Showing 189001 words to 192000 words out of 432432 words

Chapter 64 - Abban Sojoji Book 2 Hausa Novel Complete

muna jin yunwa amma mun fi so muci abinci atare da ƴar uwarmu,"
Jin wannan maganar ta Jahad,yasa jikin shi yin sanyi,da alama ba ƙaramin so suke yi ma junansu ba,
  "Ya omar kayi shiru,"muryar hosana ce tayi maganar a ƙagare,
  cikin natsuwa ya soma magana"kuyi haƙuri kunji,insha Allah yau zaku ga ƴar uwarku,bazan samu zuwa ba,amma zan turo major ya ɗauko ku,abunda nake so daku yanzu,ku ci abinci ku ƙoshi,sannan kuyi wanka ku shirya ku sanya kaya masu kyau,a kowane lokaci zaku iya ganinshi yazo,"
  Yana jiyo muryoyinsu ta cikin wayar suna ta faman fadin Wayyo daɗi yau zasu ga rishi ɗinsu,'
  Sallama yayi masu bayan ya ajiye wayar,ya juya tare da wuce wa wurin closet ɗinshi,tsaf ya shiga shirya kanshi acikin rantsattsiyar shaddar shi.

SEHRISH,

Kwankwasa ƙopar ɗakin da akayi mata ne da ƙarfi,yasa ta tashi a firgice tana faman zazzare ido,ƙankame bargon jikinta tayi tana ƙara lullu6e jikinta dashi,fuskarta duk a yamutse saboda kukan da tasha jiya,amma yanzu Alhamdulillah tun da tafarka babu wannan ciwon cikin atare da ita,tamkar bata ta6a yin ciwo ba haka ta farka,taji sauƙi sosai,
   "Reesh,baby junaid ne fa,in shigo daga ciki"?
Muryar junaid ce taji yana magana daga waje,
  akasalance tace"eh,ka shigo,"
. tura ƙopar yayi tare da sanya kafa ya shigo cikin ɗakin hannunshi ɗauke da cup sae tiriri ke fitowa daga ciki,bakomai bane aciki face Corn flakes daya haɗo mata,yaji Uwar madara acikinshi,
   Sae faman murmushi yake sakar mata,wuri ya samu daga gefen gadonta ya zauna,sannan yace"reesh ya jikin naki?jiya ko bacci banyi ba saboda damuwa da halin da kike ciki,'
  "da sauƙi junaid,yanzu bana jin ciwo atare dani,na wartsake sosai,amma ina fata kaima kana cikin ƙoshin lafiya ko?naga fuskarka kamar ta canza kamanni,kayi haske sosai kuma fuskar ta ɗan sauya haka,Lips ɗinka sun ɗan kumbura kaɗan kalarsu ta ƙara cizawa sosai'tayi maganar yayin da take ƙare ma fuskar tashi kallo kamar wata malamar duba

  Junaid yace"farin cikin da kika bani jiya shine ya canza mun kamannin fuskata,ko kin manta abunda mu kayi jiya acikin Mota tare da ke?fuskarshi ɗauke da murmushi yayi maganar,
  Cike da mamaki sehrish tace"wane abu kenan?yaushe muka haɗu acikin mota?bayan bakazo ka ɗauke ni daga school ba,ni da ka manta dani junaid,nasha wahala jiya sosai,kamar bazan rayuwa ba,na neme ka na rasa.......'muryarta tamkar zatayi kuka tayi maganar,
  "Sehrish!me kike nufi da banzo na ɗauke ki ba?ko raɗaɗin ciwo yasa kin manta da abunda ya faru jiya atsakaninmu"?
  girgiza kai tayi alamar a'a tace"Nifa bakazo ka ɗauke ni ba,jiya da aka tashi daga school ciwon ciki ya kamani,shine na shiga toilet anan na yanke jiki na faɗi saboda azabar ciwon da nasha,gaba daya nafita hayyaci na.......'gaba ɗaya sehrish ta bashi labarin abunda ya faru da ita tun daga A har zuwa Z,abu ɗaya ne bata sanar dashi ba,shine zuwan waɗan nan matasan guda huɗu da suka ɗauketa a mota,

Tun da ta soma kora mashi bayani,hankalinshi yayi mugun tashi,jikin shi har kerma yakeyi wurin cewa"reesh dagaske ne duk abunda kika faɗamun"!.
  ɗaga mashi kai tayi alamar eh,sannan tace"ka faɗamun me ya hana ka zuwa ka ɗauke ni junaid?nayi tunanin zaka dawo ka ɗauke ni,in kaji shiru ban dawo gida ba,amma bakazo ba,'
  Gaba daya ta gama rikitar dashi duk yabi ya ruɗe,muryarshi har rawa takeyi wurin cewa"wlh nazo jiya school ɗinku,kuma naɗauke ki dakaina acikin motata.......'gaba daya junaid ya kwashe duk abunda ya faru tsakanin shi da jahad ya sanar ma Sehrish,
  Zuba mashi ido tayi tana kallonshi ita kanta hankalinta ba ƙaramin tashi yayi ba da jin labarin da junaid ya bata,
  "Junaid!ban karyata ka ba!amma anya ba gamo kayi ba?zai iya yiyuwa fa aljana ce in ba haka ba,taya za'a ce tana kama dani komai da komai har ka gaza gane cewa ni ce ko bani bace,"?a ruɗe tayi maganar tana kallon junaid,
Junaid sarkin tsoro tuni idanunshi sun cicciko da kwalla tsoranshi kar ace lokacin mutuwar tashi ne yayi shiyasa ya fara ƴan gane gane,zai iya yiyuwa ma mutuwarce tafara kawo mashi ziyara kafin tayi wuff dashi,
  tuna wannan yasa shi fashe mata da kuka yana cewa"innalillahi wa'inna ilaihir raji'un shikenan lokacina yayi sehrish,dama nasan daƙyar zan wuce yau araye,....'
  Hankalinta ba ƙaramin tashi yayi ba,ganin yarda junaid ya fashe mata da kuka,da alama ya tsorata sosai'
  "Junaid ya isa haka,ka daina kuka kaji,insha Allah ba yanzu zaka mutu ba,har sai mun yi aure mun haifi ƴa'ƴa,in ma zamu mutu atare mutuwar zatazo ta ɗauke mu,'
  Jin wannan zancen na sehrish yasa shi yin tsit yana faman sauke ajiyar zuciya,ga dariya na cinta amma tana tsoran karya kuma fashe mata da wani kukan,aranta tace"Tabɗijancan su junaid ansha soyayya da al'jana,da sauƙi ma tunda iya kiss suka tsaya,"
Miƙa mata cup ɗin hannunshi yayi tare da cewa"gashi kisha,corn flakes ne ni na haɗa maki da kai na,"wani irin tausayinshi ne taji ya kamata,musamman yarda ya nuna damuwarshi akanta,har ya haɗo mata cornflakes dakanshi don tasha,'
  zuba mashi ido tayi tana kallonshi,fuskarshi duk a yamutse babu alamun natsuwa atattare dashi,duk ya firgice da jin cewa ba ita bace ya ɗauko a school ba,kuma hankalinshi bazai ta6a kwanciya ba har sae ya tabbatar da cewa ba aljanu bane suka fara kawo mashi ziyara,
  Cikin sanyin murya tace"Junaid,dan Allah ka share hawayenka kaji?ko ka manta da alƙawarin da ka ta6a yi mun na cewa ba zaka ƙara yin kuka ba"?
  Muryarshi akasalance yace"nadaina,kiyi haƙuri bazan ƙara ba," yayi maganar yayin da yake miƙe mata cup din,
  "Ba zaka ban abaki nasha ba"?
ɗagowa yayi yana kallonta jin abunda tace,tayi mashi hakan ne don ta kawar da damuwar dake a fuskarshi,
Matsawa yayi kusa da ita sosai,sannan ya zura hannunshi tare da dauko cokalin ciki,ya ɗebo cornflakes ɗin ya miƙa mata abakinta,
  Buɗe bakinta tayi ya zuba mata aciki,a hankali take murzar shi abakinta tana haɗiyar shi,yayi mata daɗi sosai saboda madarar daya zuba aciki,
Haka yaci gaba da bata abakinta tana sha,tun fuskarshi na aɗaure harya fara sakin wannan murmushin nashi,ganin ya washe daga damuwar da yake ciki yasa sehrish cewa"junaid,Wai jiya Uncle ɗin nan naku ya ƙaraso ne"?
  "Eh,yanzu haka yana acikin gidan nan ma,ya kamata kije ki gaishe su,hada aunty azeema kanwar Abbanmu itama tazo jiya,"
  wani irin farin ciki ne ya lullu6eta cike da zumuɗi tace"inaso naje na gaishe shi,amma ina jin fargabar zuwa wurin shi,"
  Junaid yace"meyasa toh?na gaya maki cewa basu da matsala,uncle dinmu mutun ne mai sauƙin kai fiye da tunaninki,haka Aunty azeemarmu ma tana da mutunci sosai,baki ga gift ɗin da takawo mun ba,zan nuna maki anjima,zaki sha mamaki,"
  murmushi sehrish tayi a lokacin harya kammala bata corn flakes ɗin,
"Bari nashiga toilet nayi wanka,idan na kammala shiryawa sai mu tafi tare da kai ka rakani wurinshi in gaishe dashi,'
Amsa mata yayi da toh,sannan ya miƙe tare da ɗaukar cup ɗin daya ajiye asaman side drawer dinta,ya fuce dashi,

Ajiyar zuciya ta sauke,bayan fitar shi ta sauko daga saman gadon tare da nufar dressing mirrow dinta ta tsaya tana kallon kanta ta cikin madubin,hannu tasa ta shafo sumar kanta da sgr ya datse mata shi,nan take ta tuna da abunda ya faru jiya lokacin daya shigo yi mata allura,wannan kallon da yayi mata ya tsaya mata aranta,da kuma kalaman da ya furta mata cikin sanyin murya,tabbas tana ji aranta cewa sgr ya fara jin abunda take ji agame dashi,duk da tasan cewa zaiyi wuya ya gane cewa akwai soyayya atattare dashi,kuma zaiyi wuya ya iya furta mata ita,
ta cikin mirror ta hango jacket din da sgr ya sanya mata,tana ajiye saman gadon,juyawa tayi cikin sauri tare da kai hannu ta ɗauko rigar sanyin tana kallonta,
  tunani tashiga yi rigar wanene wannan?taya akai tazo bedroom ɗinta kuma asaman gadon nata!?
  ƙamshin Turaren jikin jacket dinne ya bata amsar tambayar da take nema,
Matse rigar tayi a hancinta,anan ta dinga jin ƙamshin turaren Sgr sosai ajikin rigar wannan ya tabbatar mata da cewa tashi ce,a hankali tashiga tunanin ta yadda akai jacket dinshi tazo bedroom ɗinta,kodai jiya ne daya zo yi mata allura.....  '

kwankwasa kopar da akayi ne ya dawo da ita daga zurfin tunanin da tashiga,
  "Wanene"?ta tambaya tana kallon kopar,
Turo kopar azmee tayi tare da shigowa ciki tana cewa"ni ce sehrish,ya jikin naki fatan kin tashi lafiya,tun ɗazu nake ta zarya wurin leƙowa ɗakinki inga ko kin farka daga baccin,amma duk in nazo sai in same ki,kina ta sharar bacci,'
  murmushi sehrish tayi tana kallonta tace"ina kwana Aunty azmee?fatan kun tashi lafiya,ya aiki"?
"Alhamdulillah sehrish,jiya mun shiga damuwar rashinki,kuma sai gashi Allah yasa an gano ki,da ba'a ganki ba,da bansan inda zan sanya raina ba,"ta ƙarasa maganar yayin da take ƙarasa shigowa daga ciki,ta tsaya a kusa da sehrish suna fuskantar juna,
  "Aunty azmee wai meya faru dani jiya?ya akai nadawo cikin gidan nan?waye ya ɗauko ni?kuma naga wannan jacket din asaman gadona,kamar ta babban yaya ce,"
Azmee tace"ae jiya,shi da kanshi ya dawo dake acikin gidan nan,gaba ɗayanmu munyi mamakin ganinshi ɗauke da ke a kafaɗarshi,duk da banji da kyau ba,amma naji yana ba Abbansu labarin cewa acan suka same ki cikin wani garden wasu matasa suna ƙoƙarin lalata maki rayuwarki ..........'tunkan azmee ta ƙarasa maganar sehrish ta tunano da abunda ya faru jiya,sai lokacin komai ya dawo cikin kanta,wani irin farin ciki ne ya lullu6eta jin cewa Sgr ne da kanshi ya taimaki rayuwarta a hannun waɗannan miyagun da suka kai mata hari,kuma taji daɗin bugun da yayi masu,don akan idanunta ya naushi ɗaya daga cikinsu,har haƙoran shi guda biyu suka 6allo daga bakinshi,tun daga sannan ne bata ƙara sanin meya faru ba,amma tabbas taji lokacin daya ɗauke ta a hannunshi ya sanyata acikin motarshi,kuma tana da tabbacin cewa shine ya sanya mata rigar sanyinshi,kilan saboda yaga jikinta na kermar sanyi,
  Cike da farin ciki tace"Aunty azmee lokacin da babban yaya ya shigo dani cikin gidan nan akwai wannan rigar ajiki ne ko"?
  ɗaga mata kai tayi alamar eh,
Washe baki ta shiga yi kamar wadda akayi ma albishir da gidan al'janna,
  Murmushi azmee tayi ganin yarda sehrish ke ta faman murnar jin cewa sgr ne ya taimake ta,
  hannu tasa tare da dafa shoulders dinta tace"Ki shirya yau akwai walima acikin gidan nan,zuwa anjima wuraren ƙarfe huɗu za'a soma gudanar da ita,inaso kiyi kwalliya sosai yau,yanzun nan zan sanya junaid ya kar6o maki kayanki,wlh mantawa nakeyi,'
  "Aunty azmee baki ga abunda babban yaya yayi mun ba?taya zan iya yin gayu da wannan guntun gashi dake akaina"tayi maganar tana damƙo wutsiyar gashin kan nata,
  Sae lokacin azmee ta lura da kan nata,hankali atashe tace"garin yaya hakan ya faru?waye ya yanke maki gashi har haka"?
  "Babban yaya mana,saboda laifin da bani na aikata ba,ya sanya almakashi ya datse mun gashin kaina,banji daɗi ba,saboda nasha wahala wurin tara shi da yawa yanzu bansan ya za'ae nadawo dashi ba,"cike da damuwa tayi maganar,abun har yanzu yana yi mata ciwo,
"Wani laifi kenan kika aikata"?
Sehrish tace"a cikin coffee ɗin da nakai mashi jiya da safe,yana cikin sha,gashi ya sarke mashi a makoshi,ran shi ya 6aci sosai har ya yanke mun gashin kaina,wlh aunty azmee ba gashin kaina bane,ni banta6a yin kuskuren barin kaina abuɗe ba,lokacin da nake acikin kitchen,"
  shiru Azmee tayi na dan wani lokaci kafin tace"bakomai kawai,kiyi haƙuri nasan kowanene ya aikata hakan,amma banaso ki sanya damuwa aranki,"
  "Shikenan,yanzu bari naje nayi wankan,"ta ambaci hakan tare da ajiye jacket ɗin asaman gadon,
  "Kinason ƙunshi ne?idan kina ra'ayi zan zana maki da kaina na iya sosai,"
  "Inaso sosai Aunty azmee,yaushe rabon dana ga lalle a hannu na har na manta wlh,"
Azmee tace"yanzu kije kiyi wankan,kafin dai zuwa ƙarfe huɗun zamu kammala komai,'
  ta ƙarasa maganar tare da juyawa ta fuce daga cikin ɗakin,
  Wuce wa cikin toilet sehrish tayi domin yin wanka

💋Boss Bature💋

Zaune suke acikin mota su biyu,Ayaan ne ke driving ɗinsu yayin da jahan ke zaune gefen shi sae faman buga tsoki yake yi yana cewa"Ayaan wai ina zaka kaimu ne!ni fa gida nace maka mu koma,banaso afara shagalin walimar nan,bana a kusa,'
  Murmushi ayaan yayi tare da cewa"kai dai kawai ka zuba ido ka gani,wani abun mamaki ne nakeso na gwada maka,nasan cewa zai girgiza ka sosai,'ya ƙarasa maganar yayin da yake shigar da motar tasu gate din gidan Yayansu Abbas,
Jahan yace"wai dama nan zaka kawo mu?muyi me kenan?Anya kuwa ayaan kasha maganinka na safe kuwa?
  dariya Ayaan yayi tare da cewa"a'a ban kaiga sha ba,amma yanzun idan nakai ka cikin gidan nan,na nuna maka abunda nakeso ka gani,bayan mun fito zaka faɗamun ni dakai waye mai buƙatar shan magani acikin mu,"cike da zolaya Ayaan yayi maganar,
shiru jahan yayi bai ƙara cewa komai ba ya zuba ma sarautar Allah ido,
  Bayan Ayaan yayi parking ɗin motar,ya fito tare da zagayawa ya buɗe ma jahan motar tare da nuna mashi hanya da hannunshi yace"mun ƙaraso yalla6ai,"
harara jahan ya watsa mashi tare da zura ƙafafunshi ya fito daga cikin motar,yana faman ɗaure fuska ya wuce gaba ayaan yabi bayanshi suka shiga cikin gidan,
  Da sallama abakunansu suka shiga cikin babban falon gidan,a lokacin Amani na a cikin kitchen tana aikin breakfast,jin sallamarsu twins yasa ta fitowa da sauri don taga su wanene,
  Ba ƙaramin mamaki tayi ba,ganin ayaan da jahan atsaye ruƙe da hannun juna,
Ƙarasawa wurinsu tayi fuskarta ɗauke da murmushi tace"Sannunku da zuwa,ashe kune sam banyi tsammanin ganinku ba,"
  Kawar da kai gefe jahan yayi batare da yace komai ba,.
  Ayaan yace"yawwa Aunty amani,kun tashi lafiya,fatan mun same ku lafiya?
  Ta amsa mashi da cewa"Lafiya lou Alhamdulillah,nayi farin cikin ganinku,ku ƙaraso daga ciki mana,"
Jahan yace"sauri muke zamu wuce,Ayaan ka shiga daga ciki ku gaisa ni zan jiraka a mota,'yayi maganar tare da juyawa zai fuce,
  Cikin sauri Ayaan ya ruƙo hannunshi tare da cewa"haba jahan wai menene haka?just 15 mins zamuyi fa kafin mu wuce gida,'
  ɗaure fuska jahan yayi alamar an takura mashi,
  Amani kuwa murmushi kawai tayi,tana mamakin yarda suka kasance twins komai nasu iri daya,amma hali ba iri ɗaya ba,Ayaan ta 6angaren Abbansu yake,shi kuma jahan sak mommynsu ce,
  daƙyar Ayaan ya samu jahan ya bisu suka shiga cikin falon,atare suka zauna saman 3 seater,ita kuma ta zauna saman 2 seater tana fuskantar su,yarda jahan ke ta faman yatsina fuska,ba karamin dariya yaso ya bata ba,ji yake kamar ya ɗosana ass ɗinshi asaman ƙayoyi haka yake ji,

Ayaan ne ya soma magana"Aunty amani kinji mu shiru ko?ba mu sake zuwa mun duba jikin Amal ba,ban ji daɗi ba wlh abubuwa ne sunyi mana yawa,amma tana aran mu,shiyasa ma muka yanke shawarar zuwa yau mu duba ta,'
taji daɗin kalaman ayaan sosai,fuskarta ɗauke da murmushi tace"Amal taji sauƙi sosai,kullum sai ta tambayeni ina twins ɗin nan suke,musamman kai Ayaan tafi tambayarka saboda kaine ka kawota wurina,yanzu bari naje na kawo maku abun ta6awa,kafin na kira maku Amal ɗin ku gaisa,"
Ta ƙarasa maganar tare da mikewa ta wuce cikin kitchen,
Tana barin wurin jahan ya buga tsoki tare da cewa"Wlh ayaan ka bani haushi!ka zauna ka gama tsara mata ƙaryar cewa mun zo duba jikin wannan ƙarmasasshiyar yarinyar ne,yarinyar da nama manta da zancen ta ni,mtswwww,'ya kawar da kanshi gefe yana hura hanci,
Ayaan yace"Am sorry bro,nasan ban kyauta ba,amma kayi hakuri kasan banason 6acin ranka,ni aganina bamu kyauta ba,tun ranar da nakawo yarinyar nan,ba mu ƙara zuwa mun dubata ba,kuma abunda ya dace ace munyi ne,"
ta6e baki jahan yayi tare da kallonshi yace"sannu ko?sarkin tausayi,"
Jin takun tafiyar Amani ne yasa su kayi shiru,ƙarasowa ciki tayi hannunta ɗauke da tray,cups ne guda biyu,sae lemu masu sanyi acikin roba tare da plate na snacks,asaman table ta ajiye masu sannan ta juya tana cewa"bari na kira Amal din ku gaisa,"
ɗaukar lemun ayaaan yayi tare da buɗe shi ya tsiyaya masu acikin cup,ya dauki ɗaya ya miƙa ma Jahan,ya kar6a sannan shi kuma ya ɗauki ɗayan,yana sha,

Saukowa amani tayi daga upstairs,ta dawo wurinsu ta zauna saman sofa din tana cewa"gata nan zuwa,"
Ayaan yace"Allah ya kawota lafiya,"

Gaba daya sun mayar da hankalinsu wurin shan Lemun dake hannunsu,su ka jiyo takon takalminta,kwas kwas,
Ayaan ne ya fara ɗago da ido yana hangen yarinyar dake saukowa daga saman benen,juyawa yayi ya kalli amani tare da yin ƙasa da murya yace"ita ce ko"?
.murmushi amani tayi tare da daga mashi kai alamar eh,
Satar kallon jahan yayi wanda hankalinshi ba a kansu yake ba,
A hankali Amal ta ƙarasa saukowa daga saman benen ta nufo inda suke,lokacin da ta ƙaraso wurinsu fuskarta ɗauke da murmushi tace"sannunku da zuwa,"
Kai tsaye muryarta ta daki dodon kunan Jahan,daɗin muryarta ne yasa Jahan juyowa cikin sauri don yaga wacece,ai yanayin arba da wannan kyakkyawar fuskar ta Amal nan take ya saki Cup ɗin dake hannunshi ƙasa,ya tarwatse lemun ciki ya zube,
A gigice ya miƙe tsaye yana kallonta yayin da zuciyarshi ke bugawa da ƙarfi da karfi,yarda kasan hurool aini awurin kyau haka yarinyar ta koma mashi,
fara ce tass,har ma tafi Amanin haske,fatar jikinta har wani ƙyalli takeyi saboda gyaran da tasha,tabarakallah masha Allah ta ko'ina amal ta haɗa,ga manyan idanun nan nata dara dara dasu,ga dogon hancin nan nata kamar zaiyi sujjada,la66anta kuwa sunyi red colour sosai tamkar ta shafa janbaki,idan tayi murmushi kamar gonar auduga saboda hasken haƙoranta,lallai ba ƙaramin gyara Amani tayi ma ƙanwarta ba,ta canza mata kamanni sosai,ta fito a balarabiyarta,sleeping dress ne ajikinta pink colour riga da wando,ta yafa gyale fari asaman kanta,
dare ɗaya Allah kanyi bature,acewar ayaan,
Ina labarin Jahan daya miƙe tsaye ya zuba mata ido yana kallonta ko ƙyaftawa baiyi,abun tamkar a mafarki yake kallonshi,gaba daya ya gama ruɗewa,muryarshi na rawa yace"ke!kece!'cike da mamaki yayi maganar,
Amal kuwa aɗan tsorace taja baya,tana faman zazzare mashi kyawawan idanunta,ganin yarda ya harzuƙo kamar zai rufe ta da bugu,
murmushi kawai Amani ke saki ita da ayaan suna kallonshi,dama wannan duk shirin Ayaan ne,
"Aunty amani!surgery akayi mata ne?if not taya akai tayi transforming haka"? A ruɗe jahan ke tambayarta,
miƙewa tsaye amani tayi tare da takawa zuwa inda suke ta ruƙo hannun Amal tana cewa"ikon Allah ne jahan,babu wani surgery da akayi mata,gyarane kawai tasha,dama can Amal kyakkyawa ce,wannan asalin kamannin fuskarta ne ya dawo,'
Jiki asanyaye Jahan ya koma tare da zaunawa saman sofa din,har lokacin bai janye idanunshi daga kallon fuskar Amal da yake yi

Chapters

Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login