Showing 90001 words to 93000 words out of 432432 words
Chapter 31 - Abban Sojoji Book 2 Hausa Novel Complete
satar kallon shi kamar wata mara gaskiya,
Cikin zolaya yace"faɗa mun gaskiya kodai aure kikeso ne?kin rasa wa zaki faɗamawa shine kika la6e anan kina kuka ko"? ɗagowa sehrish tayi taɗan zare ido can kuma ta fashe da dariya gaba ɗaya, shima dariyar yayi dama yayi hakan ne don yasata farin ciki yasan mata daga anyi masu maganar aure sai jin kunya da dariya,
ganin haka yasa shi ƙara cewa"hmmmmm dama nasani,mu aje wannan maganar a gefe nasan cewa akwai wanda kike so acikin ƴa'ƴana don na iya haihuwa gasu nan tubarkalla masha Allah ƴan mata sai rububi sukeyi hada masu kirana awaya duk safiyar Allah suna gaishe ni wai nan suna yi ma kansu ko ƴa'ƴansu kamun ƙafa,ni kuma har yanzu basu kwanta mun araina ba,Amma ke ɗin nan ko ta dabance in har kinaso in baki ɗaya daga cikinsu dole kema ki fara kamun ƙafa daga yanxu,"
Magana yake a natse sehrish kuwa ta kasa kunne tana sauraron shi,mamaki ya gama kamata yarda Abban nasu sukutun da guda yake fira da ita lallai ba ƙaramin wayayyen mutun bane,
bayan yakai ƙarshen maganar tashi tace"amma Abba,ni bansan yarda ake yin kamun ƙafar ba," ta faɗi cikin jin kunya,
dariya yayi tabi shi da kallo sai taga ya koma mata junaid saboda tsananin kamanceceniyar dake a tsakaninsu don dai shi fuskarshi akwai manyantaka,
Bayan ya tsagaita da dariyar yace"kina nufin baki san yarda ake kamun ƙafa ba in mutun nasan abu,to ki tambayi AZMEE ta faɗa maki zata koya maki,
Jinjina kai tayi tare da cewa"insha Allah zan tambayeta,"
Murmushi yayi kafin yace"daga ynx zan fara zuba ido in ga yadda zaki fara kamun ƙafar naki,idan kinyi abu mai kyau sai na duba na gani wanne ya dace acikinsu na baki,idan marks ɗinki yakai matakin A1 to zan aura maki ɗaya daga cikin manyan ne, idan kuma Credit kika samu zan haɗaki da ɗaya daga cikin youngers ɗinsu,amma fa ki sani idan marks ɗinki yazo da matsayin(f)to zan aura maki Haroon ne........... " dariyar da sehrish ta fashe da ita ne ya hana shi ƙarasa maganar, zuba mata ido yayi yana kallonta sai ya dinga ganin kamanceceniyar fuskarsu da ta yarinyar sam yarasa gane dawa take masa kama nan da nan kan shi ya ɗaure yashiga mamakin kamannin daya gani kodae idonshi ne ke nuna mashi hakan tabbas fuskarta tayi tamkar photocopy ɗin fuskar ƙanwarsa AZEEMA,
daker sehrish ta tsagaita da dariyar tace"Abba zan tafi kitchen nabarsu suna aiki,"
Murmushi yayi tare da cewa"hakan nada kyau,kwara tun ynx ki koyi girkin shima yana daya daga cikin jarabawar da zan maki don bazan aura ma ƴa'ƴana macen da bata iya girki ba,then idan nasamu free time zan wa junaid magana ya kira mun ke don mu ƙara tattaunawa,"
Amsa mashi tayi fuskarta cike da annashuwa tabi ta gefenshi tana faman sakin murmushi ba don komai ba sai don maganar Abban nasu dayace idan marking ta F9 ne zai aura mata haroon hakan na nufin shi kanshi yasan cewa haroon cikon bencin gidan ne 🤣😂😅
Har juyawa abban nasu yayi yana kallonta a lokacin tayi nisa wurin sauka daga stairs ɗin,ajiyar zuciya ya saki saboda ganin farin ciki a fuskar yarinyar, dama yayi hakan ne don ya mantar da ita damuwar da ta shiga har ta la6e tana kuka,kama hanya yayi ya wuce,dama bedroom ɗin junaid ya nufa,
***************************
Tun ɗazu da suka kammala lunch ɗinsu after Azhar hossana da Camila suka koma bedroom din saman katafaren gadon suka baje suna bacci abun ba'a magana,ita kuwa jahad sam tagaza yin bacci tun da tayi sallar la'asar tafito daga ɗakin ta tsaya a falon tana zagaye, bakomai take burin gani ba face Ya Omar dinsu ko zafin ciwon ƙafarta yanzu tadaina ji,har wurin ƙarfe biyar da wani abu tana wannan safa da marwar in betwn seater's ɗin dake a palourn,tana cikin wannan zagayen MARSHAL OMAR ya shigo falon da sallamar shi, sam bata ji shi ba saboda ta juya masa baya tamiƙi hanya tana tafiya,
Murmushi ya saki ya tsaya yana tunanin wacece acikinsu jahad ko hossana,koma dae wacece ba ƙaramin kyau tayi masa ba acikin kayan,yaji daɗin hakan saboda dama burinshi ya gansu cikin jin daɗi da walwala,ganin bata da alamar juyowa yasa shi yin gyaran murya da ɗan ƙarfi, cikin sauri jahad ta juyo tana faman zare ido don batayi tsammanin ganin mutun ba,nan da nan wani irin farin ciki ya mamaye fuskarta da karfi ta furta"Ya Omar," lumshe idonshi yayi tare da buɗe su yana murmushi,
Watsa wa tayi da gudu tamkar zata rungume shi,sai da taje dab dashi sannan taci burki tana dariya,yana ganin hakan ya gane cewa Jahad ce,don da ace hossana ce sai tayi hugging dinshi,
"Fatan na same ku lafiya"? Ya furta yana kallonta,fuskarta awashe tace"Alhmdllh ya omar,dama tun ɗazu nake jiran zuwan ka, ashe zaka zo da har na fidda rai,
Omar yace"naso nazo ɗazu to bansamu hali ba,shiyasa na aiko maku da major don ya ɗauko ku,ina fata gidan yayi maku?
"ya omar ni nama rasa da wasu kalmomi zanyi amfani dasu wurin yi maka godiya Allah.........."tuni idanunta sun cicciko da kwalla sun soma gangarowa daga cikin idanunta,
Cikin sauri yace"Why jahad?me yasa zakiyi mun kuka bayan kinsan bana son ganin hawayen ku,sannan bana son godiya kada na sake ji,duk wani abu da nayi maku nayi shi ne don Allah,kuma haƙƙin ku ne dake akaina har yanzu ma ni ji nake kamar akwai sauran abubuwan da banyi maku ba,
..kallon shi kawai take yi yana bayani har yanzu tana mamakin kyakkyawar zuciya irinta Marshal omar,
Cikin shessheƙar kuka tace"ya omar kai wane irin mutun ne?narasa dame zan fasalta ka,kyawawan ɗabi'unka da halayenka da kyakkyawar zuciya irin taka bana tunanin a doran duniyar nan za'a samu mai irinsu,koda za'a samu sai anci baƙar wahala kuma cikin kashi 100 bai wuci asamu kashi biyu ba,kai na musamman Ne ya omar,ina taya iyayenka farin ciki sosai da samun ɗa kamarka,saboda kai abun alfahari ne........ni bansan da me zamu saka maka ba ya omar,ka bamu kyakkyawar rayuwa ka cire mu daga ƙangin rayuwar da muke ci,a lokacin da muke tunanin cewa kowa ya tsanemu bai son mu mutuwa ma kawai muke jira,sai gashi Allah ya haɗamu dakai,tun a lokacin nasan cewa kai kyauta ne daga Allah...........
tun da jahad ta soma kora jawabi ya goya hanneyen shi a faffaɗan kirjinshi ya natsuwa yana sauraronta fuskarshi ɗauke da murmushi,saboda kalamanta ba ƙaramin shigarshi su kayi ba yadda take magana a natse ga wata irin murya dake gareta mai sanyin gaske irin muryar da duk 6acin ran da kake ciki in. Ka ji ta sai ka manta dashi,ae jahad akwai natsuwa ga tawakkali nima na shaida hakan 😘
"Ya omar ka faɗamun dame zamu saka maka?nasan ma babu Ba mu da abunda zamu iya saka maka aduniyar nan face addu'a itace kawai ke gare mu,i will keep pryaing 4 u ya omar hada family ɗinka duka zan saku a addu'ata till the end of my life bazan manta ba aduk lokacin da nayi sallah ko nayi karatun alkur'ani har night prayers ma zan dinga tashi inayi just because u ya omar and ur family,
ta ƙarasa maganar tana faman sauke ajiyar zuciya har lokacin hawayen fuskarta basu tsaya da kwarara ba,
Hannu omar yasa tare da zaro handkerchief ɗinsa dake front pocket dinsa dake a t shirt din jikinshi,
Da hannun shi yasa yana wiping tears dinta a hankali,runtse idonta tayi tana jin wani irin yanayi mara misaltuwa a tattare da ita,
Muryarshi ce ta tsinkaye ta da cewa"jahad ngde ssae kalamanki kawai da kikayi mun a yanzu ma sun wadatar dani,sannan idan kuna so ku saka mun abunda nakeso shine koda nan gaba kada ku juyamun baya bana son ku canzamin inaso ku tsaya a yarda nasan ku,ina tsananin ƙaunarku sosai bana son abunda zai raba ni daku,inason zumunci ya ɗaure a tsakanina daku daganan har can......
katse shi tayi da cewa"har ina kenan ya omar,"
Cikin zolaya yace"gidan Aljanna mana," dariya tayi sosai kafin ta tsagaita da dariyar tace"insha Allah ya omar ba zamu ta6a baka kunya ba,zamu kasance kamar yarda kakeso,"
Jinjina kansa yayi sannan yace"where's my hossana banganta ba,ko tana ciki ne? Ya yi nuni da hannun shi,
Jahad tace"hossana suna ciki tare da wannan nurse camila din sai sharar bacci suke yi tun ɗazu,"
Murmushi yayi tare da cewa"naso na ganta,"
Cikin sauri tace"ya omar ka shigo daga ciki mana ka zauna na kira maka ita don itama hossana a ƙagare take data ganka,"
Omar yace"sauri nake na koma gida yanxu,ki gaishe mun da ita dae,ko kuma zan kira wayane ae akwai telephone sai mu gaisa," jinjina kai tayi tare da cewa"shikenan zan sanar mata,amma nasan zatayi kuka in taji cewa kazo kuma ka tafi bata ganka ba,
juyawa yayi yana faman sakin murmushi har ya kusa fita daga falon tace "ya omar," juyowa ya kuma yi yana kallonta,
"Tun jiya inata so in kazo inyi maka ya mai jiki,abun yana araina ɗan uwanka daka sanar mun cewa bai lpy,"
Omar yace"oh fawan da sauƙi jikin shi sosai,kada ki damu zan bashi waya inyaji sauki ssae sai kiyi mashi ya jiki,"
Jinjina kanta tayi alamar toh daga nan sukayi sallama ya fuce daga falon,
Ajiyar zuciya ta saki tare da wuce wa ciki fuskarta asake 😇
****AUNTY BABBA******
💋Boss Bature💋_
********AUNTY BABBA************
Zaune take agaban dressing mirror ranta a matuƙar 6ace fuskar nan tayi jawur saboda kukan da taci,ta zabga uban tagumi zuciyarta sai faman tafarfasa take yi,bakomai bane ya haddasa mata wannan 6acin ran ba face General ishaq daya hanata zuwa abuja,duk yarda ta kwallafa rai akan zuwa abujan ya hanata,sai da ya bari tasha wankanta ta kimtsa cikin leshi ta yafa mayafi ta ruƙo jakarta, tana fitowa ta same shi zaune a falo jikin shi sanye da gajeran wando baki,wani irin kallo yabi ta dashi tare da cewa"Ina zuwa,"
washe masa baki tayi tare da cewa"Abuja mana,kai fa kace zamuje duba jikin fawan,"
kai tsaye yace"ae nafasa wannan,ni kaɗai zanje inyaso ko a waya ne kun kira Abba kuyi masu Allah kyauta,"
Tur6une fuska tayi tare da cewa"dan Allah idan wasa kake mun ka daina,"
�?
Shima ya tamke fuskarshi yace"ba wasa nake ba,ni kaɗai zanje inyaso saina wakilce ku,"
Hankali tashe tace"Haba Abban hafsat sai da na kammala shirina, tafiya kawai ta rage zaka ce wai an fasa gaskiya ni sai naje," ta faɗi tare da ruƙe qugunta tamkar zata buge shi,
Miƙewa ishaq yayi fuskarshi ba wasa yace"to ki sani muddin kikasa ƙafarki kika bar gidan nan without my permission hmmmmmm ke kinsan mai zai biyo baya,
Yana faɗin hakan ya fuce ma daga falon yabarta,
da gudu ta koma bedroom ɗinta a ƙasa ma tayi wurgi da handbag ɗinta saman gado ta faɗa tadinga shan kukan baƙin ciki har bacci ya kwashe ta,
Ta jima tana baccin kafin ta tashi cike da kunci ta koma gaban mirror ta zabga tagumi rai a6ace,
Download>>> Dangin Rabi Complete Document
Ta jima tana tunanin meyasa general ishaq ya hanata zuwa gidansu don ta duba jikin fawan,abun ya ɗaure mata kai saboda shi da kansa yace zasu je dubiya atare amma ya canza ra'ayinsa yanzu,
tsoki ta buga tare da kai hannu ta ɗauki wayarta dake agaban mirror ɗin,contact ɗinta ta shiga ta lalubo numbar wayar HAYAAM ta danna mata kira,ringing ta shiga yi kusan sau uku ba'a ɗaga ba,
tana a cikin toilet kiran ya shigo a lokacin wayar na hannun wani matashin saurayi dake zaune saman wani haɗaɗɗen gado, daga shi sai shorts ajikin shi ya baje abun shi, ganin sunan Aunty Layla ya bayyana akan screen ɗin wayar yasa shi ɗaga murya tare da cewa"babe!babe!ur phone is ringing,
Daga cikin toilet ɗin tace"wanene ke kirana?in dae mommy ce ko Abi ka kashe wayar gaba ɗaya bana son takura,
"No basu bane,wannan auntyn naki ne Layla,"
Jin sunan Aunty laila yasa ta yin wuff ta fito daga cikin toilet ɗin, doguwa ce sosai fara sol babu ko tabo ajikinta kai kana ganin fatar nan zakasan cewa ba ƙaramin kuɗi take kashe mata ba saboda yarda take ɗaukar ido,
ta ko'ina Allah ya bata ga dogon wuya,
Bin ta da kallo saurayin yayi sam yagaza janye idonshi akanta sai kace batare suke rayuwa acikin gidan ba,
Towel ne kawai ta ɗauro ajikinta cikin hanzari ta miƙa hannunta tare da kar6ar wayar tana cewa"nashiga ukuna Aunty laila kuma a awaya?yanzu zata rufe ni da faɗan ba gyara ba dalili mtswwwwww
�?
Ta ƙarasa maganar tare da ɗaga kiran ta kara a kunnanta tana faman zazzare manyan idanunta,
A ƙule aunty babba tace"ina kika je ne inata faman kira ba'a ɗagawa?
Cikin en ina tace"Nashiga toilet ne yanzu na fito na sami wayar tana ringing asaman gado,
aunty babba tace"hmmmm kina a gida ko kina awaurin yawon gantalin naki?
Cikin sauri tace"am....ina a gida......" bata bari ta ƙarasa ba a tsawace tace"Karki kuskura kiyimun karya Hayaam ina sane da duk wani yawon gantali da kikeyi ana sanar mun da komai,saboda tsabagen iya shege da fitsara idonki ya buɗe wuyanki ya isa yanka hada tattara kaya da komawa gidan saurayi da zama koba haka akai ba? Ta tambaya azafafe tamkar tana a gabanta,tuni ran Hayaam ya 6aci juyawa ta ɗanyi ta kalli Sofwan dake kallonta bai sauraron me suke cewa amma ya lura da yanayin fuskarta daya canza saboda hayaam bata iya 6oye 6acin ranta duk mun ƙanƙantarsa,
sassauta muryarta tayi tare da cewa"Aunty layla mgnr da kika faɗa gaskiya ne,i can't hide it 4 u ni bazan iya rayuwa a cikin gidan nan ba saboda baida marar raba da kwango a wurina,fentin gidan duk ya ƙoƙe kamar munfi kowa talauci a layinmu,bama wannan ba ɗakinmu bai da banbanci da kwankon ashana katifa ce kawai duk ta gwaigwaye sai akwatin kayan mu, ko na fidda kuɗi na siyi furnitures mommy bata barin komai sai dae kawai nadawo na taras ta siyar da komai ta hanani jin daɗin rayuwa kuma kinsan ni macace mai son rayuwar hutu rayuwar ƴanci wannan shine dalilin dayasa nabar masu gidan don wlh ko abincin da suke ci ynx 6ata mun ciki yake yi saboda wannan yarinyar ƙanwar Amani ita suke ba girkin gidan,yarinyar da bata wuci 14years duk wani aiki na gidan ita take yin shi har yanzu mommy bata haƙura ba akan ɗaukar fansar abunda mommynsu tayi mata" yadda take magana kaɗai ya isa ya tabbatar maka da cewa ba ƙaramar ƴar duniya bace magana take tana faman wurga ido tana kora jawabi
Jinjina kai aunty babba tayi tare da cewa"ae ni tayimun dai dai,wato wayewa tasa kin manta da irin azabtarwar da matar nan tayi mana shine har kike ganin laifin mommynmu,kwara su kashe yarinyar ma kowa ya huta ae ni nafison su wulaƙantata," ta fadi tana faman huci kamar tana agabanta,
Download>>> Yaro Ne Complete Document
Ganin wayar tasu ba mai ƙarewa bace yasa Sofwan tasowa daga saman bed dinsa ya sauko, takawa yayi izuwa bayan Hayaam dake atsaye ya rumgumota tare da zagayo da hannayen shi ta waist ɗinta sannan ya kwantar da kanshi daga gefen wuyanta yana cewa"babe yaushe wayar zata ƙare?nifa a ƙagare nake,
ƙasa ƙasa da murya tayi tare da cewa"pls karkaja min bala'e,"
�?
Muryar aunty babba ce taci gaba cewa"Yanzu abunda nakeso dake kibar komai da kike yi ki tafi abuja gidan surukaina acan nakeso ki cigaba da zama,
Ƙiris ya rage hayaam ta saki wayar dake a hannunta saboda jin sa6on da auntyn nata ke faɗi, cikin ruɗu tace"haba dae Auntyna amma dae wasa kike yi ko?if not ni mai zai kaini gidan in-lows din mu da zama abun ma babu daɗin ji........,
Tsawa aunty babba ta daka mata tare da cewa"ke dalla yi mun shiru!duk ƙoƙarin da nakeyi akanki bakya gani!kina nan sake da baki ga wata can a gidan matsayin yar aiki Abbansu ya mayar da ita ɗiyarshi sun gatanta yarinyar har makaranta take zuwa,idan har kikayi gangancin rasa wannan damar ta komawa gidan da zama ina mai tabbatar maki da cewa Kin rasa cikar burinki na har abada," shiru hayaaam ta ɗanyi gabanta na faɗuwa saboda ba abunda ta tsana fiye da ace zata Rasa SURGEON GENERAL RAFAYET saboda mutuwar son da take yi mashi ta kwallafa rai akanshi a lokacin baya tasa naci sosai akan shi sa'adda suke zuwa gidan sosai,amma tun da ta lura cewa kafin ya ma ɗaga idonshi ya kalli mace aiki ne don sai da ta share 2 weeks a gidan sau ɗaya suka ta6a hada ido shima ɗin by mistake ne ya ɗago a lokacin,abun ya tsaya mata arai, yadda take da kyawun surar nan babu namijin da zaiganta ya kawar da ido batare da ya neme ta ba sai akan SGR,tun a lokacin ta soma fidda rai akan shi amma yanzu aunty laila ta soma dawo da ita kan network,
lumshe idonta tayi tana tuna kyakkyawar fuskarshi har lokacin sofwan na manne da jikinta ya lafe mata kamar wani maye,
ƙara kara wayar tayi akan kunnanta tace"Aunty laila komai zan iya yi akan na mallake shi,saboda shine namijin daya haɗa komai da nake kwaɗayi nake tsananin so a jikin ɗa namiji,amma abunda bansani ba aunty layla shin kina ganin zasu kar6e ni in naje gidan a matsayina na ƙanwar matar yayansu?
Wani irin shu'umin murmushi Aunty babba ta saki wato anzo dai dai wurin da tafi so, miƙewa tayi daga zaunen da take agaban mirror tashiga zagaye bedroom ɗin nata tana cewa"Hayaaam baki da Matsala indae a gidan nan ne! Kinsan yarda Abbansu ke da son ƴa'ƴa hannu biyu zai kar6eki abu daya kawai nasani shine dole sai da iznin Abi sannan zai kar6eki don haka kibarmun wannan a hannuna ni zanyi magana da mommynmu tunda ita ke juya shi da zarar tayi mashi magana zai amince!abunda kawai nakeso dake hayaam shine kiyi gaggawar komawa gidan da zama acikin watan nan!Ke bama sai kin je da komai ba tsurarki zaki tafi batare da trolly na kayanki ba,saboda inaso ki fara fakewa da cewa kinje duba Fawan ne da bashi da lafiya daga nan kawai saikiyi zaman ki dirshan babu mai tanka maki saboda duk matasan gidan miskilai ne babu ruwansu,da ace dae yana da ƴa'ƴa mata shine za'a samu matsala kinsan mu mata da bakin ciki da hassada muke....'
Murmushi kawai hayaam ke saki tana faman lumshe ido tare da cizon