Showing 297001 words to 300000 words out of 432432 words
Chapter 100 - Abban Sojoji Book 2 Hausa Novel Complete
buga kanta jikin bango,nan take Aunty babba ta baje ƙasa a sume,'
Juyawa yayi tare da aza idanunshi akan hafsat dake tsaye tana faman zabga uban kuka fuskarnan tayi jaga jaga da hawaye hada majina,nunata yayi da yatsan hannunshi sannan yace"dake da uwarki!ku tattara kayanku ku bar gidan nan!tun kafin inyi sanadin mutuwarku!muguye kawai waɗanda ba Allah aransu,"
Hannu hafsat ta aza akanta tana ambaton"Innalillahi wa'inna ilaihirraji'Un!"
Juyawa ishaq yayi da sauri zai bar ɗakin,da gudun gaske ta ruƙo rigar jikinshi tare da zubewa saman guiwowinta tana kuka tana yi mashi magiya akan,karya koreta,
"Daddy dan Allah kayi haƙuri ka yafe mun!wlh ba laifina bane,nasan mun cutar dasu,amma inaso ka sani daga baya na ƙaunace su,Daddy ka yarda dani Mommy itace take azabtar dasu,kuma itace tayi silar barin....'bata ƙarasa maganar ba sakamakon bugun daya kai mata da ƙafarshi,da sauri ta dafe gefen bakinta daya buga wurin har ya fashe,jini ya shiga ɗiɗɗigowa,dogon tsoki ishaq yaja tare da cewa"Kada ki kuskura ki ƙara kirana da sunan daddy!don ni ban haifi wata ƴa mai suna hafsat ba!tunda har kin za6i ki bi mugun hali irin na mommynki,don haka gaki ga ita,duk in da zata je ƙafarki ƙafarta,karku kuskura Dare yayi maku acikin gidan nan!don wlh sai kunyi danasanin haihuwarku da akayi acikin duniyar nan!don bazan raga maku ba,tamkar ban sanku ba,haka zan hukunta ku!kuma idan ta farka daga suman da tayi ki sanar da ita cewa NI ISHAQ NA SAKE TA,!!!!
Wani irin bugu zuciyar hayaam tayi ji kake daramm!!kamar an buga ganga,nan take ido ya raina fata,sae faman mazurai takeyi abayan gadon da ta la6e,Na shiga uku Ni hayaam An saki Aunty laila!Shikenan komai ya ƙare komai ya lalace!mun gama yawo!!
Ya ƙarasa maganar tare da kai hannu tamkar zai 6alle ƙofar ya fuce,Amani dake la6e tana sauraronsu da gudun gaske ta watsa,sae cikin ɗakin da suka sauka,Tana shiga cikin ɗakin ta daka tsalle,bakinta awashe saboda tsabar dariyar mugunta hada hawaye ke fita a idonta,Amal dake zaune saman gado tana buga game a wayar amani,ganin yadda amani keta dariya kamar wata zautacciya,yasa ta ɗan dakata da buga game ɗin tare da cewa"Aunty Amani meya sanyaki farin ciki har haka"?
Daƙyar ta iya dakatawa da yin dariyar tace"Amal ba zaki gane bane,Wani buri da nake dashi ne ya cika ayau ɗin nan!!waɗanda suka jima suna ƙuntata rayuwarmu,tun yau zasu fara gir6ar abunda suka shuka," tana magana tana dariya,
Murmushi kawai Amal tayi tare da mayar da hankalinta kan game ɗin da take bugawa,
General ishaq na fita daga ɗakin,hayaam ta lalla6a ta fito,yadda kasan lagwanin fitila haka take tafiya,jikin taƙaura yayi la'asar wannan hada magriba ma,zuƙunnawa tayi gaban Aunty babba dake baje ƙasa,ta fashe da wani irin matsanancin kuka,Hafsat na kuka itama tana kuka,babu mai lallashin wani,kowa takansa yake yi,
Cikin shessheƙar kuka hafsat ta soma magana"Allah ya isa tsakanina dake Aunty hayaam,kun cuci rayuwata duk don saboda ku ne mommy ta aikata abunda ta aikata don taga ta cika muku burinku,gashi nan yanzu abun ya shafe ni,kunja daddyna ya kore ni,Ni bansan ku wasu irin mutane bane!sam baku da zuciya kare ya lashe,kun nace kun liƙe dole sai kunyi arziƙi da gumin wasu,ku bazaku tashi ku nemi na kanku ba,sam babu Allah aranku,mugunta kawai kukasa agaba,shiyasa har yau babu wani cigaba acikin lamurranku!wlh yanzu ma kuka fara gani!indai bazaku koma ga Allah ba,,ku tsaya a iya matsayin da Allah ya ajiye ku,ku daina hangen na wasu,wannan dogon burin da kwaɗayin abun duniyar ba inda zai kai ku face ya jefa ku ga halaka....."
Itadae hayaam bata tanka mata ba,saboda bata da abun cewa,har wani zazza6i take ji ajikinta,saboda tsabar tashin hankalin da take ciki,komai ya jagule masu,
Miƙewa hafsat tayi,jiki ba ƙwari ta ƙarasa tare da janyo trolley ɗin kayansu da suka zo dashi,janshi tayi izuwa gaban wardrobe ɗin hayaam,ta buɗeta,kayansu dake aciki tashiga fitowa tana ninkesu,Cikin trolley ɗin take jerasu,
Miƙewa hayaam tayi tana tunanin inda zata samu ruwa ta yayyafa ma Aunty babba,saboda babu ruwa acikin ɗakin,kuma tana jin tsoron ta fita waje suci karo da mutumin,tana cikin wannan tunanin ta tuna da akwai fanfo cikin toilet,da sauri ta shiga ciki a tafin hannayenta ta tarbo ruwan,da sauri da sauri tazo ta yarfa mata shi a fuskarta,dogon numfashi Aunty babba taja,tun kafin ta buɗe idanunta ta shiga fadin"Ruwa!Ruwa!" jin haka yasa hayaam yin tunanin ta fita waje ta samo mata ruwan,buɗe kopar dakin tayi cikin sanɗa ta fito tana tafiya acikin corridor din dakunan nasu,cikin sa'a ta taras babu kowa a main palour din,ƙarasawa tayi wurin fridge ɗinsu,ta bude jikinta na kerma ta ɗauko robar ruwa,da gudu ta koma cikin ɗakin,
Ƙarasawa tayi tare da taimaka ma Aunty babba ta tashi zaune sannan ta miƙa mata bottle water ɗin,A tsiyace ta 6alle murfin robar,ta kafata a bakinta,yadda kasan zata haɗa da robar duka ta cinye,abun kamar yaƙi,ta damƙi robar,sae kwankwaɗar ruwan take,kwatt!kwatt!!har sae da ta shanye ruwan duka tass,sannan ta saki robar ƙasa,sai faman sauke ajiyar zuciya takeyi,hannunta na dafe da kakkauran wuyanta sae faman Murzarshi takeyi,wurin sae raɗaɗi yake yi mata kamar an barbaɗa mata attarugu,idanuwan nan nata sunyi jawur luhu luhu,sae da tadawo cikin hayyacinta sosai sannan ta kalli Hayaam tare da cewa"hayaam meya faru dani ne?ya akai na ganni akwance ƙasa?
Kafin hayaam ta buɗe baki tayi magana,tuni hafsat ta katse mata hanzarinta da cewa"Mommy!kina nufin cewa kin manta duk abunda ya faru?idan ma kin manta bari na tuna maki,Dadddy ne ya damƙi wuyanki ya shaqeki,sannan ya bugaki ajikin bango har saida kika suma,"
Shiru aunty babba tayi tana tariyo abunda ya faru,
"kuma yace mu tattara kayanmu mubar gidan nan,kada mu bari dare yayi mana,bayan haka kuma ya dankara maki saki ɗaya"rai a6ace hafsat ke maganar,
Wata irin mahaukaciyar dariya Aunty babba ta kwashe da ita kamar wata zautacciya,hakan ba ƙaramin mamaki ya basu ba,miƙewa tsaye tayi tana gyara ɗaurin ɗankwalinta tace"Da sauƙi ma,Ni nayi tunanin wani mummunan hukunci zai yanke mun,sai me don ya kore ni?sakin ma da yayi mun wlh ko ajikina,yayi a banza Ae akwai sauran igiyoyi guda biyu,Ni nasan cewa muddin Abbansu yaji cewar ya sake ni,sae yasa ya mayar dani,Ae ni wlh gaba takaini gobarar titi A jos!" To fa,
sakin baki hafsat tayi galala tana kallonta,ba ita kaɗae ba hatta hayaam abun ya ɗaure mata kai,sunyi tunanin cewa in taji ishaq ya sake ta,xata haukace masu ne,amma sae gashi ko ajikinta!zuciyar ta bushe,
Sae faman tiƙar dariya takeyi kamar sabon shiga a fagen hauka,lokaci guda kuma ta murtuke fuskarta,tare da kallon hayaam tace"Maza ki tattara kayanki,don atare dake zamu tafi,"
Hankali tashe hayaam tace"Ni kuma?saboda me zamu tafi atare"?
Shu'umin murmushin nan nata tasaki kafin tace"Saboda inaso,muje wurin bokan nan baba ibliss!wannan karan ba fashi,Dole in kawo ƙarshen auren Amani!kamar yadda zanyi zawarci itama haka nakeso tayi shi,sannan waccen mahaukaciyar yarinyar da tayi silar tona mun asiri har ishaq ya sanya hannunshi ya shaqe mun wuyana na kusa sheqawa barzahu wlh saina yi Ajalinta!!!sannan kuma aurenki da Sgr ba fashi!Wlh ko ta halin ƙaƙa!ko suna so ko basa so sai an ɗaura shi!In har kika ga ba'ayi auren nan ba!To sai dai in bana a doron duniyar nan!ko kuma shi RAFAYET ɗin Ya daina numfashi ne acikinta!sai dai kowa ya rasa wlh!da alama har yanzu basu san wacece Ni ba!zan nuna masu true colour ɗina!Ni dasu shege ka fasa!!" tana magana tana fitar da huci,
Mugun abu kokayi bacci?yace idona biyu 👀!ANA WATA GA WATA,
Zuru hafsat tayi tana kallonta,abun yafi ƙarfinta,lamarin Mommyn nata sae addu'a,tunani ta shiga yi anya Mommynta bata fara shaye shaye ba?kodai tana da iskokai ne?
Suna cikin wannan tsayuwar,aka kwankwaso ƙopar ɗakin nasu,a tsiwace Aunty babba tace"Wanene"?
"OMAR NE" koda jin muryar marshal Omar nan fa kowa ya shiga taitayinsa,
"Hayaam je ki buɗe mashi ƙopa,muji dame yazo!in shima zuwa yayi don yaci mutunci na to bismillah!kowani shege dai dai nake dashi,"kamar wata ƴar daba haka take maganar,
Buɗe mashi ƙopa Hayaaam tayi,tun daga irin kallon da taga Omar ya watsa mata tuni tashiga ƴan kame kame tana sunnar da kai,
Shiga cikin ɗakin nasu yayi,yayin da idanunshi ke akan Aunty babba wadda ke tsaye ta ruƙe qugu,sae faman jijjiga jikinta takeyi kamar wata ƴar bori,
Janye idanunshi yayi daga kanta ya mayar dasu kan hafsat,wadda ke tsaye ruƙe da trolley ɗin kayansu,ganin yana kallonta ne yasa ta ɗukar da kanta ƙasa cike da jin kunyarshi,
"Ina zaki je ne"? Yayi maganar fuskarshi a ɗaure,
Muryarta na rawa tace"dad..dy ne yace mu tattara kayanmu mubar gidan nan kada mu kuskura mu bari dare yayi mana anan,"
"Ban da ke!su kaɗai zasu tafi,"
Wani irin farin ciki ne ya lullu6e hafsat,har ta gaza rufe bakinta saboda tsabar farin ciki,"
Mayar da idanunshi yayi kan Aunty babba dake tsaye ruqe da qugu yace"Major na awaje yana jiranku,idan kun kammala shiryawa ku same shi,Nayi mashi magana zai kai ku hotel ɗin da zaku kwana kafin gobe da safe sae ku wuce maiduguri,Amma fa in kuna so kenan,sannan kuma....'ya ɗan dakata da yin maganar tare da zura hannunshi cikin aljihun jeans ɗin dake ajikinshi ya zaro bendir ɗin kuɗi na ƴan dubu dubu,a ƙalla zasu yi dubu ɗari ɗaya,ya miƙa masu,jiki na rawa hayaam ta kar6e kuɗin tana yi mashi godiya,
...murmushi Marshal Omar ya saki tare da cewa"No,ba sai kin gode mun ba,nayi ne don Allah,'
Yana kai ƙarshen maganar ya juya tare da fucewa daga dakin yana dariya gami da girgiza kanshi,
Bayan fitarshi aunty babba ta buga tsoki,tana faman hura hanci tace ma hayaam"maza ki shirya mana kayanmu,naji ana kiran sallar magrib,zae fi mu lalla6a mu fuce daga gidan batare da kowa ya ganmu ba,nasan duk sun tafi salla,"
Amsa mata hayaam tayi da toh,sannan ta juya tare da shigewa cikin toilet,
Hankalin hafsat ba ƙaramin kwanciya yayi ba,wuri ta samu gefen gadon ta zauna tana faman sakin murmushi,dama babban tashin hankalinta shine idan tabi su Aunty babba maiduguri bazata iya rayuwa cikin gidansu ba,sau ɗaya ta ta6a zuwa,bataji daɗin zama agidan ba,muggan talakawa ne,babu wani abu na more rayuwa acikin gidan,sae ma abun haushi da takaici da zaka taras,
Kusan minti Goma shabiyar sai ga aunty babba ta fito daga cikin toilet ɗin,da alama wanka tayi,xanin atampar jikinta ne tayi ɗaurin gaba dashi,ya jiƙe sharkaf saboda ta ɗauraye shi acikin toilet da ta shiga,
Batare da 6ata lokaci ba,suka shirya tsaf ita da hayaam,dogayen riguna suka sanya ajikinsu,sannan suka aza mayafi daga sama,kama hanyar fita daga ɗakin sukayi,ɗan juyowa aunty babba tayi tare da kallon hafsat tace"sannu hakima yayi maki dai dai wato hankalinki kwance zaki rabu da Mommynki ko rakiya babu"?
Miƙewa hafsat tayi tare da bin bayansu,suka fuce daga cikin ɗakin,ta ƙopar baya suka bi don kada wani yaga fitarsu,a waje suka samu Major tsaye jikin motarshi,ya goya hannayenshi asaman ƙirjinshi,yana ganin sun fito da sauri ya buɗe masu motar,
"Allah ya kiyaye hanya mommy,in sha Allah gobe da safe kafin ku wuce maidugurin zan kiraki a waya,"
Harara aunty babba ta watsa mata kafin tace"Munafuka!Hada wani raku6e fuska kamar irin zakiyi kewata ɗinnan!Ae kada ki damu ki sha kuruminki in dai ni ce zan dawo ne!nan bada jimawa ba,"tayi maganar tare da kutsa kai ta shiga cikin Motar,
"Aunty hayaam Allah ya tsare hanya,Ni dai zan wuce ciki,"
Murmushin yaƙe hayaam tayi,tare da janyota ta rungumeta,daga bisani ta shiga cikin motar,batare da 6ata lokaci ba,Mojar ya shiga mazaunin driver,yayi ma motar key,yaja ta da gudun gaske,Fashewa da kuka hayaam tayi tana leƙen gidan ta cikin gilashin motar,aunty babba sai lallashinta takeyi tana cewa"ke fa banzace,menene abun kuka anan?karki wani damu kanki,Ae babu inda zamuje,ko cikin garin nan bazamu bari ba,Ni nasan me nake shiryawa,AI YANZU WASAN YA FARA,
Cikin shessheƙar kuka hayaam tace"Aunty laila bazaki gane bane,wlh banson inyi nesa da gidan nan!ji nake kamar zan rasa shine gaba ɗaya,na kwallafa raina akan Sgr,duk da bana ganinsa amma zaman da nakeyi acikin gidan nan,yana kwantar min da hankalina,at lease muna kusa da juna,ko ba don haka ba,A yanzu ni banajin zan iya rayuwa acikin gidanmu,kwara nan gidan wlh,kaci mai kyau kasha mai kyau ka kwana a mai kyau,duk da atakure nake kwara nan ɗin da can gidan mu,Jarabar mammy kaɗae ta isa ta Ramar da mutun,babban takaici na,korar wulaƙancin da nayi ma Sofwan nasan cewa yanzu kona nemi taimako awajensa bazai kulani ba,"hannu tasa tana share hawayenta,
Tsoki aunty babba taja mtsww kefa matsakarki kenan!nace maki ki kwantar da hankalinki,ba inda zamuje amma duk kin bi kin tashi hankalinki,sannan in dai akan sgr ne ni nayi maki alƙwarin cewar saina mallaka maki shi,in dai kika ga sgr bai aureki ba to ki tabbatar cewar rayuwarshi a tazuranci zata ƙare,kuma naji kina maganar wani sofwan,uban me zaiyi mana?Ko kin manta cewar Muna da jari atare damu?daga ke harni babu namijin da zai kallemu ya kawar da kansa,Allah ya bamu hasken fata,ga dogon gashi,duk wani abu dake jan hankalin ɗa Namiji ae muna dashi Allah ya bamu,Kinga kuwa muna da hanyar da zamu samu kuɗi,don biyan buƙatunmu,'
Gaba ɗaya duk wannan surutun da sukeyi a kunnan Major,ya kasa kunne yana sauraron su,Sae faman ƙumshe dariya yakeyi acikin bakinsa,abun ban haushi abun ban dariya,
*Boss Bature*
❤REESHRAF�?
A hankali take hawan upstairs ɗin,yayin da zuciyarta ke tariyo mata abunda daddynsu ya sanar da ita,na cewa taci gaba da aiki a part ɗin SGR,kuma tayi mashi biyayya sau da ƙafa,me hakan ke nufi?small box ɗin da daddynsu ya bata,dowry ɗin wanene?ya sanar dani cewa sadakin wata ne,amma dai koma wacece wannan ba ƙaramar mai sa'a bace,halan tafi kowa kyau a duniya ne?shiyasa Aka biya sadakinta da Gold,dama ni wlh,'
Kamar wata zautacciya,sae faman surutai takeyi ita kadae abunta,
Ƙarasa hawa up din tayi,kai tsaye ta wuce part ɗin babban yaya,bata tashi jin faduwar gaba ba,sae da tazo ƙopar shiga falonsa,sannan ta tsaya tana karanto addu'o'in neman tsari,duk don kada ta fuskanci hukunci a wurinsa,bayan ta kammala addu'ar,ta shafa asaman fuskarta da kuma jikinta,kafin tasa ƙafarta ta shiga cikin falon cike da kwarin guiwa,sauke ajiyar zuciya tayi ganin babu shi acikin falon,sae dai daddaɗan ƙamshin turarensa,mai ratsa zuciya,bin falon nasa tayi da kallo,kusan 3 days kenan babu gyara,dama da shirin aiki tazo,wuce wa cikin bedroom ɗinshi tayi,nan ma babu shi aciki,da alama basu dawo daga sallar magrib ba,may be sae after isha,ko kuma ƙarfe goma sha biyun dare daya saba dawowa gida,
Shimfiɗeɗen gadonshi tabi da kallo,zanin gadon duk yayi squeezing,ga blanket ɗinsa ma nannaɗe asaman gadon,bai ɗaukeshi ba,
Hannu tasa tare da zame mayafin sarin dake ajikinta,ta ɗaure shi a qugunta,kwantacciyar sumar kanta na ɗaure acikin ribbon,saman gadon ta haye tare da sanya hannayenta tashiga ƙoƙarin tattaro bedsheet din nasa,Zancen zucin da takeyi ne ya fito fili,
"Matar babban yaya ta shiga uku,na tausaya mata Allah,mutun kullum fuskarshi a daure,kamar ta sa,babu fara'a ko kaɗan,in tayi mashi laifi kuwa zata sha zallan kwaɗi,in kuwa ta fusata shi,ɗaukar ta zaiyi kamar haka,
Tayi maganar tana tattaro bargonsa,ta ɗaga bargon sama tare da yin wurgi dashi,sannan tace"Ya jefar da ita,ko kuma yayi mata irin yadda yayi mun jiya,kamar wata ɗiyar Roba haka zai ruko wutsiyoyin gashin kanta,ya ɗaga ta sama!yana jujjuyata,
Tana cikin wannan sambatun nata,taji anyi mata gyaran Murya,a wani irin firgice ta juya don taga WANENE
*
Join this link to follow my tiktok acct👇
https://www.tiktok.com/@boss_bature?_t=8WKx0lm4jaP&_r=1
قصة حب رومانسية بين سحريش والجراح العام رفايت💋💘❤🤍❤💕💖*
*Father of soldiers*
*🔥TAKUN ƘARSHE🔥*
Waro ido waje tayi tana kallonshi,la66anta har rawa sukeyi wurin furta"bab..babban..yaya," tsananin tsoro ne ya bayyana akan fuskarta,babban abunda ya tayar mata da hankali shine batasan tun yaushe yake tsaye abakin ƙopar ɗakin ba!in kuwa har ya jima a tsaye to tabbas yaji duk abunda tace,
Yana tsaye a bakin ƙopar,ya goya hannayenshi asaman faffaɗan ƙirjinshi,farar shirt ce ajikinsa mai dogon hannu tare da wandon suits ɗinsa fari,hannun nan nashi na sanye da agogon diamond ɗinsa,Ya ɗaure sumar kansa ta baya,fuskar nan babu annuri ko misƙala zarratin,ya ɗaureta tamau,a hankali ya furta"On My bed!"
Jiki na rawa Sehrish ta sauko ƙasa daga saman gadon,cikin in ena tace"am..umm..dama gyara gadon nake yi,shine na hau sama don in samu in tattaro zanin gadon da bar....'
bata ƙarasa maganar ba,ya dakatar da ita"Shut up!banason jin komai"ya ƙarasa maganar tare da shigewa cikin ɗakin,kama hanyar fita daga ɗakin tayi,muryarshi ce ta kuma katseta da cewa"are u done"?
"A'a bangama ba,"ta bashi amsa,
"Okey,"ya ambaci hakan a yayin da yake zame agogon dake hannunshi,
Komawa ciki tayi,sannan taci gaba da gyaran gadon,tana jin lokacin daya shige cikin toilet,da alama wanka zaiyi,ajiyar zuciya ta sauke aranta tace"Allah yaso ni baiji abunda nace ba,dana shiga uku yau,nasan cewa dole ya sanyani tsallan kwaɗi,"shaf shaf ta kammala gyara tamfatsetsen gadon,ta canza mashi bedsheet,ta kuma canza mashi bargon da zai lullu6a dashi,in ya tashi kwanciya,bayan ta kammala gyara bedroom ɗin,ta dawo falo,nan ma ta shiga gyara mashi falon,Cikin ƙankanin lokaci ta kammala gyaran,ko'ina ya koma tamkar sabo,sae ƙamshi ke tashi,
Fitowa tayi daga part ɗin nashi,ta wuce kitchen don ta shirya mashi dinner ɗinsa,a kitchen ta samu Azmee ita da Saude,sun kammala dinner suna gyara kitchen ɗin,gaishe dasu ta fara yi,fuskokinsu a sake suka amsa mata,
"Aunty azmee a shirya mun dinner ɗin babban yaya,inaso zan kai mashi ne,"
Murmushi Azmee tasaki tare da cewa"Masha Allah,ki ce Anyi welcome back kenan,"
Dariya sehrish tayi har fararen hakoranta suka bayyana,bayan ta tsagaita da yin dariyar tace"ae daddy,Ya amince na cigaba da zuwa part ɗinsa,inayi mashi aiki,"
"Amma naji daɗin jin hakan sosai,yanzu bari na shirya maki dinner ɗin,"
Amsa mata tayi da toh,sannan ta tsaya tana jiranta,
Batare da 6ata lokaci ba,Azmee ta kammala shirya mata a warmers da sauran food stuffs asaman tray,ta miƙa mata,kar6a sehrish tayi tare da kama hanyar fita daga kitchen ɗin tana faɗin"nagode Aunty azmee,"
Babu kowa a main palour ɗin,yawanci duk basu kaiga dawowa cikin gidan ba,wasu kuma suna acikin ɗakunansu,tana cikin tafiya hannunta ɗauke da tray,taji maganar mutun abayanta,
"Ƴar shila,"a ɗan firgice ta juya don taga kowanene,gabanta ne ya faɗi Rassss!cike da mamaki take bin shi da kallo yaushe rabon da ta sanyashi acikin idanunta harta manta,ita duk a tunaninta ma an tura shi aikine,ashe yana nan cikin gidan,
Fuskar nan tashi ɗauke da wannan shu'umin Murmushin nashi,ya ƙarasa tare da cin burki ya tsaya tagabanta,Face to face suka fuskanci juna,