Showing 30001 words to 33000 words out of 432432 words
Chapter 11 - Abban Sojoji Book 2 Hausa Novel Complete
gidan, sai lokacin tasamu damar yin wanka tare da alwala tafito ɗaure da towel, agaban dressing mirror ta zauna saman kujera tana Shafa mai ajikinta, bayan ta kammala ta feshe jikinta da turare, sannan ta koma ta buɗe wardrobe ɗin kayanta, ta ɗauko dogon skirt brown color ta zura sannan ta sanya t-shirt fara, daga nan ta zura hijab tare da shimfiɗa carpet tayi sallah anatse, tun kafin ta kammala azmee ta turo ƙopar ɗakin ta shigo, wuri ta samu gefen gadonta ta xauna,
bayan sehrish ta kammala sallar ta naɗe dardumar ta mayar da ita cikin wardrobe tare da hijabin, sannan ta juya da fara'a tana gaishe da azmee "Ina yini aunty azmee,"
Azmee tace "lafiya lou sehrish, zo ki zauna,"
Ƙarasawa tayi ta samu wuri kusa da ita ta zauna, azmeee tace "sehrish wai ina wayarki take ne? Na lura tun ranar dana baki ita, ban sake ganinta a hannunki ba, kodai baki so ne?
zuru sehrish tayi don ita tuni ta manta da zancen wata waya, kuma ba kowa bane yaja mata hakan ba face haroon, shine silar damuwar da tashiga harta manta in da ta jefe wayar
"Ina sauraron ki ina wayar"? Azmee ta ƙara nanata mata, cikin en ina sehrish tace "Aunty azmee tun....ranar...da...kika...ban...ita..na manta inda na ajiye...ta,'
ta ƙarasa maganar tana ɗan kallonta azmee tace "Sehrish kenan kin cika shiririta yanzu wayar mai tsada ita kika 6atar? To ina so ki nemo ta yau ɗin nan duk inda take, in ma saman ceilling kika turata ki hau saman ki fiddo ta, Ki kawo min ɗaki na ina jiranki,!" tana faɗin hakan ta tashi ta fuce........
tafa hannu sehrish ta shiga yi tana tunanin ta ina zata fara neman wayar, ita kanta abuƙace take da wayar ko don ta rinƙa ɗebe kewar zama ita kaɗai aɗaki,
Tashi tayi cikin ƙanƙanin lokaci ta hargitsa ɗakin wurin neman wayarta, duk ta zabure har ƙarƙashin gado ta leƙa, ta bincika cikin laundry basket ɗinta, gaba ɗaya ta zazzago kayan wankinta dake cikinsa babu komai, agajiye ta mayar da kayan, zarya tashiga yi tana tunanin ina ta wurgar da ita, ci gaba da neman wayar tayi, a ƙarshe tayi deciding zuwa ɗakin junaid ta roƙesa ya kira layin wayar ko tayi ringing,
cikin hanzari ta ɗauki mayafinta dake ajiye saman bed ɗinta, ta yarfa shi a head ɗinsa, sannan ta fita cikin sauri babu kowa a babban falon direct upstairs ta wuce da ƙarfi take tattaka stairs ɗin ko kallon gabanta batayi burinta kawai ta isa bedroom ɗin junaid,.
Kamar daga sama taji ta bugi wani abu da ƙarfi nan take wani irin jiri ya kwashe ta, agigice tasaki wata irin ƙara ganin yarda ta tafi gaba ɗaya zata faɗi amma ina tuni yayi mata wani irin kwakkwaran ruƙo da hannu guda ya tallabo waist ɗinta,
Zazzare ido sehrish tayi cikin Jin tsananin tsoro yayin da take faman sauke ajiyar zuciya,
gabanta ne ya soma faɗuwa saboda tuna hannun wa take a ruƙe, sam tagaza ɗago ido ta kalle sa, ae tun daga ƙamshin turaren nan nasa ta shaida kowane ne,
ɗago da ita yayi ta tsaya da ƙafafunta sannan ya wuce abunshi, juyawa sehrish tayi cikin sauri tana kallonsa ba ƙaramin wanka ya ɗauka, har sai da ya fice daga babban falon sannan ta kawar da idonta sannan ta ƙarasa haye wa upstair ɗin, har time ɗin jikinta wata irin kerma yake yi hannunta na dafe da ƙirjinta,
A hankali tayi knocing ƙopar ɗakin junaid tana buga ƙopar a slow saboda zuciyarta dake tariyo mata abunda yafaru yanzun nan,
kusan 3 times tana knocking sai daga bisa tajiyo muryar junaid yace "Come in,"
Ashe door ɗin a buɗe take, tana zura ƙafarta ciki karaf taci ido dashi gaban mirror daga shi sai short towel a waist ɗinsa sam baisan cewa sehrish bace, ta cikin mirror ya hangota, aikuwa cikin sauri yace "dakata !! Kada ki shigo! Ja baya," dariya sehrish tayi sannan taja da baya ta tsaya jikin ƙopar tana cewa "Junaid yaushe ka fara jin kunyata har haka"?
daga cikin ɗakin tajiyo muryarsa yana cewa "tun ranar dana gane cewa ke maca ce.....,'
Murmushi ta saki tana faman sauke ajiyar zuciya har time ɗin temperature ɗin jikinta yayi mugun zafi ba don komai ba sai don abunda yafaru da ita yanzun nan,
"Come in Sehrish," junaid ya faɗi,
Shiga ciki tayi a lokacin harya zura jallabiya ash colour ajikinsa yana gyara hannun rigar,
wuri tasamu agefen gadonsa ta zauna tana cewa "Junaid dama wannan wayr tawa nake nema narasa inda na jefar da ita, shine nazo ka taimaka ka kiramin layin dake cikinta, may be in tayi ringing in gano ta,
Murmushi junaid yasaki kafin yace "shikenan zan kira maki ita, amma under one condition? Ya faɗi ayayin da ya tsaya agabanta ya ruƙe qugu, sehrish tace "Menene sharaɗin?
Junaid yace "Tun ran nan nake ta fama dake ki nunamin gyaran gashin ki kin ƙiya, to yau indai kina So na kira layin wayarki sai kin cire mun nagani" ya faɗi yana murguɗa mata baki,
Yamutsa fuska tayi tare da cewa "look junaid yanzu ba lokacin wannan bane, am not in mood Just ka kiramun wayar,' ta faɗi tana tsuke baki,
Bin shi tayi da kallo ganin ya ɗan ɗaure fuskar shi alamar baiji daɗi ba,
Cikin lallashi tace "junaid are u angry with me? Am sorry pls ni bazan so naga king of smile ya koma king of Angry ba,' tayi maganar da ɗan zolaya,
Ɗan sakin fuskarshi yayi sannan yace "its ok, go back to ur bedroom i wanna call u righ now,"
Murmushi sehrish tasaki tare da cewa "yawwa mutumi na, Allah yabar mun kai," ta faɗi tare da miƙewa ta wuce bedroom ɗinta cikin sauri,
Junaid kuwa acikin ransa yace "Ameen sehrish Allah yabarmun ke till the end of my life,' sannan yasa hannu ya ɗauki wayarsa dake ajiye saman mirror, contact yashi ga tare da lalubar nombar sehrish da yayi mata Saving da*FUTURE DREAM* sa'an nan ya danna mata kira,
tunkan sehrish tashiga ɗakinta ta rinƙa jin ringing ɗin wayar da ƙarfin gaske, tura ƙopar ɗakin tayi ta shiga ciki tana bin inda sautin ke fitowa, ashe tana cikin bedside drawer ɗinta, duk wannan uwar wahalar da tasha, cikin hanzari ta janyo drawer chest ɗin gida na farko, sai ga wayar ajiye sabuwarta kusan 1 month kenan tana ajiye bata mutu ba, saboda ruƙon chargyn ta, ajiyar zuciya sehrish tasaki tana shasshafa screen ɗin wayar da hannunta,
. .........................tuna da azmee dake jiranta yasanya ta fice da wayar cikin sauri ta isa ƙopar ɗakin azmee knocking tayi daga ciki taji azmee tace "in kin son bada wayar kika zo ba ki koma," wato har ta gane ce sehrish ce ta kwankwasa mata,
Gyaran murya sehrish tayi tare da cewa "Tare da wayar nazo aunty azmee,"
Azmee tace "shigo ciki,"
Tura kopar sehrish tayi ta shiga, samun ta tayi kishingiɗe saman gadonta, ganin sehrish yasa ta tashi zaune tana cewa "yanzu naji magana,"
Murmushi sehrish tasaki tare da samun wuri gefen azmeen ta zauna sannan Ta miƙa mata wayar tace "Gata,"
Azmee ta kalli wayar tare da cewa "dama ba wani abu zanyi da ita ba, ke nake so ki runƙa amfani da ita akai-akai takasance tare dake, saboda daga yanzu duk wani mai buƙatar wani abu ke zai kira kai tsaye a waya yasanar miki," jinjina kai sehrish tayi alamar gamsuwa da bayaninta,
Sannan azmee taci gaba da cewa "nikam inaso na tambaye ki, shin kin ta6a yin makaranta ne before?
ɗagowa sehrish tayi ta kalle ta a wani irin yanayi kamar wani abu yaɗan sosa mata zuciya, shiru tayi na wani lokaci kafin tace "eh nayi primary bayan nan nafara secondry karatun duk ashiriri ce ƙarshe ma muna gab da zamu shiga ss3 nadaina zuwa gaba ɗaya......' ta ƙarasa maganar asanyaye
Azmee tace "yanzu kina da burin ci gaba da karatun ne ko kuwa a'a? Ta tambaya tana kallonta,
Sehrish tace "ina so mana sosai, ina so nayi Ilmi saboda wata rana nima nazama abun alfahari, kuma wannan burin mahaifiyarmu ne, tun lokacin da ta haife mu takance Sehrish zata zama Achitecture, Hosana kuma Doctor, Jahad kuma Nurse haƙiƙa inaso nacika mata wannan burin nata.......................' idonta ne suka cuko tab da kwalla sunnar da kanta tayi ƙasa tana kallon wayar dake hannunta,
Cikin mamaki azmee ke kallonta ita kanta sehrish batasan me take cewa ba, ci gaba da magana tayi kawai tana cewa "Allah sarki a lokacin ni nafi kwarewa wurin yin zane, hosana ce mai ƙoƙari acikin mu amma yanzu bata da cikakken hankali tun lokacin da ta duro daga saman window mai tsayin gaske ..........ban......ban.......
Kasa ƙarasa maganar tayi saboda kukan da yazo mata nan take ta fashe da matsanancin kuka,
Gaba ɗaya hankalin azmee ya tashi sam tarasa gane ma sambatun da sehrish ke yi, cikin ruɗu tace "sehrish wai meke faruwa ne? Su wanene waɗannan kike magana akansu ne? ƴan uwanki ne?
ɗaga mata kai tayi alamar "Eh" jinjina kai azmee tayi tare da cewa "share hawayenki daina kuka ya isa haka, duk da bansan Labarin ki ba amma ina da tabbacin cewa wani mummunan abu yafaru acikinsa wanda ke yawan saki cikin damuwa, don haka zanso naji labarinki sehrish amma ba yanzu ba aduk lokacin da muka samu free time sosai zamu zauna ki bani shi tun daga farko har ƙarshensa,'
"Insha allah aunty azmee na yarda dake sosai baxan 6oye maki komai ba," ta faɗi ayayin da take share hawayen ta,
Bayan sun samu natsuwa su duka azmee taci gaba da cewa "Zaki fara zuwa school insha Allah....'
Cikin mamaki sehrish ta ɗago ta kalle ta tare da cewa "Makaranta? Ni kuma? Aunty azmee taya za'a ɗauke ni a school bayan ko takardun kammala primary ɗin bani dasu na rasa su,'
"Kada ki damu sehrish wannan ba wata damuwa bace, komai za'a iya yi maki shi insha Allah, kuɗi ne kawai ke magana, kuma ni zan tsaya maki harki samu don nasan muddin na tuntu6i koda kanal yusif ne da maganar zai iya sama maki hanya, bama shi ba junaid zai iya yi maki wannan hanyar cikin sauƙi ki fara daga ss1 daga baya kin zana Jsce in time ɗinta yayi,'
Wani irin farin ciki ne ya lullu6e sehrish har tagaza rufe bakinta, aranta tana cewa nan bada jimawa ba nima zan fara zuwa makaranta kamar kowa ?Alhamdulillah 😇
Hannu azmee tasanya ta kar6i wayar hannun sehrish tana cewa "ina fata junaid ya nuna miki komai ko?
"Eh harma ya tura mun wasu apps ɗin da zanyi amfani dasu,"
Azmee tace "okey, idan kina so kiyi amfani da data ko wurin yin browsing da sauransu just Wi-fi kawai zaki kunna, '
Jinjina kai sehrish tayi alamar gamsuwa, sun ɗan jima suna fira kafin daga bisani ta sallame ta, komawa bedroom ɗinta tayi cike da murna koba komai in tafara zuwa school zata haɗu da friends irinsu Hafsat Bature Domin ɗebe kewa 😇
Sehrish first day at school 😮 Can't wait to see 💃💃💃💃
Ga wanda ba suyi payment ba su hanzarta su biya before end of this week👍 Yanzu littafi Zai fara 🔥🔥🔥 (08103884440)
LAFAZI WRITERS ASSOCIATION ®_* ✍️
──────────────EPISODE 17-18
ﻗﺼ�? ﺣﺐ ﺭﻭﻣﺎﻧﺴﻴﺔ ﺑﻴ�? ﺳﺤﺮﻳ�? ﻭﺍﻟﺠﺮﺍ�? ﺍﻟﻌﺎ�?
ﺭﺍﻓﻴﺖ💋❤�?
*Mallakin Hafsat Bature Moh'd*
~BossBature~
•·•·•·•·•·•·•·•·•·••·•·•·•·•·•·•·••·•·•·•·•·•·•·�? bayan Jahad ta kammala wankan ta canza kaya ixuwa doguwar riga, hawa tayi itama saman gadon kusa da hosana suna daf da juna tace "hosana me kike tunani game da hafsat da mommynsu? Anya ba wani abu suka shirya mana ba? Kada fa ace so suke yi su kashe mu ko su zubar damu shiyasa suka tsara mana hakan,' tayi maganar cikin nuna damuwa a fuskarta,
Hosanna tace "jahad ni nasan abunda mommynsu hafsat ta shirya mana, fuska biyu tayi mana wlh, so take ta nuna mana kulawa sosai don mu saba da ita yadda in yaya Omar yazo yace zai tafi damu muƙi binsa saboda sun nuna mana kulawa.........' dakatawa tayi da maganar jin alamun tunkarowar mutun ɗakin da suke ciki,
Hafsat ce ta shigo ciki fuskarta ɗauke da murmushi tace "sannunku My sisters ya jikin naku"? Ta tambaya ayayin da take samun wuri saman room sofa ɗin tazauna,
"Alhamdulillah da sauƙi" suka bata amsa atare, mayar da idonta tayi gefen kujerar da take zaune leda ce ajiye wadda taba Jahad ta ruƙe mata bayan ta fito daga store, hannu tasa ta ɗauki ledar tana cewa "Lahh Jahad wannan ae naku ne na siya maku, Chocolate ne da sweet ko bakwa so ne"? ta tambaya tana kallonsu,
Suka haɗa baki wurin cewa "muna so," sannan jahad ta sauko daga saman gadon tasanya hannu biyu takar6a tana fadin "mungode Aunty hafsat,"
Murmushi hafsat tasaki tare da cewa "Naji daɗin sunan nan da kuka kira ni dashi, amma nafison ku kira ni da Sister Hafsat akan aunty hafsat zanfi jin daɗin hakan,"
Murmushi su kayi su dukan su, kafin daga bisani Jahad ta curo musu chocolate cookies ɗin data siya musu, guda biyu ta curo ta ɗauki ɗaya sannan ta miƙa ma hosana suka 6are suna sha,
Har lokacin idon hafsat na akansu kallonsu takeyi gwanin burgewa, dama tun ranar farko data fara cin karo dasu sun burgeta kawai baƙin hali ne irin nata yasa bata nuna ba,
Ɗagowa su kayi jin alamar shigowar mutun, AUNTY BABBA ce ta shigo fuskarta ɗauke da murmushi tana kallonsu tace "Ya jikin naku My daughters?
haɗa baki su kayi wurin cewa "da Sauƙi Alhamdulillah,"
Jinjina kanta tayi kafin daga bisa ni ta kuma cewa "Yakamata ku fito mana kuzauna a palour ko kallo ne kuyi zai ɗebe muku kewa kuma zaku samu nishaɗi,"
Amsa mata sukayi da "Toh" sannan suka sauko daga saman gadon hannun jahad ruƙe da ledar choculate ɗinsu,
A falon suka samu wuri saman gujera mai mazaunin mutun biyu su ka zauna tare da mayar da hankalin su Wurin kallon shirin da akeyi a tashar Bollywood, tuni kallon ya ɗauke musu hankali saboda daɗin dramar da suke yi ta india, dama kuma ga chocolate ɗinsu suna sha sai abun yaƙara nutsar dasu gaba ɗaya,
AUNTY BABBA kuwa wuri tasamu ta zauna agefen gadon tana fuskantar hafsat tace "Sannu Madam,"
tashi hafsat tayi zaune tana cewa "Mommy dama ina son magana dake! Wannan canjin dana gani a tattare dake shin dagaske ne? Ko duk shiri ne? ta tambaya tana kallonta don jin amsar da zata bata,
ɗan ƙayataccen murmushi AUNTY BABA tasaki tare da cewa "Hafsat kenan ! Ke naso ki fara faɗamun gaskiyar lamarin nan shin dagaske ne yanzu kin fara jin tausayin yaran nan?
"Mommy da gaske ne, natausaya musu sosai saboda bugun rashin imanin da kika yi musu, kuma ayanzu bana son wani yaƙara ƴunƙurin cutar dasu daga ni har KE !
Ajiyar zuciya aunty babba tasaki tana mai jinjina kai tace "Shin ya maganar matar da kika amsar ma kuɗi kusan miliyan shidda? Mayar mata su zakiyi kenan.....?
Hafsat tace "wannan ni tashafa mommy, zan san yarda zanyi da ita, in ma bazaiyiyu ba just zan mayar mata da kuɗinta ne,"
ɗan ta6e baki AUNTY BABBA tayi daga bisani tace "Shikenan Daughter but lemme remind u something, kin manta da uban bashin da Ake bin ki kenan u ave to think about it, how can u pay all ur debt? Dole ki buƙaci kuɗi ....................tana kai ƙarshen maganarta, ta tashi ta fuce tana faman sakin shu'umin murmushi aranta tana cewa "Yarinya kenan! Naki wasa ne,"
**********💪💪💪***************
misalin ƙarfe 5 da rabi na marece a lokacin suna dab da kammala aikace-aikacen su na girki, sai ga OMAR ya shigo cikin gidan kai tsaye kitcen ya nufa in da suke, Hankalin sehrish ba ƙaramin tashi yayi ba ganin OMAR don atsorace take dashi,
bai shiga kitchen ɗin ba tsayawa yayi daga waje ba tare da yace komai ba,
Sehrish ce tace "Aunty Azmee ga yaya Omar nan," azmee na jin haka cikin sauri ta fito izuwa inda yake tsaye da murmushi a fuskarta tace "Omar ashe kaine ina fata lafiya dai ko,"
Jinjina kansa ya ɗanyi ayayin da idonsa ke kallon sehrish wadda ke acikin kitchen taƙi ɗagowa su haɗa ido dashi, har time ɗin ya gaza gasgata abunda idonsa ke nuna masa,
ɗan gyaran Murya yayi tare da mayar da idonsa kan na Azmee yace "Sannuku da ƙoƙari, ina fata dai ban katse maku aikin ku ba"
Azmee tace "A'a wlh Ae ma mun kammala girkin gyaran kitchen ɗin ne kawai ya rage mana yanzu,"
OMAR Yace "Okey, dama aiki ne nake son kuyi mun ke da waccen Yarinyar ta cikin kitchen,'
Jin hakan yasa sehrish ɗan ɗagowa suka haɗa ido dashi cikin sauri ta sunnar da kai ƙasa,
Azmee tace "Wane kalar aiki kenan Omar?
"Zan baku makullin gidan Uncle ABUSUFYAN so nake Kuje can ku duddubamun gidan duk wani abu da ake buƙata kawai inaso ku rubuta mun shi,"
Murmushi azmee