Showing 213001 words to 216000 words out of 432432 words

Chapter 72 - Abban Sojoji Book 2 Hausa Novel Complete

yanayin yadda take magana,ganin yadda hijabin jikinta ya jiƙe sharkaf da zufa,kuma babu zafi aɗakin nasu,ga idanuwanta sunyi jawur dasu luhu luhu,jikinta kuma sai kerma yakeyi,
  Cikin sanyin murya yace"Abu pls ki saurare ni,zan fahimtar dake..kinsan ina sonki bazanso abunda zai cutar dake ba,bazan iya cin amanarki ba abu,
  damƙar hijabin jikinta tayi tare da cireta tayi wurgi da ita gefe guda,a fusace ta Sanya rezar nan abakin tafin hannunta na dama,ta tsarga wurin nan take jini ya soma tsastsafowa daga wurin
  Agigice abusufyan ya yunƙura zai kwace rezar hannunta,dakatar dashi tayi da cewa"Idan har ka kuskura ka matso zan kashe kaina ne!"
  Cikin shessheƙar kuka Abusufyan yashiga yi mata magiya yana roƙonta akan ta daina tsaga jikinta amma kamar yana tunzurata ne,
  Saboda taurin kai da kafiya irin nata ko zafin rezar bata ji ajikinta,kafin yayi wani yunƙurin abu ta sanya rezar asaman wuyanta ta shiga tsarga wurin jini ya shiga bulbulowa,
  A wannan lokacin ne abusufyan ya furta mata saki har ukku batare da saninshi ba,saboda tsoran karta kashe kanta,a gigice yace"ABU NA SAKE KI!NA SAKE KI!NA SAKE KI," 😭

Adai dai lokacin Hajiya da haris suka faɗo dakin kamar an jefo su,sakamakon Sautin ƙarar da abu ta saki da kuma kukan da abusufyan ya saki na fitar hayyaci,zubewa tayi saman gadon asume tana billayi saboda radaɗin rezar daya shigeta,

Gaba daya suka rufar mata suna ambaton Sunanta suna tambayar meya faru,a lokacin shima abusufyan ya yanke jiki asaman gadon ya sume,

Bayan wannan lokacin sai da abu tayi jinya agadon asibiti,inda Allah yaso rezar bata shiga cikin wuyan sosai ba amma ta tsaga fatar wurin sosai,

Bayan an sallameta sun dawo gida anan fa suka hadu su duka a falon gidan don jin abunda ya haddasa faɗan daya shiga tsakaninsu,Zainab bata 6oye komai ba ta basu labari hada sakin da abusufyan yayi mata,hankali atashe Abusufyan ya shiga rantsuwar cewar shi bai sake ta ba,saboda baya acikin hayyacinshi baisan ya furta mata ba,gaba dayansu babu wanda baiyi takaicin faruwan wannan al'amarin ba,musamman mahaifinta baba buzu,tun daga ranar da aka sallameta daga asibiti ko kallonta bai ƙara yi ba,in ma tagaishe dashi bai amsawa,ta 6ata mashi rai sosai,bai ta6a tunanin abu zata aikata abunda ta aikata ba saboda kishi daya rufe mata idanunta,

Abusufyan kuwa har ciwon zuciya sai da ya kusa kama shi a wannan lokacin,ba arziƙi hajiya Ameena tasa aka fitar dashi ƙasar turkey,wurin wata aminiyarta kuma abokiyar kasuwancinta,hajiya maimunatu dake zaune acan instanbul,a wurinta yaci gaba da zama,ta nisanta shi da nigeria ne saboda ta gusar da damuwar dake ƙoƙarin haddasa mashi Ciwon zuciya,

Bayan abusufyan ya koma ƙasar turkey da sati guda kacal,sai ga sayyadi yazo yi ma Abu jajen mutuwar aurenta,tun abakin gate ɗin gidan baba buzu yayi mashi korar kare,wannan abun ba ƙaramin ƙona mashi rai yayi ba,

Ana haka kuma abu ta koma yar gidan jiya,soyayyar sayyadi ta dawo sabuwa fal acikin ranta,ko bacci bata iyayi batare da tayi mafarkinshi ba,ko sallah takeyi sai ta dinga kawo zancenshi acikin zuciyarta,Tashin hankali,zuciyarta ta dinga azalzalarta akan son ta sanyashi acikin idanunta gashi an hanata fita ko nan da bakin gate bata iya zuwa saboda mahaifinta dake fushi da ita,da zarar ya ganta awaje zai nufeta afusace da nufin ya bugeta sai ta watsa da gudu ta koma ciki,hajiya da alhaji nuraddeen har haƙuri suka bashi akan komai ya wuce amma yaƙiyi,burinshi ya damƙeta a hannunshi yayi mata mugun bugu,don ya huce haushinta da yake ji,Abu ta ƙumsa mashi baƙin ciki sosai,

Ana haka,wata rana ƙawar abu ta islamiyyarsu wadda suke kira da Maryam ta kawo mata ziyara acikin gidansu,
A falo suka fara gaisawa dasu mommy kafin suka shiga cikin ɗakin abu,anan take sanar da ita cewa Sayyadine ya aiko ta a 6oye don ta kawo mata wayar da zasu dinga gaisawa dashi,'hakan ba ƙaramin daɗi yayi ma abu ba,
Nokia ce ƙarama maryam ta ciro daga cikin handbag dinta ta miƙa ma Abu,cike da farin ciki ta kar6i wayar,
  Tafiyar maryam ke da wuya,sai ga kiran sayyadi ya shigo cikin wayar,jiki na rawa ta ɗaga kiran tare da yi mashi sallama,
  ko amsa sallamar baiyi ba yace"Hmmmm abu kenan!yanzu kin tabbatar da abunda nake faɗa maki akan Abusufyan ko?ae tun farko saida naja kunnanki akan ki rabu dashi ba mutumin kirki bane amma kika ƙi jin maganata,'
Abu tace"dan Allah mubar wannan maganar,ni ko sunanshi ma bana son ji,yanzu kaine araina,banda burin daya wuce muyi aure yanzu,dan Allah sayyadina ka turo gidanmu asanya ranar auranmu,'
  Dariya sayyadi yayi kafin yace"kin manta da cewa idda kikeyi yanzu,"
Cike da damuwa abu tace"Nasani,amma ni bansan ya zanyi ba,so nake kawai mu kasance atare amatsayin ma'aurata,"
  Shu'umin murmushi sayyadi ya saki aranshi yace"yarinya kinzo hannu,"
  A fili kuma yace"yanzu ya za muyi abu?nikaina aƙagare nake da naga wannan lokacin,na ƙosa naganki amatsayin matata uwar ƴa'ƴana kuma,"
  Suna cikin wayar yunƙurin amai yazo mata,da gudu ta miƙe tare da faɗawa cikin toilet wayar na ahannunta,ta karasa gaban fanfo tana kwarara aman,
  Hankalin sayyadi ba ƙaramin tashi yayi ba,jin abu na amai,wannan ya tabbatar mashi da cewa Akwai Cikin abusufyan ajikinta,kuma muddin ya bayyana kowa ya sani babu shi babu abu,kafin ya cimma burinshi za'a ɗauki tsawon lokaci ne,
  Kunna fanfon tayi,ruwa ya zubo ta ɗebo tana kuskure bakinta da ɗayan hannun,
  Bayan ta kammala aman tadawo ɗakin a gefen gadon ta zauna sannan ta mayar da wayar a kunnanta tace"kayi hakuri sayyadina,wlh bana jin daɗin jikina ne,"
  Muryarshi har kerma takeyi wurin cewa"Faɗamun Abu!kamarya kike ji ajikin ki"?
  Abu tace"zuciyata ce ke tashi,ga wata irin kasala da nake ji.....'
  Tun kafin ta ƙarasa maganar sayyadi ya katse ta da cewa"Abu!banason ki fada ma kowa yanayin da kike ji ajikin ki!kinji ko"?
  Amsa mashi tayi da toh bazan faɗa ba,
  Yaci gaba da cewa"Ni zanyi maki maganin lalurarki,addu'a kike buƙata,insha Allah yanzu bada jimawa ba,zaki ji sauƙi ajikinki,"
  'Nagode sosai,"ta fadi kafin ta kashe wayar ta koma ta kwanta,

Kafin wani lokaci abu ta daina jin tashin zuciyar da take ji,kasalar nan duk babu ita komai ya dawo mata dai dai,har abu ta kammala iddarta babu ciki ajikinta,kuma aranar data kammala iddar aranar sayyadi yazo neman auranta wurin baba buzu,tun abakin gate baba buzu yace"meya kawoka gidan nan!"
Sayyadi yace"Naji cewa abu ta kammala iddarta,shine nazo neman auranta a wurinka,dan Allah kada ka hanani,tunda dae yarinyar nan ta nuna tana sona,kabarni kawai muyi auranmu,nayi maka alƙawarin zan kula maka da ƴarka,'
  Wani irin kallo baba buzu yayi mashi kafin yace"har abada bazaka ta6a auran abuba,indai har nine ubanta,muddin ina numfashi bazan ta6a aura maka ita ba,"
  Shu'umin murmushi sayyadi ya saki tare da jinjina kanshi yace"Idan kuma baka araye fa?ka isa ka hanani auranta?
  Shiru baba buzu yayi yana kallonshi,dariya sayyadi yayi yana girgiza kai yace"shiyasa tun farko naso ace ka bini ta lalama ka auramun ita,amma saboda taurin kai da kafiya irin taka,yasa ka hanani auran abu,har marin abu kayi saboda ta sanya hannu ta mari abusufyan,sannan kayimun korar wulaƙanci saboda nazo wurin ƴarka,dama tara ka nake yi,yau zaka mutu baba buzu,kuma a sati mai zuwa zan auri abu,'_
  Gabanshi ne yayi mugun bugu jin abunda sayyadi yace,nan take jikinshi ya shiga kerma yana rawa,wata irin zufa ce ta shiga gangarowa daga cikin ƙofofin hudar gashin jikinshi,
  Muryarshi na kerma yace"Wanene kai!ka faɗamun!meyasa kake son abu,saboda me ka shiga rayuwarta!"
  murmushi sayyadi ya saki tare da takawa ya matsa dab da Baba buzu suna fuskantar juna yace"Ni ba rayuwar zainab na shiga ba!rayuwar abusufyan nashiga,bansan zainab ba,abusufyan nasani!shisshiginka da bin ƙwaƙƙwafinka yau sun ja maka zaka rasa ranka baba buzu!kana tunanin cewa bansan bibiyata da kakeyi ba?don kawai kasan wanene ni!da wata manufa nake son ƴarka!shiyasa ba'ason mutun ya tsananta bincike wala tajassasu,da alama bakasan da hadisin ba,koda yake kaifa babu ilmin addini akanka.......'
   Tunda sayyadi ya soma magana,baba buzu ya dinga jin tsigar jikinshi na tashi,tamkar ana tsige gashin jikinshi,nan take ya zube saman guiwarshi,idanunshi sukayi jawur muryarshi na rawa yace"Kada ka kashe ni,ka barni da raina!inason nasake ganin abu a idanuna,"
  Fashewa da dariya sayyadi yayi tare da cewa"zaka iya ganin abu amma a lokacin da dukkan wasu kalaman bakinka suka daina aiki,ko uffan ba zaka iya furta mata ba,sae dai ka bita da ido kafin azare ranka,sannan kuma inaso nayi maka wani albishir baba buzu,Abu tana ɗauke da cikin Abusufyan,amma na 6oye hakan,zata haife shi ne acikin gidana kuma amatsayin ɗana.....'cike da shaƙiyanci sayyadi ke maganar,
  Jin cewa abu nada ciki yasa baba buzu jin hawaye na sauka a idanunshi,dama yaji ma yana mamakin yadda akai babu ciki ajikin abu,ashe sayyadine ya kwantar da cikin don karsu gani su hanashi auranta,"
  "Kaji tsoran Allah!kada ka cutar mun da ƴata!don Allah ka fita daga rayuwarta,wai lafin me mukayi maka ne?menene haɗinka da rayuwarmu,Ni da abu bamu ta6a cutar da kowa ba,mun taso mu biyu muke rayuwa bamu da kowa,Na roƙe ka akan ka ƙyale mun ƴa ta,koda zaka kashe ni amma kada ka ta6a abu,'
  Bakomai zai baka mamaki ba face yadda ɗai-ɗaikun mutane ke giftawa a wurin amma babu wanda hankalinshi ke kaiwa wurinsu,hatta haris sai da yazo ya wuce ta gate ɗin gidan amma bai kai idonshi wurinsu ba,kuma wannan duk aikin sayyadine,
   Juyawa sayyadi yayi ya nufi rugwagwar mashin ɗinshi dake ajiye inda yayi parking dinshi hawa yayi sannan yana kallon baba buzu yace"Zanyi amfani da abu ne don in ƙuntata rayuwar abusufyan,zan kuma yi amfani da yaron da abu zata haifa don in tarwatsa farin cikin zuri'arsu kamar yadda suka tarwatsa farin cikin namu family ɗin,nabarka lafiya,"yana ƙarasa maganar tashi ya tashi mashin ɗin da gudu yabar anguwar,
  Barin unguwar tashi ke da wuya baba buzu ya yanke jiki ya faɗi,yana mirgina mirgina a ƙasa,kumfa na fitowa daga bakinshi,sai lokacin mutane suka dawo hayyacinsu suka lura da baba buzu dake kwance yana ta harba ƙafafunshi,
  Lokaci guda mutane suka taru a kopar gidan sukayi dandazo suna kallonshi wasu na tambayar lafiya,wasu kuma nayi mashi addu'a,kafin su yanke shawarar kiran wani acikin gidan,
   Koda aka sanarma su hajiya ameena abunda ke faruwa jiki na rawa suka kwaso gaba dayansu suka zo wajen gate din gidan,
  Lokacin da abu tayi arba da mahaifinta dake kwance ƙasa yana ta birgima,zukunnawa tayi agabanshi tana jijjiga jikinshi tana faɗin'baba baba...meya faru dakai!baba dan Allah ka tashi....wayyo Allah na,nashiga uku......'haka ta dinga sambatu tana jijjiga,bawan Allah sai ƙoƙarin buɗe baki yake yi don ya sanar mata da cewa sayyadi ba mutumin kirki bane,kuma tana ɗauke da cikin abusufyan amma hakan ya faskara,anan dae rai yayi halinshi,baba buzu ya riga mu gidan gaskiya.........'
  A ranar abu kamar ta zauce saboda tsabar tashin hankalin rashin mahaifinta da tayi,haka hajiya Ameena da alhaji babu wanda baiji mutuwarshi ba,sun jima suna tunanin menene yayi silar mutuwarshi amma basu gano hakan ba,kowa ranshi na bashi cewa kamar guba ce saboda wannan kumfar da bakinshi ke fitar wa,
One week da rasuwarshi ko zaman makoki ba'a kammala ba,abu ta bijiro da maganar auran sayyadi,babu wanda baiji haushinta ba,don hajiya kamar ta rufe ta da bugu,a ƙarshe dae Alhaji nuraddeen ne ya goya mata baya,dama shi ya yarda da sayyadi kallon mutumin kirki yake yi mashi,
Batare da 6ata lokaci ba,aka ɗaura auren abu da sayyad'
   Kunji yadda akai Abu ta shiga gidan sayyad da cikin abusufyan,aurensu ko One month bai cika ba sai ga ciki ya bayyana ajikinta kuma cikin ba ƙarami ba,yayi watanni,nan fa mutane suka soma tsegumi akan cikin nata,abun ya ɗaure masu kai,aure ko wata baiyi ba ciki ya bayyana,dama ƙarami ne cikin da sauƙi,amma wannan cikin da girmanshi fa,ya haura 4 months,

Tun zuwan da tayi gida,wurin Hajiya ameenatu don ta gaishe da ita,kallo daya hajiya tayi ma cikin nata,ranta ya bata cewa cikin abusufyan ne!duk da lokacin da suka rabu da abusufyan babu ciki ajikinta babu alamarshi,

"Abu wannan cikin na jikin ki,kamar na abusufyan ne!raina yana bani haka,dama mutane na kawomin tsegumin cewa cikin jikinki yayi saurin girma daga yin aure ko wata baiyi ba sai  ya bayyana kuma da girma har haka"?
  Tur6une fuska abu tayi tare da cewa"Mommy dan Allah kidaina maganar nan,taya za'ace cikin abusufyan ne?idan cikinshi ne meyasa bai bayyana ba tun lokacin da muna tare dashi,sai bayan watanni kuma har nayi aure sannan zai fito"?
  Hajiya ameena tace"abu kenan,kika san ikon Allah?koda yake ba zanyi maki gardama ba,amma ni raina na bani cewa cikinshi ne,Amma zamu zuba ido muga lokacin da zaki haife shi,in har cikin nan yayi wata tara toh na sayyadine,amma in har kika haifeshi nan da 5 months,to na Abusufyan ne,'
  Muryarta tamkar zatayi kuka tace"Mommy nifa ba cikin abusufyan bane!na sayyadine,dan Allah mudaina maganar nan,'
  Hajiya tace"naji zan bar maganar amma ina nan ina zuba ido,kuma in aka haifi yaron zamu je ayi mashi gwajin jini don a tabbatar da yaron wanene shi............'
  Bayan abu ta koma gida cike da damuwar abunda mommy ta sanar mata,sayyadi na dawowa ta kwashe duk abunda suka tattauna ita da hajiyarsu ta sanar mashi,
  Aikuwa tun daga ranar bakin mutane ya mutu murus,babu wanda ya ƙara tanka mata game da cikin dake a jikinta,abun ya ɗaure mata kai,sa6anin da da mutane ke tsegumin ta amma yanzu ko maganar cikin babu maiyi,
  Kuma tun daga ranar Hajiya Ameena,ta fara samun ta6in hankali,na yawan mantuwa,yawan sambatu ita kaɗae da dai sauransu,a ƙarshe ma taji ta tsani zama a kano gaba ɗaya tamkar korarta ake,haka ta tattara ta koma katsina da zama,dama suna da katafaren gidansu acan wanda suka bari amma duk in suka zo garin a gidan suke zama,ita kaɗae ta koma gidan tana rayuwa acikinshi,tare da mai aikinta,kafin daga baya haris ya dawo wurinta,mahaifinsu kuma yana zuwa akai akai don ya dubasu,

After 5 months

A tsakar dare naƙuda ta taso ma abu,gashi ita kaɗae ce a gidan babu kowa,sayyadi bai dawo ba,dama wani lokacin in ya fita sai tsakar dare yake dawowa kamar aljani,

Tun daga saman gadon ta faɗo ƙasa tana faman dafe cikinta tana cizon la66anta tana kuma ambaton sunan Allah abakinta,sosai cikin ya shiga murɗa mata tare da matsanancin ciwo.


Daga ƙarshe ta zube anan wurin,bata tashi farkawa ba sai asaman gadon asibiti,kukan jariran da ta haifa ne suka tashe ta daga dogon baccin daya ɗauketa sakamakon allurar baccin da Dr yayi mata,a hankali ta buɗe idanunta ta ware su akan fuskar sayyadi dake tsaye hannunshi ɗauke da jariri naɗe acikin towel,murmushi ya sakar mata tare da cewa"Barka da sauka my wife,ina tayaki murna kin haifa mana kyawawan ƴa'ƴa," yunkurawa abu tayi ta miƙe daga zaune tana kallon yaran dake jere a gefenta guda biyu nade cikin towel ga kuma ɗaya a hannun sayyadi,wani irin farin ciki ne ya lullu6eta,saboda tsabar murna bakinta yaƙi rufuwa,muryarta na kerma tace"Wannan duk nawa ne?ƴa'ƴana ne ni kaɗai"?
sayyadi yace"namu dae,naji kina cewa duk ƴa'ƴanki ne,bayan duk ƙoƙarin nawa ne,nakudarsu ne kawai kikayi,"cikin zolaya yayi mata maganar,
Hannu tasa tare da daukar ɗaya daga cikin jariran ta buɗe fuskarta tana kallonta,gabanta ne taji ya faɗi rasss! ganin jaririyar na kama da Abusufyan,maimakon taga kamanninta kona sayyadi a fuskar yarinyar sai taga fuskar abusufyan,
bin fuskarta da kallo sayyadi yayi ganin kamar tana cikin damuwa yace"meya faru ne?yanzu fa naga kina farin cikin samun ƴan uku,lokaci guda kuma naga kin canza?
"Babu komai,"ta bashi amsa muryarta a kasalance,

Haihuwar tazo mata cikin sauƙi,a ranar aka sallame ta,suka koma gida,bakomai yafi damun abu ba face yadda mutane suka ƙi zuwa yi mata barkan samun ƴan uku,ko leƙo gidanta babu wanda yayi,tayi tsammanin danginshi zasu zo amma abun mamaki babu wanda ya leƙo da sunan ɗan uwanshi yazo duba yaranta,jikinta yayi mugun sanyi,duk taji ta tsani kanta,amma daga ta kalli ƴan ukunta sai taji farin ciki aranta,suka dae ne dangin da take dasu aduniyar nan,su take gani taji daɗi aranta,lokacin da yaran suka kai wata ɗaya aduniya,aranar wata ƴar uwarshi tazo kawo mata ziyara,ita ta taimaka wurin yi mata wankan jego,da kuma yi ma yaran wanka,duk yadda abu taso taja ta da fira don taji a ina suke da zama suna da dangi,amma matar nan da shegen wayau ko uffan bata ce mata ba,a haka har suka kammala wankan jegon matar ta koma garinsu,

Abu ba ƙaramar wahala tasha ba,wurin rainon ƴan ukunta,babu mai taimakonta,itace yi masu wanka har sau biyu arana safe da kuma dare in zata kwantar dasu,wankin kayansu da suka 6ata,ɗawainiyarsu da kuma ɗawainiyar kanta,abun duk ya jagule mata,ga sayyadi ko tsinke bai ta6a sanya hannu ya kawar mata ba,bayan kafin suyi aure shi da kanshi yake sanar da ita cewa in sukayi aure duk ranar da yake hutu bai aiki har girki sai yayi mata ashe duk ƙaryace yake yi mata,Abusufyan kuwa muddin yana agida bai barinta tayi aiki,sai dai yayi shi kaɗae ko kuma suyi atare,da kanshi yake cewa"Abuna idan har kika haifa mana ƴa'ƴa ni da kaina zan dinga yi masu wanka,idan mata ne zan dinga sharce masu gashin kansu ina gyara masu shi,bazan bari kisha wahala ba,'in ta tuna waɗannan kalaman nashi sai ta fashe da kuka,dama ita dana sani bata da daɗi,Allah ka rabamu da aikin dana sani,Amin

Kunji yadda akai Abusufyan ya auri abu,da kuma yadda akai yabar nigeria da kuma yadda akai ta haifi ƴa'ƴanshi agidan wani wanda ya taso amatsayin ubansu,

💋Boss Bature💋

Lokacin da Abusufyan yakai ƙarshen labarin nashi sai ya fashe da matsanancin kuka kamar ƙaramin yaro,cikin sauri Abba ya janyoshi jikinshi yana lallashin shi,bashi kaɗae ba hatta su fawan,jabeer,irfan,khaleed dasu twins sai da idanunsu suka cicciko da kwalla,Sgr da Omar kuwa jinjina kai kawai sukeyi,Abbas ne yace"Yanzu ina ƴa'ƴan suke?suna raye ko sun mutu ne"?
"Nima abunda nakeso na tambaya kenan,"acewar hajiya azeema da jikinta ya gama mutuwa,kowa mamakinshi ta yadda akai waɗannan abubuwan suka faru batare da Abusufyan da kuma goggon katsina sun sanar ma kowa ba,
cikin sanyin murya Abba yace"ka faɗa mana ina ƴa'ƴan suke yanzu"?
ɗagowa abusufyan yayi da idanunshi waɗanda sukayi jawur yace"ni kaina bazan iya cewa ga inda suke ba,a lokacin can baya ina bibiyar rayuwarsu,ta hanyar haris shiya kira ni a waya yake sanar dani cewa abu ta haifi ƴa'ƴa kuma yaran dani suke kama sosai,tun daga lokacin na sanya shi akan ya dinga bibiyar rayuwar yaran yana sanar dani duk wani abu dake faruwa arayuwarsu,shine yake turo mun da hotunansu ina ganinsu

Chapters

Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login