Showing 105001 words to 108000 words out of 432432 words
Chapter 36 - Abban Sojoji Book 2 Hausa Novel Complete
bokitin dake ajiye awurin kayan, sannan ta wuce izuwa inda fanfonsu yake,ruwa ta tarbo acikin shi sannn ta ɗauke shi tadawo ta ajiye, ledar klin ta dauka tare da fasawa ta zazzaga aciki sannan tashiga tsoma kayan aciki tana wankewa idonta na zubar da kwalla,
suna cikin wannan zaman suka ji ƙarar dirar mota a ƙofar gidan, washe baki mammy tashiga yi tana cewa"ƴar albarka ta iso, nasan tadawo mana da abun arziƙi, ni dae naji daɗi ƴa'ƴana badae farin jini ba........' bata ƙarasa maganar ba Hayaam tashigo cikin gidan ba ƙaramin wanka ta ɗauka ba, jikinta na sanye da swiss lace ash colour, doguwar riga akayi mata dashi, ta matse ta tsam tamkar in tayi motsi rigar zata yage saboda yarda tayi tighting ɗinta, ta kashe ɗaurin kallabi nan, mayafin kuma ta aza shi a kafaɗa,
fuskarta ɗauke da murmushi ta ƙarasa wurin mammyn tasu, tashi tayi ta rungumeta tana cewa"ƴar albarka sai yau zan saki a idona"?
Murmushi hayamm tasaki tare da cewa"Ammi yau ɗin ma sa'a kika ci, ki gode ma Allah da kika ganni yau, domin kuwa gobe zan wuce abuja nazo ne nayi maki bankwana saboda zan koma can da zama ina fata Aunty laila ta sanar dake game da komawa ta can? Ta tambaya tana kallonta,
gaba ɗaya Amal ta kasa kunne tana sauraronsu,
Washe baki tayi tare da cewa"ta sanar dani mana, ae ba ƙaramin daɗi naji ba kwara ki tattara ki tafican kema ki shafo mana arziƙi,"
Fari da ido hayaam tayi tare da cewa"baki da damuwa in dae nice mommy, arziƙi mun gama yin shi, muddin burina ya cika tuni zan canza maku tamfatsetsen gida na kece raini, na siya maku manyan motoci na alfarma sannan na biya maki aikin hajji, mommy kuɗi fa har sai kin gaji dasu wlh," ta faɗi tana faman sakin murmushi,
Cike da farin ciki mammy tace"Allah?
"wlh kuwa mommy," hayamm ta bata amsa,
ganin amal na kallonsu yasa mammyn kwatsa mata tsawa tace"zaki mayar da hankalin ki kan kayan da kike wankewa ko saina zo nan na karya maki wuya, magulmaciyar banza ƴar sa ido," jiki na rawa amal ta mayar da hankalinta kan kayan da take wanke wa,
ruƙo hannun hayamm mammyn tayi sannan tajata suka shige cikin ɗakinsu, don kar taji me zasu ce,
a hankali take wanke kayan tunani iri iri na zuwa mata aranta, tana yawan jin suna ambaton abuja abuja, kodai can aunty amani take zaune ne? Ta tambayi kanta, jinjina kai tayi tare da cewa"ina da tabbacin cewa auntyna tana zaune acan itama, dole na nemi mafita bazan zauna su kashe ni ba, zan gudu ne batare da saninsu ba," ta fadi tare da tsame rigar da ta sanya acikin ruwan wankin..........'😳
****************
A 6angaren su hossana kuwa saboda damuwar da suka shiga na jin cewa ya Omar ɗinsu na da aure gaba ɗayansu ba wanda yayi breakfast saboda damuwa, su kansu sun rasa gane dalilin dayasa suke jin kishin matar shi data kirasu a waya, abincin da jahad ta shirya masu har yayi sanyi saboda tun safe yake ajiye saman dining table babu wanda ya ta6a shi, gashi har ƙarfe ɗaya yanzu yayi na rana,
A tare suke kabbara sallah bayan sun kammala suka zauna suna addu'o'i, shiru jahad tayi tana sauraron addu'ar hossana da take yi,
"Ya Allah kasa mafarki ne ba gaske ba na cewa ya Omar yana da mata, in ma dagaske ne ya Allah kasa ya sake ta su rabu, zuciya ta tafarfasa takeyi mun bazan iya jurewa ba........'
katse ta Jahad tayi da cewa"hossana kina a hayyacinki kuwa? ya sake ta fa kika ce? Idan yana son matar shi fa?
harara hossana ta jefa mata tare da cewa"waya faɗa maki yana sonta? Auren dole ne akayi masu, da ace yana sonta ae da bai 6oye mana cewa yana da mata ba har da ciki...'
Itama jahad ɗin harar ta mayar mata tare da cewa"baki da hankali wlh,dagaske ɗin ke zararriya ce, yaya omar yana son matarshi, ke bakiji muryarta ba yarda take magana daga gani tana cikin kwanciyar hankali, kuma tana samun soyayyar mijinta tunda gashi har tana da ciki zata haifa mashi baby..........' jahad bata ƙarasa maganar ba, hossana takai ma wuyan hijabinta cakuma tana cewa"Ni ce zararriya? ɗaga kai jahad tayi alamar e,
Bugu hossana tashiga kai mata, ganin bazata iya jurewa ba yasa suka kacame da faɗa, abu kamar wasa sai da dukkansu suka sha kuka, dama ransu a6ace yake, duk don saboda matar Omar,
(Sehrish tayi tsiya)
tsaf ta kammala gyara mashi bedroom dinshi da toilet dinshi da falonsa duka ko'ina a kimtse tabar mashi shi, fitowa tayi ta sauko down stairs a lokacin duk sun kammala yin breakfast ɗin nasu babu kowa a falon, kai tsaye ta wuce bedroom ɗin Haroon gabanta na faduwa rass rass, ƙopar a rufe take don haka saita sanya hannu tare da yin knocking ɗinta, daga cikin ɗakin tajiyo muryarshi yana cewa"Wanene"?
"Ni ce," ta bashi amsa cike da ƙarfin guiwa,
buɗe mata ƙopar yayi fuskar nan ɗauke da murmushi, jikinshi na sanye da singlet fara tare da shorts baƙi,
"shigo daga ciki mana," ya faɗi yana nuna mata hanya, kallon shi kawai takeyi , sa kai tayi ta shiga ciki daga tsaye ta tsaya tana kallon shi, rufe ƙopar yayi sannan ya juyo ya kalle ta yace "wlh har naji sanyi araina dana ganki cikin ƙoshin lafiya,ae nayi tunanin e warhaka kina asibitin kwance magashiyyan rai hannun Allah.....' bai ƙarasa maganar tashi ba tace"me nayi maka? Meyasa kake son kashe ni? saboda me ka bani wannan allurar?
tafi yayi da hannunshi yana dariya, wuce ta yayi tare da samun wuri daga gefen gadonshi ya zauna yana facing ɗinta yace"Ko da ace zan iya kashe kowa a duniyar nan, ni bazan iya kashe abunda raina ke so ba!!! nasan cewa ba zaki mutu ba, akwai wanda zaizo ya taimake ki shiyasa nayi hakan ! kinfiye taurin kai shiyasa na gwada maki kaɗan daga cikin shaiɗancina, kin manta maganar da kika faɗa mun nacewa NAMIJI kike kallo? Shiyasa na haɗaki da namijin...........' ƙarasa maganar yayi yana faman tiƙar dariya, sakin baki sehrish tayi tana kallon shi. Da ƙyar ya tsagaita da maganar tashi yana kashe mata ido yace"Yarinya taji maza,baki ban labari ba ya kuka ƙare jiya?
shiru tayi tana kallon shi kawai saboda abun yafi ƙarfinta haroon ba ƙaramin shaiɗani bane,
ta6e bakin shi yayi yana kallonta sannan yaci gaba da cewa"wannan allurar da na baki, miyagu irina suke amfani da ita, aduk lokacin da mutun yayiwa kanshi allurar nan, imanin shi gaba ɗaya take cire wa, zai iya yi ma mata sama da goma sha biyar raping a lokaci guda batare da ya gaji ba tamkar engine zai dinga aiki, sannan koda ace mahaifiyarshi ce akusa dashi itama hakan ce zata faru da ita ba zai iya tantance fari ba balle baƙi, saboda gaba ɗaya take tayarwa mutun da wata irin jarababbiyar shawa'a da kuma ƙarfi na ban mamaki, kuma muddin a lokacin bai samu ya kawar da sha'awarnan ba, to fa zuciyarshi zata iya bugawa nan take,.......'
tunda ya soma bayani sehrish ke kallon shi cikin tsananin tashin hankali har sai da yakai ƙarshe sannan cikin sanyin murya tace"me yasa ka fita daban acikinsu ne? Saboda me kake son cutar da shi ne? idan ni nayi maka laifi saboda me laifin zai shafe shi?
shu'umin murmushi haroon ya saki kafin yace"tun ina yaro nake da son yin mugunta, ni ko dariya ban cika yi ba sai in anyi abun mugunta sannan take zuwa mun, burina kawai naga kowa cikin masifa da tashin hankali,natsani inga ana ta rayuwar farin ciki mai ɗaurewa, wannan ne dalilin dayasa nakeson in kawo canji acikin gidan nan,". Hankali kwance haroon ke kora mata bayani batare da nuna alamun wasa ba,
tuni taji idonta sun ciko da kwalla cike da takaici tace "tausayinka nake ji ! kana bani tausayi saboda kai abun tausayi ne, ban ta6a tunanin cewa a jinin abba za'a samu mai irin waɗannan mugayen ɗabi'un da halayen irin naka ba, saboda me yasa kai ba zaka yi koyi da sauran ba? ka zama mutumin kirki tamkar sauran"?
tasowa haroon yayi daga zaunen da yake ya ƙarasa dab da inda take a wannan karan fuskarshi babu wasa acikinta yace"kina so in shiryu ne? In zama mutumin kirki?
ɗaga mashi kai tayi alamar eh,
Murmushi haroon yayi kafin yace"kece mutun ta biyu, da kikayi mun fatan shiriya arayuwata, sai dae kash hakan bazai ta6a yiyuwa ba sehrish ni ba cikakken mutun bane kamar yarda kike tunanin....................' a wani irin firgice sehrish ta ɗago tana kallon cikin idanunshi fuskarta cike da tsoro tace"kana nufin kai ba mutun bane"?
dariya ya ɗanyi kafin yace"kona faɗa maki ba zaki yarda ba, amma bari na sanar dake wani abu da baki sani ba, ni da kaina na turo marshal Omar ɗakin sgr domin ya taimake ki ! kuma ni ne nan na hana ki furta sunana agaban Omar, na shaƙe maki maƙoshinki na hana sautin fita daga bakin ki, shin bakiyi mamakin taya akai duk nasan da wannan ba !!!!!!!!!!!
Zazzare ido sehrish tayi gabanta na faɗuwa, tuni zufa ta soma tsattsafo mata, ja da baya da baya tadinga yi tana kallon shi.....
dariya sosai haroon yayi kafin yace"Shiyasa nace ki nemi tsari daga sharrina wlh ni shaiɗanin aljani ne ba mutun ba..........'
tunkan ya ƙarasa maganar tashi Da gudun gaske sehrish ta juya tare da buɗe ƙopar ɗakin nashi ta fuce ji kake garam !!!! Ƙopar ta datse,
Fashewa da dariya haroon yayi hada dafe cikin shi, daga bisani kuma ya ɗan tsagaita da dariya tare da cewa "Yarinyar tana da kyau, shiyasa na tsoratar da ita saboda inga kyawawan idanuwan nan nata masu kashe mun zuciya," ya furta tare da kai hannun shi saitin zuciyarshi yana faman sakin murmushi...............😳 tashin hankali anya kuwa haroon 👹😈
Ko kallon gabanta ba tayi saboda gudun da take yi gaba ɗaya ta gama firgita da haroon, bata yi wani aune ba ta faɗama junaid wanda ya nufo part din nasu, aikuwa gaba ɗaya suka faɗa ƙasa a manne da juna, atare zuciyoyinsu ke bugawa, musamman sehrish yana jin yarda zuciyarta ke faman bugawa da ƙarfi da ƙarfi, sun jima a haka kusan 8 mins sannan junaid ya ambaci sunanta "Sehrish,"
lamo tayi a jikinshi tana faman sauke ajiyar zuciya sai da ta samu natsuwa sosai sannan ta ɗago daga jikinshi,tayi gefe guda zaune dirshan tana kallon shi, tasowa yayi daga kwancen da yake yana faman sakar mata murmushi, tun safe yakeson ganin ta amma basu haɗu ba sai yanzu, shima zama yayi suna fuskantar juna da ita, wankan jeans da t shirt red colour ne ajikinshi, sai faman ƙamshi yake yi,
"Me ya faru ne naga kina ta tiƙar gudu kodai motsa jiki kike yi ne? ae muna da wurin gym acikin gidan nan,'
Ya faɗi yana kallonta, tayi mashi zuru da ido,
Ganin bata da niyar yin magana yasa shi cewa "Labari mai daɗi "! cike da zumuɗi tace "dagaske ? Wani irin labari ne wannan,
"Mafarki nayi jiya,"
"Me ya faru acikin mafarkin"? ta tambaye shi cike da son ji,
gyara murya yayi tare da cewa" mafarki nayi da wani narkeken zaki acikin wani ƙurmin daji ya biyo ki da gudun gaske, kamar zaki tashi sama haka kika dinga gudu kina ihu, kinsan waye ya cece ki a wannan lokacin"? Ya jefa mata tambaya, hankali tashe tace "A'a," ƴar hararar ta yayi tare da cewa"Ni ne nan, nazo da suffar jemage na ɗauke ki da fika fiki na mukayi sama can cikin gajimare...........' ganin yarda sehrish ta fashe da dariya yasa shi dakatawa da labarin yana kallonta, nuna shi tayi ta yatsa tana cewa"junaid kaji tsoran Allah, jemage fa kace? taya jemage zai iya ɗaukar mutun ? sannu malam fesal ka feso mun ƙarya,
gaba ɗaya suka sanya dariya, ba ƙaramin nishaɗi junaid ya sanyata ba duk da fargabar da take ciki, sun jima a zaune ƙasa suna fira, kafin daga bisa ni suka tashi, shi ya wuce mosque ita kuma ta wuce bedroom ɗinta saboda tayi sallar itama,``The father Of Soldiers```
Story & Written
By
Hafsat Bature
**********
zaune take agaban mirror ta kammala shiryawa cikin doguwar rigar material blue colour mai kyan gaske, rigar tabi shape ɗin jikinta daga can ƙasa yayi ƴar baza tamkar mermaid haka shape ɗin ya bada,hoda ta ɗauka tana shafa ma fuskarta, bayan tagama ta ɗauki jan baki red colour ta murza, ba ƙaramin kyau tayi ba, set na brushes ɗinta ta ɗauko ta gyara eye brows ɗinta,bayan ta kammala gyara gashin giran, ta ɗauki ribbom ɗinta data ajiye saman mirror ɗin, tattara sumar kanta tayi tana kiciniyar ɗaure gashin amma sam tagaza saboda yawan da yayi,ita kanta tayi mamamkin yarda gashinta yake toho,ba ƙaramin tsayi yayi ba ga yawan gaske dami guda dashi,bakomai ya jawo hakan ba face mayukan da take amfani dasu na gyaran gashi sun amshi kanta sosai,
Sakin gashin tayi ya tarwatse a bayanta,saboda gajiyar da tayi da ruƙon shi,hannu takai cikin jerin perfumes dinta ta dauki kwalbar turaren flower bomb wanda junaid ya ɗaukar mata a lokacin da suka je siyayya saboda shima yana da irin shi, shiyasa ya haɗa mata dashi don suyi anko, feshe jikinta tayi da turaren ko'ina ya ji, nan take daddaɗan ƙamshinsa ya gaure ko'ina na ɗakin gaba ɗaya,mayar da kawalbar turaren tayi bayan ta kammala fesa wa, sannan ta zuba ma madubin ido tana kallon fuskarta,fuskar sgr ta dinga gani acikin mirror ɗin,nan take ta tuna lokacin da ta watsa a guje zata bar ɗakin ya biyota da gudun gaske tare da ruƙota a jikinshi,tafin hannunta tasa tare da rufe fuskarta tana faman sakin murmushi,sake tunawa tayi da lokacin da ya yage rigar jikinta kai tsaye ya afka mata,nan take taji wani irin sanyi da kasala sun rufar mata,gaba ɗaya fa sehrish ta shiga yanayi cike da shauƙi take tariyo duk wani abu da ya faru da ita a daren jiyan ta shagala sosai, taji knocking daga waje, muryarta cike da kasala tace"Wanene"?
.muryar Azmee tajiyo tana cewa"Auntynki ce," jin hakan yasa sehrish tashi tare da ƙarasawa ta buɗe mata ƙopar,tana a tsaye jikinta sanye da jallabiya ta mata maroon colour, ta yafa mayafi akanta ba ƙaramin kyau tayi ba,
sakin baki tayi tana kallon Sehrish kafin tace"Masha Allah, irin wannan kyau haka? sai kace sabuwar amarya,kinyi kyau sosai,"murmushi kawai sehrish ke saki,
matsa mata hanya tayi tare da cewa"Aunty azmee ki shigo daga ciki mana,"
"A'a basai nashigo ba, dama nazo naji ya kuka ƙare da Omar?ina fata kin sanar dashi gaskiya?
shiru sehrish tayi tana tunanin amsar da zata bata,ranta ne ya bata cewa kawai ta amsa mata da eh,saboda tana da tabbacin cewa muddin ta faɗa mata cewa takasa furta sunan haroon agaban Omar to tabbas azmeen zata iya cewa zata sanar dashi ita da kanta,idan kuma hakan ya faru to tabbas itama azmeen zata fuskanci irin abunda sehrish ta fuskanta wurin Furta sunan Haroon,kuma bazata so hakan ya faru ba don ba ƙaramin raɗaɗi taji ba,.
Sam ta tafi duniyar tunani taji muryar azmee ta katsa ta da cewa"Lafiya kuwa naji kinyi shiru baki ban amsa ba"?.
cikin sauri sehrish tace"aunty azmee na sanar dashi gaskiya kuma yace zaiyi bincike akan haroon ɗin,"
"Kin tabbata"? ɗaga kai sehrish tari alamar eh,
Jinjina kai azmee tayi tare da cewa"kayan sunyi maki kyau sosai Allah," murmushi sehrish tayi tana sunnar dakai,
Azmee ta kuma cewa"Munyi magana da junaid akan kayan nan naki da aka kai ɗinki,yace mun tailor din ya kammala ɗinki shi zaije ya amso maki kayan," cike da farin ciki sehrish tace"ngde sosoe aunty azmee na,"
�?
Murmushi azmee tayi tare da kai hannu taja kumatunta tace"bani zaki godemawa ba, ko kin manta waɗanda suka bada kuɗi akayi maki siyayyar ne"?
girgiza kai sehrish tayi tare da cewa"a'a ban manta ba,amma ina jin kunyar zuwa inyi masu godiya,"
"Gaskiya yakamata kije kam,zasu ji daɗi sosai su son cewa kinji daɗin abunda sukayi maki,ki same su kiyi masu godiya,"
"Insha Allah zanje," ta amsa mata, sakin kumatun nata tayi sannan ta juya zata futa, har ta ruƙe ƙopar zata buɗe ta jinkirta kamar mai tunanin wani abu, sake juyowa tayi tare da kallon Sehrish dake a tsaye tace"wai nikam akwai abunda nake taso in tambayeki tuntuni sai in ta mantawa,"
cike da kulawa sehrish take kallonta don jin me zata ce,
Cigaba da cewa tayi "a kwanakin baya kinyimun magana akan cewa kinason zuwa garinku domin ki duba ƴan uwanki da basa lafiya ko"? ta tambaya tana kallonta,
A ruɗe sehrish tace"ƴan uwana kuma aunty azmee? Su wa kenan ? ni ba muyi wannan maganar ba kodai kin manta ne"?
hararar wasa azmee tayi mata tare da cewa"banason wasa fa, kinsan me nake magana akai mana, nan kwanaki kikazomin kina kuka kina cewa in taimaka maki kije kiga ƴan uwanki shine kuma yanzu zaki ce mun har kin manta?
Hankali tashe sehrish tace"aunty azmee ni bani da wasu ƴan uwa, bani da kowa wlh, bansan akan me kike magana ba,"
mamaki ne ya kama azmee ganin yarda sehrish ta haƙiƙance akan cewa bata da wasu ƴan uwa kuma fuskarta babu alamun zolaya,bayan ita da kanta ta sanar da ita game dasu,
ɗaure mata fuska tayi tare da cewa"banason rainin hankali sehrish!kina nufin dama baki da wasu ƴan uwa!ƙarya ce kawai kika shirga mun?tun farkon zuwanki gidan nan aiki, kika sanar dani cewa ƴan uwanki ne basu da lafiya shiyasa kikazo neman kuɗin da za'ayi masu aiki, har na ranta maki kuɗi dubu ɗari tara domin ayi masu aiki a amatsayin kuɗin aikin ki na shekara ɗaya da rabi, shima wannan duk plan ne kika tsara mun !!!!? Rai a6ace azmee ke magana hakan ba ƙaramin ɗaga mata hankali yayi ba, tuni idonta suka soma zubar da hawaye saboda tagaza gane kan me azmeen ke magana akai,.
�?
"Aunty azmee wlh ni duk bansan anyi wannan ba! Bamu ta6a magana dake akan cewa ina da wasu ƴan uwa ba,kuma ni ban amshi wasu kuɗi ba saboda ayi