Showing 183001 words to 186000 words out of 432432 words

Chapter 62 - Abban Sojoji Book 2 Hausa Novel Complete

buɗe bakinshi ya kwashe dukkan abunda ya faru ya sanar masu,
  ba ƙaramin tausayinta suka ji ba,jikinsu duk yayi sanyi sosai,bayan komai ya daidaita,Sgr ya wuce part dinshi a gajiye,
Azmee ce tayi ƙoƙarin ɗaukar sehrish ta wuce da ita cikin bedroom ɗinta,asaman gado ta kwantar da ita,tare da jan bargo ta lullu6e mata jikinta,ta jima azaune cikin ɗakin nata tana kallonta a ranta tana tunanin ya akai ta fita daga gidan,a lokacin ta samu bacci,sae da dare ya raba sannan azmee ta koma ɗakinta,

Koda sgr ya shiga bedroom din shi,gaba daya kasala ta gama mamaye mashi ko'ina na jikinshi,hakanan ya dinga jin kamar yaje ya ganota,wane hali take ciki,ta samu bacci kuwa,tunani ya soma yi anya ba dalilin datse mata gashin da yayi bane yasa tayi yunƙurin guduwa daga wurinsu ba?saboda ya lura ba ƙaramin so take ma gashin kannan nata ba,
Ya ƙarasa zancen zucin nashi a yayin da yake ƙarasa cire kayan jikinshi,zame belt ɗin wandonshi yayi ya tube shi daga jikin trouser ɗinshi,abunda sehrish tayi mashi ɗazun ne ya faɗo mashi a ranshi,lokacin da takai hannunta asaman mararshi,tuna wannan yasa shi jin wani yanayi mara misaltuwa atattare dashi,ya rasa me yasa yarinyar take ƙoƙarin canza mashi alƙiblarshi,da alama in baiyi dagaske ba zata ci nasara akan shi ne,
Sai da ya kammala cire kayan jikinshi ya rage daga shi sae white short ajikinshi,sannan ya wuce cikin toilet don yin wanka,

Bayan ya kammala wankan ya fito jikinshi sanye da bathrobe fara,wata irin kasala ta mamayeshi,har ya gaza shirya kanshi acikin sleeping dress dinshi,a ƙarshe ya lalla6a tare da hayewa saman gadon shi,hannu ya miƙa tare da janyo pillow ya rungumo shi asaman faffaɗan kirjinshi,a hankali ya rufe idanunshi da niyyar yin bacci nan take brain dinshi,ta shiga tariyo mashi abunda ya faru tsakanin shi da sehrish,ranar da ya taka 6awon ayaba,ta tarboshi suka faɗa saman gadon shi atare,'
Mamaki ne ya kama sgr,ya shiga tambayar kanshi Why yake tunaninta?me yasa yake tuna abubuwan da suka faru atsakaninshi da yarinyar?me yasa take ta faɗo mashi aranshi?
juyi yayi asaman katafaren gadon nashi ya canza position din kwanciyar tashi,ya jima a wannan yanayin kafin ya samu bacci yayi awon gaba dashi,

A tsakar dare junaid ya farka daga bacci,dama tun kafin ya kwanta baccin yake ta addu'ar Allah yasa ya farka tsakar dare yayi sallah,sae gashi kuma cikin sa'a ya farka,dama sama rai ne abun,saukowa yayi daga saman gadon ya wuce cikin toilet,jim kaɗan ya fito daga cikin toilet din,ruwan alwala na ɗiɗɗigowa daga fuskarshi,darduma ya dauko tare da shimfiɗata,ya kabbara salla tare da wannan kyakkyawanr niyyar tashi,anatse ya shiga jera sallolin batare da gajiyawa ba,tun yanayi cikin daɗin rae,har ƙafafunshi suka soma rurruƙewa sannan ya sallame sallar tare da lankwashe kafafunshi asaman sallar ya ɗaga hannayenshi yana addu'o'i yayin da hawaye ke 6ul6ulowa daga cikin idanunshi,gwanin ban tausayi,

Bayan ya kammala addu'o'in nashi ya tattara dardumar ya ninketa,bayan ya ajiyeta,yana ƙokarin komawa saman gadon ya kwanta,wani abu ya faɗo daga cikin hancinshi,cikin sauri junaid yakai idanunshi a kasan inda abun ya fadi,
Dunƙulen jini ya gani,nan take hankalinshi yayi mugun tashi,jikin shi ya shiga kerma,gaba ɗaya yabi ya rikice ya razana sosai,ganin yarda dunkulen jinin ke faɗowa daga hancinshi,da gudun gaske ya faɗa cikin toilet,agaban basin ya tsaya tare da dukar da kanshi,dunkulen jinin ya cigaba da fadowa,tashin hankalin da ba'a sama shi date,haƙika junaid yana cikin mawuyacin hali,gashi yaƙi sanarma kowa bare atari abun da wuri,kuma da alama koma meye ya gama yi mashi Illah,

Daƙyar ya samu dunkulen jinin ya daina 6ul6ulowa daga hancinshi,ya wanke fuskarshi tare da kora jinin da ruwa ya wuce,.
Sannan ya fito daga cikin toilet din hannunshi ruƙe da tissue din daya yago,zukunnawa yayi tare da kwashe dunkulen jinin daya fara fitowa daga hancinsa ya faɗi kasan tiles din dakin,acikin tissue din ya dauke shi sannan ya jefa acikin room dustbin dinsu,
jikin shi yayi mugun sanyin da bai ta6a yi mashi ba,Wanda hakan ya ƙara tabbatar mashi da cewa da wuya ya rayu,in ba wani ikon na ubangiji ba,
jiki asanyaye ya taka izuwa wurin bedside drawer,ya ɗauki wayarshi dake ajiye anan sama,lalubo numbar mommynsu yayi tare da danna mata kira,
Ringing ta shiga yi,kusan sau uku ba'a ɗaga ba,ana hudunne ta ɗaga kiran tare da cewa"Hello,babyn Abbanshi,yau kaine da kanka ka kirani awaya?ae nayi tunanin ka manta dani"
maimakon yayi mata magana,sae ji tayi ya fashe mata da kuka,
A gigice Alexandra ta shiga ambaton sunan shi tana cewa"Ju..ju..junaid..meya faru ne!me yasa kake kuka?waya ta6a min kaine!?
Cikin shessheƙar kuka ya soma magana"Mommy ba zaki zo ba ko"! Yanayin yarda taji muryarshi yasa jikinta yin sanyi,
Cigaba da magana yayi"dama nasani baki sona mommy,da ace kina sona ba zaki kai wannan lokacin baki zo kin duba halin da nake ciki ba,Mommy so kike sae ranar dana mutu sannan zaki zo ki ga gawata!"
gabanta ne taji yayi wani irin bugu,maganar shi ba ƙaramin kashe mata jiki yayi ba,muryarta na rawa tace"pls Romeo na,kadaina wannan maganar banason ji,dan Allah kadaina......'yana jin shessheƙar kukan mommyn nasu,
cikin sanyin murya yace"Shikenan zan daina mommy,amma inaso na sanyaki acikin idanuna,inaso na ganki a matsayin mahaifiyata,don Allah kizo mommy kafin na mutu ....idan baki zo ba bazan yafe maki ba.....'
Wannan maganar ta junaid ba ƙaramin firgita momyntasu yayi ba,
Hankali tashe ta shiga cewa"its okey,zanzo zanzo kayi shiru kaji zanzo insha Allah,'
"When"?yayi maganar ayayin da yake share hawayen fuskarshi da hannunshi guda,yayin da dayan ke maƙale da wayarshi,
"Ko da yaushe kakeso junaid zanzo,"
Jinjina kanshi yayi tare da cewa"gobe mommy,idan ya wuce gobe ba zaki ganni ba,"
cikin sauri tace"zanzo kaji My baby boy,ina sonka sosai,"
Lumshe idanunshi yayi har cikin ranshi yaji wani irin sanyi ya ratsa shi,yanzu baida wani burin daya wuce ya sanya mahaifiyar shi acikin idanunshi,bai ta6a ganinta ba ido da ido,tsoranshi karya mutu bai sanyata acikin idanunshi ba,
"Naji kayi shiru baka ce komai ba"
Muryarshi a kasalance yace"Bacci nake ji mommy zanje na kwanta,dare yayi sosai,yanzu ma farkawa nayi daga bacci,shine na kiraki a waya," murmushi tayi tamkar tana a gabanshi tace"kafin ka aje wayar zan tambayeka wani abu,"
Junaid yace"ina sauraronki mommy,"
Cigaba da magana tayi "ranar daka fara gani na,ido cikin ido faɗamun wane kalar farin ciki za kayi,kuma wata irin tarba zakayi mun,"
Sae lokacin junaid ya ɗanyi murmushi tare da cewa"Bazan iya bayyana farin cikin da zanyi ba,a wannan lokacin,abu daya kawai nasan zanyi shine zan rungumeki sosai na kankameki na kwantar da kaina asaman ƙirjinki sannan na kira ki da sunan Mommyna,"
dariya sosai Alexandra tayi ba ƙaramin daɗin maganar shi taji ba,
tsagaitawa tayi da yin dariyar da takeyi sannan tace"Ni kuma kasan me zanyi a wannan lokacin"?.
"A'a sai kin faɗamun,"ashagwa6e yayi maganar,
Alexandara tace"ni kuma a wannan lokacin da zan fara sanyaka acikin idanuna a matsayin yaron dana bari tun yana ɗan jinjirinsa na tafi nabarshi ban ƙarasa shayar dashi ba,zanji kunyar ka sosai junaid kuma zan zubar da hawayena a wannan lokacin,sannan in janyo ka ajikina nayi hugging naka very tight,zan shafa sumar kanka da hannuna.....'kasa ƙarasa maganar tayi saboda wani sabon kukan da taji yazo mata,
cikin shassheƙar kukan taci gaba da cewa"Junaid ka yafe mun,na cutar dakai sosai,ban kyauta maka ba,nayi maka alƙawarin cewa muddin nazo nigeria zanyi maka duk wani abu da banyi maka ba,a lokacin da kake yaro,shayar dakai ne kawai bazan yi ba,shima ɗin don saboda ka wuce matakin da zan shayar dakaine,amma har goya ka sai nayi,komai zan maka junaid,koda yaushe zan kasance tare dakai,zan baka farin cikin da ban baka ba a lokacin da kake yaro... '
natsuwa junaid yayi yana sauraron kalaman mommyntasu,hankalinshi ba ƙaramin kwanciya yayi ba,ta faranta mashi rae sosai a daren ranar,sun jima suna waya,kafin daga bisani sukayi sallama ya ajiye wayar saman drawer din,sannan ya koma saman gadon ya kwanta,tare da aza kanshi asaman bayan Abban nasu dake ta sharar bacci,

Allah sarki junaid,bazan ta6a mantawa da wannan lokacin ba arayuwata,na zubar da hawaye na sosae akan rashin shi da nayi............"


A 6angaren su hosana kuwa,saboda sun kwallafa rai akan ganin sehrish daren ranar ko bacci ba suyi ba,a zaune suka kwana,su biyu tsakiyar gadon sun manne da Juna,
"Jahad me kike tunani"?hosana ce ta tambayata tana kallon fuskarta ganin tana ta faman sakin murmushi,
Jahad tace"Ina tunanin ko ya Sehrish ta koma yanzu?ta ƙara haske ne?ko ta ƙara kiba?Ya zata ji idan ta ganmu.!

 
  
*SANARWA SANARWA*💃💃💃💃


*ME TAKEN NA AMARYA HUTAA$$*

*MUNA FARIN CIKIN SANAR DAKU CEWA MUNA BADA HAYAR KAYAN AMARYA(WEDDING GOWN), KAYAN BRIDAL SHOWER, KAYAN BIRTHDAY PARTY, KAYAN FITAR SUNA, SANNAN MUNA BADA HEAD AND SHOULDER, MUNA DA POSS, MUNA ALKYABBAR KAI AMARYA KO TARON WALIMAR SAUKA, MUNA DA KAYAN FULANI FARARE NA YARA DANA MANYA MUNA DA NA AMARYA BLUE BLACK, SANNAN MUNA GYARAN JIKIN AMARYA DA UWARGIDA CIKIN KWANA UKU CAKAL ZAKIGA KIN KOMA TAURARUWA MAI WALWALI. MUNAYIN TURARUKAN WUTA DA HUMRA DA KOLACCAR, KOWANNE KALA KIKE BUKATA AKWAI CIKIN FARASHI MAI SAUKI.*


*LOCATION KANO*

08062073990
Ina kuke mata hamshakai wayanda suka amsa sunan su wajen mazajen su ina mata masu son qamshi shin ko kunsan tsafta bata tafiya seda qamshi ina masu son turare mai riqon gida tareda qamshin shi mai sanyaya zukata mardie collection tazo muku da dadadan turarukanta masu lasting riqon gida harma da jiki ku tuntube mu da nmb kamar haka 08136666994 inda zaku samu kaya kamar haka
Wadrobe balls
Madarar kulleccham
Vaseline kulleccham
Kajiji
Halut
Couscous
Khumrah
Da dai sauransu harda abin wanke toilet yayi tas komi dafe warshi wato BETHALEX METAL ku garzayo kar ayi baku


Ina kuke mata hamshakai wayanda suka amsa sunan su wajen mazajen su ina mata masu son qamshi shin ko kunsan tsafta bata tafiya seda qamshi ina masu son turare mai riqon gida tareda qamshin shi mai sanyaya zukata mardie collection tazo muku da dadadan turarukanta masu lasting riqon gida harma da jiki ku tuntube mu da nmb kamar haka 08136666994 inda zaku samu kaya kamar haka
Wadrobe balls
Madarar kulleccham
Vaseline kulleccham
Kajiji
Halut
Couscous
Khumrah
Da dai sauransu harda abin wanke toilet yayi tas komi dafe warshi wato BETHALEX METAL ku garzayo kar ayi baku

It's not just good ...it's finger linking good faster than fast food, better fine dining.
Snack
Awarah
Farah
Zobo
Samosa
Cup cake etc
Contact me 09063302182or 09012179727. *💋Boss Bature💋*



Join this link to follow my tiktok acct👇

https://www.tiktok.com/@boss_bature?_t=8WKx0lm4jaP&_r=1




قصة حب رومانسية بين سحريش والجراح العام رفايت💋💘❤🤍❤💕💖



Ga duk maison karanta littafin Abban sojoji,zai biya 300 ne,za'a tura mashi tundaga farko har inda muka tsaya,kuma zai cigaba da samun update dinshi akai akai,ga wanda ke buƙata zai tura mun message ta whatsapp ɗina (08103884440) kada ku bari abaku labari,




"Nima jahad,inaso naga ya rishi ɗinmu ta koma,a qagare nake da naje naganta,Allah yasa gobe ya Omar yazo ya ɗauke mu da wuri  ya kaimu gidansu,"cike da farin ciki tayi maganar,

"Da zarar mun ga rishi shikenan bamu da sauran damuwa,abu ɗaya ya rage mana shi ne ganin Mahaifiyarmu,

Inason sake ganinta bansan a wane hali take ciki ba,"jiki asanyaye Jahad ta ƙarasa maganar,
  haka suka zauna tsawon daren nan suna jiran safiya tayi.

Wuraren sallar asuba,gaba daya matasan gidan suka hallara domin zuwa gabatar da sallah,daga ciki hada Uncle ɗinsu Abusufyan,a jere suka jera tare dashi,yadda kasan tsaran su Sgr haka ya koma acikin su,

A 6angaren sehrish kuwa,raɗaɗin ciwon nan ne ya kuma tashinta daga dogon baccin daya ɗauke ta,wata irin zufa ce ta shiga gangaro mata a gefen fuskarta,jikinta na ta faman kerma,daƙyar ta iya yunƙurawa ta miƙe daga zaune tana faman ƙanƙame jikinta tana dan bin dakin da kallo,sam bata lura da jacket ɗin da Rafayet ya zura mata ba,

Jin alamun ana kwankwasa ƙopar dakin yasa ta yin saurin cewa"wanene,"
Muryar azmee taji daga waje tana cewa"Ni ce sehrish,"
Bayan ta bata amsa ta turo ƙopar ta shigo,saboda a buɗe tabar mata ita daren jiya,
  "Kin tashi kenan,"ta ambaci hakan yayin da take ƙarasawa daga gefen gadon nata ta zauna tana kallon fuskarta,
   Muryarta na kerma tace"Aunty azmee bana jin daɗi,tun jiya nake fama da ciwon ciki sosai,bansan me yasa junaid baizo ya ɗaukeni daga school ba,ina fata dai lafiyarshi qalou ko"?tayi tambayar fuskarta ɗauke da damuwa,
  Cike da mamaki Azmee tace"kamarya junaid baije ya ɗauke ki daga school ba!?nifa da kaina na ruƙe hannunki lokacin da kika dawo daga school na kawoki har cikin bedroom ɗinki sannan na shirya maki lunch ɗinki,"
  Tunda azmee tasoma kora mata jawabin nan,gaba daya duk tabi ta rikice saboda bata gane inda ta dosa ba,
  "Aunty azmee wlh bani bace,nifa bani da lafiya,ina can kwance cikin toilet ɗin makarantar mu,bana acikin hayyacina,har aka tashi daga skul bansani ba,sae bayan da kowa ya watse sannan naji sauƙin cikin nawa,shine har na samu na fito,lokacin da nazo bakin gate ɗin babu kowa acikin makarantar,mai gadi ne ma yace na koma daga waje na jira mai zuwa ɗaukar tawa..............'gaba ɗaya sehrish ta kwashe duk abunda ya faru ta sanar ma Azmee har zuwa inda taji an ɗauketa an turata cikin mota,tun daga nan ne bata ƙara sanin meya faru ba,

Hankalin Azmee fa ya tashi,abun ya ɗaure mata kai,musamman da taga Uniform ajikin sehrish wannan ya ƙara tabbatar mata da cewa daga school ɗin take,tunani ta shiga yi,shin wacece kuma Yarinyar da junaid ya ɗauko daga makaranta a maimakon ita sehrish din!kodae Aljana ce ya ɗauko!tabbas zai iya yiyuwa aljannar ce in ba haka ba,kamanninsu yayi yawa komai na fuskarsu iri ɗaya,
  jin sehrish na sakin nishi yasa azmee dawowa daga duniyar tunanin data tafi,cikin sauri ta ruƙo hannunta tare da cewa"Tashi mu shiga toilet na taimaka maki kiyi wanka da ruwan zafi,kafin mu fito nasan cewa sun dawo daga masallacin,zanyi ma wani daga cikinsu magana yayi ma babban yayansu magana akan ya baki maganin da zaki sha ki samu sauki,
  a hankali tasamu ta sauko daga saman gadon tabi azmee suka shige cikin toilet din,daga baya azmee ta fito ta barta acikin toilet din tana ƙarasa wankan,
   Zagaye ɗakin nata Azmee ta shiga yi,yayin da take cigaba da tunanin Wacece wannan yarinyar da tazo gidan ɗazu mai irin fuskar sehrish komai da komai,tabbas mutunce ba aljana ba,abun yayi confusing dinta,
   amma me yasa ta tambayeni ya Omar na nan amaimakon Sgr!
   Azmee ce ta jefa ma kanta wannan tambayar,lokaci guda ta tuna da twins ɗin da Omar yace zai kawo gidan Abusufyan ɗinsu,tabbas ba shakka yarinyar tasan Marshal Omar shiyasa har ta tambayeta shi,
  cike da mamaki azmee ta ɗan tsaya daga zagayen da take yi na wani lokaci ta ɗanyi shiru tana nazarin wani abu kafin daga bisani tace"in har dagaske ne abunda nake hasashe,wannan yaran da Omar yake Ruƙo a wurinshi,ƴan uwan sehrish ne!dama ta ta6a sanar dani cewa su ƴan ukune,kuma kamanninsu ɗaya sak!ina tunanin cewa Yaran suma a makarantarsu sehrish suke,wannan dalilin ne yasa junaid yayi kuskuren ɗauko yarinyar amaimakon sehrish !"
Bata da tabbacin abunda take hasashe ko gaskiya ne,amma ranta na bata cewa tabbas haka ne!
   fitowar sehrish daga cikin toilet,yasa azmee juyawa tana kallonta,daƙyar take iya ɗaga kafarta,jikinta na sanye da inners farare,half vest da kuma white short wanda bai kai guiwarta ba,
  Ganin yadda take tafiya tana dafe saitin mararta yasa azmee,ƙarasawa wurinta da sauri ta janyo ta ajikinta,ta taimaka mata harta haye saman gadon,abu kamar wasa sehrish ta soma yarfa hannu tana ambaton sunan Allah abakinta,daga bisani kuma tashiga bubbuga ƙafafunta asaman gadon tana matse cikin nata,
  Cikin fita hayyaci take cewa"Aunty zan mutu!cikina zafi yake mun,kamar ana ƙona ƴan hanjin cikina,ko'ina raɗaɗi yakeyi mun,"
  Jin wannan maganar ta sehrish ba ƙaramin tayar mata da hankali yayi ba,
juyawa tayi da sauri ta fuce daga cikin ɗakin,kai tsaye ta nufi main palour din tana jiran ƙarasowar su,saboda taji dirar motocinsu alamar sun shigo cikin gidan,
    Marshal Omar ne tare da Sgr suka fara shigowa cikin babban falon,yayin da Uncle abusufyan ke abayansu shi da Abbansu sae Junaid dake ruƙe da hannun Uncle din nasu acikin nashi,
  ganin azmee atsaye cikin damuwa yasa Omar cewa"meya faru ne naganki atsaye nan?
tsayawa da tafiyar suka yi gaba daya suna jiran jin amsarta,
   hankali amatuƙar tashe azmee tace"Sehrish ce bata jin daɗi sosai,tana acan ɗaki na barota tana ta kuka tana cewa zata mutu..dan Allah a taimaka mata,"
    Omar yace"subhanallahi!meya ke damunta ne?
  "Ciwon ciki ne,"ta bashi amsa,matsowa Abbansu yayi kusa dasu Omar yace"Tasha magani ne"?
  "Bata sha komai ba,"azmee ta amsa mashi,
  Mayar da idanunshi yayi kan Sgr dake tsaye ya goya hannayenshi asaman ƙirjinshi,
   Yace"Ko zaka iya taimakawa ka duba mana ita ne?in yaso ko allura ce sae ayi mata,zata fi samun relief ɗin ciwon nata,"
  sakin hannayenshi yayi daga saman chest dinshi,sannan ya kalli azmee tare da cewa"muje ɗakin nata,"
  murmushi Abbansu ya ɗan saki ba ƙaramin daɗi yaji ba,daya amince zai duba ta,shi fa yanzu abbansu kallon mata da miji yake yi masu,tun ranar daya fara kamasu manne da juna,tun daga ranar ya daina yi masu kallon wai saurayi da budurwa,fatihar ce kawai ba'a kaiga shafawa ba,
  "Yaya hussein wai wacece bata da lafiya ne"?Abusufyan ne yayi mashi tambayar a lokacin da suke wucewa daga cikin,
  Fuskar abba ɗauke da murmushi yace"Yarinyar dake taya azmee aiki ce,itace ɗazu junaid yake magana akan ba'a ganta ba,hankalinmu duk ya tashi da 6atanta,cikin ikon Allah sae gata an samu rafayet ya dawo da ita cikin gidan nan,"
Abusufyan yace"Allah ya bata lafiya,"
Abba ya amsa mashi da ameen,
  Daganan suka raba hanya dashi,kowa ya wuce bedroom ɗinshi,

Acan kuwa,bayan Azmee tayi ma sgr jagora har izuwa ɗakin sehrish,ita tafara shiga sannan ya bi bayanta har izuwa wurin gadonta,karo na farko kenan da Sgr yafara shiga ɗakin Sehrish,lokacin ne yama san inda dakin yake,tsayawa yayi daga tsaye yana kallonta,sae faman juyi takeyi atsakiyar gadon gaba ɗaya tagama fita hayyacinta saboda raɗaɗin ciwon cikinta,
  Hannu azmee tasa tare da janyo bargo ta lullu6e mata jikinta,ganin yarda surar jikinta ta fito sosai,
   "Wane kalar ciwon ciki ne takeyi"?yayi maganar ba tare daya kalli azmee ba,yana da tabbacin cewa menstruation ne,amma yafiso yaji daga bakinta,
  "Na al'ada ne,"azmee ta bashi amsa,
 

Chapters

Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login