Showing 126001 words to 129000 words out of 432432 words
Chapter 43 - Abban Sojoji Book 2 Hausa Novel Complete
part ɗinsu,
..cikin sauri sehrish tace"ka manta baka ban shawarar da kace zaka bani ba,"
dakatawa yayi da tafiyar batare da ya juyo ba yace"ku dage da addu'a," yana fadin hakan yasa kai ya wuce ciki,
Tsayawa tayi cike da zullumin maganar haroon nacewa su dage da addu'a,tana cikin wannan yanayin muryar Azmee ta katse ta da cewa"Sehrish!tsayuwar me kikeyi anan ne?nayi tunanin zan zo na same ki a cikin kitchen,'
cikin sauri sehrish ta nufe ta,tana cewa"yanzu nake ƙoƙarin shiga kitchen ɗin,wani abune ya ɗauke mun hankalina,"
Atare suka shiga kitchen ɗin,batare da 6ata lokaci ba suka soma aikace aikacen girke girken nasu kamar yarda suka saba,
Tun bayan da azmee takai hayaam ɗaya daga cikin bedroom ɗin da suka saba ajiye baƙi insun zo,zame hijab ɗin jikinta tayi,wata ƴar short gown ce ajikinta daidai guiwarta,kai tsaye toilet ta faɗa,bayan wasu ƴan mintina sai gata ta fito waist ɗinta ɗaure da towel,sai lokacin ta tuna cewa ashe tabar trolley ɗin kayanta acikin boot ɗin motar Sofwan,yanzu dole ta neme shi ko don ya kawo mata abunta,
ƙarasawa tayi tare da hayewa saman gadon ta zauna,sannan takai hannu tare da ɗauko purse ɗinta da ta ajiye asaman gadon tun shigowarta tare da Hand bag ɗinta,
wayarta ta ciro anan taga missed calls na Aunty babba har kusan uku,
Murmushi ta saki tare da bin kiran nata,wayar na fara ringing Aunty babba ta ɗaga,.
kara wayar a kunnanta tayi tare da cewa"Auntyna takaina!yanzun nan naga missed calls ɗinki,banji ma da fitowa daga toilet ba,
on the other hand aunty babba tace"kin isa gidan ne!"?
Hayaam tace"eh,yanzu hakama gani asaman gadona inaso nayi bacci don na rage gajiyar dake ajikina,amma fa aunty nasha wahala kafin nasamu shiga cikin gidan nan!"
Aunty babba tace"wahala?kamarya kenan?
Nan hayaam ta kwashe duk abunda ya faru a wurin shigowarsu cikin gidan ta sanar mata,
uban tsoki aunty babba ta saki tare da cewa"Ke kika ban haushe wlh!taya zaki tsaya yi masu kwatance cewa ke ƙanwa tace?to menene alaƙar dake tsakani na dasu ne da har zasu shaidaki!tun a lokacin yakamata ki kirani awaya sai inyi ma wani magana daga cikin gidan akan yayi masu magana su barki ki shiga,amma don kince hayaam ƙanwar matar yayansu,to koni nan da kike gani Sgr baisan sunana ba,bare har yasan naki sunan hayaam,wannan mutumin ma bana tunanin yasan kamannin fuska ta nikaina,"
yatsina fuska hayaam tayi tare da cewa"aunty inaso in kwanta bacci nake ji,"
. Aunty babba tace"to shikenan!kardae ki manta da abunda yakai ki cikin gidan,so nake kafin sati mai zuwa naji ana zancen bikinki da Sgr,kafin shekara mai zuwa kuma inji kukan jariri,"
Fashewa da dariya hayaam tayi jin abunda Aunty babba ke cewa,
Sun jima suna waya kafin daga bisani sukayi sallama,wurgi da wayar tayi gefe guda sannan ta kwanta asaman lallausan bedmattress ɗin,nan take bacci yayi awon gaba da ita,
**********************
Abun da ya faru bayan barin Amal gidan,wuraren bayan sallar la'asar mammy da Abra suka shigo cikin gidan,jikinta na sanye da hijabi abra kuwa atampa ce ajikinta ta aza mayafin asaman kafaɗarta,sai faman fira suke yi atsakaninsu,
"Mammy yanzu me zakiyi da kuɗin nan da sofwan ya baki?naga kamar suna da yawa,dama akwai ankon bikin wata ƙawata da nakeson yi,kinga sai ki aramun dubu takwas aciki inyi amfani dasu,"
. tsuke fuska mammyn tayi tare da cewa"matsalarki kenan!daga kinga wani ya bani kuɗi sai ki bijiro da maganar anko,tun wuri ma ki fidda rai don ko sisi bazan baki acikinsu ba,malam zan kaima cikon kuɗin shi sannan sauran ni zanyi amfani dasu,ko ɗan farfesu naman nan an samu ayi,dama na kwana biyu ban sha ba,
ta ƙarasa maganar a lokacin da suka ƙarasa tsakiyar filin gidan,.
Rai a6ace abra tace"mammy kalli kiga fa har yanzu yarinyar nan bata fito daga ɗakin ba,ko ubanwa takeso ya ɗaura mana girki?gidan ma ko share shi ba tayi ba!
cike da masifa mammy ta shiga kwaɗa mata kira"Amal!!Amall!!don ubanki kina ina ne?bazaki fito kiyi mana aikin cikin gida ba!
Jin shiru bata amsa masu ba,yasa mammy ce ma Abra"maza kije ki tashe ta,ta fito tayi mana aiki,ko tasha na jaki,"
Kama hanyar ɗakin nasu abra tayi har ta kusa shiga ɗakin,ta tuna wata mugunta,cikin sauri ta juya tare da nufar fanfon cikin gidan,ƙaramin bokiti ta ɗauka na plastic ta ciko shi da ruwa sannan ta wuce dashi ɗakin a hannunta,
Murmushi mammy tasaki tare da cewa"haka nakeso,ƴa'ƴana su dinga koyi dani,"ta faɗi hakan tare da sa ƙafa ta wuce cikin ɗakinta,
ae tana shiga cikin ɗakin ta aza idonta akan gadonta inda tabar kuɗin da sofwan ya bata nan taga wayaam babu komai a wurin,hannu tasa tare da murza idanunta don ta tabbatar da abunda idanunta ke nuna mata,again ta kuma ganin wayaam babu komai asaman gadon,
Cike da mamaki tace"wai ba nan na jiye kuɗin da sofwan ya bani ba?kodai na jefa su wani wuri ne bansani ba!
ta faɗi hakan tare da sanya hannu ta zame zanin gadon tana kakka6e shi wai koda zata ga kuɗin a ƙasan shi,nan ma babu,
Cikin sauri ta zuƙunna tare da zoƙa kanta tana leƙen ƙasan gadon koda sun faɗo sun shige ƙarƙashin gadon,nan ma wayaam babu su,
Hankali atashe ta miƙe tana tafa hannu ranta ajagule tace"To wai kodai kuɗin nan ƙafafu ke gare su ne?in ba haka ba taya akai suka bar saman gadon nan!nifa nan na ajiyesu ban canza masu wuri ba,"
Lokaci guda tabi ta rikice ta rasa natsuwarta,saboda mace ce mai shegen son kuɗin tsiya,har faɗi take da naira biyar ɗinta ta faɗi kwara haƙorinta guda ya cire,
Acan kuwa bayan Abra tashiga cikin ɗakin da Amal take,sam bata lura babu mutun asaman katifar ba,saboda yarda shape din bargon ya bada kamar akwai mutun acikin shi,
Ciza le6anta tayi tare da cewa"ƴar jakar uba,yau zaki gane kuranki,wato banza tasamu tun jiya kike ja mana na rago asaman katifarmu duk kin 6ata mana katifarmu da yawun bacci,yanzu zanyi maganinki,ƙazama kawai
ta ƙarasa maganar tare da ɗaga bokitin ta kwarara ruwan asaman bargon tana faman 6a66aka dariyar mugunta,abun mamaki shiru babu alamar Amal zata saki ihun jin saukar ruwa ajikinta,.
Hakan yasa dariyar abra ta soma komawa ciki,ganin yarda bargon ya lafe ajikin katifar,yasa ta gane cewa babu mutum asaman katifar,
Hankali atashe ta saki bokitin ƙasa tana faman kwala ma Amal kira,
Shiru bata amsa ba,cikin sauri ta fito tana nemanta a tsakar gidan,babu inda bata duba ba daga kitchen har cikin toilet ɗinsu duk bata nan,
da gudun gaske ta koma ɗakin mamynsu a firgice mammyn ta ɗago tana kallonta ganin yarda ta faɗo mata yasa tace"Abra lafiya meke faruwa ne"!
Muryarta har wani shakewa takeyi wurin fadin"Mammy!babu Amal acikin gidan nan!Amal ta gudu!dama saida raina ya bani cewa zata iya guduwa,'
jin hakan yasa mammy cewa"hakan na nufin itace ta kwashe kuɗin da Sofwan ya bani?
"Mammy dagaske baki ga kuɗin ba!aiko indae hakane toh Amal itace ta kwashe kuɗin,innalallahi bansan ya akai wannan daƙiƙiyar yarinyar har tayi tunanin guduwa ba,ina mata kallon shashasha....'
Katse ta mammy tayi da cewa"amma shegiyar yarinyar nan ta gama dani wlh!naci buri akan kuɗin nan,maimakon ta gudu tabarmin kuɗin shine ta haɗa dasu ta gudu,insha Allah a wulaƙance rayuwarta zata ƙare,Allah ma yasa kidnappers su ɗauketa su kwace kuɗin,sannan su lalata rayuwarta....."
"Subhanallahi!!me nake ji haka!"
Muryar Abbansu Abra ce ta karaɗe kunnansu,shigowarshi kenan cikin gidan ya same su suna ta tsinar Amal,
wani koɗaɗɗen mutum ne,tamkar baya a cikin hayyacinshi haka zubin shi yake,tsohon yadi ne ajikinshi duk yayi uban squeezing,kamar kanshi farau talauci,
ƙarasawa bakin kofar dakin yayi yana tambayar lafiya menene ya faru,
Tsawa mammy ta daka mashi tamkar ba mijinta ba haka tashiga ɗura mashi zagi
"Munafukin banza,munafukin wofi kazo kaji abunda muke tattaunawa ne!Anya bakaine kayi ma Amal hanyar guduwa daga cikin gidan nan ba!wlh ban yarda dakai ba!ka faɗamin gaskiya taya akai Amal tabar cikin gidan nan!?don nasan hakanan banza Amal baza tayi tunanin barin gidan nan ba!dole da taimakon wani,
Tuni yasha jinin jikinshi,saboda mugun tsoranta yake ji,gaba daya ta gama asirce shi,shiyasa baida ikon yin komai sai da Umarnin ta,
tsawa ta daka mashi tare da cewa"ba zaka faɗamun gaskiya ba!taya akai amal tabar gidan nan!
Zuru yayi da ido sai faman kyafta ido yakeyi yana mazurai kamar mara gaskiya,
tsoki abra taja tare da cewa"mammy dama kin daina wahalar da kanki,Abba bai ma da cikakken hankalin da zai iya taimakon Amal wurin barin gidan nan!6ata mana lokaci kawai zaiyi,ni ina ganin ki fito kawai muje mu nemo ta acikin gari,
harara Mammy ta watsa mashi tare da fitowa daga ɗakin ita da Abra suka kama hanyar fita daga gidan,
Bayan sun fuce daga cikin gidan,matsawa abi yayi tare da kai hannu ya ɗauki kujera ƴar tsugunno ya zauna asamanta,
Muryar Amal ya tuna acikin kunnan shi,ashe sun haɗu da ita akan hanya sai faman sauri take yi tamkar zata tashi sama,kamar daga sama taji an ruƙo mata rigar jikinta a firgice ta juya tana kallon shi,ganin Abbansu ne yasa ta fashe da kuka don tasan cewa zai iya mayar da ita gida,cikin shessheƙar kuka tace"Abie nasan inda Aunty amani take,bazan cigaba da zama acikin gidan nan ba,kana gani zasu kashe ni,amma ba ka iya tsawatar masu akan su daina cutar dani,dan Allah Abie kabarni in tafi,kada ka sanar ma mammy cewa ka ganni akan hanya,ka nuna cewa bakasan komai ba,"
tsananin tausayinta ne ya kama shi,nan take yaji cewa zai iya taimakonta gudun karta faɗa hannun mutanen banza,tun da ƙaramar yarinyace mai ƙananun shekaru tsaf za'a iya yi mata wayau,
"Kiyi haƙuri Amal akan dukkan abunda ke faruwa,nima bada son raina bane,bani da yarda zanyi ne gaba daya mammy ta addabi rayuwata,ta hanani dukkan wani farin ciki na rayuwata,tun bayan da Allah yayi ma mahaifiyarku rasuwa ban ƙarasamun kwanciyar hankali ba,komai na duniyar nan ya fita raina Amal,mammy ta jima tana cutar da rayuwata da kuma rayuwarki,yanzu ina da kwarin guiwar iya taimaka maki!dama abunda yasa tuntuni banyi hakan ba saboda bani da ikon yin magana dake acikin gidan,inaji ina gani an rabani da ƴata kuma ana cutar da ita akan idona,babu komai akwai ranar sakayya,"
Yana kai karshen maganar tashi ya ruƙo hannun Amal tare da janta suka tafi,da kanshi yakaita tasha sannan ya damƙa ma drivern amanarta,kasancewar drivern ɗaya daga cikin abokanshi ne ana mutunci sosai,agaban motar drivern yayi mata wuri ta zauna kusa dashi,
Sai lokacin drivern yake tambayarshi inda zasu sauke ta a abujan,shi kanshi abie baisan inda amani ke zaune ba acan,
Cikin sauri Amal tace"ina da numbar wayar Aunty amanin,idan mun isa sai ya kira mun ita awaya,nasan zata zo,"
Murmushi abie yasaki yana tsaye daga waje yashiga tofa mata addu'o'i tare da yi masu fatan sauka lafiya,
tuni Amal taji hawaye sun wanke mata fuskarta,ji take kamar ta fito daga cikin motar tabi mahaifinta,haƙiƙa ta tausaya mashi sosai,haka ta dinga jin raɗaɗi azuciyarta har motar tasu ta kusa barin tashar,ya jiyo muryar Amal tana kwala mashi kira,
"Abie!!Abie!!"
da saurin gaske ya ƙarasa inda motar take,kowa na cikin motar tsayawa yayi yana sauraron muryar yarinyar,
murmushi ta sakar mashi,tare da zura hannu cikin aljihun rigar Abra dake ajikinta,zaro kuɗin nan tayi kusan dubu arba'en,sannan ta zura hannunta ta saman glass ɗin murfin motar ta miƙa mashi su,
ganin ya tsaya yana kallon kuɗin yasa tayi saurin cewa"Abie dan Allah kada ka tambaye ni ina nasamu kuɗin,in dai ka yarda dani to ka kar6a kawai nasan kana buƙatarsu,"
Murmushi yayi tare da sanya hannu ya kar6i kuɗin,sannan a hankali glass ɗin ya soma dagawa sama,
Tana jiyo muryarshi yana cewa"ki kula mun da kanki,sannan in Allah ya haɗaki da ƴar uwarki Amani,ki gaishe mun da ita,kice Abbanta yana gaishe da ita sosai,
har motar tabar tashar Amal bata daina leƙenshi ba ta glass ɗin motar,haka zalika shima yana atsaye yana kallon motar tasu,har sai da ta 6ace ma ganin shi,sannan ya haƙura ya juya tare da kama hanya ya soma tafiya yayin da idanunshi ke akan hannunshi yana kallon kuɗin da Amal ta bashi,
Ba ƙaramin daɗin kuɗin nan ya ji ba,yaushe rabon daya ruƙe naira dubu tashi ta kanshi harya manta,ba damar ya samu kuɗi yashiga gidan shi,da zarar mammy ta gani zata amshe kuɗin,ko sisi bata son taga ya ruƙe a hannun shi,tafi son taganshi a matsiyacin shi yana yawo,wannan ba damuwarta bace,
Sanin cewa zata iya ganin kuɗin a hannunshi ta kwace mashi su hakan yasa baiyi gangancin zuwa gidan dasu ba,kai tsaye ya wuce wurin wani abokin shi mai siyar da nama abakin hanya,wuri yasamu ya zauna bayan sun gaisa ya bashi ajiyar kuɗin duka,sannan yace ya zuba mashi naman na dubu uku yaci,bai bar wurin ba sai da yaci ya ƙoshi sannan sukayi sallama da mai naman ya wuce gaba,
Murmushi abie ya saki bayan ya kammala tunanin nashi yace"Allah sarki Amal!kin taimaki mahaifinki,ba don ta bani kuɗin nan ba,da yau haka zan kwana da yunwa,"
Mammy da abrah tamkar zasu yi hauka wurin neman Amal,gida gida haka suka dinga bi suna nemanta,saƙo da lungu ba inda basu duba ba,har bayan sallar magrib suna waje wurin nemanta,a ƙarshe dasuka gaji agalabaice suka koma gidan suna faman haki kamar waɗanda suka sha gudu,tun acikin zauren gidan mammy ta yanke jiki ta faɗi a sume,saboda tsabar baƙin cikin Amal data gudar mata da kuɗinta,
. hankali atashe abra tashiga zabga ihu tana kuka tana ambaton sunan mammy,
Da alama dae mammy sai anyi jinya,
****************************
Around 11pm,
fitowa tayi daga cikin toilet jikinta na sanye da sleeping dress riga da wando,white colour,da alama tayi shirin kwanciya,tun acikin toilet take jin wayarta na ringing,hakan ne ma yasa tayi hanzarin fitowa,ƙarasawa tayi cikin sauri tare da kai hannu ta ɗauki wayar dake ajiye asaman mirror,duba sunan mai kiran tayi,ganin baƙuwar number yasa taƙi ɗaga kiran,sai tayi rejecting ɗin kiran,kafin ta ajiye wayar sai ga wani kiran ya ƙara shigowa na baƙuwar numbar,
Cike da mamaki tace"Wai wanene ke kirana a irin wannan lokacin,kuma da bakuwar number,salon ajamun bala'e,bari dae in ɗaga inji,picking call ɗin tayi tare da karawa a kunnanta,muryar namiji ce taji ya zabga mata sallama,aikuwa cikin sauri ta katse kiran tana faman dafe saitin zuciyarta,ta tsorata da jin muryar me kiran nata,koma wanene ba ƙaramin mutum bane,
tsayawa tayi tana tunanin wa tasani da wannan muryar,bata ta6a jin mai irinta ba,
tana cikin wannan yanayin sai ga message ya shigo cikin wayarta,cikin sauri takai hannu tare da janyo saƙon daya shigo daga saman screen din wayar tashiga karantawa kamar haka
_baiwar Allah,ina ta kiran wayarki kin ƙi ɗagawa,dama ƙanwarki Amal ce ta ban numbarki don na kira na sanar dake cewa kizo ki ɗauke ta,ni ne drivern daya kawota abuja,idan ba damuwa ki kira kuyi magana da ita,don kiji muryarta_
Wani irin bugu zuciyarta tayi,cikin tsananin mamaki tashiga maimaita sunan Amal,muryarta na kerma tashiga cewa'Amal!wata Amal yake nufi!ko dai Amal ƙanwata!!!
Cikin sauri ta danna ma numbar kira,yatsun hannunta har kerma sukeyi don aƙagare take da taji bayanin mutumin daya turo mata saƙon...........
Pls read this👇👇👇
*Assalamu Alaikum,barkanmu da juma'a fatan kowa na lpy,yauwa inaso indan yi wani karin haskene,aduk lokacin da bansamu yin update ba har ranar ta wuce ina kokarin ganin nayi long page don yayi covering da wanda bansamu yi ba,nasan wasu sun fahimci hakan,yayin da wasu kuma basu fahimci hakan ba sai suyi ta maganar page kaza yakamata inyi tunda banyi na rana kaza ba,duk page da nake saki yafi ƙarfin page guda a ƙa'idar page,ina haɗe 2 pages ne sometimes ma yana haura 2 pages, Shiyasa in na sanya short page wasu ke complain saboda sun saba ganin long page,sannan ban kin yin typing sai don uzurin da ba yadda zanyi,da fatan zaku fahimce ni,sannan akwai masu maganata abayan idona nacewa wai ina jan littafi? Allah sarki rashin sani yafi dare duhu,bani da wani burin daya wuce inga na kammala littafin nan ayanzu saboda abubuwa da sukayi mun yawa,bani ke jan littafin nan ba!bada son raina ba kuma hakana ke faruwa ba!yanayi ne dake nake ciki,yakamata mutane su dinga yi mun uziri bai kamata arinƙa yi mun irin waɗannan maganganun ba,duk wanda kuma yake yi Alhakina na akanshi, wai wasu ma har cewa suke yi don naga littafinna yasamu kar6uwa mutane naso. shiyasa nake jan labarin,wlh dana ji wannan maganar kamar na fasa ihu don takaici, hmmmm babu komai akwai Allah,to my real fans nagode kwarae da hadin kai da kaunar littafi na da kuke,godiya mara adadi kuci gaba da yi mun uziru kuma acigaba da yi mun addu'a,shine kawai insha Allah komai mai wuce wane,Littafin nan inaji araina cewa kammaluwarsu tazo zanyi ƙoƙarin tabbatar da hakan!insha Allah*�?
*SANARWA SANARWA*💃💃💃💃
*ME TAKEN NA AMARYA HUTAA$$*
*MUNA FARIN CIKIN SANAR DAKU CEWA MUNA BADA HAYAR KAYAN AMARYA(WEDDING GOWN), KAYAN BRIDAL SHOWER, KAYAN BIRTHDAY PARTY, KAYAN FITAR SUNA, SANNAN MUNA BADA HEAD AND SHOULDER, MUNA DA POSS, MUNA ALKYABBAR KAI AMARYA KO TARON WALIMAR SAUKA, MUNA DA KAYAN FULANI FARARE NA YARA DANA MANYA MUNA DA NA AMARYA BLUE BLACK, SANNAN MUNA GYARAN JIKIN AMARYA DA UWARGIDA CIKIN KWANA UKU CAKAL ZAKIGA KIN KOMA TAURARUWA MAI WALWALI. MUNAYIN TURARUKAN WUTA DA HUMRA DA KOLACCAR, KOWANNE KALA KIKE BUKATA AKWAI CIKIN FARASHI MAI SAUKI.*
*LOCATION KANO*
08062073990
Ina kuke mata hamshakai wayanda suka amsa sunan su wajen mazajen su ina mata masu son qamshi shin ko kunsan tsafta bata tafiya seda qamshi ina masu son turare mai riqon gida tareda qamshin shi mai sanyaya zukata mardie collection tazo muku da dadadan turarukanta masu lasting riqon gida harma da jiki ku tuntube mu da nmb kamar haka 08136666994 inda zaku samu kaya kamar haka
Wadrobe balls
Madarar kulleccham
Vaseline kulleccham
Kajiji
Halut
Couscous
Khumrah
Da dai sauransu harda abin wanke toilet yayi tas komi dafe warshi wato BETHALEX METAL ku garzayo kar ayi baku
Ina kuke mata hamshakai wayanda suka amsa sunan su wajen mazajen su ina mata masu son qamshi shin ko kunsan tsafta bata tafiya seda qamshi ina masu son turare mai riqon gida tareda qamshin shi mai sanyaya zukata mardie collection tazo muku da dadadan turarukanta masu lasting riqon gida harma da jiki ku tuntube mu da nmb kamar haka 08136666994 inda zaku samu kaya kamar haka
Wadrobe balls
Madarar kulleccham