Showing 198001 words to 201000 words out of 432432 words
Chapter 67 - Abban Sojoji Book 2 Hausa Novel Complete
wurin da suke,da alama ya kammala wayar da yake yi,wuri ya samu ya zauna yana fuskantar sehrish,daga ita har shi ba wanda ya lura da wani,
Gyaran muryar da Abba yayi mashi ne yasa shi ɗagowa yana kallonshi yace"meya faru ne yaya"?
Da ido yayi mashi nuni da sehrish yace"baka ganta bane,"
A hankali Abusufyan ya mayar da idanunshi kan sehrish dake zaune tana faman wasa da yatsun hannunta,gabansa ne yayi wani irin mugun bugu ji kake daram!!!a gigice ya miƙe tsaye hankali tashe yake kallonta,
Miƙewa Abba yayi yana kallonshi ganin yarda ya tsorata da ganin yarinyar,
Sehrish kuwa tuni ta firgita da ganin yarda Abusufyan ya razana da ganinta,hankali atashe itama ta miƙe tsaye tana kallonshi ido cikin ido,
Gaba daya fa kowa na falon ya miƙe yana kallon ikon Allah,duk atunaninsu uncle din nasu ya kamu ne shiyasa ya firgita da ganinta,
jikinshi har kerma yakeyi wurin nunata da hannunshi,ƙoƙari yake yi ya ambaci sunanta amma sam ya kasa faɗin sunan,saboda ya kakare mashi,wata irin zufa ce ta shiga gangarowa daga gafen fuskarshi,wannan abun ba ƙaramin ɗaure masu kai yayi ba,
Adai dai wannan lokacin Sgr da Marshal Omar suke saukowa down stairs atare,Omar ne agaba jikinshi sanye da shadda maroon colour,yayin da Sgr ke sanye cikin riga da wando na lallausan voile baƙi,wa'iya zubillah wato tsayawa bayyana irin yarda yadin yayi mashi kyau ma 6ata baki ne,don zan iya karashe littafin nan gaba ɗayanshi wurin kwatanta haɗuwar da sgr yayi acikin boyel ɗin wanda akai ma dinkin Senator style,irin style din da rigar bata karasa kaiwa gwiwa ba yayin da wuyan ke a matse sannan hannun rigan ya dan wuce gwiwar hannunshi kadan,yayin da takalman kafarshi da agogon hannunshi duk launi ɗaya ne da boyel ɗin jikinshi,bai sanya hula ba akanshi,sai dae ya ɗaure sumar kan tashi,a tsakiyar kanshi,hakan ba ƙaramin kyau ya ƙara mashi ba,wani irin daddaɗan kamshi ne ke fitowa daga saƙo da lungu na jikin kowannan su,fuskar nan tashi kamar ya aza mata makeup saboda tsabar kyan da tayi,yadin ba ƙaramin fito da hasken fatar shi yayi ba,yayi fari sol dashi,kamar asace don kyau,yarda kasan diamond haka ya koma,tauraro mafi haske acikin taurari.
cike da wannan tafiyar tasu ta majiya karfi suka ƙarasa saukowa daga saman benen,
Adai dai lokacin wayar Omar ta shiga ruri,hannu ya zura tare da curota daga cikin aljihun wandon shaddarshi,ganin sunan major ya bayyana akan screen din wayar yasa shi picking call ɗin ya kara wayar a kunnan shi tare da cewa"kun ƙaraso ciki ne?
On the other hand major yace"Eh,yalla6ai yanzu haka mun ƙetaro babban gate din gidan tare dasu,yayi maganar yana kallon su hosana dake zaune a back seat ta cikin mirror din gaban motar,fuskokinsu dauke da farin ciki yau zasu ga Sehrish ɗinsu,
Omar yace"Okey,ka shigo dasu kawai,"yana fadin hakan ya katse kiran sannan ya bi bayan Sgr suka ƙarasa cikin main palour din.
*SANARWA SANARWA*💃💃💃💃
*ME TAKEN NA AMARYA HUTAA$$*
*MUNA FARIN CIKIN SANAR DAKU CEWA MUNA BADA HAYAR KAYAN AMARYA(WEDDING GOWN), KAYAN BRIDAL SHOWER, KAYAN BIRTHDAY PARTY, KAYAN FITAR SUNA, SANNAN MUNA BADA HEAD AND SHOULDER, MUNA DA POSS, MUNA ALKYABBAR KAI AMARYA KO TARON WALIMAR SAUKA, MUNA DA KAYAN FULANI FARARE NA YARA DANA MANYA MUNA DA NA AMARYA BLUE BLACK, SANNAN MUNA GYARAN JIKIN AMARYA DA UWARGIDA CIKIN KWANA UKU CAKAL ZAKIGA KIN KOMA TAURARUWA MAI WALWALI. MUNAYIN TURARUKAN WUTA DA HUMRA DA KOLACCAR, KOWANNE KALA KIKE BUKATA AKWAI CIKIN FARASHI MAI SAUKI.*
*LOCATION KANO*
08062073990
Ina kuke mata hamshakai wayanda suka amsa sunan su wajen mazajen su ina mata masu son qamshi shin ko kunsan tsafta bata tafiya seda qamshi ina masu son turare mai riqon gida tareda qamshin shi mai sanyaya zukata mardie collection tazo muku da dadadan turarukanta masu lasting riqon gida harma da jiki ku tuntube mu da nmb kamar haka 08136666994 inda zaku samu kaya kamar haka
Wadrobe balls
Madarar kulleccham
Vaseline kulleccham
Kajiji
Halut
Couscous
Khumrah
Da dai sauransu harda abin wanke toilet yayi tas komi dafe warshi wato BETHALEX METAL ku garzayo kar ayi baku
Ina kuke mata hamshakai wayanda suka amsa sunan su wajen mazajen su ina mata masu son qamshi shin ko kunsan tsafta bata tafiya seda qamshi ina masu son turare mai riqon gida tareda qamshin shi mai sanyaya zukata mardie collection tazo muku da dadadan turarukanta masu lasting riqon gida harma da jiki ku tuntube mu da nmb kamar haka 08136666994 inda zaku samu kaya kamar haka
Wadrobe balls
Madarar kulleccham
Vaseline kulleccham
Kajiji
Halut
Couscous
Khumrah
Da dai sauransu harda abin wanke toilet yayi tas komi dafe warshi wato BETHALEX METAL ku garzayo kar ayi baku
It's not just good ...it's finger linking good faster than fast food, better fine dining.
Snack
Awarah
Farah
Zobo
Samosa
Cup cake etc
Contact me 09063302182or 09012179727.
*💋Boss Bature💋*
Join this link to follow my tiktok acct👇
https://www.tiktok.com/@boss_bature?_t=8WKx0lm4jaP&_r=1
قصة حب رومانسية بين سحريش والجراح العام رفايت💋💘❤🤍❤💕💖*
*Ga duk maison karanta littafin Abban sojoji,zai biya 300 ne,za'a tura mashi tundaga farko har inda muka tsaya,kuma zai cigaba da samun update dinshi akai akai,ga wanda ke buƙata zai tura mun message ta whatsapp ɗina (08103884440) kada ku bari abaku labari*,
"Meya faru Abba"? Marshal Omar ne yayi mashi tambayar yayin da yake kallonshi kafin ya mayar da idanunshi kan Abusufyan dake tsaye duk a rikice,tsayawa Sgr yayi tare da goya hannayenshi asaman wide chest ɗinshi,tunda ya ƙaraso wurin idonshi na akan Sehrish da abusufyan dake atsaye cikin wani yanayi ita Sehrish a tsorace shi kuma Uncle abusufyan duk a firgice,
Fuskar Abbansu aruɗe yace"nikaina bansan meke faruwa ba,uncle ɗinku ne tun da yayi arba da yarinyar nan duk yabi ya rikice,ya rasa natsuwarshi,"ya ƙarasa maganar yana yi mashi nuni da Sehrish,
Matsawa Omar yayi tare da dafa kafaɗar Abusufyan yace"Uncle meya faru ne?ko kasanta ne"?
Shiru Uncle sufyan yayi batare da yace komai ba amma duk yanayin shi ya canza sosai,idanunshi har lokacin suna akan Sehrish kamar yarda itama take kallonshi,
Suna cikin wannan yanayin kowa ya miƙe tsaye,
Major yayi sallama,Omar ya bashi iznin shigowa daga ciki,
6oyewa jahad da hosana su kayi a bayan major saboda fargabar haɗuwa da dangin ya Omar ɗinsu,
..murmushi Marshal ya saki yana hangen ƙafafuwansu,
Zuba ido kowa yayi yana jira yaga su wanene waɗannan dake ta 6oyewa,kowa ya mayar da hankalinshi akan Major dake tunkaro su,
Koda major ya ƙaraso wurinsu,sae yace"Jahad hosana ku fito ga ƴar uwarku nan,"
Jin haka yasa su yin hanzarin fitowa daga bayanshi,
Tashin hankalin da ba'a sama shi date,
Waro ido waje su fawan su kayi suna kallonsu,tun daga Ayaan jahan,irfan khaleed da jabeer da kuma kanal yousouf kowannansu ya gama kiɗima da wannan abun al'ajabin,kowa ya gaza buɗe baki yayi magana,kallonsu kawai sukeyi,idan suka kalli Jahad da hosana sae su mayar da idanunsu kan Sehrish,
Tsayawa sukayi daga bayan sehrish,basu da tabbacin cewa itace amma ransu na basu hakan,
Atare suka haɗa baki wurin ambaton Sunanta,
"SEHRISH"
Gabanta ne taji ya faɗi rassss,a firgice ta juya bayanta don taga su wanene suka ambaci sunanta,zuba masu ido sehrish tayi tana kallonsu,lokacin da ta juyo suka tabbatar da cewar itace rishi ɗinsu,wani irin farin ciki ne ya cika su,jiki na rawa suka tunkareta zasu rungumeta,abun mamaki sae suka ga tana ja da baya baya fuskarta da alamun tsoro tace"su wanene ku!ni bansan ku ba,dan Allah kada ku matso kusa dani,"
gabansu ne suka ji ya faɗi rass,nan take kuma idanuwansu suka cika tab da kwalla,
Muryar jahad na rawa tace"sehrish,ashe zamu sake sanyaki acikin idanuwanmu?mun rasa ki a lokacin da muke tsananin buƙatarki,ba mu ta6a tunanin cewa zamu ƙara haɗuwa dake ba,sae gashi Allah ya ƙara haɗamu..,
"Sehrish.......'hosana ce ta ambaci sunanta,
Zuba ido kowa yayi yana kallon Wannan ikon Allah,
Girgiza kai sehrish ta shiga yi jikinta na rawa tace"Ni...ban..sanku ba..dan Allah ku daina kiran sunana,banason ji,"
Fashewa da kuka sukayi su biyun jin abunda tace masu,
"Omar kun barmu acikin duhu,!dan Allah ku sanar damu ina aka samu waɗannan twins ɗin!"Abbansu ne yayi maganar yana kallon Marshal,
Abusufyan kuwa tunda yayi arba da Jahad da hosana ga kuma sehrish,batare da sanin kowa ba,yabar wurin izuwa bedroom ɗin da ya sauka,wani irin matsanancin ciwon kaine ya taso mashi,ga wani zazza6i daya lullu6e shi lokaci guda ya rasa in da zai tsoma ranshi,abun ya gama gigita shi,
Gyaran Murya Omar yayi kafin ya soma magana anatse yace"Abba waɗannan twins ɗin da kake gani,sune yaran da nake baka labari,mun haɗu dasu a asibiti cikin mawuyacin hali,na taimakesu a wannan lokacin har na kawosu gidan Uncle abusufyan don su cigaba da rayuwa acikinshi,tun da nake dasu ba mu ta6a tattaunawa agame da danginsu ba,saboda tun lokacin da na fara haduwa da su sun sanar dani su basu da kowa,bayan nakawo su gidan uncle abusufyan aranar dana fara ganin Yarinyar nan sehrish,abun ya ɗaure mun kai ganin kamanninsu iri ɗaya sak da yaran da nake ruƙo a wurina,nasha tambayar sehrish ko tana da ƴan uwa don in bugi cikinta inji ko tana da alaƙa da yaran dake wurina,amma sae tace mun ita bata da kowa,daga baya na dinga tunanin cewa kodai son da nake ma Jahad da hosana ne yasa nake ganin fuskarsu akan ta yarinyar,amma abun da ya faru jiya ne ya tabbatar mun da cewa Bani kaɗae ke ganin kamanninsu ba,junaid yaje ɗaukar sehrish lokacin da aka tashe su daga school,cikin rashin sani ya ɗauko Jahad!amaimakonta ya kawota cikin gidan nan....!
Tunda Omar ya soma magana kowannansu ya kasa kunne yana sauraronshi,fuskokinsu da alamun mamaki sosai,
"Jahad hosana da kuma sehrish,uwarsu ɗaya ubansu ɗaya,su ƴan Uku ne!na jima ina mamakin Yarda Allah ya haɗasu dukkansu a ƙarƙashin kulawar family dinmu,ni na haɗu dasu hosana a wani hali na rayuwa na taimakesu na kawosu gidan Uncle abusufyan,yayin da Sehrish aiki ne ya kawota cikin gidan nan.....'
Yana kai ƙarshen maganar Abbansu yace"Amma Omar abun ya ɗaure mun kai wlh!taya akai duk hakan ya faru?
matsawa Omar yayi wurin da su hosana suke tsaye suna faman sharar kwalla saboda ganin yarda sehrish ɗinsu ta nuna batasan su ba,duk murnar da suke tayi ta koma ciki,
Ruƙo hannun Jahad yayi cikin sanyin murya yace"Jahad,ki faɗa masu yarda akai kuka rabu da ƴar uwarku,har tsawon wannan lokacin baku atare,"
Daƙyar jahad ta Iya bayyana masu dukkan abunda ya faru,tun kafin zuwan sehrish aiki,har abunda yayi silar rabuwarsu da ita,da kuma wahalar da suka sha kafin Allah ya haɗasu da Marshal Omar,
Wani irin tausayinsu ne ya kama matasan gidan,jikin kowa yayi mugun sanyi,hatta Sgr dake tsaye yana kallonsu ba ƙaramin tausayi suka bashi ba,yaran sun sha wahala sosai,
"Amma Omar meyasa tun farko baka faɗamun komai agame dasu ba?ae da tuni mun haɗasu da ƴar uwarsu wuri guda sunyi rayuwarsu,"acewar Abbansu muryarshi tamkar zaiyi kuka yayi maganar,dama shi akwai tausayi
Omar yace"Abba,nima naso nayi hakan,kayi haƙuri da rashin sanar maka da banyi ba,amma yanzu gasu nan na kawo maku su,kuma ina fata zaku kar6esu hannu bibbiyu kamar yarda kuka kar6i ƴar uwarsu sehrish,!!!
Hankali tashe sehrish tace"Ni ba ƴan uwana bane ya Omar,wlh bansansu ba,bansan su wanene su ba,dan Allah kada ku haɗa ni dasu,bansan ganinsu,bazan iya rayuwa wuri ɗaya tare da su ba,'
Wannan kalaman na sehrish yasa kowannansu kallonta cike da mamaki,ƙiri ƙiri ga abu ya fito zahiri amma ta nuna cewa ba ƴan uwanta bane!bayan sunji cewa saboda su ne tazo aiki agidan don ta samu kudi,"
"Rishi mune ba ƴan uwanki ba!sehrish yau da kanki kike faɗin hakan!dan Allah kidaina cewa haka,wlh zuciyata zata iya bugawa na mutu....'jahad ce tayi maganar yayin da idanunta ke fitar da wasu zafafan hawaye masu ɗumin gaske,
..hosana tace"sehrish kin manta ni nima?kin manta hosanarki da kika bari kwance gadon asibiti bata acikin hayyacinta"?muryarta asanyaye tayi maganar,
gaba ɗaya sun rikita sehrish,ko son kallonsu bata yi,in su kayi magana ƙara mata ciwon kai sukeyi,kamar yarda suke kuka haka itama ta fashe da kuka tana rantsuwar cewar batasan su ba,
tashin hankali!
Sai lokacin kanal yousouf yace"Ina azmee take ne?fawan kaje ka kira mana ita,ina da tabbacin cewa tasan wani abu game da yarinyar nan,tunda tafi kusanci da ita,zai iya yiyuwa akwai wani abu da ta ta6a sanar mata,'
Fawan ya amsa mashi da toh,sannan cikin sauri ya wuce sashen su azmee don ya kira ta,
Ganin yadda su Hosana da jahad ke ta kuka yasa Abbansu junaid cewa"Ku zo nan,"
Hannunsu cikin na juna suka ƙarasa wurinshi,
bin fuskokinsu yayi da kallo na wani lokaci,kafin ya sanya tafin hannayenshi yana goge ma hosana hawayenta,cikin lallashi yace"kudaina kuka ya isa haka,kada ku sa damuwa aranku,yanzu lokacin farin ciki ne,tunda ƴar uwarku tana atare daku yanzu kuma insha Allah,babu wanda zai ƙara rabaku da ita,"
Cikin shessheƙar kuka jahad tace"Amma ta nuna batasan mu ba ai,"
Abba yace"kada ku damu da wannan,wasa take yi maku,zuwa anjima zata dawo dai dai ne,'
"Rishi ba wasa take mana ba,"acewar hosana,bayin Allah gaba ɗaya duk zazza6i ya lullu6esu,
Tunda fawan ya sami azmee aɗakinta,ya sanar da ita game da bayyanar ƴan uwan sehrish,farin ciki ya cikata ta shiga faɗin"Alhamdullillah,Alhamdulillah"
Jiki na rawa ta biyo bayan fawan suka nufo falon,
Tunkan su ƙarasa ciki take hangensu Jahad da hosana dake tsaye agaban Abbansu junaid,abun ba ƙaramin ɗaure mata kai yayi ba,yanzu ta ƙara tabbatar da cewar Dagaske ne!sehrish tana da ƴan uwa,kuma su ƴan ukune,hakan na nufin cewa Sehrish ba ƙarya tayi mata ba,
Tana ƙarasowa sehrish ta nufeta tare da faɗawa jikinta ta rungumeta tana kuka tana cewa"Aunty azmee ni bansan su wanene waɗannan ba masu kama dani,sunce wae sun san ni,bayan ba haka bane,ni bani da wasu ƴan uwa,'bubbuga bayanta azmee ta shiga yi tana lallashinta,
"Azmee muna sauraronki,ko akwai wani abu da kika sani game da ƴan ukun nan!kunfi kusanci da Sehrish nasan cewa dole akwai wani abu da ta ta6a sanar maki agame da rayuwarta,"
Marshal Omar ne yayi maganar,
Azmee tace"Sehrish bata ta6a sanar dani wani abu game da rayuwarsu ba,amma ina da masaniya akan Ƴan uwannan nata........'gaba ɗaya azmee ta sanar dasu,yarda sukayi da sehrish tun farkon zuwanta,da kuɗin da ta nema awurinta na biyan kuɗin aikin hosana,duka kaf ta kwashe ta sanar dasu,
"A lokacin ni da kaina,na kar6i acct numbar likitan da yake kula da ƙanwar tasu,na tura mashi kuɗi dubu ɗari tara na aikin yarinyar,acikin kuɗaɗen dana jima ina tarasu na albashina da kuma wanda kuke bani don inyi hidimar kaina....'
Tunkan ta ƙarasa maganar Sgr ya dakatar da ita da hannunshi,
Sai lokacin ya samu damar buɗe bakinshi yace"Meyasa baki sanar da waninmu game da waɗannan yaran ba!bayan ta sanar dake halin da ƴan uwanta suke ciki?sannan waya baki iznin bata kuɗi har 90k batare da sanin kowa ba?kuma kika hana ta zuwa ganin ƴan uwanta saboda kunyi yarjejeniyar zatayi aiki acikin gidan nan harna tsawon shekara ɗaya da rabi,Why AZMEE!?
Hankalin azmee ba ƙaramin tashi yayi ba jin tuhumar da sgr yake yi mata,
"Ba laifina bane Rafayet!duk wani abu daya faru nayi ne saboda sehrish!bakomai ne yajawo hakan ba face
tsoron kar asirinta ya tonu ku gane cewa ita mace ce ba namiji ba,Abban ku ya nemi mai aiki namiji,amma sai ga sehrish tazo aiki amatsayin namiji,dagani harku babu wanda yasan cewa ita mace ce ba Namiji ba,Ni ce na fara gane cewa ita mace ce,akwai wata rana da naje kiranta don muyi aiki,anan na same ta akwance babu gashin bakin nan da take sanyawa ga kuma dogon gashi akanta hakan ya tabbatar mun da cewa ita mace ce ba namiji ba,koda na sanar mata cewa nagane ita mace ce,a lokacin ta dinga roƙona akan na rufa mata asiri batason kowa ya sani,saboda sanin halin matasan gidan nan da nayi na rashin son ganin mace acikinsu,kuma ga laifin ƙaryar da tayi na zuwa a matsayin namiji,wannan ne dalilin dayasa na rufa mata asiri ban sanar ma kowa ba,daga baya kuma bayan kowa ya gane cewa ita mace ce,naso nayi mata maganar ƴan uwanta amma sehrish sai ta nuna mun cewa ita bata da wasu ƴan uwa aduniyar nan ita kaɗaice........'tun daga farko har ƙarshe azmee ta sanar dasu dukkan wani abu daya faru tsakaninta da sehrish akan maganar ƴan uwanta,da kuma abunda junaid ya sanar da ita na wayarshi da sehrish take ɗauka a 6oye tana kiran ƴan uwanta,komai ta sanar dasu,
Gaba daya sun gamsu da bayananta,duk da basu ji daɗin halin da ƴaran suka kasance aciki ba,sun so ace tuntuni sunsan da zancen,da tuni sun jima da kasancewa a wurinsu,
Jin takun tafiya yasa suka ɗan juya don ganin wanene,Hajiya azeema ce ta fito daga masaukin da ta sauka,ta ca6a ado,wurinsu ta nufo tana tambayar lafiya? mai ya faru ta gansu atsaitsaye cirko-cirko?
Koda ta ƙaraso cikin babban falon karaf idanunta suka sauka akan Jahad hosana da kuma sehrish dake manne da azmee taƙi sakinta,saboda halin da take ciki,
Cike da mamaki tace"Ya hossein!su wanene waɗannan ƴan ukun masu masifar kama?ƴa'ƴan wanene?
Abba yace"wannan wani case ne da muke tattaunawa akanshi,shiyasa kika ganmu atsaitsaye,zan sanar dake komai bayan mun dawo daga sallar magrib naga lokaci ya ƙarato,"
Ya ƙarasa maganar tare da kallon azmee yace"Ki wuce da sehrish ɗakinta,sannan waɗannan ƴan uwan nata ki sama masu ɗakin da zasu zauna kafin mu dawo daga sallah,"
Omar yace"a'a Abba banaso arabasu,yaran nan sun kwallafa rai akan ƴar uwarsu,jiya saboda murnar jin cewa tana a gidan nan,ko bacci basuyi ba,kuma basu ci abinci ba,saboda sunyi alƙawarin cewa atare da ƴar uwarsu zasu ci abinci,don haka inaso a haɗasu ɗaki ɗaya da ita,kuma ashirya masu lafiyayyen abinci suci tare da ita,ko tana so ko bataso,"
Jinjina kai Abba yayi tare da cewa"Shikenan,hakan ma yayi Azmee ki tabbatar da kin haɗasu wuri ɗaya tare da ƴar uwarsu,"
"Insha Allah zanyi hakan,"ta amsa mashi,sannan ta kalli su jahad da hosana tace"ku biyoni mu tafi,"
tayi maganar tare da ruƙe hannun sehrish dake ta faman faɗin bataso bataso a haɗata ɗaki ɗaya dasu,ahaka suka wuce bedroom ɗinta,
Bayin Allah,duk sunji sun tsani kansu saboda juya masu bayan da sehrish tayi,duk irin ɗoki da murnar ganinta da sukeyi amma ta nuna batasan su ba,kamar wasu bare haka take kallonsu,haƙiƙa zuciyoyinsu ba ƙaramin karaya sukayi ba,
Bayan azmee ta tafi dasu Jahad,anan su abba suka tsaya suna ƙara tattaunawa atsakaninsu,abun ba ƙaramin ɗaure masu kai yayi ba,lamarin ya rikirkitasu,bakomai yafi tsaya masu aransu ba,face yarda Sehrish ta nuna