Showing 156001 words to 159000 words out of 432432 words
Chapter 53 - Abban Sojoji Book 2 Hausa Novel Complete
saki,da sauri Ayaan ya ɗauko robar ruwan tare da kafata a bakin Jahan nan take ruwan ya dinga shiga acikin bakinshi daƙyar daƙyar,wani na shiga wani na fita,ahaka yasamu ya bashi,bayan ya kammala yayi wurgi da robar ruwan gefe guda,sannan ya zauna tare da zabga tagumi yana jiran ganin sakamakon da zai biyo baya,hawaye sai shararo mashi suke a idanunshi,aranshi yana cewa"idan na rasa jahan bansan ya zanyi da rayuwata ba,nima zan bishi ne kawai,"
Yayi maganar tare da runtse idanunshi yana matse hawayen dake fita daga eyes ɗinshi,
Kafin Ayaan ya ankare,wannan baƙin hayakin ya soma kurɗaɗowa ta cikin ƙofofin hancin jahan,yarda kasan an koro shi daga cikinsa,haka ya dinga fitowa kafin kiftawar ido,hayaƙin yayi disappearing gaba ɗaya,tamkar bai ta6a existing ba,
Fitarsa ke da wuya,zufa ta soma tsastsafowa a jikin jahan,kamar an watsa mashi ruwa ajikinshi,haka zufar tashiga feso mashi,a hankali bakinsa ya buɗe ya shiga ambaton"La'ila ha'illallah!
A wani irin firgice Ayaan ya ware idanunshi sai lokacin ya kalli jahan dake kwance zufa ta gama wanke mashi jikinshi,wani irin farin ciki ne ya cika Ayaan la66ansa har rawa suke yi wurin ambaton sunan shi"ja..jahan"
Amsa mashi yayi da"Na'am,"
"Alhamdulillah!Alhamdulillah!Allah na gode maka!" Ayaan ne ke faɗin hakan yayin da yakai hannunshi yana tatta6a fuskar jahan dake ƙoƙarin buɗe idanunshi,
Tunani yazo ma Ayaan aranshi yace tabbas Ruwan cikin robar can ba normal ruwa bane da suka saba sha,akwai wani abu atattare dashi,tun da gashi Yaba jahan yasha kuma ya tashi da irin yanayin daya tashi dashi ɗazu da rana daya sha ruwan,ya tashi yana zufa kuma shima Jahan gashi zufar ce ke fita,hakan na nufin cewa shima Jahan ya warke kenan,
Ƙarasa tunanin nashi yayi tare da kai goshinsa ƙasa yayi sujjada yana ma Allah godiya,🥰
Bayan Jahan ya gama farfaɗowa,Ayaan ya taimaka mashi wurin kaishi toilet yayi wanka,nan take yaji wata irin natsuwa ajikin shi,basu 6ata lokaci ba wurin hayewa saman gadonsu,tare da lullu6ewa da bargo saboda baccin da kowannansu ke ji,yau gaba dayansu sunyi bacci cike da kwanciyar hankali,kuma Ayaan Yaci alwashin sai yayi investigation akan wannan robar ruwan da suka sha,
(Banji daɗi da ruwan addu'ar nan ya zube ba,wlh nima ina buƙatar shi don nasha)
Yanayi mara daɗi,a daren ranar Omar ya kwana yana kukan zuciya saboda abunda yayi ƙoƙarin aikata ma Hosana, ya kwana da tunanin wane hali suke aciki?sunyi bacci kuwa?baida amsar tambayoyin shi dole sai inya gansu,gashi baya jin zai iya takawa yaje dubasu saboda fargabar karsu gane cewa shine yayi masu wannan abun kunyar,matsananciyar damuwar daya sa ma ranshi ne da tunane-tunane ya haifar mashi da wani irin severe headache na 6arin kai,yaji jiki adaren nan har magani yasha amma bai sauka ba,a haka ya kwana yana juyi asaman gadonsa,
Adaren ranar nan dai abubuwa dayawa sun faru masu daɗi da marasa daɗin ji,dama haka rayuwa take ba kullum ake jin daɗin ta ba,idan yau anyi farin ciki,gobe zai iya kasancewa baƙin cikine,idan yau anyi dariya gobe zai iya kasancewa kuka ne,haka rayuwar ke tafiya babu wani yanayi da yake kasancewa permanently,Allah yasa mu dace,yasa mu fi ƙarfin zuciyoyinmu,kuma ya kare mu daga aikata aikin danasani,wasu sun ɗauki rayuwar duniya wani abu,da har suka ɗauke ta da zafi suna aikata abunda suka ga dama,sun manta da cewa acikin seconds za'a iya zare ransu su bar duniyar gaba ɗaya suje su fuskanci abunda suka shuka,duka nawa ne jin daɗin duniyar?basa tuna donme aka halicce su,ta wace ƙopa suka faɗo duniyar nan,taya zasu koma ga mahaliccinsu?daga kai fa sai likkafaninka za'a binne ka cikin ƙabarinka,sai kuma halinka daka je dashi,na gari ne kona banza,😢Allah yasa mu cika da kyau da imani🙏
Wuraren sallar Asuba Sgr ya farka daga dogon baccin daya ɗauke shi,a hankali ya buɗe eyes ɗinshi,yayin da bakinsa ke ambaton addu'ar tashi daga bacci,a kasalance ya miƙe daga kwancen da yake saman doguwar kujerar,mamaki ne ya kama shi ganinshi kwance a palour ɗinsa yana bacci instead of saman gadon shi,ya jima yana mamakin yarda bacci yayi awon gaba da shi adaren jiyan nan,sauko da ƙafafunsa yayi ƙasa,idanunshi suka sauka akan tray ɗin da sehrish ta kawo mashi na dinner ɗinsa da baici ba jiya,tsayawa yayi yana ƙoƙarin tuna abunda ya faru adaren jiya,yunƙurawa yayi tare da tashi tsaye daga saman sofa din ya soma takawa walking slowly,jin sul6in wani abu a ƙasan tafin kafarshi yasa shi yin saurin kai idonshi wurin yana kallo,mamaki ne ya kama shi ganin Mayafin yarinyar nan yashe a kasa,yasan cewa shiya cire mata mayafin amma abunda ya ɗaure mashi kai zaman me gyalenta keyi acikin part ɗinsa?
russunawa yayi tare da kai hannunshi ya ruƙo gyalen tare da ɗagowa dashi yana kallon shi,sai lokacin ya tuna abunda ya faru jiya tsakanin shi da ita,na commanding ɗinta da yayi akan tayi tsallen kwaɗi,to ina yarinyar take,tambayar daya jefa ma kanshi kenan,
Cikin sauri ya zagayo ta bayan sofas ɗin tunkan ya ƙarasa ya hangi yarinyar kwance magashiyyan a sume bata motsi,tasha wahala sosai sam baiyi tunanin cewa zata cigaba da yin frog jump ɗin ba,yasan ba komai ne yaja hakan ba face tsananin tsoronshi da take ji,shiyasa bata yi tunanin ta tafi ba,tunda taga bacci yayi awon gaba da shi,
A hankali ya ƙarasa takawa inda take sannan yaɗan zuƙunna agabanta yana kallon sumar kanta data rufe mata fuskarta,hannu yasa tare da ruƙo gashin kan nata,ya janye mata shi daga saman fuskarta ixuwa gefe guda,
Zuba ma kyakkyawar fuskarta ido yayi yana kallon yarda tayi jaga jaga da hawaye duk ta yamutse saboda kukan da tasha,idonta sun kumbura,haka la66anta ma sunyi suntum dasu,tsananin tausayinta ne ya kama shi,baiji daɗin baccin daya ɗauke shi ba,da baibari tasha wahalar nan ba,ba da nufin ya cutar da ita yayi hakan ba,kawai yaso ya ɗan hukuntata ne donta kiyaye shi sosai,
miƙewa yayi tare da nufar wurin fridge ɗinshi,ya buɗe ya ɗaukko bottle water daga ciki mai sanyi,sannan ya dawo inda sehrish take ya cire murfin tare da ɗebo ruwan a hannunshi ya yayyafa mata shi a fuskarta,ruwan na sauka asaman fuskarta,taja dogon numfashi tare da sauke nannauyar ajiyar zuciya,a hankali tashiga mutsu mutsu zata buɗe idanunta,
"Get up" yace,jin muryarshi yasa sehrish ware idanunta akan sgr dake zuƙunne agabanta,jikinta har kerma yake yi wurin yunƙurawa tare da tashi daga kwancen da take ta zauna,tun kafin taji me zaice ta shiga bashi haƙuri tana cewa"dan Allah ka yafe mun babban yaya,bazan ƙara maimaita kuskuran da nayi....,.'
Kasa ƙarasa maganar tayi,a firgice ta shiga girgiza mashi kai ganin yadda ya ɗago da hannunshi,duk a tunaninta marinta zaiyi amma sai taga akasin hakan,a hankali ya aza tafin hannunshi a saman lallausar fatar gefen fuskarta,ɗan zaro ido sehrish tayi tana kallon fuskarshi,yayin da shi kuma yake kallon brownish lips ɗinta dake ta faman kerma,
Almost 5 mins sannan yace"Tashi ki tafi,"ya ambaci hakan tare da zame hannunshi daga gefen fuskarta sannan ya miƙe tsaye hannunshi ruƙe da bottle water ɗin yana maida murfin robar,daddagewa sehrish tayi tare da yunƙurawa daƙyar ta miƙe,aikuwa nan take ƙafafunta suka bada wani irin sauti ƙasss!,a gigice ta saki wata irin razananniyar ƙara nan take ƙafafun suka gaza ɗaukarta,gaba ɗaya ta tafi zata kife ƙasa,sai dai ina kafin takaiga ƙasan tuni hannun sgr ya damƙi qugunta kwakkwaran ruƙo yayi mata da hannu ɗaya,gabanta ne taji yayi wani irin bugu daga bisani kuma ta shiga sauke ajiyar zuciya ba ƙaramin tsorata tayi ba,har lokacin hawaye ne ke zubowa daga cikin idanunta,janyota Sgr yayi ta faɗo saman jikin shi gaba ɗaya,sannan ya ɗan russinar da kanshi tare da ɗago da ita,ya sanyata a saman kafaɗarshi,yadda kasan ya ɗauki wannan ɗiyar robar ƴar tsana,haka ya sa6i sehrish asaman shoulder ɗinshi,tafiya ya soma yi ɗauke da ita,ya ƙarasa wurin fridge ɗinshi tare da ajiye roban ruwan dake hannunshi,sannan ya juyo tare da kama hanya ya fito daga part dinshi kai tsaye ya nufi downstairs,ajiyar zuciya sehrish ke ta faman saukewa tayi lamo abunta,yadda take jin daɗin kafaɗar tashi tamkar ta hau Jirgin sama,
A natse yake taka matattakalar benen ɗauke da ita har ya ƙarasa saukowa da ita cikin Main palour ɗin nasu,bin ko'ina yayi da kallo babu kowa da alama basu kammala shirin zuwa yin sallar asubahin ba,duk da dama lokaci bai ƙarasa yi ba,a lokacin ake ta haramar fara kiran sallan,
Tunani ya shiga yi a ina zai sauke yarinyar,don shi bai ta6a sanin ma a ina yarinyar take rayuwa acikin gidan ba,har wani lumshe ido sehrish take yi saboda yanayin da ta shiga wata irin kasala ga baccin da take ji,ta gaza yarda cewa sgr ne da kanshi ya sa6ota asaman kafaɗarshi,jin abun take kamar a mafarki,duk da halin da take ciki amma har addu'a take yi cikin ranta Allah yasa dagaske ne ba mafarki bane,
Yana cikin wannan tsayuwar ɗauke da sehrish a kafaɗarshi,kwatsam Abbansu ya fito daga bedroom ɗinshi ya tunkaro main palour din,sai faman sauri yake yi don yaje ya tashi sauran su tashi su kimtsa lokacin sallah yayi,tunɗazu yake trying numbers ɗinsu don ya tashe su amma mutum ɗaya ne kawai yayi picking call ɗin,wato kanal yousouf,amma sauran babu wanda ya ɗaga alamar basu tashi daga bacci ba,
Da wa Allah ya haɗa shi?ae yana fadowa babban falon karaf idanunshi suka sauka akan Sgr dake ɗauke da Sehrish a kafaɗarshi,har sai da gabanshi ya faɗi,cikin sauri Abba ya ɗan ja da baya saboda kar Sg rafayet ya ganshi,har wani murza idonshi yake yi da hannayenshi don ya ƙara tabbatarwa da kanshi abunda yake gani,wai ko idanunshi ne ke nuna mashi ba dai-dai ba,lamarin ya ɗaure mashi kai,tsananin mamaki ne matuƙa ya kama shi,har ƙara leƙawa yake yi don ya tabbatar ma kanshi wanene acikin matasan nashi ya ɗauko mace a kafaɗarshi,
Hasken fatar sgr,da kuma wannan doguwar ƙirar tashi ne suka tona mashi asiri,uwa uba doguwar sumar kanshi,
Doubting ya shiga yi yana cewa"Anya kuwa shine?kodai idona ne ke nuna min ba dai dai ba,kodai tsufa ne yazo mun gadan gadan harya sa nake ganin hakan!kai wannan fa Rafayet ne ba wani ba,yarinyar daya ɗauko a kafaɗarshi kuma wannan yarinyar ce sehrish!ita kaɗae ce ƴar matashiya acikin gidan!idan har zargina ya tabbata toh me ya haɗa shi da yarinyar ne harya ɗaukko ta saman kafaɗarshi?Hakan na nufin a bedroom ɗinshi ta kwana"? Ya jefa ma kanshi tambaya,gaba ɗaya ya kuma ruɗewa,
Can dai yace"Ina yi mashi kyakkyawan zato,amma tabbas akwai alamar tambaya anan!"
Shiru ya ɗanyi yana ƙara leƙensu,abunne ya daure mashi kai sosai tunda yake bai ta6a ganin sgr da mace haka ba,aranshi ya shiga cewa kodai Ya fara kula mata ne?wata'ƙil akwai wata alaƙa atsakanin shi da yarinyar,'
Jinjina kanshi yayi tare da cewa"Biri yayi kama da mutum tabbas!sai yanzu na gane inda ya samu jan baki asaman ƙirjinshi,Oh ni hussein ina nan sake da baki ana mun aika aika acikin gidana!nagode ma Allah daya nunamin wannan abu akan idona,nasan me zanyi!"
Yana fadin hakan ya juya tare da komawa part ɗin nasu,don ya tashi sauran dama Upstairs ya nufa don ya tashi Omar,abunda yasa ya koma saboda baison sgr ya ganshi ya gane cewa ya ganshi ɗauke da Yarinyar a kafaɗarshi,
Jin takun tafiya yasa Sgr juyawa don yaga wanene,Azmee ce ta fito tana ta faman ƴan waige-waige,bakomai ne ya fito da ita ba face neman Sehrish, taje bedroom ɗinta donta tashe ta daga bacci taga babu kowa,hakan yasata fitowa don ta nemeta acikin gidan,
"Ke,zonan,"a ɗan firgice Azmee ta kallo inda yake,dama tunda taji an ambaci hakan tasan cewa Sgr ne,saboda shi kaɗai ke mata wannan kiran kai tsaye kamar wata ƙaramar yarinya,ko sunanta bai iya faɗi sai dae ke,don shi a yadda ya ɗauka duk wata mace ƙarama take awurinshi,
Fargaba ta shiga yi,ganin Sehrish kwance a kafaɗarshi,zullumi ta shiga yi acikin ranta,tsoranta kar ace wani abu ta aikata masa,
ƙarasawa tayi kusa dashi murya na rawa tace"Gani yalla6ai,"
Ko uffan baice mata ba,a hankali ya saukko da sehrish daga saman kafaɗarshi ya tsayar da ita akan ƙafafunta dake ta faman kerma,cikin sauri Azmee ta ruƙo hannunta,hankali tashe take kallonta ganin yadda ko'ina na jikinta ke kerma,cike take da son jin me ya faru da ita,Me ya haɗata da sgr da har ya ɗaukkota haka asaman kafaɗarshi,
Juyawa sgr yayi cikin sauri ya haye saman stairs da sauri da sauri yake taka steps ɗin sai da yakai step na ƙarshe sannan ya ɗan tsaya kamar mai nazarin wani abu,
A lokacin azmee ta ruƙo sehrish tana taimaka mata wurin yin tafiya,a hankali a hankali suka nufi part dinsu,gaba ɗaya sehrish taji wani irin yanayi a tattare da ita,sam bataso sgr ya sauketa daga saman kafadarshi ba,don ba ƙaramin relief ta samu ba,ita kaɗae tasan yarda take ji aduk lokacin da takasance tare dashi,
Runtse idonta tayi yayin da hawaye ke cigaba da zubowa sun jiƙa mata fuskarta sharkaf,suna cikin tafiyar nan,ranta ya bata cewa ta ɗan jiyo ta kalle shi,taga yana nan ko ya tafi,
A hankali ta ɗan juyo da fuskarta, ta kalli upstairs din,adaidai lokacin shi ma Ya juyo da fuskarshi a wani slow,kai tsaye idanunshi suka sauka acikin nata dake kallon shi,gaza janye idanunshi yayi daga kallon hawayen dake shararowa a fuskarta,wani irin tausayinta ne yaji ya kama shi,saboda yasan cewa shine silar zuban hawayen nata,kamar yarda yake kallonta,itama haka take kallonshi duk da sunyi nisa da juna,a hankali ya lumshe idanunshi tare da ɗauke kanshi daga kallonta ya ƙarasa hawa upstairs ɗin da sauri ya wuce bedroom ɗin shi,
Sai bayan da ya 6ace ma ganinta sannan itama ta juyar da kanta tare da mayar da hankali wurin yin tafiyar,har cikin bedroom azmee takaita,ta taimaka mata wurin hayewa saman gadon,ta kwanta yayin da idonta ke kallon ceiling ba komai take tunawa ba,face yarda Sgr ya tarbo waist ɗinta a lokacin da tazo faɗuwa,da kuma lokacin da ya ɗaurota asaman kafaɗarshi,da kuma kallon nan daya juyo yana yi mata kafin ya tafi,
Zama azmee tayi daga gefen gadon tana kallonta tace"Me ya faru dake ne sehrish?meya haɗaki da sgr dana ga ya ɗaukko ki asaman kafadarshi"?
bata 6oye mata komai ba ta sanar da ita duk abunda ya faru a tsakaninta da sgr,
Jinjina kai Azmee tayi tare da cewa"u ave to be very careful rishi,tun farko saida na gargaɗeki akan shi,amma baki ji ba ko?
Muryarta tamkar zatayi kuka tace"Aunty azmee ina kiyayewa,wannan ma matsala aka samu har na manta da gyalena asaman gadonshi,banyi tsammanin zai dawo ba a wannan lokacin......'
Shiru Azmee ta ɗanyi kafin tace"Shikenan amma duk da haka ki ƙara kiyayewa nan gaba,karki ƙara yin gangancin maimaita kuskuren da kikayi yau,"
Sehrish tace"Insha Allah bazan ƙara ba,"
"Allah yasa,ni zan wuce,ki daure ki tashi kije kiyi sallah,"
Amsa mata tayi da"toh," sannan azmee ta miƙe tare da fucewa daga bedroom ɗin nata,ajiyar zuciya sehrish ta sauke,tunda ta kwanta ko kwakkwaran motsi wannan bata iya yi ba,jikinta duk yayi mata tsami,ta so ta tashi ta ɗan gasa jikin da ruwan zafi amma sam tagaza motsi,kamar an aza mata Bulo asaman jikinta haka ta dinga ji,yayi mata wani irin nauyi,a wannan yanayin bacci yayi awon gaba da ita.
_💋Boss Bature💋_
A washe gari
Around 7:00am
A firgice Jahad ta farka daga dogon suman da tayi,sakamakon jin saukar ruwan sanyi da tayi asaman fuskarta,a gigice ta tashi zaune,lokaci guda ta fara ambaton sunan Hosana!hosana!
"Jahad ki buɗe idonki Ni ce fa"
Jin muryar mutum a kusa da ita yasa ta ware idanunta tana kallonta,bakowa bace face Nurse Camilla,zuwanta kenan ta shigo cikin falon taci karo da Jahad a sume ƙasa,hankalinta ba ƙaramin tashi yayi ba,da sauri ta ɗauko ruwa mai sanyi ta yayyafa mata,
A hankali jahad ke kallonta da idanunta waɗanda suka rune saboda kukan da tasha,
Sanye take cikin jeans da t- shirt tare ta ɗaure sumar kanta da ribbom,
a ɗan ruɗe tace"Jahad me ya faru ne?na shigo na same ki a sume menene ya faru dake ne"?
Cikin shessheƙar kuka tace"Hossana tana cikin ɗaki,bansan tana a raye ba ko ta mutu,jiya da daddare wani ya faɗo mana a cikin bedroom ɗin mu har yayi ƙoƙarin yin raping ɗinta........'kasa ƙarasa maganar tayi saboda kukan daya kufce mata,hankali a matuƙar tashe camilla ta miƙe tare da nufar hanyar zuwa ɗakin nasu,
Miƙewa jahad tayi tabi bayanta cikin sauri,zuciyarta nata faman bugawa saboda fargabar a wane hali hossana ke ciki, karfa ace wannan mutumin ya ƙara dawowa don ya cutar da ita,
Yadda jahad ta bar hosana haka suka sameta,naɗe cikin bargon a sume bata motsi,
Hawa saman gadon camila tayi ta ƙarasa kusa da Hosana tare da kai hannu ta shafa wuyanta,kallon jahad tayi dake atsaye cike da fargaba tace"dauko mun ruwan da na bari a falo," amsa mata tayi da toh sannan ta fuce daga cikin bedroom ɗin,within minutes sai ga Jahad ta dawo hannunta ɗauke da bottle water ta miƙa ma Camilla,hannu tasa ta kar6a sannan ta buɗe murfin ta debo ruwan tare da watsa ma hossana a fuskarta,nan take hossana tafarka daga suman da tayi,a wani irin razane ta zabura zata yaye bargon jikinta tana cewa"karka ta6ani Abba banso banso!ka ƙyale ni in tafi,inba haka ba Ya omar zai kashe ka...."
Cikin sauri Jahad ta haura saman gadon tare da rurruƙeta tana gyara mata bargon jikinta gudun kar tsiraicinta ya fito,ganin tana ta faman fisge fisge tana hargowa yasa Camilla tayi mata magana cikin sanyin murya tace
"Hosana!ki kwantar da hankalin ki,babu kowa anan da zai cutar dake,Ni ce Sister Camilla tare da ƴar uwarki jahad a kusa dake,dan Allah ki shiga natsuwarki,"cikin rarrashi takeyi mata magana,
Jahad tace"Hossana gani a kusa dake ki buɗe ido ki kalle ni,"
Jin muryar jahad yasa hossana ta buɗe idanunta tana kallonsu ɗaya bayan ɗaya,fuskar nan tayi sumtun saboda kukan da tasha,idanunta duk sun ƙankance,
"kiyi haƙuri hossana,koma waye Allah bazai barshi ba,nayi ƙoƙarin na kwace ki daga hannunshi amma Allah bai nufa ba,inda na gode ma Allah da bai ƙarasa nufinshi akanki ba,nayi ƙoƙarin na kira ƴa Omar,amma layinshi yaƙi shiga,amma zuwa anjima zan ƙara jaraba kiran shi,nasan zai ɗaga,"
Cikin shessheƙar kuka tace"Jahad ki kira mun shi,a kiramun ya Omar yazo,inason naganshi,shi nakeson gani,"
Jiki a sanyaye Jahad tace "Kada ki damu zan kira maki shi,insha Allah,"
gaba ɗaya lamarin ya girgiza Camilla,ta jima tana hasashen waye yayi ƙoƙarin cutar da yaran