Showing 219001 words to 222000 words out of 432432 words
Chapter 74 - Abban Sojoji Book 2 Hausa Novel Complete
hukunci daga wurinshi,'
Hankali tashe hayaam ta miƙe tsaye tana kallon Azmee tamkar za tayi kuka tace"don Allah aunty azmee ki taimaka mun,wlh banso in bar gidan nan!na saba da zama acikinshi,anan nake samun duk wani jin daɗin da nakeso,acan gidanmu duk babu waɗannan kayayyakin more rayuwar,nasan zaki taimaka mun,"
Dariya azmee tayi tana kallonta ko yaushe tazo da har zata ce tayi sabo da mutanen gidan ta ayyana a ranta,
"Aunty azmee dan Allah ki taimaka mun,in xauna acikin gidan nan,nasan yana jin maganarki,ki roƙa mun shi akan yabar ni in cigaba da zama,wlh bazan ƙara shiga shirgin kowa ba,zanyi rayuwata cikin salama,"
Azmee tace"Tabɗijancan!so kike kija mun bala'e ko?ina zaman lafiyata agidan nan,Wacece ni?da har kike tunanin Sgr zaiji maganata?kin manta matsayina ne acikin gidan nan?kefa kike da alaƙa dasu ko kin manta ne"? Da biyu azmee tayi mata maganar saboda wulaƙancin da hayaam tayi mata,
Magiya hayaam ta shiga yi mata tana roƙonta akan ta nema mata mafita tamkar zata zuƙunna mata saman guiwarta,don ita sam bata shirya barin gidan yanzu ba,tabb yo mima akai kenan"ta fada cikin ranta.
Sosai abun yaba azmee dariya,
"Hanya ɗaya ce hayaam in zaki iya!idan har kinason cigaba da zama acikin gidan nan"!
jiki na rawa hayaam tace"Ina sauraronki aunty azmee,wlh koma manene zan iya ni,"
Azmee taci gaba da cewa"daga yau zaki dinga yin shigar maza,kinasa gashin baki kamar yadda sehrish tayi a lokacin da tafara aiki acikin gidan nan kinga sai kizama kamar sabon mai tayani aiki"
Waro ido waje Hayaam tayi tare da cewa"Haba Aunty azmee ni zanyi shigar maza?so kike na ƙasƙantar da kaina har yarinyar can ta raina ni"
Azmee tace"that's the only solution,if not sai dae fa ki tattara kayanki ki bar gidan nan!"ta karasa maganar tana jiran jin ta bakin hayaam din don tasan da kyar zata amince dama shiyasa ta fadi mata hakan,
gyaɗa kai hayaam tayi tace"shikenan zanyi tunani in ga in zan iya,kafin nan zanci gaba da 6oye ma ganinshi"
Azmee tace"to shikenan kiyi yadda kika ga yafi maki,ni dai gaskiya ba ruwana,kuma fa dole ki rika futowa kina taya ni aiki,indai kina a cikin gidan nan, don bazai yiwu ba ki zaune a daki baki komae gaskia "
Hannu hayaam ta aza akanta tana faɗin"Nashiga uku!
dariya Azmee tayi kafin ta kuma cewa"hayaam zamanki fa bazaiyiyu acikin gidan nan ba,Sgr ya riga da ya kore ki!muddin ya sake ganin fuskarki dole ya hukuntaki,kuma kinga gwaggonsu ta katsina tazo,!matar nan bazata ta6a bari ki zauna acikin gidan nan ba,in har taji cewa ke ƙanwar matar yayyansu ce,nan zaki ga tashin hankali,sae ta kunyataki acikin jama'a,shiyasa nace kiyi shigar maza kawai,Ni zan taimaka maki muna yin aiki atare inyaso duk wanda ya tambayeni xance mashi abokin aiki ne na samo,nasan babu wanda zai zargi wani abu,
Komawa hayaam tayi ta zauna gefen gadon cike da damuwa,gaba ɗaya taji ta tsani kanta,da tana zaman lafiyarta acikin gidan,kwaɗayinta da zalamarta su suka ja mata,gashi ita gskia bata jin zata iya yin wani shigar maza wannan ai kaskanci ne,
"Na manta ban sanar maki ba!"
Rai a6ace hayaam tace"Menene!"
Azmee tace"SEHRISH TAGA ƳAN UWANTA,ASHE ƳAN UKUNE SU,YANZU HAKA SUNA ACIKIN GIDAN NAN!BAKI GANSU BA,ABUN FARIN CIKI KAMANNINSU IRI ƊAYA SAK!BAKI TA6A BANBANTA SU,"
A razane Hayaam ta miƙe tsaye hannunta dafe da saitin zuciyarta tace"WAI DAGASKE AUNTY AZMEE?
AZMEE TACE"Zan maki ƙarya ne?yaran suna nan,kyawawan gaske,HOSANA DA JAHAD!!!!!"
Jiki amace hayaam ta koma ta zauna,gabanta na faɗuwa rasss rasss!tama rasa ina zata tsoma ranta taji dadi,
Murmushi azmee ta saki tare da juyawa ta kama hanyar fita daga ɗakin,buɗe kopar tayi tare da sa kai ta fuce,
Kamar jira take azmee ta fita,nan fa ta fashe da kuka kamar ranta zai fita,saboda tsabar 6acin rai,wani irin ƙululun baƙin ciki ne taji ya tokare mata maƙoshinta,komae ya jagule mata,tabbas tana bukatar tayi magana da Aunty laila,lokaci guda yadda sukai da yaya babbar ya shiga dawo mata, sambatu tashiga yi tana bugun bed mattress kamar wata zautacciya,
Bayan kammala sallar isha'e,atare suka dawo cikin gidan,a babban falon suka kuma zama kamar ɗazu dae,
Gyaran murya Abbansu yayi kafin yace"Ina yaran suke ne?wani yaje ya kira mana su,domin jin ta bakinsu"
Miƙewa fawan yayi kamar dama jira yake yi,wucewa ɗakin sehrish yayi bayan ya isa ya kwankwasa masu ƙopa,jahad ce ta buɗe mashi kopar jikinta na sanye da hijabi da alama bata jima da kammala salla ba,
Fuskarshi ɗauke da murmushi yace"Abba nason ganinku,idan ba damuwa ku fito mu tafi atare,"
Jahad tace"Toh,bari na kirasu,"ta fadi hakan tare da juyawa ciki ta kira hosana da sehrish wadda har lokacin bata motsaba,tana nan saman gadon ta ƙanƙame jikinta,
"Hosana kuzo Abbansu na son ganinmu!hada sehrish kema ki taso,"
Maƙe kafaɗa sehrish tayi alamar bazata taso ba,
"Sehrish dan Allah kidaina abunda kikeyi,nasan duk don saboda ganinmu ne,idan har baki so zuwanmu ba zamu bar gidan nan,"acewar jahad,
ɗaure fuska Sehrish tayi tare da kawar da fuskarta gefe tana faman hura hanci,
babu yadda basuyi ba akan sehrish tabiyo su amma taƙi binsu,har fawan sae da ya leko yayi mata magana amma ko kallo ma bai isheta ba,
A ƙarshe suka ƙyaleta,suka bi bayan fawan ya shiga babban falon tare dasu,
gaba daya hankalin kowa ya dawo kansu,musamman Abusufyan dake zaune agefen abbansu,ji yake kamar ya tashi ya rungumosu ajikinsa,su twins kuwa dasu irfan zuba masu ido kawai sukayi suna kallonsu,haka Omar da Abbas da kuma hajiya azeema,kowa burinshi yaran su tabbata ƴa'ƴan abusufyan ne,duk sun ƙagu suji cewa yaransa ne,tabbas da ba ƙaramin farin ciki zasu ji ba,
Sgr dae tunda ya ɗago ya kallesu ya gane cewa babu sehrish acikinsu,bayan yaji cewar dukansu Abbansu yace a kira mashi,
Abbansu ne yace"Ina ɗayar take ne?ni bana gane ma wacece babu acikin ku!
Omar yace"waɗannan hosana da jahad ne!sehrish ce babu acikinsu,"
Abbas yace"Masha Allah,gaskiya banta6a ganin yara masu kamanni irin nasu ba,Allah dae yasa mu tabbatar da abunda muke hasashe akansu....'
"Meya hanata zuwa"?muryar Sgr ce ta karaɗe kunnuwansu,har sae da su jahad suka ɗan tsorata dashi,dama tunda sukazo hankalinsu ke kanshi saboda launin kwayar idonshi ba ƙaramin ɗaukar hankali takeyi ba,
Fawan yace"Ba yadda bamu yi da ita ba,amma tace bazata zo ba,kamar tana cikin damuwa sosai,ko kallona fa batayi ba,da naje kiransu,'
A zafafe Sgr ya yunkura tare da miƙewa daga saman kujerar da yake ya nufi sashensu Azmee,
"Kuzo ku xauna kusa dani,"hajiya azeema ce tayi masu magana yayin da takeyi masu nuni da hannunta,
Hannunsu ruƙe cikin na juna,suka ƙarasa wurin sofa ɗin da hajiya azeema take,a gefenta suka zauna,duk jikinsu asanyaye saboda basu saba dasu ba,tunda suka zauna jahad ke kallon Abusufyan,saboda tunawa da maganar gwaggon katsina da tayi ɗazu na cewa shine mahaifinsu,kanta ya gama ɗaurewa,tashiga tambayar kanta taya akai hakan zata kasance?meke shirin faruwa da rayuwarsu ne?dama suna da dangi ne?wai su wanene su?ya akai rayuwarsu take a birkice ne?
tambayoyi iri iri tashiga yi ma kanta waɗanda bata da amsar su,
ƙasa ƙasa hosana tayi da muryarta tare da kai bakinta saitin kunnan jahad tace"Wancan mutumin sai kallonmu yake yi jahad,ni duk nabi na tsargu wlh,tsoranshi nake ji,shi da wannan kyakkyawan mai wasu kalar kwayar idanu kaman aljani....'
"Dan Allah hosana ki daina mun magana a kunne na,wai ke bakya ganin mutanene kuma duk idanunsu na akanmu,ni kaina atsorace nake wlh,yaya Omar kaɗae nake kallo naji dan sauki,da ace baya a wurin nan da tuni na gudu...'jahad ce tayi wannan maganar,cikin raɗa tayi mata ita don kar aji su,
A lokacin da Sgr ya ƙarasa bedroom dinta,tura ƙopar yayi tare da faɗawa ciki,tsayawa yayi yana kallonta,ta takure kanta,jikinta sae kerma yakeyi yayin da hawaye ke saukowa daga cikin idanunta,sam bata lura dashi ba har sae da yayi gyaran murya,a firgice ta wurga idanunta akan fuskarshi,gabanta ne taji ya faɗi rass,nan take kermar jikinta ya ƙaru sosai,
"Taso muje"!babu wasa a fuskarshi yayi maganar,girgiza mashi kai tashiga yi tana cewa"bazan iya tafiya ba,ƙafafuna ciwo suke yi mun,dan Allah kuyi haƙuri ku ƙyaleni,inji da abunda ke damu na,'
Abun ya ɗaure mashi kai,yadda take yi mashi jayayya,tabbas akwai matsala hakanan dae yarinyar bazata ƙi bin umarninshi ba,
Bai tsaya wani 6ata lokaci ba,ya ƙarasa shiga cikin ɗakin har saman gadonta ya bita,sai faman ja da baya takeyi,gaba daya ya ɗaukota tare da azata asaman kafaɗarshi ya fito da ita,sai kuka takeyi mashi tana cewa ya sauketa ita bazata je ba,su rabu da rayuwarta,suna ƙuntata mata,har bugun bayanshi ta dinga yi da hannayenta don ya sauketa,duk yana jinta,
tashin hankalin da ba'a sama shi date!
"Ga babban yaya nan ɗauke da sehrish din daman nasan sai dae ya ɗaukota,"acewar fawan,jin sautin kukanta yasa kowa yakai hankalinshi wurinsu,abun ba ƙaramin ɗaure masu kai yayi ba,ƙiri-ƙiri tana gudun ƴan uwanta,bayan duk alamu sun nuna cewa su ɗin fa ƴan ukune,
Koda Sgr ya ƙaraso wurinsu, a tsakiyar inda kowannansu yake,sai ya sauko da ita,Kamar dama jira takeyi ya sauke ta ƙasa da gudu ta kama hanya zata bar wurin,aikuwa a zafafe ya damƙo waist ɗinta da ƙarfi ya maido ta jikinshi,
Har Abbanshi na cewa"ka bi ta a hankali don Allah,ta tsorata sosai,bansan meke damunta bane, ko ƴan uwan nata ne ke batasan gani "abusufyan kuwa runtse idanunshi yayi,har cikin ranshi yake jin soyayyar yaran,
Cikin shessheƙar kuka take faɗin"Na bani,na shiga uku!Na lalace!dan Allah ku rabu dani!ku barni na tafi, banason ganinsu!ni ba ƴan uwana bane!ciwon kai suke sani idan ina kallonsu,raɗaɗi nake ji acikin zuciyata kamar ana ƙonata...."
Hankalinsu ba ƙaramin tashi yayi ba jin abunda sehrish ke cewa,yanayin yadda take maganar zai tabbatar maka da cewar da gaske take tana jin duk wani abu da ta faɗi,musamman Sgr daya ruƙota,yaji jikinta da wani irin Zafi,har shi kanshi zafin na shafar jikinshi,
Abusufyan ne yace"kuyi mata addu'a don Allah,zai iya yiyuwa akwai sihiri ajikinta,wani zai iya shiga tsakaninta da ƴan uwanta saboda ni shaidane akan yadda suke son junansu!nagani da idona,basa rabuwa da junansu kullum suna manne da juna,banta6a ganin ƴan uwa masu son junansu ba irin yaran nan,tun kafin su mallaki hankalinsu suke tsananin son junansu.....'
Cike da mamaki Abba yace"meyasa kake tunanin cewa akwai sihiri ajikinta?
kowa ya kasa kunne yana sauraronshi,
"In har da gaske sune ƴa'ƴana kamar yadda nake hasashe to tabbas an shiga tsakaninsu ne,saboda mutumin da suka taso awurinshi,nayi bincike akanshi,bama haka ba shi da kanshi ya rabani da bibiyar rayuwarsu da nake yi,kowa zaiyi mamakin taya nabar yaran rayuwarsu ta wulaƙanta batare dana taimaka ma rayuwarsu ba,ko kuma na sanar ma wani daga cikin dangina don a taimaki rayuwarsu,ba laifina bane tursasamun akayi........'
Kasa ƙarasa maganar yayi saboda hawayen da suka shiga kwaranyowa daga cikin idanunshi,
Abbas yace"Akwai sauran labari kenan, bari mu gyara zama don a idasa warware mana komai,"
ɗagowa yayi da idanunshi da suka yi jawur har sun dan fara kumbura ya kalli sgr tare da cewa"idan ba damuwa,inaso ka zauna tare da ita akusa dakai,saboda ka ruƙeta karta gudu,in yaso sai kayi mata addu'ar koda bata dawo hayyacinta ba,zataji sauƙin radaɗin ciwon kan da takeyi,
"Okey,"ya amsa tare da samun wuri ya xauna,asaman laps ɗinshi ya zaunar da Sehrish,sosai ya ruƙota jikinshi,tunda ta kwantar da kanta asaman wide chest ɗinshi,numfashinta ya fara daidaita,a hankali kuma zafin jikinta ya soma raguwa,saitin kunnanta yakai ƙaramin bakinshi yana karanta mata addu'o'i,bugun zuciyarta ne ya soma raguwa,jikinta kuma ya rage kermar nan da yake yi,
"Ina gwaggon take ne?naga bata fito ba inaso ayi komai agabanta tare da Dr haris kuma"abusufyan ne yayi maganar yana kallon Abban nasu
Fawan ne ya kuma miƙewa tare da cewa"Bari naje na kirasu,'
cike da zolaya jahan yace"Messenger,aikinka na kyau,"murmushi kawai yayi tare da wucewa ciki,ae yau ji yake kamar ya zuba ruwa ƙasa yasha don murna don kuwa ranshi ya gama bashi cewa su jahad din yan'uwansu ne.
Ba da jimawa ba,sae ga Gwaggon katsina ta fito har yanzu undin nan ne ajikinta Allah ma yasa irin dogon nan ne mai kauri,tana biye da bayan fawan tana dungurin keyarshi tana cewa"Shegen bisa,da kanshi kamar na tamola,baccin ma baza abar mutun yayi ba,matsalar mutun yazo gidan jikoki kenan duk subi su addabi rayuwarshi.....'
Muryar Abba ce ta katse ta da cewa"gwaggo ku samu wuri ku zauna,magana ce mai muhimmanci zamuyi,"
Har zata zauna idonta suka sauka karaf akan Sehrish dake zaune asaman laps ɗin Sgr,hankali tashe tace"mun shiga uku!yanzu agabanku ake wannan aika-aikar amma babu wanda ya tanka?hosana ce ko jahad?wacece acikinsu?wlh bazan bari a lalatamun ƴa'ƴan Abusufyan ɗina ba,dasu zamu koma katsina ayau.......'
..da sauri Haris ya katseta da cewa"Dan Allah gwaggo kidaina wannan sambatun naki,bakiji abunda abba yace ba!magana mai mahimmanci za'ayi,ki samu wuri ki zauna kuma kiyi shiru,'
Wurga mashi harara tayi kafin ta wuce tare da samun wuri ta zauna,shima haris ya zauna agefenta,sai da suka xauna sannan ta lura da hosana da jahad dake zaune gefen hajiya azeema,
Da sauri ta mayar da idonta kan sehrish don taga wacece ita,ko dae idanunta ne suka fara samun matsala don taga kamar kamanninsu iri ɗaya sak,
"Harisu,kana ganin abunda nake gani kuwa,wai yaran nan har nawa ne masu fuska iri ɗaya"?
A dan ƙule haris yace"Eh,su uku ne!ko kinmanta su nawa ne,na faɗa maku Abu ta haifa!wannan ae cikon ƴar ukun tasu ce,'
"Oh to,yanzu nagane"ta fadi tana faman gyara zamanta,
Sae da kowa ya natsu sannan abusufyan ya kalli su hosana da jahad yace"Ya sunan mahaifiyarku ne?kuma waye mahaifinku"? Yayi masu tambayar ne don ya fara tabbatar da cewar sune ɗin dai dagaske,
Har suna haɗa baki wurin cewa"Sunanta Zainab,amma anace mata abu ƴar buzuwa,sannan mahaifinmu kuma sunanshi Sayyadi.......'tunkan taƙarasa maganar kowanne daga cikinsu ya shiga sakin murmushi,jin sun ambaci dai dai da sunayen da abusufyan ya gama bada labari akansu,tunkan aje ko ina suka tabbatar da cewar sune dae ƴa'ƴan abusufyan ɗinsu,
"Ina mahaifiyarku take yanzu"?ya kuma tambayarsu,
Jahad tace"bamu son inda take ba,amma koma a ina take bata acikin hayyacinta,lokacin da tabarmu tasamu ta6in hankali,'
jiki asanyaye ta ƙarasa maganar,
"Yanzu zaki iya bamu labarin abubuwan da suka faru arayuwarku gaba daya,har izuwa lokacin da kuka rabu da junanku"?
ɗaga mashi kai tayi alamar eh,
Kafin abusufyan ya ƙara cewa wani abu,Abba ya katse mashi hanzarinshi da cewa"Yakamata,ka fara sanar dasu game da alaƙar da take tsakaninka da mahaifiyarsu"
Jinjina kai abusufyan yayi kafin yace"zaku iya tunawa da mutumin daya ta6a zuwa wurinku lokacin kuna ƴan ƙanana,har ya ɗauke ku hoto a wayarshi?lokacin da zan tafi kuka dinga kuka kuna cewa na tafi daku baku son zama da mahaifinku"?
A razane hosana da jahad suke kallonshi yayin da suke ƙoƙarin tunawa da wannan lokacin......'
Murmushi abusufyan yayi tare da cewa"nasan ba zaku iya tunawa da wannan lokacin ba!,amma mun sha haɗuwa daku wani lokacin kuna ku kadae,wani lokacin kuma tare da mahaifiyarku........'
Batare da 6ata lokaci ba,abusufyan ya basu labarin rayuwarshi da abu a takaice yadda zasu fahimta,sai lokacin suka san asalin mahaifinsu da kuma kakansu baba buzu daya rasu,da kuma irin rayuwar da abu tayi tare da abusufyan kafin su rabu,ta auri ya sayyadi,sunsha kuka sosai,aransu suna jin ƙuncin abunda mahaifiyarsu tayi masu,ashe duk itace taja masu bala'en da suka fuskanta,
Kowa yayi shiru na wani lokaci suna sauraron kukan dasu hosana da jahad sukeyi gwanin ban tausai,banda sehrish wanda tayi lamo ajikin Sgr,duk wani abu da suke faɗi acikin kunnanta,amma bata ɗago ta kallesu ba,har yanzu dae bata dawo dai dai ba,
Daƙyar su Omar suka lallashe su,kafin daga bisani Abbansu yace"Jahad yanzu ke muke sauraro!munaso muji irin rayuwar da kukayi a hannun mutumin nan!"
Duk wannan abun dake faruwa akan kunnan Haroon,ya jima da shigowa batare da sanin kowa ba ya la6e yana jin labarin da abusufyan ke ba su jahad,na rayuwarshi da mahaifiyarsu,hankalin shi yayi mugun tashi,gaba ɗaya ya tsorata ya rikice,wata irin zufa ce tashiga gangarowa a fuskarshi,bakomai ya razanar dashi ba face ganin Ƴan ukun gaba ɗayansu sun haɗu acikin gidan kuma ga Ubansu da kanshi ya gane cewa ƴa'ƴanshi ne wannan alama ce dake nuna cewar asirinsu ya kusa tonuwa,
Tuni zufa tasoma tsastsafo mashi acikin jikinshi,sharkaf ta jiƙa t shirt ɗin jikinshi duk kuwa da ba zafi,jan ƙafarshi yayi tare da lalla6awa cikin sanɗa ya wuce bedroom ɗinshi,
Zagaye ya shiga yi acikin ɗakin,gaba ɗaya jikinshi sae faman rawa yakeyi,yama rasa inda zai tsoma kanshi kamar wani zautacce haka ya koma,a fusace ya dunƙule hannunshi tare da kai ma madubin ɗakin naushi,nan take glass ɗin jikinshi ya tsastsage ya zube ƙasa,
Hannunshi ya shiga fitar da jini,ko kaɗan baiji xafin hakan ba,raɗaɗin da zuciyarshi ke yi mashi yafi raɗaɗin glass ɗin daya shige shi,
Da ƙarfi ya furta"That's impossible!ƙaryane ba gaske bane!!wlh bazan rasa rayuwata ba!dole na rayu ko da kowa zai rasa ranshi,zanyi komai zan yi don ganin na kwaci kaina!!
Yana magana yana sakin huci,idanuwan nan nashi sunyi jawur dasu luhu luhu,
Cikin sauri ya zura hannunshi tare da ciro wayarshi daga cikin aljihun jeans dinshi ya danna ma wata number kira,cikin sa'a aka ɗaga kiran!
Wata irin muryace ta karaɗe kunnanshi mai tsoratarwa"Ba saida nace maka karka sake kira na ba!Tun farko ya mukayi dakai?
hankali atashe haroon yace"Ni ba wannan maganar tasa na kira ka ba!ka faɗamun taya akai kukayi gangancin barin yaran nan har suka haɗu da danginsu!!!!!!!
"Wasu yara kenan!"
Haroon yace"Ƴan ukun nan!na gansu da idona acikin gidan nan!yanzu haka gasu can a falon gidan nan sun taru suna jin labarin rayuwar yaran nan!
Nan take muryar mutumin da suke waya dashi ta canza,
"Wai kana nufin hosana!jahad!sehrish!duk sun haɗu anan cikin gidan naku ko mi"?
A ƙule haroon yace"Eh mana!akansu nake magana,wlh kowa yayi ta kanshi!saboda yarinyar nan dole ta ambaci sunanka acikin labarin da zata bayar kuma kasan cewa muddin waɗannan namun dawan guda biyu sukaji mugayen abubuwan da kuka aikata dole su binciko ka duk inda ka shiga kuwa,kuma koda a ƙarƙashin ƙasa ka 6oye,!
Fashewa da dariya mutumin yayi kafin ya tsagaita