Showing 288001 words to 291000 words out of 432432 words

Chapter 97 - Abban Sojoji Book 2 Hausa Novel Complete

ɗakin,gefen gadon ya zauna tare dasa hannu ya bubbugga ƙafarɗarshi""Junaid!junaid"! Da ƙarfi yake ambaton sunan nashi,yatsina fuska junaid ya shiga yi yana faɗin"Wai wanene ke son takuramin"!
  Yayi maganar yana ɗan ware idanunshi masu ɗauke da bacci,
  Harara abbansu yaa jefa mashi tare da cewa"Ubanka ne,buɗe idonka ka gani mara matunci" koda yaji muryar. abbansu sae ya ƙara tamke fuska,yana faman murguɗa masa baki,Abba yace "Eyyyeh!ni kake murguɗa ma baki," zumbura masa baki yayi,hada sa hannu ya toshe kunnuwansa don karma yaji muryar abban nasu,
 
"Nasan maganinka yaro"yayi maganar tare da kai hannunshi saman side drawer ya ɗauko bottle water ɗin dake ajiye a sama,buɗe murfin robar ya shiga yi yana faɗin"Zaka tashi ko saina watsa maka ruwan nan,"
  Wuri wuri yayi masa da ido,yana jira yaga in dagaske abban nasu ruwan zai watsa mashi,
  Jin yayi banza dashi yasa shi ɗebo ruwan a murfin robar,ya watsa masa shi da sanyinsa asaman fuskarshi,aikuwa a gigice ya tashi zaune jikin shi na kerma,hankalin abbansu ba ƙaramin tashi yayi ba ganin yadda ya tsorata daga watsa mashi ruwa a fuska,abu kamar wasa sai ga junaid yana kuka hawaye jaga jaga a fuskarshi,
  Tsawa abbansu ya ɗan daka mashi tare da cewa"Yi mun shiri rigimamme kawai,"
  Wannan maganar da abbansu yayi ba ƙaramin ƙona mashi rai tayi ba,saukowa yayi daga saman gadon yana shassheƙar kuka yace""kuma Allah tunda ka kore ni,ɗakinsu sehrish zanje na kwana,"yayi maganar tare da bubbuga ƙafarshi ya fuce,
  Sakin baki abbansu yayi yana kallonshi har ya fuce daga ɗakin,girgiza kai kawai yayi tare da gyara kwanciyarshi,

Junaid kuwa bayan fitarshi daga ɗakin Abbansu,bedroom ɗinsu sehrish ya wuce kai tsaye,cikin sa'a ya samu ƙopar ɗakin a buɗe,hannu yasa ya tura door din,sannan ya shige ciki,

Sun cika gadon su uku abunsu,sae faman sharar bacci sukeyi banda mutun ɗaya wadda ta rufe idanunta tamkar maiyin bacci, gaba daya hosana ta yaye masu bargon da suka lullu6e dashi,dama ita bata iya kwanciyar bacci ba,zaiyi wuya ta kwanta batare da ta faɗo ƙasa ba,dalilin dayasa suke sanyata tsakiya kenan saboda gudun karta faɗo,sehrish na kwance a left hand,hosana tana a middle ɗinsu,yayin da jahad ke a right hand,saitin inda yake tsaye,hannu yasa tare da kashe masu hasken ɗakin da sehrish ta bari a kunne,lalla6awa yayi ya haye saman gadon,gefen jahad ya kwanta, tare da ja masu bargon ya lullu6esu duka,cikin ƙankanin lokaci bacci ya ɗaukeshi,tabbas Sehrish taji lokacin da aka kashe masu hasken ɗakinsu,amma batayi tunanin ta buɗe idanunta ba don taga wanene,saboda halin da ta shiga,Zuciyarta ba tayi mata daɗi ga hawaye sae faman shararowa suke yi daga cikin idanunta,babban abunda ke damunta shine wani hali sgr yake ciki?Yayi bacci ko idonshi biyu?bataso abunda ya faru ba,sai dae ba yadda ta iya dole tabi umarnin mahaifinta da wannan zancen zucin bacci ya sace ta,
tashin hankali,Junaid fa ya shige acikinsu sae faman sharar baccinsa yake,sun manne ma juna shi da jahad,duk a tunaninta sehrish ce,hada ƙara rungumoshi ajikinta,


   *mu haɗu on monday donjin yadda zata kaya don kuwa akwai ƙura! Amrish zata Rayu ko kuwa akasin hakan?Wai ma wacece Amrish ɗin nan?su waye iyayenta?shin Sgr zai amince da auren sehrish?a yadda yake jin kanshi ɗin nan?Me zai faru idansu jahad suka Tsinci junaid acikin ɗakinsu saman gadonsu?*😨😱
   *Su aunty babba manya Naki na nan tafe*🤣 *💋 Boss Bature💋*



Join this link to follow my tiktok acct👇

https://www.tiktok.com/@boss_bature?_t=8WKx0lm4jaP&_r=1




قصة حب رومانسية بين سحريش والجراح العام رفايت💋💘❤🤍❤💕💖*

*Father of soldiers*

*🔥TAKUN ƘARSHE🔥*



Wuraren ƙarfe 3:00 na dare,Jahad tayi wani kwakkwaran juyi cikin bacci zata gyara kwanciyarta,aikuwa taji an ƙanƙameta sosai an matse ta,numfashinta har wani kokawar ɗaukewa yake yi,ƙoƙarin janye jikinta ta shiga yi amman hakan ya faskara,saboda ruƙon da akayi mata bana wasa bane,cikin baccin ta dinga faɗin"Sehrish!ki sake Ni!kin matseni,numfashi na zai ɗauke" daƙyar sound ɗin ke fita saboda throat ɗinta da ke abushe,saboda thirsty da take ji,tun tana ambaton hakan ƙasa kasa har takai ga ɗaga muryarta "Sehrish!!dan Allah ki sake ni,baki ji nace kin matse ni ba? Shiru babu mai bata amsa domin kuwa duk bacci suke yi,


Jahad kuwa tuni ta gama galabaita hakan yasa ta tattare iya ƙarfinta na ƙarshe ta ingije junaid daga jikinta,ya ɗan yi baya,hakan yasa ta samu sarari,hannu tasa tare da zame bargon ta fiddo da kanta,tana faman sauke ajiyar zuciya,zufa duk ta wanke mata jikinta duk da weather ɗin nasu akwai sanyi,matsuwar da tayi ne yasa ta zubda gumi,juyawa ta ɗan yi tare da kallon gefen hannun hagunta,kasancewar akwai hasken electric bulbs ɗin da suka gauraye gidan daga waje da kuma na corridor ɗinsu gana main palour,Sune suka ɗan bama ɗakinsu haske,duk da an kashe Globe ɗin ɗakin nasu,dama kuma Sehrish ta lalata bedside lamp ɗin ɗakin,lokacin baya data kwala ma Haroon a goshinsa,

Ƙura ido jahad tayi tana ƙare masu kallo,gani take tamkar idonta ba dai dai suke nuna mata ba kamar mutun biyu ne kwance a gefen hagunta,hannunta ta miƙe tare da yaye masu Sehrish bargon da suka rufa dashi,gabanta ne ya faɗi rass!ganin Sehrish ga kuma hosana baje suna ta sharar bacci,nan take hankalinta yayi mugun tashi,wani irin tsoro ne ya lullu6eta,tabbas akwai mutun ɗaya 6angaren damanta,wanda suka kwana rungume da juna a ƙanƙame,wanda yayi silar taushe numfashinta,tashin hankali! kasa juyawa tayi don taga wanene saboda tsabar tsoro,sae dai ta zura hannayenta dake ta faman kerma ta laluba don taji in da gaske wani ne kwance a wurin,Sumar kan junaid ta shafo da hannunta,a razane ta zame hannunta,la66anta na kerma ta shiga furta"La'Ila ha'illah Anta subhanaka,Inni kuntu minazzalumin,"daga bisani ta shiga faɗin"innalillahi wa'inna ilaihirraji'Un!!,

Muryarta na kerma ta shiga kwalama su sehrish kira kaɗan kaɗan don kada aljanin ya farka,"Hosana!Sehrish!!dan Allah ku tashi!Mutum mutumi acikin ɗakinmu saman gadonmu!ina tunanin Aljani ne ya faɗo ɗakinmu don ya cutar damu,Wayyo Allah na" babban tashin hankalinta aljanin na akusa da ita,in ma cutar dasu yazo yayi toh ta kanta zai fara tunda itace a kusa dashi,

Tuni zufa ta gama wanko mata a fuskarta,numfashi kanshi daƙyar take fitar dashi don kada aljanin yaji yasan cewar idonta biyu,
  "Sehrish!Sehrish!!hosana!wai ba zaku tashi ba?dan Allah ku tashi kuga abunda na gani,asaman gadon mu,"tana magana hawaye na sauka daga idonta,don ita ta riga ta sallamawa kanta cewar ajalinta ne yazo,

   Duk wannan surutan da Jahad ke yi kaf a kunnan Sehrish,wadda ke lamo tayi nisa cikin zurfin tunanin da take yi,Duk a tunaninta Jahad mafarki takeyi shiyasa take sambatu,wannan dalilin ne yasa bata motsa ba,kuma bata tanka mata ba,idanunta ne kawae ke arufe amma idonta biyu,likimo kawai tayi,

Jahad na cikin wannan yanayin taji an aza mata hannu asaman waist ɗinta,a wani irin Firgice ta fashe da wata irin gigitacciyar ƙara,wadda tayi silar tashin hosana daga bacci,hatta sehrish sai da ta razana,a tare suka tashi zaune ita da hosana suna kallon Jahad dake ta ihun neman agaji,ai koda Hosana da sehrish suka ga hannun mutum a saman qugun jahad,a gigice suka duro daga saman gadon da gudun gaske har suna tuntu6e wurin tunkarar ƙopar ɗakin don su buɗe ta su gudu,jahad kuwa sam taƙi motsawa,sai ihu take tana kuka,waɗanda take tunanin cewa zasu taimaketa sun gudu sun barta asaman gadon ita kaɗai,jikinsu sae faman kerma yakeyi burinsu su buɗe ƙopar su gudu amma taƙi buɗuwa,hakan yasa Sehrish watsawa da gudu,ta shige toilet taja ƙopar ta rufe,ganin haka yasa hosana tunkarar wardrobe ɗinsu,ta buɗe gidan ƙasa da babu kaya sosai acikinsa sae bedsheets,Ta faɗa ciki tare da jan murfin wardrobe ɗin ta rufe shi,kowa yayi ta kansa kenan,duk wannan budurin da akeyi Junaid bai sani ba,domin kuwa ba ƙaramin abune ke iya tashinshi daga bacci ba,irin mutanen nan ne masu nauyin baccin tsiya,

Jahad na cikin wannan halin na firgici,taji an aza mata ƙafa asaman jikinta,firgitar da tayi ne yasa tayi wurgi da junaid gaba ɗaya,ya tafi dama yana dab da bakin gadon,aikuwa ji kake timmmm!ya ƙundumo ƙasa kanshi ya bugu sosai saman tiles,
raɗaɗin da yaji ne yasa shi farkawa daga baccin,ya fashe da matsanancin kuka,

   Gaban jahad ne ya faɗi rass!!jin sautin kukan Junaid,rarrafowa tayi ta dawo gefen gadon tare da ɗan leƙawa don ta tabbatar ma kanta abunda kunnuwanta ke ji,Zaro ido waje tayi cike da mamaki take kallonshi,yadda kasan wani jinjiri ya 6are baki sai kuka yake yi,da ƙarfi ta ambaci sunanshi"JUNAID"dakatawa yayi daga yin kukan da yakeyi jin an ambaci sunanshi,wurga idanunshi yayi akan jahad,yayi mata wuri wuri da ido yana kallonta,
  Muryarta na rawa tace"juj..junaid!dama kai Ne?me kake yi acikin ɗakin mu?
cikin shessheƙar kuka yace"Nifa Zuwa kawai nayi don in taya ku kwana,"
...zuba mashi ido kawai tayi tana  kallon fuskarshi don abun ya fi ƙarfinta,
  Daga cikin toilet ta jiyo Muryar Sehrish tana ce wa"Jahad wai dagaske junaid ne?Naji kin ambaci sunanshi"?
  A ƙule jahad tace"Bansani ba,ku fito ku gane ma idonku,kunaji ina kukan neman taimako amma duk kuka watsa a guje kuka barni,yanzu da wani mugun abunne ba junaid ba,da Allah kaɗae yasan me zai biyo baya,"
  buɗe ƙopar sehrish tayi tare da fitowa daga cikin toilet ɗin,hosana ma ta buɗe wardrobe ɗin tare da fitowa daga ciki,suka tunkari inda junaid yake kwance yana faman sauke ajiyar zuciya,sae faman lumshe ido yakeyi,saboda baccin dake a idanunshi,
  "Junaid!" sehrish ce ta kira sunanshi,ware idanunshi yayi akanta yana kallonta,
.."junaid me kake yi a ɗakin mu?waya kawo ka?anya baka fara shan ƙwaya ba"
  Harara ya wurga mata tare da murguɗa mata baki yace"bansani ba,duk kun bi kun takura rayuwata,hakanan kawai ina baccina kun tashe ni,laifi ne in na kwana aɗakinku,ni ba ɗan uwanku bane"? Sakin baki sukayi suna kallonshi,hosana tace"wlh saina faɗa ma Daddy da Ya Omar,ince ka shigo ɗakinmu ka kwanta mana asaman gadonmu,ƙato dakai,"tana kai ƙarshen maganarta,junaid yace"idan kin tashi ki faɗama Kaka ƙarewar daddyn,mai kan kurciya kawai" wannan maganar ba ƙaramin fusata hosana tayi ba,jikinta har rawa yakeyi wurin dauko pillow daga saman gadonsu,ta buga mashi asaman fuskarshi,koda ganin hakan,sehrish ma ta ɗauko pillow ta shiga taya hosana,jahad tace"wlh nima bazan ƙyale ka ba,junaid saboda ka bani tsoro,kuma babu kyau ma tsoratar da musulmi,"tasa hannu ta ɗauko pillow itama,nan fa suka tasa junaid kamar sun samu jaki,suka dingi jibgarshi da pillows,tun yana yi masu magiyar su daina har ya sake fashe masu da kuka yana bubbuga ƙafafunshi,suna cikin bugun nan nashi,suka ji tsit junaid ya daina motsi,cikin sauri Jahad ta kalli jikin pillown hannunta,Ɗigon jini ta gani,ɗagowa tayi da nufin ta nuna ma su Sehrish aikuwa karaf idonta ya sauka akan pillown dake hannun sehrish da hosana,duk ɗigon jini ne ajikin pillown hannunsu,Tashin Hankali!
  Gaba ɗayansu ba ƙaramin kiɗima suka yi ba,ƴan hanjin cikinsu suka kaɗa,zagaye shi su kayi a zuƙunne suna kallon fuskarshi,
  Fashewa hosana tayi da kuka tana faɗin"Wlh babu ruwa na!bani na kashe junaid ba!"maganar da tayi ba ƙaramin tsoratar dasu tayi ba,tuni ido ya raina fata,daga wasa!?
  Jijjigashi suka shiga yi atare suna ambaton sunanshi"Junaid!junaid!!!ka tashi!dan Allah junaid ka tashi!!Wayyo Allah munshiga ukun mu!!dan Allah baby junaid ka tashi," ko motsi wannan junaid baiyi ba,matsawa sehrish tayi tare da kanga kunnanta asaman hancinshi don taji in yana numfashi,ɗufff taji babu numfashi da sauri ta sanya tafin hannunta asaman kirjinshi saitin zuciyarshi nan ma taji zuciyar tashi tadaina bugawa,a wani irin sukwane ta ɗago da idanunta waɗanda sukayi luhu luhu cike tab da hawaye tana kallonsu Jahad da hosana,jiki a mace tace"ZUCIYAR JUNAID BATA BUGAWA HAKAN NA NUFIN MUNYI SILAR MUTUWAR JUNAID"!!!
  Girgiza kai jahad ta shiga yi tana cewa"Junaid bai mutu ba,dan Allah ki daina faɗan hakan,kada ya tabbata dagaske,"tayi maganar a yayin da take kai hannu tana tatta6a fuskarshi"junaid!junaid!ka tashi dan Allah ka tashi junaid,"
   Ganin yaƙi motsi yasa suka fidda rai da cewar junaid zai tashi,kifa kai sukayi su duka ukun suna shessheƙar kuka,ɗan ɗagowa jahad tayi tare da kai idonta kan fuskarshi,Abun mamaki sae ga murmushi ya bayyana akan fuskarshi,dimples ɗinsa guda biyu sun lotsa,Wani irin ihun farin ciki ta saki tana fadin"Bai mutu ba!junaid wasa yake yi mana,gayanan yana murmushi,'jin haka yasa su sehrish saurin ɗagowa da kawunansu suna kallonshi,sae faman wangale baki yakeyi yana dariya,abun ba ƙaramin ɗaure masu kai yayi ba,
  "Junaid"sehrish ce ta ambaci sunanshi,a hankali ya buɗe manyan idanunshi yana kallonsu one by one,sai faman 6a66aka dariya yakeyi,
  Har suna haɗa baki wurin cewa"Kai junaid!meyasa zakayi mana haka?wlh ka tsoratar damu sosai,"
  "Wanda yasa kuka bugeni,ko tausayina bakuji,kun wani taru akaina kuna jibgata kamar kunsamu jaki amale,shiyasa nima na rama da gangan na ɗauke numfashina don kuyi tsammanin kona mutu"yayi maganar yana murguɗa masu baki,Ajiyar zuciya suka shiga saukewa,
  "Junaid dan Allah kayi haƙuri,bazan ƙara bugunka ba,kada ka faɗama kowa,"acewar hosana,
  Harara ya jefa mata tare da ƙara tamke fuskarshi,
  Cikin sanyin murya jahad tace"junaid baka da lafiya ne?mun ga jini ajikin pillow lokacin da muke bugunka,kuma da alama daga hancinka muka gogo shi,"
  Shiru ya ɗan yi yana kallonta kafin yace"Lafiyata ƙalau Ni,nose bleeding ne ba wani abu ba dama ina yawan yinshi,yafi zuwa mun da daddare,shiyasa baku ta6a gani ba"
  "Amma ka faɗama Abba ko wani game da nose bleeding din"? Girgiza kai yayi alamar a'a,da alama baison maganar,don haka yace"pls nidai mubar wannan zancen,kusan yadda za kuyi dani don Allah bazan iya komawa bedroom ɗina ba,tsoro ma nakeji,"yayi maganar ashagwa6e,
  Jiki asanyaye jahad ta kalli su sehrish tace"kuje ku kwanta,bari ni na rakashi ɗakin nashi," mikewa su kayi atare da ita da hosana suka koma kan gadon suka kwanta,tare da jan bargo suka lullu6e,
    Miƙewa daga zaune junaid yayi yana cewa"Allah sai dai ki goyani,don na riga dana faɗa maki cewa ƙafafuna ciwo suke yi mun bazan iya taka stairs ba,"
  Murmushi jahad tayi tare da cewa"shikenan,zan goya ka amma ka bari sai munje wurin benen tukunna in goya ka," amsa mata yayi da toh,sannan ya mike tare da ruƙo hannunta cikin nashi yace"Tashi muje,"mikewa tayi suka fita atare,suna tafiya tana satar kallon gefen fuskarshi kamar wani zautacce sai faman sakin murmushi yake yi,hakanan ta dinga jin gabanta na faɗuwa,lamarinsa ba ƙaramin mamaki yake bata ba,kokonto ta shiga yi anya wannan ɗigon jinin da suka gani na ha6o ne? Yanayin yadda abun ya afku tamkar ba jinin ha6o bane,tabbas akwai dae wani abu dake damunshi wanda baison kowa ya sani,
Tana cikin zancen zucin nata taji yace"Mun ƙaraso wurin stairs ɗin,yanzu ki goyani,ki kaini har bedroom ɗina,kuma ki kwantar dani,"
  Amsa mashi tayi da toh,sannan ta zuƙunna,ya daddage ya haye saman bayanta,tare da kwantar da kanshi luff kamar wani jinjiri,zagayo da hannayenshi yayi ta saman stomach ɗinta,hakan ba ƙaramin yanayi ya jefa ta ba,ji tayi tamkar bazata iya miƙewa tsaye ba,saitin kunnanta taji daddaɗar muryar nan tashi mai haɗe da shagwa6a"jahad ki tashi mu tafi,bacci nake ji,"
  Daƙyar ta iya mikewa tsaye goye dashi abayanta,hannu tasa ta tallaboshi sosai,sannan ta haye saman benen,tana tafiya tana tangal tangal har ta ƙaraso ɗakin nashi,hannu tasa ta ɗan tura ƙopar sannan ta shige ciki,Talal suka samu kwance yana ta sharar bacci,ƙarasawa tayi tare da sauke junaid saman gadon,ya gyara kwanciyarshi,bargo taja ta rufe mashi body ɗinsa zuwa neck ɗinsa,tana ƙoƙarin juyawa tabar wurin,taji ya ruƙo hannunta cikin nashi,jimmm tayi tana jiran jin me zaice mata,
  "Jahad"ya ambaci sunanta da wata irin murya ta mai jin bacci,
  "Na'am,"ta amsa mashi kiran a yayin da take juyowa" murmushi ya sakar mata tare da sanya yatsan hannunshi acikin dimple ɗin fuskarshi yace"Kiss me pls," bakomai ya faɗo mata aranta ba,face abunda ya ta6a faruwa atsakaninsu,cikin motarshi,daga zuwa manna mashi kiss a side face ɗinsa,bakinta ya goce izuwa cikin bakinsa,a ranar zauce mata yayi,
  Maƙe masa kafaɗa tayi alamar bazatayi mashi kiss ɗin ba,bubbuga ƙafarshi ya shiga yi yana yi mata shagwa6a,hakan ba ƙaramin burgeta yayi ba,saboda wani irin kyau da yake bayyana akan fuskarshi aduk lokacin da yake shagwa6a,tamkar tayi hugging ɗinshi ajikinta haka ta dinga ji,
   "Baza kiyi mun ba ko"?yayi maganar.yayin da idanunshi ke ƙoƙarin lumshewa,
   "Shikenan,zanyi maka,amma ka rufe idanunka," da sauri ya rufe su yana jiran jin la66anta asaman fuskarshi,tsayawa tayi asaman kanshi,tana karanto addu'o'i tana tattofa mashi akan fuskarshi,daga ƙarshe ta haɗe yatsun hannunta guda biyu na hannun damanta,a hankali ta aza yatsun nata asaman la66ansa,sannan ta furta sautin kiss ɗin da bakinta,wani irin farinciki ne ya lullu6e junaid,duk a tunaninshi bakinta ne ta aza asaman nashi,baisan cewa wayau tayi mashi ba,tasa yatsun hannunta amatsayin la66anta,
rufe mashi fuskarshi tayi da bargon,sannan ta kama hanyar fita daga bedroom ɗin,
   "I Love u so much jahad," muryar junaid ce ta katse mata hanzarinta,dakatawa tayi tare da ɗan juyawa tana kallonshi,yana acikin bargon ya furta mata wannan kalmar,
   "Kina sona jahad"?
Wani irin ƙayataccen murmushi ne ya sauka akan fuskarta,bata bashi amsar tambayarba,cikin sauri ta fuce daga ɗakin nashi,ta koma bedroom ɗinsu ta kwanta zuciyarta cike fal da farin ciki,ta ji daɗin kalmar da junaid ya furta mata,duk da bata da tabbacin cewar ko dagaske yake yi mata," da wannan tunanin bacci ya ɗauketa,

  *Boss Bature*

    🤍❤�?
Washe Gari,

Kwance take asaman katifarsu,ta saki baki tana ta sharar baccinta,sae faman jan minshari takeyi kamar Ragon layya ga miyan bacci dake gangarowa ta cikin bakinta da ta bari a buɗe,tana cikin baccin nan taji Ringing ɗin wayarta da ƙarfin gaske har cikin dodon kunnanta,hannu tasa tare da toshe kunnanta tana faman buga tsoki,alamar an takura mata,bata ɗaga kiran ba,har ya katse kuma sai ga wani kiran ya ƙara shigowa,a hargitse Abra ta miƙe ranta a matuƙar 6ace,tasa hannu ta dauki wayar dake ajiye gefenta,picking call ɗin tayi tare da kara wayar a kunnanta Cike da masifa tace"Wai Uban wanene ke kirana tunda sanyin safiya"?
  Kafin ta rufe bakinta taji ance"Ubanki ne!" har sai da gaban abrah ya faɗi rasss,cikin sauri ta janye wayar daga kunnanta tare da kallon screen ɗin wayar don ta shaida mai kiran nata,Sunan Aunty babba ta gani,yatsina fuska tayi kafin ta mayar da wayar a kunnanta,"ina kwana aunty,an tashi lafiya"
  Rai a6ace Aunty babba tace"Ruƙe gaisuwarki,sakarya daƙiƙiya zaman uban mi kike ke da Mammy da har kuka bari AMAL ta gudo daga mai duguri tazo Abuja wurin Amani?!" jin wannan maganar yasa abrah ta zabura,don har sai da ta daki ƙirjinta da hannunta,Hankali atashe tace"Aunty laila dagaske Amal tana abuja wurin Amani!"
  "Ƙarya zan maki ne?Kuna nan sake da baki har yarinya ƙarama tayi maku wayau ta gudu,Yanzu baki ga yadda Amal ta koma ba,Yarinya ta zama ƴar hutu kamar wadda ta taso a gidan naira,Tamkar bata ta6a shan

Chapters

Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login