Showing 69001 words to 72000 words out of 432432 words

Chapter 24 - Abban Sojoji Book 2 Hausa Novel Complete

ya amsa mata da cewa"Come in,"

  Shiga ciki tayi zuciyarta na dar-dar lokacin da ta aza idonta akanshi yana zaune gaban dressing mirror saman chair din dake gaban madubin, ya sanya tafin hannayensa ya tallabo gefe da gefen fuskarsa ya zabga tagumi agaban mirror, sam babu riga ajikin shi daga shi sai short green colour, da alama ma daga wanka ya fito yagaza yin komai shine ya zabga tagumin, Sumar kanshi duk ta barbazo ta rufe masa gefen face dinsa, da wasu siraran gashi da suka sauko ta saman fuskarsa idonshi na arufe saboda gajiyar da ta lullu6e ga66ansa da kuma baccin da yake ji ga kuma yunwa duk shi kaɗai



tsayawa sehrish tayi jiki asanyaye tana kallon shi tsananin tausayin shi ne yakamata ganin yarda ya zabga tagumi da hannayensa biyu, alamar baya jin daɗi

  Ta jima tana kallon shi kafin ta ɗanyi gyaran murya tace "dama abinci ne na kawo maka, bansan ko kana buƙata ba," ta fadi adan tsorace gudun kar tayi kuskure a maganarta,

   daker ya buɗe bakinsa tare da cewa"keep it on the table, then i wanna see u," gabanta ne ya faɗi rass ! jin abunda yace na yana son ganinta ƙarasawa tayi ta ajiye masa dinner din saman table ɗinsa, sannan ta matsa kusa dashi ta tsaya sannan tace "gani,"

  Hannu yasa ya ɗauko wata ƙaramar kwalba ta magani daya ajiye a saman mirror din sannan ya miƙa mata tare da cewa "rub it on my back," ya fadi tare da kifa kansa saman gaban mirror ɗin yadda zata samu damar murza masa maganin,

tama rasa ta ina zata fara shafa masa shi, gaba daya duk tabi ta rikice wai yau itace sgr da kansa ya bata magani don ta shafa masa abayansa, jikinta har kerma yakeyi tsoranta kar ta fasa masa fatar bayansa saboda hasken fatar fes tamkar in kasa yatsa jini zai fito,

  Matsawa ta ƙara yi dab dashi sosai sannan ta buɗe mufin kwalbar, tasa yatsa ta lakuto maganin tare da ɗan russinawa ta lakuta masa shi abayan, sannan tasanya hannunta a hankali tana shasshafa masa shi, tun da Allah ya halicce ta bata ta6a jin skin mai tsananin laushi da daɗin tabawa ba irin fatar bayan sgr, 

Shi kuwa ajiyar zuciya kawai yake saukewa saboda relief daya fara samu sosai na ciwon da ga6o6insa suke masa, tun sehrish nayi masa da hannu ɗaya har takai ga ajiye kwalbar maganin ta sanya duka hands ɗinta a faffaɗan bayansa tana yi masa massage, a tunaninsa in ta kammala zata cire hannunta ne, amma sai yaga ta zarce gaba ɗaya babu alamar zata daina shafa masa gashi kuma yaji ko'ina na bayansa yaji maganin sosai, shiru kawai yayi bai ce komai ba, almost one hour kenan sehrish na shafa masa magani har sai da ya ɗan ɗago da kansa daga kwancen da yake tare da cewa "Har yanzu maganin bai shafu bane"? Cikin sauri ta janye hannunta tare da ɗagowa tana kallonsa suka haɗa ido ta cikin mirror,

  gabanta ne taji ya ƙara faɗuwa rass ganin yarda kwayar idonsa ke shining sai taga tamkar tana canza launi ne daga blue zuwa green,.  

  sunnar da kanta tayi ƙasa tana faman haɗe yatsun hannunta dake dankare da maganin data shafa mashi,

lumshe idonsa yayi tare da sake buɗe su yace "kin haɗo mun da coffee ne? ya tambaya a kasalance hakan ba ƙaramin kashe ma sehrish jiki yayi ba, tuni ta nemi natsuwarta tarasa sai ta kama en ena tana faman wurwurga ido

 "Its ok, idan babu akawo mun shi," ya faɗi tare da mayar da idonshi ya lumshe su,

Juyawa sehrish tayi cikin sauri ta fuce izuwa kitchen donta haɗo masa, a lokacin har azmee ta kammala shirya masu abincin dinner ɗin a dining amma babu kowa asaman shi alamar basu kaiga fitowa ba,

 tayi mamakin hakan duk da tasan cewa duk suna cikin damuwa ne,bata ji daɗin hakan ba, tasa ba ganin mutanen gidan cikin raha suna nishaɗi suna cin abinci yau kuma wayaam babu kowa, Yau da gobe kenan,

   tana acikin kitchen ɗin bayan ta kammala haɗa masa coffee din ta ruƙo cup ɗin a hannunta, sai ga haroon ya faɗo mata kamar daga sama cikin sauri taja da baya hankalinta atashe, daga shi sai vest da singlet, shu'umin murmushi ya saki yana kallonta yace "ke shine nasa ki kaimun abinci kika ƙi ko? Ke ga isassa mai walkin sa harni ɗan masu gida zan saki aiki, ki bijire mun," ya faɗi yana kallonta

  Murya na rawa sehrish tace "kayi hakuri dama na fara kaima babban yaya ne, kafin na kawo maka nakan......'

 Bata ƙarasa ba ya katse ta da cewa "Sorry for your self sehrish! wlh kin shiga uku ! kin jefa kanki cikin masifa, daga rana irin ta yau inaso kullum ki kasance cikin yin sallar dare kina rokan Allah akan ya kare ki daga Sharrina," zaro ido tayi tana kallonsa jin abunda yace cikin tsananin tashin hankali tace "saboda me zaka ce haka"? laifin me nayi maka, dan Allah kabarni inyi rayuwata cikin salama,"

  Fashewa da dariya yayi kafin ya tsagaita da cewa "kinsan wani abu?kina da kyau sosai musamman idan kika tsorata idanunki ba ƙaramin fizgata sukeyi ba, idan kika amince a shirye nake dana aure ki, kuma zan shiryu nadaina duk wani abu da nake yi, amma idan kika bijire mun I pity u wlh," cikin sanyin murya yake yi mata magana,.

  Tamkar zatayi kuka tace"Dan Allah na roƙe ka kayi hakuri nidai ka fita daga cikin rayuwata, kabarni dan Allah kaje can ka samu mace irinka ka aura, amma ni ina da wanda nake so," tayi maganar tare da bi ta gefensa gabanta na faduwa ta wuce cikin sauri,

  murmushi kawai haroon yayi tare da jinjina kansa aransa yace "nasan ba kowa take hari ba face wancan mai zubin ifritan, ni kuma ba zan ta6a bari hakan ta faru ba, target ɗina na farko da zanyi zan fara 6ata sunanki ne a wurinsa," yana fadin hakan ya saki shu'umin murmushi tare da wuce wa room ɗinsa



 

Maganganun da haroon ya faɗa mata sun tsaya mata arai, tunaninta ya rayuwarta zata kasance nan gaba acikin gidan batasan me haroon zai yi mata ba,

tana tunanin tana tattaka stairs ɗin jiki amace, adai² lokacin Marshal ya shigo gidan cikin sauri saboda yarda yake agajiye shima, har sai da ta juyo daga saman stairs din ta ɗan kalle sa, ta other side ɗin yabi ya wuce part ɗinsa da hanzari sam bai lura a ita ba,

   bakomai bane ya faɗo mata arai face yaran da taji yace zasu zauna gidan Uncle Abusufyan ɗinsu, ko ya ɗauko su? ta tambayi kanta 

cikin sauri ta wuce part ɗinsa bedroom ɗinsa ta shiga da sallama ya iznin shiga, a lokacin harya dawo gefen bed ɗinsa ya zauna yana cin abincinsa, yau ba sai ya jira anyi saving ɗinsa,

  ƙarasawa tayi kusa dashi sannan ta samu wuri agefen plate ɗin abincinsa ta ajiye masa cup ɗin," 

A hankali ya furta "thanks,' a tunaninsa zata tafi amma sai yaga tayi masa tsaye akansa, sam bata son ta tafi tabarshi saboda a ganinta in ta tafi bazai ƙarasa cin abincin bacci zai iya ɗakarsa,

Hannu yasa ya ɗauki cup of coffee ɗin data kawo masa sosae yasha, bayan ya kammala ya ajiye shi, sannan ya gyara kwanciyarshi ya kwanta luf abunsa, ya janyo blanket ɗinsa ya rufe har zuwa chest ɗinsa nan take bacci ya ɗauke sa, 

bata bar bedroom ɗin nasa ba sai da ta tabbatar tayi masa addu'a tukunna tasa hannu ta kwashe kayan abincin acikin tray ta fuce dasu a hannunta,

   Kitchen ta koma da hanzari ta haɗa ma Marshal Omar nasa shima acikin tray sannan ta wuce masa dashi part ɗinsa,

tana shiga a lokacin ya fito sanye da jallabiya fara wuri ya samu asaman 3 seater ya zauna hannunsa ruƙe da wayarsa ganin sehrish yasa shi sakar mata murmushi tare da cewa "kamar kinsan a yunwace nake abunda nake jira kenan,"

  Murmushi ta saki tare da ƙarawa ta ajiye masa tray ɗin asaman table ɗin dake a gabansa sannan tace "Ya mai jiki ya omar, naji abunda ya faru Allah ya kiyaye gaba, ya tonu asirin su,"

  "Ameen Ameen," ya amsa mata, hannu tasa ta buɗe warmer tare da ɗaukar plate da saving spoon zata zuba masa abinci taji yace "baki tambaye ni twins ɗina ba"? Murmushi ta ɗanyi tare da ɗagowa ta kalle shi tace "dama ƴan biyu ne"? Yace "eh kamannin su ɗaya sak, ke ma haka fuskarki irin tasu ce sak komai da komai,"

   gabanta ne taji ya faɗi jin abunda omar yace dakatawa tayi da zuba mashi abincin tana son tunano wani abu arayuwarta amma sam takasa tunawa, tabbas tana jin cewa akwai wani abu da ta manta arayuwarta mai matuƙar muhimmanci agare ta, a duk lokacin da tayi ƙoƙarin tunawa sai taji zuciyarta tayi mata wani irin nauyi sosai,

"Wata rana zan kawosu ku ga juna, saboda inaso ki ga abun al'ajabin da nake son nuna maki,"

Cikin sauri tace "Shikenan ya Omar Allah ya kaimu lokacin nima zanso nagansu,"

ta jima suna dan fira dashi kafin daga bisani ta bar part ɗin nasa ta koma ɗakinta, 

 Bayan Omar ya kammala cin dinner ɗinsa fitowa yayi tare da wuce wa ɗakin da suka kwantar da fawan

  Yanayin daya samu Twis zaune zun zuba mashi ido ga kanal yusif shima zugudum duk cikin jimami, gyaran murya yayi duk suka ɗan ɗago kana yace "ku tashi ku je ku kwanta, tun da ya samu bacci" 

  Amsa mashi su kayi da "toh" sannan suka miƙe tare da fuce wa daga ɗakin shima yusif yayi yabi bayansu, zama Omar yayi daga gefen fawan dake ta faman sharar bacci, addu'o'i ya shiga karantowa yana tatto fa masa, ya jima yana yi masa addu'a sannan ya tashi yabar ɗakin tare da tufe masa ƙopa,

****************

Wuraren ƙarfe sha biyu ya fito cikin sanɗa hannunsa ɗauke da pillow yana duddubawa yaga in ba kowa duk sunyi bacci lokacin murmushi ya saki tare da cewa "sheggu saboda wancan ɗan shilan shine duk suka susuce har suka gaza cin abinci, bari na ƙarasa shi lahira sai in ga ya zasu yi, zasu bi shi ne

 Yana faɗin hakan ya wuce ɗakin da suka kwantar da fawan cikin sanɗa ya tura ƙopar tare da sa ƙafa yashiga cikin, bin shi yayi da kallo jinjina kansa yayi sannan ya lalla6a ya haye saman gadon tare da ɗaga pillow ɗin ya taushe ma fawan hancinsa dashi , nan take fawan yafarka tare da zazzare idanunshi yana mutsu-mutsu sam bashi da sauran ƙarfi ajikinsa da zai iya kwatar kansa........... ... ...

sai faman kiciniya fawan yake yi saboda ya kwaci kansa daga hannun haroon wanda ya taushe masa fuska da pillow da mugunta ma yake kara danna masa shi, tun fawan yana wutsil wutsil da ƙafafunsa numfashinsa na kokarin daukewa gaba daya har jikinsa ya fara saki, suna cikin wannan halin aka kwankwaso kopar da karfin gaske,a wani irin tsorace haroon yayi wurgi da filon dake hannun shi, yayi wuff tamkar giftawar walkiya ya afka bayan labule ya boye yana faman zazzare idanun shi kamar na mujiya tsoran shi kar ace wani ne ya taso cikin daren nan,
Hannu yasa a hankali yaɗan buɗe labulen don yaga kowanene, gabansa ne yayi bugun bugu ganin Abbansu ya shigo ciki jikinsa sanye da jallabiya fara, cikin sauri haroon ya mayar da labulen ya rufe ruff tuni zufa ta soma tsattsafo masa a jikinsa tamkar wanda aka tsamo daga kogin maliya,


�?




   ganin yarda fawan ya tashi zaune saman gadon yana faman hargowa yana fadin "zasu kashe ni ! bansan me nayi masu ba! Sun biyo ni don su kashe ni, ku ce musu su daina azabtar dani !!!! Gaba ɗaya ya zauce sai zuba sambatu yake yi yana zazzare ido,
   A hanzarce Abban nasu ya ƙarasa tare da haye wa saman gadon dab dashi yana cewa"fawan sannu ya jikin? ka dawo cikin hayyacin ka ko? ka kwantar da hankalin ka, kana a gida yanzu babu wanda zai iya cutar da kai,'. 


�?




   girgiza kai fawan yashiga yi yana sake maimaita cewa "Har yanzu suna nan, bibiyata suke yi so suke su kashe ni, ni bansan me nayi masu ba," yana magana daker daker yake sakin numfashi, hancinsa har ya fara bleeding kaɗan jinin ke ɗigowa,
   tallabo fuskarsa Abban nasu yayi tare da ɗago da ita don ya kalle shi sosai yace "fawan Ni ne fa,Abban ku ina tare dakai, babu wani anan da zai cutar da kai,"
  A hankali fawan ke kallon Abban nasu yayin da idon shi ke rurrufe wa yace "Abba ruwa zan sha," ya faɗi agalabaice,


�?




   Cikin sauri Abban nasu ya matsa tare da kai hannun shi saman bedside drawer ganin dakwai bottle water mai sanyi ajiye asama, ɗauko wa yayi tare da buɗe murfin ya kwafa masa abaki yana sha, jikin shi har wani kerma yake yi tamkar zai kwace roban ruwan daga hannun Abban nasu daya kwafa mashi, ganin yarda yake shan ruwan throat ɗinsa har wani sauti yake fitarwa kwattt!kwattt!! Saboda yarda yake kurbarsa a zafafe,

ba ƙaramin tausayi yaba Abban nasu ba, tamkar ya zubar mashi da kwalla haka yake ji, daurewa kawai yake yi
  Sai da ya shanye kusan rabin ruwan sannan ya janye mouth ɗinsa alamar ya ƙoshi, sannan Abban nasu ya rufe robar ruwan ya mayar da ita saman side drawer din ya ajiyeta,
  Sannan ya mayar da idon shi kan fawan dake ta faman sauke ajiyar zuciya yana fidda sound na radaɗin ciwo abakinsa,
  Haroon daka la6e acikin labule yace "shegen yaji dannar manya,an gaya ma jin ƙamshin mutuwa wasa ne,dole ka nemi ruwa yaro, ba don jatuminka ya faɗo cikin ɗakin nan ba, da yau saina aika ka barzahu wurinsu munkar, gskiya Abba ya kawo mun cikasss amma ba komai mu haɗe gaba,' ya faɗi yana cizon la66ansa,
  Haroon kenan duk da yana cikin tashin hankali amma hakan bai hana shi sambatun nan nashi ba, mutuwa ce kawai zata iya zuge zeep ɗin bakinsa, 
muryar shi na rawa yace "Abba ashe zan ƙara rayuwa? abba nasha wahala sosai tamkar bazan rayu ba,ashe da rabon na sake ganinku a idona"? Ya faɗi yayin da idonshi ke zubar da kwalla,
   shima Abban nasu jiki asanyaye yace"Fawan nasani wlh,nashiga damuwa sosai game da halin da kake ciki har nagaza runtsawa saboda son nazo naga wani hali kake ciki,kayi haƙuri fawan iya cuta dae sun cuce ka sosai sun raunata dukkan ga66an jikinka, amma nayi maka alƙawarin cewa ɗaya daga cikinsu bazai sha ba, wlh muddin ina da raina da kuma lafiyata saina ƙuntata duk wani jin daɗinsu na duniyar nan,"
  Lumshe ido fawan yayi tare da kwantar da kanshi a kafaɗar Abban nasu yana sauke ajiyar zuciya sannan yace "Abban sunce fansa suke ɗauka akan family ɗin mu,wannan harin da suka kai mana, ba don kowa su kayi shi ba face saboda mu kawai," 
Jin wannan maganar ta fawan tasa zuciyar Abban nasu yin wani irin bugu duk da yasan maganar revenge ɗin amma baisan cewa akan ƴa'ƴansa bane abun zai afka,
  "Insha Allah, Allah bazai ta6a Basu nasara ba fawan,zamu tashi tsaye wurin ganin mun kawar da koma su wanene su,Kuma zamu dage da addu'a akan Allah ya tonu asirinsu ya Kuma Kare Mana zuri'ar mu da dukkan al'umar musulmi,"
  "Ameen Abbana," ya amsa mashi daker,
  Haroon dake a la6e bayan curtains duk yana sauraronsu gaba daya ya ƙagu abban nasu ya fuce daga dakin shima ko ya samu ya gudu,tuni kafafunsa suka soma daskare wa suna mashi raɗaɗi saboda tsayuwar da yayi, ga wani irin fitsari daya matse shi, sai uwar zufa ke wanko masa daga fuskarshi, runtse idanun shi yayi yana cewa "wayyyo Allah na, ko yaushe wannan tsohon zai ware nima in samu in gudu,lallaima mutumin nan wato saboda wannan ɗan shilan shine harya gaza yin bacci, ya wani kwaso kafafunshi yazo don ya gan shi,ina sane da komai wato ya daura son duniya ya aza masu,duk ranar dana hallaka ɗaya daga cikinsu zanga in haukacewa zaiyi ko kuma zaiyi suicide ne,' 
  Ya faɗi yana cizon lips dinsa yana wani irin huci, bude idonshi yayi tare da sa hannu ya sake bude labulen a hankali ya leƙa su, har time din abban nasu na zaune dirshan saman bedmattress din, fawan kuma ya kwantar da kanshi a kafaɗar shi,da alama ma bacci yayi awon gaba dashi gaba ɗaya ya lafe masa kwance luffff abunsa, 
  Tuni ran haroon ya ƙara 6aci saboda takaici da baƙin cikin dayake ji aduk lokacin daya ga Abbansu na nuna ma ƴa'ƴan alexandra soyayya,zuciyar shi tafarfasa take yi saboda jin haushi, mayar da idon shi yayi kan pillow dinshi da yayi wurgi dashi kasa, nan gabansa ya faɗi tsoranshi kada abban nasu yaga fillon don za'a iya samun matsala,
  Bari dae in taƙaice maku zance,Abban su bai bar ɗakin ba anan bacci ya ɗaukesu su duka biyun azaune fawan kwance a shoulder ɗinshi,
  Kamar yarda suka kwana a zaune suna bacci haka Sir Commender Haroon ya kwana a tsaye ba bacci duk yarda yayi motsi zai fito sai Abban nasu ya buɗe ido, hakan ne ya hana shi fitowa daga bayan labule, 
  ya kuke tunanin wanda  ya kwana atsaye idonshi buɗe fuskarshi zata kasance, koda yake fa soja ne 😂

   (Wata dae tace commendern ƴan Iska dae, Bana sojoji ba)😹😹😹

****************************Morning

tun da sassafe sehrish tafarka daga guntun baccin daya ɗauketa bayan Sallar asuba anan saman sallayar ta kwashe da bacci, duk jikinta amace tafarka sai faman hamma takeyi saboda yunwar da take ji, gashi yesterday night bata samu enough sleep ba saboda tayi nafilfilin dare,
   tunawa da school yasa ta yin hanzarin tashi tashiga toilet shaf shaf tayi wankan ta,
fitowa tayi jikinta ɗaure da towel fari, a bakin ƙopar toilet ɗin ta tsaya tana kallon uniform ɗinta da sukayi uban squeezing tun jiya da tadawo school ta cicciresu ta jefar saman gadonta bata ninke su ba kuma anan tabarsu,girgiza kai tayi sannan ta ƙarasa agaban mirrow ta tsaya tana shafa body oil ɗinta,bayan ta kammala ta feshe jikinta da turare sannan ta koma ta buɗe wardrobe ɗinta, hannu tasa ta ɗauko ɗayan uniform ɗinta mai pencil skirt ɗin nan sannan ta dawo ta ajiyesu gefen gadon tashiga zura su ajikinta, tana cikin sa

Chapters

Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login