Showing 3001 words to 6000 words out of 432432 words
Chapter 2 - Abban Sojoji Book 2 Hausa Novel Complete
ɗauki kalbar turaren SHUMUKH ya feshe shi sannan ya mayar ya ɗauki wani turaren na Jar yana fesawa, mutun ne mai tsananin son ƙamshi shiyasa baya gajiya da bin jikinsa da turare,
Shiru sehrish tayi zuciyarta na ɗar ɗar, kusan 15 minsa sannan Boss Man ɗin yace "Ni zan zo ne"? Ya tambaya yana jiran amsa,
Cikin sauri sehrish ta ƙarasa hankali atashe ta tsaya daga bayansa jikinta na rawa,
Cikin natsuwa yaso ma magana" Wacece ke"?
Waro ido waje sehrish tayi jin abunda yace murya na rawa tace "Ni.....mai.....aiki...ne ...." a wani irin slow sgr ya juyo kai tsaye ya tunkare ta gadan gadan, a tsorace sehrish ke ja da baya tana kallonsa tuni zufa ta gama wanko mata sharkaf a jikinta,
Sam idonsa basa a kanta ƙasa suke, har sai da suka ƙurewa bangon gaba ɗaya, yarfa hannu sehrish ta shiga yi a tsananin tsorace take karanto addu'o'in da duk suka zo mata abakinta, kuma abayyane take yi saboda tsaban ruɗi tuni ƴan hanjin cikinta sun motsa, gaba ɗaya jikinta rawa yake yi kamar wadda sanyi yakama,
Hannunsa yasa ya daki wall ɗin data ke manne ajikinsa ya aza hannun anan jikin bangon ya dafe sannan yace "ƙarya ke bana so arayuwata, am gonna ask u some questions idan aka min ƙarya za'a fuskanci matsala,"
Ya faɗi yayin da idonsa ke a lumshe tamkar a datse suke ba don komai ba sai don gudun kada mai aikin ya Sume a ƙaro na biyu saboda launin ƙwayar idonsa dake razanar da shi, .
Kallon shi kawai take yi zuciyarta na bugawa da ƙarfi, daker take haɗiye yawu ga wani fitsari daya matse ta tunda taji ya ambace ta da mace tasan cewa ya gano ta kenan,
"maca ce ko Namiji"? ya tambaya yana jiran amsa,
Shiru tayi tana tunanin amsar da zata bashi, muddin tamasa ƙarya wannan ba ƙaramin shaqa zata sha ba,
Wannan shirun da tayi masa shiya fusata shi, buɗe Blue eyes ɗinsa yayi duka akanta , ta firgita sosai amma sam ta sanƙare ta gaza motsi da alama suman tsaye tayi
Hannunsa yasa ya damƙi hular kan sehrish yayi wurgi da ita tare da mayafin duka, nan take sumar kanta tasoma warwarowa tana saukowa saman kafaɗarta, kyakkyawan sumar kanta mai matuƙan kyan gaske ga laushi,
mayar da hannunsa yayi saman gashin bakin da take sawa ya cire shi shima, nan take ainihin kyakkwar fuskar reesh ta bayyana a matsayim mace 😊😉
sam fa bata motsi idonta sun kakkafe sun ƙame, kamar wata saƙago haka tayi,
jinjina kai sgr yayi maganar Adams ta tabbata, yayi mamakin ganin yarinya ƙarama kamar wannan da ƙarfin halin Yin shigar Maza tazo gidan sojoji aiki, ko nawa aka biyata don tayi hakan? Ya tambaya aransa, sam shi baya tunanin ta haura 12years saboda ƙarantarta dayake gani agabansa Ko shouder ɗinsa tsayin sehrish bai kai ba, daga tsaye inda yake yana kallon tsakiyar kanta saboda ba ƙaramin tsayine dashi ba, kowa yazo gabansa kallon ƙarami yake masa,
Janye hannunsa yayi daga jikin wall ɗin da sehrish take sannan yayi tattaki izuwa inda fridge ɗinsa yake, buɗewa yayi ya ɗauko bottle water mai sanyi sannan ya dawo inda take tsaye,
ya buɗe murfin ya yayyafa mata, a wani irin firgice sehrish ta girgiza ta dawo in sense ɗinsa, sai faman zazzare kyawawan idanunta take, bin chest ɗinsa tayi da kallo izuwa face ɗinsa cikin tsoro, hannu tasa ta shafa sumar kanta gabanta ne ya faɗi jin wayam babu yar hularta, hankali tashe ta wurga idonta inda sgr yayi watsi dasu.........nan fa tashiga faɗin "innalallahi wa'inna ilaihirraji'un dan Allah kayi haƙuri.....nashiga ukuna........' tana kuka tana magana , gaba ɗaya yayi mata rumfa tamkar Zaki haka take ganin sa agabanta 😳😳😳
Idonsa na kumshe yana sauraronta left hands ɗinsa na riƙe da bottle water ɗin, yayin da ɗayan hannun kuma ya mayar dashi jikin bangon ya dafa, sehrish kuma na agabansa suna fuskantar juna,
"haɗiye wannan kukan bana so" cikin hanzari sehrish ta dakatar da kukan tashiga taitayinta, bakomai take kallo ba fa ce damtsen hannunsa, tunani kawai take yarda zai kai mata naushi tabbas tasan sai dai Uwarta ta haifi wata (Hafsat bature ana magana) 😂
Cikin natsuwa yasoma magana__________________________________
Abt payment 300 ne, still muna free pages ne wanda suka shirya 08103884440 sumin magana
👍💋💋💋ABBAN SOJOJI💋💋💋*
*🔥The Father Of Soldiers🔥*
ﻗﺼ�? ﺣﺐ ﺭﻭﻣﺎﻧﺴﻴﺔ ﺑﻴ�? ﺳﺤﺮﻳ�? ﻭﺍﻟﺠﺮﺍ�? ﺍﻟﻌﺎ�? ﺭﺍﻓﻴﺖ❤🔥💞💘�?
*Story & Written by*
*Hafsat Bature Muhammad*
~💋BOSSLADY💋~
_Sabuwar Marubuciya, mai tafe da sabon salo💫_
*Abban Sojoji part 2*
*EPISODE 2*
*💞LAFAZI WRITTERS ASSOCIATION*💞
Cikin natsuwa ya soma magana "tambaya biyu kawai Wacece ke? Kuma waya turo ki"?
Cikin rawar murya sehrish tace "Ni ba kowa bace ba, kuma babu wanda ya turon.......'. Interrupting ɗinta yayi da cewa "ki mun magana a hankali don bana fahimta sosai,"
Gyara muryarta tayi sannan taci gaba da cewa "Sunana Sehrish, kuma ni babu wanda ya turo ni, banzo da nufin na cutar da kowa ba, aiki kawai nake don nasamu kuɗi........' buga wall ɗin da yayi yasata dakatawa a tsorace "Nace wa ya turo ki!!?
Hankali atashe tace "Allah shine shaidata, wlh ni babu wanda ya turoni, banzo da nufin na cutar da kowa ba, ƴan uwana ne Basu lafiya an kwantar dasu asibiti ana buƙatar kuɗin aiki shine na nemi aiki gidan wata hajiya...............sehrish bata 6oye masa komai ba ta faɗa masa tass dalilin zuwanta da dalilin yin shigarta na maza batayi masa ƙarya ba ko kaɗan, ta ƙarasa masa labarin tana faman zubda hawaye tsoranta wane hukunci zaiyi mata don tasan watan Cin Ubanta ya tsaya, shiru su kayi na wani lokaci, kafin daga bisa ni Babban yayan yaja da baya ya juya
bedroom ɗinsa ya shige kafin daga bisa ni, ya fito hannunsa ɗauke da wayarsa wuri yasamu ya zauna saman sofa ɗin sannan yaba sehrish damar ta matso kusa, sai da tafara tattara hularta da mayafin da yayi watsi dasu, ta ruƙesu a hannunta sannan jiki asanyaye ta matsa inda yake kamar wadda tayiwa sarki ƙarya, jikinta sai faman kerma yake,
yace "su nan su? da sunan state da sunan hospital da aka kwantar dasu? and the date!?
Murya na rawa tace "Hosana Sayyad, da jahad sayyad an kwantar dasu a Fmc katsina........"
duka ta faɗa masa hada date ɗin da aka kwantar dasu duka don bata manta ba,
danna wayar yashiga yi kafin daga bisani ya danna calling, ta soma ringing, nan take aka ɗaga wayar suka soma magana,
Duk sehrish na tsaye tana kallonsa yadda yake speaking anatse,
Bakowa ya kira ba face Babban Likita, dama already sai da yafara tura masa message na sunan yaran da bayanan dayake son sani sannan yakira, kuma anci sa'a On duty yake,'
Tabbas yayi mamakin ganin kiran Surgeon general rafayet, kuma yayi mamakin jin sunan yaran da yakeson aduba mishi files ɗinsu, tabbas yasan yaran, waɗanda Omar ya taimaka daga wurin Police, ranshi ne ya bashi cewa may be Omar yasanar mishi game dasu ne that's why yake neman Information akansu , without wasting time Babban likita ya binciko masa files ɗinsu Hosana Da jahad na rashin lafiyarsu duka bayanan ya masa snaping dinsa ya tura masa ta whatsapp ɗinsa,
bayan sun kammala phone ɗin, Sgr ya shiga whatsapp ɗinsa ya duba, sai ga Files ɗin yaran na rashin lafiyarsu raɗau da sunansu ajiki Hosana Sayyad Da Jahad Sayyad,
Ajiyar zuciya yasaki yanzu ya shaida maganar Yarinyar duba time yayi dare yayi ga wani bacci daya ke ji gashi ko dinner ɗinsa bai cin ba, Ga yarinyar nan dake tsaye duk a tsorace don yana ganin yadda yatsun ƙafarta ke kerma,
gyaran murya yayi sannan yace "You're not guilty of anything, the mistake you made shine shiga na maza after knowing that it is forbidden in Islam for a girl to dress like a male,' yayi maganar yana danna wayar hannunsa...
Murya na rawa Sehrish tace "bazan ƙara ba........'
Jinjina kansa yayi kafin yace"As from now i don't wanna see u wearing this dress again! u can go" ya bata Umarni ta tafi
Wayyo Allah sam sehrish ta gaza rufe bakin ta don mamaki, kama hanyar fita tayi tana waiwayansa da kansa ya shiga saving dinner ɗinsa yana ci,
Tsantsar farin ciki ne ya cika sehrish sam ta rasa inda zata tsoma ranta, ae tana fita daga part ɗinsa ta buga Wani uban tsalle na murna fuskar nan kamar wacce akayiwa Albishir da gidan Aljanna, watsa wa tayi da gudu gudu sauri sauri tana tattaka Stairs ɗin tana saukowa down a babban falon dama ba kowa nan fa tashiga rawar murna tana zagaye sofas ɗin dake a falon kamar wata yar baby,
Duk wannan abun da take yi akan idon Sgr domin kuwa ya biyo bayanta ashe yana daga can Upstairs yana kallonta, don bai cika yarda da mutane ba shiyasa yayi following back ɗinta don yaga reaction ɗin da zata yi bayan da ta fita daga part ɗinsa,
abunda yayi tsammani ba shi ya gani ba, zura hannayansa yayi cikin aljhun wandon baccinsa yana kallon Ikon Allah,
Sam sehrish bata son babban yaya yana kallonta ba, ita kaɗai tasan farin cikin da take ciki, ta jima tana mamakin yarda Sgr ya kasance mai matuƙar sauƙin kai har haka a tunaninta zai bata horo mai tsanani daga nan akore ta kuma daga gidan,
Nace "*Sehrish ba ke kaɗai ba hatta Hafsat bature da sauran makaranta labarin rayuwarki sunyi tsammanin hakan tabbas Surgeon general Rafayet ya bamu mamaki, haƙiƙa shi ɗin na daban ne*"😍
Yanzu abunda ya rage wanda take yi ma fargaba shine sauran matasan gidan shin zasu amince a ranar da ta bayyana kanta a matsayin mace !? Uwa uba Abban su,kuma tuna wannan yasa jikinta yin sanyi, dakatawa tayi daga yin wasan da takeyi na zagaye gujerun babban falon, jiki a mace ta kama hanyar bedroom ɗinta, ranta ne ya bata cewa akwai mai kallonta, Cikin sauri ta juya ta kalli upstairs a time ɗin har sgr yabar wurin ya koma part ɗinsa
Ganin wayam yasa ta sauke ajiyar zuciya,ba ɗakinta ta wuce ba ɗakin aunty azmee ta wuce don sam tagaza daina murna tafison ta sanar mata abunda yafaru yau ɗin nan da zafi zafinsa,
Haryanzu hannunta na ruƙe da hularta da mayafin duka ta ƙanƙame su, tsayawa tayi a ƙopar ɗakin tana bubbugawa ,
Azmee dake zaune saman darduma tasha hijabi ajikinta ga qur'ani agabanta hannunta kuma na riƙe da Cazbaha sai faman gyangyaɗi take yi, jin bugun ƙopa yasata cewa "Wanene"
sehrish dake tsaye a bakon ƙopan tace"Nice aunty azmee"
Murmushi azmee tayi tare da cewa "Ashe bakiyi bacci ba," tayi maganar tare da tashi daga dardumar ta buɗe mata ƙopa,
Shiga ciki sehrish tayi tana faman zabga murmushi,
a ɗan ruɗe azmee ke kallonta bayan ta rufe ƙopan tace"Yau wata rana! Sehrish kece da Murmushi haka a fuskarki? Wane albishir ne akayi maki?Cos I forgot when last naga wannan annurin a face ɗinki" cikin mamaki azmee ke wannan maganar kafin ta mayar da idonta kan Hular sehrish dake ruƙe a hannunta ta kuma cewa "Ikon Allah yau kuma hularce da mayafin duka a hannu?
Dariya kawai sehrish take yi daker ta tsagaita tace "Aunty azmeee abun mamaki! Abun farin ciki !"
Cike da ɗoki azmee tace "menene shi?
Nan sehrish ta shiga zayyana mata abunda ya faru tsakaninta da Babban yaya daga farko zuwa ƙarshe
Baki washe azmee ta ɗaga hannunta sama tana cewa "Alhamdulillah ! Alhamdulillah godiya ta tabbata ga Allah subhanahu wata'ala naji daɗin wannan lamarin sehrish domin kuwa Babban yaya shine nafi ji dama, gashi kuma cikin sauƙi ya amince wayyo Allah murna bansan inda zan sa kaina ba don daɗi" cike da jin daɗi azmee ke magana fuskarta a washe
Sehrish tace "Amma aunty azmee su fa sauran kina ganin zasu amince in suka sani"? Ni ina tsoran ta yarda zan fara fitowa a matsayin mace cikin gidan nan," tayi maganar murya asanyaye tana kallon azmee
Ƙarasawa azmee tayi ta dafa kafaɗarta sannan tace "Sehrish matsalarki tazo ƙarshe! tun da har babban yayansu ya amince ba ki da sauran damuwa, Abbansu ne kawai zamu jira muji ta bakinsa, yanzu abunda nake so dake kije kawai ki kwanta kiyi bacci zuwa gobe zamu ga yadda badaƙalar zata kaya idan matasan gidan nan suka ga tukur mai aikinsu a matsayin Mace lallai akwai tashin hankali, " azmee tayi maganar da dariya a fuskarta, sehrish kuwa dafe saitin zuciyarta tayi tana zazzare ido tace "Allah sa su amince suma,"
"Insha Allah" azmee tabata amasa afterwards suke yi sallama, sehrish ta koma bedroom ɗinta cike da zullumi haye wa tayi saman gadonta, ta janyo pillow ta rungume tana sakin murmushi tunawa da haɗuwarsu ta yau da babban yaya, Allah kenan a daren nan Haroon ya ƙuntata mata, har tayi addu'ar sai Allah ya nuna masa Iyakarsa akanta, to yanzu ga Iyakar tasa nan muddin sauran suka amince da ita kuwa, taci alwashin sai ta Ci mutuncin Haroon 😡👊
A fili tasoma magana " gajan haƙuri kenan Irin na ɗan adam, yanzu da na kashe kaina da shikenan nayiwa kaina, ashe Allah yana dab da kawomin sauƙi arayuwata," ta faɗi tana faman murmushi wani irin nishaɗi take ji ayau , ta kuma cewa "Anya ma zan iya bacci kuwa? gashi ina fargabar mai zai faru gobe? kwara kawai nayi Bacci na goben tayi saurin yi, AYI TA, Ta ƘARE kawai🙅, In jalasa jalasa 😂 in Zahaba Zahaba shine kawai 😅😂😹😹😹
tana gama faɗan hakan bacci yayi awon gaba da ita, kai kana ganin yadda reesh ke bacci kasan tana cikin kwanciyar hankali,
murmushi Hafsat Bature tayi tana kallonta wadda ke tsaye shigowarta kenan ta window tabiyo da suffar Farar Tantabara kasancewarta Aljanar sehrish, hannu tasa tajanyo bargo ta lullu6e sehrish dashi sannan ta 6ace 6aaat..............😇
______________________________________
Kwance suke acikin store ɗin su biyu abunsu, kamar yadda Jahad ta saba yi musu dabara, na jera masu jarkoki su koma kamar single bed sai su kwanta suna facing ɗin junansu sam bacci yagaza ɗaukarsu zullumin su mai zai biyo ba? Wata alƙibla rayuwarsu zata fuskanta yanzu?
"Jahad idan Aunty hafsat ta zubar damu ina kuma zamu dosa"? Hosana ta tambaya tana kallon jahad wadda ta zuba mata ido,
Cikin sanyin murya tace "Nima kaina bansani ba hosana, ina tsoran hakan," ta faɗi zuciya a karye
Hosana tace "Dama Allah ya ɗauke mu yakai mu duniyar sama ko? ko duniyar taurari inda ba mutane muyi rayuwarmu mu kaɗai tare da yaya Omar tunda kowa baison mu shi kaɗae ke son mu ko?
Wannan maganar ta hosana tasa jahad fashe wa da dariya daga kwancen da suke ta rinƙa 6a66aka dariya kaman kamar me,
Hosana ta ɗan 6ata fuska don ita bada wasa tayi maganar ba,
Daker jahad ta jinkirta da dariyar tace "Sorry hosana dole nayi dariya mana, wa kika ta6a ganin an ɗauke daga nan an kaisa sama ?
Shiru tayi tana zumbura baki, jahad taci gaba da cewa "sannan kince tare da yaya Omar kaɗai zamu tafi saboda yana son mu, Shin kin manta da Sehrish ne"? Ita kuma fa? akwai wanda yayi mana wahala ne kamarta? sehrish tana son mu fiye da kowa na duniyar nan, saboda mu tashiga duk wani hali da take ciki ayanzu duk da bansan yaya rayuwarta take ba...............wani irin kuka ne yaci ƙarfin jahad har takasa ƙarasa maganar da take yi,
Nan take jikin hosana yayi mugun sanyi tunawa da Sehrish ƴar uwarsu mai tsananin son su da ƙaunarsu, tuni itama idonta sun cicciko da hawaye murya na rawa tace "Ya Allah hada sehrish za'a ɗauke mu akai mu duniyar Taurari.....'
dakatawa da magana tayi ganin Jahad dake kuka ta fashe da dariya, wato tayi tazarce daga kukan da take Zuwa dariya ba don komai ba sai don jin abunda Hosana ke cewa, share hawayenta tashiga yi tana faɗin "Hosana wasan ya isa haka, muyi magana ta hankali, yanzu yaya za'ayi yaya Omar yasan halin da muke ciki kafin Hafsat da Momynta su sa azubar damu yakamata muyi tunanin hakan in ba haka ba zamu shiga wani mugun hannun ne ko mu ƙare rayuwarmu adaji..............' jinkirtawa tayi da maganar tana sauraron shawara daga wurin hosana,
"To ya zamuyi mu sanar mishi jahad? Bayan kullum waccen matar mai kama da samudawa mai kumatun alkubus tana tsare mu da ido duk in yazo tana hanamu kwakkwaran motsi,"
Shiru jahad tayi tabbas dole su nemi mafita in ba haka ba, zasu fuskanci tashin hankali
Can tayi wani dogon tunani tace "Hosana mai zai hana, mu samu paper da biro sai mu rubuta mishi, in yazo sai ki lalla6a kisan yarda zakiyi ki tura masa a aljihunsa? Ko da rungumesa ne sai kiyi kamar yarda kikayi a asibitin nan kin tuna"?
Murmushi hosana tasaki anzo inda keyi mata ƙaiƙayi kallon jahad tayi tace "Shawara mai kyau, amma taya zamu rubuta mishi to? Bamu da paper ba biro jahad,"
Shiru jahad tayi kafin tace "Akwai !!! Na tuna acikin wannan ɗakin da Momyn hafsat takaimu acikin wannan ƴar lokar naga Memo da biro,"
Cike da farin ciki hosana tace "dama ƙopa a buɗe take, yau ta manta bata rufe mu ba, jahad ki lalla6a ki ɗauko ki rubuta masa,"
Miƙewa jahad tayi tana faɗin "Zan fita dan Allah hosana karki biyo ni, nasan halin ki, in