Showing 201001 words to 204000 words out of 432432 words

Chapter 68 - Abban Sojoji Book 2 Hausa Novel Complete

batasan ƴan uwanta ba,bayan ga shaidunan sun bayyana karara nacewar ƴan uwanta ne su,kome yasa haka!?

"Wai ni ina Uncle abusufyan yake ne!ko kun lura da yanayin da ya shiga lokacin da yayi tozali da Sehrish!"Khaleed ne yayi maganar yana kallon fuskar Abban nasu,
  Fawan yace"Nima nayi mamakin razanar da naga yayi lokacin daya ganta,"
  Jahan yace"ku ka sani ko kwalliyar da tayi ne,yasa ya tsorata da ganin kyawun fuskar.....'bai ƙarasa maganar ba saboda kallon da Sgr yayi mashi,tsit yayi da bakinshi,
  "Gaskiya bana tunanin haka jahan,!sae dae wani abun na daban ne yasa shi firgita,"acewar Ayaan,kowa dae da abunda yake tunani acikin ranshi,
  Marshal Omar yace"Kowa ya wuce yayi shirin sallah,kafin a fara kira,"
  Amsa mashi sukayi da toh,sannan suka kama gabansu kowa ya nufi room dinshi,jikinsu duk a mace,sun jima basuji tausayin wani ɗan adam ba kamar yarda sukaji tausayin su sehrish,sun tausaya masu sosai ganin irin halin rayuwar da yaran suka shiga,
  Bayan tafiyarsu,falon ya rage daga Abbansu sai Omar da Sgr sai kuma kanal yousouf,
   "Ni fa ina zargin Uncle Abusufyan abba!kamanninshi da yaran nan yayi yawa abun is over,komai na fuskarsu irin nashi ne!kuma tun daga kan yarda ya firgita da ganin sehrish yasa na tabbatar da cewa akwai wani abu aƙasa,bayan wannan kuma akan idona uncle abusufyan yabar wurin nan agigice jikinshi na rawa ganin ƴan uwan yarinyar nan,ya kamata muje muga a wane hali yake ciki,sannan kuma muji dalilin dayasa ya razana da ganin yaran,"!
  Jinjina kai Abbansu yayi jin abunda kanal yousouf yace,Tabbas ya yarda da maganarshi,don shi kanshi ya lura da halin da ƙanin nashi ya shiga,yana son jin meyasa shi firgita da ganin yaran!
  Batare da 6ata lokaci ba,Suka nufi ɗakin Abusufyan atare,

Lokacin da suka tura ƙopar ɗakin nashi suka shiga ciki,samunshi sukayi zaune dirshen a ƙasa gefen gado yana ta faman sharar hawaye hannunshi dafe da kanshi,sae faman sambatu yakeyi shi kadae,
Hankalinsu ba ƙaramin tashi yayi ba,musamman Abbansu,da sauri ya ƙarasa wurinshi,tare da zubewa kasa daga gefenshi yace"abusufyan meya same ka ne!meya faru!me yasaka zubar da hawayenka har haka ne?dan Allah ka faɗamun wlh hankalina ya tashi sosai........'gaba daya duk ya ruɗe ganin halin da abusufyan ke ciki,
  Daga gefen gadon Sgr da Omar suka zauna suna kallonsu,yayin da kanal yousouf yake tsaye ya goya hannayenshi asaman ƙirjinshi,turo ƙopar aka kumayi,Hajiya azeema ce tabiyo bayansu,
"Subhanallahi Meya faru ne!naga Abusufyan na kuka?wani abu ya sameshi ne"?fuskarta ɗauke da damuwa tayi maganar ayayin da take ƙarasawa ciki ta samu wuri saman stool na gaban dressing mirror ɗinshi ta zauna tana fuskantar su,
gaba daya suka haɗu suna tambayarshi dalilin yin kukan nashi,
Sai faman share hawaye yake yi,ya gaza buɗe baki yayi magana,
  "Uncle dan Allah kadaina kukan nan,duk ka sanyamu acikin damuwa,idan akwai wani abu dake damunka dan Allah ka sanar damu,koda bamu da maganin damuwar taka,zamu taya ka da addu'a akan Allah ya yaye maka ita,"Marshal omar ne yayi maganar cikin tausasa murya,
Hajiya azeema tace"Ƙanina dan Allah ka sanar damu mana,meyasa ka ware kanka anan kana kuka kai kaɗae kamar wani ƙaramin yaro?mu fa nan danginka ne wanda baka da kamarsu aduniyar nan,dan haka kada kaji komai ka faɗa mana damuwarka insha Allah,zamu nemi mafita atare,'
  ɗagowa yayi da idanuwanshi wadanda sukayi jawur suka kumbura saboda kukan da yasha ya kalli yayan nashi la66ansa na kerma yace"ƴa'ƴana yaya,Su ne damuwata,saboda su ne nake zubar da hawayen nan,na cuci rayuwarsu akan idona rayuwarsu ta wulakanta batare da na ɗauki mataki ba.........'
  Hankali atashe Abba da Azeema suka haɗa baki wurin cewa"Ƴa'ƴa kuma!wasu ƴa'ƴa kake magana akai kenan!"
  ganin yarda suka razana da jin maganarshi yasa jikinshi yin sanyi dama yasan dole suyi mamakin jin cewa yana da ƴa'ƴa,
Sgr da Omar kuwa shiru sukayi suna sauraran abunda Uncle ɗin nasu ke cewa,
 
Jin yayi masu shiru yasa ran Abban nasu 6aci a fadace yace"ba zaka buɗe baki kayimana magana ba!

Sam ya rasa ta yarda zai fara sanar dashi game da ƴa'ƴan da yake magana akai,tsoranshi karya ƙi amincewa da zancen shi,yana fargabar abunda zai biyo baya in ya sanar dasu cewa yaran nan ƴa'ƴanshi ne,

  "Kai nake sauraro abusufyan!ka sanar mun akan wasu ƴa'ƴa ne kake magana!'wannan karan a rikice abba keyi mashi magana,

  cikin sanyin murya Abusufyan yace"Yaya hossein,ina magana akan ƴa'ƴana ne,waɗanda na haifa,na haifi ƴa'ƴa batare da saninku ba...........'
A razane abbansu junaid ya miƙe tsaye yana kallonshi yace"What!!abusufyan kai da kanka kake faɗamun cewa kana da ƴa'ƴa naka na kanka!?Anya ba kunne na ne ke jiyomun ba dai dai ba,"yayi tambayar fuskarshi da alamun ruɗu acikinta, jiki na rawa abusufyan ya miƙe tare da
ruƙo hannun abban acikin nashi yace"dan Allah ka zauna yaya,zanyi maka bayanin komai,tabbas dagaske ne ina da ƴa'ƴa abba,kuma suna nan araye,jini na ne su,'
  dafe kai Abba yayi saboda wani irin jiri daya ji yana niyar kwasar shi,dakyar ya iya buɗe baki yana ambaton"innalillahi wa'inna ilaihirraji'un!abusufyan ka cuce mu Kuma ka yaudare mu ka zubda ƙimar family dinmu!ashe dama abunda ka aikata kenan shiyasa ka gudu kabar ƙasar nan!?saboda kayi ma wasu ciki kana tsoran asirinka ya tonu shine ka tattara kabar ƙasar nan!"ƙarasa maganar yayi yayin da hawaye ke gangarowa daga cikin idanunshi,abun ba ƙaramin gigita su yayi ba gaba dayansu,basu ta6a tunanin cewa abusufyan dinsu zai iya aikata wannan mummunan abun ba,

A faɗace yaci gaba da magana"ka faɗamun gaskiyar lamarin tun kafin ranka ya 6aci!tun yaushe wannan abun ya faru baka sanar mun ba!wacece ko kuma suwa kayi ma ciki har aka haifa maka ƴa'ƴa!kuma ina ƴa'ƴan suke,
  gaba ɗaya abusufyan yasha jinin jikinshi ƙoƙari yake yayi mashi bayani amma  ya kasa,

Marshal Omar ne yace"Abba,pls mubi komai asannu har mu samu uncle  ya warware mana komai,Ni ina da tabbacin cewa Uncle abusufyan bazai ta6a aikata abunda muke zarginshi dashi ba,dole akwae wani dalilin.
  Girgiza kai Abbansu ya shiga yi ranshi atsananin 6ace yace"Kabarni Kawai Omar,abusufyan ya gama da mu,bansan iya zunubin da ya aikata ba,da yasa harya gudu yabar ƙasar nan tsawon lokaci,

Amman tunda ni bazai sanar dani gaskiyar Lamarin ba, bari na kira Ammi a waya na sanar da ita abunda ya aikata,may be ita zai iya yi mata bayani tunda ni bazaka faɗamun ba!"
  Yana ƙarasa maganar ya zura hannu acikin aljihun wandon shi yana ƙoƙarin curo wayarshi don ya kira ammi,
  Cikin sauri abusufyan ya ruƙo hannunshi muryar shi har kerma takeyi wurin cewa"ya..ya hossein ka saurareni dan Allah,ina ƙoƙarin na fahimtar dakai ne,muddin ka sanar ma ammi wannan maganar zan tattara kayana nabar gidan nan ne!saboda bazata ta6a fahimtata ba,kamar yarda kai zaka fahimceni.......'
  jikin Abbane yayi sanyi ganin yarda Abusufyan ke ta faman zubar da hawayenshi,
  Sassauta muryarshi yayi cikin lallami yace"ka sanar dani Abusufyan!taya akai ka samu ƴa'ƴa"?
  Hannuwanshi duka biyun yasa ya rike kanshi da yake jin kamar zai fashe,ga wata uwar zufa da ke zubo mashi har ta jika wuyan shaddar jikinshi,sai faman girgiza kanshi yake ya rasa ta ina zai fara komae ya dagule masa,da ka kalle shi zaka fahimci bai cikin hayyacin shi,
   Kanal yousouf ne ya dan yi gyaran murya kafin yace"Abba ni ina ganin muje muyi sallah kilan uncle zai samu natsuwa yayi cikakken bayani don na fahimci kaman bai acikin hayyacin shi ma" jinjina kai Abban yayi don shima ya fahimci hakan,ya mika masa hannu tare da cewa"taso muje muyi sallah amman in muka dawo dole kayi mana cikakken bayani" daga masa kai Uncle Abusufyan yayi alamar ya amince daga haka suka fito gaba dayansu suka nufi masallaci kowa da abunda yake sakawa a ransa.

Zamu so muji yarda wannan al'amarin ya faru,taya akai abusufyan da bai ta6a aure ba ya samu ƴa'ƴa',taya akai yayi aure batare da sanin Danginshi ba?suwaye ƴa'ƴan nashi da yake magana akai,amsoshin duka wadannan tambayoyin na a bakin Abusufyan,batare da 6ata lokaci ba zamu nutsa cikin labarin da Abusufyan zai ba yayan nashi hossein da zarar sun dawo daga masallacin.

A6angaren su Sehrish kuwa,tunda azmee ta shigar dasu hosana da jahad a ɗakinta,gaba ɗaya ta takure kanta saman gado,jikinta sae kerma yakeyi ko son ganinsu bata yi,hakan ba ƙaramin raunata zuciyoyinsu yayi ba,zuba mata ido kawai sukayi suna kallonta yayin da hawaye ke zuba a fuskokinsu,a gefen gadon nata suka zauna,
  Jahad tace"banta6a tunanin cewa zakiyi mana haka ba sehrish,nayi tunanin zakiyi murnar ganinmu bayan tsawon lokaci da bamu haɗu ba,amman sae gashi kin juya mana baya,agaban mutane kika nuna cewa baki san mu b....!"
  Tunkan takai ƙarshen maganar Sehrish ta kwatsa mata tsawa tana cewa"Karki ƙara yi mun magana!ni ko muryoyinku bana son ji wlh,bansan su wanene ku ba,kawai kunzo don ku takura ma rayuwata ne..,...'
  Cikin shessheƙar kuka hosana tace"dan Allah sehrish ki daina faɗin hakan!bana jin daɗi,meyasa zakiyi mana haka?Yanzu kin manta da hosanarki?ga kuma jahad?rishi dan Allah kidaina yi mana wannan wasan,'
Hannu sehrish tasa tare da toshe kunnuwanta alamar bata jin ma abunda suke cewa........'

    Duk wannan budurin da akeyi Hayaam na kumshe aɗakinta batasan meke wakana ba,tsoranta karta fito su haɗu da Babban yaya awaje,don tasan muddin yaganta acikin gidan sai yasa an wurgar mashi da ita waje,wannan dalilin ya hana ta fitowa,

Amani kuwa har sun kammala kimtsawa ita da Amal zasu zo gidan,sai ga Abbas ya shigo gidan,a lokacin suna tsaye ita da Amal acikin falon gidan,
tarar shi tayi tare da cewa"Kai fa muke ta jira tun ɗazu mun kammala shiryawa,"
  Abbas yace"sai dai kuyi haƙuri,yanzun nan Abba ya kira ni awaya ya sanar dani cewa wani babban al'amari na faruwa agidan,inyi sauri inxo Suna jira na,bana tunanin cewa suna yin wannan walimar ma,"
  Jiki asanyaye tace"Allah yasa dae ba wani abunne ya faru ba,bari mu hakura to in komai ya dai dai ta munje,"daga haka Abbas ya shige ciki yayi abunda zai yi ya fice.
  Wannan ne abunda ya hana su Amani zuwa gidan,

Bayan sun kammala Sallar magrib,atare suka dawo a nan babban falon suka Hallara gaba ɗayansu banda Azmee da Hayaam da kuma su Sehrish,a lokacin Shima C.g Abbas ya ƙaraso gidan,kowa ya samu wuri ya zauna,Su fawan jabeer da kuma Irfan suna zaune a 3 seater,Abbansu tare da Uncle abusufyan suna zaune asaman 2 seater,Omar kuma tare da Sgr da Kanal yousouf suna xaune ne aɗayar 3 seater ɗin,Abbas da khaleed suma suna zaune asaman 2 seater,sai Aunty azeema dasu jahan kowanne na akan one seater,

Gyaran murya Abba yayi tare da kallon Abusufyan dake zaune zugudum agefenshi yace"kamar yarda ka buƙaci mu hallara gaba ɗayanmu a falo,gashi nan duk mun haɗu a wuri ɗaya kai muke sauraro,"
Nannauyar Ajiyar zuciya Abusufyan ya sauke kafin ya soma magana calmy yace"abunda yasa nace ku haɗu ku dukan ku wuri ɗaya,saboda inaso in bayyana maku cewa ina da ƴa'ƴa,kuma ƴa'ƴan nan na same su ne ta hanyar daya dace,Banaso wani ya zargeni ne da laifin aikata zina,wlh ni tunda nake arayuwata ban ta6a kusantar zina ba,ban ta6a kasancewa tare da matar da ba muharramata ba ina nufin ba matata ba.......'
  Shiru yayi na ɗan wani lokaci alamar yana nazarin wani abu,duk suka kasa kunne suna sauraron shi,kowa burinshi yaji taya akai Abusufyan ɗinsu ya samu ƴa'ƴa,kuma suwaye ƴa'ƴan nashi!?

"Shekara ashirin da ƴan kai da suka gabata,mun samu sa6ani da Ammi saboda rashin jin maganata,babu jituwa atsakanina da ita,bakomai yake haɗani da ita ba,face irin rayuwar dana taso inayi,abota da mata,na maidasu tamkar maza awurina yarda nake friendship da mata ko maza bana kulawa haka,wannan abunne ke 6ata mata rai,saboda ta tsani ta ganni tare da ƴan mata,ko in aka bata labarin cewa anganni tare da mace acikin mota,nan fa hankalinta zai tashi,a ƙarshe data rasa yarda za tayi dani shine,ta tattara mun kayana gaba ɗaya tace in koma Kano wurin ƙanwarta Hajiya Ameena inci gaba da zama acan,saboda nafi ƙarfinta ba zata iya dani ba don ta lura kaina rawa yakeyi,amma tana da tabbacin cewa in na koma wurin ƙanwarta zan shiryu in dawo dai dai,

Wannan ne farkon abunda ya rabani da gidanmu na koma wurin goggon mu da zama gaba daya,don ta gyaramun tarbiyyata kamar yadda ku su yaya hossein kuka sani,maimakon hakan sai ta sangarta ni saboda tsananin son da takeyi mun wanda ko ɗanta a wannan lokacin bata nuna mashi irin son da takeyi mun,komai nakeso shi takeyi mun,wankane kawai ba tayi mun,idan nayi laifi kuwa ko na janyo faɗa awaje rufe ido takeyi taita zazzaga masifa kuma tana sane cewa ni ne mai laifin,in mun shiga gida tayi ta lallashina tana bani haƙuri,

TUSHEN LABARIN,
Alhaji nuraddeen mai dala,hamshaƙin mai kuɗi ne kuma attajirin gaske,na bugawa a jarida,babban ɗan kasuwa ne wanda yayi kaurin suna a harkar kasuwancin saye da siyarwa atsakanin ƙasashe daban daban,haifaffen garin zariya ne,kuma yana ɗaya daga cikin Aminnan Salahuddeen,aiki ne ya kawo shi katsina kafin daga baya lokacin daya fara kasuwanci ya yanke shawarar komawa garin kano da zama saboda kasuwancinshi yafi ƙarfi acan,wannan dalilin ne yasa shi tattarawa ya dawo gaba ɗaya da zama anan kano tare da iyalanshi a katafaren gidanshi dake a unguwar Nasarawa g.r.a anan jihar kano,farkon haɗuwarshi da hajiya Amina kanwar Ammi wato goggon katsina,tun lokacin da suka je ɗaurin auren Salahuddeen da Ammi a jihar yobe damaturu,acan ya ganota ya ƙyasa,basu baro wurin ɗaurin auren ba sae da aka shafa fatiharsu su duka biyun a lokaci guda,

Yaronsu ɗaya wanda sai da sukayi aure da jimawa kafin Allah ya albarkace su dashi,ba kowa bane wannan face Dr haris babban likita,shine ɗa ɗaya tilo da suke dashi,kafin Ammi ta mallaka mata Abusufyan don tagyara mata tarbiyarshi,sae suka kasance su biyu ne ƴa'ƴan dake a wurinta,ɗanta da kuma ɗan yayarta abusufyan,tom da kuma jerry,don gaba ɗayansu basa jin magana a wannan lokacin,ƴan abi yarima asha kiɗane,atare suke fita yawon dare,sun iya zuwa club a haɗu da ƴan mata ayita rawa,zuwa wurin party kuwa koba a gayyace su ba sai sunje,wannan shine rashin jin da ammi ta tsana na abusufyan,shi dae haka rayuwarshi take baida burin daya wuce afita yawo tare da ƴan mata akashe masu kuɗi,kullum yana manne dasu,shi dai kawai yaji mace akusa dashi ba namiji ba,kuma bawai don yayi wani abu da ita ba,sam shi wannan bai agabansa,

Ana haka su Abusufyan suka samu hutun makaranta,atare da dr haris suka je kai ziyara zariya wurin danginsu,

Bayan tafiyarsu ne,Hajiya Amina da Mijinta alhaji nuraddeen suka tafi umra,dama tun kafin su tafi alhaji ya sallami mai gadin gidansu baba buzu don yaje ƙasarsu niger ya gano danginshi kafin su dawo,

Ba ƙaramin daɗi yaji ba,saboda dama atakure yake na rashin ganin ƴar shi tilo da yake da ita,kullum yana cikin damuwar rashin yarinyar a kusa dashi,saboda halin da ya barota acan,basu da kowa danginsu duk sun tarwatse ba haɗin kai,ga talauci dake damun kowannansu,ita kanta yarinyar ya barta ne a hannun matar babanshi,tunda baida kowa iyayenshi duk sun rasu,matar nan ta tsani yarinyar ta takurama rayuwarta gata irin tsoffin nan ne masu mitar tsiya,duk wani aiki yarinyar take ɗauramawa,girki,sharar gida,wanki,ɗebo ruwa,kuma ƙarama ce alokacin bazata wuce 16 years ba,

Koda baba buzu yazo niger ganin gida,zuwan bazata yayi masu bai sanar ma kowa da maganar zuwan nashi ba,saboda yana so yaba Abu mamaki kuma yaga irin farin cikin da zatayi idan ta ganshi,kwatsam yana shiga gidan ya samu matar baban nan tashi zaune saman abu ta danneta a tsakar gida,yarinyar sai ihu takeyi tana wutsil wutsil da ƙafafunta,ita kuma matar sae sambatu takeyi tana cewa"Babu abunda zai hana inƙi kasheki acikin gidan nan Abu,dan ubanki ni zakiyi ma asarar tsintsiya?kin barta a ƙasa har ruwan sama ya jiƙata baki ɗauketa ba!ko don kina taƙamar ubanki ne ke turo mana da kuɗi muna siyan kayan abinci....'
Hankalin baba buzu ba ƙaramin tashi yayi ba a wannan lokacin,ganin zai rasa ƴarshi ɗaya tilo akan tsintsiyar shara da bata wuce naira hamsin ba,ba ƙaramin fusata yayi ba,a ranar ko zama gidan baiyi ba ya ɗauki ƴarshi ya tafi da ita gidan wani amininshi,tamkar ya zubar mata da hawaye haka yaji a wannan lokacin,yarinyar duk ta rame ta fige ta ƙanjame kamar ba mutun ba,yarinyar da duk garinsu babu wanda ya kama ƙafarta a wurin kyau,tun lokacin da mahaifiyarta ta haifa mashi ita,Allah yayi mata rasuwa tabar mashi ita ƴar jinjira da ita,shi yaci gaba da kula da yarinyar,mutane sunsha zuwa suna nuna mashi kuɗi don ya bar musu yarinyar su ruƙe awurinsu amma yaƙi amincewa da hakan,saboda son da yake yi mata,

Bayan hajiya Amina sun dawo nigeria ita da mijinta,Baba buzu ya shirya tafiya tare da ƴarsa abu,babu yarda abokinshi baiyi dashi ba akan ya bar mashi Abu suci gaba da kular mashi da yarinyar a hannunsu,amma ina yace ae ƙafarshi kafar abu,bazai ƙara gangancin barinta a wurin wani ba,kwara ta kasance atare dashi,yana jin motsinta a kusa dashi,zaifi samun kwanciyar hankali,

Da daddare suka ƙaraso nigeria bayan uwar tafiyar da suka sha agalabaice suka iso cikin gidan,ruƙe da hannun Abu ya shigo cikin falon gidan,lokacin hajiya ameena na zaune saman kujera mai mazaunin mutun uku tana kallo a tv,tun da sukayi sallama ta dago ta kellesu ganin baba buzu yasa ta saki fara'a tana cewa"marhabun lale ƙaraso ciki mutumina,ashe kana kan hanya banyi tsammanin zuwan.....'bata ƙarasa maganar ba,saboda ganin yarinyar dake ruke da hannunshi,
.mikewa tayi tare da zame farin glass ɗin dake a fuskarta tace"baba buzu wannan yarinyar fa?yar waye kazo da ita,"
  bai bata amsa ba,sae da suka ƙarasa wurin kujerar da take tsaye,suka zauna kasa saman carpet,sannan ya soma magana"hajiya shannunku da dawowa,ya gajiyar tafiya,'
"Lafiyalou Alhmdulillah,"
Taƙarasa maganar har lokacin idanunta na akan abu,komawa tayi tare da zama saman kujerar sannan tace"bakayi mun bayani game da yarinyar nan ba,"Tayi maganar tana nuna Abu dake ƙankame jikin abbanta

  Fargabarsa kada ya sanar dasu cewa ƴarshi ce,suƙi kar6arta baisan inda zai kai yarinyar ba,ya kwaso yarinya ya kawo masu batare da ya sanar dasu ba,

dakyar ya iya buɗe baki muryarshi kamar zaiyi kuka yace"yarinyar wurina ce hajiya sunanta Abu,ina neman alfarmar ku taimaka mun ta zauna awurina,saboda bata da kowa acan niger,dama a hannun kishiyar babata take zaune,matar bata da imani naje na shame ta tana gallazama yarinyar nan,ban ta6a sanin abunda ke faruwa ba,sai da nayi masu zuwan bazatan nan.......'komai ya kawashe ya sanar ma hajiya ameena,
  Kamar jira takeyi ya kai ƙarshen maganar tashi,nan ta rufe shi da faɗa tana cewa"Amma baba buzu ka bani mamaki wlh,yanzu duk irin shaƙuwar dake tsakaninmu dakai,duk irin yarda muka ɗaukeka

Chapters

Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login