Showing 21001 words to 24000 words out of 432432 words

Chapter 8 - Abban Sojoji Book 2 Hausa Novel Complete

irin bacci ne ke fusgar shi, ga uwar yunwa yana ji, ji take tamkar ta bashi tea ɗin abaki yasha, cikin sauri ta haɗa masa tea ɗin a cup ta ɗan tura masa agabansa tace "gashi nan,'
buɗe blue eyes ɗinsa yayi a hankali sannan yakai hannu daker ya ɗauki cup ɗin yakai bakinsa yana ɗan kurba da zafinsa, ya sha ba laifi kusan sau biyu tana ƙara masa yana shanye wa,
Bayan ya kammala tace "kayan dinner ɗin fa na mayar dasu"? Ta tambaya cike da jin tsoran amsar da zai bata,
"In akwai fruits ki haɗo mun," ya faɗi tare da mayar da jikinsa ya kwantar akan pillow,
Tattara kayan tea ɗin tayi sannan ta fuce dasu ta ajiye su a tray din dake ɗauke da warmers na abincin sannan ta ɗauke shi ta fita dashi kitchen ta shiga ta ajiye su, sannan ta ɗebo mashi fresh fruits acikin fridge,
A plate ta zuba mashi su sai da tafara yayyanka mashi su sannan, tana ƙoƙarin fita suka ci karo da Haroon tsaye abakin ƙopar kamar aljani,
Da ƙarfi ta furta "A'uzu billahi minashshaiɗanin rajim,'
Haroon ya fashe da dariya tare da cewa "Ni ne shaiɗan ɗin, ko kin ga ƙaho akaina ne?
"Eh," ta bashi amsa,
Yatsina fuska yayi yana bin jikinta da kallon frm up to down kafin yace "Haɗaɗɗiyar Sura,"
tace "Tubarkallah masha Allah,"
Murmushi yaɗanyi kafin ya kuma cewa "ki dai bi ahankali naga kamar zakiyi rawar kai Kada kici ka zaƙewa mana domin kuwa har yanzu fa baki da wani matsayi acikin gidan nan, duk inda za'aje adawo bakya wuce ƴar aiki, sannan na lura kina shisshige ma wancan ifritun ko? to inaso ki sani wancan dashi da dutse duk ɗaya suke indai agame da feelings ne, mace bata gabansa koda zai kula matan ma bana tunanin irin ki, ae ma zaren ba kalar yadin bane iska ce kawai zata wahalar da mai kayan kara.........
tun da yasoma magana idon sehrish suka soma ciccikowa da kwalla amma bata bari hawayen sun zuba ba, ganin zai bata mata lokaci yasa ta bi ta gefensa ta fuce da sauri, tana jiyo dariyarsa sam tarasa gane ma haroon, batasan mai ta tsone masa ba,
time ɗin da tashiga bedroom ɗin SGR samun shi tayi yana ta faman sharar baccinsa alamu sun nuna cewa ma tunda tasa ƙafa ta fuce ya fara baccin, tsayawa tayi akansa tana kallonshi hannunta na riƙe da fruits ɗinsa,
Yayin da idonta Suke cike da hawaye saboda kalaman haroon ita kanta tasani tabbas SGR ba tsaran yinta bane kwata-kwata bama haɗi, jinjina kanta tayi aranta tace "nasani kafi ƙarfina nesa ba kusa ba, kuma nasan cewa kafin ni akwai wanda suka ruga ni faɗawa wannan tarkon bila adadin, Amma inaji araina babu wadda zata soka dan Allah kamar yadda nake sonka, tun bansan ya kamannin fukarka suke Ba, da sunanka kawai nakamu da tsananin ƙaunarka kuma zan cigaba da addu'a akan hakan koda bazan ci nasara ba aƙarshe...Ana ahabbuk kasiran BABBAN YAYA.........❤�?
Wani irin juyi SGR yayi har sai da Sehrish ta ɗan tsorata gudun karya farka ya ganta, gyara kwanciyar shi yayi, yadda yake sakin numfashi anatse yana bacci ba ƙaramin tafiya yayi da ita ba,
Ajiye fruits ɗin tayi saman table sannan ta matsa a hankali cike da fargaba ta janyo lallausan blanket ɗinsa jikinta na ɗan kerma ta samu ta hayo dashi jikinsa ta lullu6a masa har zuwa neck ɗinsa,
Murmushi ta ɗan saki ganin ta kammala batare da ya farka ba, juyawa tayi ta tattaka izuwa inda makunnin hasken ɗakin yake ta kashe mashi shi, nan take ɗakin ya soma kyalli yana bada wani irin haske har sai da ta ɗan razana, ashe furnitures ɗin dakine masu wannan sparkling light ɗin launi daban daban suke badawa, aduk time ɗin da aka kashe hasken ɗakin Yayi dark gaba ɗaya su kuma sai su soma bada nasu hasken mai launuka, fuska ɗauke da murmushi sehrish ke kallon wannan ikon Allan Bin su take yi da kallo tun daga Bed ɗinsa da bedside table ɗinsa, drawer ɗin da ke ɗauke da mirrow jerin wurin Closet ɗinsa gaba ɗaya sun ɗau hasken nan, sai taga ya ƙara yi mata kyau sosai,
Lalla6awa tayi ta koma inda yake kwance tana kallon fukarshi yadda eye lashes dinsa suka fito radau zira zira dogaye kasancewar idon na'a rufe, sun kwanta luf,
Addu'ar bacci tashiga yi mashi saboda tasan cewa bai samu damar yi ba ayarda ya kwanta ɗin nan agajiye ta jima sannan ta ɗan tattofa masa ajikin bargonsa, kamar karta bar ɗakin haka take ji
(Nace ba mai zai hana kawai ki kwana anan Ehen 😂)
hannu tasa ta ɗauki Kayan marmarin dake acikin plate ɗin sannan ta fuce dashi bakowa a babban falon Dama tun fitowar farko da tayi duk sun kammala dinner ɗinsu sun shige cike aranta tace "Allah sarki su fawan hada rashin su yasa yanzu basu cika haɗuwa atare suna cin abinci ba ko zama a palor suna fira, ko yaushe zasu dawo? Duk da ina tsoran abunda zasu ce in suka ganni a
Matsayin mace, Especially fawan nasan halinsa sosai baijin magana shine ya ta6a bani horo harna galabaita," ta ƙarasa zancen zucin nata , bedroom ɗinta ta wuce da fruits ɗin saboda dama itama bata ci komai ba, asaman gadonta ta zauna tsakiyar gadon ta lankwashe ƙafa tana shan fruits ɗin tass ta shanye su sannan ta ajiye plate ɗin asaman side drawer ɗinta, dama empty yake tunda ta rotsa ma haroon fitilar saman shi akai, bata sake ajiye komai asaman wurin ba,
sauko wa tayi tashiga toilet saboda bata yi sallar isha'e ba, alwala tayi sannan ta dauko hijab ta zura bayan ta shimfiɗa carpet ta gabatar da salla,
Tana gama wa ta naɗe carpet ɗin ko addu'a bata tsaya yi ba, ta tura su cikin wardrobe sannan ta haye saman gadonta taja bargo ta kwanta daker tayi addu'a kafin bacci 6arawo yayi awon gaba da ita.................(Shin ko kun lura cewa Sehrish ta manta dasu hosana da jahad bakamar da ba? hmmmmm rayuwa kenan baka ta6a sanin asalin ya mutun yake sai yasamu wurin zama koya samu abun duniya nan zaka ga zahirinsa😥)

_____________________🌹🌹🌹____________________

In midnight Hosana tafarka da matsanancin Ciwo, wani sabon raɗaɗin ciwon ne ya taso mata agigice tafarka tana kuka tana zabga Uban ihu tana faɗin "Innalallahi wa'inna ilaihiraji'un , La'ila ha illallah muharammadur rasulillah Wayyo Allah na, mutuwa xanyi, gaba ɗayansu suka farka hankali atashe tun daga jahad har hafsat dake kwance saman Sofa sai da tafarka a tsorace,
taruwa su kayi akanta jahad na faman yi mata addu'a tana tofa mata cikin kuka take faɗin "Hosana ki daina magana ciwon bakin ki zai ƙara raunata, dan Allah kiyi haƙuri innalallahi bansan ya zanyi ba,'tafaɗi tare da fashewa da wani sabon kukan itama, dama sai da ranta yabata cewa raɗaɗin ciwon hosana zai iya dawo wa sai gashi ya dawo, fuskar tayi suntum la66an sun kumburo hancinta ma yayi girma, idanunta ma sun kumbura duk kwantsa ko buɗe su bata iyayi saboda sun datse sosai, ita kaɗae tasan azabar da take sha ga haƙoranta suma nasu Zogin daban, ko'ina ciwo hakanne yasa ta haukace taita faman zabga salati tana kiran Sunan Allah da manzon sa 😭*💋💋💋ABBAN SOJOJI💋💋💋*

*🔥The Father Of Soldiers🔥*

ﻗﺼ�? ﺣﺐ ﺭﻭﻣﺎﻧﺴﻴﺔ ﺑﻴ�? ﺳﺤﺮﻳ�? ﻭﺍﻟﺠﺮﺍ�? ﺍﻟﻌﺎ�? ﺭﺍﻓﻴﺖ❤‍🔥💞💘�?

*Story & Written by*
*Hafsat Bature Muhammad*

~💋BOSSLADY💋~


*EPISODE 11-12* Ita kan ta Hafsat ba ƙaramin tashin hankali tashi ga ba ganin halin da yarinyar ta shiga, da alama ma raunukan nata sun ɗuri ruwa dole sai an fitar da ruwan Ya Salam, Yarfa hannu kawai take yi tana zabga uban kuka, hankali atashe JAHAD ta kalli hafsat tare da cewa "Aunty dan Allah ki taimaka mu mayar da ita asibiti aduba ta.....' ta ƙare maganar tana faman zubda hawaye,
Ita kanta hafsat tunanin da take yi kenan can ne kawai mafi ta, ta shi tayi jiki na rawa ta ɗauko hijab ta zura sannan ta ɗauki mukullin motarta da ta bari a saman mirror,
da kanta ta cuccu6i hosana daker ta ɗauko ta a kafaɗarta, ta fuce da ita cikin sauri itama jahad tabi bayanta a babban falon suka samu aunty babba saman Sofa hannunta ɗauke da plate ta dafa taliya sai faman ci take a tsiya ce saboda yunwar da ta taso ta, duk ihun da hosana take yi a kunnanta amma batayi yunƙurin tashi ba, balle taje ta dubo meke faruwa,
Ganinsu afujajen yasa ta miƙewa tana cewa "Hafsat ina zuwa cikin daren nan? Ina zaki kai ta?
Batare da hafsat ta kalle ta ba tace "Zan mayar da ita asibiti ne," hankali atashe aunty babba tace "Saboda me !! Acikin daren nan ! Ki barta kawai inyaso gobe dr yazo ya duba ta har gida,"
tsoki hafsat taja dama a ƙule take da Mommyn nata saboda duk ita taja mata halin da suke ciki,.

Wuce ta tayi tana cewa "da yake ba jikin ki bane ae dole ki ce haka,'

Bin su kawai aunty babba tayi da kallo har suka fuce, abayan mota hafsat ta kwantar da hosana, sannan suka shiga gaba ita da jahad, taja motar da gudu ta fuce da ita a wani privet hospital takai ta, cikin sa'a suka karbi hosana kuma nan take suka shiga bata taimakon gaggawa,

Yayin da hafsat da jahad suka samu wuri suka zauna nan waje suna jira saman waiting chairs, runtse ido kawai jahad ke yi tana faman karanto addu'a, tsigar jikinta har tashi take yi saboda jin yarda ihun hosana ya cika asibitin gaba ɗaya baiwar Allah, ita kaɗai tasan azabar da take sha,

Ita kanta hafsat dake gefenta jikinta duk ya gama mutuwa haƙiƙa taji tausayin Yarinyar fiye da tunanin mai tunani,

Jim kaɗan suka ji tsit babu kukan hosana babu alamar shi, jin hakan yasa jahad yin zumbur ta miƙe ta tunkari ƙopan ɗakin da suka kwantar da ita, tsoranta kar ace hosana ta mutu ne shiyasa suka ji shiru,
turo ƙopar Nurse tayi ta fito cikin sauri jahad ta tare ta tana cewa"dan Allah sister ya jikin nata yake? ta tambaya a ɗan ruɗe
Nurse ɗin tace "Alhamdulillah, kada ki sa damuwa aranki, jikinta da sauƙi sosae anyi mata dressing na raunukan nata sannan Mun taimaka mata da pain relievers yanzu haka allurar bacci mu kayi mata, addu'a kawai zaku ci gaba da yi mata,' tana faɗin hakan ta wuce gaba,
Ajiyar zuciya jahad tasaki har hankalin ta ya kwanta sosai, komawa tayi ta zauna gefen hafsat wadda ke ta faman yin gyangyaɗin bacci,
Rufe idonta kawai tayi tana faman ci gaba da yiwa hosana addu'a, bata jin zata iya runtsawa a daren nan,
tsawon awanni suna anan jugum time ɗin hafsat ta jima da yin nisa a baccin ta, jahad kuwa na nan ido buɗe, kamar daga sama taji hosana na kiran sunan ta ƙasa ƙasa da farko tayi tunanin gizau muryarta keyi mata amma daga baya ta tabbatar da cewa ita ɗin ce ke kiranta,
Cikin hanzari ta miƙe ta shiga ɗakin samun ta tayi ta tashi zaune saman gadon, ba ƙaramin farin ciki bane ya cika jahad, ganin yadda fuskar hosana ta sa6e an matse mata ruwan anyi dressing ɗin wurin ga bandage nan a forehead ɗinta da saman hancinta, duk da fuskar ta canza sosai kamar ba ita ba, idanuwanta sun buɗe sosai tana ganin jahad takama Murmurshi 😥

Faɗawa saman gadon jahad tayi ta rungumo ta sosai ajikinta tana faɗin "Allah sarki hosana ashe kin farka ban sani ba kina ta kiran suna na, ya jikin naki? Akwai inda ke miki ciwo yanzu"? Tayi tambayar tana janye jikinta daga na hosanar,
Daker ta iya cewa "Naji sauƙi sosai jahad ba inda ke mun ciwo yanzu, amma magana tana mun wahala,Kuma ina jin jikina kamar ba nawa ba"
hannu jahad tasa tana shafa gefen fuskarta tace "Insha Alah zaki dawo dai-dai hosana, yanzu hankali na ya kwanta tun da naga kina murmushi nasan cewa sauƙi ya samu, yanzu ki faɗamun wanene yayi maki wannan bugun mutuwar?'
turo baki hosana tayi tana cewa "Wannan mara imanin, saboda nazo na same ta, ta shaƙe maki wuya kamar zata kashe ki, na bata haƙuri ta ƙyale ki ta ƙiya shine na gartsa mata Cizo a hannun, wannan ne fa kawai yasa ta kamani ta jibga ta faffasa mun fuska..........," shessheƙar kukan da take yi ne ya hana ta cigaba da maganar
Cikin sanyin Murya jahad tace "ashe duk don saboda ni ne tayi maki wannan bugun, babu komai akwai ALLAH ! , Zai bi mana haƙƙin mu duk wanda ya zalunce mu Allah zai saka mana insha Allah!
Jinjina kai hosana tayi tana share hawayen ta tace "Yaya Omar bazai ƙyale su ba, duk sai sun gane kurensu.....
ta faɗi wit angry face can kuma ta sake cewa "Jahad komai yasa yaya Omar har yau baizo ya duba mu ba"?
Jahad tace "muyi mashi Uziri hosana, ni nasan cewa yana sane damu kuma zaizo nan very soon,'
Sun jima suna yin fira atsakanin su, ita kanta jahad tasan cewa hosana juriya kawai take yi tana yin surutu, daker tasamu hosana ta koma ta kwanta, itama a gefenta ta ra6a ta kwanta, lokaci guda bacci ya kwashe su su duka,

Ba ƙaramin bacci suka sha ba, don kuwa har sai da gari ya waye rana ta fito sannan jahad tafarka, hosana kuwa nata faman sharar baccin ta, ganin yadda hosana ke bacci anatse ya ƙara tabbatarwa da jahad cewa tasamu sauƙi sosai, tashi tayi ta cire hijab ɗin dake jikinta, ta shige toilet ɗin dakin Alwala tayi sannan ta fito ta ɗauki hajiabin ta zura, tana faman tunanin in da zata samu tayi sallah don babu carpet,
  Fitowa tayi don ta duba hafsat samu tayi bata anan inda tabar ta jiya babu ita ba alamarta a wurin, sai taji hankalin ta ya ɗan tashi tsoranta kar ace guduwa tayi tabarsu a asibitin,
  Hankali atashe ta fito harabar asibitin ga mutane nan nata wuce wa wasu na shigowa wasu na fuce wa, sai faman waige waige take yi tana neman hafsat, har wurin ajiye motoci taje taga ko zata ga motarta amma babu ita, hakan na nufin tabar asibitin kenan, da alama ma tun asubahi tabar asibitin, tuni jikin JAHAD yayi mugun sanyi,
  Koma wa tayi tasamu wurin inda taga wasu mata zazzaune suna fira, tayi musu sallama suka amsa mata da fara'a
   Tambayarsu tashiga yi idan suna da abun sallah su ara mata, nan wata daga cikin su ta miƙa mata sallaya ɗinsu da suka zo da ita, anan harabar jahad tayi sallah bayan ta kammala ta mayar masu da dardumar sannan ta koma ciki a kasalance, bakowa tafi ji ba face HOSANNA, yanzu in da gaske hafsat tafiya tayi tabarsu yaya zasu yi? Ina zasu dosa? bakomai ma yafi damunta ba face Hosana in tafarka ta son dole akwai yunwa atattare da ita, gashi ita ba ta da ko sisi balle ta siya musu abunda zasu samu su Ci,
   Gefen hosana tasamu ta zauna wadda ke kwance tana faman sharar bacci, tagumi ta zabga tare da zuba mata Ido tana kallonta, in taƙaice muku tsawon lokaci ba hafsat ba alamarta 😧😳 Gashi in sunce zasu kai kansu gidan duka ba wanda yasan hanyar da zai bi, saboda da daddare ne kawai suka fito daga gidan baza su iya shaida kwatancen gidan ba, gashi ko Sunan unguwar basu Sani ba, ajiyar zuciya jahad tasaki aranta tana jin cewa hutu ne yazo musu, zasu ci gaba da rayuwarsu ne kawai akan titi,

_____________________SEHRISH__________________

Around 8 Ta farka kai tsaye kitchen ta wuce har time ɗin rigar jiya ce ajikinta da rolling ɗinta, a kitchen ta samu Azmee harta kusan kammala breakfast din gaba ɗaya, bayan tayi sallama ta shiga suka gaisa da junan su, Daga bisa ni azmee tace "Ina fata jiya kin kai ma SGR dinner ɗinsa ko? don na shigo na taras da kayan abinci a warmers ko ta6a su ba ayi ba,'
   Sehrish tace "Na babban yaya ne, Jiya bai samu yaci ba dana kai masa, Tea kawai yasha daga baya yace mun yana buƙatar fruits, shine kafin naje na kawo masa har bacci ya ɗauke sa,'
  Jinjina kai azmee tayi tare da cewa "Allah sarki da alama jiya sun sha aiki ne that's why harya gaza cin abinci, Yanzu bari na shirya miki breakfast ɗinsa ki kai masa da sauri saboda nasan dole ya tashi da yunwa,'
   Sehrish ta amsa mata da Toh, ta tsaya tana jiran ta shirya mata kayan breakfast ɗin nasa,
Shiru tayi tana tunano maganar da HAROON ya faɗa mata jiya, akwai abunda ya tsaya mata arai take son fitar dashi
"Aunty azmee dan Allah me ake nufi da ZAREN BA KALAR YADIN bane? ta tambaya tana kallom azmee dake shirya abinci cikin warmers asaman kitchen drawers din dake jere,
  Ba tare da ta juyo ta kalle ta ba tace "idan aka ce Zaren ba kalar yadin bane, a tunani na ana nufin kamar abunda bai dace da wani ba, a misali kamar ace kina son wani wanda yafi ƙarfin ki nesa ba kusa ba, bari na baki wani misali ma kamar yanzu ace mace tana Son Namiji wanda ya kasance hamshaƙin mai kuɗi ne ko mai mulki ga ilmi ga kyau gashi prominent dae, ke kuma ace kin kasance ƴar talakawa ce koma kina aiki a ƙasan

Chapters

Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login