Showing 174001 words to 177000 words out of 432432 words
Chapter 59 - Abban Sojoji Book 2 Hausa Novel Complete
biya kuɗin aikin hosana da kuma na maganin da za'a siyamun,babu yarda muka iya alokacin wannan kaɗae ce mafita,muna ji muna gani ƴar uwarmu ta tafi neman kuɗi saboda ta nema mana lafiyarmu,ya Omar Sehrish tayi duk wata gwagwarmaya akanmu,damu da ita duk kanmu ɗaya,amma ita tamkar uwa take a wurinmu,tamkar yaya take a wurinmu,bamu da tamkarta aduniyar nan,rishi har ranta zata iya sadaukarwa saboda mu,nayi kukan rashinta sosai,nayi baƙin cikin yin nesa da ita........tun muna yara muke tsananin son junan mu,rayuwarmu a wulaƙance mukayi ta sakamakon mugun uba da muke dashi wanda bai ta6a nuna mana soyayya ba........'fashewa tayi da matsanancin kuka,
Gaba daya jahad ta gama kashe masu jikinsu yayi sanyi,
dakyar ta tsagaita da yin kukan taci gaba da magana"bayan sehrish ta tafi aiki,cikin sa'a ta samu kuɗin aikin hosana ta biya,lokacin da aka sallame mu daga asibiti,muka koma gidan tsohuwar da take kula damu,anan muke rayuwarmu,kullum muna kiranta awaya mu gaisa da ita,ita ma kuma tana kiran mu awaya taji ya lafiyar mu take,akwai wani lokaci da maganin hosana ya ƙare,ciwonta ya soma dawowa ta dinga hauka tana ƴan buge buge,hankali na ya tashi,gashi bamu da kuɗin da za'a siya mata wasu magungunan,shine na yanke shawarar sanar ma rishi halin da ake ciki,don ta taimaka mana dana magani,na tura mata saƙo ta waya,sai gashi ta turo mun da amsar cewa mu tura mata da acct number,cike da zumuɗi na zura hijabi na shiga gidan makwabtanmu wurin ɗiyar matar,don ta rubutamin acct number ɗinta tun da mu bamu da ita,ashe lokacin da na fita daga gidan,hosana tafarka daga bacci tana son shiga toilet,shine ta ɗauki wayar dana bari saman jakar kayanmu ta shiga toilet da ita,kafin nadawo cikin gidan hosana ta jefar da wayar cikin masan,wannan shine silar da muka rasa sehrish gaba ɗaya,saboda ba mu da wata hanyar da zamu iya magana da ita,sae ta wannan wayar.......'ƙarasa maganar tayi tana faman share kwallar da ke kwaranyowa daga idanunta,
sunnar dakai omar ya ɗanyi,yayin da yake jin zuciyarshi wani kala ba daɗi,haka shima major duk tausayin yaran ya kamashi,musamman ƴar uwarnan tasu sehrish,yarinyar tayi bajinta sosai,
ɗagowa omar yayi tare da kallonta yace"Jahad,inaso ki faɗamu taya akai kuka shiga hannun ƴan sanda?wane laifi kuka aikata ne"?
Cikin shessheƙar kuka tace"bamu aikata laifin komai ba ya Omar,sharri ne akayi mana,abunda ya faru bayan hosana ta jefar da wayar acikin rami,sae ga tsohuwar nan da take rainon mu ta shigo cikin gidan,anan ta same mu ni da hosana muna faɗa akan wayar da ta jefar mana,sai take tambayar meya faru ne muke faɗa,shine na sanar da ita abunda ya faru,hankalinta ya tashi sosai akan wayarta da mukayi mata asararta,rai a6ace ta shige cikin ɗaki ta rufe ƙopa,duk bamuji daɗi ba lokacin saboda bata ta6a nuna mana 6acin ranta ba irin na ranar,atsaye muka kwana muna bata haƙuri akan ta buɗe mana ƙopa mu shiga ciki,saboda a gidan ɗaki biyu ne,amma ɗaya ya rushe saboda ruwan saman da aka ta6ayi mana mai ƙarfi,ya Omar aranar waje muka kwana har ciwon hosana ya tashi,kafin washe gari kuma taji sauƙi,koda muka farka munyi tsammanin zata buɗe mana ƙopar amma abun mamaki sae muka ga ƙopar adatse,tun muna sa ran zata buɗe mana kopar har muka fidda rae,a ƙarshe agidan makwabtan mu muka shiga yin sallar asuba,anan ma muka ci abinci,da mamansu yarinyar ta tambayemu meya faru,muka sanar da ita duk abunda ya faru,shine yarinyar gidan ta rakomu har gidan mu,muka haɗu tare da ita muna babbuga ƙopar,a ƙarshe hosana ce tayi ƙoƙarin 6alle ƙopar......anan muka samu gawarta,ashe tun daren jiyan ta mutu.......mutane kuma suka daura mana laifin kisan nata,saboda sun gano cewa guba aka bata taci,wannan ne dalilin da yasa ƴan sanda suka kaimu police station,bayan an gama tattara hujjojin da za'a miƙa mu kotu dasu,sae kuma ciwon hosana ya tashi acikin cell,wannan ne farkon fitarmu daga cikin cell aka kai hosana asibiti,Ya omar kaji yarda akai muka kasance a hannun ƴan sanda..... "Ƙarasa maganar tayi yayin da hawaye ke ta faman sintiri a fuskarta,
"Ina mahaifiyarku take ne"?omar ne ya kuma tambayarta,
Jahad tace"bamu san inda take ba,bani da tabbacin cewa tana a raye kota mutu,abu ɗaya nasani koma a wane hali take yanzu indae tana araye to bata acikin hankalinta,"
Jinjina kai Omar yayi kafin yace"Insha Allah zan bincika komai a sannu zan gano duk wanda yayi sanadiyar shigarku cikin wannan halin,bazan ƙyaleshi ba,koda uban da ya haifeku ne,zan yanke mashi hukunci daidai da zunubin da ya aikata,'
major yace"wannan gaskiya ne,yalla6ai Allah ya taimaka kuma yayi jagora,nidae yanzu babban burina shine ƴan ukun nan,su kasance a ƙarƙashin kulawar family ɗinku,"
Omar yace"abun ya ɗaure mun kai major,kaji wani iko na Allah nan,gaba ɗaya yaran su ukun suna a ƙarƙashin kulawar family dinmu,duka Allah ya haɗasu awurinmu batare da saninsu ba,kuma batare da sanin mu ba,ita ɗayar ƙaddarar aiki ce ta kawota gidan mu,yayin da su kuma su hosana da jahad,ƙaddarar zaman asibiti ce ta haɗani dasu a lokacin da hosana ke hauka hannunta ruƙe da bindiga,Major abun akwai wata sarƙaƙiya acikinshi,tabbas akwai abunda Allah yake nufi da waɗannan yaran!akwai wani abu da Allah ke son bayyana mana shiyasa ya haɗasu duka awurin mu!"
Zuba mashi ido jahad tayi tana kallonshi ita kanta abun ya ɗaure mata kai,
Shi kanshi major ya shiga kokonton cewa Anya yaran basu da alaƙa dasu Marshal Omar?juyawa yayi ya dan kalli fuskar marshal sannan ya mayar da idonshi akan hosana,sae lokacin ya dinga ganin wata irin kamanceceniya atsakaninsu sosae,tabbas akwai wata alaƙa ta jini a tsakaninsu,shiru kawai yayi baice komai ba,
Kowa ya tafi duniyar tunani hafsat bature ma,ta ɗan ajiye typing tana tunanin wannan abun daya ɗaure mata kai tamau...,
"Ya Omar,"gaba dayansu sukayi firgit suna kallon Hosana dake kwance tafarka tana faman mutsistsike idanunta,jin muryar Omar yasa ta ambaci sunan shi,
Murmushi ya dan saki tare da ambaton sunanta "Hosana",
miƙewa tayi zaune tana ƙare masu kallo gaba ɗayansu,tashi Omar yayi ya koma gefenta ya zauna yana kallonta,
lokacin da ta tabbatar cewa shine saita fashe mashi da kuka tana cewa"Ya omar fushi nake dakai,meyasa ka tafi kabarmu kadaina zuwa wurin mu?laifin me mukayi maka da har kayi mana wannan horon"?
Lallashinta ya shiga yi yana cewa"Am really sorry hosana..pls stop crying and wipe ur tears,komai ya wuce yanzu muna tattaunawa ne game da ƴar uwarku Sehrish...... '
Tunda ya ambaci sunan sehrish hosana tayi tsit ta nemi kukan da takeyi ta rasa la66anta har rawa sukeyi wurin cewa"Anganta ne ya omar?"
Murmushi Omar ya saki tare da cewa"An ganta hosana!ƴar uwarku da ku ka jima kuna nema,ashe itace yarinyar dake yi mana aiki agidan......"bai ƙarasa maganar ba hosana ta fashe da kukan murna tana cewa"Ya omar tana ina?ina rishi ɗinmu take?inaso naganta!tana ina,wayyo Allah na....'
Yarfa hannunta tashiga yi saboda tsabar farin ciki bakinta yaƙi rufuwa hawaye na zuba fuskar kuma ɗauke da dariyar farin ciki,
Itama jahad farin cikin ne tsantsa afuskarta yau takasance babbar rana agaresu rana mafi girma arayuwarsu ranar da Allah yasa suka gano inda ƴar uwarsu sehrish take,dole suyi farin ciki,bama su kaɗai ba,hatta masu karanta labarin rayuwarsu da kuma marubuciyar data zauna ta tsara labarin ita da kanta tana taya su farinciki,Ya Allah ka ƙara danƙon ƙauna atsakaninmu da ƴan uwanmu masu son mu,Allah ka bamu ikon faranta ma juna da kuma taimakon junanmu,a gudu tare kuma atsira tare�?
Omar ya jima a wurinsu hosana kamar karya tafi ya barsu haka yaji,abunda yasa bai tafi dasu yau ba saboda Yarinyar gidan tasu da ba'a gani ba,yafi son sai sun ɗauko yarinyar sannan ya kaisu gidan nasu don suga ƴar uwarsu ido da ido,zai so yaga wannan farin cikin a fuskokinsu,
Bayan tafiyar su Marshal Omar,jahad da hosana duk sun bi sun ruɗe saboda tsabar murna ko abincin rana basu ci ba,sai faman sintiri sukeyi acikin babban falon nasu,aƙagare suke dasu ga sehrish,zuciyarsu sae faman azalzalarsu take akan son ganinta kamar suyi hauka.
💋BOSS BATURE💋
Ga wani tashin hankalin kuma,duk yadda sojojin nan suka so su kama sehrish abun yaci tura domin kuwa sehrish ta kubce masu,babu irin neman da basuyi mata ba,amma babu ita 6at ta 6ace kamar al'jana,abu kamar wasa har bayan sallar La'asar basu ganta ba,
Niko sehrish ina kika shiga ne!kai jama'a daga antaro nan sae kuma nan ya ruguje,
tunda Abbansu ya sanar mashi game da zuwan Aunty azeema,jiki na rawa junaid ya fito daga dakin Abbansu da gudun gaske ya nufi ɗakin da aka saukar da ita,faɗawa cikin ɗakin yayi ko sallama babu saboda tsabar ɗoki,a lokacin tana daga zaune saman gadonta tana daddana wayarta,sam bata lura dashi ba,bata ji shigowarshi ba,sae dae kwatsam taji faɗowarshi jikinta,gaba ɗaya ya ƙanƙameta sosai,yana yi mata kukan shagwa6a wai yayi missing ɗinta sosai,
Dariya sosai hajiya Azeema tashiga yi tana cewa"Oh ni junaid,tun ɗazu nake ta tambayar ina babynmu yake ina babyn mu yake,duk na ƙosa naganka naso ace ina shigowa cikin gidan nan kaine mutun na farko da zaka fara tarbata da wannan sumbatar taka,"
ta ƙarasa maganar tare da ɗago shi daga jikinta tana bin shi da kallo tace"Masha Allah,junaid kaine ka koma haka?ka ƙara girma sosai kyakkyawan yarona,nayi missing ɗinka sosai,"
murmushi junaid ya sakar mata tare da cewa"mommy azeema ina tsarabata?me kika kawo mun"?
Dariya tayi tana girgiza kai tace"Tsarabarka na nan junaid,wannan karan nazo maka da abun ban mamaki,inaso inga farin cikin da zakayi idan nabaka tsarabar nan,"
cike da zumudi junaid yace"tana ina,"
Harara ta ɗan watsa mashi tare da cewa"Shine damuwarka?ka manta baka bani kiss dina ba,"
matsawa junaid yayi tare da kai bakinshi gefen fuskarta ya manna mata kiss sannan ya ɗago yana kallonta yace"yanzu sai aban tsarabata ko"?
Dariya tayi tace"ɗaukomin trolley ɗin kayana,"tayi maganar tana yi mashi nuni da trolleyn da Kanal yousouf ya jingine mata ajikin wardrobe,
jiki na rawa junaid ya saukko daga saman gadon ya taka izuwa wurin wardrobe din ya ruƙo trolleyn tare da janyoshi har wurin gadon ya miƙa mata shi,sannan ya zauna daga gefe ya zuba ido yana jiran ganin tsabar da tayi mashi,
hannu tasa ta buɗe trolley din ta curo wani ɗan kit ƙarami sai faman ƙyalƙyali yake yi yadda kasan da gold akayi jikinshi,tunkan ta buɗe shi junaid ke ta faman haɗiye yawu yarda kasan yaga abunci,
Murmushi ta danyi tare da kallon fuskarshi tace"close ur eyes,"
Rufe ido junaid yayi kamar yarda ta umarta,
Murmushi ta kuma yi tare da buɗe akwatin tace"Now Open ur eyes,"
A hankali junaid ya buɗe idanunshi kai tsaye suka sauka akan danƙareran Zoben diamond ɗin da ta siya mashi tare da agogonshi,sae faman ƙyalli suke suna ɗaukar ido,diamond bana wasa ba,wanda aƙalla price ɗinsu yayi miliyan ɗari uku,
Waro ido waje junaid yayi yana bin su da kallo saboda tsabar farin ciki ya gaza rufe bakinshi,hannunshi na kerma ya kar6i akwatin yana ƙare masu kallo,
Cikin tsantsar farin ciki yace"aun...aunty..wannan duk nawa ne"?
dariya Azeema tayi ganin yarda yabi ya rikice ta wani 6angaren kuma ba ƙaramin daɗi taji ba,saboda bata da wani burin daya wuce taga ta faranta mashi,tana son ganin farin cikin junaid sosai,yaron tun yana ƙarami take tsananin son shi,
"Junaid duk naka ne wannan,Na musamman ne nasa akayi maka shi,duk duniya babu mai irin shi sae kai kaɗae,ni da kaine na bada sample ɗin yadda za'a haɗa maka shi,ka duba a jikin zoben ka gani,Harafin J ne ajiki wato farin sunanka,"
Wani irin farin ciki ne,ya cika junaid,a ƙarshe daya rasa abun cewa kawai sae ya fashe mata da kuka Yana cewa"mommy azeema,narasa da wasu kalmomi zan iya gode maki,babu su abakina,kin sanyani farin ciki sosai da wannan kyautar da kika bani.
Hannu tasa tare da shafo gefen fuskarshi izuwa cikin sumar kanshi tace"kasan dae babu godiya atsakaninmu ko?nayi maka wannan ne saboda inga farin cikin ka,kuma Alhamdulillah nagani kuma naji daɗi sosai,abu ɗaya zakayi mun yanzu shine ka share hawayenka,bana son ganinsu suna zuba,"
Cikin sauri junaid ya sanya hannunshi tare da goge hawayenshi duka,sannan ya mayar da hankali yana kallonta,
Cigaba da magana tayi a natse"junaid kana addu'a kuwa"?
gabanshi ne yaji yayi wani irin bugu jin tambayar da Aunty azeema tayi mashi,baisan dalilin dayasa tayi mashi wannan tambayar ba,
A ɗan ruɗe yace"Mommy meyasa kikayi mun wannan tambayar"?
shiru ta ɗanyi kamar mai nazarin wani abu kafin taci gaba da cewa"junaid bibiyar rayuwarka akeyi!"
Hankali atashe junaid yace"Ni kuma mommy azeema,to meyasa ake bibiyar rayuwata?su wanene ke bibiyar rayuwata,me nayi masu?kuma me suke so atare dani?"gaba ɗaya ya gama ruɗewa,
"Just calm down ur mind,ba wani abu bane na tashin hankali ba,banaso ka sanya damuwa a ranka junaid,amma ya zama dole na sanar dakai,akwai wata baiwa da Allah yayi mun,duk in nayi mafarki yana xama gaskiya,bawan da yasan da hakan sai ni,abubuwa da yawa kafin su faru acikin gidan nan,ni nake fara ganinsu acikin mafarki na,Allah yana nuna mun...'ajiyar zuciya ta dan sauke tana kallon junaid daya kasa kunne yana sauraronta,
kafin taci gaba da cewa"Nayi mafarki akan ka junaid,mafarkin ya tsoratar dani sosai,wannan dalilin ne ma yasa na nace akan saina zo,ba don komai ba sai don na ganka naga wani hali kake ciki......'
gaba daya hankalin junaid yayi mugun tashi muryar shi na rawa Yace"Mommy azeema,dan Allah ki fahimtar dani wani kalar mafarkine wannan?wani mummunan abune zai faru dani ne?mutuwa zanyi ko?dama najima ina ji araina cewa bazanyi tsawancin kwana ba.........'bata bari ya ƙarasa maganar ba,tasa tafin hannunta ta rufe mashi bakinshi,tsit junaid yayi jikinshi na rawa,zuciyarshi naci gaba da bugawa da ƙarfi da ƙarfi,
Cikin sanyin murya tace"Junaid,babu wanda ya isa yayi maka abunda Allah baiyi maka ba!tabbas rayuwarka na cikin hatsari sosai saboda duk wani dake son ganin bayan zuri'armu ta wurinka zai biyo junaid,dole sae da kaine za'a iya cutar damu junaid saboda kaine lagwon kowannanmu,kaine farin cikin mu gaba ɗaya.....' ƙarasa maganar tayi tare da zame hannunta daga bakinshi,
Jikin junaid yayi mugun sanyi,bakomai ya faɗo mashi aranshi ba face wannan ɗigon jinin dake ɗigowa daga hancinshi,da kuma daren ranar nan daya farka tsakar dare yaga wani baƙin hayaki ya fito daga cikin madubin ɗakin Abbansu,ya tunkaroshi ya shiga ta ƙopar hancinshi,a lokacin bayan ya farka washe gari,duk tunaninshi mafarki ne yayi ba gaske ba,amma yanzu da Aunty azeema tayi mashi wannan maganar sae wani tunanin ya faɗo mashi aranshi,tun daga daren ranar da hayaƙin nan ya shiga ta ƙopar hancinshi,a washe garin ranar jinin nan ya soma ɗiɗdigowa daga hancinshi,tabbas akwai wani 6oyayyen abu dake shirin faruwa dashi,
Tuna wannan abun yasa junaid ɗagowa idanunshi awaje yana kallon mommy azeema yace"Nashiga uku!mommy ina cikin tashin hankali!mutuwa zanyi bazan rayu ba...kashe ni zasu yi....bazasu bar ni da raina ba ..zasu rabani da Abbana'
Ganin yarda junaid yabi ya gigice yasa ta ruƙo hannunshi sosai tace"Ka natsu junaid!ba kayi imani da Allah bane?
Cikin shessheƙar kuka yace"nayi Imani da Allah mommy azeema,amma ni bana so na mutu yanzu,inaso na rayu ko don nacika ma abbana burinshi da kuma burin da nake dashi... '
Katse shi tayi da cewa"tunda kayi imani da Allah,to inaso kasa aranka cewa babu wani mahaluƙi daya isa ya cutar dakai a faɗin duniyar nan face da izinin sa,sannan inaso ka dage da addu'a na sanka junaid baka ba addu'a mahimmanci sosai,kuma ita addu'a da kake gani takobin mumini ce,ka tashi tsaye ka dage da addu'a ka yaƙi duk wani wanda ke son ganin bayanka,kayi mun alƙawarin hakan,nima kuma zan tayaka da addu'ar,sannan zanyi ma abbanku magana akan ya dinga tashin ka tsakar dare kunayin sallah atare koda ace shi bai tashi ba,in har ka farka to ka shiga toilet ka dauro alwala kayi sallarka,sannan kuma zan sanar ma sauran ƴan uwanka duk zanyi masu magana akan su tayaka da addu'a Allah ya tsare mana babynmu,'
Wani irin sanyi yaji ya ratsa zuciyarshi,kalaman Aunty azeema ba ƙaramin sanyaya mashi zuciya su kayi ba,ya samu ƙwarin guiwa sosai awurinta,har ya daina jin damuwa a ranshi,
"Kana da budurwa"?cike da zolaya tayi mashi maganar,don ta kawar da damuwar dake aranshi,
Sunnar da kai junaid yayi tare da cewa"am...um....eh..'
Dariya Aunty azeema tayi tana cewa"wai kunya ta kake ji ne?dalla faɗamun ni inji,"
Hannu yasa yana ɗan sosa ƙeyarshi yace"mommy azeema,akwai wadda nakeso sosai,kuma itama tana sona sosai,acikin gidan nan take,tare da Aunty azmee suke aiki,yau ta sanyani farin ciki sosai mommy,ta kar6i soyayyata,aure kawai ya rage yanzu inyi ma Abbanmu magana.....'kasa ƙarasa maganar yayi ganin yarda Azeema ta saki baki galala tana kallonshi,
Cike da jin kunya junaid ya kifa kanshi asaman laps dinta yana faman tiƙar dariya,
Suna cikin wannan rahar,wayar Hajiya azeema ta shiga ruri,tsagaitawa tayi daga yin dariyar da take,sannan takai hannu tare da ɗaukar wayar dake ajiye gefenta,ta duba mai kiran nata,a fili tace"Abbanku ne ke kirana,bari na ɗaga naji me zaice mun,"ta ƙarasa maganar tare da kara wayar a kunnanta,
Lamo junaid yayi kwance saman laps ɗinta,ba komai yake tunawa ba face soyayyar da suka sha tare da rishi ɗinsa acikin mota,soyayyarta ƙara ninkuwa takeyi acikin zuciyarshi,musamman da ta kar6i soyayyarshi hannu bibbiyu kuma ta amince zata aure shi,yanzu bai da sauran damuwa,dama itace damuwarshi kullum fargabarshi taya zai tunkareta da zancen soyayyar,zata amince ko bazata amince ba!?
Yana cikin wannan zancen zucin nashi yaji muryar azeema tana cewa"Alhamdullillah!Alhamdulillah mun gode ma Allah daya sauke su lafiya,ba don na tara gajiya ba,da ba abunda zai hana nima na biku Airport din mu tarboshi ..'
cike da farin ciki junaid ya ɗago yana cewa"Mommy,Uncle ɗinmu ne ya ƙaraso nigeria"?
Fuskarta dauke da murmushi tace"Eh,yanzu Abba ke sanar dani cewa sun shirya zasu tafi airport ɗauko shi,jirgin nasu bai kaiga ƙarasowa ba,amma kafin su isa airport din zai ƙaraso da yardar Allah,
Cikin sauri junaid ya sauko daga saman gadon jikinshi na rawa yace"Mommy azeema,ki ajiye mun gift ɗina a wurinki,zanzo na kar6a anjima,inaso zanje airport ɗin nima tare dasu Abbanah,'ko amsarta bai saurara ba,ya fuce da sauri da sauri,
Murmushi Azeema tayi yayin da take bin bayanshi da kallo har ya fuce,
Goggon katsina
Da gudun gaske ta fito daga cikin ɗakinta,hannunta ruƙe da wayarta saboda tsabar farin cikin jin zuwan Abusufyan ɗinta da abbansu junaid ya sanar mata,
Adai dai lokacin Saude da dr haris suna manne da juna saman 3 seater a falo suna shan soyayya,yana ƙoƙarin manna mata kiss asaman wuyanta,kwatsam sai ga