Showing 12001 words to 15000 words out of 432432 words

Chapter 5 - Abban Sojoji Book 2 Hausa Novel Complete

sanin Abbansu ba ko Babban yayansu ba, haushin su yarinyar da aka ƙaƙaba musu wadda basu san daga ina aka tsinto ta ba, gashi kuma har ana ɗaura musu responsibilities ɗinta,

"Naji kunyi shiru"? Abbansu ya tambaya yana kallo su,
Kanal yusif yace "Atm ɗin yana a cikin side drawer ɗina, junaid yaje ya ɗauko in zasu tafi,"
  Jinjina kai Abbansu yayi tare da cewa "Haka nake son ji ku fa"?
  har suna haɗa baki wurin cewa "akwai kuɗi cash a ɗakin mu junaid yaje ya ɗibi yarda zai ishe su,in kuma Atm suke so shima yana anan saman mirror muka barshi...." suna magana suna yatsina fuska irin an musu dolen nan,

Kanal yusif yace "A'a Abba ba sai sun bada nasu ba, kawai suyi using da Atm ɗina zasu ishe su har ma su rage," acewar kanal yusif,
   Abban su yace "a'a ni nafison su sauke nauyin dake akansu na ƙanwarsu yakamata tun yanzu su son yadda zasu ɗauki ɗawainiyar mace kafin Allah yasa lokacin auransu yazo,"
. atare suka haɗa baki wurin cewa"Aure kuma Abba,"
  "Eh mana" ya amsa musu,
Kallon Ayaan jahan yayi tare da cewa "tashi mu tafi lokacin aiki yayi " miƙewa Ayaan yayi yana cirar tissue yace "Abba mu mun wuce,"
  Murmushi Abbansu ya saki tare da cewa "adawo lafiya, aure dae ba fashi in lokacinsa yayi mutun ko bai so saina ɗaura masa in yaso ya haɗiyi zuciya ya mutu, zan zauna in ta zuba muku ido ne,"
   fashewa da dariya junaid yayi bashi kadae bama hada su azmee da sehrish, kanal yusif dae murmushi kawai yayi,

Na wani lokaci kowa yabar dining ɗin cikin zumuɗi sehrish ta wuce don ta shirya zasu tafi Shopping mall ɗoki har ba'ayi, shima junaid bedroom ɗinsa ya wuce don ya kimtsa yau zasu yi fita ta musamman da sehrish don ya tsara har ice cream sai sunje sha, haka itama azmee kimtsawar take yi don su fice,

Haroon sam yagaza fitowa saboda kunyar haɗuwarsa da sehrish baisan martanin da zata yi mashi ba, dama jiya ta yarda masa magana a cikin toilet ina ga yau da tasamu ƴanci Allah kaɗai yasan Zagin da zaisha, ga yunwa yana ji amma sai faman zarya yake aransa yana faɗin "Ke ma bazan ƙyale ki ba Yarinya saina ƙasƙantar dake kuma bazan fasa abunda nayi niyya ba akan Ki,*YANZU WASAN YA FARA* 🙆

Fitowa azmee tayi jikinta na sanye da doguwar riga ta atampha ta kashe ɗaurin kallabi, sai ƙamshi take cikin hanzari ta wuce kitchen saboda tunawa da Marshal Omar wanda bai fito yin breakfast ba kuma ba'a kai masa ba, shaf shaf ta shirya masa a tray ta wuce part ɗinsa ta shiga da Sallama babu kowa a falonsa hakan na nufin koma bacci bai tashi ba, ajiye masa tayi asaman ƙayataccen table ɗinsa sannan ta fuce,

Tana saukowa down stairs taci karo da haroon wanda ke tafiya cikin sanɗa zai shige kitchen wai don karya ci karo da Sehrish
  girgiza kai azmee tayi aranta tace "Shi ko haroon ko lafiya yake faman tafiya cikin sanɗa haka kamar mara gaskiya, Ni wlh nama manta dashi ashe yana nan,'
  Gyaran murya tayi tare da cewa "barka da fitowa mlm haroon," firgit yayi tare da juyowa ya kalle ta, ajiyar zuciya yasaki ganin azmee ce "Aunty azmee barka dae fatan an tashi lafiya, shine aka manta dani ina ta fama da yunwa yanzu da ban fito ba da shikenan sai dae yunwa ta kashe ni ko? Ya tambaya hada ruƙe qugu dama ransa a 6ace yake.........
  Azmee tace "Kayi haƙuri wlh ni sam na manta ban lura da baka fito ba ba,"
  ta6e baki yayi tare da cewa "koda yake dama ae ni ba'a sona na lura, bama kallon mutun ake mun ba acikin gidan nan kowa ya raina ni,"

Murmushi azmee tasaki tana kallonsa tace "kadaina cewa haka bana jin daɗi, koda kowa zai guje ka amma kasan ina tare da kai ko? Ka ta6a ganin inda UWA ta Guji ƊANTA?" tayi maganar ne don ta kwantar masa da hankali ganin ya ɗan fusata,
  Sakin fuska haroon yayi sannan yace "Shikenan nadaina aunty azmee tunda baki so, yanzu dai a haɗa mun breakfast ɗina wlh yunwa nake ji har wani jiri nake gani,
   Wuce sa azmee tayi tana cewa "a ina za'a kaima abincin anan ko a ɗakin ka," cikin sauri yace "Ki haɗamun kawai natafi da abuna ɗakina naci,Zai fiye mun kwanciyar hankali na" 
  Kitchen ɗin tashiga ta haɗa masa a tray sannan ta miƙa masa jikinsa na rawa ya kar6a ya wuce ɗakinsa,
  Gefen gadonsa ya zuna hannunsa har kerma yake yi yana cusa abincin abakinsa, kamar daga sama yaga sehrish ta bayyana agabansa jikinta sanye da Kayan Sadaukai na Yaƙi, hannunta ruƙe da Zungureriyar wuƙa kanta na ɗauke da Kambun Sarauta, hankali atashe haroon ya fesar da donuts ɗin daya cunkusa abakinsa yana kallonta cike da tashin hankali, fashewa da dariya sehrish tayi tare da cewa "Kai Haroon! Ƙaryarka taƙare ! ka jima kana ƙuntatamun gashi yanzu Allah ya ɗaukakani, babu wata sauran barazana daga gare ka ta ƙare, nazo ne don na ɗauki fansa akan ka, yanzun nan zan fille kanka da wannan wuƙar ta hannu na,
  Da ƙarfi sehrish ta ɗaga wuƙar zata fille ma haroon kai, aikuwa a firgice ya miƙe tsaye yana dafe saitin zuciyarshi a tsorace

Lokaci guda Sehrish ta 6ace masa 6aaat hakan na nufin ba ita bace idonsa ne ke masa gizau,amma shi tabbas ita yagani kodai yarinyar Aljana ce ? Ya tambayi kansa,.wannan ba kowa bace face Hafsat Bature Aljanar sehrish 👿
Koma wa yayi ya zauna yana ci gaba da cin breakfast ɗinsa anatse, yayin da ransa ke saƙa mashi abubuwa da dama game da mummunan ƙudirinsa

__________    💪    ______________

OMAR a hankali ya soma buɗe idanunsa bakinsa na ambaton addu'ar tashi daga bacci, yayin da zuciyarsa ke cike fal da son ganin Tagwayensa, tun da asuba daya sha maganin mura bacci mai nauyi yayi awon gaba dashi sai yanzu Allah yayi mashi ikon Farkawa daga bacci, a hankali yasa hannun sa ya janye blanket ɗin daya lullu6a dashi jikinsa na sanye da Night dress riga ce dai dai guiwa mara nauyi, fararen idanuwansa yafara kaiwa ya kalli agogon dake manne jikin bango ƙarfe 12 na safe yayi mamakin yadda lokaci ke gudu har haka, ko don yayi overdose na maganin muran daya sha ne yasa shi yin dogon bacci har haka,
  Cikin sauri ya yunƙura ya miƙe direct toilet ya wuce , brush yafara yi yana tsaye agaban wash basin amma idonsa Fuskar Jahad da Hosana take hasko masa ta cikin mirro ɗin gabansa, shaf shaf yayo wanka ya fito jikinsa sanye da Bathrobe(rigar wanka) fara, wadda ta tsaya masa adai-dai guiwarsa, Marshal Omar kenan Son kowa ƙin wadda tarasa 😉
  kai tsaye wuce wa yayi ya ɗauki wayarsa dake a saman gadonsa, sak irin ta sgr ce, Company ɗaya ce waya ce ta musamman domin Manyan jami'an sojoji irinsu kirar Companyn Iphone Ce, hamshaƙiyar waya haɗaɗɗiyar gaske wadda kuɗinta sun haura 30millions, ba kuɗinta bane abun mamaki ba a'a amfaninta shine abun dubawa, ƴar bala'en wayace bakowa ma zai iya Controlling ɗinta ba sai mamallakinta.
  dannata ya soma yi Contact ɗinsa ya shiga kai tsaye numbar aunty BABBA ya laluba, ya buga mata Calling ta shiga ringing, burinsa tayi picking yasanar da ita cewa Zai shigo kaduna don ya duba su Hosana da Jahad, almost 3 times ba'a ɗaga kiran ba, domin kuwa wayar tabar ta agida, canza ra'ayi yayi ya dannawa Wayar Hafsat kira,

Suna a asibitin nan zaune saman waiting seats, bacci duk ya kwashe su daga zaune don daren jiya ba wanda ya runtsa sai da sassafe wurin ƙarfe 10 suka samu baccin wahala shima saboda likita yasanar dasu cewa Yarinyar da ranta bata mutu ba, farkawa ne kawai batayi ba doguwar suma tayi, shine suka ɗan samu natsuwa suka baje suna bacci kamar wasu shanaye ga uwar yunwa na cinsu, kiran Omar ne yashigo da ƙarfin gaske a wayr hafsat dake acikin purse ɗinta data aza saman cinyarta, a firgice suka farka su duka wuri wuri da ido, cikin hanzari hafsat ta zura hannunta cikin purse ɗinta ta duba me kira sunan MARSHAL OMAR ne ya bayyana, dafe ƙirjin tayi hankali atashe tace "MUNSHI GA UKU ! MOMMY YA OMAR NE KE KIRA"😳

   Mu haɗu ranar monday Insha Allah🙏

Kar amanta da paymemt wanda suka shirya sumin magana 08103884440, 300 ne VIP kuma 700 ga wanda basa ra'ayi a grp*💋💋💋ABBAN SOJOJI💋💋💋*

*🔥The Father Of Soldiers🔥*

ﻗﺼ�? ﺣﺐ ﺭﻭﻣﺎﻧﺴﻴﺔ ﺑﻴ�? ﺳﺤﺮﻳ�? ﻭﺍﻟﺠﺮﺍ�? ﺍﻟﻌﺎ�? ﺭﺍﻓﻴﺖ❤‍🔥💞💘�?

*Story & Written by*
*Hafsat Bature Muhammad*

~💋BOSSLADY💋~


*Abban Sojoji part 2*

*EPISODE 7-8*

*AYAAN* arab name ne for boys means God's Gift (kyautar Allah) ❤️


Waro ido waje aunty babba tayi tana faɗin "Shikenan komai ya ƙare, Hafsat kada ki ɗaga kiran nan, katse shi kwai , a rude take magana, Hafsat tace "Mommy how can i reject his calls ! Idan zuwa zai fa ? ba kwara na ɗaga naji mai zai ce ba, don mu son yadda za'ae mu dakatar dashi ba.....' ta ƙare maganar tare da ɗaga kiran ta ƙara a kunnanta tana Zabga sallama,
Hankali atashe aunty babba ke cewa "Kisa wayar handsfree," cikin hanzari hafsat ta mayar da kiran handsfree don aunty babba tasamu damar jin abunda Marshal Omar ɗin zai ce,
  Bayan ya amsa mata sallama yace "Zan Shigo kd yau insha Allah ki sanarwa Mommynki," yana faɗin hakan ya katse kiran since bfr hafsat tace wani abu,
Cikin tashin hankali Hafsat ta janye wayar daga kunnanta,a wani slow tana kallon mommynta wadda itama kallon nata take yi ido azare,
  Murya tamkar zatayi kuka tace "Mommy duk ke kika ja mana wannan bala'en da muke ciki, gashi nan daga ni har ke ba wanda ya runtsa daren jiya rabon mu da abinci ma tun jiyan, yanzu kuma gashi Ya Omar zaizo, Ina fata kin tanadi bayanin da zakiyi masa game da Twins ɗinsa da kika Faffasa ma fuska, ki ka canza musu kamanni, nayi imanin kema Ya omar bazai barki ba, sai ya Canza miki kamanni, don Allah naushi ɗaya zai ma kumatun nan naki Mommy sai an neme su an rasa a fuskarki,'
Tuni ido ya raina fata, aunty babba tace "hafsat ki daina mun waɗan nan suratan naki ki barni inji dakaina, yakamata musan abun yi before Omar ya diro garin nan,'

Zama su kayi zugum kowa zuciyarsa na bugawa daram daram, kowa da irin idea dake zuwa masa akai,
  Jahad kuwa na a ɗakin da aka kwantar da hosana dama gado biyu ne aciki, itama doctor sai da ya duba ta, baccin wahala kawai take yi saboda allurar da dr yayi mata don tasamu bacci, duk inta farka sai ta ambaci sunan Hosana saboda itace aranta, so take tama fi ƙarfin allurar da dr yayi mata, don ƙoƙori take ta tashi da ƙarfin gaske don taje ma hosana wadda ke kwance magashiyyan rai hannun Allah 😥

______________________________________

Bayan Omar ya kammala wayar fitowa yayi daga bedroom ɗinsa ya zauna a palor saman sofa yana yin breakfast ɗinsa anatse, wayarsa ce ta shiga ringing wadda ya ajiye agefensa, kai idonsa yayi ya duba Gwaggon katsina ce ke kiransa, murmushi yasaki don kusan kullum saita kira layinsa ta tambayesa ina Ƴa'ƴan Abusufyan ɗinta ya basu su gaisa, hannu yakai ya ɗauki wayar ya kara a kunnansa yana faɗin "Gwaggona kenan fatan kin tashi lafiya,"
Daga can 6angaren gwaggon katsina tace "Allah sarki Omar jiya ko isasshen bacci ban samu ba saboda tunanin ƴa'ƴan abusufyan ɗina, Jiya zuciyata tayi ta bugawa inaji kamar wani abu ya same su, dan Allah Omar karka bari a cutar dasu,
Sai faman zuba take masa a waya sam taƙi bari yace wani abu har sai da ta gaji ta dakata da maganar sannan Omar yace "Ki kwantar da Hankalin ki goggo na, Ƴa'ƴan abusufyan ɗinki suna nan cikin ƙoshin lafiya,"
  Ajiyar zuciya tasaki kafin tace "Suna tambayata ko? Suna atare da kai Omar? Ka basu dan Allah muyi waya mana,"
  omar yace "Goggo kin manta suna a kaduna,ae gidan Yaya ishaq nakai su..."
Kamar tana agabansa ta zabga salati
tana cewa "La'ila ha illallah Mahammadar rasulillah Omar ! dama gidan Ishaq ka kaisu? Gidan wannan matar Shuwa mai ƙirar samudawa sam matar nan bata da Imani, zuciyarta irin ta kafuran farkon ce wlh, shikenan ni Allah kaɗae yasan wane hali ƴa'ƴan abusufyan ɗina suke ciki .  ......fashe masa da kuka goggon katsina tayi,

Sam omar ya gaza gane ma goggon tasu, a tunaninsa haukan nata ne ya tashi, in ba haka ba ina matar ishaq keda aibu har haka, gashi kuma ta fashe mashi da kuka, cikin rarrashi yace "Calm down your mind Goggona, ƴa'ƴan abusufyan ɗinki suna cikin ƙoshin lafiya, yau ma nake shirin zuwa in dubo su,'
   Cikin shessheƙar kuka tace "To shikenan amma dan Allah Omar nidai nafison su bar gidan matar nan, adawo mun dasu nan in basu kulawa kamar yadda na kula da mahaifinsu tun yana yaro,"
Murmushi Omar yasaki sannan yace "Insha Allah my aunt don't worry ur self abt them, suna Lou and insha Allah in naje zan basu waya ku gaisa kiji muryarsa may be u will be calm,"

  "Shikenan Omar kada ka manta sai na jika,"
   Ya amsa mata da cewa "Insha Allah"

daga bisa ni su kayi sallama ya ajiye wayar yaci gaba da Cin breakfast ɗinsa,

Acan ciki kuwa tuni Sehrish ta shirya kayan mazan ne ajikinta tunda su ke gare ta, hijab kawai tasanya ajikinta brown colour, azmee kuwa dama atampa ce ajikinta, Mayafi kawai ta lullu6a a jikinta ba ƙaramin kyau tayi ba, suna a babban falon sai ga junaid shima ya sauko, bin shi da kallo sehrish tayi jikinsa na sanye da suits baƙaƙe kamar ma'aikacin banki, yayi kyau sosai acikinsu abun sai wanda yagani, sai faman murmushi yake saki da white teeth ɗin nan nasa kamar gonar auduga,
"Gsky junaid bazan iya jerawa dakai ba, Irin wannan kyan haka," sehrish ta faɗi tana nuna shi da hannu,
  Ƴar dariya junaid yasaki kafin yace "duk kyan da zanyi bazan fi ki ba, ke fa maca ce, ni kishi ma nakeyi don nasan yanzu zaki fara ɗaukar wanka da zarar munyi Siyayyar nan,"
  Murmushi sehrish tasaki ita kanta har ta hango ta cikin Gown ta gayu wow, azmee ma murmushin take saki, atare suka jera suka fuce, a cikin Motar Junaid haɗaɗɗiyar gaske, Shi ke driving yayin da sehrish ke a gefensa sai faman fira suke suna zuba, azmee na a back seat tana sauraron su  wani lokacin ma tana sa musu baki suna firar atare, suna ta tiƙar dariya abinsu gwanin burgewa, har suka isa katafaren shopping mall ɗin mai matuƙar girman gaske, sehrish taga haɗuwa yau dae karo na farko data fito kuma karo na farkon data fara ziyartar wuri irin wannan, atare suka fito suka shiga wurin, Mutane gasu nan kowa ya ɗau wanka ana ta siyayya ba kowa ya tsone mata ido ba face ƴan mata da samarin dake a wurin, duk sai taji kunya ta kamata ganin yarda Matasan matan dake a wurin siyayyar suka ɗau wanka iya wanka, ita kuwa kallo ɗaya za'ae mata ansan bazata wuce ƴar aiki ba,
  6oyewa ta rinƙa yi abayan junaid da Azmeee, dariya kawai junaid keyi don ya gano dalilin dayasa sehrish jin kunya tana la6ewa abayansu,

Sam ruwan ido ya hana sehrish Sa hannu ta ɗauki wani abu, junaid ne kawai da azmee ke faman ɗebar mata kayayyakin sawa iri iri masu kyan gaske na mata, yawanci arab gowns ne, turkish dress, night dress, Pakistan, english wears komai jidar sa kawai suke yi, laces ne atampa ce, materials, shadda,  Everything,
  Duk tana tsaye tana kallonsu kowanne ya cike shopping basket dake hannunsa, sai dai in sun matsa nan tabisu, in kuma anzo abunda zata gwada tasanya su bata taje dressing room ɗin dake a wurin ta sanya,
lokacin da suka zo wurin jerin panties da bra, hannu junaid yasa ya ɗauko brazier ya ɗago da ita yana cewa "Sehrish Ga wannan gwada mu gani,"
Sam bata lura ba tana ta faman kalle kalle, ganin hakan yasa shi ta6o hannunta yana nuna mata bra ɗin dake hannunsa yana cewa "Ina magana," aikuwa cikin jin kunya ta zaro ido tare da sa hannu ta rufe fuska tana faɗin "junaid dan Allah kadaina menene haka agaban mutane," fashewa da dariya yayi cikin mamaki yace "menene aciki? Kunya kuma ni bansan wannan zancen ba, ni dae ki amsa kawai kije ki gwada in tayi maki, in batayi ba acanza wata shine kawai,"
  Hannunta na kerma ta karba tana ɗan kallon shi, har time ɗin dariyarsa yake Don shi mamaki ta bashi wai kunya,
  Shiga dressing room ɗin tayi hada datso kopa, faskekan madubi ne aciki ya cike bangon, cikin hanzari ta tu6e hijab ɗinta da rigarta, ta shiga kiciniyar zira bra ɗin daker hada su sakin nishi,
  Tsayawa tayi tana kallon kanta acikin mirrow ɗin wow, ta fito ɗas abunta dama tubarkallah masha Allah full ɗinsu suke, bra ɗin ta hau raɗau launin ta maroon colour ce, abunda sehrish take ma mamaki yarda akai junaid ya nemo bra dai-dai size ɗinta,duk jerin braziers ɗin dake a wurin,
Cikin hanzari ta cire ta, ta mayar da rigarta da Hijab ɗinta, sannan ta fito, karaf suka ci karo dashi abakin ƙopan ɗakin,
  a ɗan razane tace"junaid yaushe kazo nan," hannu yasa ya ɗan sosa sumar kansa yana cewa "Naji kin jima ne, shine nazo in ga ko kin gaza sawa ne, sai in taimaka miki.....," ganin yarda ta waro ido waje yasa shi dakatawa, muryarta har wani shaƙewa take yi wurin cewa "Junaid kana nufi brazier ɗin zaka taimaka mun nasa !!" ta tambaya a rikice,
  Kai tsaye yace "eh mana,"  Jinjina kai sehrish tayi tare da wuce shi aranta tana mamakin hali irin na junaid shidae ba ruwansa komai normal ne a wurinsa,
  tsayawa ta ɗanyi da tafiya ta ɗago ta kallesa Cike da tuhuma tace "Ya akai kasan size ɗina?
  Da buɗar bakinsa sai cewa yayi "Ni dana ga Zahiri,"
Cikin sauri yasa hannu ya rufe bakinsa saboda su6ul da

Chapters

Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login