Showing 51001 words to 54000 words out of 432432 words
Chapter 18 - Abban Sojoji Book 2 Hausa Novel Complete
zanso ko na tuna sunan shi daga gani cele ne shi sosai,"
Sai faman surutu suke yi suna yaba kyan junaid,
"Kai nifa bazan iya jure ba, sai nayi ma shi magana," ɗaya daga cikinsu ta faɗi atare suka iso dab da su junaid da sehrish, su uku ne matan
junaid yace "Sannun ku fa," suka amsa mashi da "Yawwa," sannan ɗaya daga cikinsu tace "Kamar na sanka,"ta faɗi cikin rangwaɗa
Junaid yace " Sunanki Parveena," zaro ido su kayi jin yadda junaid ya faɗi sunan ɗaya daga cikinsu kai tsaye, Nuna ɗayar yayi ta tsakiyarsu yace "ke kuma Sunanki Amrish ta ƙarshen kuma sunanki Naja'at," ya faɗi da murmushi a fuskarshi, su kuwa sai faman yarfa hannu suke yi suna kallon shi cikin mamaki jin yadda ya zayyana sunayen su gaba ɗaya,
Cikin mamaki wadda ya kira da Amrish tace "Dan Allah ya akai kasan sunayen mu"?
Ta tambaya cike da zumuɗin son jin amsa,
Duk wannan abun dake faruwa akan kunnan sehrish wadda ke ruƙe da rigar junaid taɗan la6e abayansa,
Junaid yaci gaba da cewa "Ban son ku ba nima kawai abunda nasa ni ke Amrish kece kullum kike isarmu da surutu a group, ke kuma parveena baki da aikin yi sai turo hotunan Chacolate iri-iri, Sannan ke kuma Naja'at kinfi kowa iya turo hoton abinci duk in zaki ci sai kin turo mana hotansa,"
Gaba ɗayansu suka saka ihu da sowa har suna haɗa baki wurin cewa "Wai dama kaine ! junaid romeo ko?
Murmushi junaid ya saki tare da cewa "Ni ne, bamu ta6a haduwa ba amma muna yin chat sosai ta whatsapp a group, na ruƙe fuskar kowannan ku da sunayen ku,".
Ba ƙaramin farin ciki su kayi ba, Amrish ta nuna sehrish tare da cewa "wannan fa? sister ɗinka ce"?
Junaid yace "Eh, younger sis ɗina ce, new comer ce yau tafara zuwa,"
Parveena tace "No wonder, that's why naga tana hiding kanta abayanka, amma kamar batason mutane ko? Naga ko son kallon mu bata yi,"
Junaid yace "No just kin gane shagwa6a6iya ce, Last born ɗin mu ce bata saba shiga cikin mutane ba kullum tana a gida, so aduk lokacin da aka fito da ita cikin mutane tana ɗan razana,"
tunda ya soma jawabi sehrish ke kallon shi baki asake, jin irin ƙaryar daya zuƙa mata nafarko yace ƙanwarsa ce ita, kuma ya laƙwafa mata sharrin cewa tana shagwa6a bayan shine shagwa6a66e, jinjina kanta kawai takeyi,
Amrish tace "Ayyah na tausaya mata but she's so cute kuma ta fito daga babban gida yakama ace tana shiga mutane,"
ta6e baki sehrish tayi tana ɗan kallonsu, 6an6aro hannunta junaid yayi daga jikin rigar shi, sannan ya miƙa ma Amrish yace "Gata nan dan Allah amana na baki ita, ki tafi da ita ba ta son komai ba da yake ita ɗin rainon kakarmu ce, sai ahankali," 😆
Murmushi Amrish ta saki tare da kar6ar hannun Sehrish tace"aikuwa na gode sosai da wannan kyautar, kuma zan ruƙe amana,"
Cikin raha sukayi sallama da Junaid yayin da suka shiga ciki da Sehrish duk ta zama tamkar mutun-mutumi , suna tafiya tana waiwayon junaid shima kansa sam yagaza tafiya kallonta kawai yake yi, sai yaji duk kewarta ta kama shi daker ya ɗaga mata hannu tare da yi mata bye-bye,'
Sannan ya buɗe motarsa ya shige, yayi mata key sannan yaja ta da gudu yabar makarantar, sai da yayi nisa da driving ɗin sannan yayi parking ɗin motar agefen titi yana shesshekar kuka yana cewa "ko na minti ɗaya bana son rabuwa dake sehrish kewarki nake yi," yayi maganar tare da curo handkerchief ɗinsa daga front pocker ɗin rigarsa yana faman share hawayensa, ya jima acikin motar duk kasala ta dabaibaye shi daker ya iya tayar da motar yaci gaba da driving ya miƙi hanyar komawa gida 😥
Parveena da Naja'at Class ɗinsu suka wuce, Amrish ce tayi ɗawainiya da Sehrish ta raka ta har Admin ɗinsu wurin principal ɗin makarantar, maca ce hamshakiyar gaske tun da taji sunan sehrish tagane cewa daga Family ɗin Salahuddeen Hussein take, hakan yasa ta sake mata sosai har tana jan ta da fira, daga bisa ni taba ma Sehrish Sunan Class ɗin da zata zauna, Science department ne kuma an ci sa'a Class ɗinsu ɗaya da Amrish SS1 science C, Madaddalar ƴan iska ba 😂
(Nima Science C nayi a school ɗinmu wlh basa jin magana, dama anyi ittiƙafi babu wanda yakai ƴan C rashin jin magana)
Hannunta na ruƙe dana Sehrish suka tunkari benen da zai sadaka da Upstairs ɗin makarantar, anan Classes ɗin suke akwai kuma na down,
sehrish dae sai bin ko'ina take da kallo makarantar ta haɗu kamar ba wurin ɗaukar karatu ba saboda tsaruwarta ga wuraren shaqatawa,
shiga Class ɗin sukayi mutun goma ne a cikinsa a ƙa'ida kowane class mutun 12 ne kacal acikinsa maza 6 mata 6, idan aka haɗa da Sehrish da Amrish 12 kenan student ɗin cikin sa,
gaba ɗaya Ido yadawo kan Sehrish kowa da irin kallon da yake yi mata, Mazan class din kuwa tuni sun soma sakin baki suna cewa "Wow so beautiful, so hot, She looks so sexy,"
Gabanta ne ya faɗi kowa da irin abunda yake cewa, Matan kuwa wani irin kallo suke binta dashi irin kallon hadarin kajin nan,' ƙara ƙanƙame school bag ɗinta tayi daga tsayen da take,
Amrish ce ta soma magana" Hello Class we ave a new comer today, She's from awesome family, i hope zaku bata hankalin ku domin tayi mana Introducing kanta,"
ta ƙarasa maganar tare da kallon Sehrish tace "Pls introduce ur self,"
ɗan gyaran murya Sehrish tayi sannan ta soma cewa "am....Sehrish Salahuddeen Hussein by name, 17years old.... Alhamdulillah I love the Way i am,"
Wannan bayanin na sehrish yasa su gaba ɗayansu Clapping hands ɗinsu suna tafa mata, musamman ƙarshen maganarta ta ƙayatar dasu,
Sun mata kyakkyawar tarba duk da akwai waɗanda tunda ta shigo ma basu ɗago da kansu ba daga saman desk sun kife shi kamar masu bacci,
Kowane seat mutun ɗaya ne, Amrish ta sama ma Sehrish gurbi a Middle Roll na Class ɗin 0a Second seat Amrish kuma na'a First seat, sai da tafara neman alfarma wurin asalin mai seat ɗin na sehrish akan tabar mata, kuma cikin sa'a ta amince shine har tasamu gurbi abayanta, komai yazo mata cikin sauƙi kuma ba ƙaramin daɗi taji ba na haɗuwarta da AMRISH 💃
******************AUNTY BABBA***********************
tun da sassafe suna kwance wayarta ta soma ringing a firgice ta farka jikinta na sanye da kayan bacci brown colour, leƙa fuskar Ishaq tayi taga koya buɗe ido samun shi tayi sai faman Sharar baccin sa yake, don haka a hankali ta lalla6a ta sauko daga saman gadon cikin sanɗa,
Bayan ta sauko ta ɗauki wayarta data ajiye saman side drawer ɗin shi, sannan ta lalla6a ta shige cikin toilet ta duba mai kiran nata mutumin da tayi tsammani shi ta gani wato*BABA ALAMU* murmushi ta saki cikin sauri ta ɗaga kiran ta kara a kunnanta tun kafin tayi magana baba alamu yace "Na faso gari fa, tun jiya da daddare inata kiran layin ki baya shiga,"
Aunty babba tace "wlh bansan ka kira ba, dayake nabar wayar acikin ɗakina sai da asuba na ɗauko ta, tun jiya nima nake jiran kiran naka mutumina,"
Dariya baba Alamu yayi sannan yace "Ae ke baki sani ba, jiya muna dira gari na kwaso rugwagwar motata na shigo unguwarku don in sanar maki kawai sai naga waɗannan Masu fuskar shanayen tsaitsaye ruƙe da bindiga ae ba arziƙi naja motata na koma,"
Fashewa da dariya aunty babba tayi tace"Ae mijina ne yadawo jiya shiyasa kaga sojoji nan,"
Baba Alamu yace "Oh to ashe angon ne yadawo, yanzu dae ya za'ayi wurin fitar da yaran kinsan fa wlh shegen tsoran Soja nake, don kwanaki sun ta6a tarar mu a hanya suka sanya mu tsallen kwaɗi a tsakiyar titi da rana tsaka,"
Aunty babba tace "Ae basu da Imani, musamman in suka ji su acikin kakin nan sai su dunga ɗaukar kansu tamkar wasu dodonni, yanzu abunda za'ayi kana ina ne?
Baba alamu yace "yanzu haka na fito da mota ta ina kan hanyar zuwa unguwarku amma fa bazan shigo ciki ba sai dai ki san yarda zakiyi a fito da yaran,
Aunty babba tace "Shikenan ka jira ni, zaka ga kirana yanzun nan bada jimawa ba,".
bayan ta kammala maganar ta kashe wayar sannan ta fito daga cikin toilet ɗin cikin sanɗa ta lalla6a ta fuce daga ɗakin,
Kai tsaye ta nufi ɗakin hafsat ta shiga, tsayawa tayi tana kallonsu hussana da jahad dake ta faman sharar bacci baje saman gadon hafsat, yayin da ita kuma hafsat ɗin ke kwance saman doguwar kujerar ɗakin tana bacci, da alama dukansu daga tashin asuba suka koma bacci,
jinjina kanta tayi sannan ta ƙarasa dab da hafsat ta ɗansa hannu ta bubbuga ƙafarta, a dan firgice hafsat tafarka tana cewa "wanene,"
Murya ƙasa ƙasa aunty babba tace "ke ki taso inason magana dake,"
Bin ta da kallo hafsat tayi tana yamutsa fuska Alamar bacci bai ishe ta ba, daker tasa hannunta ta janye bargon data lullu6e rabin jikinta da tashi sannan ta miƙe tsaye tabi bayan aunty babba, suka fito daga ƙopar ɗakin suna fuskarta junansu hafsat tace "Meya faru mommy naga kin tashe ni ina tsaka da bacci na? Aunty babba tace "Mutumin fa wanda zai kai su hussana da jahad gidan marayu ya ƙaraso....,"
jin hakan yasa hafsat canza fuska tuni tace "Mommy yanzu dole sai kin raba ni da yaran nan? Wai me suka tsare maki ne? Dan Allah mommy kibarsu suyi rayuwarsu cikin salama, sun sha wahala fa baki tausayin su?
tsoki Aunty babba ta buga tuni ta tamke fuska tace "Tausayin Uban me? menene alaƙata dasu? ke bana son zancen banza mun riga da mun gama magana dake don haka ! Ke nake so ki fidda yaran nan daga cikin gidan nan!! In yaso zan baki numbarsa in kin fitar dasu acikin motarki sai ki kira shi ki bashi su ya tafi dasu can Orphanage home ɗin,"
Murya asanyaye hafsat tace"shikenan mommy amma ina so ki sani haƙƙinsu ba zai ta6a barin mu ba! Sai Allah ya saka musu duk wani cin zalinsu da mu kayi,!!!!!!!!!!!!!!!! tana faɗin hakan ta juya tare da shigewa cikin ɗakin,
wani irin matashin murmushi aunty babba tasa ki tare da cewa "Komai zaki ce ki ce, nidae in dae burina zai cika ba abunda bazan iya aikatawa ba ehen,"
acan ciki kuwa bayan hafsat ta shiga wuri tasamu gefen gadon ta zauna maimakon ta tashe su sai kawai tafashe da kuka mai cin rai
Sautin kukanta ne ya farkar da jahad a firgice ta tashi zaune hankali atashe take cewa "Subhanallahi Aunty hafsat meya faru naga kina kuka? Meya same ki? jahad ta tambaya fuskarta cike da nuna alamun damuwa,
Ci gaba da kukan hafsat tayi sam ta gaza cewa komai jikinta har wani jijjiga yake yi, jahad ta kuma cewa "dan Allah sister hafsat ki daina kuka, ban ta6a tunanin zanga wannan ranar ba, idan wani abu ke damunki, zan taya ki addu'a Allah ya yaye maki
jin wannan maganar ta jahad yasa hafsat ƙara sautin kukan nata, ɗagowa tayi ta kalli jahad idanunta jawur suna fitar da zafafan hawaye tace"Jahad ba saboda kaina nake wannan kukan ba, face saboda ku ! Ina tausayinku, Nasaba daku zan iya cewa akanku nafara jin tausayin wani ɗan adam aduniyar nan !!
tun da jahad taji hakan gabanta ya faɗi Rasssss !! Duk da hafsat bata fito fili ta faɗa mata kai tsaye abunda yasa ta kuka ba,
miƙewa hafsat tayi tana faman sharar hawaye tace "Ki tashi hussana ku shirya inaso zan fita daku,"
Jiki a mace jahad tace "Toh," cikin sauri hafsat ta fuce daga ɗakin,
Jahad kuwa jikinta har kerma yakeyi saboda tsoran inda hafsat zata kaisu, daker tasamu hussana ta farka daga bacci sannan ta sanar da ita cewa ta tashi su shirya Sister hafsat zata fita dasu,
Batare da sunyi wanka ba, tsaka tsami kawai su kayi acikin toilet sannan suka fito suka shirya, jahad ta zumbula doguwar riga Orange colour ta yafa mayafi launin fari akanta, ita kuma Hussana riga ce Square neck green colour, sai Skirt Ethnic maxi ta sanya ajikinta yana da dan faɗi ya bude da ƴar bazarsa, ba ƙaramin kyau su kayi mata ba, Mayafi tasamu launin skirt ɗin black colour mai ɗigon fari² ajikinsa, tayi rolling ɗinsa tamkar yadda Jahad tayi,
Kallon hussana kawai jahad keyi kallon tausayi don ita ranta yana bata cewa lokacin barinsu gidan ne yayi, yanzu kuma zasu fuskanci wata ƙaddarar !!!
lokacin da suka fito daga ɗakin hannunsu ruƙe dana juna, Aunty babba na'a falon sai faman zagaye zagaye take yi, tana ganinsu ta nufo su cikin sauri gudun kada ishaq ya farka daga bacci ya fito yagansu,
Tana ƙaraso wa inda suke tace "Ku biyo ni," sannan ta juya ta miƙi hanyar fita daga falon, bin bayanta su jahad su kayi gabansu na faɗuwa, suna fitowa daga falon a harabar gidan tuni hafsat ta fito da motarta, buɗe musu motar aunty babba tayi tana cewa "Maza ku shiga ciki, ku jira hafsat yanzu zata zo, Allah ya kiyaye hanya," ta faɗi tana faman tiƙar dariya sannan ta rufe musu motar,
Kusan minti goma sha biyar suna zaune jigum cikin motar gaba ɗayansu babu mai magana duk jikinsu yayi mugun sanyi ganin yarda Aunty babba ke faman yi musu dariya, tun daga haka suka gane cewa ba lafiya," 😳😳😳
_wannan na jiya ne da banyi ba, da Anjima zan saki next page insha Allah kuma shine, Ga masu son cigaba da karanta Littafin Abban Sojoji su tuntu6e ni ta wannan numbar (08103884440)
[9/16, 2:19 PM] 💋BOSS LADY💋: 💋💋💋ABBAN SOJOJI💋💋💋
The father Of Soldiers Story & Written by_*Boss Bature*
page 27
Fitowa hafsat tayi hannunta janye da trolley ba komai bane aciki ba fa ce kayansu jahad, ɗayan hannun nata kuma na ruƙe da basket na breakfast dinsu data haɗo masu, 😥😥😥
Tana isowa ta buɗe boot ɗin motar ta saka trolley ɗin sannan ta rufe, duk aunty babba na tsaye ruƙe da qugu tana sakin murmushi,
Bude back seat ɗin hafsat tayi inda su jahad ke zaune ta miƙa musu basket ɗin, hannu na kerma jahad ta kar6a,
Sannan ta rufe musu murfin motar, har tasa hannu zata buɗe gaban motar ta shiga ta juyo ta kalli aunty babba idonta jawur tace "Baki bani numbar mutumin ba, wanda kika ce zai kaisu Orphanage home ɗin,"
cikin sauri aunty babba ta ɗago wayarta dake hannunta, tashiga contact numbar baba alamu ta lalubo, sannan ta shiga karanto ma hafsat ita kuma tana rubutawa a wayarta, bayan ta kammala sa numbar tashige cikin motar kafin ta rufo ƙopar ta aza idonta akan aunty babba tace "Ina fata kin ji daɗi mommy, yau hussana da jahad zasu bar miki gidanki, sai ki zuba ruwa a ƙasa kisha don murna,"
tana faɗin hakan ta datse motar tare dayi mata key, ta juya sitiyarin motar tayi baya² da ita sannan ta karya kwana ta juyar da ita direct ta nufi gate ɗin gidan ta fuce da motar aguje,
Lumshe ido Aunty babba tayi afili tace "Alhamdulillah na kawar da wannan matsalar, yanzu abunda ya rage mun shine zuwa wurin boka domin gudanar da target ɗina na gaba," tana faɗin hakan ta nufi cikin gidan fuskarta washe yau ta rabu da alaƙaƙai,
sai da ta ɗan yi nisa da motar ta fito bakin titi sannan ta dakatar da driving ɗin, wayarta ta ɗauko dake ajiye agefe, Lambar baba alamu ta danna ma kira, bayan ya ɗaga ta sanar dashi kwatancen inda motarta take,
bayan ta katse kiran ta ambaci sunan Jahad da Hussana, atare suka amsa mata da "Na'am," juyo taɗanyi ta kallesu da idanunta waɗanda suka canza launi, cikin sanyin Murya tace"kun san inda za'a kai ku"?
Har suna haɗa baki wurin cewa "A'a,"
Shiru taɗanyi kafin taci gaba da cewa "Gidan marayu !!!!!!!'
Zaro ido su kayi gaba ɗayansu hankali atashe suna kallonta, hussana da tagaza jurewa tuni ta soma kuka tana cewa "Yaya Omar fa? dan Allah kar akaimu can ku bari yaya Omar yazo ya ɗauke mu mana, ni bana son mu rabu dashi,"
Murmushin takaici jahad ta saki tare da cewa "Aunty hafsat ba wai gidan marayun ke bama so ba, kawai ni so nake naji da sanin yaya Omar za'a kaimu can"?
girgixa kai hafsat tayi tare da cewa "Jahad bada sanin shi ba, kuma nima ba da son raina ba na amince da hakan, amma ina so ku sani can shine zaifi muku zama cikin salama, saboda shi kan shi ya Omar ya manta daku tun da gashi ko kira a waya