Showing 102001 words to 105000 words out of 432432 words

Chapter 35 - Abban Sojoji Book 2 Hausa Novel Complete

kira tana cewa"Jahad!!Jahad!! ashe dama ya omar yana da aure shine bai fadamana ba,
    Yadda hossana ke kwala mata kira yasa ta fitowa daga kitchen cikin sauri ta nufe ta tana cewa"Hossana lafiya meya faru ne kike kwalamun kira? Ke da waye a waya? Ta tambaya a yayin da take ƙarasawa wurinta,
  duk sehrish ta kasa kunne tana jinsu, 
Cikin shessheƙar kuka hossana tace"Ashe dama ya omar na da aure bai fadamun ba," 
  Cike da mamaki jahad tace"kai haba wai dagaske? 
  "Eh mana gatanan muna magana awaya," ta faɗi rai a6ace tana miƙa ma jahad telephone ɗin,,
  Hannu jahad tasanya ta kar6i wayar sannan anatse tace"Assalamu Alaikum,"
fuska dauke da murmushi sehrish tace"Wa'alaikum salam," 
 Jahad tace"ina kwana aunty," 
  "Lafiya lou," sehrish ta amsa,
 Jahad ta kuma cewa"dagaske ne kece matar yaya Omar"? ta tambaya tamkar tana a gabanta, Sehrish tace "eh nice,"
  jinjina kai jahad tayi tare da ɗan ta6e baki tace"Amma bai ta6a sanar mana ba, dan Allah sabon aure ne ko tsoho "
  Ƙiriss ya rage sehrish ta fashe da dariya daƙyar ta basar da ita tare da cewa"tsoho ne, mun jima atare ynx haka ma ina ɗauke da juna biyu ina fata zaku zo suna in na haihuwa,"
   Jiki asanyaye jahad tace"insha Allah idan ya barmu zamu zo, amma aunty baki faɗa mana sunanki ba"?
   Ƙara kashe murya sehrish tayi tare da cewa"sunana Zainab amma mijina yana kira na da Hayaty,"

KARANTA ZAFAFA 2022

✓Gurbin Ido... Na Huguma (Zafafa2022)
✓Inaya By Mamuhgee (Zafafa2022)
✓Sanadin Labarina By Hafsat Rano (Zafafa2022)
✓Babu So... By Billyn Abdul (Zafafa2022)
✓Farhatal Qalb By Mss Xoxo (Zafafa 2022)


  Jinjina kai jahad tayi tare da kallon hossana wadda ke tsaye cikin ƙunar rai,
  Sun jima suna waya da sehrish kafin suyi sallama, mayar da wayar sehrish tayi ta ajiye saman seater ɗin, sannan ta koma tana faman tiƙar dariya,

   ɗagowa jahad tayi ta kalli hossana gaba ɗayansu jikin su yayi mugun sanyi, duk basu ji daɗin cewa ya omar yana da mata ba, sam hossana ta gaza jurewa komawa tayi saman 2 seater ta faɗa tare da kifa kanta tana kuka, jahad kuwa kitchen ta wuce saboda tabaro dankalin da take soya masu, ita kanta jurewa kawai take yi amma ba ƙaramin ɗaci taji ba na jin cewa ya Omar dinsu yana da aure, tsayawa tayi agaban fan din dake asaman gass sam ta kasa juya dankalin saboda tashin hankali, cikin sanyin murya tace"koma wacece matar shi ina tayata murna sosai, domin kuwa tayi dacen miji nagari........' kwalla ce ta zubo daga idonta ɗas ta zuba ƙasa, 😖


�?



   Shigowa omar yayi cikin falon nashi, sehrish na ganin shi nan da nan ta shiga natsuwarta, 
  "Ina kwana ya omar"? 
 kallonta yayi tare da sakar mata murmushi yace"lfy lou Alhmdllh, ki zauna mana," ya faɗi tare da samun wuri ya zauna asaman 3 seater, 
wuri tasamu itama ta zauna suna fuskantar juna,
   sunnar dakai tayi ƙasa tana jiran jin mai zai ce mata,
  Cikin natsuwa ya soma magana "Am really  sorry abt wht happend last night, banji daɗin abunda sgr yayi maki ba, nasan abun zai tsaya maki aranki,amma inaso ki sani ba yin kanshi bane! wannan allurar ce da kika kai mashi ya sanar dani cewa ke kika kai mashi ita...........' hankali tashe sehrish take kallon shi a tunaninta sgr ya tuna abunda ya faru ne, 
  Cigaba da magana omar yayi anatse yace"Calm down ur mind, sgr ba zai iya tuna abunda ya faru ba a yanzu amma fa dole ya tuna wata rana abun zai dawo mashi ne akan shi, so nake ki fadamun a ina kika samu allurar da kika kai mashi ? Da sanin ki kika kai mashi ita? Ya tambaya yana kallon fuskarta cike da tuhuma ,
  Lokaci guda duk ta dabarbarce ta rasa natsuwarta, 
    " Tell me the truth who brought it to u? don nasan ba ke kika dauko ta ba, in fact bamu da irinta acikin gidan nan...'
   shiru tayi tana kallon shi zuciyarta na raya mata ta fada mashi gaskiya kawai,
    murya na rawa tace"Ya omar ni ba da sani na ba Allah, babban yaya yayi mun rubutu a paper ya bani, ko a lokacin sai da nace mashi ni bansan meya rubuta ajiki ba, amma yace mun naje na ɗauko mashi kawai saboda baya cikin hayyacin shi ne, lokacin dana fito da takardar a hannuna  ina zullumin meya rubuta ajiki shine kawai sai ga h.....h.....' wani irin ruƙo taji anyima maƙoshinta tamkar wani abu ya tokare wurin,nan take taji numfashinta na shirin ɗaukewa gaba ɗaya, kakari tashiga yi tana ƙoƙarin furta sunan haroon amma sound ɗin ya ƙi fidduwa daga bakinta, abun mamaki abun al'ajabi, 
  Ganin yarda zufa ke tsattsafo mata gefe da gefen fuskarta gashi sai faman numfarfashi take yi sama sama,
  Hakan ba ƙaramin tayar mashi da hankali yayi ba cikin sauri yace"Ke lafiya meke faruwa ne? Ko baki da lafiya ne?
   cikin kuka tace"maƙoshina ne ke mun ciwo, nagaza furta sunan wanda yaban allurar raɗaɗi nake ji a wurin,
    tashi marshal omar yayi tare da ƙarasawa wurin frigde din dake a falon shi, buɗe wa yayi tare da ɗauko bottle water mai sanyi, sannan ya dawo ya zauna dab da sehrish ya buɗe murfin robar ya miƙa mata, cikin sauri ta kar6a tana sha sai da tashanye kusan rabi sannan ta janye tana faman sauke ajiyar zuciya,
  Hannu omar yasaka tare da kar6a robar daga hannunta yasanya murfin ya rufe sannan ya ajiye robar ruwan a ƙasa, mayar da idonshi yayi akan sehrish sannan cikin natsuwa yace"pls taimako nake so kiyi mana,bansan wacece ke ba amma har a raina naji, na yarda dake dan Allah karki sa na fara zarginki, ki fadamun gaskiya wanene ya baki allurar da kika kai mashi? allura ce mai haɗarin gaske a lokacin da Allah baisa na faɗo na ceceki a hannun shi ba tabbas ba zaki rayu ba....
   Hankali atashe sehrish ta ɗago idanunta tana kallon shi, nan da nan taji wasu hawayen sun sake wanko mata fuskarta cikin shessheƙar kuka tace"ya omar wlh ni bansan komai akai ba bazan iya cutar dashi ba kuma nima bazan so na cutar da kaina ba..........'
   jinjina kanshi yayi tare da cewa"to ki fadamun wanene ya baki allurar"? 
  buɗe baki tayi zata furta haroon nan take ta sake ji an damƙi maƙoshinta saboda zafin da taji kawai saita fashe mashi da kuka saboda ta rasa yarda zata yi ta sanar mashi........' 
  Zuba mata ido yayi yana kallonta tana ta faman shan kuka, tuni yaji tsananin tausayinta ya kamashi,musamman daya dinga ganin fuskarta kamar su jahad ne ke kuka, 
   Cikin sauri ya dakatar da ita da cewa"its okey, kiyi hakuri banyi hakan dan na 6ata maki rai ba, inaso kawai na gano wanda ya baki allurar ne don inyi investigation akan shi, amma tunda bakison faɗi, zaki iya tafiya, 
   tsagaitawa tayi da kukan tana kallon shi cikin sanyin murya tace"dan Allah  kada ka zargeni wlh bazan iya cutar da wani acikin gidan nan ba, saboda na ɗauke ku tamkar ƴan uwana na jini na.......'
     murmushi Omar ya ɗanyi kafin yace"don't worry ur self nima kamar yarda kika ɗauke mu haka muka ɗauke ki, ki kwantar da hankalin ki komai ya wuce insha Allah,amma aduk lokacin da kika tuna sunan wanda ya baki ita, ki hanzarta sanar mun pls......'
   "Insha Allah zanyi hakan," tashi tayi tare da yi mashi sallama ta nufi hanyar fita daga falo dinsa, a hankali take tafiya hannunta dafe da saitin zuciyarta, muryar shi ce, ta sake katse ta da cewa"yana buƙatar a gyara mashi bedroom ɗinsa yakamata ki je, a firgice ta juyo tana kallon shi, ganin yarda ta razana ne yasa shi cewa"ki kwantar da hankalin ki, kada abunda ya faru jiya yasa ki dinga jin tsoranshi, nasan ko wanene ɗan uwana, am really proud of him, ki saki jikin ki in ba haka ba zai gane cewa wani abu ya faru adaren jiya,
   jinjina mashi kai tayi tare da cewa"toh zanyi yarda kace," tana fadin hakan tasa kai ta fuce,
   Murmushi Omar yayi saboda tunawa da babban aikin da sgr yaso yayi jiya, tabbas da yarinyar ta rasa ranta don ayadda yake jin wannan ƙarfin ba ƙaramin illatata zaiyi ba,
   "godiya ta tabbata ga Allah subhanahu wata'ala da yabani ikon zuwa adai dai wannan lokacin har na ceci rayuwarta, na kuma taimaki ɗan uwana daga aikata wannan aika aikan," ya furta yana faman sauke ajiyar zuciya,

*************💋

Gaba ɗaya sun hallara a saman dining chairs suna yin breakfast dinsu, Abban su tare da junaid, sai Ayaan da jahan ga kuma su irfan khaleed da jabeer da kuma Fawan, har yanzu bai fara sanya riga a jikinshi ba sai dae gajeran wando kawai yake zurawa yayi ta yawon shi,
  "Aunty azmee ina reesh take ne, banganta ba"? Junaid ya tambaya yana kallon azmee dake tsaye tana saving dinsu, 
   Abbansu ma yace"tun ɗazu nake so in tambaye ta nima, yau banga daughter ɗita ba ina tashiga ne?
  Murmushi azmee tayi tare da cewa"tashiga sashen Omar ne," 
  cike da mamaki jabeer yace"wacece kuma sehrish? ko dai wannan yarinyar dana gani tana yawo acikin gidan nan? Ya tambaya yana kallonsu,
  irfan yace"nima ina taso na tambaya wlh, naga kyakkyawar yarinya tana ta yawo acikin gidan nan gwanin burgewa,"
  da buɗar bakin fawan sai cewa yayi "Oh wai dama mutun ce? Ae ni nayi tunanin ko idona ne ke ganemun ita shiyasa ban ta6a tambaya ba," dariya suka fashe da ita gaba ɗayansu banda shi fawan din da yayi mgnr, saboda shi bada wasa yayi maganarshi ba, duk a tunanin shi ko ya samu ta6uwa ne shiyasa yake ganinta, 
     "Sunanta Sherish tare da azmee suke aiki, amma na mayar da ita ƙanwarku ina fata zaku ji daɗin hakan, tunda dama baku da ƙanwa mace," acewar abbansu,
   kallon juna su kayi atare kafin fawan ya kuma cewa"ni duk ba wannan ba, wai ina tukur mai aikin mu ne? Nayi kewar shi sosai tunda muka dawo banga gifcin shi ba acikin gidan nan,"? ya tambaya yana kallon junaid dasu twins,
  murmushi suka shiga saki gaba ɗayansu batare da sunce komai ba, 
   Khaleed yace"wannan sullu6iyon mai aikin namu, dama nasan bazai kai labari ba halan an kore shi daga aikine"?
   Junaid ne yace"kai yaya fawan yanzu kuna nufin baku gane wanene tukur ba? Wannan yarinyar fa itace fa tayi shigar maza tana mana aiki........' 
  Saboda tsabar ruɗu har suna haɗa baki wurin cewa"Are u serious!? ɗaga kai yayi tare da jaddada masu maganar shi yace"of course ku tambayi abba kuji," 
   Kallon abban nasu sukayi suna jiran jin bayani murmushi yayi tare da cewa"itace mai aikin da kuka bari a matsayin namiji," 
   cikin mamaki suke kallon shi sam sun gaza cewa komai saboda abun yafi ƙarfinsu wai tukur mai aikinsu ne ya koma mace ? dama maca ce tayi shigar namiji kenan? Murmushi fawan yayi aranshi yace "lallaikam nama har gida," kamar abbansu yaji mai yace sai ɗagowa yayi ya kalli fuskokinsu yace"ko da gigin wasa bana son wani ya ta6a mun ɗiyata,ko kallon banza wannan ban amince wani yayi mata ba," 
   har suna haɗa baki wurin cewa"Insha Allah hakan ma bazata faru ba, ae ƙanwarmu ce," dariya junaid yayi ƙasa ƙasa saboda yasan halinsu sarai musamman fawan,

 Sehrish~
 
Koda ta fito daga part ɗin omar, wuri ta samu anan upstairs ɗin ta zuƙunnna tana shan kuka ba don komai ba sai don baƙin cikin kasa furta sunan haroon da tayi, taso ta sanar ma Omar kodan ta fita zargi amma hakan yaci turo saboda maƙoshinta da taji an shaƙe mata shi, babban abunda take fargaba shine kada su fara zarginta akan abunda ba laifinta bane, yanzu kuma duk ranar da sgr ya tuna da wannan abun daya faru a tsakaninsu dole ya tuhume ta, batasan wane irin kallo zaiyi mata ba,😖
  "Ashe so yayi ya kashe ni !" ta furta cikin sanyin murya, "ni bansan me nayi mashi ba, ya Allah ka kare ni daga sharrin shi, ya Allah kada ka bashi nasara akaina," 
  tana cikin wannan tunanin sam bata ji takon tafiyarshi ba, fitowarshi kenan daga part dinsa ya kimtsa cikin suits farare ba ƙaramin kyau suka yi mashi ba, 
  tsayawa yayi yana kallon ikon Allah yarinyar da yake ta faman jira ta gyara mashi bedroom dinshi itace zuƙunne tana shessheƙar kuka, cike da mamaki ya ƙarasa har inda sehrish take sam bata zaci ganin shi ba, sai dae taga ƙafafunshi masu sanye da haɗaɗɗun takalma, gabanta ne taji yayi wani irin bugu duk da bata san wanene ba amma tana da tabbacin cewa shi neeee saboda ƙamshin turaren nan nashi,
   ƙara ƙanƙame jikinta tayi tana faman zazzare ido a tsorace, muryarshi ce ta ratsa kunnanta da cewa"ke tashi tsaye," 
  cikin sauri sehrish ta miƙe tsaye jikinta na kerma kamar wadda taga wani horror sam taƙi yarda ta kalli fuskarshi saboda ta tsorata dashi, 
    shiru ya ɗanyi baice komai ba tamkar mai nazarin wani abu, hannunta yabi da kallo sai faman kerma yatsun hannun suke yi, 
  "Are u okey"? ya tambayeta,cikin sauri tace"eh" 
   "Okey agyaramin bedroom ɗina," yana faɗin hakan ya kama hanya  ya wuce,
  Sam takasa janye idanunta daga kallon bayanshi  har sai da ya 6ace ma ganinta, sannan ta wuce part din nashi, lokacin data shiga bedroom dinshi ba komai ta tuna ba face abunda ya faru atsakaninsu daren jiya, bin shimfiɗeɗen gadon shi tayi da kallo har yanzu zanin gadon a cukuikuye yake, saboda damben da suka sha jiya, hannu takai tare da yaye bedsheets ɗin nashi ta rungumo shi a kirjinta tana shinshina ƙamshin turarensa, ita kaɗae tasan irin yanayin da tashiga a wannan lokacin duk da firgicin da take ci amma hakan bai hanata jin wannan yanayin ba.............💋😉

*💋Boss💖Bature�?*✍️

A galabaice take hura wutar murhun wani irin uban hayaƙi yake fitowa baƙiƙƙirin duk ya cika kitchen din, idanunta sunyi jawur kamar na mai shan taba, matashiyar yarinyace da bazata wuce shekara goma sha huɗu ba aduniya, a wani matsakaicin gida na masu rufin asiri, jikinta na sanye da koɗaɗɗen zani na atampha tayi ɗaurin gaba dashi, duk ya yayyage jikinshi yayi baƙiƙƙirin saboda dauɗa, gaba ɗaya ita kanta yarinyar abun ban tausayi ce, ta bushe ta rame ta ƙanjame yadda kasan skelaton haka take, saboda kasusuwan wuyanta da suka firfito mata waje kamar zasu fito daga fatar jikinta saboda tsabar rama, saboda koɗewar da fatar jikinta tayi baza ma a iya tantace launin fatarta ba, fara ce ko baƙa 😢

sai faman goho take yi agaban murfin tana hura wutar da bakinta amma wutar taƙi kama wa, zuƙunnawa tayi gaban murhun ta zabga uban tagumi hawaye na faman kwararowa daga idanunta, cikin murya kuka ta soma cewa"Ya Allah ka kawomin karshen wahalar da nake sha acikin gidan nan........' 
   Muryar mammynsu ce ta katse ta da cewa"AMAL!! wai uban wa kike so yayi wankin nan ne? zaki fito kiyi shi ko saina maki dukan tsiya ne? Hankali atashe tace"mammy iccen girkin ne ɗanye baya ci, tun ɗazu nake faman wahalar hura shi amma yaƙi ruruwa," 
  Uban tsoki matar ta buga tare da cewa"wannan ba damuwa ta bace ba, ki tabbatar da kin hura wutar ta kama,sannan ki fito ki wanke mana kayan mu, bayan kin gama kuma ki share gidan," 
   cikin ƙunar rai ta amsa mata da "toh,"
Sannan taci gaba da hura wutar don ta kama, 
   cigaba da magana matar tayi tana cewa"Yayarki nacen gidan huta, ta manta dake gaki nan a wulaƙance kin zama tamkar baiwa a wurin mu, da ace tana sonki ae bazata barki a hannun mu ba,"
   Shiru Amal tayi hawaye na zuba daga idonta, har yau tagaza yarda cewa yayarta zata iya yi mata hakan, saboda me zata tafi tabarta hannun waɗannan mugayen? Ta tambayi kanta,
   muryar mammyn tasu ce ta sake katse ta da cewa"hmmm dama tsiyar talaka kenan anyi mata hanyar arziƙi amma ta manta da mutane, baƙin halinku iri ɗaya dana uwarku, ae duk laifin laila ne ko uban waya faɗa mata ana yiwa ƴa'ƴan kishiya abun arziƙi," tana zaune saman gujera ƴar tsugunno sai faman sambatu takeyi kamar zautacciya, wata tsamurarriyar mata ce fara siririya ta fara tsufa don gashin kanta harya fara hurhura, jikinta na sanye da atampa riga da zane, ta tsoge ɗaurin ɗankwalin nan ture kaga tsire, hannunta na ruƙe da aswaki sae faman kwalkwalar haƙoranta takeyi wadanda sukayi jawur saboda tsabar cin goro, kai kana ganin ta zaka shaida cewa ba ƙaramar jarababbiya bace, irin tsaffin nan da basa gajiya da mita,
   daƙer Amal tasamu wutar ta huru, sannan ta fito agalabaice, kai tsaye ta wuce inda uban kayan wankin suke dila guda,gaba ɗaya kayan sawarsu ne su duka dana uwar dana su abra da hayam, ga zannuwan gado da barguna duk sun tara mata su don ta wanke, abun babu imani acikin shi, babu irin wahalar rayuwar da yarinyar bata shaba,uƙuba iri iri suke yi mata, ko bacci bata samu, in ma tayi baccin da duka suke tashinta, ko kuma taji saukar ruwa bokiti guda ajikinta, fatar jikinta duk cizon sauro ne gashinan ruɗu ruɗu, saboda awaje take kwana, su kuma su shige ɗaki sai ita kaɗai ga tsora da Allah yayi mata, kullum cikin zullumin mai zai faru da ita take yi, duk yarda taso su haɗu da yayarta abun yaci tura, a halin da ake ciki ita kanta Amani batasan cewa yarinyar na raye ba, tun wani zuwa da tayi suka sanar da ita cewa yarinyar ta 6ace an neme ta an rasa, hankalinta ba ƙaramin tashi yayi ba, a lokacin tasha kuka sosai wurin neman yarinyar amma babu ita babu alamarta, tun tana sanyawa a nemo mata ita har tagaji ta daina saboda kullum babu labarin anga yarinyar shiyasa ta fidda rai da ita, ashe lokacin 6oye yarinyar sukayi a gidan makwabtansu acikin wani ɗaki aka rufe ta kamar akuya, duk in amani zataso maiduguri sai su kaita can gidan ajiya har tazo ta tafi bazata sani ba, hakan yasa basu ta6a haɗuwa da ita ba tun auranta da Abbas na wata takwas a lokacin abun ya faru, taso ta ɗauki yarinyar ta zauna a wurinta amma saboda baƙin hali irin nasu sun hanata ganin ƴar uwarta....😭
    "Maza ki hanzarta ki wanke mana kayan," muryar mammynce ta katse ta,
    Hannu tasa ta ɗauki

Chapters

Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login