Showing 228001 words to 231000 words out of 432432 words
Chapter 77 - Abban Sojoji Book 2 Hausa Novel Complete
shigowa gidan don taga meke faruwa ne,anan ta samu abu a sume ruwa ta ɗebo ta yayyafa mata ta farka,miƙewa tayi zaune tare da sanya hannu ta dafe saitin zuciyarta tana ambaton Innalillahi wa'inna ilaihirraji'un!ya Allah ka ɗauki raina tun kafin baƙin cikin mutumin nan ya kashe ni,Sayyadi ka cuci rayuwata ka gama dani nashiga uku! Wayyo Allah na!
Tasha kuka kamar ta zauce,daƙyar maman sadeeq ta lallashe ta bayan ta tsagaita da yin kukan take tambayarta meya faru,bata 6oye mata komai ba ta kwashe ta sanar mata,a lokacin maman sadeeq har hawaye sai da ta zubar masu saboda tsabar tausayin yaran,ranar yini sukayi suna jimamin abunda ya faru atare kuma suka duba yaran don su tabbatar in bai lalata su ba,duk da sun tambayesu ko ya masu wani abu a wurin sunce a'a,bayan tafiyar maman sadeeq ta koma gida mijinta ta samu tayi mashi magana akan Yayi ma sayyadi magana akan abunda yake aikatawa saboda abun yayi yawa,yana cutar da rayuwar yaran, nan gaba zai iya lalata masu rayuwarsu gaba ɗaya har ma yayi silar Rasa ransu,
Jinjina kai Malam yayi tare da cewa"Hmmmm taya zan tunkari mutumin nan?me zan iya yi mashi?Mutumin da kana ja mashi aya yana fassarata!taya zai fahimci cewa badai dai yake aikatawa ba?bayan yasani kuma yake take sanin!Tabbas na tausaya ma rayuwarsu amma babu ta yadda zan iya taimakon rayuwarsu sae dae na bisu da addu'a kawai,Allah shine zaiyi maganinshi"shi kanshi Abban sadeeq sae da ya zubar masu da kwalla,ya tausaya ma rayuwar yaran,tabbas suna cikin masifa,
Bari in taƙaice maku labarin,sayyadi shine yayi sanadiyar ta6in hankalin hosana,a tsakar dare suna bacci ya ɗauketa batare da sanin kowa ba,ya kaita gidan wani Babban ɗan siyasa kamar yadda suka tsara dashi akan cewa zai kai mashi ita yayi amfani da ita don cin nasarar za6en shi,sam batasan ya ɗaukota ba sae dae kawai ta ganta asaman gadon mutumin,fasa ihu tayi da sauri ta diro daga saman gadon tana ƙanƙame jikinta,mutumin nan babu kunya babu tsoran Allah ya shiga tu6e kayan jikinshi agabanta,a tsorace tace mashi fitsari take ji,ya nuna mata hanyar toilet taje tayi fitsarin yana jiranta,
Jiki na rawa ta shige cikin toilet ɗin ta rufo ƙopar,Kunna fanfo tayi don kar yaji ƙarar abunda zatayi,zagaye tashiga yi acikin toilet din tana neman abunda zata fasa window ɗin kewayen,annan ƙasa ta samu wasu ƙarafuna masu ɗan tsayi kamar an ta6ayin gyaran wani abu a toilet ɗin aka ajesu nan,
Hannu tasa ta ɗauka jiki na rawa ta haye saman toilet seat ɗin dake a rufe,ta faffasa windown da sauri da sauri duk mutumin nan baijiyota ba,sai da ta fasa glass din ya tarwatse sannan ta biyo ta windown duk batayi tunanin cewa bayan yana da tsayi ba,kawai ta afka,gaba ɗaya ta bugi floor ɗin da ƙarfi kanta ya fashe,hancinta da bakinta duk suka bugu ga sauran kananun glass da suka yayyanketa ta,gigitacciyar ƙara ta saki saboda azabar da tasha,amma hakan bai hanata yunƙurawa ta miƙe da gudun gaske ta nufi hanyar fita daga gidan,mai gadin gidan na sallar dare ta samu ta fice da gudu ta karamar kopa tana kuka ta miƙi hanya gashi dare ne,
Acan kuwa tsakar dare Oummansu na bacci ta jiyo muryar jahad tana cewa"oumma ki tashi,hosana bata a gida fa,banganta ba,har kewaye na duba amma babu ita bansan ina taje ba,hankali atashe abu ta farka,a lokacin itama sehrish ta tashi,gaba daya suka shiga nemanta,duk sayyadi na ɗakinshi yana jiyo hayaniyarsu bai tanka masu ba,da suka duba ko ina basu ganta ba,anan fa hankalinsu ya ƙara tashi,fitowa sukayi suna bi gidaje suna tambayarta wasu a amsa masu da bata nan,wasu gidajenma ba mai zuwa balle ya basu amsa,kai tsaye suka miƙi hanya suna duddubawa ko wani mummunan abu ya faru da ita ne,lokacin da suka hau gefen titi suna tafiya........
Adai dai time ɗin Hosana ta shigo kan hanyar da gudu tana kuka hannunta dafe da kanta dake ta zubar da jini,tana ambaton oumma, oumma,
a gigice suka kai idanunsu wurinta,da gudun gaske suka tunkareta,abu na ƙoƙarin dakatar da ita akan ta kauce daga saman titin amma sam bata a cikin hayyacinta,wata mota ce ta bugeta da ƙarfin gaske gaba ɗaya ta kife ƙasa,mai motar na bugeta yaja motar da gudu yabar wurin alamar cewa da gangan ya bugeta,ashe ɗan siyasan nan ne yabiyo ta,bayan ya jima yana jiranta ta fito daga toilet bata fito ba,kawai ya afka ciki anan ya samu ta fasa glass ta gudu,yana huci ya fito ya mayar da kayanshi,ya bi bayanta cikin motarshi,don karta tona mashi asiri yasa yayi mata haka don ta mutu,
Zubewa sukayi agabanta suna ta kuka suna ta faman jijjigata a ƙarshe Abu ta sanya hannu ta ɗauketa,a ƙafa suka taka da sauri da sauri saboda babu abun hawa,gashi sae bleeding takeyi,suna cikin tafiyar nan sai ga Mijin maman sadeeq cikin napep,ashe tun lokacin da suka je gidan neman Hosana,bayan tafiyarsu ya gaza samun natsuwa shine ya biyo bayansu,napep ɗin ma bata shi bace arota yayi,saboda mashin ɗinshi babu mai,
Adai dai inda suke ya tsayar da abun hawan nashi,tunda yaga halin da hosana ke ciki bai tsaya tambayar ba'asi ba yace su shiga ciki,
A daren ranar suka kaita asibiti,likitoci suka shiga duba ta,tun nan aka sanar dasu cewa Sai anyi mata aiki,ana buƙatar kuɗi miliyan ɗaya da rabi,nan fa hankalinsu ya tashi,saboda ko sisi basu da ita,
Har washe garin ranar ana kan abu ɗaya,andai samu an fara treating ɗin raunukan jikin nata,aikin dai ne ya gagara,sun jima a asibitin nan ana neman taimakon kuɗin da za'ayi mata aiki amma ba'a samu ba,sayyadi ko leƙo asibitin baiyi ba,bayan shine silar komai don ubanshi,
Sanadin haukacewar mahaifiyarsu kuwa,lokacin anata neman yarda za'a harhaɗa kuɗin aikin hosanan,duk wani abu mai dan amfani tasa an sayar dama ba wasu abun kirki suka rage mata ba,don duk ta siyar da kayayyakinta wurin kula dasu Sehrish,a lokacin abu duk ta gama fita hayyacinta ta kode ta rame,duk da dae kyawunta na nan,amman inka ganta zaka yi tunanin ta girmi shekarunta saboda wahalar rayuwa,
ta yanke shawarar zuwa gidan ta duba taga idan sayyadi yana nan jin shiru bai neme su ba,ko labarin kwanciyar hosana asibiti baije mashi bane,
Tana sa ƙafarta tsakar gidan nanfa ta dinga jin wannan gurnanin abunda sukeyi mara daɗin ji,ranta yayi mugun 6aci,kitchen ta nufa ta ɗauko tukunya ta zubo ruwa a fanfo kusan rabin tukunyar mai fadi,bayan ta ɗaura ruwan sai da ta jira ruwan ya tafasa sosai yana huci sannan ta sauke shi,tsumma ta ɗauko ta ruƙo tukunyar dashi,ta nufi ɗakin nashi,cikin sa'a sun bar ƙopar a buɗe dama da yawan lokutta basa rufe ƙopa turo ta kawai sukeyi,
Faɗawa cikin ɗakin abu tayi,mutun shida ta samu kamar wasu mayu manne da juna,aikuwa tana ƙarasawa wurin gadon,ta ɗaga tukunyar gaba ɗaya ta maka masu ruwan zafin ajikinsu,wa'iyazubillah,agigice suka rabe da junasu,wata irin gigitacciyar ƙara suka shiga saki ta azabar radaɗin tafasasshen ruwan zafin nan da abu ta watsa musu,ihu suka dinga yi suna birgima,fatar jikinsu duk ta ɗame ta lalace,
Duk atunaninta hada sayyadi acikinsu ashe yana acikin toilet,razananniyar ƙarar daya jiyo daga cikin bedroom ɗinshi ne yasa shi fitowa daga cikin toilet din,Waro ido waje Sayyadi yayi tare da aza hannunshi akai yana ambaton"Innalillahi wa'inna ilaihirraji'un!Abu baki da hankali ne!!kinsan ko me kika aikata?
Idanunta jawur ta kalleshi rai amatuƙar 6ace tace"Na sani,kuma ina cikin hayyacina,wlh naso ace hada kai acikinsu na haɗa na ƙona,uban kowa ya huta da wannan masifar.....'
Bai bari ta ƙarasa maganar ba ya kifa mata mari zazzafan gaske har sae da gefen bakinta ya fashe,
Ɗagowa tayi da idanunta dake zubar da hawaye tace"Banji zafin marin da kayi mun ba!ada inajin shakkarka amma yanzu bana jin tsoranka acikin zuciyata,Wlh saina tona maku asiri duniya tasan me kuke aikatawa,daga nan in na fita gidan radio zanje in yaɗa duk wani mugun abunda kuke aikatawa,'
Wani irin huci ya shiga yi zufa na gangarowa daga jikinshi sae tsuma yake yi,hannu yakai tare da shaƙo wuyanta ya bugata jikin wardrobe ɗin dakin,
Sannan ya soma magana da wata irin murya mara daɗin ji yace"Ke daƙiƙiyace har yanzu bakisan ciwon kanki ba!kina tunanin cewa zan bari ki tona mun asiri ne!!kafin na juya maki tunaninki,inaso nasanar dake cewa Hosana jahad da sehrish ba ƴa'ƴa na bane!Da cikin abusufyan na aure ki!kuma nine na kashe mahaifinki baba buzu,saboda yana ƙoƙarin hanani auranki!'
Wasu irin hawaye ne masu zafin gaske suka shiga gangarowa a fuskarta,tsabar baƙin ciki da takaici yasa ta gaza magana,saboda wani irin ƙululun baƙin ciki daya tokare mata maƙoshinta,
ƴa'ƴan naki ma bazan barsu ba!ɗaya bayan ɗaya saina kashe su!'
Yana faɗin hakan ya saki wuyanta,da gudun gaske abu ta fito daga cikin ɗakin nashi tana kuka,a ƙopar gidan ta tsaya tana faman ambaton sunan baba buzu tana cewa babana ka kashe mun ka raba shi da ranshi,ka kashe mun babana ko,kuma zaka rabani da ƴa'ƴana suma ka kashe su ko......'haka ta dinga sambatu ita kaɗae,
Tun daga wannan lokacin abu ta haukace ta miƙi santa tana faman sambatu,
Wannan shine silar rabuwarsu da mahaifiyarsu basu ƙara sanin inda take ba,
Abunda kuma yayi silar komawarsu katsina,labarin neman da mahaifinsu yake yi masu don ya kashe su kamar yadda ya fada ma abu,ya isar masu maman sadeeq,ko aikin ba'ayi ma hosana ba,amma ta miƙe saidae babu hankali ko kaɗan,da taimakon Mijin maman sadeeq ya sanyasu a mota tare da damka ma direban amanarsu,bayan yasa anyi ma hosana allurar bacci ya bama Sehrish address ɗin gidan tsohuwar nan,wadda ta kasance kishiyar mahaifiyarshi ce anan suke zaune,tsohuwa mai kirki koda yayi mata bayanin halin da yaran suke ciki ta tausaya masu sosae ta kuma ce zata rike su da tsakani da Allah,shima kuma yayi alkawarin zai rinka turo da dan abunda Allah ya hore,
Da daddare suka isa unguwar ba tare da sanin kowa ba,sai da aka taimaka masu kafin aka samu suka shiga da hosana gidan,a ɗaki ake rufeta saboda haukan da takeyi,na bugun mutane da jefe jefe,tsaf zata iya kashe mutun,
Wannan shine silar komawarsu gidan tsohuwar nan,tayi masu halarci arayuwa,ita ta dinga nema masu tallafi don a maida hosana asibiti ayi mata aiki,haka sehrish ma bata zauna ba,har wankau suke yi suyi guga itada jahad suna tara kuɗin da za'a kai hosana aiki,kafin tsotsai ya ritsa da jahad,
Akwai wani lokaci da suka je gidan wani ɗan majalissa jin labarin cewa yana taimaka ma marasa lafiya waɗanda ake buƙatar kuɗin da za'ayi masu aiki,tsohuwa da sehrish suka je gidan mutumin,yayin da suka bar jahad a gida tana aikin wanki,
Tana cikin yin wankin nan ta dinga jin kukan hosana gwanin ban tausayi tana cewa dan Allah su buɗe mata ƙopa su taimaki rayuwarta mutuwa za tayi,tana son ganin ƴan uwanta,me yasa kullum suke ƙumsheta a ɗaki,zafi ya isheta,itafa tana da hankalinta,ba mahaukaciya ce ita ba,tana da hankalinta,
Natsuwa jahad tayi tana sauraranta,yanayin yadda hosana ke kalamanta yasa tayi tunanin cewa kodai ta samu lafiya ne,tun tana tsoran buɗe mata ƙopar har dae tausayinta ya kamata sosai,da sauri taje ta buɗe mata ƙopar,
Kamar jira take a buɗe da ƙarfi ta damƙi wuyan jahad da hannunta,ta janyota cikin ɗakin,tana cewa"dama kece kika sace ni ko?kika rufe ni acikin ɗakin nan kina cutar dani!yau Allah ya kamaki!wlh saina rama,
Duk yadda jahad taso ta kwaci kanta a hannun hosana abun yaci tura saboda wani irin mahaukacin ƙarfi ne ke gareta,buga kan jahad tashiga yi ajikin bango,jahad ta fasa ihu saboda azabar da taji,nan take jini ya shiga bulbulowa daga goshinta,kuma hakan baisa hosana ta daina bugunta ba,har saida taga jahad ta daina motsi sannan ta saketa,
Adai dai lokacin tsohuwa da sehrish suka dawo cikin gidan,da gudu suka faɗo ɗakin da hosana take ganinshi a buɗe nan suka samu jahad wanwar ƙasa jini na zuba,itama hosanar tana baje ƙasa sai faman mirgina-mirgina takeyi numfashinta na fita sama sama,
Wannan shine silar da aka kwantar da hosana da jahad asibiti,har akayi ma jahad ƙarin jini,ita za ayi mata aiki,
Inda Allah ya taimakesu asibitin suna da wata ƙungiya wadda manyan masu kuɗi ke tallafawa marasa lafiyan da za'ayi ma aiki da wani parcentage,sun samu kuɗin amma akwai cikon da zasu yi dubu ɗari tara likitocin suka buƙata a wurinsu,
Sehrish tasha wahala sosai wurin neman cikon kuɗin nan,duk inda taje neman taimako sae an nemi ta bada kanta sannan abata kuɗin,anan ne wata mata dake jinyar wata a ward din da aka kwantar dasu hosana take ba sehrish labarin hajjaju dake ɗaukar ƴan aiki tana samo masu aikatau suna yi kuma suna samun alheri dayawa,saboda gidajen manyan masu kuɗi take samo masu aiki,matar tace in taci sa'a ma,aranar da tafara zuwa aiki sai tace ma masu gidan su bata kuɗin aikinta na shekera ko biyu ne,in aka dace zasu bata kuɗin,bayan matar ta bata address din gidan,tun daga ranar sehrish kullum sai taje ƙopar gidan hajjaju nemanta,har Allah yasa ta samu ganinta,
Atakaice tarihin su sehrish hosana da jahad kenan,duk da bakomai aka fayyace ba, amma mutun zai gane inda aka dosa,
💋Boss Bature💋
Jikin kowa yayi mugun sanyi,masu raunin zuciya acikinsu tuni sun soma zubar da hawaye,hatta jahan dake da taurin kai sai da ya matse kwalla,Abusufyan kuwa tuni ya fashe da kuka,haka gwaggon katsina kamar ƙaramar yarinya haka ta dinga kuka tana fadin"Allah ka tsine ma Sayyadi da duk zuri'arshi!Allah ya wulaƙanta rayuwarshi kamar yadda ya wulakanta rayuwar ƴa'ƴan abusufyan ɗina,
Hatta Abbansu sae da ya matse kwalla shi da Abbas da su fawan,kowa ya harzuƙa ransu yayi mugun 6aci,tsananin tausayin su Jahad hosana da sehrish ne ya kamasu,marshal Omar kuwa sunnar da kanshi ƙasa yayi idanunshi sunyi jawur jikinshi sai kerma yake yi,zuciyarshi har wani tafarfasa takeyi saboda tsabar 6acin rai,
Sehrish kuwa lokacin da Jahad ta kammala bada labarin tasa kuka ita da Hosana,
Nan take ta miƙe daga jikin Sgr,hankali a matuƙar tashe take kallonsu yayin da zuciyarta ke bugawa da ƙarfi da ƙarfi,kowa zuba mata ido yayi yana kallonta ganin yadda jikinta ke rawa tana kallonsu hosana da jahad,
Muryarta na rawa ta ambaci sunansu"Hosana jahad kune.........'tana faɗin hakan ta yanke jiki ta faɗi asume,
Da sauri abusufyan da hajiya azeema sukayo kanta hada su jahad ɗin,
Sam Sgr bazai iya jurewa ba,yunƙurawa yayi azafafe ya juya tare da nufar upstairs ya koma bedroom ɗinshi,agaban mirror ya tsaya yana kallon fuskarshi wadda take daure tamau,gaba daya jikinshi sae kerma yake yi saboda tsabar 6acin ran da yake ciki,wata irin zufa ce tashiga gangaro mashi daga gefe da gefen fuskarshi,tabbas idonshi Idon Sayyadi...............................
*SANARWA SANARWA*💃💃💃💃
*ME TAKEN NA AMARYA HUTAA$$*
*MUNA FARIN CIKIN SANAR DAKU CEWA MUNA BADA HAYAR KAYAN AMARYA(WEDDING GOWN), KAYAN BRIDAL SHOWER, KAYAN BIRTHDAY PARTY, KAYAN FITAR SUNA, SANNAN MUNA BADA HEAD AND SHOULDER, MUNA DA POSS, MUNA ALKYABBAR KAI AMARYA KO TARON WALIMAR SAUKA, MUNA DA KAYAN FULANI FARARE NA YARA DANA MANYA MUNA DA NA AMARYA BLUE BLACK, SANNAN MUNA GYARAN JIKIN AMARYA DA UWARGIDA CIKIN KWANA UKU CAKAL ZAKIGA KIN KOMA TAURARUWA MAI WALWALI. MUNAYIN TURARUKAN WUTA DA HUMRA DA KOLACCAR, KOWANNE KALA KIKE BUKATA AKWAI CIKIN FARASHI MAI SAUKI.*
*LOCATION KANO*
08062073990
Ina kuke mata hamshakai wayanda suka amsa sunan su wajen mazajen su ina mata masu son qamshi shin ko kunsan tsafta bata tafiya seda qamshi ina masu son turare mai riqon gida tareda qamshin shi mai sanyaya zukata mardie collection tazo muku da dadadan turarukanta masu lasting riqon gida harma da jiki ku tuntube mu da nmb kamar haka 08136666994 inda zaku samu kaya kamar haka
Wadrobe balls
Madarar kulleccham
Vaseline kulleccham
Kajiji
Halut
Couscous
Khumrah
Da dai sauransu harda abin wanke toilet yayi tas komi dafe warshi wato BETHALEX METAL ku garzayo kar ayi baku
Ina kuke mata hamshakai wayanda suka amsa sunan su wajen mazajen su ina mata masu son qamshi shin ko kunsan tsafta bata tafiya seda qamshi ina masu son turare mai riqon gida tareda qamshin shi mai sanyaya zukata mardie collection tazo muku da dadadan turarukanta masu lasting riqon gida harma da jiki ku tuntube mu da nmb kamar haka 08136666994 inda zaku samu kaya kamar haka
Wadrobe balls
Madarar kulleccham
Vaseline kulleccham
Kajiji
Halut
Couscous
Khumrah
Da dai sauransu harda abin wanke toilet yayi tas komi dafe warshi wato BETHALEX METAL ku garzayo kar ayi baku
It's not just good ...it's finger linking good faster than fast food, better fine dining.
Snack
Awarah
Farah
Zobo
Samosa
Cup cake etc
Contact me 09063302182or 09012179727.
*💋Boss Bature💋*
Join this link to follow my tiktok acct👇
https://www.tiktok.com/@boss_bature?_t=8WKx0lm4jaP&_r=1
قصة حب رومانسية بين سحريش والجراح العام رفايت💋💘❤🤍❤💕💖*
Zagayeta su kayi gaba ɗayansu,su jahad na ambatar sunanta,fawan ne ya ɗauko masu ruwa a fridge ya dawo ya miƙa ma uncle ɗinsu,kar6a yayi tare da buɗe murfin ya ɗebo ruwan hannunshi nata kerma ya watsa mata shi a fuskarta,nan take ta farka tana faman yin atishawa,Alhamdulillah suka shiga faɗi suna kallonta,yunkurawa tayi ta tashi daga zaune tana bin su da kallo ɗaya bayan ɗaya kafin ta mayar da idanunta akan Su hosana da jahad da suka zuba mata ido,
Muryarta na rawa tace"jaj..jahad hos...sana...ku ne?ko dae idona ne ke nuna mun ba dai dai ba?
Ba ƙaramin farin ciki ne ya lullu6esu ba sehrish ta dawo cikin hayyacinta ta gane su,atare suka faɗa jikinta suka rungume juna suna kuka,
Murmushi kawai Abusufyan ke saki bashi kaɗae ba ma fuskar kowannansu na ɗauke da murmushi,musamman Abbansu junaid farin ciki kamar ya zuba ruwa a ƙasa yasha,haka hajiya azeemarsu har cewa take yi"yanzu nan waɗannan ƴan ukun duka namu ne?ƴa'ƴan mu ne?Allah abun godiya,yau dole in yi nafilar dare don miƙa godiyata ga Allah S.W.A daya nuna mun ƴa'ƴan abusufyan ɗinmu da ranmu kuma da lafiyarmu,Ashe dae da rabon yara suga danginsu,bayin Allah sun sha wahalar rayuwa,amma bakomai har yanzu lokaci bai ƙure mana ba,zamu nuna maku soyayyar da baku samu ba arayuwarku,Zamu baku duk wani jin daɗi na duniya da kuka rasa,zamu gatanta ku,sai mun cika ku da farin cikin da zaisa ku manta duk wani ƙunci da kuka ta6a fuskanta arayuwarku,waɗanda kuma sukayi silar jefa rayuwarku cikin hatsari tabbas sai sun ɗanɗani kuɗarsu sai sunji dama ba'a halicce su cikin duniyar nan ba,
Abbansu junaid ya kar6e da cewa"Ae daga rana irin ta yau su fara ƙirgen kwanakin mutuwarsu,saboda ƙarshen su yazo,sun tabka babban kuskuren ta6a jinin SALAHUDDEEEN HUSSEIN!Wallahi thumma tallahi