Showing 42001 words to 45000 words out of 432432 words
Chapter 15 - Abban Sojoji Book 2 Hausa Novel Complete
jin gabanta na faɗuwa, bata kai ga hawa benen ba, taji dirar motoci cikin gidan nan take ta sake jin faɗuwar gaba, cikin sauri ta haye upstairs ɗin da hanzari ta shiga bedroom ɗin junaid a lokacin yana cikin toilet yana wanka, ajiye masa tray ɗin tayi saman table, sannan tafito da sauri-sauri ta fito daga babban falon ta tsaya abakin ƙofar shigarsa, .
Kamar dai ranar da SGR da Omar suka zo Nigeria tare da uban security guards na sojoji haka yau ma, tsoro ne yakama sehrish gudun kar ace US zasu koma,
Tana ganin lokacin da suka shiga cikin motocinsu kuma nan take motocin ajere suka nufi dogon titin da zai fidda ka daga cikin gidan,
Komawa ciki tayi da gudun gaske ta faɗa kitchen tana faman kwalama aunty azmee kira, a ɗan razane azmee ta juyo ta kalle ta tare da cewa "Sehrish lafiya kuwa kike ta faman kwalamun kira haka!?
Cikin tsananin tashin hankali tace "Aunty azmee meke faruwa ne? Yanzun nan naga Babban yaya tare da Yaya Omar, sun fito fuskokinsu ba annuri kuma ga tarin motoci can sun fita dasu,"
tsayawa azmee taɗan yi jimmmmmmm tana ɗan tunani kafin tace "Tabbas ina hasashen cewa Us zasu tafi Saboda ɗazu da safe naji ƙishin-ƙishin ɗin cewa Momynsu matar Uncle ɗinsu donald tana fama da blood cancer, To ina da tabbacin cewa kodae ta rasu ne...........'
Zaro ido sehrish tayi cikin tsananin tashin hankali take furta "Innalallahi wa'inna ilairaji'un Allah yasa bata mutu ba, Yanzu shikenan in suka koma ko yaushe zasu dawo.....'
Murmushi Azmee tayi kafin tace "naga kin tayar da hankalin ki, nasan saboda Tafiyarsu Rafayet ne bawai don jin mutuwar ba,
Hannu sehrish tasa tare da rufe fuska saboda hawaye da taji sun tafo mata,
bin ta da kallo kawai azmee tayi cike da mamakin ganin tana shessheƙar kuka,
Matsawa tayi kusa da ita tare da dafa ta tace"Sehrish !! Wannan kukan na menene? Ba dai don tafiyarsu bane?
shiru kawai tayi batare da tace komai ba, ita kaɗai tasan me take ji aranta, gaba ɗaya fuskarta ta damuje da hawaye,
Jinjina kai azmee tayi tare da cewa "Ki koma ɗaki ki kwanta kawai,"
Cikin kuka sehrish tace "a'a aunty azmee zanyi aikin,"
Azmee tace "a'a banaso ki tafi kawai zan ƙarasa abuna,"
Juyawa sehrish tayi tare da fuce wa daga kitchen ɗin ta koma bedroom ɗinta, saman gado tafaɗa tare da cigaba da kukan, To fa sehrish komai yasata yin kuka? Allah wa'alamu,
Azmee kuwa ta jima tana mamakin dalilin kukan Sehrish tarasa gane mata, aranta tana cewa "Badai saboda tafiyar SGR take kuka ba? Don ta lura da yadda sehrish ke matuƙar ƙaunarsa, sam bata iya fira batare da ta, Amabaci sunan shi ba ita dae kawai tafison jin Ana maganarsa,nan zakaga sakewarta,
"Lallai ne akwai Babbar Matsala, muddin abunda nake zargi ya tabbata,ya zama dole in ja ma Sehrish burki, don gujema kamuwa da CIWON ZUCIYA,"!! Azmee ta faɗi acikin ranta,
_______________________
Sehrish kuwa Tuni wani Irin zazza6i taji ya rufe ta lokaci guda, jikinta har kerma yake yi wurin janyo bargonta dake asaman gadonta ta lullu6e jikinta dashi, tana faman fidda numfashi mai zafin gaske, sam tarasa ina zata tsoma ranta ita kaɗai tasan irin raɗaɗin da take ji acikin zuciyarta
Har wuraren Sallar Magrib sehrish bata motsa ba, tana nan yarda take ƙudundune cikin barko,tamkar mai bacci alhalin nan Idonta biyu jikinta ne kawai da bayayi mata daɗi, Acan ciki kuwa fitowa junaid yayi bayan yasha baccin sa, ya sauya kayan jikinsa izuwa riga da wando, lokacin daya sakko down yayi mamakin ganin Azmee ita kaɗai tana faman jera masu dinner a dining, ƙarasawa yayi cikin sauri yana cewa"Aunty Azmee ina sehrish ɗin ne? Ita bazata fito ta tayaki ba? Azmee ta ɗan ɗago ta kallesa tare da cewa "Junaid ni kaina bansan meke damun Sehrish ba, Lafiya lou fa muke aiki da Ita, amma tunda tazo ta tambaye ni game da babban yayanku da Omar da taga sun fito fuskarsu cikin wani irin yanayi, kuma taga Sun fita tare da motoci dayawa, shine nake ce mata may be Us zasu je, tunda ɗazu da safe naji ƙishin ƙishin ɗin cewa Matar Uncle ɗinku donald tana fama da blood cancer may be ta rasu ne.....shine fa kawai sehrish takama kuka har nace mata ta koma ɗakinta kawai ni zanyi aikin," ta ƙarasa maganar cikin damuwa, Junaid kuwa shiru yayi hankalinsa ya rabu gida biyu, sam ya rasa gane inda maganar Azmee ta dosa, cikin mamaki yace "Us kuma? Taya babban yayan mu zaibar ƙasar nan batare da sani na ba? Anya kuwa aunty Azmee am just doubting about it bana tunani Us zasu je, kuma Matar uncle donald bana tunanin ta rasu gaskiya, tunda da naji ko a wurin Abban mu ne, Ni dai Allah yasa ba wani abu bane ya faru mummuna," ya faɗi cikin tashin hankali kafin ya wuce yana cewa "Bari naje wurin Sehrish ɗin naji meke damunta,"
Azmee tace "to shikenan,"
A hankali ya tura ƙopar ɗakin yashiga da sallama, tsayawa yayi yana kallonta yarda take ƙudundune cikin bargo, A hankali ya kira sunanta "Sehrish..........' shiru bata amsa masa ba, ƙarasawa yayi izuwa gab da gadon nata yaɗan zauna gefe tare da sa hannu ya yaye mata bargon dake jikinta, dogon numfashi taja tare da cewa "Junaid ka mayar mun da bargona, Sanyi nake ji," Junaid yace "Reesh wai meke damunki ne? Aunty azmee ta faɗamun cewa kinbar kitchen kina faman kuka? Cikin kuka tace "Junaid wai dagaske ne cewa Babban yaya da Yaya Omar us zasu koma yau? Sakin baki junaid yayi yana kallonta cikin tsananin mamaki amma bai kawo ma ransa komai ba sai cewa yayi "Sehrish dama akan wannan kika shiga damuwa? to ki kwantar da hankalin ki, Yaya Omar da yaya Rafayet bana tunanin sun bar ƙasar nan ne, Aunty azmee ce kawai tace maki hakan a hasashen ta, just calm down ur mind My lovely sis... . ...........jin abunda junaid yace yasa ta sauke ajiyar zuciya tare da miƙewa zaune daga saman gadon tana cewa "ngde da jin hakan junaid, naji ma anata kiran sallar magrib bari naje nayi alwala," junaid yace "to shikenan nima bari naje nayi salla,pls reesh karki ƙara sa damuwa irin haka, kuma in kin kammala sallar, ki fito muyi dinner atare," Murmushi ta sakar masa tare da cewa "Ok my lovely bro, da zarar nayi sallah zan fito nima," lumshe ido junaid yayi tare da buɗe su akanta fuskar nan ɗauke da Murmushi, sai da yaga sehrish tashiga toilet sannan yafuce hankalinsa a kwance..........................�?
remain 2 pages free su ƙare, wanda baiyi payment ba ya hanxarta Yi, Abban Sojoji 300 ne, discount da nayi na Abbban sojoji fans group ne kawai 200, Vip kuma 700, bank details ɗin da za'a tura,3196407426 First bank, Bature Hafsat Muhammd Evidence of payment 08103884440
[9/13, 11:08 AM] 💋BOSS LADY💋: *💋💋💋ABBAN SOJOJI💋💋💋*
•·•·•·•·•·•·•·••·•·•·•·•·•·•·•·•·�?
*_LAFAZI WRITERS ASSOCIATION ®_* ✍️
──────────────EPISODE 23-24
ﻗﺼ�? ﺣﺐ ﺭﻭﻣﺎﻧﺴﻴﺔ ﺑﻴ�? ﺳﺤﺮﻳ�? ﻭﺍﻟﺠﺮﺍ�? ﺍﻟﻌﺎ�?
ﺭﺍﻓﻴﺖ💋❤�?
*Mallakin Hafsat Bature Moh'd*
~BossBature~
•·•·•·•·•·•·•·•·•·••·•·•·•·•·•·•·••·•·•·•·•·•·•·�? Fitowa tayi tana faman yarfar da ruwan alwalar dake hannunta,hijab da sallaya ta ɗauka a wardrobe, ta shimfiɗasu tare da kabbara sallah,bayan ta kammala tabar darduman anan saboda in an kira isha'e, hijab ɗin ta cire tare da ajiye shi saman gadon sai ta ɗauki Mayafinta, ta yafa shi akanta,
Fitowa tayi kai tsaye ta wuce dining, a lokacin junaid ma yana a wurin tare da Haroon sai kanal Yusif duk suna zaune, yayin da Azmee ke faman ɗawainiyar Zuba masu abinci,
Ƙarasawa tayi tare da cewa "Sannu da aiki Aunty Azmee,"
Juyowa azmee tayi tare da kallonta tace"Yawwa mutuniyar sarkin kuka, Lamarinki naban mamaki kamar me iska,"
Sunnar da kai Sehrish tayi tana ɗan Murmushi kafin daga bisani ta gaishe da Kanal yusif da fara'arsa yace "Our Princess,duk yau ban saki a idona ba, Yakamata ace kina sakewa da ƴan uwanki sosai,"
Murmushi kawai Sehrish tayi tare da zama kusa da junaid suna facing ɗin kanal yusif da haroon ta hannun dama,
Zuba mata abinci azmee ta soma yi a plate, junaid dake a gefenta yace"Da ace baki fito ba ko, da bazanci komai ba Allah,"
Kafin sehrish tace wani abu haroon yayi saurin cewa "Saboda ciki ɗaya kuka fito ko? murmushi junaid yayi tare da cewa "Yaya Haroon yadda na ɗauƙi Sehrish ta wuce haka a wurina," ta6e baki Haroon yayi yana kallonta, Harara Sehrish taɗan wurga masa tare da murguɗa masa baki, jinjina kansa yayi tare da cewa "An fa samu freedom of sitting the same table da Ƴa'ƴan masu gida dole ayi iya shege,
Jin wannan maganar ta Haroon ta sanya junaid ɗaure fuska lokaci guda yace "Yaya haroon me kake nufi da hakan?
Haroon yace "Abunda ranka yabaka"
Dakatawa kanal yusif yayi daga cin abincin da yakeyi ya ɗan bubbuga plate ɗin dake gabansa da cokalin hannunsa ya bada sauti sannan ya aza idonsa akan na Haroon, Ganin irin kallon da kanal yusif ya jefa masa ne yasa shi, yin tsit ya shiga taitayinsa,
Mayar da idonsa yayi kan Sehrish yace"Sister Yaushe ne zaki fara zuwa school ɗin? yayi hakan ne donya mantar da ita maganar haroon, ganin yarda tayi sanyi lokaci guda,
daƙyar ta ƙaƙaro murmushi tare da cewa "Gobe ne insha Allah,"
Kanal yusif yace "Masha Allah,A matsayina na yayan ki, akwai wani jan hankali da nakeso nayi maki, kin ga gobe zaki fara zuwa, kuma zaki fara haɗuwa da sababbin ƙawaye iri-iri,akwai good friends waɗanda zasu dunga ƙarfafa maki guiwa akan karatu ta hanyar baki shawarwari masu kyau,bayan su kuma akwai bad friends gur6atattu waɗanda majority ɗinsu ba karatu ya kaisu ba,Asarar kuɗin iyayensu kawai suke yi, basa karatu ƴan abi yarima asha kiɗane,babban ma tashin hankalin yanzu majority na irin waɗannan ƙawayen ƴan Lesbian ne,fitsararru marasa kunya waɗanda suka gagari iyayensu da malamansu, burinsu kawai su 6ata tarbiyyar wasu, bana so ki kasance ɗaya daga cikin irin waɗannan ko kusa, dayawa wasu suna kuskuren yin abota da irin waɗannan bad friends ɗin, sai suce ae basu suke aikatawa ba,sun manta cewa zama da maɗaukin kanwa shi ke kawo farin kai,to koda gigin wasa bana so ko fira ta haɗaki da irin waɗan gur6atattun balle harku ƙulla Abota, Ina gargaɗin ki akan hakan ! And i want u to know that Ke yanzu kina ɗaya daga cikin Mutuncin gidan nan!! Kuma kinsan yarda sunan family ɗinmu ya karaɗe ko'ina, ba inda ba'asan Jinin SALAHUDDEEN HUSSEIN ba, don haka yazama dole ki kiyaye mutuncin family ɗinmu da kuma ƙimarsa, ina fata kina fahimtar abunda nake cewa"? Ya tambaya yana kallon sehrish wadda ta natsu tana sauraronsa cikin sauri tace "Ina fahimtar duk wani abu da kace yaya yusif, kuma insha Allah zan kiyaye faruwar hakan,kuma naji daɗi sosai harma baxan iya misaltawa ba,saboda na samu ɗan uwa nagari wanda yake mun nasiha akan na tsira da mutunci,babu wanda ya tunasar dani akan hakan sai kai, kuma insha Allah bazan ta6a baku kunya ba, zan kasance ɗaya daga cikin abun Alfaharin gidan nan,"
taƙarasa maganar yayin da idonta suka ciko da kwalla, gaba ɗaya Azmee da Junaid sun kasa kunne suna sauraron maganar tasu, dukansu babu wanda baiji daɗin maganar Kanal yusif ba, Illa mutun ɗaya Wato Haroon wanda ke ta faman tur6une fuska yana faman hura hanci aransa yana cewa "Insha Allah ni kuma bazan taba barin ki ki xama abun alfaharin gidan nan ba, balle har ki samu matsayi acikinsa, saina san yarda zanyi in tarwatsa komai har inyi sanadiyar korarki acikin gidan nan," ya faɗi yana kallon sehrish rai a6ace yana faman tura dambun nama abakinsa har yana shaƙewa,
Kanal yusif kuwa murmushi ya saki sannan yaci gaba da cewa "Allah ya yarda Sehrish,Nima inason ki zama Abun alfaharin mu gaba ɗaya," ya ƙarasa maganar tare da sanya hannu ya ɗauki glass cup dake ɗauke da Lemu mai sanyi yakai bakinsa yana kur6a,
ƙasa-ƙasa da murya junaid yayi tare da cewa "sehrish nima fa naso nayi maki nasiha akan zuwanki makaranta, amma kash sai gashi Yaya yousouf ya riga ni, amma duk da haka ban makara ba, don Allah sehrish karki canzamun koda kin fara zuwa school don nasan zaki ƙara wayewa sosai..........'
Murmushi sehrish ta saki jin abunda junaid yace, kafin tace "Insha Allah junaid hakan baxata ta6a faruwa ba,mu aminnan juna ne zamu kasance atare ako wane hali na rayuwa, kaine abokin shawara na,"
ajiyar zuciya junaid ya saki aransa yana ƙara samun kwanciyar hankali jin bayanan da sehrish tayi masa,
wayar haroon ce dake acikin aljihunsa ta soma ringing taken waƙar nan da ake cewa "ɗan duniya hayaƙin taba," jin ringing ɗin wayar yasa kanal yusif girgiza kai tare da cewa "Allah ya shirya ka,"
Haroon yace "Ameen don son Annabi," sannan yayi saurin tashi daga dining ɗin yakama hanyar fita daga falon yana zaro wayar daga aljihun wandonsa, ɗaga kiran yayi tare da karawa a kunnansa yana cewa "Shegen bisa ashe har ka isa hotel ɗin, ae ko gani nan zuwa Yanzun nan Allah yasa ka taho mana da harkar nan..........' ya yi maganar da dariya a fuskarsa kafin yasa kai ya fuce,
Bayan sun kammala dinner ɗin junaid suka wuce masallaci tare da kanal yousouf jin ana kiran isha'e,.
Itama Sehrish bayan ta kammala dinner ɗin tare da azmee suka kwashe kayan da sukayi amfani dasu izuwa kitchen, Sehrish ce ta wawwanke su tare da jerasu a ma'ajiyarsu,
Bayan ta fito suka ci karo da azmee tace " Inaso naje na kwanta,pls kada ki bari bacci ya kwashe ki, idan Twins sun dawo ki tabbatar kin kai masu dinner ɗinsu, Shima Abbansu pls ki kaimasa nasan ƙila sai wurin 12 zasu shigo,.
Sehrish tace "To aunty azmee insha Allah baxanyi bacci ba, zan kai masu in sun dawo,"
daga nan azmee ta wuce ɗakinta, itama sehrish bedroom ɗinta tashiga, sai da tafara shiga toilet ta kuskure bakinta, dama da alwalarta,
Fitowa tayi ta ɗauki hijab ɗinta da ta ajiye saman gadonta, ta kabbara sallah
_________________________________________________
Tuni General ishaq ya iso gidan ya cika tab da mutane tare da jami'an sojoji da suka rakosa, su Aunty babba sai faman rawar kai akeyi miji ya iso gari, a lokacin hafsat har ta shirya kanta itama tsaf ta kimtsa cikin haɗaɗɗen cord lace Ash colour mai adon duwatsu,rigar mai dogon hannu sai skirt ba ƙaramin kyau kayan su kayi mata ba, gashi dama takware wurin iya kashe kallabi, tare da Mommyn nata da wasu daga cikin abokanan aunty babba da suka zo dana hafsat suke taimakawa wurin tarbar baƙi da abunsha dana ci,
"Jahad ya Omar shiru kodai ya manta damu ne"? Hussana ta faɗi fuska tamkar zatayi kuka tana kallon jahad suna zaune dab da juna daga gefen gadon hafsat,
"Hussana bana tunanin hakan, Ya Omar yana son mu sosai ni ina da tabbacin yana sane damu,kuma zaizo ne insha Allah," acewar jahad
Hussana tace "Ni inajin tsoron a rabamu da ya Omar, wlh banso banso....'
Kamar daga sama suka ji Muryar Aunty babba tace "Saboda ƙanin ubanki ne ko? ta faɗi ayayin da take shigowa, arazane suka miƙe tsaye su duka suna kallonta, su biyu suka shigo cikin ɗakin ita da wata hajiya, amma ita ta tsaya daga baya
Kusa dasu taje sannan tasoma magana "Ko da gigin wasa bana so wata daga cikin ta leƙo da kanta daga cikin ɗakin nan ! Saboda Mijina ya dawo kuma banaso ya gan ku, ina fata kun gane?
Cikin sauri suka haɗa baki wurin cewa "Insha Allah aunty bazamu fito ba,"
ta6e baki tayi sannan ta juya bayanta ta kalli matar da suka shigo tare tace "Hajjaju gafa yaran nan da nake faɗa baki, Omar yakawo min cikin gidana,"
ƙarasa shigo wa ciki matar tayi jikinta na sanye da shadda gezna green colour tasha uban aiki a wuyan rigar, tayi ɗaurin ɗan kwalin ture kaga tsiya sannan ta yarfa gyalenta a kafaɗarta,
Alokacin da matar ta ƙaraso Jahad taganta nan take gabanta yayi wani irin bugu zaro ido tayi tana kallonta saboda son tuna inda tasan fuskarta,
Hajjaju kuwa tana ganin su hussana da jahad farat ɗaya ta gane su, a ɗan razane ta dafe ƙirji tare da cewa "Kaiii !!!" taja maganar da ƙarfin tana kallonsu cikin mamaki da al'ajabin wannan Ikon Allahn,
tuni aunty babba tagama ruɗewa ganin yadda hajjaju ta razana da ganinsu, da kuma yarda jahad ta firgita itama wannan alama ce dake nuni da sun san juna kenan ko yaya,
Cike da mamaki Aunty babba tace "Wai meke faruwa ne hajiya rabi? kinsan su ne?
Cikin sauri hajjaju tace "A'a bansan su ba, Kamar dae nata6a ganin mai kama dasu ne,"
tayi maganar tare da ruƙe hannun Aunty babba taja ta, suka fuce daga ɗakin,
Kallon jahad hussana tayi tare da cewa "Jahad wacece wannan matar? Naga kin razana da ganinta,"
"Nima so nake na tuna inda nasanta," Jahad ta faɗi tana faman cizon akaifar hannunta da takai abakinta,
Hajjaju kuwa da taja Aunty babba suka fuce can suka nufa wurin kitchen suka tsaya, ga mutane sai faman shige da fuce suke,.
"Dan Allah ki faɗamun gaskiya hajjaju raina na bani cewa kinsan yaran can ko? Aunty babba ta tambaya tana kallonta cike da son jin ƙarin bayani daga wurinta,
Jinjina kai Hajjaju tayi tare da cewa "Yau naga ikon Allah, Lallai ne duk zakaran da Allah ya nufa da cara,to fa sai yayi ta, haƙiƙa nayi matuƙar mamakin yarda akai har Allah ya haɗa Omar da waɗannan yaran , kai kaga wani ikon Allah nan ! mai matuƙar ban mamaki da Al'ajabi?
Hajjaju tayi maganar cikin nuna mamakinta,
Aunty babba kuwa cewa take yi "Hajjaju