Showing 78001 words to 81000 words out of 432432 words

Chapter 27 - Abban Sojoji Book 2 Hausa Novel Complete

sam bakinta yaƙi rufuwa don murna, ita kanta jahad bakinta a buɗe don murna fararen hakoran nan nata kamar gonar auduga, adai dai bakin gate ɗin major ya tsayar da motar sannan ya danna horn da ƙarfin gaske,
  sai gashi an buɗe masu gate ɗin ta ciki, ba kowa bane face abokin Major ɗan leƙen asirin shi, acikin gidan ya kwana saboda omar ya dauke shi aiki, bayan alherin da yayi masa na kyautar mota sabuwa mai kyau da tsadar gaske, ga kuma uban salary daya yanka masa,😇
   A hankali major ya shigar da motar cikin gate ɗin ɗan dagatawa yayi da driving ya zuge glass ɗin motar ya kalli osman yace "Shege mutumina, ka ga yarda ka canza jiya izuwa yau har wani haske ka fara? Cike da zolaya yayi maganar,
  Dariya Osman yayi tare da cewa "ba dole kaga canji ba,an gaya ma yin karin kumallo da farfesun kaza wasa ne? mutun ya kwana a ac,sannan yayi wanka acikin kwami haba ae dole ma ne in canza," 
  gaba ɗaya suka fashe da dariya jin abunda yace,
   Major yace "nifa wasa nake maka malam, taya zaka canza kawai daga jiya zuwa yau don ka kwana a ac, kayi breakfast da farfesun kaza? Nace sannu ko uban son banza ae sai nan da irin one month haka,nan zamu ga canji,
  Murmushi osman yayi tare da cewa " ka shiga ciki ka sauke su,in ka dawo zamuyi magana dakai, akwai labari mai daɗi,"


�?


   Major yace "okey bari nazo," yayi maganar tare da sauke glass din motar ya wuce dasu ciki, adai adai stairs ɗin da zai sadaka da main palour ɗin gidan ya sauke su,
   Buɗe motar Camila tayi ta fito, sannan suma su jahad suka fito daga ciki suna ƙarewa katafaren gidan kallo ya haɗu iya haɗuwa abun ba'a magana, Omar yasa an canza mashi komai nashi an ƙara ƙawata gidan sosai,
   gaba dayansu sun ƙame suna kallon haɗuwar gidan, ganin basu da niyyar shiga daga ciki yasa major cewa "let's go in pls," 
  Cikin rashin sani jahad ta take ƙafarta ba don komai ba sai don hankalinta daya tafi wurin ƙarewa gidan kallo,ƙara tasaki tana yarfa hannu tana faɗin "wash Allah na," jin haka yasa camila tayi saurin dawowa ta inda suke, ta taimaka mata wurin yin tafiya don su shiga ciki,
Major ne yayi masu jagora su kuma suna abayan shi, har suka shiga cikin haɗaɗɗen jigunannan falon,nan fa suka baza ido suna kallon haduwarshi, wasu irin matsiyatan royal sofa set ne acikin sa masu numfashi ɗunɗuma ɗunɗuma a jere launin su brown colour,ga wasu set na Cushions Jere asamansu difference colour,duk gasu nan ba ƙaramin ƙawata kujerun su kayi ba, daga tsakiya wani ƙayataccen table ne legs dinshi brown ne, while daga saman glass ne, an ajiye flower asaman shi, ga fruits basket mai dauke da kayan mar mari, ba komai yafi tafiya da hankalin hossana ba face tanƙameman kwan filitar dake bama ɗakin haske tamkar zai faɗo ma mutun akai haka yake, sai kuma tv stand din dakin faskekiyar plasma ma ce mai dauke da speakers na jin sauti, ga wani telephone table dage a gefe, bari dae in taƙaice maku zance komai wannan da kuka sani a palour an zuba masu shi, 
  Sai faman yarfa hannu hossana take yi, yarinya fa takusa zauce wa ganin irin gidan da yaya Omar dinsu ya gwangwaje su dashi, wani abun ma sai mun shiga bedroom,
   Jahad kuwa murmushi kawai take saki tana bin ko'ina da kallo,ita kanta Camila gidan ba ƙaramin burgeta yayi ba komai tsaf a natse ba tarkacen hauka,
   Can dae hossana tace "Allah yasa ba mafarki nake yi ba,dan Allah koma mafarki nake yi jahad kada ku tashe ni," ta fadi tana faman hadiyar yawu,
Dariya su kayi gaba ɗayansu, Major yace "wannan zahiran ne ba mafarki ba ne, kaɗan daga cikin irin son da ya'ya omar dinku yake yi maku kenan,zai iya yin komai akanku more than u think, ni dae fatana agare ku shine ku kasance masu yi mashi biyayya, ku bishi sau da ƙafa kada kuyi amfani da son da yake yi maku wurin karya mashi zuciya,ko ku ce zaku canza halayyarku saboda wata dama da kuka samu, yanzu lokaci ne da zaku more rayuwarku bayan duk wahalar da kuka sha," 
  Sosai major yashiga yi masu nasiha, duk sun kasa kunne suna sauraronshi,sannan kuma suna amsa mashi da insha Allah,
  Bayan ya kammala daga ƙarshe yace "ku samu wuri ku zauna mana,nasan kuna jin yunwa yanzu zan sa ayi maku oder na abincin da zaku ci, sannan ga bedroom nan zaku iya shiga ciki ku huta,"
  A natse suka ƙarasa tare da samun wuri suka zauna fuskar nan fa awashe,
  Mayar da idonshi yayi kan Camila yace "zamu tafi tare ne? Na sauke ki a asibitin ko kuwa,"
  cikin sauri tace "no i will stay here wit them,cos i ave done my work bani da sauran duty till tomorrow,"
  Murmushi kawai major yayi sannan yace "okey," sannan yasa kai ya fuce,
A jiyar zuciya ta sauke tare da samun wuri itama ta zauna, bayan ta ajiye jakan kayan data zo da ita,
  kallon juna suka shiga yi suna murmushi,yanayin iskar falon badae daɗi ba yadda sanyin ac ke ratsa sassan jikin mutun,
   Ganin sun zauna shiru yasa Camila cewa "ba ku buƙatar shiga daga ciki ne? ta tambaya tana kallonsu
  Jahad ce tafara cewa "inason nayi wanka, hossana ma tace "nima," 
  tashi camila tayi tare da cewa "mu shiga daga cikin ɗakin to, nima inason nayi wankan," tayi maganar tare da ɗaukar jakar kayanta,
  gaba tayi suka bi bayanta ɗaya daga cikin bedrooms ɗin suka tunkara, ƙoparsa a rufe take amma bada key aka datse ta ba, hannu tasa ta tura nan take ƙopar ta buɗe, shiga ciki su kayi atare,
haɗaɗden bedroom mai ɗauke da tafkeken gado fankacece, yaji lumbutsetsiyar katifa lallausar gaske ga wasu matassan kai masu laushi asama an jera su, irin gadon da kana hawa saman shi ko bakayi niyyar yin bacci ba nan take zai ɗauke ke saboda daɗinsa 🥱 an gyare komai an shimfiɗe shi da bedsheet,side by side na gadon akwai side drawers, masu ɗauke da lamps, 
daga can ɗayan bangaren ɗakin kuwa wurin Closet dinsu ne, ga wani haɗaɗɗen Dressing mirror an cika masu front dinshi da kayan make up da tsadaddun mayuka na jiki, komai an sanya masu, jerin wurin takalmansu,hand bags da sauran abubuwa da dama ba abun da omar yabari komai ansa masu,
   jahad ce tafara shiga toilet ɗin don a ƙagare take da tayi wanka,lokacin da ta shiga cikin toilet nan fa taga zallar haɗuwa ta jima tana bin ko'ina da kallo kafin daga bisa ni tayi wankar daker tare da yin alwala saboda in an kira sallah tayi, fitowa tayi a hankali waist dinta daure da towel mai ɗan tsayi wanda ta samu acikin toilet ɗin, hannunta na ruƙe da doguwar rigarta da ta cire, samun su tayi zazzaune daga gefen gadon suna fira da hossana da Camila,
  Ganin ta fito yasa camila tashi ta shiga toilet ɗin,
a cikin laundry basket ta turo rigar, sannan ta ɗan juya ta kalli hossana dake ta faman lumshe ido alamar bacci tace "karfa kiyi bacci don na son halinki, ki bari kiyi wanka ke ma," 
  Murmushi tayi kafin tace"ae bazan iya bacci ba jahad, saboda gani nake kamar in na kwanta zan farka na ganni a gidan wannan matar da ta azabtar damu,nakasa yarda cewa wai mune acikin wannan katafaren gidan nan mu kaɗai abun mu,gsky yaya omar ba ƙaramin ƙaunarmu yake yi ba," 
   Jahad tace"nikaina ina mamakin hakan hossana,ashe akwai wata rana da zato mana irin wannan,mun samu yaya mai son mu tamkar ƙannensa duk don saboda mu ya Omar yabar komai nasa don ya ceci rayuwarmu,har yanzu ina mamamkin hakan hossana, yaya omar ya sanar dani cewa ɗan uwanshi yana kwance rai hannun Allah babu tabbacin cewa zai rayu,amma a hakan ya tsallake shi yazo wurin mu wannan wane irin mutun ne?samun mai iri Kyakkyawar zuciyarshi zaiyi wuya a faɗin duniya
(shiyasa Hafsat bature take kamu) 🙄
   ta yi maganar ne a lokacin datakai wurin closet tana neman ta inda zata buɗe shi,tana aza hannunta a jikin closet din nan take doors din dake jiki suka zuge da kansu, har sai da jahad ta ɗan tsorata tayi baya,tasowa hossana tayi itama tana kallon wurin kayan nasu, yadda suke tagwaye haka omar yasa aka jera masu komai kala biyu, jerin wurin pyjamas ɗinsu daban, jerin wurin dogayen riguna daban,jerin wurin jeans da t shirt daban, ga jerin under wears shima daban, komai nasawa ajiki an zuba masu shi,har sun wuce iyaka,
  "jahad har naji inason nayi wanka wlh,saboda in canza kayan jikina," acewar hossana dake ta faman yarfa hannu tana kallon kayan,
  Hannu jahad tasa tare da curo wasu pakistan masu kyan gaske,tana shafa jikinsu tunkan tasa har ta gano kyan da zasu mata, 
     a gefen gado ta ajiye su, sannan ta koma gaban mirror tana shafe jikinta da ɗaya daga cikin mayukan da tagani ajare, bayan ta kammala ta kuma feshe jikinta da turare mai ƙamshin gaske,
   Sannan ta dawo ta tsaya a gefen gadon tana zura kayan ajikinta, duk hossana na can tsaye wurin closet ɗin tana ƴan ta6e ta6e,ji take tamkar tabi kowannansu ta gwada ajikinta, 
  Bayan jahad ta gama kimtsawa cikin pakistan din komawa tayi gaban mirror tana kallon jikinta,riga ce mai dogon hannu har guiwar ƙafarta sai wandon burgujeje irin nasu,ta yafa mayafin asaman kafaɗarta, sumar kanta kuma ta zubo a bayanta, murmushi kawai takeyi tana kallon kanta a cikin mirrow,
  Muryar hossana ce ta katse ta da cewa"kinyi kyau sosai jahad saina ga kin koma mun tamkar ketrina kef," 
    Jahad tace"sannu shugaban makaryata ni bada ketrina nake kama ba sai dae helen,oumma tace kamannin mu sak irin nata,' tayi maganar tana gyara gefen gashinta da hannunta,
  Hossana tace"wacece helen kuma"?
  "Ƴar film ce mana ta ƙasar ethiopia," Jahad ta bata amsa atakaice, kafin hossana ta ƙara cewa wani abu, sai ga Camila tafi to daga toilet din daga ita sai ɗan pant da bra, cikin sauri suka sanya tafukan hannayensu tare da rufe fuskokinsu cikin jin kunya,
  tsayawa tayi tana kallonsu cikin mamaki take cewa"why are u hidding ur face pls? Can i know
  Jahad tace"mun ji kunya ne," 
  Murmushi camilla tayi tare da girgiza kai tace"kuna da kunya sosai,in dae haka ne kam ba zaku iya rayuwa a ƙasar mu ba," 
   "Wata ƙasa ce"? Hossana ta tambaya,
  Camila tace "Mexico,"
Jinjina kai tayi tare da cewa"ni ko sunan ƙasar ma ban ta6a ji ba gsky...."jahad ce ta katse ta da cewa "hossana zoki wuce kije kiyi wankan kema," 
Amsa mata tayi da toh sannan ta wuce cikin toilet ɗin,
  Ita kuma jahad ta kama hanyar fita daga ɗakin har lokacin fuskarta na rufe da tafin hannayenta, abun sai ya ba camilla dariya sosai,
  Sai da ta fita daga bedroom ɗin sannan ta soma sauke ajiyar zuciya, shiga cikin falon tayi, tana ƙare masa kallo, zagaye shi ta shiga yi tana tatta6a dogayen curtains ɗin dake kewaye dashi,
   Sallamar Osman ce ta dakatar da ita, cikin sauri ta amsa mashi da wa'alaikum salam,sai da ya fara tambayar iznin shiga daga ciki, ta amsa mashi sannan yasa kai cikin falon,
   Hannun shi na ruƙe da manya ledoji na abincin da yayi masu oder a restaurant,yarda yaga jahad ta kimtsa tamkar ba ita bace ya gani  acikin daji ba sume cikin ciyayi,ba don akwai dressing na ciwo a forhead dinta ba, da bazai iya shaida taba, 
.murmushi kawai yayi tare da miƙa mata ledojin hannun shi, cikin sauri tasa hannu ta kar6a tana yi masa godiya,
  Har ya juya zai fita sai kuma ya juyo ya kalle ta yace"pls game da abunda ya faru da ku a gidan yayan Omar,wurin matar yayan shi kada ku sanar dashi komai don nasan zai tambaye ku ne,
  Murmushi jahad tayi tace"insha Allah ba zamu sanar mashi ba," 
  "Yawwa" ya faɗi tare da juyawa yasa kai ya fuce,
   Ajiyar zuciya ta sauke tare da ajiye ledojin a saman table,tana jiran su kammala kimtsa wa su fito suci atare,
   Goya hannayenta tayi a ƙirjinta tana faman sakin murmushi,bakowa ne ke faɗo mata aranta ba face yaya Omar dinsu,ta ƙosa ta sashi a idonta saboda tayi mashi godiya sosai,kuma tayi missing din wannan kyakkyawar fuskar tashi,
   tana cikin wannan tsayuwar sai ga Camila ta fito fes abunta har ta canza kayan jikinta,v neck shirt ce ajikinta fara sai wando jeans, ta ɗaure sumar kanta da ribbom,fuskarta asake ta ƙaraso tare da samun wuri saman 3 seater ta zauna tana kallon jahad tace"kina so ciwon naki ya dawo sabo mu koma asibiti gobe ko?
  Girgiza kai jahad tayi tare da cewa"a'a bansan na take ta bane,ciwon bai mun zafi yanzu ina ji kamar naji sauƙi ma," 
   Tace "duk da haka yakama ki kula just in case," 
  Amsa mata tayi da toh sannan tace "ga abinci nan,an aiko mana shi," ta fadi tare da ƙarasawa wurin table ɗin ta matsar mata dashi kusa da kujerar da take zaune,
   Sannan itama ta samu wuri ta zauna a kusa da ita,hannu camila tasa ta buɗe ledar ta farkon,kayan ciye ciye ne gasu nan chips, bugger, shawarma da sauran wasu tarkacen, ɗayar ledar kuma da ta bude masu fried meat ne (tsiren nama) mai yawan gaske yaji kayan haɗi sai ƙamshi yake yi,
  Dole ne su buƙaci plate don haka jahad ta tashi tare da cewa "bari na ɗauko mana plate," camila tace "plate yayi kaɗan tray zaki samo mana," 
Amsa mata tayi sannan ta tunkari doors din dake a cikin falon tana neman kitchen babu alamar kitchen na a wurin,
  "Ki duba down stairs baza arasa acan ba," acewar camila,
  Cikin sauri jahad ta hau benen da zai sauke ta a dowm stairs tana sauka cikin sittingroom din ta hango kitchen ɗin, tasha mamakin ganin yarda aka ƙawata ɗakin, 
  Cikin hanzari ta wuce kitchen ɗin an tsara shi sosai,ƙarasawa tayi jikin kitchen shelves anan ta samu trays a jere ta ɗauki ɗaya,komai na cikinsa sabone wasu acikin kwalinsu wasu kuma a buɗe suke, tare da cokali ta haɗo masu da knife saboda taga tsiren naman basu zuge shi ba acikin tsinken shi yake,zasu buƙaci su yayyanka shi in zasu ci,
  Fitowa tayi daga kitchen ɗin sannan ta koma upstairs ɗin, tunkan ta ƙarasawa ta samu hossana zaune agefen camila hannunta ɗauke da tsiren naman nan ta tura abaki sai ci take kamar kura,hankalinta kwance, bakomai bane ya burge jahad ba face ganin yarda hossana tayi wani irin kyau cikin gajeran skirt mini tare da riga ƴar t shirt tabi shape din jikinta, hada ƴar hoda ta shafa ma fuskarta da jan baki,
   Ganin jahad ta soma washe mata baki, girgiza kai jahad tayi tare da cewa "dama nasan dole kiyi ƙara'e hossana irin wannan ɗaukar wanka haka,"
   "Kaɗan kika fara gani ma,aunty camila ma tace in ta samu hutun aiki zata kaimu saloon a gyara mana gashi tare da ƙunshi ma duka za'a yi mana," 
  murmushi jahad tayi a lokacin taƙarasa wurin table ɗin, aza tray ɗin tayi asaman shi sannan ta samu wuri ta zauna itama suka saka Camilla a tsakiyarsu,
   ita ta baje masu tsiren acikin tray ɗin ta jera masu shi,sannan ta zuba masu chips ɗin daga gefe,
   Nan fa suka gyara zama duka ukun suka tasar ma kayan lashe lashen, ba baka sai kunne, ba kaji komai sai sautin taunar shi da suke abakinsu,

**********************SEHRISH

tun da english teacher ɗinsu ta fita daga class ɗin, sehrish ta kifa kanta asaman desk din gabanta tana ta sharar bacci, har amrish ta gane mata daga jiya izuwa yau sam bata gajiya da yin bacci,alamu ma sun nuna cewa bata fahimtar komai kanta dashi da kwankwon ashana duk ɗaya suke,tashi amrish tayi tare da fitowa daga seat ɗinta ta ɗan sa hannunta tare da bubbuga bayan sehrish tace"ki tashi mu tafi time ɗin break yayi," kusan sau uku tana tashinta daƙer ta buɗe idonta da suka canza launi saboda bacci, miƙa tayi tare da yin hamma alamar yunwa take ji ga baccin ma bai isheta ba, fitowa tayi daga seat ɗin nata tana cewa"ashe har lokacin break yayi "
Amrish tace"taya za'ae ki sani, bayan baccinki kawai kike tasha, anya kuwa ma kina yin bacci a gida ne? Ta tambaya tana kallonta a yayin da suke fita daga class ɗin,
  "Ina yin bacci mana sosai,"_
"To meyasa kike yin bacci a class?ko karatu ma bakya saurara salon azo yin test ko exam kiyi ta baza idanu kina kallon question paper kina cizon biro ko? Ta fadi fuskarta ɗauke da dariya, itama sehrish din dariya tayi tana cewa "insha Allah hakan ma bazata faru ba,kafin lokacin zanyi karatu sosai,"
  Suna tafiya suna fira har suka isa Lunch room ɗin nasu atare suka shiga ciki, students duk sun hallara suna ta having lunch dinsu,
  ruƙo hannun sehrish tayi tare da kaita gaban table ɗin da zasu zauna,sai da rishi ta zauna saman table chairs din sannan amrish ta wuce ciki don ta amso masu abunda zasu ci,
  Ajiyar zuciya sehrish ta saki tana kallon students din dake zaune a wurin suna cin abincinsu suna shan fira abunsu,zahiri su take kallo amma abaɗi ba komai take tunawa ba face fuskar SGR ɗinta,murmushi ta saki aranta tana cewa "koyana ina yanzu?me yake yi?ko yaci abincinsa?Allah yasa dae baibar cikin shi da yunwa ba,
babu mai bata amsar tambayarta, cigaba da cewa tayi"bani da wani burin daya wuce naganshi cikin nishaɗi batare da wata damuwa ba,amma narasa dalilin dayasa kullum fuskarshi aɗaure baison yin fara'a,inaso na kawo sauyi a cikin zuciyar shi ya Allah ka bani wannan damar da zan zama ɗaya daga cikin farin cikin ran shi," 
   Gaba ɗaya tayi nisa acikin tunaninta, batasan meke wakana ba kwatsam taji hannun mutun a ƙirjinta an shafa mata, a wani irin firgice ta buɗe idanunta gabanta na faɗuwa,
   Bin su da kallo tayi atsananin tsorace, kai kana ganinsu kasan tantiran ƴan iska ne,su biyu ne mata jikinsu na sanye da uniform riga da wannan mini skirt ɗin,kai kace ba musulmai ba saboda ko head babu akansu, iya gashi ne kawai suka ɗaure abayansu shima ɗin

Chapters

Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login