Showing 381001 words to 384000 words out of 432432 words

Chapter 128 - Abban Sojoji Book 2 Hausa Novel Complete

yaji sautin saukar ruwa daga cikin toilet,sai yayi tunanin cewa wanka yake yi,Ashe fanfo ne Aka bari a kunne ba'a kashe ba,
   Daƙyar suka samu kowa ya haƙura da ganin junaid,Omar yace su wuce ɗakunansu kowa yaje ya huta,an kwaso gajiya,
  "Nifa ban yarda dasu babban yaya ba,Shi da ya Omar akwai wani abu da suke 6oye mana Allah,"Acewar Jahan,
A yayin da suke shiga bedroom ɗinsu,
  Ayaan yace"nikaina na lura da hakan,musamman faces ɗinsu,kamar sunsha kuka Allah,Gaskiya hankalina bazai kwanta ba,sai naga junaid,ni ban yarda wanka yake yi acikin toilet ba,"
  Jahan yace"mu bari mu huta,Zuwa dare sai muje ɗakin nashi,nasan lokacin idan ma wankan ne ya gama,"
  Ƙarasa shiga cikin ɗakin sukayi,kowa ya shiga rage kayan jikinshi,Jahan ne ya fara shiga waka,Ayaan ya zauna gefen gadon yana jiranshi ya fito shima ya shiga wankan,
   A can falo kuwa,Mommynsu ta tsare Sgr da Omar,Tasa su gaba tayi tana binsu da kallo one by one,dama bakowa Sgr yafi ji ba fa ce Mommynsu,tana da wuyar sha'ani,
  "Mommy,"Sgr ne ya ambaci sunanta,
bata amsa mashi sunan nata daya kira ba,sai cewa tayi"you didn't answer my question,It seems like you are hidding something for us!Rafayet where is junaid!kada kuyi mun ƙarya nasan ba halinku ba ne,just ku faɗamun Gaskiyar abunda ya faru,"
  Murya na rawa Omar yace“Am..mommy,Junaid fa yana a toilet yana wanka zai fito ne...m"daƙyar ya ƙarasa maganar ganin irin kallon da take yi mashi,kallon tuhuma,kallon ban yarda dakai ba
"Wai taya za ku ce mun junaid yana wanka?Nifa ba ƙaramar yarinya bace,balle kuce zakuyi mun wayau,tun daga kan fuskarku na gane cewa akwai wani abu daya faru dashi...."
  Saussauta muryarta tayi,sannan taci gaba da magana"pls idan wani abu ne ya faru da Romeo ɗina ku sanar dani,i will accept it,"yadda tayi maganar yasa su kaji jikinsu ya ƙara mutuwa,
  "Am listening to u guys,ku faɗamun meya faru dashi ya mutu ko"?
  Gabansu ne ya faɗi rass!da sauri Sgr ya ruƙo hannunta muryarshi na kerma yace"Mommy dan Allah kiyi haƙuri,ki rufa mana asiri,I will explain to u mu shiga daga cikin bedroom ɗin..."
  "Rafayet,meyasa zaka sanar da ita"?Omar ne yayi maganar fuskarshi a yamutse,
  "To ya kakeso nayi Omar,Mommy bazata ta6a yarda ba,kwara kawai mu faɗa mata gaskiyar abunda ya faru,Ka wuce wurin Daddy,ni zanji da Mommy,'
  Ya ƙarasa maganar tare da jan hannunta,Suka wuce upstairs bedroom ɗinshi,
  Ajiyar zuciya Omar ya sauke,Ya jima atsaye yana tunanin Yadda zasu ƙare da Abbansu,tsoranshi kada farat ɗaya zuciyarshi ta buga idan yaji cewa Anyi garkuwa da junaid kamar yadda suka tsara,
  "Omar,lafiya kuwa,"firgit ya ɗanyi tare da kai idanuwanshi wurinta,Azmee ta nufo shi,Ganinshi a tsaye kamar akwai damuwa atattare dashi,
  Dakyar ya ƙaƙaro murmushin yaƙe yace"bakomai,"
    "Omar,dama inaso na tambayeka ne,Wai ina junaid ne?tun jiya da suka fita shi da jahad shiru har yau basu dawo ba,nashiga damuwa sosai akan rashin ganinsu,har cewa yayi idan suka je shan ice cream zaiyi min tsaraba," ta ƙarasa maganar tana kallonshi,
  "Aunty Azmee,bazan iya 6oye maki ba,Junaid da jahad anyi kidnapping ɗinsu...."jin wannan maganar yasa Azmee ta dafe ƙirjinta da ƙarfi,idanuwanta suka firfito waje,hankalinta yayi mugun tashi,
  "Innalillahi wa'inna ilaihirraji'un!"kusan sau biyar tana maimata kalmar,
   siraran hawaye ne suka soma saukowa saman cheeks ɗinta,ji tayi tamkar bazata iya ɗaga ƙafafunta ba,saboda nauyin da sukayi mata,
  "Junaid da jahad suna buƙatar addu'armu Azmee,"acewar Omar,
  Daƙyar ta iya buɗe baki tace"Nashiga uku!Yanzu junaid da jahad aka ɗauke mana...."
Katse ta Omar yayi'pls Aunty azmee,ki daina ɗaga sautin muryarki,na faɗa maki ne don ki taimaka mana,Wurin kwantar da hankalin sauran mutanen gidan nan,Mun shiga damuwa sosai,saboda gudun halin da zasu shiga,musamman mahaifinmu...."
  Cikin shessheƙar kuka tace"Ya Allah ga bayinka nan!ka tsare manasu a duk inda suke,Ya Allah ka ku6utar dasu daga hannun azzaluman da suka yi garkuwa dasu,wannan wata irin masifa ce......"kuka ne yaci ƙarfinta,da gudun gaske ta juya tare da tunkarar kitchen,zama tayi ta dingi kuka kamar ranta zai fita,gani take yi kamar zasu rasa su ne,Ta ƙwallafa rai akan junaid,tana jinshi tamkar ɗan cikinta saboda ta shayar dashi,baiwar Allah,
  Jiki asanyaye Omar ya wuce bedroom ɗin Abbansu,tsaye ya same shi har ya zura kayan bacci ajikinshi,ta cikin mirror ya hango Omar,juyowa yayi fuskar shi ɗauke da murmushi yace"halan junaid ya fito daga wankan ne"?yayi tunanin abunda ya kawo shi ne,
  "Abba,me kake buƙata na kawo maka"ya tambaye shi ne don ya kawar mashi da tunanin Junaid aranshi
Murmushi Abba yayi tare da cewa"Sannu Azmee,Yau kaine ka kar6i aikinta kenan"?
  Duk da halin daya ke ciki na fargaba sai da ya ɗan murmusa,jin abunda abban yace,
   "No,kawai inaso na baka kyakkyawar kulawa ne saboda nayi kewarka,ka fara faɗamun abunda kakeso sai in kawo maka,"
  Murmushi Abba ya ɗan yi kafin yace"shikenan,junaid nake son gani ka kawo mun shi,idan ma ya fara bacci ka ɗauko mun shi,ina jiranka,"ya ƙarasa maganar tare da samun wuri gefen gadonshi,yana kallon Omar da yayi mashi zuru da ido,
  "Omar,lafiya ka zubamin ido kana kallona'?
  "Babu komai Abba,bari na ɗauko maka junaid ɗin,"yayi maganar tare da juyawa yabar ɗakin,Zaman jiran dawowarshi Abba yayi,sai faman sakin murmushi yake yi,harya ƙosa Omar ya ɗauko mashi Baby Junaid ɗinshi,

A 6angaren Omar yana fita daga bedroom ɗin abban nasu,kaitsaye kitchen ya wuce,Anan ya samu azmee zaune saman kujera tana ta matsar kwalla,
"haba Aunty azmee,meyasa zakiyi mun haka?Addu'a yakamata kiyi masu akan Allah ya bayyanar mana dasu,kukan da kike yi bazai amfane su ba,"
  Zame hannuwanta tayi daga saman fuskarta,idanuwanta sunyi jawur dasu luhu luhu,
  "Omar,ba zaka gane bane,dole inyi kukan rashin su junaid,ko ka manta shakuwar dake tsakanina dashi ne'?
  Shiru omar yayi yana kallonta,Allah yaso bai sanar da ita gaskiyar abunda ya faru ba,da baisan abunda zai biyo baya ba daga gareta itama,
Lallashinta ya shiga yi har ya samu ta saukko,Tsayawa yayi ta shirya mashi dinner asaman tray,ya kar6a ya wuce ɗakin Abbansu,ita kuma ta shiga ɗaukar kayan abincin da ta shirya masu tana kaiwa dining,


Lokacin da Omar ya koma bedroom ɗin Abbansu,yana shiga ciki Abbansu yaga tray a hannunshi sai ya ɗaure fuskarshi tare da cewa"Nifa ba yunwa nace maka inaji ba,Junaid nace ka ɗauko mun,"
  Saman table omar ya ajiye tray din tare da samun wuri gefenshi ya zauna,ruƙo hannayenshi yayi tare da sassauta muryarshi
   "Abba pls,kaci abincin ka ƙoshi,idan ka kammala zamuyi magana dakai,"
  Shiru yayi yana kallonshi kamar mai nazarin wani abu yace"Shikenan zuba mun abincin naci,Allah yasa naji alkhairi,"
Serving ɗinshi Omar ya soma yi,sosai yaci abincin bayan ya gama da abincin,Omar ya tsiyaya mashi Lemu me sanyi a cup,yasha,
  "Yanzu ina sauraronka,wata maganace zamuyi,"
  "Abba ko zaka ɗan kwanta ne?ina ga kamar hakan zaifi,muna magana inayi maka tausa,"
  Abun ya daurewa Abbansu kai,gyara kwanciyarshi yayi saman gadon sannan yace"ina sauraronka toh,"
  Hawa saman gadon Omar yayi,A hankali ya fara yi mashi massage ɗin kafarsa,
   A tsanake ya soma magana"Abba dama game da junaid ne,nasan ka yarda dani sosai,kuma zaka fahimce ni ne,
  Tunda ya ambaci sunan Junaid,Abba ya miƙe daga zaune da sauri yana kallonshi
  daurewa Omar yayi tare da cigaba da cewa"mun shiga matsananciyar damuwa Abba,idan ka lura da fuskokinmu duk sun sauya saboda tsabar tashin hankalin da muke ciki...."dakatar dashi Abba yayi ta hanyar ɗaga mashi hannu,
   "Ka fito fili ka faɗamun ainihin abunda ke faruwa Omar,sai 6oye 6oye kake yi mun,dama ni tuni sai da raina ya bani cewa wani abu ya faru da junaid,dan Allah ka sanar dani!ina ɗana yake"?hankalinshi atashe yayi maganar,
  Cike da fargaba Omar ya ɗaura da cewa"Abba,junaid yana cikin ƙoshin lafiya,sai dai baya atare damu,Jiya bayan fitarsu shan ice cream tare da jahad,kidnappers su kayi garkuwa dasu,bana so ka tashi hankalinka Abba,Ni nayi maka alƙwarin zan dawo maka da ƴa'ƴanka,cikin ƙoshin lafiya batare da sun samu koda ƙwarzane ajikinsu ba....."duk wannan surutan da Omar keyi baisan cewa Abbansu ya jima da sumewa ba,tunda ya ambaci sunan kidnappers sunyi garkuwa dasu,Bai ƙara sanin inda kanshi yake ba,
  "Abba!"ya ambaci sunanshi,yayin da yake kallon fuskarshi,Hannu yasa tare da dafe goshinshi,Dama saida ranshi ya bashi cewar hakan zata iya faruwa,
  Idanuwanshi ne suka cuccuko da kwalla,kamar ya fasa ihu haka yake ji,ta ko'ina babu sauƙi,dirshan ya zauna saman gadon fuskarshi a yamutse,ya zuba ma Abban nasu ido yana kallonshi,

Adai dai Lokacin Sgr ya shigo bedroom ɗin tare da Mommynsu,tasha kuka duk da irin juriyarta,daƙyar ya samu ya shawo kanta,shima ɗin don yayi mata alƙwarin cewa zai dawo mata da ɗanta har gida ba tare da komai ya same shi ba,jin motsin shigowarsu yasa Omar waigawa yana kallonsu,har suka ƙarasa shigowa wurin gadon,Gefen gadon Sgr ya zauna,Mommy ta tsaya daga tsaye tana kallon Abba dake a zaune ido rufe,
  "Omar,ka faɗa mashi ne"!?ɗaga mashi kai Omar yayi alamar eh,Ya kuma cewa"ko ya samu bacci ne"?
  Girgiza kai yayi tare da cewa"a'a,taya zan faɗa mashi wannan tashin hankalin yayi bacci?Kaima ka sani,tun kafin ma na ƙarasa sanar dashi ya sume a zaune,Na rasa abun yi ne shiyasa nayi zugum ina kallonshi,
  Miƙewa Sgr yayi da sauri ya fuce daga ɗakin don ya ɗauko masu ruwan da za'a yayyafa mashi,
  "Mommy,dan Allah ku ƙara haƙuri akan 6atansu junaid,in sha Allah we will try our best don muga mun dawo dasu cikin gidan nan,"
Jinjina kai tayi "Na yarda daku Omar,Nidai burina ku dawo mun dasu cikin gidan nan,Na tambayi Son game da kidnappers ɗin ya sanar dani cewa,Sau ɗaya suka kira waya,Kunyi magana dasu kuma har sun baku Junaid kunyi magana dashi,Naso ace sun bar wata kafa da zatasa ayi tracking layinsu,Amma kashe yace mun Sun kira da hidden number ne,abunda nakeso naji shi ne,basu buƙaci adadin kuɗin da suke so ba?ni koma nawa ne zan bada a kar6ominsu,"
  Jikin Omar ba ƙaramin sanyi yayi ba,gwanin ban tausayi haka yake kallonta,Aransa yana ayyana irin tashin hankalin da zata shiga idan taji cewa,Junaid ya mutu ta hanyar take shi da mota,
  "Omar kayi shiru baka ce komai ba,"ta jifa mashi tambayar,tana kallonshi,
  Girgiza mata kai yayi"A'a Mommy,basu buƙaci komai ba yanzu,Sun sanar damu cewa,Zasu tuntu6emu idan buƙatar hakan ya taso,kuma sunyi warning ɗinmu,kada mu kuskura muyi gigin yin investigation akansu,if not zasu illatasu ne,shiyasa bamu yi wani yunƙuri ba ayanzu,Amma yanzu mu kanmu kiransu muke jira,muji nawa suke buƙata sai a tura masu,"ba don yaso ba haka ya dinga shirga mata ƙarya,kamar yayi kuka wai yau shine ke yin ƙarya,duk da yayi ba'ason ranshi ba,Dole ce tasa su yin hakan,
  Turo ƙopar Sgr yayi hannunshi ruƙe da bottle water,ƙarasawa yayi tare da buɗe murfi ya tarfa ruwan asaman tafin hannunshi,Sannan ya shafa fuskar Abban nasu,Nauyayyar ajiyar zuciya ya sauke tare da ware idanuwanshi akansu yana kallonsu ɗaya bayan ɗaya,a hankali ya furta"Ina junaid"?
  Omar na ƙoƙarin buɗe baki yayi mashi jawabi,Alexandra ta katse mashi hanzarinshi da cewa"Ku barni dashi,dare yayi sosai yakamata kuje ku kwanta ku huta,kafin gobe,"ta fadi hakan ne don tasan cewa ba karamin tashin hankali suma suke ciki ba da ganin yanayin su,
    Saukowa daga saman gadon Omar yayi tare da ruƙo hannun Sgr yace"Mu tafi,"sallama su kayi mata tare da fucewa daga ɗakin,
Hawa saman gadon tayi suna fuskantar juna,tallabo fuskarshi tayi da hannayenta biyu,suka zuba ma juna ido,na wani lokaci kafin tace"Hubby,ka natsu ka saurare ni,Nasan zaka fahimce ni,Kuma kai musulmi ne!kayi imani da ƙaddara mai kyau ko mara kyau haka ne"?kamar wani ƙaramin yaro haka ta mayar dashi,
Nodding kai yayi mata alamar eh,
  Murmushi ta ɗan sakar mashi tare da cewa"haka nake son ji my hubby,"dakatawa ta ɗan yi da yin jawabin tana kallonshi,saboda ta kasa furta mashi abunda take so ta faɗa,farin ruwa ta gani ya kwanta acikin idanuwanshi,la66ansa na kerma yace"Pls tell me the truth,Meya faru ne?kowa ya sauya mun,Dama ni sai da raina ya bani cewa wani abu ya faru da baby junaid ɗina,"jikinshi har ya fara kakarwa kamar wanda sanyi ya kama,
   Hawaye ne suka ciko tab a idonta,
"Am sorry to say,Junaid yana cikin ƙoshin lafiya,Amma baya atare damu,Rafayet ya sanar dani cewa,since yesterday night around 8 suna kan hanyar dawowarsu gida,kidnappers suka ɗaukesu gaba ɗayansu,"
  Jin wannan maganar yasa hankalinshi yayi mugun tashi,wata irin zabura yayi yana ƙoƙarin saukowa daga saman gadon,Da sauri ta ruƙo rigar jikinshi"dan Allah ka natsu ka saurare ne...."
   Girgiza kai ya shiga yi yana faɗin"banga ta zama ba,Anyi garkuwa dasu junaid ɗina,Wlh bazata sa6u ba,duk inda junaid da jahad suke adawo mun dasu cikin daren nan in har anason zaman lafiya,wannan wani irin shashanci ne?har junaid ya kwana a hannun kidnappers tun jiya arasa wanda zai ƙwatosu daga hannunsu,Banga amfanin sojojin dana tara acikin gidan nan ba,Nikaina bani da amfani kenan!Kowa ma bai da amfani mun zama tamkar kwankwan ashana,tunda har bazamu iya ceto rayuwarsu ba,"idonshi ya rufe sai faman zazzaga masifa yakeyi,Ƙarasa saukowa yayi daga saman gadon,buguzun buguzun ya kama hanyar fita daga bedroom ɗin nashi,da sauri Alex tabi bayanshi,tana ambaton sunanshi
  Ko sauraronta baiyi ba,da alama ya zauce ne,
  "Yau ƙafata kafarsu junaid zamu dawo cikin gidan nan duk inda suke saina dawo dasu,abun ban haushi wai anyi garkuwa dasu junaid?sai kace ƴa'ƴan wani me siyar da kifi abakin titi,Ƴa'ƴana ne fa!Ni chief of army staff na Nigeria gaba ɗaya,banga amfanin matsayin da nake dashi ba Allah,tunda har za'a iya yin kidnapping ɗin ya'yana,wlh bazan yafewa kaina ba,in har bandawo da junaid cikin gidan nan ba,"ranshi amatukar 6ace yake yin maganar,jijiyoyin wuyanshi duk sun firfito waje,
  "Pls hubby Calm down ur mind,Ina zaka je ne?acikin daren nan!indai akansu junaid ne,na tabbata zasu dawo ne"
  Guntun tsoki yaja tare da cewa"baki da hankaline,da alama bakisan zafin haihuwa ba,Shiyasa kike faɗin hakan,"
  "Ni fa na haifeshi,taya zaka ce mun bansan zafin haihuwa ba?Ya kake so nayi ne?ka ƙi tsayawa nayi maka bayani,
  Su Marshal na zaune asaman sofa,kowa da abunda yake saƙawa aranshi,kwatsam suka jiyo muryoyinsu,nan fa suka miƙe suna kallonsu,
   Ganin Abbansu ya nufi hanyar fita daga falon ko takalma babu a ƙafarshi,da sauri suka sha gabanshi,
  Rufe ido yayi atsiwace yace"Ku matsa ku bani wuri,wlh Omar ka bani mamaki,ko ince kun bani mamaki,How many hours su junaid na a hannun kidnappers amma baku iya ƙwatomun shi ba,babu wani mataki da kuka ɗauka,to ni zanje in dawo da abuna,"yana magana huci na fitowa daga bakinshi,
   Ruƙo shi Omar yayi tare da fashewa da matsanancin kuka,Girgiza mashi kai ya soma yi batare da ya furta mashi komai,jikin Abbansu ba ƙaramin sanyi yayi ba,Cos ya manta when last yaga hawaye a fuskar Omar,tabbas abun na ci masu rai sosai,Mayar da idanuwanshi yayi kan Sgr,Hawaye ya gani kwance Luf acikin idanuwanshi,wanda tunda yake arayuwarshi bai ta6a ganin ruwan hawaye a idon Sgr ba,tun ma da aka haifeshi har suna expecting ko baida cikakkiyar lafiya ne,
   "Omar!kuka kake yi mun"?yayi maganar yayin da hawaye suka soma wanko fuskarshi,Kallon Sgr yayi tare da cewa"Kaima kukan zaka yi mun"?
  Duƙar da kanshi yayi ƙasa,gaba ɗaya jikin kowannansu yayi sanyi,
  "Abba,ka tausaya mana muna cikin matsananciyar damuwa na rashin Su junaid atare damu,Mun rasa yaya zamuyi,munyi tunanin zaka ƙarfafa mana guiwa wurin ganin mun ceto rayuwarsu,Amma sam kaƙi tsayawa kaji abunda muke son mu sanar dakai balle har musa ran zaka fahimce mu...."ya ƙarasa maganar tare da sanya tafin hannunshi yana share hawayen dake sauka a fuskarshi,
   "Abba,saboda rashin su junaid,ko bacci ba muyi ba,Yadda muka ga dare haka muka ga rana,Ga rafayet nan saboda shi,Ya baro kano ya dawo Abuja tunda sanyin safiya,dukanmu nan babu wanda ya iya kora koda ruwa ne ta maƙoshinsa,duk don saboda 6atansu junaid...."dakatawa ya ɗan yi da yin maganar yana kallon Abban nasu,da alama ya fara saukowa
  "Kaine ka haifemu,kafi kowa sanin su wanene mu!me zamu iya da kuma wanda baza mu iya ba!Nasan ka yarda damu sosai,Idan har akwai wanda zai bada shaida akanmu kaine Abba!meyasa bazaka yi mana uziri ba?idan har bamu bi komai a hankali ba wurin ganin mun ceto rayuwarsu,Toh zamu rasa su ne gaba ɗayansu!"
  Juyawa Abba yayi ya soma tafiya cikin falon,Saman sofa ya zauna,ganin haka yasa suma suka dawo saman Sofa ɗin suka zauna suna fuskantarshi,Itama Mommy ta samu wuri daga gefen shi ta zauna,

Duk wannan abun dake faruwa akan idon ƙannensu,don tun lokacin da Abbansu ya fito yana sambatun nan,Kowannansu ya fito daga bedroom ɗinshi,Jikin kowannansu yayi mugun sanyi,jin cewa Anyi kidnapping ɗinsu Junaid,Abun ya ta6a masu zuciya sosai,

"Har tsawon wani lokaci,kuke so na baku ku dawo mun dasu junaid"?Acewar Abba,
  Shiru sukayi gabansu na faɗuwa,Omar ne yayi ƙoƙarin cewa"1 week"a hanzarce Sgr yace"Omar that's impossible,ka manta yarda mu kayi dasu ne?Sunyi mana alƙawarin cewa in dae aka yi masu yadda suke so zasu sakosu,Amma ba a tare ba,saboda suna ganin za'a gano su adau mataki, akwai yiyuwar su fara sauko junaid shi kaɗai acikin satin nan ko kuma su fara sakin Jahad,Ni ina ga kamar one month yayi,Kafin lokacin in sha Allah mun dawo dasu duka acikin gidan,
  Girgiza kai Abbansu ya ɗan yi tare da cewa"Har one month!su junaid basa atare damu?idan suka cutar dasu fa?
  "Abba sunyi mana alƙawarin cewa in har zamu biyasu yadda suke so,bazasu cutar mana dasu ba,"
  "Nawa suka buƙata"yayi tambayar yana kallon faces ɗinsu,
"har yanzu dai su muke jira,sunce zasu kira su sanar damu,sannan sunce mu kwantar da hankalinmu,Bazasu ta6a cutar dasu ba,Zasu basu kyakkyawar kulawa,kuɗi kawai suke buƙata ba wani abu ba,"Omar ne ya kora mashi jawabin
  Cike da takaici Abba yace"just because of money,suka ɗauke mun ƴa'ƴana?Ae da sun sani sun nemi tallafi a wurinmu konawa ne zamu basu basai sun ɗauke mun su ba,"
   Miƙewa yayi sam babu kuzari ajikinshi,tafiya ya soma yi dakyar yake iya ɗaga ƙafarshi,har sai da yabar wurin Sofas ɗin,Sannan ya dakata da yin tafiyar,ya waiwayo tare da kallonsu,gaba ɗaya idanuwansu na akanshi,
  Magana ya soma yi masu babu wasa a fuskarshi"Omar!"
  "Na'am Abba"ya amsa mashi,
"Rafayet"shima ya amsa mashi"Na'am Daddy,"
   "Na yarda daku sosai,abu biyu nake tsammani daga wurinku,Na fako ku dawo mun dasu junaid,Cikin ƙoshin lafiya,Na biyu kuma ku kawo mun waɗannan gur6atattun mutanen da sukayi garkuwa dasu,Wallahi thumma tallahi idan har ku kasa yi mun waɗannan abubuwan dana lissafa maku,inaso ku sani Za ku rasa ni ne,NA HAR ABADA,daga yau zuwa 30 ga watan da zamu shiga,a kowace rana zan fara sa ran dawowarsu acikin gidan nan!kuma daga ranar ku fara ƙirgen ranakun da su kayi mun saura acikin duniyar nan

  *Tashin hankali!*
Mikewa Mommynsu tayi tare da kallonsu gwanin ban tausayi

Chapters

Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login