Showing 171001 words to 174000 words out of 432432 words
Chapter 58 - Abban Sojoji Book 2 Hausa Novel Complete
kamar tasanni itama...?
Bata ƙarasa zancen zucin nata ba,azmee ta ƙaraso tare da janyota jikinta ta rungumeta tana cewa"Sannu da dawowa kyakkyawata,ya school din?
Tayi maganar tare da raba jikinta daga na Jahad,
Zuru jahad tayi duk tabi ta dabarbarce ta rasa ganema wannan abun al'ajabin,tamkar a mafarki haka take ganin wannan ikon Allah,
"Rishi lafiya naga kina bina da kallo?kodae bakya jin daɗi ne?nayi magana baki amsa mun ba"
Cikin en ina jahad tace"am...um...lafiya lou,makaranta Alhamdulillah,'
Azmee tace"ko ke fa,shigo daga ciki na hada maki lunch ki ci,ko kya dawo daedae don na lura yau ba ƙaramar yunwa kika kwaso ba,"
Tayi maganar tare da ruƙo hannun jahad taja ta suka nufi dakin sehrish,da kanta ta buɗe mata kopa tare da shigar da ita ciki tace"ki zauna ki huta,yanzu zan haɗo maki lunch,"tana faɗin hakan ta rufe mata dakin,
Abun ya gama ɗaure mata kai,juyawa tayi tana ƙarema bedroom ɗin kallo ba ƙaramin kyau yayi mata ba,daga bisani kuma ta shiga damuwa akan wane hali hosana ke ciki,tasan cewa zasu nemeta sosai,kuma in basu ganta ba hankalinsu bazai ta6a kwanciya ba,
komawa tayi daga gefen gadon sehrish ta ɗan zauna,ya zama dole in koma gida,kada hosana tayi ta kukan rashina akusa da ita,bansani ba ko zan samu ya omar acikin gidan nan ba,ni ba komai yafi ɗauremun kai ba face yarda suke nuna kamar sun sanni,bayan bamu ta6a haduwa da kowannansu ba,to kodae dukkansu suna da mental illness ne?ta jefa ma kanta tambaya,
Turo kopar azmee tayi tare da shigowa hannunta ɗauke da tray wanda ta shirya mata lunch,ƙarasawa tayi tare da ajiye mata tray din asaman bedside drawer dinta tace"Wannan farfesun da kike gani,hajiya azeema na shirya mashi,ƙanwar abbanku da nake gaya maki,tana nan ta iso,nasan bakisanta ba,amma kin ta6a ganinta lokacin da Sgr da Omar suka dawo daga U.S kin tuna"? Fuskarta ɗauke da murmushi takeyi mata maganar,
Jin ta ambaci sunan Omar yasa jahad cewa"Ya Omar na nan"?
Azmee tace"eh,yana acikin part dinshi,amma meyasa kika tambaye shi?maimakon ki tambayeni mutumin ki Sgr"?
"Babu komai,kawai inason ganin shi ne,"ta bata amsa,
Azmee tace"ki bari idan kin kammala shan farfesun sae kije ki same shi adakin shi,'
gyaɗa kai jahad tayi tare da cewa toh,nagode sosai,bari na fara sha,
Juyawa azmee tayi tare dayi mata sallama ta fuce daga dakin,a ranta tana tunanin ko wani abu ke damun rishin ne taga duk tayi sukuku.
Zama jahad tayi tare da dauko plate ɗin dake ɗauke da farfesun,sae uban ƙamshi ke tashi,duk da tana cikin tashin hankali hakan bai hanata shan farfesun nan ba,sae da taci ta ƙoshi, sannan ta miƙe tare da shiga toilet ta wanko hannayenta,
Bayan ta fito komawa tayi saman gadon ta zauna cike da zullumin mai zai biyo baya,
_💋Boss Bature💋_
Marshal Omar na kwance saman gadonshi yayin da idanunshi suke kallon saman ceiling bakomai yake tunani ba face hosanar shi,kowane hali take ciki yanzu?taci abinci kuwa?tambayoyi iri iri ya shiga yi ma kanshi,
yana cikin wannan tunanin wayarshi dake ajiye gefenshi ta shiga yin ringing,miƙa hannu yayi tare da daukar wayar,duba mai kiran nashi yayi ganin sunan Major ya bayyana akan screen din wayar yasa shi saurin ɗaga wayar tare da karata akan kunnanshi,
Ko sallama major baiyi mashi ba saboda tsabar tashin hankalin da yake ci,
"Yalla6ai yarinyar nan fa ta 6ace,an neme ta an rasa ko'ina na makarantarsu,ɗazu osman ya kira ni awaya yake sanar dani cewa yaje ɗaukarsu a school,hosana kaɗae ya gani banda jahad,mun duba ko'ina babu ita,"
Waro ido waje Omar yayi ba arziƙi ya sauko daga saman gadon yana cewa"Major!ban fahimci me kakeson sanar dani ba!kayi mun da yaren da zangane,"
Major yace"yalla6ai,jahad ce ta 6ace a school,'
Rai a6ace Omar yace"Garin yaya hakan ta faru!taya akai Osman yayi gangancin da har ya bari jahad ta 6ace bai ganta ba!'duk inda take ku nemo mun ita in ba haka ba,ran kowa zai 6ace don bazan lamunta ba,"
Yana ƙarasa maganar ya kashe kiran,gaba daya ya rasa inda zaisa kanshi yaji daɗi,hankalin shi ba ƙaramin tashi yayi ba,tsoronshi kar ace jahad ta gudu ne don taje nemanshi saboda halin da hosana ke ciki,
Zagaye ya shiga yi acikin ɗakin nashi,zuciyarshi nata tafarfasa saboda tsabar 6acin ran da yake ciki,abubuwa sunyi mashi yawa,yana cikin damuwa sosai,ga kuma wata damuwar da major ya ƙara mashi,na 6atan jahad,
ɗago da wayar ya sake yi a hannunshi ya shiga dialing wasu numbers,
sannan ya dannama numbar kira,nan take kiran Ya shiga aka ɗaga wayar,
tun kafin yayi magana wata murya kakkaura ta karaɗe kunnanshi da cewa"We are waiting for ur command sir,"
Cikin harshen turanci omar ya shiga basu bayani akan 6atan jahad,
Ya ƙarasa maganar tare da cewa yanzun nan zan tura maku da hoton ta,banason ta ƙara 1 hour awaje,duk inda take ku nemota,adawo mun da ita gida,"
"Okey sir,'suka amsa mashi,sannan yayi rejecting kiran nasu,
sai bayan daya kashe wayar sannan ya tuna cewa baida hotonsu,amma yasan baza arasa ba wurin osman,
Batare da 6ata lokaci ba,ya kira osman awaya,bugu ɗaya osman ya ɗaga kiran cike da fargabar abunda omar zai sanar mashi,
"Osman!"
Murya na rawa osman yace"Na'am yalla6ai,"
"Inaso ka turomin hoton jahad yanzu in kana dashi awayarka,inma babu ka ɗauko mun hoton fuskar hosana,ina jiranka yanzu karka 6ata mun lokaci,'
yana kai ƙarshen maganar tashi ya katse kiran,cigaba da zagaye ɗakin yayi yana jiran osman,
within 15mins,sai ga kiran osman ya shigo,
ɗaga kiran yayi tare da karawa a kunnanshi,
On the other hand Osman yace"yalla6ai na turo da hoton,ta cikin Whatsapp dinka,"
"Okey," ya amsa tare da katse kiran,yatsun hannunshi har kerma sukeyi wurin duba whatsapp dinshi,anan yaga hoton da Osman ya turo mashi,zuba ma hoton ido yayi yana kallonshi,nan take yaji kewarta ta kama shi sosai,hoton hosana ne Osman ya ɗauko mashi,da alama sabon hotone yayi mata da wayarshi,ko uniform dinta bata cire ba,fuskarta da alamun hawaye saboda kukan da tasha na 6atan Jahad,
Lumshe idonshi yayi tare da buɗesu akan hoton yana ƙare mashi kallo,a hankali ya furta"I love u so much hosana,nayi missing ɗinki sosai,kamar nayi hauka,nashiga damuwa sosai akan rashin sanyaki a idona,bazan iya jurewa ba hosana,kina buƙata ta a kusa dake,zanzo don na lallashe ki nasan zaki shiga damuwa sosai akan rashina da kuma rashin jahad akusa dake,
Tura masu hoton yayi sannan ya kira major awaya ya sanar dashi cewa ya jira shi a waje,gashi nan fitowa,
Yana kammala yin wayar cikin sauri ya fito daga part ɗinshi,ya sauko downstairs,da sauri da sauri yake nufar hanyar fita daga main palour din,
yana ɗaga ƙafarshi zai fita yaji an ambaci sunan shi"Ya Omar,"
gabansa ne yaji yayi wani irin bugu,aranshi yace"wannan ae muryar Jahad ce,
da saurin gaske ya juya tare da kai idanunshi wurin da jahad take tsaye sanye cikin uniform tana kallonshi,fitowarta kenan daga bedroom din sehrish,cikin sanɗa take tafiya zata gudu daga gidan,kwatsam ta hango shi sai faman sauri yake yi zae bar gidan,
Kanshi ya gama ɗaurewa binta yayi da kallo gaba ɗaya ya rikice aranshi ya shiga tunanin cewa anya ba kunnan shi bane suka jiyo mashi muryar jahad!wannan ae yarinyar gidansu ce sehrish,muryarta ce tayi mashi gizo yaji kamar ta jahad,
Murmushi ya saki tare da nufarta yana cewa"Sister har kin dawo daga school ɗin?ya karatun naku,ina fata kina mayar da hankali ko?
Kamar zatayi kuka tace"Ya Omar,Jahad fa ce! Nice jahad,ya Omar meyasa ka tafi kabarmu,"!
Zaro ido waje Omar yayi cike da mamaki yake kallonta, muryar shi na rawa yace"Jahad!dagaske kece kodae kunnena ne ke jiyemun ba dae dae ba"?
fashewa tayi da kuka tare da ƙarasawa wurinshi ta kwantar da kanta asaman ƙirjinshi tana cewa"Ya omar dama kana nan,da ranka da lafiyarka amma kadaina zuwa wurinmu?meyasa ya Omar?bakasan halin da muka shiga ba ni da hosana,na rashin ganin ka,'
tashin hankalin da ba'a sama shi date,
ruko hannunta Omar yayi tare da janta suka shiga cikin wani corridor inda ba kowa,sannan ya kalle ta cike da mamaki yace"Jahad!nagaza yarda cewa kece!taya akai kikasan gidan mu har kika zo?
cikin shessheƙar kuka tace"bani na kawo kaina ba,kawo ni akayi,wannan ƙanin naka junaid,wanda ka ta6a nuna mana hotonshi nida hosana a gida,shi ya ɗaukko ni daga school ya kawo ni gidan nan,bansan meyasa ya ɗauko ni ba,ya nuna kamar yasanni bayan bamu ta6a haduwa dashi ba.....'
Tun kan ta ƙarasa maganar Omar yace"subhanallahi!an samu matsala,junaid yayi kuskuren ɗauko ki jahad,Yarinyar gidan nan yaje daukowa a school,da yake kuna kama da ita sosai,komai na fuskarku iri ɗaya sak,shiyasa ya ɗaukko ki amaimakonta,'
mamaki ne ya kama jahad jin abunda Omar yace,sae lokacin ta tuna da sunan da Junaid ya dinga kiranta wato Reesh,taya akai suke kama da yarinyar gidansu har kanin nashi ya gaza banbantasu!" ta jefa ma kanta tambayar da bata da amsarta,
"Jahad,muje na sauke ki gida,in yaso sai mu ƙarasa tattaunawa acan,"
Ya ƙarasa maganar tare da fitowa ruke da hannunta suka fice daga cikin babban falon,anan waje ya samu Major tsaye jingine da mota yana jiranshi,
Koda ya ganshi ruƙe da hannun jahad mamaki ne ya kamashi,dama shi bai ta6a ganin Sehrish ba,tunda ba shiga ciki yake yi ba,basu ta6a arba da ita ba,
Fuskarshi dauke da murmushi yace"Sir!anganta kenan"?
Omar yace"eh,ba rabon musha wahala,wai junaid ne ya ɗaukota daga school shi duk atunanin shi wannan yarinyarce ta cikin gidan nan,da yake kamanninsu iri daya sak,'
major yace"ikon Allah,amma ni ban ta6a ganin yarinyar ba,'
ya ƙarasa maganar a yayin da yake buɗe masu mota suka shige ciki,sannan ya tashi motar yabar gidan ɗauke dasu,
_💋Boss Bature💋_
A 6angaren sehrish kuwa,tana cikin tsayuwar nan agefen titi tana jiran zuwan junaid,sai ga motocin waɗannan fusatattun sojojin da Omar ya turo don su nemo mashi jahad,ae koda sukayi arba da sehrish,suka duba hoton da Marshal Ya tura masu suka ga iri ɗaya fuskar,sae ransu ya basu cewa itace yarinyar da Omar yace su nemo mashi,
Da sauri suka tsayar da motocin nasu tare da diddirowa daga saman motocin tamkar wasu zakuna haka suka tunkari sehrish,
Kamar ance ta juya,idanunta sukayi arba da waɗannan sojojin dake tunkararta hannunsu ruke da bindigu,bakomai ne ya fado mata a ranta ba face Ƴan boko haram da ƴan bindiga daɗin dake ta sace mutane agari,
ja da baya tashiga yi gabanta na faduwa
maimakon suyi mata magana cikin daɗin rae sai suka daka mata tsawa tare da cewa"ke zonan"!
Aikuwa a firgice sehrish ta watsa da gudun gaske ta saki jakar makarantarta ƙasa,bin ta sukayi da gudun gaske,tana gudu suna bin ta tamkar zata tashi sama,
yarda kasan wadda taci ƙafar kare haka ta dinga gudu,ita kanta batasan inda ta dosa ba,gudu kawai takeyi,
adaidai nan su Omar suka ƙaraso gidan uncle Abusufyan,Wayarshi ta shiga ruri,cikin sauri ya fiddota daga cikin aljihun wandonshi,yayi picking call ɗin tare da kara wayar a kunnanshi yayi sallama,
Muryar ɗaya daga cikin sojojin ce yaji yana cewa"Sir,munga yarinyar da ake nema,amma taƙi bari mu kama ta,'
Hankali tashe Omar yace"Kada ku bari ta kufce maku,kuyi ƙoƙari ku kamota,kuyi mata magana cikin sanyin murya,saboda yarinyar tana da tsoro sosai,kun firgitata ne shiyasa ta gudu,
"Okey sir,ya amsa mashi tare da katse kiran,
"Yalla6ai meya faru ne"!
Cike da takaici Omar yace"Major,an samu matsala!sojojin dana tura don su nemo mun jahad,sunyi arba da yarinyar gidan mu,dama na faɗa maka cewa kamanninsu sak iri ɗaya,ɗazu nace ma Osman Ya ɗauko mun hoton fuskar hosana,saboda in tura masu suyi amfani dashi wurin nemo min jahad,to da wannan hoton su kayi amfani wurin nemanta shine Allah ya haɗasu da ita yarinyar da junaid yayi musanya da jahad,'
Tunda yasoma magana jahad ke kallonshi cike da mamakin wannan wani irin kamanni ne,dayasa har ba'a gane banbancinsu!?
Major yace"Amma nayi mamaki yalla6ai!wannan wata irin kamanceceniya ce atsakaninsu da har ba'a iya bambanta tsakaninsu"!
Omar yace"nikaina major abun ya jima yana ɗaure mun kai wlh,da farko nayi tunanin cewa saboda ƙaunar da nakeyi ma su hosana ne yasa nake ganin fuskarsu akan fuskar yarinyar,amma yau da junaid ya dauko jahad a matsayin ita yarinyar,sai na tabbatar da cewar ba gizau bane,tabbas kamanninsu ne ɗaya!
Major yace"abun mamaki abun al'ajabi!yalla6ai kada kace na cika ka da surutu,dan Allah yaya kuke da ita yarinyar?ko ƴar wurin uncle ɗinku ce,' ya ƙarasa maganar adaedae lokacin da yayi parking ɗin motar a cikin gidan Abusufyan,
murmushi Omar yayi tare da cewa"ƴar aikin gidanmu ce,sunanta Sehrish! Yarinyar tana da kirki sosai shiyasa Abbanmu ya mayar da ita tamkar ɗiyarshi,yanzu amatsayin kanwarmu take............'
Waro ido waje Jahad tayi cike da tsananin mamaki ta furta"SEHRISH!!!!!!!!!!!!!!!!"
juyawa Omar yayi yana kallonta jin yarda ta ambaci sunan kamar tasanta,shima major juyowa ya danyi daga zaunen da yake a front seat din suna kallonta,
"Jahad kin santa ne!"?
Muryarta na kerma tace"Ya...Omar...Bansan ko ita bace ba,amma akwai ƴar uwarmu da muka jima muna nemanta,kamanninmu sak iri ɗaya,Mu ƴan ukune dani da hosana da kuma ita,Sunanta Sehrish atare aka haife mu,ciki ɗaya muka fito tare da ita,arana ɗaya kuma a lokaci ɗaya.......'
Kallon juna Omar da major sukayi cike da mamaki suke sauraronta,sae da takai ƙarshen maganarta,sannan Omar yace"Dama ke da Hosana ba twins bane!!!"?
ɗaga mashi kai tayi alamar eh,tace"WE'RE TRIPLET".
Wannan shirin da kuke karantawa ba ammasco bane suka ɗauki nauyin kawo maki shi ba,Boss bature ce da kanta,ta shirya kuma ta gabatar,😂
Idan har kinji daɗin wannan update ɗin,kiyi following din acct dina a tiktok😍😂ga link can na bada daga sama
*SANARWA SANARWA*💃💃💃💃
*ME TAKEN NA AMARYA HUTAA$$*
*MUNA FARIN CIKIN SANAR DAKU CEWA MUNA BADA HAYAR KAYAN AMARYA(WEDDING GOWN), KAYAN BRIDAL SHOWER, KAYAN BIRTHDAY PARTY, KAYAN FITAR SUNA, SANNAN MUNA BADA HEAD AND SHOULDER, MUNA DA POSS, MUNA ALKYABBAR KAI AMARYA KO TARON WALIMAR SAUKA, MUNA DA KAYAN FULANI FARARE NA YARA DANA MANYA MUNA DA NA AMARYA BLUE BLACK, SANNAN MUNA GYARAN JIKIN AMARYA DA UWARGIDA CIKIN KWANA UKU CAKAL ZAKIGA KIN KOMA TAURARUWA MAI WALWALI. MUNAYIN TURARUKAN WUTA DA HUMRA DA KOLACCAR, KOWANNE KALA KIKE BUKATA AKWAI CIKIN FARASHI MAI SAUKI.*
*LOCATION KANO*
08062073990
Ina kuke mata hamshakai wayanda suka amsa sunan su wajen mazajen su ina mata masu son qamshi shin ko kunsan tsafta bata tafiya seda qamshi ina masu son turare mai riqon gida tareda qamshin shi mai sanyaya zukata mardie collection tazo muku da dadadan turarukanta masu lasting riqon gida harma da jiki ku tuntube mu da nmb kamar haka 08136666994 inda zaku samu kaya kamar haka
Wadrobe balls
Madarar kulleccham
Vaseline kulleccham
Kajiji
Halut
Couscous
Khumrah
Da dai sauransu harda abin wanke toilet yayi tas komi dafe warshi wato BETHALEX METAL ku garzayo kar ayi baku
Ina kuke mata hamshakai wayanda suka amsa sunan su wajen mazajen su ina mata masu son qamshi shin ko kunsan tsafta bata tafiya seda qamshi ina masu son turare mai riqon gida tareda qamshin shi mai sanyaya zukata mardie collection tazo muku da dadadan turarukanta masu lasting riqon gida harma da jiki ku tuntube mu da nmb kamar haka 08136666994 inda zaku samu kaya kamar haka
Wadrobe balls
Madarar kulleccham
Vaseline kulleccham
Kajiji
Halut
Couscous
Khumrah
Da dai sauransu harda abin wanke toilet yayi tas komi dafe warshi wato BETHALEX METAL ku garzayo kar ayi baku
It's not just good ...it's finger linking good faster than fast food, better fine dining.
Snack
Awarah
Farah
Zobo
Samosa
Cup cake etc
Contact me 09063302182or 09012179727.
*💋Boss Bature💋*
Join this link to follow my tiktok acct👇
https://www.tiktok.com/@boss_bature?_t=8WKx0lm4jaP&_r=1
قصة حب رومانسية بين سحريش والجراح العام رفايت💋💘❤🤍❤💕💖
Abban sojoji paid book ne,ga duk maison karanta cigabanshi zai biya 300 ne za'a tura mashi nabaya har inda muka tsaya,ga mai buƙata direct zaiyi mun magana ta whatsapp ɗina 08103884440, pls banda phone calls,Mijina ya hana ana kira na awaya🤭🤫
❤🤍❤
Gaba ɗaya farin ciki ya lullu6e Marshal Omar da kuma major,tunda su kaji bayanin Jahad suka tabbatar da cewar ba shakka Itace ƴar uwartasu da take magana akai,
"Jahad,wannan maganar ba anan ya kamata muyi ta ba,mu shiga daga ciki"
buɗe motar Omar yayi tun kafin major ya buɗe mashi,fitowa jahad tayi itama,sannan shima major ya fito,duka dae a tare suka ɗunguma izuwa cikin gidan,har lokacin jikin jahad rawa yake yi,saboda tsabar doki da kuma zumuɗin ganin cewa Sehrish ce yarinyar da Omar ke magana akai,
Lokacin da suka shiga cikin palour ɗin atare,hosana na a kwance saman 3 seater,tasha kuka harta gaji shine ta ɗan kishingiɗa nan,bacci ya kwashe ta, ko uniform din bata cire ba,bin ta da kallo Omar yayi bakomai ya faɗo mashi a rai ba,face abunda yayi ƙoƙarin aikata mata,tausayinta ne ya kama shi sosae,tsayawa yayi atsaye ya zuba mata ido ko kyaftawa baiyi,
"Ya Omar,ka zauna mana,"muryar jahad ce ta katse mashi kallon da yake ma hosana,
Wuri ya samu saman 2 seater ya zauna,jahad kuma ta zauna asaman 1 seater,mayar da idonshi yayi kan major ganin ya tsaya daga tsaye yace"bismilllah mana,ave seat," ya nuna mashi gefen shi,murmushi major yayi tare da ƙarasawa ya zauna daga gefen Marshal,
"Jahad,inaso kiyimun bayani sosai yarda zan fahimta game da ƴar uwarku,taya akai kuka rabu da ita har tsawon wannan lokacin'? Omar ne ya jefa mata tambayar,gaba ɗaya suka zuba mata ido suna sauraron jin abunda Jahad zata ce,
"Ya omar ba da son ran mu muka rabu da ita ba,ƙaddara ce ta rabamu da ita,amma muna son junan mu sosai.....'dakatawa tayi da maganar yayin da idanunta suka cicciko da kwalla,
Anatse taci gaba da magana"ƴar uwarmu tana son mu sosai,tasha wahala akanmu,a lokacin baya Dani da hosana an ta6a kwantar damu asibiti,za'ayi ma hossana aiki,ana neman kuɗi kusan dubu ɗari tara da za'ayi mata aikin,bamu da ko sisi,bamu da mai taimakon mu sae Allah,mu kaɗae muke rayuwarmu tare da wata tsohuwa wadda take ruƙon mu a wurinta,wannan dalilin ne yasa sehrish ta nemi aikatau,don ta