Showing 375001 words to 378000 words out of 432432 words
Chapter 126 - Abban Sojoji Book 2 Hausa Novel Complete
yi gefe guda ta daki ƙasan tiles,
A razane suke kallonshi,wata irin zufa ce ta soma gangarowa ta gefen fuskarshi,ɗaya bayan ɗaya yake binsu da kallo,jikinsu sai kerma yake yi,Dr Emran ma ƙoƙarin guduwa yake yi,Armstrong kuwa sai lalla6ashi yake yi akan su sanar dashi abunda ke faruwa tun kafin ya birkice masu,
"Rafayet"!muryar Marshal Omar ce ta dawo dashi cikin hayyacinshi,jiki na rawa ya juya yana kallonshi,a hankali Omar ke buɗe idanuwanshi waɗanda sukayi jawur dasu,zufa ta ko'ina ajikinshi duk da sanyin A.c ɗin dake akwai,da sauri Sgr ya koma gefen gadon ya zauna tare da ruƙo hannunshi,
"Omar pls tell me,what's happening wit u?meyasa na ganka a asibiti?Are u not feeling well"?daƙyar Marshal ya samu ya yunƙura tare da mikewa ya zauna,numfashinshi da huci yake fita,bawan Allah yaji jiki sosai,wasu zafafan hawaye ne suka wanke mashi fuskarshi,
Muryarshi na rawa yace"Bro,Yaushe ka dawo Abuja?
Muryar Sgr tamkar zai yi kuka yace"Omar duk ba wannan ba,Where's Junaid?nadamu akan son ganinshi,Daddy ma yana ta kira na saboda rashin samun Junaid a waya..."ya ƙarasa maganar yana faman haɗiyar yawu,
Marshal na ƙoƙarin buɗe baki yayi mashi magana,Karaf idanuwanshi suka sauka akan Major dake girgiza mashi kai alamar karya kuskura ya faɗa mashi,kasa magana Omar yayi,sai ma zuba mashi ido da yayi yana kallonshi,
"Wai menene haka?kowa na tambaya sai yayi mun shiru babu magana?meke faruwa ne!in wani abu ne ya faru ba zaku sanar mun ba ne?Ni fa Musulmi ne!nayi imani da ƙaddara mai kyau ko mara kyau,ku faɗa mun mana......"ya ƙarasa maganar fuskarshi ɗauke da matsananciyar damuwa,
Daƙyar Omar ya iya buɗe baki yace"Babu abunda ya faru,Junaid yana lafiya...."tunkan ya ƙarasa maganar Sgr yace"That's impossible!Taya zaka ce mun junaid yana lafiya kuma in yarda?To idan yana nan a nuna mun shi inaso in ganshi!Meyasa layinshi a kashe?meyasa nake ganin hawaye akan fuskarka?
Daurewa kawai Omar keyi,saboda kukan dake cinshi,So yake ya fashe da kuka ko ya samu ya rage raɗaɗin dake acikin zuciyarshi,
Tausasa murya Sgr yayi"pls Omar,ka sanar dani!ina ƙanina yake?wani abu ya faru dashi ne?saboda shi jiya ko bacci ban samu ba,
Da sauri Omar ya sanya tafin hannunshi tare da share hawayenshi,
"Rafayet!I won't hide it for u,Junaid was kidnapped...."daƙyar ya ƙarasa maganar ganin irin kallon da Sgr ke jefa mashi,kallon tuhuma,
"Omar,ni kake faɗama cewa Anyi kidnapping ɗin junaid"?shiru Omar yayi batare da yace mashi komai ba,
"Omar,If it is true,Junaid was kidnapped,as a Senior Soldier with the rank of Marshal,you will be brave enough to rescue him,bawai na ganka kwance a gadon asibiti ba kana zubar da hawaye,"tausasa muryarshi yayi"don Allah Omar ka faɗa mun gaskiyar abunda ya faru,kada kasa zuciyata ta buga,Ina junaid ɗina yake?meya faru dashi?yanayin yadda yayi maganar ne yasa jikinsu kara yin sanyi lakwas,
Daƙyar Major ya daure ya cije,ya yi karfin halin bude baki yace"Sir,Junaid ya riga mu gidan gaskiya!junaid ya koma ga mahalicci....."bai ƙarasa maganar ba sakamakon Zaburar da yaga Sgr yayi gadan gadan ya tunkareshi,yana faɗin",repeat what u just said Major!"yana magana yana naɗe hannun rigarshi alamar zaiyi dambe,da sauri Omar ya ambaci sunanshi Rafayet,wanda hakan ya dakatar dashi tare da juyawa yana kallon Omar,
Cikin shesshekar kuka Marshal yace"Junaid has gone forever,wanda yafi mu sonshi ya kar6i abunshi,jiya da daddare around 8,Suna kan hanyar dawowarsu acikin mota shi da jahad,ta fita ta siya masu ice cream tabar junaid acikin Motar,kafin ta dawo,babbar mota tabi ta kan motarshi,Rafayet bamu samu komai daga sassan jikin junaid ba,Ya ƙone ƙurmus acikin motar........"kasa ƙarasa maganar yayi,ya fashe da wani irin matsanancin kuka mai cin rai tare da buga hannuwanshi saman gadon,
Tashin hankali!!!Kasa motsawa Sgr yayi daga tsayen da yake,kamar an dasa mashi aya,Tsit ka ke ji,kowa yasha jinin jikinshi Sgr kawai suke kallo,
Almost 15 mins,Kafin ya motsa pink lips ɗinsa a hankali ya furta"Omar!Do you wanna say that Junaid is dead?
Jinjina mashi kai marshal yayi alamar eh,abun mamaki sai suka ga yana murmushi gami da girgiza kanshi yace"I can't believe that junaid is gone,this is a fabricated lie, Omar you're just kidding me and I don't want it...."
Tsananin tausayinshi ne ya kama Omar,dama yasan cewa zaiyi wuya ya yarda cewa Junaid ya mutu,
"Sir,we are really sorry.....'Dr Emran ne ya ambaci hakan,a sukwane Sgr ya juya tare da kallonshi aruɗe yace"Sorry for what"?
Shiru yayi baice komai ba,ɗaya bayan ɗaya yake kallonsu,a wani irin yanayi mara misaltuwa,fuskarshi duk ta hargitse,jikinshi yayi laushi,guiwarshi ta sage,ƙafafuwanshi sun gaza ɗaukarshi,ga6o6in jikinshi duk sun saki,Zuciyarshi ta raunata sosai,
Wani farin ruwa ne ya kwanta luf acikin fararen idanuwanshi,jinjina kanshi kawai yake yi batare da ya furta komai ba,temperature ɗin jikinshi yayi zafi sosai,yadda ko mutun ya matso kusa dashi,sai yaji hucin jikin nashi,wata irin zufa ce ta soma tsastsofa mashi,a jikinshi lokaci guda ya jiƙe sharkaf,gaba ɗaya sun zuba mashi ido suna kallonshi,gwanin ban tausayi,
"Wai Junaid ne ya mutu?tatsuniya ce ko mafarki"?muryarshi na kerma yayi maganar,
"Enough is enough! What do you want me to say to our father? How can I inform him about Junaid's death?saboda shi ko bacci baiyi ba jiya,Nima haka,meyasa mutuwa zata yi mun yankan ƙauna ne?
Sulalewa yayi saman guiwowinshi wani irin biji biji ya fara gani a idanuwanshi,a hankali ya shiga furta"Innallilahi wa'inna ilaihirraji'un,Ya Allah kasa mafarki nake yi ba gaske ba,meyasa ni bata ɗauke ni ba ta ƙyale Junaid?Why!why!'da sauri Dr Emran tare dasu Major suka kewayeshi suna tottofa mashi addu'o'e asaman kanshi,wani irin jijjiga jikinshi ya soma yi,hakan ba ƙaramin ɗaga masu hankali yayi ba,a Ruɗe marshal ya saukko daga saman gadon ya nufosu jiki ba ƙwari ya zube agaban Sgr wanda tuni ya yanke jiki ya faɗi,kuka sosai Omar yake yi kamar ya haɗiyi zuciya,rungume Sgr yayi sosai ajikinshi,Ya tsorata da jin irin zafin da jikin Sgr ya ɗauka,tamkar hucin wuta ,
"His body temperature was very high,I think he got a heatstroke,yana buƙatar Emergency treatment,"Dr Emran ne yayi maganar,batare da 6ata lokaci ba a gaggauce suka ɗaukeshi izuwa saman medical bed ɗin da Omar ya sauka suka kwantar dashi,doctors ne suka taru akanshi,ga jinin shi ya hau sosai,
Daga waje suka koma,Saman waiting seats suka zauna suna jiran tsammani,ɗage kanshi yayi jikin seat din yasa Hanky ya rufe fuskarshi,Allah kaɗai yasan irin raɗaɗin da yake ji acikin Zuciyarshi,bakowa yafi ji ma tausayi ba,Fa ce Abbansu,don muddin yaji irin Mummunar mutuwar da Junaid yayi tofa Zuciyarshi zata buga ne,A rasa duka biyun,Sojojin dake a kewaye dasu,sai tausarshi sukeyi ganin yadda kamanninshi suka sauya saboda damuwa,
"Haƙuri zamuyi yalla6ai,nasan abun da ciwo,raɗaɗinshi yafi ƙunar wuta,Amma ya zamuyi?mutuwa ce tana akan kowa,Junaid addu'armu yake bukata a yanzu,Allah ya jiƙanshi,ya gafarta mashi zunubbanshi,Yasa can yafi mashi nan,Su kuma waɗanda suka shirya mutuwarshi,Allah ya tonu asirinsu,don bazamu ƙyalesu ba,sai sun ɗanɗani kuɗarsu,"sosai Major ya shiga tausarshi yana ƙara ƙarfafa mashi guiwa,
a hankali Omar ya zame hanky ɗin dake akan fuskarshi,ta kumbura sosai la66ansa sunyi suntum,idanuwanshi sunyi jawur dasu luhu luhu,daƙyar ya iya buɗe baki yace"Nagode sosai Major,naji daɗi sosai,kalamanka sun dan sanyaya mun zuciyata,Amma inaso ka sani rashin Junaid atare damu babban gi6i ne,wanda babu wanda zai iya cike sa,he's our weakness!maƙiyanmu sunci galaba akanmu!Sun kashe mana duk wani ƙwarin guiwa da muke dashi!laifin me junaid ya aikata da ya cancanci wannan ɗanyen hukuncin?Yaron da baison komai ba,Soyayyar ƴan uwansa kawai ya sani,burinshi koda yaushe ya sanya kowa farin ciki,amma yau an samu wasu marasa imani,Marasa tausayi,sun yi silar mutuwarshi!wlh ɗaya daga cikinsu bazai shaba,Sai sunyi danasanin haihuwarsu da uwarsu tayi acikin duniyar nan,"yana magana hawaye na wanke mashi fuskarshi,
Major na ƙoƙarin buɗe baki yayi magana,Suka jiyo hayaniya daga can cikin asibitin,Sautin kuka suka jiyo mai sautin gaske,Gaban Omar ne ya faɗi rasss jin Muryar jahad wadda tun a jiyan su major suka sa aka maido ta nan,A hanzarce suka miƙe tsaye suna kallon wurin da sautin ke fitowa,da gudun gaske take tunkarosu nurses sun biyota da gudu,sae ihu takeyi tana faɗin"wuta!wuta!Junaid yana acikin wuta,ataimaka a fito mun da ɗan uwana,kada ta ƙona shi,"wannan shine sambatun da takeyi,tashin hankali!
Duk da jikinshi ba ƙwari haka ya nufeta,tare da ruƙota jikinshi,idanuwanta sun juye kwata kwata bata iya gane wanene agabanta,ita dai kawai sunan junaid take ambato acikin bakinta,hankalin Omar ba ƙaramin tashi yayi ba,tsoranshi kar ace ta samu ta6in hankali,don da alama abunda ke shirin faruwa kenan,
"Jahad!ki natsu ki kalleni,Ya Omar ne fa"
Kuka takeyi sosai,jijiyoyin wuyanta duk sun firfito waje,don bala'e Allurar kashe jiki akayi mata,Amma babu abunda allurar tayi mata,tamkar an ƙara mata ƙarfin jikinta,baiwar Allah taga tashin hankalin da bata ta6a gani ba,kuma akan Masoyinta da take tsananin so,
Jijjigata ya shiga yi yana ambaton sunanta"Jahad!Ina zaki je?
Firgita tayi agigice ta dinga faɗin"Gashi can!yana kuka wuta!wuta!ke ci ajikinshi!Yana kuka,Ya Omar a fiddo shi kada ya mutu ya barni,"da ƙarfi take yin maganar tamkar maƙoshinta zai 6allo,ƙoƙarin ƙwacewa take yi daga hannunshi don taje wurin abunda idanuwanta ke hango mata,Ko ina ta kalla,sai taga motar junaid tana ci da wuta,shine abunda idanuwanta ke nuna mata,
Hawaye ne suka kuma wanke mashi fuskarshi,tsananin tausayin jahad ne ya kamashi,gaba ɗaya babu natsuwa atare da ita,ta haukace ta gigice ta firgice,kamar wadda tayi shekara ɗaya tana hauka,
Hannu yasa tare da sa6arta saman kafaɗarshi,saboda rashin ƙwarin jikinshi,har tangal tangal yayi kamar zai faɗi daƙyar ya samu ya tsayar da kanshi,wuce wa nurses ɗin sukayi gaba yabi bayansu,yana jin yadda jahad keta bugun bayanshi,ta dunƙule hannayenta sae ɗumarshi take yi don ya saketa,Allah sarki innocent girl kamar jahad,yau ta zauce har tana bugun Ya Omar ɗinsu,
Er nurses ɗin suka wuce har zuwa room ɗin da aka kwantar da ita,Shiga yayi da ita ciki,a lokacin har jikinta ya fara saki,alluran da aka ɗurka mata sun fara aiki,a hankali ya kwantar da ita saman gadon,kamar matacciya haka ta koma,ko yatsanta bata iya ɗagawa,la66anta sun bushe sosai,sun farfashe sakamakon ciccijesun da tayi,tsayawa yayi daga tsaye yana kallonta,idanuwanta suna a rufe,tunda yake a rayuwarshi bai ta6a fuskantar tashin hankali irin na jiya da kuma yau ba,bai ta6a cin karo da mummunar rana ba,irin ta yau,ta ko'ina babu sauƙi,zuciyarshi har wani tafarfasa takeyi saboda ƙunar da takeyi mashi,
Shigowa cikin ɗakin Major yayi tare da wani baturen Likita,jin sallamarsu yasa Omar juyawa yana kallonsu,da sauri ya tunkari Doctor ɗin yana tambayarshi dangane da jahad,
"She is having a panic attack as a result of the incident"acewar Dr Antony,
Dafe kai Omar yayi da hannu ɗaya ya ɗan runtse idanuwanshi tare da buɗesu,Muryarshi a kasalance yace"Yanzu Doctor babu yadda za'ae yarinyar ta dawo cikin hayyacinta!"
Dr Antony yace"It will be very difficult for us to overcome her now,but we will do our best to see her regain consciousness,"
"Pls Dr,try as much as u can"
Jinjina kai Dr antony yayi,tare da dafa kafaɗar Marshal don ya lura baya acikin hayyacinsa
"Calm down ur mind,she will be ok,zamu yi iyakar bakin ƙoƙarinmu wurin ganin mun shawo kanta,"
Daga haka Major ya ruƙo hannunshi suka fito daga waje,zama fa bai gansu ba,Zarya ya shiga yi tsakanin room ɗin da Jahad take ciki dakuma room ɗin Sgr,sam ya kasa samun natsuwarshi tuni ya mance da shima mara lafiya ne,ana cikin wannan tashin hankalin,Tsautsayi yasa Omar ya kar6i wayarshi daga hannun Major,Yana kunnata kwatsam!sai ga kiran Abbansu ya shigo cikin wayar kamar jira yake yi,!
Zubawa screen ɗin wayar ido yayi,tare da ɗagowa ya kalli Major,tun kafin ma yayi magana,major ya riga shi cewa"Abba ne ko"?ɗaga mashi kai yayi alamar eh,
"Seriously I can't pick his calls,saboda bansan amsar da zan bashi ba,if he asks about junaid,"ba don yaso ba haka ya katse kiran Abbansu,Abunda bai ta6a yi ba arayuwarshi,
yana ƙoƙarin kashe wayar gaba ɗaya sai ga message ya shigo ta sama,hannunshi na kerma ya buɗe message ɗin,fearfully ya soma karantawa,
_Omar kun kyauta ku dukanku,kowa yaƙi ɗaga kiran wayata,dama inaso in sanar dakai cewa,Yau zamu dawo gida_
Saboda tsabar kiɗima,Omar baisan lokacin daya saki wayarshi ba,ta faɗi ƙasa sosai ta daki tiles ɗin,
"Innalillahi wa'inna ilaihirraji'Un!Allahumma ajirni fil masibati wa'aklifni khairan Minha"wannan shine abunda yake ambato acikin bakinshi,
"Major menene mafita?Ka taimaka min!abubuwa sunyi mun yawa,Ya zanyi da rayuwata!Babu Junaid,Jahad ta zauce!Ga Sgr ma a kwance gadon asibiti,Na shiga uku ni yau!wannan wace irin baƙar rana ce!?
Wani irin tausayinshi ne ya lullu6e major,janyoshi yayi ajikinshi ya rungumeshi sosai,dama a buƙace yake da ya samu kafaɗar da zai aza kanshi,Ya zubar da hawayenshi sosai,ko ya rage raɗaɗin dake acikin zuciyarshi,
Cikin shessheƙar kuka yace"Major menene mafita yanzu?Ya zanyi da Abbansu?
Hannu major yasa yana ɗan bubbuga bayanshi yace"Sir,in sha Allah komai zai tafi dai dai,bazamu rasa abunyi ba bi'iznillahi,"
Ruƙo hannun Omar yayi suka koma saman waiting seat ɗin suka zauna,kwantar da kanshi ya kumayi asaman kafadar major,sai faman sauke ajiyar zuciya yakeyi,bakomai yake faɗo mashi arai ba,fa ce Fuskar Baby Junaid ɗinsu,mai ɗauke da wannan kyakkyawan Murmushin,
*Boss Bature*
*Sehrish*
Around 1:30 na rana,
Zaune take asaman Sofa ta zabga Uban tagumi,tunda Daddynsu ya sanar da ita game da tafiyar Sgr Abuja,take jin kanta kamar ba cikakkiyar mutun ba,Bataso tafiyarshi ba,duk da ta yi mamakin tafiyar tashi,kewarshi duk tabi ta lullu6eta,ga kewar gida yau 3 days kenan suna a kano,Yanzu gidan ya rage daga ita sai Oummansu,tun kafin a fara kiran sallah,Maman sadeeq suka koma gidansu,Abusufyan ne ya ɗaukesu acikin motarshi,hannu takai tare da ɗaukar wayarta dake ajiye agefenta,Contact ta shiga tare da lalubo numbar jahad ta buga mata kira,
Guntun tsoki taja,jin layin nata a kashe,Layin Junaid ta kira Shima a kashe,hakan ba ƙaramin ɗaga mata hankali yayi ba,Layin Hosana ta kira,a lokacin sun kammala haɗama Omar breakfast ɗinshi,har ta koma ɗaki ta shiga toilet tayi wanka,tana zaune gaban mirror tana kwalliya jikinta sanye da gown,wayarta dake ajiye saman drawer ta soma ringing,duk a tunaninta ya Omar ɗinta ne,jiki na rawa ta miƙe hada tuntu6e wurin yin saurin ɗaukar wayar,koda taga kira daga Sehrish ne,jiki na rawa tayi picking call ɗin tare da kara wayar a kunnanta,
Tunkafin Sehrish tayi magana,hosana ta ruga ta cewa"Wai yaushe zaku dawo ne?gidan fa ba kowa ni kaɗaice,
"Hosana wai ina jahad ne?ina kuma junaid?basu dawo daga shan ice cream ɗin bane tun jiya da suka fita?na shiga damuwa saboda rashin samunsu a waya,"
Hosana tace"Nima bansan inda suka je ba,babu fa kowa gida,daga ni sai Aunty azmee,ya Omar bansan shima ina yaje ba,"
Hankalin sehrish yayi matuƙar tashi,la66anta na kerma tace"Hosana!yaya Rafayet baizo nan gidan ba"?
"Eh,baizo ba,ni banga kowa ba,"
Nan take ranta ya bata cewa wani abu ya faru acikin gidan,kuma bada kowa ya faru ba,fa ce Su Junaid da suka fita shan ice cream,saboda rashin dawowarsu cikin gidan
"Rishi ko breakfast na gaza ci,ina cikin matsananciyar damuwa,"
Ajiyar zuciya Sehrish ta sauke tare da cewa"Hosana ki kwantar da hankalinki,Zasu dawo cikin gidan ne,Yanzu zan sanar dake wani abun farin ciki nasan zaki ji daɗi sosai,
Muryarta aɗan shagwa6e tace"toh faɗamun menene"
Sehrish ta miƙe tare da nufar ɗakin Oummarsu tana faɗin"Nasan Daddy bai sanar dake ba ko"?
Hosana tace"meke nan"?
Shiga cikin ɗakin tayi wayarta manne a kunnanta,
Video call ta mayar da kiran nasu,bayan ta samu wuri ta zauna gefen Oummansu dake ta bacci hankalinta a kwance,
"Hosana kalli ki gani,Wacece wannan,"tayi maganar tare da saita Screen ɗin wayar saitin fuskar Oummansu,
Ƙura ido hosana tayi tana kallon fuskar oummasu,almost 7 mins,a hankali wani kyakkyawan murmushi ya bayyana akan fuskarta,a ruɗe tace"rishi Oumman mu ce ko?
"Eh itace,naso na sanar dake tun jiya,baki dauki wayan ba kuma bansamu halin sake kiran ba,An samu Oummanmu,Amma bata acikin hayyacinta ta samu ta6in hankali,
Uban tsalle hosana ta daka,da gudun gaske ta fito daga ɗakinsu,kaitsaye ta nufi kitchen inda ta baro Azmee tana gyare gyare,Cikin rashin sani Hosana taci karo da haroon,ta bangaje shi sosai har wayar dake hannunta ta kubce mata,kaitsaye ta faɗi ƙasa ta daki Tiles Screen ɗin ya fashe,
Hannu hosana ta aza asaman kanta ta fashe da wani irin matsanancin kuka,tana faɗin"Wayyo Allah wayata!Ka kashe mun wayata,Wlh bazan yafe maka ba,Allah ya isa,"
Rai a6ace haroon ya ɗaga hannu zai mareta,adai dai lokacin Azmee ta fito daga kitchen ɗin,A ruɗe ta ƙaraso ta damƙi hannunshi,wani mugun kallo daya jefa mata sai da gabanta ya faɗi rass saboda launin idanuwanshi da sukayi jawur dasu,fuskar nan tashi tayi suntum da ita,da sauri azmee ta saki hannunshi,cikin sanyin murya tace"Allah ya huci zuciyarka,"
Harara ya wurga mata tare da jan dogon tsoki mai sautin gaske,matsawa yayi izuwa inda wayar hosana take a ƙasa,Ya sanya faffaɗan tafin kafarsa mai sanye da takalmi,Ya take wayar ya rugurguzata,hakan ba ƙaramin ƙona ma hosana rai yayi ba,Abun ka ga mai ta6in hankali,Kamar kura ta mamayeshi tare da gartsa mashi cizo asaman damtsen hannunshi,Dama ƴar singlet ce ajikinshi,ƙoƙarin janyeta ya dinga yi amma taƙi cire haƙoranta daga saman fatar hannun,har sai da ta fasa shi,jini ya shiga tsastsafowa a wurin,waro ido waje haroon yayi ganin ta fitar mashi da jini a fatar jikinshi,ƙwaƙƙwarar damƙa yakaima Gashin kanta,Hankalin Azmee ba ƙaramin tashi yayi ba,Ga tsoron shiga huruminshi take yi don tasan halinshi ba imani ya cika ba,Yasha ɗaga hannu zai mareta,
Wurgi yayi da hosana,gaba ɗaya ta tafi zata faɗi ƙasa,Azmee takai hannu zata ruƙota,
Tsawa ya daka mata tare da cewa"kika kuskura kika ta6a ta abakin aikin ki cikin gidan nan!uwar shisshigi kawai,ki tsaya a iya matsayinki,"jiki asanyaye azmee ta tsaya tuni idanuwanta suka cicciko tab da ƙwalla,tana ji tana gani haka hosana ta kife ƙasa,fuskarta ta bugu sosai har hancinta ya fashe,
Haura ƙafa yayi ya wuce Can medical room ɗinsu,saboda yayi dressing raunin da taji mashi,
"Hosana"Azmee ce ta ambaci sunanta,tare da zuƙunnawa agabanta,tasa hannu ta janyota ajikinta,Lallashinta ta shiga yi,abun ba ƙaramin ƙona mata rai yayi ba,Haroon ya 6ata mata rai,
Cikin shessheƙar kuka tace"Aunty azmee,Kalli yarda ya fasa mun wayata,mutumin can baida imani shi ba jininmu bane,"hannu Azmee tasa tana share mata hawayenta,
"Kiyi hakuri hosana,Allah shi zai saka maki,"
Daƙyar azmee ta samu ta lallasheta,har ta rakata ɗakinsu ta kwantar da ita tana ta ajiyar zuciya,cikin lokaci ƙanƙani bacci ya ɗauketa,
Dawowa falon Azmee tayi wurin da wayar Hosana ta fashe,hannu tasa ta ɗauki wayar tana kallon screen ɗin,Ya dagargaje sosai baka iya ganin komai,
A 6angaren Sehrish kuwa,duk tabi ta ruɗe lokacin da taji sautin kukan hosana,kafin haroon ya taka wayar ta ƙarasa mutuwa gaba ɗaya,zumbur ta mike tana