Showing 9001 words to 12000 words out of 432432 words

Chapter 4 - Abban Sojoji Book 2 Hausa Novel Complete

Kallon juna Ayaan da jahan su kayi sannan suka kalle ta atare suka haɗa baki wurin cewa "Wanene Sehrish kuma? Kanal yusif shima cike da mamaki yake kallon azmee jin sai faman kwala kira take yi, zuba ido su kayi don suga wanene wannan sehrish ɗin da Azmee ke faman kira, shin baƙo su kayi ne a gidan nasu ko kuwa?
buɗe ƙopa sehrish tayi gabanta na faɗuwa ta tunkaro hanyar dining area ɗin, jikinta na kerma a tsorace take tafiya,
gaba ɗayansu suka ɗago suna kallon ta tun kafin ta idasa bayyana a area ɗin da suke, bin ƙafafunta su kayi da kallo waɗanda ke sanye da ƴan silifas ɗinta na gado, sai faman kerma yatsun ƙafarta suke yi,
Time ɗin da sehrish ta idasa fitowa a raxane jahan ya miƙe tsaye, ayaan kuwa baisan lokacin da ya saki cokalin dake hannunsa ba ya faɗa cikin plate ɗin dake agabansa, kanal yusif kuwa kallon abun yake kamar a mafarki,
Bin ta suke da kallo cikin mamaki, kamar a mafarki suke kallon lamarin, ƙarasowa tayi ido a zazzare jiki na kerma, riga da wandon nan ne ajikinta , ta cire gashin bakinta, ta kuma zuba da doguwar sumar kanta har gab da waist ɗinta, ta fito asalin macen ta Tsaleliyar budurwa ƴar matashiyya,
A rude jahan yace "Azmee who's she ? daga ina ta faɗo cikin gidan nan? Da iznin wa!?
Ayaan kuwa cewa yayi "Ku kuke ganin mu bamu muke ganin ku ba ! Wannan Hurool ainin fa? daga aljanna ta gudo?
Kanal yusif sam yagaza magana bayani kawai yake jira daga wurin azmee, ita kanta azmee ta ɗan razana da reaction ɗin da suka bayar, Sehrish kuwa a gefen azmee ta tsaya tana faman zare ido,
"Azmeee Explain !!!!' jahan ya faɗi azafafe harda dakar table ɗin gabansa da tafin hannunsa,
Murya na rawa azmee tace " Kuyi haƙuri dan Allah...Am wannan da kuke gani ba kowa bane face Tukur mai aikin ku, nasan zakuyi mamakin hakan......
Dakatawa tayi ganin yarda Ayaan da kanal yusif suka miƙe atare, cike da ruɗu Kanal yusif yace "What ! Wai wane tukur ɗin ake magana ! Ba dai wannan yaron mai aikin namu ba, kina nufin dama mace ce ba namiji ba ....? Ya tambaya hankali atashe ,
Daga sehrish har azmee sun tsorata,
Hannu jahan yasa yasake bugun table ɗin abincinsu yace "Impossible bazai ta6a yiyuwa ba ! muddin kuwa hakan ta kasance dole yarinyar nan ta fuskanci hukunci mai tsanani kuma tabar gidan nan ayau ɗin nan,
Fashewa da kuka sehrish tayi saboda tsorata da maganar Jahan gashi idonsa na akanta ya zare su,
"Dan Allah ku kwantar da hankalin ku, laifi ne nasan ta aikata amma kuyi mata afwa, sam bata da niyar cutar da kowa.....' dakatar da ita Ayaan yayi da cewa "Ba wannan zancen ! Saboda ƙarfin hali irin na Yarinyar nan, tayo shigar maxa ta saje acikin mu tana mana aiki, babu sirrin mu da bata sani ba, babu irin firar da bama yi agabanta, har yawo muke yi da towel a ƙugunmu, muyi yawo da gajerun wanduna duk idonta na akai, kaf ta haddace ashe kallon mu kawai take yi,"
bil'haƙki ayaan yake kora bani, gaba ɗayansu ba komai suke ji mawa ba face yadda sehrish ta saje A cikinsu matsayin namiji na tsawon lokaci tana masu aiki, duk a tsammaninsu namiji ne ashe maca ce, tagama sanin sirrinsu saboda babu irin firar da basa yi agaban ta, sannan babu irin shigar da basa yi suna yawo duk a idonta,
Hannu Jahan yasa yana ƙoƙarin zare belt ɗin wandonsa da nufin ya jibgi sehrish saboda yafi kowa fusata, gashi dama su Mace bata agabansu balle suga kyanta ko wani abu haka don su tausaya mata,
A tsorace sehrish ta ƙanƙame kanta ta 6oye abayan aunty azmee tana faɗin "Nashiga uku ! Dan Allah aunty azmee ki basu haƙuri, kada su buge ni...zan tafi nabar musu gidan,
ture kujerar gabansa yayi gadan gadan ya tunkari sehrish zai jibge ta,
Kamar daga sama suka ji Muryar Abban su yace "Kada ka kuskura ka ta6a ta!'
Atare suka ɗago suna kallonsa kowannan su na huci,
Ruƙe yake da hannun junaid cikin nasa, yana sanye da jallabiya junaid kuma na sanye cikin riga fara da wando baki, ya tsorata da ganin halin da sehrish ke ciki gashi kuma yayi mamakin ganin ta ta bayyana kanta a matsayin mace, ga kuma jahan tsaye ruƙe da belt wato zai jibge ta,
Idasa isowa sukayi inda suke tunkan abbansu yace wani abu Ayaan yace "Daddy dama wannan yaron tukur mai aikin gidan mu mace ne ba namiji baa !!
murmushi Abbansu yasaki yana kallon su yadda duk suka zabura,
Mayar da idonsa yayi kan Yarinyar dake 6oye abayan azmee yace "Ke zonan,"
"Sehrish ki fito Abbansu na kira,"
Azmee ce ke tunasar da ita, fitowa sehrish tayi jiki na kerma ta ƙarasa inda Abbansu yake tsayawa tayi at front of him murya na rawa take faɗin "dan Allah kuyi haƙuri ku yafe mun, nasan nayi laifi wlh ni banzo da niyar na cutar da kowa ba.....'
tsawa Jahan ya daka mata da cewa "Rufe ma mutane baki kona zo nan na nakaɗa miki shegen duka,"
Abbansu yace "Ya isa haka Jahan, bana so kowa yasake magana," shiru su kayi gaba ɗayansu suna sauraron mai abban nasu zai ce,

Shin ina haroon duk wannan abun dake faruwa yana a tsaye fitowarsa kenan, gaba ɗaya ransa ya gama jagulewa mamakinsa yarda akai yarinyar ta bayyana kanta A matsayin mace bayan bai idasa cimma burinsa ba, na tsoratar da ita, Amma ganin yadda su Jahan suka fusata yasa shi jin daɗi aransa burinsa karsu amince su tada 6alli sai anyi mata horo sannan a koreta shi kuma zaiyi amfani da wannan damar wurin ƙuntata mata,

tsayawa yayi da murmushin mugunta a fuskarsa don yaga ya ƙarshen bada'ƙalar zata kaya,
Daga shi sai gajeran wando fari ajikinsa tsaye ruƙe da ƙugu, ɗayan hannunsa na ruƙe da Brush da alama ma daga toilet ya fito,

burinsa yaji mai Abban nasu zai ce,
gyaran murya Abbansu yayi sannan ya soma cewa "Na riga da nasan komai game da yarinyar! Domin junaid ya jima da sanarmun komai agame da ita, duk abunda junaid ya nuna yana so aduniyar nan koma menene shi zan amince dashi, Junaid ya nuna cewar yana son Zaman yarinyar nan agidan nan, don Haka Na AMINCE masa,!"
Cikin mamaki suke kallon abban nasu, Haroon kuwa tuni yayi wata irin raxana har Brush ɗin dake hannunsa ya faɗi ƙasa sbd jin abunda Abbansu yace,
Murmushi kawai junaid ke saki, kallonta Abban su yayi tare da cewa "Ya Sunan Ki"? Sehrish dake tsaye agabansa idonta cike tab da kwalla duk ta tsorata murya na rawa tace "SEHRISH"
Jinjina kai Abbansu yayi tare da sa hannun shi ya shafa gefen fuskar sehrish yace "Daga yau Ba sunanki Sehrish ba,"
cikin mamaki suke kallon Abban nasu, itama sehrish ɗin kallonsa take tana jira taji sunan daya canza mata, azmee kuwa Alhamdulillah kawai take faɗi aranta,
"Kinsan menene sunan ki daga Yau"? abban nasu ya faɗi yana kallonta,
Cikin sanyin murya Reesh tace "a'a".
murmushi Abban nasu yayi sannan yace "daga Yau sunanki *SEHRISH SALAHUDDEEN HUSSEIN ABBAN SOJOJI*"
😇😇😇

Sakin baki su kayi suna kallon Abban nasu

Duk wannan Abun dake faruwa akan idon SGR wanda ke saukowa down stairs jikinsa na sanye da t-shirt mai gajen hannu baƙa, sai dogon wando fari, sun bi shape ɗin jikinsa ya fito Handsome stylish ɗinsa, ya ɗaure sumar nan ta baya ba ƙaramin kyau yayi ba, a hankali yake tattaka steps ɗin cikin tafiyar nan tasa ta majiya ƙarfi, duk suka ɗago suna kallon shi................
__________________________________
🔥The Father Of Soldiers🔥*

ﻗﺼ�? ﺣﺐ ﺭﻭﻣﺎﻧﺴﻴﺔ ﺑﻴ�? ﺳﺤﺮﻳ�? ﻭﺍﻟﺠﺮﺍ�? ﺍﻟﻌﺎ�? ﺭﺍﻓﻴﺖ❤‍🔥💞💘�?

*Story & Written by*
*Hafsat Bature Muhammad*

~💋BOSSLADY💋~

*💫LAFAZI WRITERS ASSOCIATION 💫*

*Abban Sojoji part 2*

*EPISODE 5-6*


Ida sa iso wa inda suke sgr yayi idonsa yakai kan Jahan daya zare belt ruƙe a hannunsa, tunkan yayi magana jahan yayi hanxarin mayar da belt ɗinsa, mayar da idonsa yayi kan Abban nasu tare da cewa "Gm dad fatan an tashi lafiya," murmushi Abban su yasaki da cewa "Lafiya Lou son ina fata kaima haka,"
Sgr yace "Alhamdulillah," sannan ya samu wuri ya zauna saman ɗaya daga cikin dining chairs ɗin, kowa so ya ke yaji mai Babban yayan nasu zai ce, musamman haroon burinsa Sgr yace bai amince da zamanta ba, don yasan in dai yace hakan to Zaman sehrish ya ƙare a gidan,
Ita kuwa sehrish hankalinta kwance saboda tasan yarda su kayi jiya dashi haka azmee ma, gyaran murya sgr yayi kafin yace "tsayuwar me kuke yi"? Ya tambaya yana kallon su jahan Ayaan da kanal yusif, koma wa su kayi kowa ya xauna junaid ma yasamu wuri ya zauna, sai Abban nasu dake tsaye sehrish na agabansa yaci gaba da cewa "daga yau kin zama ƙanwarsu kema ƴa' ce acikin gidan nan, duk wani abu da uba keyi ma ƴarsa nima zan miki shi, kuma duk wani abu da junaid zaiyi acikin gidan nan kema zaki iya yin shi, kuma duk wanda yayi yunƙurin 6ata miki acikinsu ki sanar mun zaki ga yarda zanyi dashi,"

Zuru su kayi suna sauraron Abban nasu, sehrish kuwa murmushi kawai take saki koba komai yau tasamu Uba wanda zatayi prouding dashi a faɗin duniya,
ɗago idansa yayi ya kalli Babban yayan nasu, wanda azmee taci gaba da saving ɗinshi breakfst ya kira sunan shi "RAFAYET" amsa wa yayi da "Na'am Abba," batare da ya juyo ba ya kalle su,
Abban yace "Ina fata kaji komai ga me da yarinyar nan ? bansan ko kana da abun cewa ba" ya tambaya yana kallonsa,

kowa ya saurara don jin ta bakinsa, haroon Allah Allah yake akan Babban yaya karya amince da zamanta,
Boss man ɗin sai da ya gama sipping Coffee ɗin dake hannunsa a natse sannan yace" Umarninka Shine abun bi" amsar da ya bayar kenan, wani irin farin cikine yaci ka Abban nasu saboda shi da yake tunanin zai ƙiya gashi ya amince da duk jawabinsa kai tsaye ma yace Umarninsa shine abun bi, wato duk abunda yace game da yarinyar ya amince,
"Kufa kuna da Abin cewa"? Abban nasu ya tambaya yana kallom su, cikin sauri suka haɗa baki wurin cewa "Abba ae magana taƙare kawai tunda Babban yayan mu ya amince mu su wanene da baza mu amince ba"?
Wannan maganar tasu tasa Azmee yin ƴar dariya ƙasa ƙasa,
Jinjina kai Abban su yayi sannan yace "hakan yayi mun, sannan ko da gigin wasa ban amince wani ya cutar mun da ƴa ta ba,"
"An gama magana Abba" suka bashi amsa atare yace "Yawwa haka nake son ji, sannan ya mayar da idonsa kan Sehrish wadda ke faman sakin murmushi tayi zuru tana cizar akaifar hannunta da takai bakinta, ba kowa take tunani ba face Haroon yadda zata Zazzaga mashi rashin mutunci, dama taci alwashin hakan
Muryar Abban su ce ta katse mata tunanin nata da cewa " daughter ki zauna kiyi breakfast tare da Abban ki da kuma ƴan uwanki," ɗan zaro ido sehrish tayi jin yace zata zauna taci abinci acikinsu cikin mamaki tace "Abba anan," tayi maganar tana nuna dining table ɗinsu,
"Eh nan nake nufi" ya bata amsa sannan ya ruƙo hannunta gavan ta na faɗuwa suka samu wuri suka zauna tana gefen Junaid Abbansu kuma na gefenta sun sa ta tsakiya, Babban yayansu kuma Na a side ɗin Abban nasu, ta hannun dama yayin da suke facing Ayaan Jahaan da kanal yusif su da suke hannun haggunsu,
"Azmee ke ma ki samu wuri ki zauna A cikin mu," abban su ya faɗi yana kallonta ,
da fara'a a fuskarta tace "ngde ssae Abba, amma ni nafison a barni a iya matsayi na, nafi jin daɗin kasancewata haka, dama damuwa ta Sehrish ce gashi kuma ta samu Ƴanci ka ƴanta ta, Allah ne kaɗai zai iya saka maka, haƙiƙa kai na musamman ne ka kasance ɗaya daga cikin mutanen da ake Alfahari dasu aduniya kuma ake alfahari da Ƴa'ƴansu kowa burinsa yayi koyi da kyawawan ɗabi'unka da halayanka Abba ba abunda zamu ce sai dai Allah yaci gaba da tsare mana kai, ya tsare zuri'arka, Ya kare ka daga sharrin mahassada da maƙiyan ka, Allah yaci gaba da ɗaukaka darajarka da ta ƴa'ƴanka a faɗin duniya, kamar yadda kake faranta ma wasu Kaima Allah ya faranta maka aranar gobe ƙiyama yasa Aljanna tazama makomarka................azmee bata tsaya ba haka taci gaba da yiwa Abbansu addu'oi' dasu kansu , gaba ɗaya sunji daɗin addu'o'inta kuma dukkansu suke amsa mata da Ameen ameen,

daga bisa ni kowa ya mayar da hankalinsa ga abincin dake agabansa zanso kuka sehrish duk ta gaza samun natsuwa ba wai don bata jin daɗin kasancewarta atare dasu ba, sai don tsoran su ayaan da jahan da take yi, saboda wani irin kallo da suke mata Sam tagaza gane kallon menene wannan, dama fa su ƴa'ƴan Alexandra wuyar sha'ani ke gare su kamar uwarsu haka suke basu cika yarda da mutane ba ko kuma sake musu, junaid ne kawai mai sauƙin kai saboda kaf halayansa shigen na Abbansu ne,

shin wai ina haroon ? Ae tuni ya koma cikin bedroom ɗinsa cikin tsananin ƙunci ransa yayi mugun 6aci sai faman yawo yake a ɗakinsa cike da jin baƙin ciki aransa sai faman huci yake bakowa yafi bashi haushi ba face Abbansu da Babban yayansu saboda sune suka nuna Amincewarsu da ita, a can ƙasan zuciyarshi kuma bakowa yafi ƙuntata masa ba fa ce*JUNAID* Saboda shine silar komai daya fara sanar da Abbansu akan maganar yarinyar, dama junaid ya jima yana ci masa tuwo a ƙwarya don ya lura Yaron Abbansu yafi Son shi fiye da kowa tunda har bai iya 6oye son da yake mashi agaban kowa, Kuma ya Lura cewa Babban yayansu ya mutu akansa hakan na nufin shima Yafi Son*JUNAID* bama su kaɗai ba kowa na gidan in kana so kaga fusatar shi to ka ta6a junaid nan xaka ga tashin hankali, shiru yayi a lokacin ya koma gaban mirror ɗinsa yana kallon fuskar shi ta cikin madubi, a fili yace "saboda*Junaid* Abba da Babban yaya suka mare Ni, a gaban ƙanne na, mutun Uku da suka kasance maƙiya na acikin gidan nan muddin inaso In ƙuntata musu dole saina Cutar da *JUNAID* 😳

ya faɗi tare da sakin wani irin shu'umin murmushi yace "Haroon kenan Mai Fuska biyu ! Wasu suna mun kallon shashasha ɗan giya yayin da ni kuma nake masu kallon garori wannan Alwashi ne na ɗaukarwa kaina saina Tarwatsa farin cikin gidan nan kuma ba da kowa zanyi amfani ba fa ce *JUNAID* 👌💔

"na'am " ya amsa yana Satar kallom sehrish da ta kira sunan shi ta wutsiyar idon shi, "nifa tsoro nake ji junaid nagaza cin abincin dake gaba ba," murmushi junaid yasa ki tare da cewa "CALM DOWN your mind reesh, ke fa ynx ƴar gida ce, ki saki jikinki ki ci Abincin ki a natse," murmushi tasaki yayin da ta sa hannu cikin plate ɗin dake gabanta mai ɗauke da fried chicken taci gaba da ci, ta6e baki Jahaan yayi yana kallonta aransa yace " ƴar shisshigi da kutsu bansan daga ina aka samo wannan yarinyar ba yanzu haka bata Wuce Zariyya dama gata nan kamar Zararrriya sai faman zare ido take,' ya yi maganar yana Hura hanci kamar wanda akayiwa dole yana Cusa bugger abakinsa, Ayaan kuwa cewa yake yi aransa "ƙarfin hali irin na Ifritanyar nan kalli yadda ta wani shige tsakanin Abban mu da junaid tana cin abinci ita ga isasshiya mai walkin sa, ala dole ga ƙanwar Sojoji zaki gane kurenki ! Jibi kunnuwanta don Allah kamar na Zomo falo falo sai faman ƴan ƙefce ƙefcen ido take kamar wadda aka aza A saman kujerar lantarki......,😂

Har cikim ranta sehrish duk ta tsargu da su Twins kamar tasan abunda suke cewa aransu, Azmee ce keyi mata alamar ta kwantar da hankalinta don itama ta lura da abunda su twins ke mata, wani irin Kallon hadarin Kaji 😾😼

Tuni sgr ya bar dining ɗin dama breakfast ɗinsa shaf shaf yake yinsa gyaran murya Abbansu yayi ya kalli azmee yana cewa "idan mun kammala ku shirya ke da sehrish da Junaid saboda yi wa daughter siyayyar kayan sawa da abubuwan amfani na mata, hada ma Saloon da gyaran jiki duka komai nake so ayi mata,'
Atare Jahan da Ayaan suka ɗago suna kallon Abban nasu, shima kanal yusif abun ya basa mamaki, Sehrish kuwa murmushi kawai take saki haka Junaid daɗi kamar ya rufe sa,
Azmeee tace "To Abba Insha Allah komai za'ayi mata,"
"Ke ma hada ke, azmee siyayyar duk zakuyi," cike da farin ciki azmee tace "Mun gode sosai Abba Allah yasa ka da alkairi,"
mayar da idonsa Abban nasu yayi kansu Ayaan da jahan da kanal yusif yace "Bafa ni zan biya kuɗin siyayyar ƙanwarta ku ba, wannan nauyin ku ne, don haka kowa ya tattaro ya bada gudummuwa,

babu wasa a fuskar shi yayi maganar, shiru su kayi don baza suyi mashi musu ba, Abban nasu yaci gaba da cewa "Yusuf kai zaka biya kuɗin siyayyar kayan sawanta, Jahan kuma shi zai ɗauki nauyin kayan ado na mata da za'a siya mata, sannan Ayaan shi kuma zai ɗauki nauyin na gyaran jiki hada takalma da bags ɗin da za'a siya mata ina fata duk kunji," sam takaici ya hana twins yin magana bawai kuɗin bane damuwarsu ba sam basu da matsalar kuɗi saboda bada albashinsu suka dogara ba, Mahaifiyarsu duk ƙarshen wata tana tura masu makudan kuɗi dollars wannan ba tare da

Chapters

Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login