Showing 84001 words to 87000 words out of 432432 words
Chapter 29 - Abban Sojoji Book 2 Hausa Novel Complete
yake kwance yana bacci, cike da tausayi yake kallon shi yadda yake jan numfashi da ƙarfi da ƙarfi,
ƙarasawa yayi tare da hayewa saman gadon yayi zaman cin tuwo tare da zabga uban tagumi yana kallon shi hawaye na zuba a fuskarshi,
Jin shessheƙar kukan junaid a kunnan shi yasa shi farkawa daga baccin da yake yi, ya buɗe idon shi a hankali yana kallon shi, yarda ya tallabe fuskarshi hannu bibbiyu ya tasa shi gaba yana sharar kwalla,a hankali fawan ya furta "junaid "
Kallon shi kawai junaid yake yana cigaba da matsar kwallo,hankalinsa ba ƙaramin tashi yayi ba ganin yarda jikin fawan yayi ruɗu ruɗu da bulali wurin yayi jawur ya faffashe duk da anyi masa dressing na wurin an shafa masa magunguna,ga kuma ɗinkin da akayi masa a chest ɗinshi,
dakyar ya daddage ya tashi daga zaune yana fuskantar junaid ɗin daya tasa shi gaba,
"Junaid," fawan ya sake ambaton sunan shi a karo na biyu ganin yarda ya zabga tagumi yana kallon shi hawaye na zubowa gefe da gefen fuskarshi, zama su kayi suna fuskantar juna, kallon shi kawai junaid keyi batare da yace uffan ba,
daƙyar fawan ya ƙaƙaro murmushi yana kallon shi, hannun shi yakai tare da shafa gefen fuskar junaid yace "bari nabaka wani labari ƙanina,"
junaid ya zuba mashi ido yana sauraron shi,
fawan yace "lokacin da waɗannan miyagun suka ɗauke ni ko, suka shiga dani wani ƙogon dutse mai rikitarwa, suka ban za6i biyu, su kashe ni ko su azabtar dani wanne nakeso, kasan me nace masu? ya fadi yana kallon shi, girgiza kai junaid yayi alamar a'a,
Fawan yaci gaba da cewa "a lokacin kai kawai ka faɗo mun araina, aranar da zamu tafi kai ta zabga kuka kana cewa babu inda zamuje ƙafarka ƙafarmu dakyar abba ya shawo kanka, ka tuna abunda ka faɗamun lokacin?
shiru junaid yayi yana tuna lokacin daya cakumi rigar fawan yana ce "ya fawan kayimun alƙawarin cewa zaka dawo araye inaso na sake ganin ka,' a lokacin fawan yace mashi "junaid ae tafiya ba mutuwa bace, insha Allah zan dawo araye in Allah ya yarda," murmushi junaid yayi tuna wannan
shima fawan murmushin yayi sannan yaci gaba da cewa "saina ce masu ni bana tsoran mutuwa, ban isa na hana kaina mutuwa ba in lokacina yayi, kamar yarda kuma baku isa ku hana kan ku mutuwa ba idan tazo maku, sai ɗaya daga cikin su yace mun "Ka za6i ka mutu kenan? mu kashe ka kawai? Saina girgiza kai nace "a'a ku azabtar dani kuyi mun duk irin hukuncin da zakuyi mun amma kubar ni da raina saboda akwai ƙaramin ƙanina da nayi ma alƙawarin cewa zandawo da raina, inaso na cika mashi wannan alƙawarin nasa na gani na araye, bana so na karya mashi zuciya nafiso ko mutuwarce ma to na mutu agabanshi yadai ganni da raina...............' dakatawa fawan yayi da maganar saboda hawayen da suka zuzzubo mashi, junaid kuwa tuni ya fashe da wani irin matsanancin kuka mai cin rai,
haɗe kansu su kayi wuri ɗaya suna faman shessheƙar kuka atare,
dakyar fawan yaci gaba da cewa "Shine suka bankamun kayan maye sannan suka ɗaure ni tamkar dabba, su ka dunga zuba mun bulali da kaca a jikina har saida suka ga jini na zuzzuba ajikina amma hakan bai ishe su ba, ba don su babban yayan mu sun zo ba to da tabbas kashe ni sukayi niyyar yi a lokacin, Amma alhamdlh naji daɗi sosai da Allah yacika mun burina na ganin na rayu don na cika maka alƙawarinka......
.. murmushi junaid ya saki tuni ya ji sanyi ya ratsa mashi zuciyarsa,
janye kansa yayi daga na fawan sannan yace "kana jin yunwa in kawo maka abinci"?
girgiza kai fawan yayi tare da cewa "junaid a ƙoshe nake,ɗazu azmee ta haɗamun kakkauran tea tare da fruits na sha,naji daɗin su sosai,"
"Bari nabarka ka huta sosai, na katse maka baccinka, amma ka sani zan dawo don atare zamu kwana," yayi maganar yana ƙara jaddada masa ayayin da yake sauka daga saman gadon,
Murmushi kawai fawan ke bin shi dashi harya fice daga ɗakin,komawa yayi a hankali ya kwantar da bayansa saman filonsa tare da lumshe idon shi,
Cikin sauri junaid ya fito tare da tunkarar hanyar fita saboda tunawa da sehrish wadda ke a school, lokacin tashin su yayi gashi time na salla na kokarin wuce shi, yana dab da fita daga ƙopar Amani ta kwada masa kira, dakatawa yayi tare da juyawa yana kallon ta da murmushi a fuskarsa, cikin sauri ta ƙaraso gab dashi tana cewa "ina zaka je ne? Junaid yace "inaso zance masallaci ne nayi sallah, daganan zan wuce na dauko sehrish daga school,"
ɗan jinjina kai tayi kafin tace "wannan yarinyar da muka gani ɗazu itace sehrish"? Ta tambaya tana kallon shi duk da tasan akanta yake magana
"Yeah itace," ya bata amsa atakaice tare da fucewa yana cewa "Sauri nake aunty amani time ɗin sallah zai wuce ni,"
Juyawa amani tayi tana jinjina kai, a ƙagare take da junaid ya dauko yarinyar daga school saboda tana son ta sake ganinta har ma ta yi magana da ita,
*wannan kenan*😍👍
Ina kuke mata hamshakai wayanda suka amsa sunan su wajen mazajen su ina mata masu son qamshi shin ko kunsan tsafta bata tafiya seda qamshi ina masu son turare mai riqon gida tareda qamshin shi mai sanyaya zukata mardie collection tazo muku da dadadan turarukanta masu lasting riqon gida harma da jiki ku tuntube mu da nmb kamar haka 08136666994
�?
�?
�?
*Boss Bature*
Who's the AVENGER❗‼️⁉️
**************************
Har suka koma Class jikin sehrish a sanyaye ita kuma amrish fuskarta ta nuna alamun damuwa sosai game da abun da zeenat tace mata, gaba ɗayansu dae babu daɗi har suka taso daga school ɗin,tsayawa su kayi daga wajen school din sai ga drivern Amrish ya ƙaraso, juyawa tayi ta kalli sehrish tace"Ni zan wuce,sai mun haɗu gobe in Allah yakaimu,"
Jinjina kai sehrish tayi tare da cewa"Allah yakaimu lpy,"
"Ameen" ta amsa mata sannan ta wuce cikin motar,
ta jima a tsaye tana jiran ƙarasowar motar junaid dalilin dayasa bata hau bus ba kenan saboda tasan dole yazo ɗaukarta,masu motoci saiyi mata tayi suke don tazo su rage mata hanya amma taƙi yarda tahau motar kowa saboda tasan cewa ba kowa bane zai ɗauke ta don Allah ba,
tana cikin wannan tsayuwar ta hango motar junaid ya shawo kwana,murmushi ta soma saki tamkar tayi tsalle don murna tunkan ya ƙaraso ta tunkari motar da sauri,
yana tsayar da motar ta sanya hannu ta buɗe motar sannan tashiga ciki tare da rufe motar,
juyawa tayi ta kalle shi tare da cewa "ka manta dani ko"? Ina ta faman jiranka,"
ɗan murmushi yayi yace "am sorry ba da son raina ba reesh, kina araina ynx ma daga mosque na wuto nan,' ya ƙarasa maganar yana kallonta, bin fuskarshi tayi da kallo alamun damuwa ta gani sosai atattare dashi,tuni itama taji zuciyarta babu daɗi, cikin sanyin murya tace "junaid kayi kuka yau ko? kuma kana cikin damuwa"?
jinjina mata kai yayi alamar eh,
ɗan 6ata fuska tayi tare da cewa "dan Allah junaid kadaina sa damuwa aranka wlh bana so, natsani naga mutun mai cike da farin ciki irinka a Yanayi na damuwa,'
A kasalance yace "don't worry ur self,zan daina ne reesh da zarar nasamu abunda nakeso, ki sani acikin addu'arki da kuma sauran ƴan uwana,'
"Insha Allah junaid bana mantawa da kowannan ku acikin addu'a ta," ta fadi tana jaddada masa maganarta,
"Yanzu kayi mun dariya in gani magana kona samu kwanciyar hankali,"
tunkan takarasa maganarta, ya wage bakinsa yana dariya,bin fararen haƙoransa tayi da kallo a jere tsaf suke tamkar mai tallar maclean saboda kyal ɗinsu, ga 2 dimples dinsa da suka lotsa sosai,
Yatsanta takai acikin dimple ɗinsa ta zura shi saboda burgetan da yayi, sun jima suna shiririta acikin motar kafin ya tayar da motar suka miƙi hanya, cike da nishaɗi suke sauraron waƙar da junaid ya kunna masu ta lilin baba,natsuwa yayi a hankali yake driving yana sauraron muryar rishi dinsa dake bin waƙar
"Kaine zuciya take ta yabo🎶kaine nawa in da rai da rabo, amanar zuciya ka damkeee, da kaine zanyi Wuff, zanyi wuff zanyi wuff🎶🎶
Fashewa da dariya junaid yayi saboda daɗin waƙar da yaji, sai yaji tamkar dashi take, musamman da tadinga nuna shi da hannu tana cewa(dakaine zanyi wuff)
Tana kai baitin ƙarshe shima ya ɗauka,
"Ke ce zuciya take ta yabo kece tawa inda rai da rabo,amanar zuciya ki damkeee, da kece zanyi wuffff !🎶
Zuba mashi ido sehrish tayi tana kallon shi, yana driving yana raira wakar kuma yana ɗan waiwayon ta,
gaba ɗaya sun shagala basuyi aune ba, suka ji wata mota a bayanzu ta bugi motarsu da karfin gaske,ƙarar da sehrish ta saki ne yasa junaid sakin sitiyarin motar gaba ɗaya, aikuwa nan take motar ta karkace ta nufi wata tamkekiyar bishiya da gudun gaske,
Waro ido sehrish tayi tare da cewa "Junaiiiid !! Innalallahi wa'inna ilaigirraji'un,
Ƙanƙame shi tayi ajikinta saboda gaba ɗaya yagama rikice wa, gaba ɗaya sun ƙanƙame juna, maimakon Sehrish ta taimaka mashi ya rike sitiyarin motar yayi control dinta, Amma saita janyoshi jikinta ta kankame suka bar motar Tana control din kanta,
Cikin ikon Allah motar ta kashe kanta adai dai bakin bishiyar ƙiris ya rage su gabje ta da ba ƙaramin buguwa zasu yi ba,
Ajiyar zuciya suka shiga sauke wa tare da dagowa atare suna kallon bishiyar, Allah ya takaita wahala da motar ta kashe,
Sai faman zazzare Ido suke Yi su duka biyun, sun ji kamshin mutuwa, juyawa Sehrish yayi tare dasa hannu ta zuge glass din motar Don taga wanene ya bugi motarsu,
wata bakar motace Mai black tunted kirar range Rover, Kamar jiranta suke ta leƙo,suma na cikin motar suka zuge nasu glass din motar,
Gabanta ne yayi mugun bugawa daraaam !! Ganin mutanen dake cikin motar, giggan Yan iska ba Imani a fuskarsu bakeke ne wulik, kana ganinsu kasancewa turo su akayi, da gangan suka bugi motar Junaid din,"
duk Tasha jinin jikinta, ɗaya daga cikinsu ne ya ɗago mata hannu tare da cewa"hi We're sorry guys mun bugi motarku batare da mun sani ba,kuyi mana afwa,amma yakamata kija masa kunne ya dinga kulawa wurin yin driving yana yin tukin ganganci, hakan zai iya halakar daku wata rana,"
Suna faɗin hakan suka ja motar tasu da gudun gaske suka bar wurin,
Ajiyar zuciya ta sauke tare da juyawa ta kalli junaid wanda yayi wuri wuri da ido, duk a tsorace yake da abunda ya faru dasu,
Murya asanyaye tace "junaid kayi sauri mubar wurin nan,"
daker ya iya tashin motar sannan yaja ta da baya baya suka baro jikin bishiyar, ya hau kan titi dasu sannan ya miƙi hanyar gidan,.
gaba ɗaya sehrish jikinta ya gama yin sanyi saboda ta hasko wani abu game da bugun motar junaid da sukayi,maganar da sukayi mata tamkar gargaɗi ne sukayi mata akan wani abu da zai faru dasu,tabbas tashiga ruɗani,
A hankai suka shiga babban entry din gidan, yayi parking motar sannan suka fito atare kowa na faman sauke ajiyar zuciya,atare suka jera suka nufi cikin gidan
ɗan kallon sehrish yayi ganin tamkar ranta ya 6aci don haka yace "am sorry rishi laifina ne,nayi ganganci dana kunna mana waka acikin mota har muka shagala sosai,"
fuskarta a yamutse tace "its not ur fault junaid, ba ka yi tuƙin ganganci ba,da gangan suka bugi motar mu,karka sama kanka damuwa ni bana ganin laifinka, Allah zai saka mana ma,"
tuni yaji sanyi ya ratsa ransa, bayan sun shiga babban falon ta wuce bedroom ɗinta, shima kuma ya wuce nasa ɗakin,
Shaf shaf ta tu6e uniform ɗinta, asaman gadon tabarsu tare da school bag din duka, toilet ta fada tayi wanka tare da dauro alwala, tana fito wa ta bude wardrobe dinta tare da ciro wata gown mara nauyi ta zura, sannan ta shimfiɗa carpet ta zura hijab tare da kabbara sallah, anatse tayi sallarta, bayan ta kammala bata ko nemi abinci ba saboda taci tayi hani'an a school, gado kawai ta haye tare da baje wa tana bacci,
Shima junaid daya wuce nashi dakin nashi ya faɗa toilet ya yi wanka tare da canza kayan jikin shi izuwa riga da wando,
Yana kokarin fitowa daga ɗakin sai ga su twins sun faɗo ciki atare sun ɗau wankan jeans da t shirt,
Yana ganin su ya saki fara'a tunkan su fara magana yace "maganar kiran mommy ce ko"?
dariya su kayi atare, ayaan yace "ashe dae ka gane,Allah yasa bamu takura maka ba,"
girgiza kansa yayi tare da cewa"a'a yanzun nan zan kirata insha Allah,"
Jahan yace "yawwa masoyi junaid mai son farin cikin ƴan uwan shi,pls idan ka kirataa wayar,kayi mata biyayya kaji? kada kace zaka ƙi mata magana, ita mahaifiyarmu ce,idan bata son ɗaya daga cikin mu ae bazama ta ɗauki cikinmu ba balle har ta ruƙe sa na tsawon wata rana, kuma tayi naƙudar haihuwarsa,nasan kai mai ilmi ne junaid kasan hukuncin wanda ya sa6a ma iyayensa dan Allah ka manta da komai," yarda jahan ke yi masa nasiha cikin daɗin rai yasa shi jin sanyi aransa harma yaji cewa ya ƙosa ya kirata a wayar,
"Shikenan ya jahan da ya ayaan,zan kirata yanzun nan amma ba a gabanku zanyi wayar ba,idan nagama dae zan sanar daku duk yarda mukayi da ita,"
Cike da farin ciki suka ce "yawwa ɗan ƙanin mu, yanzun nan kuwa zamu fita daga ɗakin,sai mun ji ka," suna fadin hakan suka juya tare da fucewa daga ɗakin hada rufo masa ƙopar da kyau,
ɗan murmushi junaid yayi sannan ya koma gefen gadonsa ya zauna tare da kai hannu ya ɗauki wayarsa dake asaman side drawer,
Zuba ma screen ɗin ido yayi yana tunanin ta yarda zai fara kiran mommyn tasu, for the first time zaiji muryarta,a lokacin baya kusan kullum saita kirashi awaya bai ɗauka don ko saving na numbarta baiyi ba,saboda haushin ta da yake ji,
A hankali yashiga danna wayar, kai tsaye cikin messages yashiga saboda akwai last messages da ta tura mashi, buɗe sakon yayi ya ƙara karanta shi "Thanks 4 ignoring me, i won't call u again bye,"
tanan ya ɗauki number tare da danna mata kira, ta shiga ringing,
Almost 3 times tana ringing ba'a ɗauka ba,ana huɗunne yana ƙara kira tayi picking,shiru yayi baice komai ba,har sai da tashiga tambayar wanene jin anyi mata shiru, yanayin muryarta akasalance saboda bacci,
Cikin harshen spanish take tambayar wai wanene,
Sai a lokacin junaid ya ambaci sunan "Mommy," shiru tayi tana nazari don ta gano muryar wacece wannan acikin ƴa'ƴanta,bakowa bane ya faɗo mata aranta ba face Romeo ɗinta duk da basa waya amma abbansu na turo mata voice ɗinshi da yake mata recording aduk lokacin da suke fira dashi ko kuma lokacin da yake tsaka da shagwa6a,
tuna wannan yasa Alexandra cewa "Romeo ɗina ne"? Ta tambaye shi donta tabbar cewa shiɗinne da take hasashe,
Ashagwa6e yace "junaid ɗin abbana ne,"
Jin hakan yasa alexandra tashi daga kwancen da take asaman shimfiɗeɗen gadonta, cikin sauri takai hannu ta kunna bedside lamp, bedroom ɗin nata ya ɗanyi haske tamkar zata iya gashinin zahiran agabanta, cikin tsananin farin ciki tace "allah yasa ba mafarki nake ba,romeo da kan shi yau ya kira ni a waya, harya kirani da sunan mommyn shi, cikin tsantsar farin ciki take maganar,
Duk junaid na sauraronta sai da takai aya sannan yace. "Mom ki ƙaddara cewa mafarkine, saboda bashi da banbanci da mafarkin cos i called u by force ba don son raina ba, ya faɗi with angry face tamkar yana agabanta,
murmushin takaici tayi kafin tace"na sani dama saka akai ka kira ni,koma manene laifina ne nasan fushi kake yi dani,baka sona romeo ni kuma nadamu dakai sosai.....' ta faɗi cikin muryar kuka,
"Mom ba ki sona,da ace kina sona da baki tafi kinbarni ba a lokacin da bansan komai ba soyayyarki kawai nake buƙata da kulawarki, amma duk wannan bai dame ki ba,kin tafi kinbar ɗan jinjiri ya yi rai ko kar yayi duk bai dame ki ba,kashe ni kika so kiyi............'
Fashe mata da kuka yayi mai cin rai, nan da nan hankalinta ya tashi duk yadda taso ta lallashe shi ya daina kukan amma yaƙiya,janye wayar tayi daga kunnanta tare da zuba ma screen ɗin wayar ido tana sauraron kukan shi, har cikin ranta ba ƙaramin ɗaci ta ji ba, tama rasa ta yarda zata fahimtar dashi, Sai da junaid yayi mai isar shi sannan ya tsagaita yana faman sauke ajiyar zuciya,
Jin haka yasa tace "pls can i turn it to video call,cos i wanna see u face to face,"
Rai a6ace junaid yace "ban amince ba mommy,if u really want to see my face then come to nigeria,"
Murmushi taɗanyi sannan ta kuma cewa "ka yafe mun junaid ɗin abbansa,ba don bana sonka ba na tafi nabarka, nafi kowa sonka junaid saboda ni na haifeka,duk da nasan cewa a wurinka bancancanta na amsa sunan mahaifiya ba, amma inaso kaa sani nikaina ba'a son raina nabar ƴa'ƴana ba, bakowa bane ya son da wannan ba saboda ba kowane zai yarda dani ba, amma an takuramun an ƙuntatamun ko bacci bana iyayi a ƙarshe ma naji ƙasar gaba ɗaya tafita raina na dinga jin tamkar ƙona fatar jikina akeyi wannan shine dalilin dayasa nabar ƙasar, kai kuma abunda yasa ban tafi dakai ba shine, soyayyar da mahaifinka ke yi maka,idan na tafi dakai ya zai ji a zuciyar shi? shi kan shi bai fahimci hakan ba kowa tunaninsa na tafi don son raina ne amma ba haka bane junaid, akwai wani 6oyayyen lamari dake faruwa acikin gidan nan,nayi ƙoƙarin na fahimtar da abbanku saboda ni ina da masaniya akan wani abu, amma abbanku sai ya nuna mun cewa kawai don na tsani baƙar fata ne yasa nake zargin wasu,bayan ba haka bane ni duk wanda na tsana hakanan batare da wani dalili ba to yana da wata muguwar manufa ne... '
Shiru junaid yayi yana sauraronta, bai cika ɗaukar komai serious ba arayuwarshi amma maganar mommynsa taɗan ta6a shi kaɗan, bazai ce