Showing 294001 words to 297000 words out of 432432 words
Chapter 99 - Abban Sojoji Book 2 Hausa Novel Complete
sannan yace"Hosana tayi mun dai dai jahad!idan har aka biye ta taki,bazaki ta6a bari a hukunta mara gaskiya ba,saboda tausayinki,abunda nakeso ki gane jahad,Irin waɗannan mutanen masu baƙar zuciya,idan har ba'a dinga hukunta su ba,to basu ta6a gane kuskurensu,balle har suyi nadamar abunda suke aikatawa su daina," jinjina kai jahad tayi fuskarta ɗauke da murmushi tace"Hakane ya Omar,kayi gaskiya,Sehrish ma ta ta6a fadamun hakan,lokacin da nayi ƙokarin hukunta hosana akan tonan asirin da taso tayi ma matar Ya ishaq,' sun jima atsaye suna magana kafin daga bisani Omar ya ruƙo hannayensu tare da shigowa dasu cikin gidan,
Hankalin aunty babba fa yaƙi kwanciya,babban abunda takeyi ma fargaba shine kada Hosana ta tona mata asiri agaban surukansu,kusan sau uku tana shiga toilet saboda cikinta daya katsa,har wurin ƙarfe 2:30,bata daina safa da marwar nan ba,acikin ɗakin,ƙafafunta har sai da suka fara yi mata raɗaɗi sannan ta samu wuri ta zauna daga gefen gadon tana faman sakin huci,shigowa hafsat tayi cikin ɗakin,fuskarta jawur sae faman kuka takeyi,aunty babba na ganinta ta miƙe hankalinta a matuƙar tashe ta shiga tambayarta Meya faru,Cikin shessheƙar kuka hafsat tace"daddy ne,Yayi mun faɗa sosai akan abunda muka aikata masu hosana,har mari na sai da yayi,kuma yace daga yanzu babu ni babu shi,In nemi wani uban,!"
Hannu aunty babba ta aza asaman kanta tana ambaton"Innalallahi wa'inna ilaihirraji'un!wayyo!nashiga uku!shikenan Hosana ta gama dani ta tona mun asiri wurinsu ishaq,Wayyo Ni laila,Zawarci ba fashi," tana magana tana cizon yatsanta,
Fitowar hayaam kenan daga cikin toilet taji suna wannan maganar,jikinta ba ƙaramin sanyi yayi ba,babban abunda take ji ma tsoro shine Ishaq ya saki Laila,saboda tasan cewa muddin ya saki aunty babba,to zamanta a gidan ya qare!!tunda bata da wata aƙala dasu,!Tashin hankali,ishaq bai ta6a gigin ta6a jikin hafsat ba,duk irin girman laifin da take aikatawa,amma yau akansu hosana Tasha mari,idan har hakane menene hukuncin aunty babba?ita da ta ɗauki nauyin shirin gaba daya,OMG!! Rungumota hayaam tayi ajikinta tana lallashinta,daƙyar ta samu hafsat tayi shiru,
*Boss Bature*
❤🤍❤💋Boss Bature💋*
Join this link to follow my tiktok acct👇
https://www.tiktok.com/@boss_bature?_t=8WKx0lm4jaP&_r=1
قصة حب رومانسية بين سحريش والجراح العام رفايت💋💘❤🤍❤💕💖*
*Father of soldiers*
*🔥TAKUN ƘARSHE🔥*
Wuraren ƙarfe shida na marece,ta fito daga cikin toilet,jikinta na sanye da towel fari ta ɗaure shi a saman ƙirjinta,da alama wanka tayi aciki,jahad ta samu zaune saman gadonsu,hannunta ɗauke da wayarta tana ɗan daddanawa,tsayawa tayi a ƙopar toilet ɗin ta ruqe ƙugunta tare da ɗan ɗaure fuskarta tace"Jahad!bana hanaki ɗaukarmin waya ba?kin manta abunda ya faru ran nan?kika kusa kashe mun waya gaba ɗaya!,yanzu da ace ta lalace dashi kenan wa zai siyamun wata"?
Fuskar jahad ɗauke da murmushi tace"Daddy mana!ae yace zai siya mana Phones gaba ɗayanmu,hada ke ma zai canza maki wata,hada ma laptop xai siya mana,"
Washe baki Sehrish tayi tare da cewa"Wai dagaske"?
"Eh,mana,shi da kanshi ya faɗi hakan,Kuma yace next week zamu koma school da kanshi zai mayar damu,don kada wani ya ɗaga mana yatsa,"ta ƙarasa maganar fuskarta dauke da dariya,sehrish kuwa tunda jahad tayi maganar school ba kowa ya faɗo mata aranta ba,face ƙawarta AMRISH,lokaci guda ta faɗo mata acikin ranta,nan take kuma taji gabanta ya faɗi rass,
Ganin fuskarta da alamun damuwa atattare da ita,yasa jahad kiran sunanta"Sehrish,meya faru ne?maimakon inga kina farin ciki?ko baki son komawa school ne?baki gaji da zaman kashe wando ba acikin gida?
Muryarta asanyaye tace"ba haka bane jahad,kawai na tuna da wata school friend ɗita ne,Nayi missing ɗinta sosai,Yarinyar tana sona sosai,itace take ƙarfafa mun guiwa akan in ringa yin karatu,in daina bacci a class,Gaskiya banyi mata adalci ba,sam na manta da ita,ni nasan cewa amrish ta neme ni har ta gaji,"
Jahad tace"Eyya,gaskiya baki kyauta mata ba,gashi sunan ku shigen iri ɗaya ke da ita,ni tun kafin ma in ganta har naji ina sonta,saboda tana son ƴar uwata sosai,Amma meyasa ba zaki jaraba kiranta ba tunda ga waya ko baki da numbarta ne?
"Ina da numbarta,kinsan kwanakin nan hankali na duk ba'a kwance yake ba,tun lokacin da muka daina zuwa school,ban ƙara bi takan wayar ba,sai ma na ganta a hannunki ne sannan nake tunawa da cewar ina da waya,Allah sarki Amrish ɗina,bansan wani hali take ciki ba,gashi bansan gidansu ba,"
Mikewa jahad tayi ta nufi wurin da Sehrish take tsaye,mika mata wayar tayi tare da cewa"Ki jaraba kiranta mana,sai mu gaisa,"
Kar6ar wayar Sehrish tayi,ta shiga cikin contacts ɗinta,ta lalubo numbar amrish,sae dai kash tana kiran layin taji wayar akashe,ɗayan layinta na Airtel ta kira shima akashe yake,hakan ba ƙaramin tayar mata da hankali yayi ba,
"Bansan meyasa ba'a samun layinta ba,amma mu bari da anjima sae mu jaraba kiranta mu gani kilan ta kunna wayar,"tayi maganar tare da miƙa ma jahad wayar ta kar6a,sannan ta koma gefen gadon ta zauna,ita kuma ta wuce gaban wardrobe tana lalubar kayan da zata sanya,
Turo ƙopar ɗakin nasu hosana tayi,da sallama abakinta,juyowa sehrish tayi tana kallonta haka itama jahad,
Nuna Sehrish tayi da yatsanta manuni,kafin tace"RISHI KIZO INJI DADDYN MU YACE KI SAME SHI A ƊAKIN SHI,KADA KI WUCE MINTI BIYAR"
Rasss!taji gabanta ya faɗi,
"Hosana dagaske ni daddy ke kira?kuma ni kaɗai yace inzo"?
"Eh,ke kaɗae yake son gani,"
Cikin sauri ta juya tare da zura hannunta cikin wardrobe ɗin,ta lalubo wasu pakistan riga da wando,rigar fara ce,har guiwa daga ƙasanta kwalliyar duwatsu ne,wandon kuma pink colour ne,bai da kwalliya ajikinsa,irin falazun nan ne burgujeje,mayafin kayan ta yafa Shima pink colour,gaban madubi ta koma ta ɗauki flower bomb ɗinta,ta feshe jikinta dashi,sai da ta fara kallon fuskarta a mirror ta ɗan sakarwa kanta murmushi,sannan ta kama hanyar fita daga ɗakin,
Jahad tace"Allah yasa alkhairi ne!kullum in daddy zai kiramu atare yake kiranmu amma yau ke kaɗae kawai yake son gani,"ta ƙarasa maganar tana nuna bayan sehrish da hannunta,
Murmushi kawai ta saki kafin ta buɗe ƙopar ta fuce,
Da sauri da sauri take tafiya don karta wuce minti biyar ɗin da Hosana tace,tana ƙarasawa baƙin ƙopar ɗakin takai hannu kenan zata buɗe,taga an ja ƙopar daga cikin ɗakin,da alama wani ne zai fito,zubama dogayen yatsun hannunshi ido tayi,farare tass ya ruƙe handle ɗin ƙopar dasu,wani irin daddaɗan ƙamshi ne ke fitowa daga ɗakin,nan take ta gane Cewa BABBAN YAYA NE,mamaki ta shiga yi mai ya kawo babban yaya a ɗakin daddynsu?bayan sa6anin da suka samu a tsakaninsu,ko sun shirya ne,?
Bata ƙarasa zancen zucin nata ba,SGR ya ƙarasa fitowa daga cikin ɗakin Abusufyan,wankan suit ne ajikinshi farare,kyau iya kyau,
Tsayawa yayi cak kamar an dakatar dashi,Sehrish kuwa tuni gabanta ya shiga faɗuwa,tun daga ƙasa har sama yabi ta da kallo,Yarinyar ko ƙafaɗarshi tsayinta bai kai ba,
Daƙyar sehrish ta iya buɗe baki tace mashi"Ina yini"
Tamkar bazai amsa mata ba,don har sai da ya wuceta ya ɗan yi nisa sannan taji yace"Lafiya,"yana faɗin hakan ya ƙara gaba,su babban yaya irin wannan shan ƙamshi haka,
Jiki asanyaye ta shiga cikin ɗakin da sallama abakinta,A zaune ta samu Uncle abusufyan,daga gefen gadonshi,juyowa yayi tare da kallonta fuskar nan tashi ɗauke da murmushi yace"Daughter,"
"Na'am daddy,ta amsa mashi tare da ƙarasawa,ta samu wuri saman sofa ɗin dake fuskantar gadonshi ta zauna,suna facing ɗin juna ita dashi,sannan tace"gani daddy hosana ce ta sanar dani cewa kana nema na,"
"Eh hakane,ni na ce ta kira mun ke,"
Natsuwa tayi tana jiran jin me zaice mata,sae faman wasa takeyi da yatsun hannunta,
"Gobe yaushe"?yayi tambayar yana kallonta,
..fuskarta ɗauke da murmushi tace"Friday," jinjina kanshi yayi tare da cewa"Masha Allah,Juma'a babbar rana,zaifi kyau in aka kafa tarihi aranar juma'a,ina tunanin kamar zai yi wuya a manta dashi,ko ba haka ba daughter?
Dariya sehrish tayi kafin tace"gaskiya ne daddy,juma'a itace babbar rana,duk abunda ya faru a ranar friday,zaiyi wuya a manta dashi,"
Abusufyan yace"Shiyasa nake so gobe na ɗaura maki aure,ko bakya so"?
Da sauri tasa tafukan hannunta tare da rufe fuskarta,tana dariya,
"Na ƙosa na fara ganin ƴan jikoki na," cikin zolaya yayi mata maganar,
"Dan Allah daddy,ka daina faɗin haka wlh kunya nake ji," cikin shagawa6a tayi maganar har lokacin bata zame tafin hannunta daga saman fuskarta ba,
Miƙa hannu Abusufyan yayi tare da janyo drawer chest ɗinsa gida na tsakiya,ya ɗauko wani small box Golden Colour mai shegen kyau,sae faman ƙyalli yake yi yadda kasan da Zallar Zinari akayi shi,
Ruƙo shi yayi a hannunshi yana jujjuya shi,ɗan ɗagowa yayi yana kallon sehrish wadda ta rufe fuskarta,
Gyaran murya yayi mata tare da cewa"Buɗe fuskarki mana," a hankali ta zame hannunta daga kan fuskarta,kai tsaye idanunta suka sauka kan small box ɗin dake hannun Daddynsu,ɗan zaro idanunta tayi tana ƙare mashi kallo,akwatin ya burgeta sosai,jikinshi sae ƙyalli yakeyi mai matuƙar ɗaukar ido,da jan hankali,cike da zumuɗi tace"daddy wannan fa?wlh yayi kyau sosai,ban ta6a ganin irin shi ba,"
Ƴar dariya Abusufyan yayi tare da cewa"koya burge ki ne"? ɗaga mashi kai tayi alamar eh,
Jujjuya akwatin yayi tare da cewa"Sadakin wata Ne,aka biya da Gold,"
Waro ido waje sehrish tayi cike da mamaki tace"daddy!dagaske ka ke dowry ne aka biya da Gold,but daddy who's she? Dariya abusufyan ya kuma yi ganin yadda tabi ta ruɗe da jin abunda yace,
"Dagaske nake ba wasa ba,sadakin wata Mai sa'a ce,Jinin nasara,"
"Daddy,can i see it pls"?
Miƙa mata small box ɗin yayi hannunta har kerma yake yi wurin kar6arsa,janyewa Abusufyan yayi fuskar nan tashi ɗauke da dariya yace"Da hannun hagu kuma?hannu biyu zaki sa ki kar6a,sannan in zaki kar6a ki tabbatar da kinyi bismillah,don Abun yayi albarka,"
Murmushi sehrish tayi tare da gyara natsuwarta,sannan ta miƙa hannanyenta duka biyun,tayi bismillah kafin ta kar6e shi daga hannun abusufyan,wani irin sanyi ne taji ya ratsata,jujjuya akwatin ta shiga yi tana ƙare mashi kallo,yana da nauyi duk da ƙarantar shi,hakan ya tabbatar mata da cewar,abune mai daraja acikinsa,ƙoƙarin buɗe akwatin ta shiga yi,da sauri Abusufyan ya dakatar da ita"kada ki buɗe shi,ki adana shi a wurinki,bana so kowa ya gani,kuma kada kowa yasan inda kika ajiye shi,"
Abun ba ƙaramin ɗaure mata kai yayi ba,
"Amma daddy,sadakin wata ne fa?kuma naji ka ce in ajiye shi a wurina,saboda Me"?
Bai bata amsa ba,sae ma kwantar da bayanshi da yayi saman gadon nashi,ya ɗan kishingiɗa,ya aza kansa saman pillow,yana kallonta,ta zuba mashi ido tana jiran jin amsar da zai bata,
Ƙayataccen murmushi ne ya bayyana akan fuskar Abusufyan,ya jima ahaka suna kallon kallo shi da Ƴar tashi,kafin yace"Zaki samu amsar tambayarki,amma ba yanzu ba,ki bani lokaci zan neme ki,yanzu zaki iya tafiya,"ya ƙarasa maganar yana nuna mata hanyar fita daga ɗakin,
Tamkar wadda aka zarewa lakar jikinta,haka ta miƙe jiki ba kwari,wani irin faɗuwar gaba kawai take ji,daƙyar ta iya ɗaga ƙafarta,tana tafiya tana waiwayen daddyn nasu,daya zuba mata ido yana kallonta,tabbas akwai wani abu da yake 6oye mata,sai da takai bakin ƙopar ɗakin,tana ƙoƙarin buɗe kopar ta fita,taji ya ambaci sunanta
"SEHRISH" da sauri ta juya tana kallonshi,
"Game da abunda ya faru tsakaninki da babban yayanku,Nasan ranshi ya 6aci sosai,ya baki Umarnin kiyi mashi aiki,amma na hanaki a matsayina na mahaifin ki,inaso kije ki bashi haƙuri,'
Waro ido waje sehrish tayi a ɗan tsorace tace"daddy in bashi haƙuri fa ka ce?wlh tsoro nake ji,jiya ranshi ya 6aci sosai,idan na kuskura naje wurinshi yau karya ni zaiyi nasan,"
Yadda tayi maganar ba ƙaramin dariya yaso ya bashi ba,fuskarta tamkar zatayi kuka,
"Don't worry ur self,SGR bazai ta6a gigin bugunki ba,saboda ba halayyarsa bace,"
Haɗiyar yawu tayi,tana sauraronshi,ɗan dakatawa yayi da yin maganar,kafin ya ɗaura da cewa"daga yanzu inaso,ki cigaba da aiki a ƙarkashinsa....' tunkan ya ƙarasa maganar Sehrish tace"Amma daddy,ka hanani zuwa part ɗinsa fa"
"A yanzu na soke wannan!inaso ki yi mashi biyayya,ki bishi sau da ƙafa,komai yake so kiyi mashi kawai!part ɗinsa kuma koda wani lokaci zaki iya zuwa ki shiga,even in the midnight,indai ya buƙaci ganinki ki je kawai,"
Gaba ɗaya Abusufyan ya gama ruɗar da ita,la66anta har kerma sukeyi wurin cewa"dad..dy!bangane me kake nufi ba,dan Allah ka fahimtar dani,"
"Ki tafi kawai kiyi duk abunda nace maki,idan lokaci yayi zan sanar maki,"
Juyawa tayi tare da zura ƙafarta,tabar bedroom ɗin nashi,lumshe idanunshi yayi tare da buɗesu,ya ƙurama ceilling ɗin sama ido yana kallonshi tamkar mai karanta wani abu ajikinshi,tunani ya shiga yi acikin zuciyarshi,ya shiga tariyo abunda yaji a kunnuwansa,
_Na amince zan aureta,bana son abun ya ɗauki lokaci,bana son taron mutane,kuma banaso kowa ya sani,saboda ba auren dundundun bane,nan da wata uku zan sake ta,zan aureta ne ba don ina sonta matsayin matata ba,sae don tayi mun aiki kafin na bar nigeria_
Hannu Abusufyan yasa tare da ɗaukar wata takarda dake ajiye saman side drawer ɗinshi,zuba ma takardar ido yayi yana kallonta,Agreement paper ce (Takardar yarjejeniya)mai ɗauke da signatures na mutun uku,"
Ajiyar zuciya ya sauke tare da zura ta cikin drawer chest ɗin daya fiddo akwatin nan da ya bama sehrish ya sanya takardar aciki ya ajiyeta,sannan ya mayar da ita ya datse,rufe idanunshi yayi bakowa bane ya faɗo mashi arai ba face ABU,nan take yaji kewarta ta lullu6e shi,Allah sarki abu,tana raye kota mutu?
A 6angaren Sehrish kuwa bayan fitarta daga bedroom ɗin Abusufyan,a ƙopar ɗakinsu ta tsaya,warware mayafin da ta laga akanta tayi,sannan ta lullu6e small box ɗin dake hannunta don kada wani ya gani,tura ƙopar ɗakin tayi sannan ta shiga daga ciki,babu kowa acikin ɗakin,sautin ruwan da taji ne daga cikin toilet ya tabbatar mata da cewar Jahad ce ke wanka,cikin sauri ta lalla6a gaban dressing mirror ɗinsu,ta zuƙunna gaban drawer ɗin dake ɗauke da mirror ɗin,ta janyo gida na ƙarshe,ta tura small box ɗin acikinsa can ƙurya ta turashi,sannan ta rufe,tana faman sauke ajiyar zuciya,miƙewa tsaye tayi har lokacin bata daina mamakin abubuwan da Uncle ya faɗa mata ba,abun ya ɗaure mata kai sosai,
Safa da marwa ta shiga yi acikin ɗakin,takasa zama saboda yanayin da ta tsinci kanta aciki,
*Boss Bature*
❤🤍❤
AMRISH,
Tun jiya da daddare data farka,tana bullayi asaman gadon bayan an samu nasarar ceto rayuwarta,doctor yayi mata allurar bacci bata ƙara farkawa ba,yini tayi a kwance tana bacci kamar matacciya,hankalinsu zeenatu ba ƙaramin kwanciya yayi ba,musamman Mommyn Amrish ɗin,bata ta6a tunanin amrish zata rayu ba,amma cikin ikon Allah sae gashi taji sauƙi sosai,poison ɗin da tasha bai kaiga yi mata illa ba,sunyi gaggawar kaita asibitin kuma likotoci sun taru akanta wurin ceto rayuwarta,wannan ne yasa bata jigata ba sosae,amma still da sauranta don ba ƙaramin galabaita tayi ba,yanzu haka ma ƙarin ruwa ne aka sanya mata,
Mommynta na zaune asaman plastic chair din dake agaban gadonta,fuskar nan tayi jawur da alama ba ƙaramin kuka tasha ba,ga rashin baccin da basu samu ba adaren jiya,gaba ɗaya hankalinta na akan Amrish dake kwance magashiyan tana bacci,
Zeenatu na a zaune daga gefen gadon da amrish ɗin take kwance,duk sunyi zuru suna kallonta,tunda safe Sofia ta koma gidansu,ita kaɗae ta rage saboda tace bazata koma gidansu ba har sai Amrish taji sauƙi sun koma gida,
Suna cikin zaman nan,kwatsam Amrish ta buɗe idanunta ta zazzaresu a wani irin firgice ta sanya hannu ta fizge robar ƙarin ruwan da akeyi mata,hankali atashe Zeenatu tace"Mommy amrish ta farka!ta cire ƙarin ruwan da aka sa mata,"jin wannan maganar yasa Mommyn yin firgit ta dawo cikin hayyacinta daga zurfin tunanin da ta shiga,sai dai kafin suyi wani yunƙuri,tuni Amrish ta diro daga saman gadon,ta watsa aguje,zeenatu na ƙoƙarin tarota,takai mata wani kakkwaran naushi a saitin Cikinta,nan take zeenatu ta zube ƙasa hannunta dafe da cikin,ta fasa uwar ƙara tana faɗin"Wayyo Allah na!cikina!nashiga uku,
Ko waiwayonta amrish batayi ba,hanyar fita kawai ta nufa,da gudu ta fice daga ɗakin,bin bayanta Mommyn tayi tana yarfa hannu a ruɗe take faɗin"Help!help!!dan Allah jama'a ataimaka a taro mun ita!mara lafiyace zata gudu,'
Da gudu wasu nurses suka bi bayan amrish,hada wasu daga cikin masu zuwa dubiya,
"Amrish dan Allah ki tsaya!wai meke damunki ne!bakiji ina magana ba!ina zaki je ne!," hankali tashe mommyn ke magana,amma ko sauraronta amrish bata yi ba,duk wanda ma yayi ƙoƙarin tarota bugu take kai mashi kamar ƴar wrestling,gashi wani irin ƙarfine da ita kamar na Doki,in ta daki mutun sai ya kusa zaucewa,duk yadda suka so su kama amrish,amma abun yaci tura,domin kuwa 6att suka neme ta suka rasa acikin asibitin,saƙo da lungu babu inda basu duba ba,amma babu ita babu alamarta,ko mai kama da ita ma babu,nan fa hankalin kowa ya tashi,hatta security guards ɗin dake tsaron gate ɗin asibitin,sae da aka tambayesu,sun tabbatar da cewar basu ga fitarta daga asibitin ba,sae dai ko a wani wurin ta 6oye,Hatta Cctv footage sae da aka bincika,amma ba aga ta hanyar da Amrish tabar cikin hospital ɗin ba,kuma ba'aga wurin da ta 6oye ba,wannan abun ba ƙaramin ɗaure masu kai yayi ba,yarinya kamar mai iskokai?babban abunda zai baka mamaki ƙarfin daya zo mata,mutumin dake kwance magashiyan a gadon asibiti,amma ya tashi farat daya da irin ƙarfin nan a jikinshi�?
Saboda tsabar tashin hankalin da Mommyn Amrish ta shiga,nan take ta yanke jiki ta faɗi ƙasa asume,sai dai nurses suka cuccu6eta aka shiga da ita ciki,suka kwantar,itama zeenatu sae da suka kwantar da ita don kuwa ba ƙaramin buguwa tayi ba,naushi ɗaya tayi mata aciki,amma sae da jini ya zuba a bakinta,
*ANA WATA GA WATA!JAMA'A INA AMRISH TA SHIGA NE*?😳😳😳
*Aunty Babba*
Fitowarta kenan daga cikin toilet tana faman dafe cikinta,ɗagowa tayi tana kallon hayaam dake zaune gefen gadon ta zabga uban tagumi da hannayenta biyu,Hafsat kuwa na asaman gadon kwance ta lullu6e da bargo jikinta sae kerma yake yi,wani irin zazza6ine mai zafi ya rufar mata,tunda rana tagaza motsa jikinta,abun gwanin ban tausayi,
Kwatsam!sukaji an banko ƙopar ɗakin nasu,dafe ƙirji Aunty babba tayi tana kallonshi,sae faman huci yakeyi yadda kasan mayunwacin zaki,da ƙafarsa ya tura ƙopar ɗakin ta rufe,hayaam na ganinshi a razane ta haye saman gadon,jiki na rawa ta wuntsila daga ƙasan gadon ta 6oye,tana faman zazzare ido,
Cikin inda inda ta ambaci sunan shi"I..ishaq!"
A zafafe ya ƙarasa inda take,kwakkwarar damƙa yakai ma wuyanta,ya shaqeta sosai,yadda ko ihu bazata iyayi ba,saboda tsabar raɗaɗin da taji nan take ta saki fitsari a wando,wani irin gumi ne ya shiga tsattsafowa daga gefen fuskarta,idanunta sunyi jawur cike tab da kwalla,ƙwayar idon tamkar zata zazzago ƙasa,
A ruɗe hafsat ta fasa uwar ƙara,ganin abunda daddynta ke ƙoƙarin yi,gadan gadan so yake ya kashe Mommynta,da gudun gaske ta duro daga saman gadon tana kuka,
"Kafin ki kashe su!Ni zan fara kashe ki!muguwa kawai!Nayi danasanin aurenki laila!nayi danasanin saninki da nayi,Nayi danasanin haɗa zuri'a ɗaya dake,Allah ya isa tsakani na dake!Na tsaneki!kin fita araina!ban sonki!bansan ganinki!"daƙyar sautin muryarshi ke fita saboda tsabar 6acin rai,a fusace ya