Showing 309001 words to 312000 words out of 432432 words
Chapter 104 - Abban Sojoji Book 2 Hausa Novel Complete
tazo fuskarta a ɗaure,a fusace take ruƙo hannuna ta tura ni cikin mota,mu tafi,hakan ba ƙaramin dariya yake bani ba Inajin daɗin kishina da takeyi sosai,amma kishin da takeyi mun yajawo rabuwarmu da ita ba don naso ba......"kasa ƙarasa maganar yayi,saboda wani abu da yaji ya taso mashi mara daɗin ji acikin zuciyarshi,tuni idanunshi sun cicciko da kwalla,
tsananin tausayin Abbansu ne ya kamasu duk jikinsu yayi sanyi,daƙyar jahad ta iya buɗe baki tace"daddy,dan Allah kayi haƙuri da duk abunda ya faru tsakaninka da Oumman mu,nasan cewa abun yana yi maka ciwo acikin zuciyarka,Oumman mu bata kyauta maka ba,gashi sanadin hakan ta jefa rayuwarta cikin haɗari da kuma rayuwarmu,sau dayawa takan zauna tayi ta kuka,musamman da daddare ko runtsawa bata iya yi,kullum cikin ambaton sunanka takeyi tana cewa haƙƙin Abusufyan ne yake bibiyar rayuwarta,na cutar dashi sosai,Mijina yana so na amma na butulce mashi,saboda baƙin kishi na,nayi danasanin rabuwa dashi sosai,Ya Allah ka yafemun,mu lokacin duk bamu san abunda take nufi ba...."tuni hawaye sun shiga wanke mata fuskarta,itama sehrish hawayen ne suka soma shararowa daga cikin idanunta,Hannu Abusufyan ya sanya tare da janyo su ya rungumesu sosai ajikinshi,sae lokacin ƙwallar dake cike taf cikin idanunshi ta shiga wanke mashi fuskarshi,muryarshi a kasalance ya soma magana"Oummanku yarinya ce sosai,Ko a lokacin ban ruƙe ta a raina ba,saboda akwai ƙuruciya sosai atattare da ita,Nasha wahala sosai akanta,saboda Allah ya jarabce ni da tsananin sonta,ina sonta sosai,har yanzu soyayyar da nake yi mata na nan yadda take,babu abunda ya canza,Nayi kukan zuciya a lokacin dana rasa ta,kamar in zauce,lokacin dana ji zancen aurenta da sayyadi,Allah kaɗae yasan ƙuncin dana ji acikin zuciyata,bakomai nake tunawa ba,fa ce Amanarta da mahaifinta ya damƙa mun,ya yarda dani sosai baba buzu,yasan cewa banajin magana,ga ƙuruciya dake ɗibana amma a haka ya toshe kunnuwansa Ya aura mun ƴarsa,Naji daɗi sosai,A lokacin kamar kamar me,Allah ya jiƙanshi,
Atare suka amsa mashi da Ameen,ɗagowa dasu yayi daga jikinshi yana ƙoƙarin kai hannu ya share hawayen dake zuba akan fuskarshi,da sauri suka riga shi sanya tafukan hannyensu suna goge mashi hawayenshi,
Murmushi ya saki,don ba ƙaramin daɗin hakan yaji ba,
"Dama nasani wata rana zaku share mun hawaye na,gashi Allah ya nuna mun ranar da raina kuma da lafiyata,"
Yayi maganar tare da sanya hannayenshi duka biyu,asaman fuskokinsu yana share masu hawayensu,bayan ya kammala goge masu hawayen,yace"oh namanta,ban baku tsarabar masallaci ba,"da sauri ya zura hannunshi cikin aljihun wandon jikinshi,
Farar leda ce ya curo mai ɗauke da dabino da goro,
Miƙa masu yayi tare da cewa"hada aya da kwakwa nasiyo maku amma ta hosana ce ita kaɗae zan bamawa,wannan dai gashi ku raba a tsakaninku,"
Kar6ar ladar jahad tayi fuskarta ɗauke da murmushi,sehrish tace"dama na lura kafi ji da hosana,"
Abusufyan yace"eh mana,saboda itace autarku a yanzu,nafi sonta,kuma nafi ji da ita,"
Zumbura baki sehrish tayi tare da cewa"yanzu duk irin cizon da tayi mana a jikinmu baka gani ba?
"Nagani mana,ae gwaggo ta tabbatar mun da cewar ba yin kanta bane,Ya sayyadi ne yazo da suffar kura yayi maku wannan aika aikar....."karasa maganar yayi tare da fashewa da dariya,suma dariyarce ta kufce masu,
Wucewa cikin ɗakin nasu,yayi tare da zama daga gefen gadon yana kallon hosana dake kwance tana bacci,baki a buɗe,
Da sauri ya sanya hannunshi,a cikin aljihun ya curo ledar dake ɗauke da yankakkar kwakwa da ƙullin aya acikinta,
Kwakwar ya ciro,cike da tsokana ya zurata cikin bakin hosana,cikin bacci hosana ta kama kwakwar ta shiga taunarta abakinta,
Dariya sosai sukayi abun ba ƙaramin nishaɗi ya basu ba,
Wuri suka samu suka zauna,suna kallon tsokanar da Daddynsu ke yi ma Hosana,
gaba ɗaya ta cinye kwakwar daya sanya mata abakinta,wata kwakwar ya kuma curowa,tare da zura mata abakinta,kamar wata kura haka ta kama kwakwar tana gartsa,tana taunewa acikin bakinta,
"Daddy,ɗan janye kwakwar mu gani ya zatayi,"acewar jahad,
A hankali ya shiga ƙoƙarin janye kwakwar daga cikin bakinta,ta cije ta da haƙoranta,yana ja tana rurruƙeta,dariya sosai Abusufyan yake yi abun ba ƙaramin nishaɗi yake sanyashi ba,
Da ƙarfi ya janye kwakwar aikuwa a firgice hosana ta farka,fuskarta a yamutse,zuba mashi ido tayi tana kallonshi,muryarta a kasalance ta ambaci sunanshi"daddy!"
"Na'am,hosana,"ya amsa mata,yunƙurawa tayi dakyar ta miƙe daga zaune tana ƙare mashi kallo kafin ta kwantar da kanta asaman kafaɗarshi,tana faman lumshe ido saboda baccin da tasha,
"Kin tashi lafiya?ko baccin bai isheki bane?
A shagwa6e tace"Ya isheni,yunwa ma nake ji,Cikina babu komai,gashi ko wanka banyi ba,Su jahad duk sunyi wanka basu tashe ni ba,balle inyi nima,"ta ƙarasa maganar tana kallonsu sehrish dake a bakin gadon,murguɗa masu baki tayi tare da harararsu,
"Shikenan,bari in na fita yanzu zanyi ma azmee magana,sae ta shirya maki lunch ko"?
..ɗaga mashi kai tayi alamar eh,
Miƙa mata ledar kwakwar yayi"kar6i nan,tsarabarki ce,ta masallaci kada ki ɗanma kowa kinji ko"?
Fuskarta ɗauke da murmushi ta kar6i ledar daga hannunshi
"Nagode sosai daddyna,kuma bazan ɗan masu ba,"
Wurga mata harara jahad tayi tare da cewa"Sannu ko?daddynmu zakice ba daddyna ba,ae bake kaɗae bace a wurinshi ba,"
Gatsina mata hanci hosana tayi tare da ƙara rungumo Abusufyan ajikinta don suji haushi,hakan ba ƙaramin dariya ya bashi ba,
"Daddy,ƙamshin turaren jikinka akwai daɗi sosai Allah,"tayi maganar tare da sanya hancinta ajikin rigar shaddar jikinshi tana shaƙar ƙamshin turaren kamar wata mayya,
"Idan kinaso ma,zan ɗauko maki kwalbar turaren gaba ɗaya,sae ki dinga shafawa kema hakan yayi maki"?
Girgiza kai tayi"a'a daddy,kabarshi kawai,Ya Omar ya hanani shafa turare,idan na shafa wannan turaren zaiyi ƙamshi sosai,kuma idan Yaji bazaiji daɗi ba,zaice hosana bakijin maganata ko?to daga yau babu ni babu ke,ni bazan zauna da mai kunnan 6era ba,'
Fashewa da dariya su jahad sukayi,tuni hosana ta ɗaure fuskarta tana harararsu,Abusufyan yace"yayi kyau babyn Omar,yana da kyau ki dinga jin maganarshi,kina yi mashi biyayya,kada ranshi ya 6aci,"
Cike da jin kunya hosana ta janye jikinta daga na Daddynsu,ta janyo pillow ta rufe fuskarta dashi,
Wayar Abusufyan ce ta shiga yin ringing,har lokacin fuskarshi ɗauke da murmushi,yace"Bari na shiga ciki,zansa azmee ta shirya maku launch,"
"To daddy,"suka amsa mashi da sauri ya fuce,
*JUNAID ROMEO*
Tashin hankalin da ba'a sama shi date,Tun wurin ɗaurin aure da junaid yaji sanarwar ɗaurin auren Babban yayansu,tare da Rishi ɗinsa,acikin masallacin ya yanke jiki ya faɗi a sume,saboda baisan da zancen ɗaurin auren ba,kwatsam yaji ana sanarwar,
A bedroom ɗinsa Omar ya kwantar dashi,bayan sun yayyafa mashi ruwa ya farfaɗo,koda ya buɗe idanunshi yaga Abbansu ga kuma yayyansu Isha da Abbas,ga Marshal Omar da sauran matasan duk suna tsaye akanshi,Fashewa yayi da matsanancin kuka mai cin rai,Cikin shesshekar kuka yace"Wayyo Allah na!Wlh an cuce ni,Abba kana sane da cewar ni ke son sehrish amma ka aura ma babban yayan mu ita,wlh bazan yarda ba,Ae ni na fara sonta,don me za'a aura mashi ita!ashe baku sona,hakanan kuke nuna mun soyayya,Wlh nidai bazan yarda ba,abba ka cuce ni sau nawa ina faɗa maka cewar inasonta,Ita nake da burin in aura amma....." bai ƙarasa maganar ba,Omar ya daka mashi tsawa wadda ta gigitar dashi,
"Rufe ma mutane baki junaid!shashasha kawai!Abban ne kaka cewa ya cuce ka?kai ko kunyar yin zancen aure agaban mu baka ji?ubanwa zaiyi maka aure da ƙananun shekarunka?kai da ita waye zai raini wani in anyi maku auren"?
Tafin hannayensa ya sanya tare da rufe fuskarshi,yana cigaba da kukan kuma hakan baisa ya daina sambatun da yake yi ba,
"Ya omar ba zaka gane bane,Abun da ciwo,wlh ina sonta sosai,ina son rishi,kuma itama tana sona,wlh ba babban yayanmu take so ba,Ni take so,don me za'a aura mata shi..."
A zafafe Omar ya zabura zai kai mashi mari a kan fuskarshi,da sauri Abba ya ruƙo hannunshi tare da cewa"Kuyi mashi uziri,wlh nasan yana sonta sosai,banta6a tunanin cewa junaid ya san so ba,ni duk a tunani na wasa yake yi mun,ashe dagaske yakeyi,dole yaji ciwo acikin zuciyarshi saboda ya saba da ita sosai," muryarshi a sanyaye yayi maganar,Abun ya ta6a mashi zuciyarshi,tsananin tausayin junaid ne ya kamashi,
Shi kanshi marshal Omar jikinshi ba ƙaramin sanyi yayi ba,kowa yasan da irin shakuwar dake atsakaninshi da sehrish amma ba suyi tsammanin cewar dagaske sonta yakeyi ba,
Hatta su ishaq dake tsaitsaiye cirko cirko agaban gadon nashi ba ƙaramin tausayi ya basu ba,duk yabi ya burkice,fuskar nan tayi jawur da ita,jijiyoyin jikinshi duk sun bayyana,
Adai dai lokacin da Abusufyan ya ƙaraso kopar ɗakin junaid ɗin,kasa shiga ciki yayi saboda jin maganganun da sukeyi aciki,hankalinshi ba ƙaramin tashi yayi ba,jin cewar junaid sehrish yake so,kuma adalilinta ne ya suma a masallaci,
Duk yadda suka so su shawo kan junaid da lallashi don yayi shiru abun ya faskara,hancinsa har ya fara bleeding,hankalinsu yayi mugun tashi,
Matsawa sukayi kusa dashi suna lallashinsa,Ja da baya ya dinga yi asaman gadon har ya ƙure ma head board ɗin gadon,sautin muryarshi ashake saboda tsabar kukan daya sha,
"Ku rabu dani,bana son ganin kowa!ba kunfi so na mutu ba!to zan mutu ne yanzun nan sae hankalinku ya kwanta,"
Hawaye ne suka cicciko tab a idanuwan kowannansu,
"Junaid dan Allah kayi haƙuri,Allah ya riga daya ƙaddara faruwan hakan,dama can ita ba matarka bace," Acewar Abbas,
Girgiza kai ya shiga yi yana cewa"yaya abbas,bazaku gane bane,bakusan yadda nake ji acikin zuciyata bane,tafarfasa take yi mun,wlh bazan iya jurewa ba,inason rishi sosai,idan har kuna so kuga farin ciki na,to akwance ɗaurin aurenta da babban yayanmu a aura mun ita shine kawai,in ba haka ba mutuwa zanyi,Wayyo Allah rishi ɗina,"yana magana yana shessheƙar kuka,
Abbas yace"Calm down ur mind junaid,akwai mata da yawa agari suna yawo kyawawan gaske,ga ƙanwar matata nan Amal,baka ganta ba ƴar ƙarama dai dai kai,idan kayi hakuri zaka samu wadda tafi ta ma,"
Bubbuga kafafunshi yayi asaman gadon tare da cewa"Ya Abbas wlh banson kowace mace in ba ita ba,Sehrish itace juliet ɗina ita kawai nakeso,kodai aban rishi ko kuma in haɗiyi zuciya in mutu,"to fa,!junaid ya tashi hankalin kowa,yaƙi saurarar kowa,yau an ta6a romeo shugaban ƴan soyayya,
Cikin lallashi Abbansu ya ambaci sunanshi"Babyn Abbanshi,"
Wani irin kallo ya wurga ma abban nasu idanuwan nan sunyi luhu luhu saboda tsabar kukan daya sha,
"Ni ba babynka bane,Romeo ɗin mommynsa ne,saboda baka sona Abba,"ya karasa maganar yana faman matse kwallar dake sharara daga cikin idanuwanshi,
Shiru Abbansu yayi bai ƙarasa maganar tashi ba,junaid yafi jin haushinshi akan kowa,saboda yasan da cewar yana sonta amma ya ɗaura mata aure,duk da shi bai ɗauki maganar tashi serious ba,sae yau daya haukace masu,
Turo ƙopar Abusufyan yayi jikinshi duk ya mutu,tsabar tausayin junaid ne ya kamashi,
Juyowa suka yi suna kallonshi,matsa mashi hanya sukayi ya wuce,har izuwa gaban gadon junaid din,
Zuba mashi ido yayi yana kallonshi,duk ya fita cikin hayyacinshi ya zama abun ban tausayi,wannan ya tabbatar mashi da cewar ba ƙaramin son sehrish yake yi ba,
ɗagowa junaid yayi tare da kallon Uncle ɗin nasu,Cikin shessheƙar kuka yace"Un..cle!hada kai aka ɗaura ma rishi ɗina aure da babban yayan mu,bayan kunsan cewa ina sonta sosai,"
Hawa saman gadon abusufyan yayi tare da janyo junaid ya rungumoshi ajikinshi yana ɗan bubbuga bayanshi da hannunshi,cikin lallashi yace"Junaid,Ni bansan cewa kana sonta ba,da banyi kuskuren aura ma rafayet ita ba,kasan cewa inason ka sosai,kowa ma yana sonka,kuma zamu iya yin komai saboda farin cikinka,hatta rayukan mu ma zamu iya badawa domin ceto rayuwarka,balle kuma ƴar uwarka?sae ita zata gagara?"
"Amma..uncle..meyasa ku ka ɗaura mata aure da babban yayan mu?maimakon ni"?daƙyar yake magana,
"Kayi haƙuri junaid,dama Allah ya ƙaddara cewar ita ba matarka bace,Matar babban yayanku ce,"
ɗagowa yayi daga jikin Abusufyan din fuskarshi jaga jaga da hawaye hada majina,yana kallon uncle ɗin yace"yanzu kuna nufin cewa,babu ni babu rishi?in haƙura da ita kawai?kun za6i ku rasa ni kenan"?
ruƙo hannunshi abusufyan yayi tare da sassauta muryarshi yace"haba junaid,in sha Allah ba zamu rasa ka ba saboda sehrish,ae ba ita kaɗai bace ba,Ko ka manta cewar su ƴan ukune?kuma kamanninsu ɗaya,Idan kayi haƙuri zan baka auren ɗaya daga cikinsu,"
Da sauri Marshal Omar ya katse mashi hanzarinshi da cewar"Wacce acikinsu,"?
dariya abbansu yayi ganin yadda omar ya ɗan tashi hankalinshi,
Abbas yace"Uncle,kada fa kayi mashi alƙawarin auren ɗaya daga cikinsu,saboda junaid bai da wayau baisan wasa ba,kuma koda za'ayi mashi aure ba yanzu ba,sae yayi hankali nan da in ya kai shekara talatin,"yana kai ƙarshen maganarshi,Ishaq ya ɗaura da cewar"Bazai yiwu ba ayi ma junaid aure a yanzu,bayan ga yayyensa nan duk sun manyanta kowa na bukatar aure,yayi haƙuri dai akwai matar abokina na nan,yanzu haka tana dauke da ciki,idan ta haifi jinjirin muka ga mace ce,sae ayi masu magana,su ajiye mashi ita,in ta girma lokacin yayi hankali sai a aura mashi ita,"
Suna cikin maganar nan,Junaid ya sume,a jikin Abusufyan,a ruɗe abusufyan ya shiga jijjiga shi yana kiran sunanshi"Junaid!Junaid!!"
Hankalin Abbansu atashe yace"Duk laifinku ne!meyasa bazakuyi shiru da bakinku ba,gashi nan ya ƙara sumewa,kuma ina da tabbacin cewar maganganun da kuke gaya masa ne suka ƙona mashi rai,"
Hannu Omar yasa tare da ɗauko bottle water ɗin dake ajiye saman side drawer dinsa,ya cire murfin tare da mika ma abusufyan,A hannu ya tar6o ruwan sannan ya watsa mashi a fuskarshi,
Dogon numfashi yaja tare da sauke nauyayyiyar ajiyar zuciya,
Shafa fuskarshi Abusufyan yayi tare da cewa"Junaid,"
Tunkafin ya buɗe idanunshi yace"Uncle mutuwa zanyi,"
"Junaid dan Allah kadaina kira mana mutuwa,Indai kan sehrish ne,NI NAYI MAKA ALƘAWARIN CEWA ZAN AURA MAKA ƊAYA DAGA CIKINSU IN HAR TANA SONKA,"
Muryarshi a kasalance yace"Uncle nasan wasa kake yi mun,kada kayi mun alƙwarin da bazaka iya cika mun ba,Zan haƙura kawai in rungumi ƙaddarata,"_
Wannan maganar da junaid yayi ba ƙaramin kashe masu jiki tayi ba,
Tuni hawaye suka cicciko a idanuwan Abusufyan,muryarshi na kerma yace"meyasa kace haka junaid"?
"Uncle,bani da wayau,ni yaro ne har yanzu,kowa yana yi mun kallon sakarai,kuma bani da aikin yi,a haka zaka bani auren ƴarka""?
A hankali wasu siraran hawaye suka shiga gangarowa a saman fuskar Abusufyan,daƙyar ya iya buɗe baki yace"Junaid!duk rashin wayonka baka kaini ba lokacin da ina yaro,bana jin magana har sa'insa nake yi da Mahaifiyata,na iya rashin kunya saboda ni bana jin kunyar kowa,ni ina mu'amala da mata muje party,muje night club,Ka faɗamun ɗaya daga cikinsu wanne kake yi?
"Ko ɗaya bana yi"ya bashi amsa,
Murmushi abusufyan yayi kafin ya cigaba da cewa"kana da kyakkyawar zuciya junaid kai mutumin kirki ne,kana son kaga farin ciki a fuskar kowannan mu,saboda me Ni zan gaza sanya ka farin ciki?Duk da banajin magana amma ahaka Mahaifin Oummansu Sehrish ya bani auren ƴarsa,Nima don haka daga yau ka sanya aranka cewar na baka Auren JAHAD!idan ma akwai mai sonta cikin yayyenka sai dai yayi haƙuri yabar maka,
Wani irin Farin Ciki ne ya lullu6e junaid,lokaci guda ya nemi kukan da yake yi ya rasa,bashi kaɗae ba hatta sauran ƴan uwan nasa dake tsaye a wurin ba ƙaramin daɗi suka ji ba,Musamman Abbansu,Yaji daɗi har cikin ranshi,
Cike da zolaya abusufyan ya kallesu tare da cewa"Ko akwai mai ja acikin ku ne"?
Fashewa sukayi da dariya gaba ɗayansu,tare da haɗa baki aurin cewa"Mu mun isa?Uba ya mallaka ma ɗansa auren ƴarsa?waya isa yaja daku?ae magana ta ƙare"
Sae lokacin junaid ya fashe da dariya har fararen haƙoransa suka bayyana masu ɗauke da matsakaiciyar wushirya siririya,mai kyan gaske,
"Surukina,fadamun me kakeso yanzu"?
Cikin shagwa6a junaid yace"Maganin ciwon kai,sannan ina jin yunwa sosai,"
"Bari inyi ma jahad magana takawo maka,hakan yayi maka"?
Cike da jin kunya junaid ya rufe fuskarshi da tafukan hannayenshi,yana dariya ƙasa ƙasa,
Zolayarshi suka shiga yi,har sai da suka sanya shi farin ciki sosai,sannan suka bar cikin bedroom ɗin nashi,ya kasance shi kaɗae ne acikin ɗakin kwance asaman gadon,kamar wani zautacce sae faman sakin murmushi yake yi,bakinshi yaƙi rufuwa,
Turo ƙopar ɗakin nashi,akayi da sauri yakai idanunshi wurin,Azmee ce ta shigo hannunta ruke da tray,lunch ne ta shirya mashi,ƙarasawa tayi tare da ajiye mashi tray ɗin saman front table din gadonshi,
Mikewa yayi daga zaune,yana gaisar da ita,
"Ina yini Aunty azmee,ya aiki,"
Fuskarta ɗauke da murmushi tace"Lafiya lou junaid Alhamdulillah,"
Ta karasa maganar tare da ɗaukar plate ta buɗe warmer mai dauke da chicken pepper soup serving spoon ta sanya tana ɗaukar cinyar kazar tana sanya mashi a plate,kallonta yakeyi sae ya dinga ganin kamar jahad ce,saboda tsabar son ya ganta musamman da yaji an mallaka mashi ita,
"Idan ka kammala ci,ga magani nan Uncle ɗinku ne yace na baka kasha,"tayi maganar tana nuna mashi maganin dake ajiye asaman tray ɗin,
"Nagode sosai Aunty azmee,"
"Na lura kamar kana cikin farin ciki sosai yau,"_
Murmushi ya saki tare da cewa"Aunty azmee,Am so,so happy today,Uncle abusufyan ya bani auren Jahad,Ya mallaka mun ita,"
Waro ido waje Azmee tayi cike da mamaki tace"Wai dagaske"?
ɗaga mata kai yayi alamar eh,Hannayenta ta daga sama cike da tsantsar farin ciki tace"Alhamdulillah!Allah na gode maka!ashe dae ina da rabon ganin aurenka junaid,Allah ya nuna mana lokacin,"
"Ameen ameen,"ya amsa mata,
"Dan Allah kaci abincin nan sosai,kaci ka koshi angon jahad,"
Rufe fuskarshi yayi yana dariya ƙasa ƙasa, itama dariyar ce ɗauke akan fuskarta har ta kammala zuba mashi abincin,sannan ta kama hanyar fita daga ɗakin,sae da junaid yaji alamun ta bar bedroom ɗin nashi sannan ya buɗe fuskarshi yana faman sakin murmushi
*Haroon*
Motarshi na qoqarin shiga cikin hotel yaji an ambaci sunanshi"Ya Haroon,"gabansa ne ya faɗi rass jin Muryar mutum mai mahimmanci a wurinshi,da sauri yaci burki tare da zuge glass ɗin motar a slow,
Tsaye take jikinta na asanye da Uniform,yadda kasan mahaukaciya,gashin kanta duk ya tarwatse ya hargitse,babu gyara,ƙafafunta babu takalma,tayi buɗu buɗu da ita,waro ido waje haroon yayi yana kallonta,tamkar a mafarki,kusan minti 5 kafin ya buɗe motar,ya fito har lokacin kayan jiya ne ajikinshi,a hankali yake tunkararta yana ƙare mata kallo,ita kuwa da gudun gaske ta tunkareshi,faɗawa tayi saman ƙirjinshi tare da zagayo da hanneyenta ta bayanshi,ta ƙanƙame shi sosai,lokaci guda ta fashe da matsanancin kuka,
Lumshe idanunshi yayi tare da sanya hannunshi abayanta,yana ɗan bubbuga bayan nata,a hankali ya ambaci sunanta"AMRISH"
Boss tabarku da tunani,Bashin friday ne na biyaku,kowa yasan cewa weekend banayin posting,Don haka mu haɗu On monday,in Allah yakaimu da rai da lafiya,don jin Yadda zata kaya👍
*SALON NA DABANNE🔥*
*kada fa ku manta har yanzu muna acikin Littafin Abban Sojoji ne Takun ƙarshe wanda Ni hafsat Bature Na rubuta*
💋Boss Bature💋*
Join this link to follow my tiktok acct👇
https://www.tiktok.com/@boss_bature?_t=8WKx0lm4jaP&_r=1
قصة حب