Showing 135001 words to 138000 words out of 432432 words

Chapter 46 - Abban Sojoji Book 2 Hausa Novel Complete

mu tafi,bansan menene amfanin tambayarta ba,
   mayar da idonshi yayi akan na Jahan yace"pls ka bani time,zan faɗa ma dalilin dayasa nake tambayarta,"
  tsuke fuska jahan yayi yana faman hura hanci,
   "Ina sauraronki," muryar ayaan ce ta katse mata tunanin data tafi,
  Murya asanyaye tace"ƴar uwatace ita,na jima ina nemanta bamu ta6a haɗuwa da ita ba,ita ma kuma nema na takeyi,tunda tayi aure na rabu da ita,shine yanzu nasamu sunan garin da take nazo,amma bansan a ina zan sameta ba,abu ɗaya kawai nake dashi numbar wayarta,drivern daya kawoni ya kirata a waya ya sanar da ita cewa tazo ta ɗauke ni,batazo ba shine wasu mutane suka biyoni acikin tashar,wannan ne dalilin dayasa nayi gudu harna faɗa saman titi Motarku ta buge ni.........'
   jinjina kai Ayaan yayi tare da cewa"Yanzu idan na kaiki gidan Auntynki,Ni kuma wani tukuici zaki bani,"
   cike da mamaki tace"kasan inda take ne"?
  Lumshe idonshi yayi tare da cewa"a'a bansan inda take ba,amma inaso zan kaiki wani wuri in ba damuwa,bari nasa doctor ya sallame ki,sai mu tafi atare,Zaki bini?
   shiru ta danyi tana tunanin karfa tayi gangancin binsu wani abu ya faru da ita,tunda ita dae batasan ko su wanene ba,amma ta wani 6angaren taji cewar zata iya binsu saboda ta yarda dashi sosai,ba don komai ba sai don yarda yake yi mata magana cikin lallami,"
   amsa mashi tayi da eh,miƙewa ayaan yayi daga saman chair din,ruƙo hannun jahan yayi tare da janshi gefe guda yace"ko kasan cewa numbar da yarinyar can ta bani na kira mata auntynta,ta matar Ya Abbas ce Amani!"
  Fuska ɗauke da mamaki Jahan yace"Really?kenan ƙanwarta ce ita,amma indai hakane ya akai ita yarinyar ta kasance haka?
  Ayaan yace"abunda nake tunani kenan nima,"
   jahan yace"Ba shakka,dama na jima ina tunanin taya akai Ya ishaq da Ya Abbas suka auri waɗannan matayan nasu,Nidae raina ya jima yana bani cewa matsiyatan talakawa ne,saboda koda mu kaje ɗaurin aure fa a maid,bakaga tsohonsu ba wani zararre dashi,yadin jikinshi duk ya koɗe,zariyar wandonshi fa har ƙasa take ja,abun kunya...'
  Rufe mashi baki Ayaan yayi cikin sauri saboda yarda yake magana yana ɗaga Voice ɗinshi,yarinyar zata iya ji,
   "Pls jahan its okey,mubar wannan zancen nidae yanzu so nake mu ɗauki yarinyar mukaita gidan Auntyn nata...'tunkan Ayaan ya ƙarasa maganar Jahan yace"Wai a motar wa kake nufin za'a kaita?ae wlh waccan sauran ramin bazata ƙara zauna mana a motar mu ba,sai dai ka tsaida taxi ta kai ku atare,ni kaga tafiyata"yana kai ƙarshen maganar tashi ya juya tare da fucewa daga cikin room ɗin,
   girgiza kai kawai Ayaan yayi tare da cewa"sai yanzu nasan da wa nake tare,Jahan sam baka da mutunci,haihuwarmu kawai akai atare amma zuciyoyinmu ba iri ɗaya bane,ni ta 6angaren Abba nake kai kuma ta 6angaren Mommynmu kake da kuma Ammi dama sune masu zafi,'

Batare da 6ata lokaci ba,Ayaan yasa aka sallami Amal ba don komai ba sai don yayi suprising ɗinta,kamar yarda jahan yace sai dai su hau taxi hakan ce tafaru,a bakin Hospital ya tsayar masu da taxi suka shiga ciki atare,

**********************Reeshi

Zaune suke acikin class sun natsu suna sauraron karatun da akeyi masu,malaminsu ne mai koyar dasu islamic studies,tun da ya fara karatun ya lura da yarinyar dake kwance tana yi mashi bacci acikin class,shiru kawai yayi baice komai ba,sai da ya kammala karatun sannan yace"wacece waccan yarinyar dake yi mun bacci acikin class"?ya tambaya yana nuna sehrish da maker ɗin hannunshi,
  kamar jira ƴan class ɗin sukeyi ya tambayesu nan fa kowa yashiga bada bayani,
   "Uncle ae wannan yarinyar da kake gani sleeping sickness gare ta,ba'a ta6a yin darasi ba idonta biyu,kullum cikin bacci take kamar mai tsohon ciki," fashewa da dariya ƴan class din sukayi,
  Wani kuma yace"sir,da zarar tearcher ya shigo cikin class shikenan zaka ga ta fara hamma,daga nan sai bacci,"
   Bayan ya gama sauraron bayanansu,ya taka ya ƙarasa inda seat din sehrish yake,hannu yasa tare da ɗan bugun desk din,a firgice sehrish tafarka tare da ɗago da kanta daga saman desk ɗin tana kallonshi,
   jallabiya ce ajikinshi fara,ya tara dogon gemu,kana ganinshi zaka san cewa ba ƙaramin malamin addini bane,fuskarshi na manne da farin glass yayin da kanshi ke anaɗe da rawani,
    hankali tashe sehrish ke kallonshi tayi wuƙi wuƙi da ido saboda tsoran karya hukunta ta akan baccin da take yi mashi a class,
   Cikin harshen larabci yace mata ta miƙe tsaye,jiki na rawa sehrish ta miƙe tana faman zazzare ido,
   "Kalli cikin idona,"ya bata umarni,sunnar dakai sehrish tayi tana faman jin wani irin bugun zuciya,maimaita mata ya sake yi da cewa"bakiji me nace ba!ki kalli cikin idona!"
   ƙin ɗagowa tayi da idonta ta kalleshi,kuma nan take jikinta ya shiga yin kerma,
  Ƴan class ɗin duk sun zuba ido suna kallonsu,musamman amrish da tashiga damuwa ganin kamar malamin nason takurawa ƙawarta,
  Cikin sauri tace"pls uncle ayi mata afwa,bazata ƙara ba,'
  Batare da ya kalleta ba yace"Amrish ba laifi tayi mun ba,in fact nikeson taimakonta,shin wannan yarinyar ƴar wani gida ce"?ya tambaya yana jiran amsarsu,har lokacin sehrish na tsaye kanta na kallon kasa a matuƙar tsorace take,
   amsa mashi su kayi da cewa"bamu san a wani gida take ba,lokacin da aka kawota class ɗinnan tayi introducing ɗin kanta amman bata faɗa mana family status ɗinta ba,,'
  Amrish tace"nima bansan taƙamaimai daga inda take ba,amma akwai wani elder bro dinta dana sani sunan Shi Junaid romeo,muna shiri sosai dashi,'
  mayar da idonshi yayi kan fuskar sehrish yace"Ke!a wani gida kike?su wanene iyayenki?
  murya na rawa tace"Ni....ni..daga family din SALAHUDDEEN HUSSEIN nake Abban sojoji....'tunkan ta ƙarasa maganar malamin ya waro ido waje yana kallonta,bama shi ba hatta sauran student ɗin cike da mamaki suke kallonta,sun jinjinawa gidan da tafito bakomai yafi ɗaure masu kai ba face yarda ta kasance ba ruwanta da kowa haka,bayan duniya tasan da zamansu,
  "Kina nufin ke ƙanwar Surgeon genaral rafayet ce!da marshal Omar!"?
Amsa mashi tayi da cewa"eh,"kuma har lokacin bata ɗago da ido ta kalleshi ba,
  Jinjina kanshi yayi yana tuna wani abu daya ta6a faruwa dashi wanda ke da alaƙa da gidan,"
    gajiya da tsayuwa sehrish tayi nan take idonta suka soma shararo da kwalla,don bata da juriyar wahala irin hakan,tun lokacin data fara rayuwar hutu da jin daɗi,
   "Insha Allah bazan fasa ba,kamar yarda nayi kyakkyawar niyyar taimakawa tun a lokacin baya,don haka zan taimaka maki tunda Allah ya haɗani dake," malamin ne yayi wannan maganar,sannan ya mayar da idonshi kan amrish dake zaune a seat ɗinta tana kallonsu yace"Amrish idan na kammala yi maku karatu ki same ni a office ɗina zan baki ruwan addu'a kiba wannan yarinyar tayi amfani dashi,"
Amsa mashi tayi da toh sir,sannan yaja da baya tare da juyawa ya koma wurin board,
   Jiki asanyaye sehrish ta koma tare da zaunawa tana faman sauke ajiyar zuciya,aranta tana mamakin ruwan addu'ar mi zai bama amrish ta bata,gaskiya ni bazanyi amfani dashi ba,lafiya ta lou,koya ban zubarwa zanyi.......'
  Sai faman sambatu takeyi ƙasa ƙasa sam takasa samun natsuwa har sai da Malamin yabar Class ɗin,tashi amrish tayi tare da binshi don ta amso mata ruwan addu'ar dayace zai bata.

bayan mai taxi ɗin ya sauke su,hannunshi ruke dana Amal suka shiga cikin gidan,gaba ɗaya duk tabi ta susuce tana kallon katafaren gidan duk a tunaninta kodai gidansu ne ya kawo ta? Lokacin da suka shiga katafaren palourn babu kowa acikin shi,tsayawa yayi tare da ita atsaye yana jiran ganin ko wani zai fito,ita kuwa Amal wuyanta kamar zai tsinke saboda kalle kalle muryar Ayaan ce ta katse ta da cewa"har yanzu ciwon na maki zafi?girgiza kai tayi tare da cewa"a'a babu zafi ina lafiya,"
  "Okey,ki ɗan ƙara jira nasan matar gidan zata fito ne,bari na sake kiran layinta,"
  Hannu yasa tare da ciro wayarsa yana ƙoƙarin danna ma Amani kira,kunnan shi suka jiyo mashi takun takalmanta kwas kwas,ɗagowa su kayi gaba ɗaya suna kallonta,hannunta na ɗauke da tray da alama kayan breakfast ɗinsu da suka ci na safen nan ta fito dashi daga bedroom ɗinta dake a upstairs,jallabiya ce fara ajikinta ta yafa mayafin akanta,
  A hankali take saukowa down stairs sam bata lura da mutane ba,ƙura ido Amal tayi tana kallonta sam takasa gane wacece,juyawa ta danyi tare da kallon Ayaan tana neman ƙarin bayani,a lokacin shima idonshi na akanta yace"baki gane ta ba ko"?
  ɗaga mashi kai tayi alamar eh,murmushi yayi tare da cewa"Bari ta matso kusa,"
  Gyaran murya Ayaan yayi wanda hakan yasa Amani tayi firgit tana kallonsu,murmushi ta saki ganin Ayaan cikin sauri taƙarasa saukowa daga saman stairs ɗin ta tunkaresu,zuba mata ido Amal tayi tana kallonta tabbas taso ta shaidata amma abunda yayi confusing ɗinta shine,taya zata kasance wadda take tunani tunda saurayin ya kawota gidan tafi tunanin ko Auntynshi ce,
  Tunkan Amani ta ƙarasa inda suke,hankalinta yakai ga Amal binta da kallo ta dinga yi cike da mamakin ina Ayaan ya samo wannan yarinyar haka,duk taji jiki kodai ya fara taimakon marayu ne,
  tsayawa tayi kusa dasu idonta na akan Amal ita ma kallonta takeyi,ji tayi gabanta na faɗuwa rasss rassss,cikin sauri ta mayar da idonta akan Ayaan murya na rawa tace"who...who is she pls?
   Murmushi ayaan yayi yace"i don't even know,ni dai ta bani numbar auntynta ne tace na kira mata ita,shine dana sa numbar Auntyn nata sai sunanki ya bayyana akai,that's why nayi deciding kawota wurinki,maybe adace.........'tunkan ya ƙarasa maganar a firgice Amani ta saki tray ɗin hannunta ya tarwatse ƙasa,zube wa tayi saman guiwowinta kusa da Amal ɗin ta ruƙo hannunta tana cewa"Amal kece dagaske nake gani,ko idona ne Innalillahi wa'inna ilaihirraji'un,"!!!
  Tuni hawaye sun cicciko acikin idonta,
  Itama Amal ɗin tuni ta fara shararo hawaye saboda ta ganeta yanzu musamman data ambaci sunanta,
  Cikin shessheƙar kuka tace"Ni...Ni ce aunty Amani,ashe dama zan sake ganinki arayuwata.........'kukane yaci ƙarfinta hakan ne yasa takasa ƙarasa maganar,atare suka fashe da kuka suna yi kamar kamar me,
   Muryar Ayaan ce ta katse su da cewa"pls Aunty amani,ki lallasheta akwai wounds ajikinta idan tana kuka hakan zai ƙara mata raɗaɗin ciwon,"dakyar Amani ta tsagaita da kukan nata kallon fuskarta har izuwa jikinta,tayi matuƙar tsorata da ganin yarda yarinyar ta tsotse ta rame ta ƙanjame kamar kwarangwal,ƙashin wuyanta kamar zai ballo waje,komai na yarinyar da zai nuna cewa ita macece babu shi,sai dai ta hanyar shigarta ta mata da kuma muryarta,
   Janyota tayi ajikinta tare da rungumeta sosai tana ci gaba da ambaton sunanta"Amal amal ɗita ce ta koma haka?meya faru dake Amal ya akai kika 6ata,ki ka tafi kika barni inata nemanki Amal,"
  Ganin halin da suka shiga yasa Ayaan yanke shawarar tafiya yabarsu,juyawa yayi kawai tare da kama hanya ya fuce daga falon dama jahan sai doko mashi calling yake,

  Anan ƙasa Amani da Amal suka zauna atare suna fuskantar juna,
  "Amal kina jin yunwa"? Jin wannan tambayar yasa hawaye suka ƙara cika mata ido,yaushe rabon da wani ya tambayeta tana jin yunwa harta manta Allah sarki ɗan uwa mai ɗaɗi,musamman in ya kasance shaƙiƙin kane kuma kuna son junanku,
   Murya asanyaye tace"bana jin yunwa naci abinci a asibiti,"
   Jinjina kai Amani tayi tare da cewa"inason jin Ya akai kika 6ata Amal kika barni?mammy ta sanar dani cewa bakyajin magana wai kina zuwa yawo sun hanaki kin ƙiya shine kika 6ace aka neme ki aka rasa....'
   Girgiza kai tashiga yi yayin da hawaye ke cigaba da sharara a idonta tace"Aunty amani wannan duk ƙaryace suke yi maki!nagode ma Allah da ya haɗani dake,a yau inaso zan sanar dake komai game da irin cin zalin dasu Mammy sukayimun na raba ni dake,
   Hankali tashe Amani ke kallonta murya na kerma tace"faɗamun meya faru dake!wani irin cin zalin su kayi maki,"
  Batare da 6ata lokaci ba,Amal ta zayyana mata duk irin ƙarairayin da sukeyi mata akan cewa ta 6ace,da kuma irin wahalar da takesha a hannunsu da kuma kaita da sukeyi gidan makwabtansu ana kulleta,babu abunda Amal ta 6oye mata kaf takwashe ta sanar da ita,
  A kiɗime Amani ta miƙe tsaye cikin tsananin 6acin rai,jikinta har kerma yake yi,wasu irin zafafan hawaye ne suka shiga shararowa a idonta,
   Sai faman cizon yatsa take yi tana danasani,kai aƙarshe data rasa abunyi sai ta sake fashewa da wani matsanancin kukan tana girgiza kai tana cewa"Wlh bazan ta6a raga masu ba!mugaye azzalumai kawai,banta6a ganin mutane masu zuciyar kafirai ba irin tasu,Sun cutar dake Amal kuma sun cutar dani sun yaudareni sunyi mun ƙarya suna samun kuɗi awurina na cewa za'a ba malamai suyi addu'ar neman sa'a akanki ashe duk ƙarya ne!!!!basu tsaya a iya kanmu ba sun cutar da mahaifiyarmu har saida tabar duniya ga mahaifinmu da suke ta gana ma azaba,nayi tunanin soyyaya suke nuna min ta ƴan uwantaka shiyasa na saki jiki dasu har nake ƙoƙarin taimaka musu wurin cimma wannan mummunan ƙudirin nasu,ashe cutata suke suna can suna gana ma ƙanwata azaba,na cuci kaina!tun yanzu Allah ya fara nunamin irin kuskuren da nake ƙoƙarin yi na taimakama waɗancan bijimayen.......'tsagaitawa tayi da maganar tana faman shessheƙar kuka,daga bisani ta ɗaura da cewa"wlh saina tarwatsa duk wani plan ɗinsu uban kowa ya rasa don bazan kyalesu ba,muddin ina numfashi hayaam ko abra ɗaya daga cikinsu bazai ta6a auran jinin salahuddeen hussein ba!!!!,
abun ba ƙaramin ƙona ma Amani rai yayi ba,ta fusata ainin zuciyarta har wani tafarfasa take yi saboda 6acin rai,
Hannu tasa tare da matse kwallarta sannan ta juya tare da takawa takai hannu ta ruƙo hannun Amal ta miƙar da ita tsaye,sannan ta wuce da ita cikin bedroom ɗinta gado ta nuna mata tare da cewa"Amal ki kwanta ki huta kin raunata sosai,amma karki samu damuwa tunda Allah ya haɗaki dani ƙarshen wahalar ki tazo insha Allah,zakiyi rayuwa tare da Auntynki zan baki kyakkyawar kulawa,kuma zan kira doctor domin ya ƙara dubamin lafiyarki da kyau har kiji sauƙi,
Ba ƙaramin daɗi Amal taji ba farin ciki har bakinta ya gaza rufuwa,sai da amani ta tabbatar cewa Amal ta kwanta sosae saman gadon sannan ta zauna daga gefen gadon tana kallonta har bacci yayi awon gaba da ita,amani bata bar wurin ba,kallonta take hawaye na zuba a idonta haƙiƙa su Mammy da Aunty babba ba ƙaramin cutarta su kayi ba,
Jinjina kai tayi tare da cewa"rama cuta ga macuci ibada ne,Aunty laila kin shiga uku dani,zanbi duk hanyar da zanbi don ganin na tarwatsa plan ɗinki,dama ke jani talau ce sai yarda akai dake sannan kike bi,zanyi amfani da wannan damar wurin lalata shirinki"
Haka Amani ta dinga tufka da warwara a ƙarshe ta shirya nata plan ɗin.
****************
Hayaam na zaune saman gadonta hannunta ruƙe da wayarta tana jiran shigowar kiran Sofwan,harta fidda rai da zai kawo mata trolley ɗin sai ga message ɗinshi ya shigo wayarta,cikin sauri ta buɗe tana karantawa,
_hi beb ya kike ya kwanan gidan surukai ina fata kina lfy,nafa zo gidan ki turo wani ya amsar maki trolley ɗin kayan,don bazasu bar ni nashigo ba_
Jin hakan yasa tayi saurin saukowa daga saman gadon tare da ɗaukar dogon hijabinta dake ajiye saman gadon,zurawa tayi ajikinta sannan tafito daga cikin bedroom ɗin,kama hanya tayi ta fito main palour ɗin tana wurga ido don tasamu wanda zai kar6ar mata kayanta,tana cikin wannan tunanin sai ga Fawan ya fito daga part ɗinsu,
kwala mashi kira tayi cike da kisisina tace"Fawan"!
ɗagowa yayi yana kallonta da wannan kallon nashi na rainin wayau,
cikin sauri hayaam ta nufe shi sai da tazo kusa dashi sannan tace"dan Allah taimako nakeso kayimun,wani brother ɗina ne ya kawo mun trolley ɗin kayana,an hanashi shigowa ciki shine nace ko zaka taimaka ka amso mun,"
Yatsina fuska fawan yayi tare da cewa"Am sorry ni bazan iya wannan wahalar ba,zan dai kira ɗaya daga cikin security guards ɗin na basu umarnin su barshi ya shigo abokina ne inyaso sai kije ki kar6o kayanki,"
washe baki hayaam tashiga yi tana cewa"thank u so much fawan,kana da mutunci sosai naji daɗin taimakonnan da kayimun,' ɗan ta6e baki fawan yayi tare da kai hannu ya ciro wayarshi a aljihun rigarshi,call ya buga tare da kara wayar a kunnanshi,ɗaga kiran akayi sannan ya sanar dasu cewa subarshi ya shigo abokinshi ne,amsa mashi sukayi sannan ya kashe kiran,
batare da ya kalleta ba yace"kije ki amso kayanki,"
da hanzari Hayaam ta juya tare da kama hanyar fucewa daga falon sai faman sauri take yi kamar zata tashi sama,
Ruƙe ƙugu fawan yayi tare da cewa"Ikon Allah,nifa bangane ma Yarinyar can ba,Naji tana cewa zata amshi trolley ɗin kayanta me hakan ke nufi"?ya jefa ma kanshi tambaya,cizon la66ansa yayi tare da cewa"zaki gane kuranki ne,"yana faɗin hakan ya kama gabansa

*💋Boss Bature💋*

Wuraren ƙarfe 1:30 junaid ya ɗauko sehrish daga school,tun acikin mota ya lura da yanayinta duk a yamutse babu natsuwa a tattare da ita,har tambayarta yayi ko bata jin daɗine,sai ta sanar dashi cewa bacci ne kawai take ji,jin haka yasa ya ƙara gudun motar har suka ƙaraso cikin gidan,
Fitowa tayi daga cikin motar tare da komawa ta buɗe back seat ɗin ta curo school bag ɗinta sannan ta wuce cikin gidan da sauri,
Abun ya ɗaure ma junaid kai,ganin ta tafi batare da ta jirashi ba kamar yarda suka saba shiga cikin gidan hannunsu ruƙe dana juna,
hannu yakai tare da buɗe motar ya fito bayan ya rufeta,ya kama hanyar shiga interior ɗin gidan,koda ya shiga main palour ɗin kai tsaye ya wuce upstairs bedroom ɗinshi don shima a gajiye yake,
wani irin zazza6ine ya rufar mata,dama tun lokacin da suka haɗa ido da wannan malamin taji gaba ɗaya yanayinta ya sauya,tana shiga bedroom ɗinta tayi wurgi da school bag ɗin ƙasa,sannan ta faɗa saman gadonta tare da kwantawa tana faman juyi asaman shi,
A wannan yanayin bacci yayi awon gaba da ita,
Turo ƙopar bedroom ɗin nata junaid yayi anan ya same ta tana ta faman sharar bacci ajiyar zuciya ya sauke tare da juyawa zai fuce daga ɗakin karaf idonshi suka sauka akan Bottle water ɗin da malamin nan yaba Amrish takai mata,ashe lokacin da ta shigo ɗakin tayi wurgi da jakar nan take robar ruwan ta gangaro daga cikin jakar,saboda ta manta bata rufe zeep ɗin wurin data sanyata ba,
Murmushi junaid yayi yace"Oh ni reeshi kamar wata

Chapters

Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login