Showing 15001 words to 18000 words out of 432432 words
Chapter 6 - Abban Sojoji Book 2 Hausa Novel Complete
bakan da yayi, kamar zatayi kuka take kallonsa tana cewa "Junaid hakan na nufin ka ta6a gani na babu kaya ko"?
Girgiza kai yayi yana faɗin "No ba haka bane reeesh, baki fahimce ni bane, Ina nufin....," sam ya gaza samun amsar da zai bata gashi ta tsare shi da ido tana jiran amsar shi,
Muryar azmee ce ta katse su da cewa "tsayuwar me kuke yi ne? Ku hanzarta mana muyi mu kammala, yaushe har muka wuce wurin Saloon ɗin," cikin sauri junaid yace "Hakane aunty azmee muje kawai yanzu saura me ya rage," Ya tambaya yana kallonta
yayi hakan ne don ya gusarma sehrish da tuhumarsa da take yi, cikin sauri suka wuce tabi bayansu itama,
A ranar yini su kayi siyayya Kamar zasu kwashe kayan Mall ɗin,komai sai da suka siyar mata shoes & bags ne Cosmetics komai wannan ba abunda suka bari,
Daga nan suka wuce wurin haɗaɗɗen Saloon ɗin duk acikin Mall ɗin yake, a lokacin junaid ya koma cikin mota yana jiran su,
Already sun kammala purchasing ɗinsu an jera Manyan akwatinan guda uku biyu sunfi girma a boot aka zuba su, Wasu kayan kuma na acikin Manyan Shopping bags an zuba su har a cikin back seat na motar,
Murmushi kawai junaid ke saki ya langwa6ar da kansa jikin seat ɗin motar, babban burinsa shine yaga yarda sehrish ɗinsa zata fito amatsayin mace a fili ya furta "Can't wait to seee" tabbas yanzu ne yasan yasamu abokiyar rayuwa wadda zasu kasance atare na har iya tsawon rayuwarsu, shigowar sehrish rayuwarsa ta canza mishi wasu abubuwan da dama da yake kewarsu,daga ciki harda kewar Mommynsu da tatafi tabarsa tun yana jinjiri wannan abun ya ta6a mishi zuciya sosai raɗaɗin na'a ransa yana jin cewa duk cikinsu shike bata so, hakan yasa shima baya sonta duk in ta kira waya tana so abashi tayi magana dashi baya kar6a, har ila yau junaid bai ta6a ganin Mommynsu ba ido da ido sai dae a hoto, babu yarda batayi ba akan akawo mata shi Sydney amma abbansu yace muddin tana son ganin shi ta tako tazo da kanta in ba haka ba ita dashi har abada, saboda batayi mashi adalci ba,' wannan kenan
Ya jima yana tunane tunane shi kaɗae abunsa yana ta faman sakin murmushi, adai dai time ɗin Sehrish ta fito tare da Aunty azmee,
Ƙaraso wa su kayi ta bude gaban motar ta shiga aunty azmee kuma ta shige baya sannan junaid ya tayar da motar yana faɗin "Har an kammala saloon ɗin"?
ya tambaya yana ɗan kallonta tace mashi "Eh,'.
"In munje gida za'a nuna min," ya faɗi da ɗan murmushi a fuskar shi, kai tsaye yabar bakin Mall ɗin yaja Motar kai tsaye ya nufi hanyar gida dasu duk da yaso su biya wurin shan ice cream amma shi kanshi a gajiye yake yafi buƙatar gidan don ya huta, Dama jikinsa sam ba irin na ƴan wahala bane,
Motarsu na shiga babban entry ɗin gidan adai-dai time ɗin kuma Motarsu Marshal Omar ta fuce daga gidan, Tasu na shigowa tashi na Fice wa,
🙅
Bayan yayi parking ɗin motar, wani sergeant ya ƙaraso ya kwashe akwatinan da junaid ya fito a boot ɗin motarsa, , Hada jakunku nan siyayyar na cikin back seat ɗin duk ya fiddo su, yayin da sojan ke kwashe su izuwa cikin gidan,
Agajiye azmee da sehrish suka shiga cikin Babban falon bakowa alamar duk sun fita, azmee ta taimaka mata suka shigar da kayan ɗakin suka jibge su da nufin in sun huta an jera su a wardrobe ɗinta,
Cike da zumuɗi sehrish ta cire hijabinta don taga gyaran gyashin da akayi mata, Gaban mirror ta tsaya tana kallon gashinta, haɗaɗɗen gyaran gashi akayi mata mai haɗe da Twist,
Sai ta rinƙa jinta tamkar Queen saboda haɗuwa, ta jima tana kallon kanta a mirror kafin ta wuce toilet don yin wanka da alwala,
Shaf shaf ta fito jikinta ɗaure da toilet, wardrobe ta wuce ta samu riga da wandonta ta zura ajikinta sannan ta ɗauki hijab da dardumar salla ta shimfiɗa, ta kabbara sallah A natse ta Gabatar da sallar,
Bayan ta kammala Jiki na rawa ta cire hijab ɗinta ta ninke tare da abun sallar asaman gado ta ajiye su,
Zama tayi tana bubbude kayayyakin da aka siya mata na cikin jakun kunan, sam bakinta yaƙi rufuwa, wani haɗaɗɗen takalmi ta ɗauko high heels ta ciro shi daga kwalinsa tana gwadawa a ƙafarta ita kanta ta razana daganin yarda ƙafarta ta fito ɗass acikinsa gashi ash colour jikinsa duk kyalli yake ga wasu igiyoyi na ɗaure sa ya haɗu,
Shigowa azmee tayi tana faɗin "Kai!kai! Irin wannan zallar kyau haka gaskiya naji tsoran haɗuwar da zakiyi anan," .
Dariya sehrish tayi tana cewa "dama yanzu nake so in jera kayan acikin wardrobe bansan ma ta inda zan fara ba,"
Azmee tace "kada ki damu ae shiyasa nazo saboda nata Ya ki jera su Muyi mu gama, akwai sauran aiki agabanmu ga gyaran cikin gida ga kuma aikin Kitchen,'
Miƙewa sehrish tayi ta janyo akwati nan biyu da hannunta izuwa wurin wardrobe ɗinta ta jingi ne su,itama azmee ta janyo ɗayan akwatin tana cewa "Ki barmun jeran kawai, kije ki gyara cikin gidan kafin na kammala Canza ma ɗakin nan naki kamanni," .
Murmushi sehrish tasaki tare da cewa "Toh aunty azmee," Sai da tafara ɗaukar mayafinta a cikin wardrobe ɗin sannan ta fuce tana murmushi,
Babban falon tafara gyarawa duk da babu wani datti a tsaftacensa yake, shaf shaf tagama, cikin hanzari ta wuce upstairs don gyara ɗakin babban yayansu, tana cikin taka steps ɗin taji motsin mutun a down, juyowa tayi don taga kowane ne, Karaf idonta suka sauka akan na HAR0ON, sam yagaza ɗauke idonsa akanta kallon kallo suka shiga yiwa juna, duk a tunaninsa sehrish zata mayar masa da martani amma abun mamaki sai yaga tasakar mashi wani irin ƙayataccen murmurshin kashe zuciya tamkar ta soke shi da kibiya a ƙahon zuciyarshi haka yaji, don har saida yasa hannu ya tarbe saitin zuciyarshi, wani irin sabon kyau yaga yarinyar tayi mishi (nace ba kabari sai ta fara ɗaukar wanka tukunna munyi wannan maganar,"
Juyawa sehrish tayi cikin hanzari ta wuce apartment ɗin SGR, tabbas taso ta mayarwa Haroon martani amma daga baya tagane cewa ba buƙatar yin hakan, yanzu fa ita tamkar Princess take ƴa ɗaya tak ga Shugaban sojoji kuma ƙanwar sojoji, dole ne taja class muƙami iya muƙami, wannan kaɗae ya isa ya kashe haroon saboda ƙululun baƙin ciki,
Zuru haroon yayi sam yagaza motsi daker ya iya ɗaga ƙafarsa ya soma tafiya jiki a mace, Har time ɗin tafin hannunsa na a dafe da saitin zuciyarshi
Bin shi da kallo junaid yayi wanda fitowar shi kenan daga sashen abbansu,
Ƙarasawa yayi cikin sauri ya nufi haroon yana faɗin "Yaya Haroon lafiya meke faruwa ne, naga ka dafe zuciyarka, ince dai ba wani abu ya same ka ba,'
ɗagowa da ido haroon yayi yana kallonsa yace "Jini Junaid,"
Jin wannan yasa junaid tallabo shoulders ɗinsa yana faɗin "Subhanallahi jini kuma a ina yaya haroon,"
da wannan muryar tasa ta ƴan giya yace "Yanzu duk jinin dake kwaranyowa daga zuciyata ba ka gani ba? Kibiyar da aka soka mun fa? Ko shima baka gani ba"? Ya faɗi a susuce yana kallon junaid,
Baki asake junaid ke kallon ikon Allah shidai baiga komai ba a ƙirjin haroon hannunsa ne kawai daya tallabe wurin,
Cikin ruɗi yace"yaya haroon babu komai fa a wurin hannunka ne kawai daka sa ka dafe,
Muryar tamkar zaiyi kuka yace"Manxon Allah yayi gaskiya Junaid, shikenan bakomai jeka kawai Allah yayi maka albarka, ya kare ka daga sharrin Maƙiya,
Ya faɗi tare da janye hannun junaid daga kafaɗarsa ya wuce sa yana cigaba da sambatu
Girgiza kai junaid yayi tare da cewa "Allah ya baka lafiya yaya haroon ya yaye maka wannan shaye-shayen da kake fama dashi,"
Yana gama faɗan hakan ya wuce direct ɗakin sehrish don yagaza runtsawa burinsa kawai yaganta ta zura kayan mata ajikinta, yana shiga ya samu azmee tana faman jejjera mata kayan a cikin wardrobe ɗinta, ko ina da abunda aka zuba aciki, gasu nan komai ajere, gwanin kyau,
Jin sallamar junaid yasa ta juya da fara'a tana amsa mashi,
Yace "Aunty azmee ina Sehrish ne i thought zanzo na same ta anan ne,"
Azmee tace "ae tuni ta fita don gyara cikin gidan kasan munbar aiki dayawa shiyasa bamu samu hutu ba,"
ɗan zumbura baki yayi tare da cewa "Aunty azmee wane aiki kuma? Mu dawo agajiyen sai kuma ta kama wani aikin, gaskiya bai yiyuwa zanje na dakatar da ita,' ya faɗi tare da juya ya fuce
Murmushi azmee tasaki aranta tana fadin "Romea kenan, Allah dae yasa sehrish tazama mallakin ka, duk da nasan abune mai wuya ayi mashi aure at his age, bansani ba shi da ita waye zai raini wani shi shagwa6a ita kuma shiririta, amma kuma raina na bani cewa akwai wanda sehrish ke so ga dukkan alamu...............
ta ƙare maganar zucin nata ayayin da ta koma gaban dressing mirror ɗin sehrish dayake wayaam babu kayan kwalliya kona shafawa illa kwalba ɗaya tak na turaren junaid da tata6a satar mashi wanda har yau bata ta6a amfani dashi ba,
Janyo trolley ɗin dake ɗauke da cosmetic tayi ta shiga jera mata su, da turarurruka da mayukan jiki masu kyau da ƙamshi da sauransu, sai gashi mirror ɗin yafito sosai na ƴar budurwa,
Cikin ƙanƙani lokaci rishi ta kammala gyara masa part ɗinsa, da wata irin yunwa ta fito ga bacci tana ji tana saukowa down suka ci karo da junaid dake tunkaro stairs ɗin,
da murmushi a fuskarta tace "Junaid dama idonka biyu ae nayi tunanin kana can kana sharar bacci,'
yatsina fuska yayi tare da cewa "taya zan iya bacci bayan banga gyaran gashinki ba, zuwa nayi ki nuna min in gani," ya faɗi hada ruƙe ƙugu,
Dama tana kallon fuskarshi tasan rigimar ta motsa ga Idonshi sai faman lumshewa suke yi alamar bacci yake ji over,
Saukowa ta yi tana cewa "Shikenan zan nuna maka ammma kabari nafara samun natsuwa tukunna, yanzu kitchen zanje na gyara kuma yunwa ma nake ji,"
Shiru yayi baice komai Ba dayaso hannu kawai zaisa ya tu6e mayafin data yafa, abunda ya hanasa yin hakan baiso wani yagani cikin Yayyensa balle ya ƙyasa, don kishinta yake ji ayanzu kamar kamar me,
Shiga gaba sehrish tayi ta nufi hanyar kitchen, cikin hanzari yabi ta yana faɗin "Nima yunwar nake ji, zan tayaki mu gyara kitchen in mun kammala cin abincin atare,
"Shikenan bita zaizai," ta bashi amsa tana dariya, shima dariyar yayi jin sunan da tasa mashi,
"Idan baki so zan daina bin ki,' ya faɗi ayayin da suke shiga kitchen ɗin,
Sehrish tace"Nafison hakan ae, saboda kana ɗebe min kewa sosai,"
Jin hakan yasa junaid sakin murmushin murna,
Wuce wa yayi yazauna saman ɗaya daga cikin dining chairs ɗin dake kewaye da dinner table yana cewa "Ki haɗa mana corn flakes kawai mu sha, in akwai snacks ki haɗo mana dashi,
Ta amsa mashi da "Toh,"
A cup biyu ta haɗa musu sannan ta haɗo masu da snacks suka zauna suna sha suna fira, �?
________________AUNTY BABBA______________________
Suna cikin wannan fargabar wayar hafsat ta sake yin ringing, cikin hanzari tunkan tasa hannunta ta ɗauka aunty babba ta riga ta ɗaukar wayar asaman cinyarta, a tunaninta Omar ne amma tana dubawa taga Sunan My Dad ya bayyana, ɗagowa tayi ta kalli hafsat hankali atashe tace "Abbanki ne ke kira, Allah yasa dae ba dawowa zaiyi ba, ya salammm ni bansan meke faruwa dani yau Ba
Hannu hafsat tasa ta kar6i wayar, ta amsa kiran sannan takara a kunnanta tana zabga Sallama,
Janar ishaq ya amasa mata da cewa "Wa'alaikum salam my daughter, ina mommynki take ne, i ave been trying her phone number tana ringing ba'a ɗagawa why"? Ya tambaya yana jiran amsa,
Murya na rawa hafsat tace "am..dama...umm...tabar wayar a ɗaki ne ina ji, saboda ta shiga kitchen,
tayi maganar tana kallon mommyn nata data ke faman dafe zuciya,tana sauraron mai zai ce saboda wayar na a handsfree,.
Genar ishaq yace "shikenan ki sanar da ita cewa cikin week ɗin nan zan dawo insha Allah,".
"Shikenan daddy Allah ya dawo daku lafiya," sukayi sallama ta ajiye wayar tana faɗin "Tabɗijan Can akwai matsala fa,"
Aunty babba kuwa miƙewa tayi tana faɗin "Nashiga uku ishaq zai dawo ga zuwan Omar yau, bansan me zan fuskanta ba a wurin kowannan su... '.
Muryar hafsat ce ta katse ta da cewa "Amsar fa abayyane take mommy, ke ma kin sani Allah,saki ukun nan sun Wajaba Akan ki muddin Abba yaji abunda kika aikata, saboda wancan karan Ladi mai aikin mu da kika ma bugun mutuwa sai da ya aika ki maiduguri bayan marukan da kika sha awurinsa ina ga waɗan nan bayin Allahn da kika naƙasa har Su biyu, gasky mommy kin shiga Uku, ga kuma ƴa Omar zaizo ni addu'ata Allah yasa Abba kada ya sake ki yabarki kawai da hukuncin Omar na zuwa prison kowa ma ya huta.....
Hankali tashe aunty babba tace"Hafsat prison fa kika ce? So kike akaini can kin gaji dani kenan"?
Rai a6ace hafsat tace "dole nagaji dake mommy, duk ke kika ja mana wannan masifar da muke ciki muna zaman lafiyar mu,' ta faɗi a ƙuke hada buga tsoki kamar bada uwarta take magana ba,
Jinjina kai aunty babba tayi batare da tace komai ba, adai dai time ɗin dr ya fito daga ɗakin da aka kwantar dasu hosana, jiki na rawa tabishi tana faɗin "dr ya jikin nata ta farfaɗo,"?
dr yace "Alhamdulillah tafarka yanzu haka bacci take yi itama saboda allurar da nayi mata,"
ɗaga hannu tayi tana cewa "Alhamdulillah har naji ɗan sauki, amma dr babu yarda za'ae ciwon fuskarsu ya warke nan take? kumburin ya sa6e, ni dr kodai surgery za'ae musu ne acanza fuskar,' tayi maganar in serious matter tana kallon shi,
Wani irin kallo dr ɗin ke yi mata yama rasa amsar da zai bata,
wuce wa gaba yayi ya tunkari Office ɗinsa yana cewa "sam Bazaiyiyu ba gsky,ba muyin irin wannan aikin anan, kuma fuskarsu batayi komai ba da za'a canza musu Ba,da alama madam kema kina buƙatar Aduba ki,' sarai taji abunda dr ɗin yace amma bata ji zafin maganarsa ba, saboda bata cikin natsuwarta a yanzu,
Yini su kayi cikin fargaba ba salla ba salati dama ba ita bace agabansu ba, an saba haɗa salloli ayisu a lokaci guda,Saboda duniya aka sa agaba Ba lahira ba,
gajiya su kayi gaba ɗayansu da zaman asibitin ga uwar yunwa kamar suyi hauka, ga zullimi da fargabar zuwan Omar, ganin har Magrib tayi babu kiran Omar yasa suka fidda tsammani da zuwan shi,
Ƙarshe basu jira dr yayi discharge ɗinsu ba, aunty babba ta ɗauko hosana dake kwance saman gado agalabaice ta sa6o ta a kafaɗarta ta fito da ita, sai cikin mota ta kwantar da ita, Jahad ma tashiga motar baiwar Allah ga zazza6i tana ji, gashi dr yace suna buƙatar jini su duka biyun amma babu yarda zasu yi, rayuwarsu a tagayyare sai yarda akayi dasu,
Shiga motar hafsat tayi mazaunin driver aunty babba na gefenta suka ja motar suka bar asibitin, a time ɗin har dr ya biyo su da sauri sauri don ya dakatar dasu amma ina tuni har sun bar arean asibitin.............
A tsiyace ta shiga da motar cikin gidan tayi parking ɗinta, tana fito wa ta wuce ciki saboda jirin da take ji na yunwa, fitowa itama aunty babba tayi sam bata tsaya taɗauki hosana ba ta shige ciki itama,
Hankalin jahad ba ƙaramin tashi yayi ba ganin sun tafi sunbar hosana kwance sai faman nishi take saki numfashinta na fita daker-daker,
bata son yaya zatayi ba ta ɗauke ta saboda itama babu sauran ƙarfi ajikinta, fitowa tayi daga cikin motar tana faman zubda hawaye, Iya cuta dae an cuci rayuwarsu,
Ganin yarinya tsaye abakin mota yasa wani soja ƙaraso wa yana faɗin "Lafiya dai ƴan mata meke faruwa ne,"
Cikin shessheƙar kuka jahad tace "ƴar uwata ce ciki kwance bata lafiya bansan yarda zan shiga da ita ciki ba,"
Sojan yace "Can I help"? Jahad tace masa "eh" saboda bata da wata mafita da ta wuce hakan,
Buɗe motar yayi ya zura hannunsa ya sungumo hosana dake kwance magashiyyan ya ɗaurata a kafaɗarta ya shige da ita ciki jahad ta bi bayansa,
A saman 3 seater ya kwantar da hosana, jahad tayi masa godiya sannan tasamu wuri daga ƙasa ta zuƙunna fuskarta na dai-dai saitin ta hosana,
Hawayen fuskarta har ɗiɗɗiga suke yi a fuskar hosana, addu'o'i tashiga karantowa tana tofa mata,.
Duk hosana na jinta tana so ta buɗe idonta amma ta kasa saboda kumburar da su kayi, tana so ta buɗe bakinta tayi ma Jahad magana amma tagaza saboda haƙoranta kansu sun raunata sosai don ba'a rasa mai girgiɗi acikinsu, ga la66anta da sukayi suntum sam bata iya motsa su,
Cikin kuka jahad tace"Hosana na sani nasan akwai abunda kike son faɗa mun amma kin kasa, kada ki damu ina jin duk wani raɗaɗi da kike ji azuciyarki, inaji inama ace zan iya ɗauke maki zafin ciwon da kike ji da tuni nayi wlh.......taƙarasa mgnr tare da kifa kanta ajikin hosanna,sun jima a haka wulaƙance babu wanda ya leƙo su, sai daga bisa ni hafsat tafito har tayi wanka da alama ta canza kayan jikinta, doguwar riga ce tasanya har ƙasa, ta ɗaure gashin kanta,
Binsu da kallo tayi gwanin ban tausayi ita kanta duk rashin imaninta yau ta tausaya ma twins ɗin,girgiza kai tayi tare da wuce wa ta nufi kitchen,
Jim kaɗan sai gata ta fito hannunta ɗauke da tray mai girma, Tea set ne ɗauke asaman shi, sai French toast ɗin da ta hado masu dashi da sauran snacks, duk da tasan ma daker zasu iya ci
Bedroom ɗinta ta shigar masu da shi ta ajiye Tray ɗin asaman table ɗin dake a dab da gadonta, Sannan ta fito ta nufe su jin takun tafiyar hafsat yasa jahad ɗagowa daga kwancen da take tana kallonta da rinannun idanuwanta da suka jigata,
Hafsat batayi mata