Showing 144001 words to 147000 words out of 432432 words

Chapter 49 - Abban Sojoji Book 2 Hausa Novel Complete

ya tsagaita da dariyar yace"Omar ka iya zolaya Allah kamar mahaifiyarku,yanzu rafayet kakeso nayima auren dole?so kake ya tashi bomb acikin gidan nan"?
  "Abba baka fahimce ni ba,tunda muka taso tare da ɗan uwana,komai namu iri ɗaya muke yinshi tamkar twins haka muke,duk abunda nayi rafayet sai yayi shi,haka shima duk abunda yayi nima saina yi shi,yanzu abba aure ne zai banbanta ni da ɗan uwana"?
  In serious matter Omar ke magana,wannan yasa Abban nasu ya gane cewa ba zolaya bace yake mashi,har cikin ranshi yake maganar kuma ba ƙaramin jin abun yake ba acikin zuciyarshi,bai gama zancen zucin nashi ba omar yaci gaba da cewa"Abba tuntuni ban ta6a sanar dakai ba,amma yau zan sanar dakai komai,najima inason na cika maka burinka na ganin cewa munyi aure, ba don komai ba sai don saboda farin cikinka,bakomai ne yasa nayi jinkirin yin aure ba face Rafayet!inason aure bawai banaso ba,rafayet shine dalilin dayasa naƙi yin aure,saboda ina ganin cewa kamar banyi mashi adalci ba,inna riga shi yin aure,saboda mun saba komai atare duk wani cigaban da zamu samu atare muke samun shi abba,taya zanso na samu wannan babban cigaban batare da ɗan uwana ba"? Ya ƙarasa maganar muryarshi asanyaye yana kallon Abban nasu,
Gaba ɗaya Omar ya gama kashe ma Abban nasu jiki,ba ƙaramin tausaya mashi yayi ba,lalle ba ƙaramar shaƙuwa bace a tsakanin shi da ɗan uwanshi ba,tun da har zai iya hana kanshi wani jin daɗi na rayuwarshi saboda ganin cewa tamkar baiyi mashi adalci bane,
   "Abba,na jima ina jiran ganin cewa ɗan uwana ya fara soyayya koya fara maganar aure,amma har yanzu ba wani sauyi abun ba ƙaramin ta6amin zuciyata yake ba,bana faɗi ne kawai saboda nasan faɗin bashi da amfani zan 6ata bakina ne kawae,sau da yawa ina janshi da fira akan mace don na bugi cikinshi naji koya fara ra'ayin yin aure amma kullum babu wani cigaba game da haka,Abba rafayet shine yasa Omar ɗinka ƙin yin soyayya tun da jimawa kuma shine ya hana nayi aure,wanda bani da burin daya wuce wannan arayuwata....,.......'
  Kasa ƙarasa maganar yayi saboda siririn hawayen daya zubo mashi a idonshi na hannun dama,
  Cikin sauri abban nasu ya sanya hannunshi tare da yin saurin goge masu shi yace"Omar ban ta6a tunanin haka ba,meyasa tuntuni baka sanar dani wannan maganar ba?meyasa nagaza fahimtarku amatsayina na mahaifinku?ashe shaƙuwar dake tsakaninku har takai haka?nagode ma Allah sosai da kuka kasance masu son junanku,ina matuƙar alfahari daku ƴa'ƴana," magana yakeyi yayin da idanunshi suke cike tab da kwalla,
  Sehrish kuwa dake la6e bayan labule sai faman shessheƙar kuka takeyi ta rufe bakinta da tafukan dukkan hannuwanta,tsananin tausayinsu ne ya kamata,tunda take a rayuwarta bata ta6a ganin ƴan uwa masu matuƙar ƙaunar junansu ba irin ahalin salahuddeen hussein,akwai soyayya da shaƙuwa tsakaninsu,zumuncin dake tsakaninsu mai ƙarfi ne sosai,da ace kowane ahali zasu kasance haka da ba ƙaramin cigaba za'asamu ba,amma yanzu zamanin da muke ciki,babu wannan soyayyar atsakanin shaƙiƙai ma,sai kaga na waje ma wani can yafika kusanci da ɗan uwanka shaƙiƙinka,idan kuwa akazo kan shiga matsala ko damuwa tofa zaka ga mutum indai bashi ta shafa ba,babu ruwanshi da damuwa akan halin da ɗan uwanshi yake ciki,sai ma ya kasance ɗan uwanka yana cikin ƙunci da matsanancin damuwa,amma kai kuma hankalinka kwance sai ma ajika kana ta faman tiƙar dariya,mai makon arunƙa jajantawa juna,shiyasa dayawa zaka ga na waje ma wani yafika kusanci dashi saboda yafi damuwa da ɗan uwan naka,wanda dayawa hakan ke jefa rayuwar ɗan uwan cikin hatsari,ba'a janshi ajiki cikin gida tun daga iyayen har ƴan uwan,bakamar salahuddeen hussein ba, ya ɗauki ƴa'ƴanshi tamkar abokanan shi,ƙaramin ɗanshi ma tamkar amininshi ya mayar dashi,kuma hakan yasa basa jin shakkar sanar da mahaifinsu abu in ya same su,ko neman shawara awurinshi,wanda a yanzu zaka ga cewa wani a gidansu tsoro ma yake ji ya sanar cewa wani na cutar dashi awaje,saboda wasu iyaye basa tsayawa su fahimci ƴa'ƴansu daga sun ji abu sai afara hantarar mutum in ƙarami ne kaga an haɗa mashi da bugu ma,babu wannan shaƙuwar ta iyaye,da ƴan uwantaka da har mutum zai iya faɗin damuwarshi acikin gidansu,sai dae ya nemi abokinshi ya sanar dashi halin da yake ciki instead of wani nashi nakusa dashi,daga nan kuma awajen in Allah yasa abokin ba nagari bane shine zaka ga anzo ana danasani, don mafi akasarin mutane na fadawa mugun hali ne ta sanadiyyar abokai,ku yi koyi da wannan ahalin wurin nuna ma junanku soyayya,ku zama naku ku kaɗai babu mai jin kanku👌👍

Sehrish bata bar bedroom ɗin sgr ba,har sai da aka kira sallar magrib suka fita tare da abbansu domin zuwa yin sallar magrib sannan ta samu cikin sauri ta ɗage curtains ɗin,da hanzarin gaske ta sungumi mayafinta sannan da sauri hadda gudu ta haɗa wurin barin part ɗinsa,
Saukowa downstairs tayi a lokacin duk sun tafi salla masallaci,kai tsaye kitchen ta nufa tunkan ta ƙarasa ta hangi Azmee da hayaam suna ta haramar kammala dinner ɗin ranar,duk sai taji babu daɗi taso ace tare da ita suka fara,jiki asanyaye ta shiga kitchen ɗin da sallama a bakinta,
Juyowa sukayi suna kallonta atare,da alama ma sun kammala aikin nasu,Azmee ce ke haɗawa Hayaam warmers acikin tray tana kaiwa dining,
"Kin kammala gyara mashi part ɗin nasa ne?azmee ce ta jefa mata tambaya,
"Eh,nagama,"
"Ya akai kika daɗe acan ne"?
Sunnar da kai tayi tana wasa da yatsun hannunta saboda ta rasa amsar da zata bata,
Hayaam kuwa sai faman wurga mata harara take yi kamar kwayar idonta zata faɗo ƙasa,
Murmushi azmee tayi tare da cewa"ki wuce kije kiyi sallah,kada ki samu damuwa,nasan cewa wani abunne ya tsayar dake,"
Ajiyar zuciya sehrish ta sauke kafin ta juya tasa kai tabar cikin kitchen ɗin,bedroom ɗinta ta nufa domin tayi sallah,

A 6angaren su hossana kuwa,tun bayan da suka dawo daga school suke ta faman saran zuwan Omar amma baizo ba,burin jahad ta sanar dashi cewa taga ƙaninshi a school ɗinsu,gaba ɗaya yinin ranar sunyi shi ne cike da kewar Ya omar ɗinsu musamman hossana ko lunch bata ci ba tunda suka dawo gashi ko'a school ma bataci komai ba,saboda tayi alƙawarin cewa tare da ya omar zasu ci abinci zai bata abaki,hakan yasa taƙi cin komai,duk yarda jahad taso ta fahimtar da hossana akan ta zauna taci abinci sam taƙi,har dai tagaji ta ƙyaleta,
sai faman zagaye takeyi acikin bedroom ɗinsu,fuskar nan ɗauke da murmushi ae tunda tayi arba da Romeo sam tagaza samun natsuwa wani irin tsantsar son shi da ƙaunarshi takeji kamar kamar me,fiye da yarda take jin ya omar ma lokacin da taso shi,saboda shi son da tayi mashi hada ƙarin don ta kyautata mashi ne akan irin ɗawainiyar da yake yi dasu,shi kuma kalar son da take yi ma junaid kallo ɗaya tayi ma kyakkyawar fuskarshi tabi ta rikice,kuma tunda Omar ya furta cewa ƙaninshi ne nan take taji ya kwanta mata aranta,sai dai abunda jahad bata sani ba shine,junaid ba babba bane kamar yarda take tunani,

**********haroon
Gaba ɗaya ya rikita ɗakin nashi wurin neman kuɗin da su Twins suka bashi,sam hankalin shi ya gaza kwanciya yama rasa inda zaisa kanshi,wata irin zufa ce ke gangaro mashi a fuskarshi saboda tsabar 6acin rai,yafi ƙarfin awa 2 yana neman jakar kuɗin amma babu ita ƙasa ko sama,an ɗauke ta daga ɗakinshi babu ita babu alamarta,yayi ma bedroom ɗin nashi kaca kaca wurin binciken inda jakar kuɗin take,kamar zaiyi hauka saboda yarda ya zauce,sun rigada sun gama tsara plan ɗinsu,
shirin tafiya kawai ya rage mashi daga zuwa ya ɗauki jakar kuɗin an ɗauketa daga ɗakinshi,gashi ya rasa wanda ya shigo har cikin bedroom ɗinshi ya ɗaukar mashi ita,komawa yayi gefen gadonshi ya zauna yana faman huci kamar wani zaki,tunani ya shiga yi wanene zai iya shigowa ɗakinshi ya ɗaukar mashi jakar kuɗin shi?kodai su twins ne suka yi mashi wayau,don sunsan cewa ya goge videon shine suka ɗauke jakar kuɗin,tabbas kuwa sune saboda su kaɗai ne suka san da kuɗin acikin bedroom ɗinshi,
Jinjina kanshi yayi yana huci yace"yara kenan harni zakuyiwa wayau,ƙananun ƴan iska kawai masu kwana da wando,saboda sun mayar dani shashasha shine suka zagayo ta bayan idona suka ɗauki jakar kuɗin,wlh sai kunyi danasani saina illata rayuwarku gaba ɗaya muddin baku maido mun da kuɗina ba,"ya faɗi a lokacin da ya miƙe tsaye zumbur yana faman naushin tafin hannunshi na dama da hannunshi na hagu,tashin hankali da ba'a sama shi date,

**********************Amani
Zaune take saman 3 seater,yayin da Amal ke zaune kusa da ita,ta fito fess abunta tayi wanka ta bata kaya ta canza duk da rigar tayi mata yawa saboda kayanta ne taba ma amal ɗin ta sanya kafin zuwa gobe zata je da ita shopping mall ta zabi abunda take so,ta kuma yi mata siyayyar kayan sawa da sauran abubuwa na rayuwa wanda zata buƙata,
Hannunta na ruƙe da wayarta,shiga contact ɗinta tayi tare da nemo numbar Aunty babba ta buga mata call,nan take wayar tashiga ringing,

Hafsat na faman zarya acikin parlourn nasu taji shigowar kira a wayar mommynta dake ajiye saman hannun kujera,cikin sauri takai hannu tare da ɗaukar wayar,ganin sunan Amani ya bayyana ne yasa ta juya tare da tunkarar kitchen ɗin,tunkan taƙarasa aunty babba tafito daga kitchen din jin ringing ɗin wayarta,miƙa mata wayarta tayi tare da cewa"Amani ce ke kira,"
Yatsina fuska tayi tare dasa hannu ta kar6i wayar bayan tayi picking ta kara wayar a kunnanta tana cewa"Sai yau kika tuna dani"?_
on the other hand Amani tace"Am really sorry auntyna takaina,kullum kina araina,kawai abubuwane sunyi mun yawa,"
tsoki aunty babba taja tare da cewa"Abubuwa su kayi maki yawa,ciki gare ki ko goyo"?_
Amani tace"ko ɗaya daga cikinsu babu,pls mubar zancen ae nabaki haƙuri,yanzu akwai maganar da nakeso nayi maki pls,"
Aunty babba tace"kunne ke ji,"
"dama maganar Amal ne!wai har yanzu ba labarinta?ba'asan inda take ba?nagaza samun kwanciyar hankaline saboda mafarkin da nayi jiya agame da ita,"
Shu'umin murmushi Aunty babba tasaki tare da cewa"Yawwa dama inaso nayi maki magana game da Zancen neman Amal,munyi waya da mammy ta sanar dani cewa an samu wasu malaman da zasuyi mata sauka,manyan malamai ne na addini kuma da zarar sunyi saukar nan ake cin sa'a buƙata ta biya,"
Ƙiriss ya rage Amani ta saki dariya,don tsabar takaici da ban haushi,aranta tace wai sai yaushe matar nan,zata daina ƙarya ne?
Juyawa tayi ta ɗan kalli Amal dake zaune hankalinta kwance idonta na kallon plasma tv ɗin dake facing dinsu,tana kallon tashar mbc 3,
gyara murya Amani tayi tare da cewa"Masha Allah,gaskiya ba ƙaramin daɗi naji ba auntyna takaina,ashe ansamu wasu malaman ae ni indai akan Amal ne ko nawa ne zan iya badawa,ko bani dasu zan nemo ne,'_
Jin haka yasa aunty babba,janye wayar daga kunnanta tana faman 6a66aka dariyar mugunta,duk hafsat na tsaye tana kallonta baki asake saboda tasan da zancen neman Amal ɗin,kuma a gabanta Jiya abra ta kira mommyn nata tana sanar da ita cewa Amal ta gudu,sarai tasan cewa yarinyar ta gudu shine kuma takeson ƙara cutar da Amani saboda tsabar son abun duniya?
"Yanzu nawa zan tura kenan"?acewar Amani,
Aunty babba tace"ba wasu kuɗine masu yawa ba,dubu ɗari takwas ne,ae ni nayi mamakin ma yarda suka faɗi kuɗin da sauƙi har haka,"
murmushin takaici amani ta saki kafin tace"okey,zanyi maki magana indae na samu kuɗin,yanzu dae mu koma zancen Hayaam,shin har yanzu tana maid ne ko tazo Abujan nan"?
"Tun jiya fa ta ƙaraso,yanzu ae ta jima da zama ƴar gida,"ta ƙarasa maganar tana washe baki,anzo inda tafi auki,
ɗan ta6e baki amani tayi tace"Okey yayi kyau,yanzu komai zai fara tafiya dai dai,akwai wani albishir da zanyi maki,"
Natsuwa Aunty babba tayi tare da cewa"ina sauraronki ƙanwata,faɗamun albishir ɗin,"
Shu'umin murmushi Amani tasaki tare da miƙewa daga saman sofa ɗin tabar Amal zaune tana kallo,takawa tayi nesa da falon,sannan tace"Nasan inna faɗa maki albishirin nan ko bacci ba zaki iya yi ba saboda tsabar farin ciki,"
A ƙagare Aunty babba tace"dan Allah shaƙamun mana kanwata wane irin albishir ne wannan,
Murmushi Amani ta kuma yi sannan tace"nasamo ma Hayaam maganin mallaka a wurin wani hamshaƙin boka,aikin shi tamkar yankan wuƙa yake,saboda Ni shaidace akan idona aka ta6a amfani da maganin kuma yaci,"
Cike da farin ciki Aunty babba tace"Wai dagaske"?
dariya amani tayi tare da cewa"dagaske mana!,wata neigbour ɗinace keson ƙanwarta ta auri ƙanin mijinta,sun rasa yarda zasu jawo hankalinshi acikin gidannan saboda mutunne mai matuƙar ji dakai,kamar dai sgr,ina baki labari kwatsam sai ga wata ƙawarmu ta bamu labari akan wani shu'umin boka,agabana aka shirya zuwa wurin bokan suka amso maganin,a yanzu dai labarin da nake baki,yarinyar na nan ta aure shi hada ciki ma sai faman shan soyayya suke abun gwanin burgewa,"_
Saboda tsabar Murna Aunty babba ta gaza rufe bakinta dakyar ta iya cewa"Yanzu ya za'ae kenan asama ma Hayaam maganin?nawa zamu nema"?
"Ko sisi basai kin bada ba Auntyna,fisabilillah na amso ma hayaam maganin da kuɗina ai nima kanwata ce ko,nidae burina shine inga ta auri sgr Abra kuma ta auri marshal Omar,"
washe baki Aunty babba tashiga yi tana cewa"Allah sarki Amani,ashe haka kika damu da ƙannen namu?gaskiya ba ƙaramin daɗi naji ba,yanzu kenan Hayaam zatazo ta kar6i maganin gidanki kenan"?
Amani tace"eh,in ma batasamu zuwa ba ni zanje nakai mata shi,babu damuwa,"_
Sun jima suna waya kafin daga bisani firar tasu ta ƙare anan,
Tuntsirewa da dariya Aunty babba tayi tana tafa hannu tashiga cewa"ban ta6a ganin ƴar wahala ba irin Amani,duk irin abunda nakeyi mata amma ita burinta ta taimakamun wurin ganin na cimma burina,gaskiya na tausaya mata,abun tausayi,
girgiza kai kawai hafsat tayi tare da wucewa ciki tabar mommyn nata tana ta faman sambatu,
A can 6angaren kuwa fashewa da dariya Amani tayi tare da cewa"Aunty laila kenan!ke atunaninki kinyi mun wayau bakisan cewa Amanin da kika sani ada ba ita bace ayanzu ba,ashirye nake dana kwance dukkan wasu notikan kanki,zan mayar dake kamar wata zararra,ita kuma hayaam zanyi amfani da wannan damar wurin ganin na canza mata halittar jikinta,kamar yarda kuka canzawa Amal kamanni ta tsotse ta rame ta ƙanjame haka itama nakeson ta koma,dama ance ramuwar gayya tafi ta gayyar zafi,that's my plan!

Tana faɗin hakan ta juya tare da komawa wurin Amal ta zauna,kallonta Amal tayi tare da cewa"Aunty amani,dan Allah kiyi haƙuri da abunda zan faɗa maki,bansan ko zai 6ata maki rai ba,nasan cewa su mammy sun cutar damu sosai,amma kada kice zaki ɗauki fansa,mubarsu da Allah kawai shi zai saka mana,sannan in zamu iya mu taimaki mahaifinmu don yana cikin mawuyacin hali"
Shuru kawai amani tayi batace mata komai ba,amma fa har yanzu tana akan bakanta,maganar mahaifinsu kuwa tasan matukar mammy na numfashi bazata barshi ya sarara ba,don ba karamar shedaniyar mata bace,ita kanta yanzu tana shakkun in don Allah aka hadata da Abbas.

_💋Boss Bature💋_

______________________tunda yadawo daga masallaci yake jin jikinshi wani irin yanayi mara daɗi,bedroom dinshi ya shiga tare da nufan saman gadonshi ya haye yana faman sauke ajiyar zuciya,pillow ya jawo tare da aza kanshi a saman shi yana faman lumshe ido,yana cikin wannan yanayin yaji fitar wani abu daga hancinshi mai ruwa ruwa,cikin sauri junaid ya tashi daga zaune yana kallon pillown nashi,zuba ido yayi yana kallon jinin daya ɗigo daga hancinsa,abun yayi matuƙar ɗaure mashi kai,kafin yayi wani yunƙuri sai ga wani ɗigon jinin ya sake fitowa daga ƙopan hancinshi,abu kamar wasa jinin ya dinga ɗiɗɗigowa saman bedsheet ɗinshi,
  Hankali tashe junaid ya sauko daga saman gadon da saurin gaske ya faɗa cikin toilet ɗinsa,kai tsaye ya nufi wash basin,dafa shi yayi yana kallon fuskarshi acikin mirror ɗin,hancin shi yabi da kallo ganin yarda hancinshi ke cigaba da bleeding,sam bai damu ba saboda yasan cewa yana yawan yin nose bleeding,don haka tunaninshi ha6o ne kawai,
  Hannu yakai tare da kunna tap ɗin,ruwa ya soma shararowa da gudun gaske,tarba hannunshi yayi tare da ɗebo ruwan ya watsa a fuskarshi yana wanke blood ɗin,murzar wurin ya shiga yi don jinin ya tsaya amma yaƙi daina zuba,ya kusan 15mins a haka sannan jinin ya dakata da ɗigowa,ajiyar zuciya ya saki tare da kai hannu ya kashe tap din,
  Sannan ya fito daga cikin toilet ɗin,yana ƙoƙarin ɗaga ƙafarshi ya nufi gadonshi,wani irin jiri ya kwashe shi,hannu ya aza asaman kanshi tare da ambaton sunan Allah,yayin da idanunshi ke ganin mashi biji biji,
  Yana cikin wannan yanayin Sehrish ta faɗo cikin ɗakin ambaton sunanshi ta shiga yi "junaid, junaid.....,"
  ganin shi atsaye abakin ƙopar toilet ya sata tsayawa tana kallonshi tare da cewa"baby junaid meya faru ne naganka haka?baka jin daɗine,"
   Jin muryarta yadinga yi acikin kanshi tamkar ana buga ganga,hakan yasa ya yanke jiki zai faɗi gadan gadan,
  A wani irin slow sehrish ta ƙarasa wurin da sauri ta ruƙo shi suka faɗi ƙasa atare,hankalinta ba ƙaramin tashi yayi ba jin yarda yake kokowar fitar da numfashinsa,hankali a matuƙar tashe take faɗin"Innalillahi_!junaid!meke faruwa dakaine!me yake damunka ne?ka faɗamun dan Allah,
   Ko iya ɗaga la66ansa ba yayi bare ya iya furta mata wata kalma,hannunshi dake kerma yasa tare da ƙara ƙanƙameta sosai ya kwantar da kanshi asaman ƙirjinta yana cigaba da ƙoƙarin fitar da numfashinsa,hankalin sehrish ba ƙaramin tashi yayi ba,tuni ta soma fitar da ƴan matan hawaye,yanke shawarar zuwa ta sanar ma wani tayi don a hanzarta zuwa aga halin da yake ciki,ƙoƙarin janye jikinta tayi daga nashi,tamkar zata rabashi da ranshi haka yaji,ƙanƙameta ya kuma yi sosai da sosai sai lokacin ya iya furta"rishi kada ki tafi ki barni a yanayin da nake ji zan iya mutuwa,"
Cikin shessheƙar kuka take cewa"junaid ka bari inje in sanar dasu,idan wani abu ya same ka fa"?
   "A'a nidai kada ki tafi kibarni,"ya ambaci hakan da wata irin kasalalliyar murya,tsananin tausayinshi ne ya kamata,mayar da hannunta tayi abayanshi tare da ƙara rungumo shi ajikinta tana tofa masa addu'a,lamo yayi ajikinta yana faman sauke ajiyar zuciya,lokaci guda kuma numfashin ya daidaita kamar yarda yake ada,komai nashi yadawo normal,wani irin sanyine ya ratsa zuciyarshi,idonshi na arufe yake shaƙar ƙamshin turaren rishi ɗinsa,gaba ɗaya ya shiga yanayin da bai ta6a shigar irinsa ba,
Muryarta ce ta katse

Chapters

Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login