Imaan tace "Toh" yace "Sleep tight dear, banda kunna Ac" yar dariya tayi tace "Toh daddy byeee" katse wayar tayi ta mike ta kai ma Ammi daki sannan ta dawo dakinta ta shige duvet. Yau Friday Imaan na dawowa schl bayan tayi wanka tana kokarin saka kayanta taji k'aurin abincin da Ammi ta bar mata a kitchen kan gas don tana shigowa gidan Ammi ta fita kasuwa yin cefane, da gudu ta fita daure da towel don kashe gas din don dama sae da Ammi tayi mata kashedi kan cewar kada ta yarda abincin ta ya kone, muryar inna ta ji a balcony tana cewa "Aa kawai ni dai naga kwana biyu bata shigo bane shine nace in xo in duba ko jikin ne, tunda haka Allah yyi ta mai laulayi, ni jiya ma ko abinci basu kawo min ba wllh, in ma ba ta da lafiya ita Aishar baxata iya takowa ta kawo min abincin ba tunda ba uwarta Habiba bace, abu dai gashi ba tsari da ni fitinanniyar tsohuwa ce ba Bukar xan kira ince matarsa ta bar ni da yunwa ba?" muryar Yusuf imaan taji yana dariya yace "Toh ae an kai maki daga gidanmu naga" da sauri Imaan ta shige daki ta dau Hijab dinta ta fito ta shige kitchen ta kashe gas din sannan ta bude kofar kitchen din ta fice tana murguda baki ta sa Hijab dinta da iyakarsa gwiwa, ko takalmi bbu kafarta ta dinga tafiya har ta zagayo front din gidan, Mujaheed ne xaune kan farin kujera yana waya, ta turo baki ta wuce sa da sauri, ko minti biyar ba ayi da wucewarta ba shi ma ya ji muryar inna tana tahowa, mikewa yyi da sauri tun kan ya bar wajen ta gansa, da karfi ta kwalo masa kira tana murmushi, ya ki juyowa har ya sha corner, Yusuf sai danne dariyarsa yake, Inna ta bude baki tace "Wato ni Mujaheed xai walakanta ina kiransa ya min banxa kai shaida ne ko Isuhu" tana magana tana kunce ha6ar xanin xata goge kwalla, Yusuf ya kasa daurewa ya fara dariya yace "Ke fa kika ce kar ya sake xuwa bangaren ki..." A fusace tace "To shi mahaukaci ne bai san bacin rai ba" Karo Mujaheed ya kusa yi da Imaan dake kokarin lekowa taga ko inna ta taho bangaren, ya hade rai yace "Baki gani ne?" Tana shafa Inda ya bugeta tace "Ko ba inna bace, ta wani biyoni gidanmu anjima tace ina mata rashin kunya" tafiyarsa yyi ya bar ta wajen tsaye, ta turo baki ta bi bayansa, jin tafiyarta a bayansa ya tsaya ya juyo yace "Wai me yasa kike bi na ne" Tace "Ni ba bin ka nake ba tafiyata kawai nake" Tsayawa yyi ya daure fuska yace "To yi tafiyar ki, bana son ganin ki kusa da ni" ba ta ce komai ba ta fara tafiya kamar mai counting steps dinta, yana ta tsaye yana jiran tayi nisa ganin ynda take tafiyar ya girgixa kai ya wuce ta cikin lokaci kankani, sai a sannan ta kara saurinta har ta jera da shi, d'an murmushi yyi bai dai ce komai ba bai kuma kalleta ba, sai da suka kusa entrance din kitchen din part dinsu tace "Yaya ka mance promise da ka taba min 2 years back koh?" Kallonta yayi kamar baxai ce komai ba sai kuma yace "Na me?" Ta wara manyan idanuwanta tace "Idan nayi saukan al-quran, gashi mun kusa in few months time" tabe baki yyi xai bude kofar kitchen din yace "I can't recall...." Ta xaro ido ta rikosa da sauri tace "Wllh nasan baka mance ba" Buge hannunta yyi yana mata wani kallo yace "Keee" Ta turo baki tana kallonsa, yace "Sakeni kar in mare ki" sake sa tayi ya bude kofar kitchen din ya shiga ya kulle, tana ta tsaye wajen bayan few minutes ta murguda baki ta wuce, ta kitchen dinsu ta bi ta kulle kofar sannan ta wuce dakinta ta sa kayanta. Yau tunda Imaan ta tashi take ta murna, gaba daya farin cikin ta ya kasa boyuwa, Kitchen ta shiga tace "Ammi da yaushe daddy xai iso?" Bude baki Ammi tayi tace "Kina kallon agogo kuwa Imaan?" Imaan tace "Ammi wai yau ma da daddyna xai dawo sai naje islamiyya?" Ammi ta mata wani mugun kallo tace "Uwar me xa ki xauna ki min ko yace maki da safe xai taso, common kin 6ace min a nan kin je kin shirya ko sai na 6ata maki rai" a hankali Imaan ta juya a sanyaye ta koma bedroom dinta ta fiddo uniform dinta ta shiga sa wa, sai da Ammi tayi mata jan ido ta amince da yin breakfast da ta hada mata, tana xaune dinning tana shan shayin da kyar Maimoon ta shigo parlon sanye da uniform, Ammi dake goge goge a parlorn tace "Maimoon ku yi wucewar ku kar ta bata maku lkci ko da kafa ne sai ta je" dariya kawai Maimoon tayi ta fita, Imaan ta mike don kanta ganin takwas ya wuce ta dau jakarta ta fita tana matsar kwalla ko ta kan kudin makarantar bata bi, Ammi dai ko kallonta bata yi ba, Tsaye taga Mujaheed jikin motar banda masifa babu abinda yake ma kannin nasa, duk kallonsa kawai suke babu wanda yace komai, "Don samun waje nan nan da islamiyyar ma sai an kai ku a mota ku ga yan gayu ko, to wllh ni ba driver din kowa bane a cikin ku da xa a dinga cewa in ajiye ku a makaranta, Yusuf da ya ga xai iya sai yyi, I won't tolerate that shittt" A hankali Ummi tace "Amma ya Mujaheed kawai don kana nan ne yasa xaka kai mu ai ba kai ke kai mu ba dama, kuma Abba yace kila Monday xa mu samu sabon driver...." wani kallo ya dinga mata fuska daure, ta sunkuyar da kanta, Imaan da isowanta kenan ta bude motar xata shiga ya dakatar da ita yace "Kee, do I look like drivern gidanku da xaki ajiye ni for the past 15 mins a nan, to ke daga yanxu ma xa ki fara naki trekking din" yana fadin haka ya nuna mata makeken gate din gidan yace "Bi can ki kama hanyar makarantar" ta wani gwalo ido tana kallonsa, lkci daya ta juya kamar xata yi kuka xata koma part dinsu tace "Ni dai ban ta6a tafiya da kafa ba...." Wani tsawa yyi mata yace "Wllh ki ka yarda na takowa har Inda kike sai na sa ki kuka" tsayawa tayi tana hawaye don bata mance last abinda ya mata ba, ya nuna mata gate on a serious note yace "Bi can" Gate din ta nufa tana kuka ya jira