Showing 141001 words to 144000 words out of 432432 words

Chapter 48 - Abban Sojoji Book 2 Hausa Novel Complete

gaba dashi,almost 6 mins sai ga sehrish ta fito daga cikin toilet ɗinshi,tunkarar gadon tayi saboda ta ɗauki mayafinta sai da ta kusa dab da gadon sannan idonta suka hango mata Boss Man ɗin nata kwance yana bacci,wani irin bugu taji zuciyarta tayi mata har sai da taɗan ja da baya tana kallonshi,hannu tasa tare da ɗan murza idanunta donta tabbatarwa idonta abunda take gani wai ko gizau ne,amma zahiran taƙara shaida cewa sgr ne da kanshi ya dawo,
Hankali kwance yake baccin shi,ya zagayo da left hand dinshi ta saman sumar kanshi,yayin da hannun damanshi ke asaman shafaffen cikinshi,
Ji tayi bazata juri kallon surar jikinshi ahaka ba saboda gudun jefa kanta cikin matsala,don ba ƙaramin fisgarta yake yi ba,kamar irin magnet din nan,
Har ta kama hanyar fita daga bedroom din nashi cikin sauri taji jelar gashinta na gogar hannunta,tsayawa tayi Cak tunawa da Mayafinta data ajiye asaman gadon nashi kafin tashiga gyara mashi toilet ɗinshi,a hanzarce ta juya tana kallon inda ta ajiye mayafin,waro ido waje tayi cike da fargaba ganin yarda sgr ya mamaye mayafin nata gaba ɗaya,ya kwanta asaman shi,tabɗijan can
Tunani tashiga yi kodai ta tafi tabar mashi mayafin tunda ba iya ɗaga shi zatayi ba,wata zuciyar kuma tace,idan ya farka ya samu mayafin naki asaman gadonshi bakya tunanin cewa zai iya zargin wani abu akanki?dole ya tuhume ki akan miya kawo mayafinki saman shimfiɗarshi,haka in kika fita ba mayafin wani ya ganki kin fito daga part dinshi haka fa,kiyi tunani sehrish barin mayafin risky ne,haka zalika daukarshi ma zai iya zama risky,
Runtse idanunta tayi tamkar ta fasa ihu saboda tsabar takaici,taji haushin cire mayafinta da tayi tun farko da bata jefa kanta cikin matsala ba,
Nan fa tashiga tunanin yarda za'ae ta dauke mayafinta batare da Sgr ya farka daga baccin shi ba,
cikin sanɗa sehrish ta soma tafiya a hankali tana tunkararshi a tsorace batare da sautin takon tafiyarta na fita ba,
Sai da tazo dai dai kusa dashi sannan tashiga cizon yatsa tana tunanin wai ma taya zata janyo mayafin daga jikinshi,Sehrish da kasada,
Hannu tasa tare da ɗan kamo mayafin daya leƙo daga bayanshi tana janshi a hankali don ya sulalo daga bayanshi,amma ko motsi wannan baiyi ba don ba ƙaramar danna sgr yayi mashi ba,gaba ɗaya nauyin jikinshi na akan mayafin taya zata iya janye shi!?
tun tana jan mayafin a hankali yana turjewa har takai ga hasala tashiga janshi da ɗan ƙarfi har sai da sehrish tashiga fitar da wani irin gumi a fuskarta,sakin mayafin tayi tana faman huci,duk da haka bata daddaraba,sai tasa hannu tare da dafa mattress ɗin ta haye saman gadon kaɗan daga gefenshi,hannu takai zata ruƙo mayafin karaf idonta suka sauka akan farar fatar ƙirjinshi,mayar da idonta tayi akan damtsen hannunshi,haryanzu akwai sauran zanen nan nashi na tattoo bai ƙarasa gogewa ba gaba ɗaya,tun farkon zuwanshi 9ja tare da zanen ajikinshi ya dawo kamar tambari ne na mukaminshi ba ƙaramin kyau yayi mashi ba,
Gaba daya sehrish ta shagala da kallon surar jikinshi,kafin tayi wani aune,Sgr yayi wani irin kwakkwaran juyi zai gyara kwanciyarshi,aikuwa gaba ɗaya ya haɗa da sehrish yayi juyin tare da sanya hannunshi yayi hugging ɗinta tighly a faffaɗan kirjinshi,duk a tunaninshi pillow ne ya rungumo hakanne yasa ya matseta sosai a ƙirjinshi kamar yarda ya saba rungume pillow in zaiyi bacci wani sa'in,tashin hankali da ba'a sama shi date,
Tabɗijancan,ƙiris ya rage sehrish ta saki fitsari saboda tsabar tsoran da taji,hankalinta yayi matuƙar tashi,saboda tasan mai zai biyo ba in sgr ya farka yaganta manne ajikinshi,yasan na jiya taimakon shi tayi gudun karya faɗi,na yau kuma mai zai kira shi!?meya kawota saman gadonshi da har ta faɗa jikinshi!?
yarda ya matseta a ƙirjinshi ko kwakkwaran motsi sehrish ba ta iya yi,ba ƙaramin ruƙo yayi mata ba,tunkan ya farka taga irin hukuncin da zai yi mata harta fara zubar da hawaye,kai tsaye kuma hawayen suke shafar fatar jikinshi,
sai faman shessheƙar kuka takeyi ƙasa ƙasa yayin da la66anta ke gogar fatar breast dinshi,gaba ɗaya Wannan jan bakin data shafa ya koma a fatarshi,sosai zanen lips ɗin sehrish ya fito raɗau tare da kalar jan bakinta maroon colour,duk bata lura da hakan ba,saboda la66an nata amanne suke a wurin,
Tana cikin wannan yanayin tajiyo takun tafiyar mutum a falonsa alamar ana tunkaro bedroom ɗinshi,hakan ba ƙaramin firgita sehrish yayi ba,nan take tashiga haɗiyar yawu a tsananin tsorace,
Muryar Abbansu tajiyo yana cewa"Wai har yanzu rafayet bai dawo bane?inaso naji ko sunyi waya da Mommynshi ne game da zuwanta Nigeria,'
"Innalillahi wa'inna ilaihirraji'un,"sehrish ce ta ambaci hakan acikin zuciyarta,"Shikenan na mutu wayyo Allah na,ya Allah ka kawomun ɗauki,daga wannan sai wannan......'bata ƙarasa zancen zucin nata ba tajiyo muryar Marshal Omar yana bashi amsa da cewa"Abba ashe muna da manyan baƙi cikin watan nan,don munyi waya da goggon katsina ma ta sanar dani cewa mu shirya ma zuwanta don in ta tashi zuwan bazata zata yi kuma ba zata tafi ba har sai taga An shafa fatihar kowannan mu.....' ya ƙarasa maganar da dariya a fuskarshi,
Suna tafiya suna nufar bedroom ɗin sgr yayin da suke fira a tsakaninsu,
Abban nasu yace"Albishirinka,"
Cike da zumuɗi Omar yace"Goro,"
"Fari ko ja"? Abban nasu ya tambaya fuskarshi ɗauke da murmushi,
Omar yace"Fari,"
ƙayataccen murmushi Abban nasu ya saki kafin yace"Uncle ɗinku Abusufyan shima yana nan tafe insha Allah,sannan Auntynku azeema tana nan tafe,uwa uba kuma Ammynku itama tana nan tafe,don haka ku shirya don ta sanar dani cewa muddin tazo sai an ɗaura auran kowannanku,da alama zata zo tayi yaƙi da tazuranci ne acikin gidan nan.....'ƙarasa maganar yayi muryarshi ɗauke da dariya,shima Omar dariyar yayi yana girgiza kai yace"Abba Allah yaso ni,ina da wadda nakeso,don haka ni bani da matsalar komai wlh,Alhamdulillah Allah ya kawota Lafiya musha biki,'
Cike da mamaki Abban nasu yace"wai dagaske Omar kana da wadda kakeso?hakan na nufin kayi budurwa baka sanar dani ba"?
ɗaga kai Omar yayi alamar eh,wani irin farin cikine ya cika abban nasu har ya gaza magana sai faman sakin murmushi yake yi yana cewa"Ikon Allah,"

A ƙopar shiga bedroom ɗin sgr suka tsaya suna cigaba da tattaunawa cike da nishaɗi atsakaninsu,

Saboda tsabar tashin hankali har wani zazza6i ya lullu6e sehrish tuni temperature ɗin jikinta yayi wani irin zafi,zuciyarta har wani bugu takeyi daram!daram!!fargabarta karsu shigo su same su a wannan yanayin ita da sgr,
Hayaniyar da suke yi ce,ta fara disturbing ɗin baccin nashi,hakan yasa ya fara motsi alamar zai farka,waro ido waje sehrish tayi cike da fargaba jin alamar zai farka,
Hannunshi ya janye daga ruƙon da yayi ma sehrish,hakan ne ya bata damar kufcewa daga jikinshi,kamar walƙiya haka ta mirgina tare da faɗawa ƙasan gadon,sam bata ji zafin buguwar da tayi ba,tana faɗowar nan ta yunkura tare da miƙewa tayi wuff ta faɗa bayan labulan ɗakin shi,
Shigarta ke da wuya,Abba da marshal suka shigo cikin ɗakin nashi atare bakunansu ɗauke da sallama,
A hankali sgr ya soma buɗe idanunshi dake cike da bacci ga wata irin kasala data mamaye shi don baccin bai ishe saba,daƙyar ya iya sa hannunshi tare da dafa mattress ɗin ya tashi daga zaune tare da jingina back ɗinsa asaman pillow yana kallon Abban nasu tare da Omar sai faman lumshe ido yake yi,
Zama Abban yayi daga gefen gadon nashi yana kallon fuskar kyakkywan yaron nashi yace"Rafayet bacci kuma a irin wannan lokacin?ko baka ga time bane?
Sai lokacin sgr yakai idonshi akan diamond clock ɗin dake manne a bangon ɗakinshi ƙarfe 6:30 na yamma,
lumshe idonshi yayi kafin ya waresu akan Abban nasu yace"Abba bansan time ɗin da baccin ya ɗauke ni ba"
jinjina kai abban nasu yayi
kafin yayi yunƙurin cewa wani abu karaf idonshi suka sauka akan jan bakin sehrish dake zane asaman breast ɗinshi,
waro ido waje abban nasu yayi tare da cewa"Kai me nake gani haka kodai idona ne"?yarda yayi maganar a ruɗe yasa marshal Omar ɗan matsowa daga tsayen da yake ya russina yana ƙare ma Ƙirjinshi kallo,cike da mamaki Omar yace"ba shakka Abba,ba idonka bane wannan alamar sumbata ce,ga zanen la66an mace nan raɗau asaman fatar kirjinshi,
Gaba daya sun gama confusing ɗin Sgr,sam bai gane inda zancen nasu ya dosa ba,"
Hankali atashe Abbansu yace"Rafayet tell me the truth!wa kayi feeding haka har ta goga maka jan baki asaman breast dinka!!!"
Saboda tsabar kiɗima tuni jikin sehrish ya soma tsastsafo da wata irin zufa,duk da sanyin ac dake gauraye da ko'ina,
Ganin yarda sgr ya dabarbarce kamar bai gane kan me suke magana ba,hakan yasa omar ƙarasawa gaban dressing mirror ɗinshi,yasa hannu tare da ɗauko ƙaramin madubin dake ajiye asaman shi,
Ƙarasowa yayi wurinshi tare da saita mashi madubin yarda zai gani da kyau,
Ware manyan idanunshi yayi yana kallon zanen la66an dake asaman chest ɗinshi cike da tsananin mamakin a ina ya same shi.......


*SANARWA SANARWA*💃💃💃💃


*ME TAKEN NA AMARYA HUTAA$$*

*MUNA FARIN CIKIN SANAR DAKU CEWA MUNA BADA HAYAR KAYAN AMARYA(WEDDING GOWN), KAYAN BRIDAL SHOWER, KAYAN BIRTHDAY PARTY, KAYAN FITAR SUNA, SANNAN MUNA BADA HEAD AND SHOULDER, MUNA DA POSS, MUNA ALKYABBAR KAI AMARYA KO TARON WALIMAR SAUKA, MUNA DA KAYAN FULANI FARARE NA YARA DANA MANYA MUNA DA NA AMARYA BLUE BLACK, SANNAN MUNA GYARAN JIKIN AMARYA DA UWARGIDA CIKIN KWANA UKU CAKAL ZAKIGA KIN KOMA TAURARUWA MAI WALWALI. MUNAYIN TURARUKAN WUTA DA HUMRA DA KOLACCAR, KOWANNE KALA KIKE BUKATA AKWAI CIKIN FARASHI MAI SAUKI.*


*LOCATION KANO*

08062073990
Ina kuke mata hamshakai wayanda suka amsa sunan su wajen mazajen su ina mata masu son qamshi shin ko kunsan tsafta bata tafiya seda qamshi ina masu son turare mai riqon gida tareda qamshin shi mai sanyaya zukata mardie collection tazo muku da dadadan turarukanta masu lasting riqon gida harma da jiki ku tuntube mu da nmb kamar haka 08136666994 inda zaku samu kaya kamar haka
Wadrobe balls
Madarar kulleccham
Vaseline kulleccham
Kajiji
Halut
Couscous
Khumrah
Da dai sauransu harda abin wanke toilet yayi tas komi dafe warshi wato BETHALEX METAL ku garzayo kar ayi baku


Ina kuke mata hamshakai wayanda suka amsa sunan su wajen mazajen su ina mata masu son qamshi shin ko kunsan tsafta bata tafiya seda qamshi ina masu son turare mai riqon gida tareda qamshin shi mai sanyaya zukata mardie collection tazo muku da dadadan turarukanta masu lasting riqon gida harma da jiki ku tuntube mu da nmb kamar haka 08136666994 inda zaku samu kaya kamar haka
Wadrobe balls
Madarar kulleccham
Vaseline kulleccham
Kajiji
Halut
Couscous
Khumrah
Da dai sauransu harda abin wanke toilet yayi tas komi dafe warshi wato BETHALEX METAL ku garzayo kar ayi baku

It's not just good ...it's finger linking good faster than fast food, better fine dining.
Snack
Awarah
Farah
Zobo
Samosa
Cup cake etc
Contact me 09063302182or 09012179727.*💋Boss Bature💋*



Join this link to follow my tiktok acct👇

https://www.tiktok.com/@boss_bature?_t=8WKx0lm4jaP&_r=1




قصة حب رومانسية بين سحريش والجراح العام رفايت💋💘❤🤍❤💕💖

Ansamu long page🥱


________________________Zuba mashi ido su kayi suna jiran amsa,Omar yace"pls ka faɗa mana gaskiya kawai,wacece wani abu ya shiga tsakaninka da ita har akasha wannan Love haka?kaga dai daga ni sai Abba babu wanda zaiji abun da ya faru,"wani irin kallo sgr ya wurga yana mashi ƴar harara yace"Omar bana so, ka fara ko"?
  Murmushi Abban nasu yayi kafin yace"abunda Omar ya faɗa gaskiya ne,Son bai kamata ka 6oye mana komai ba tunda Allah dai yasa yau asirikinka ya tonu munga komai,ashe kana kula mata har romance kake dasu asaman gado ko?faɗamun ƴarwa ka kwamushe acikin ɗakinka har akai abun arziƙin nan bansani ba,"cike da zolaya Abban nasu ke magana,
  ɗaure fuska Sgr yayi tare da haɗe girarsa wuri guda ya tsuke small lips ɗinshi yana kallonsu,yarda suka tasa shi gaba suna tuhumarshi kamar wani ƙaramin yaro ba ƙaramin hasala shi yayi ba,gashi sam ya rasa amsar da zai basu tunda bai isa ya ƙaryata abunda suka gani ba asaman ƙirjinshi,don shi kanshi a ruɗe yake da lamarin abun ya ɗaure mashi kai,taya aka samu jan bakin mace raɗau haka asaman ƙirjinshi!?bai gama zancen zucin nashi ba muryar Omar ta katse mashi tunani,
  "Abba zargi fa ya tabbata,kalli ka gani,"Omar ne yayi maganar yayin da yake ruƙo mayafin sehrish dake a ƙasan laps ɗin Sgr ya danne shi,
   dafe kirji abban nasu yayi cike da razana yace"ƙalu innalillahi wa'inna ilaihirraji'un Rafayet!wannan fa?ya akai yazo wurinka"?ya tambaya hankali tashe yana kallonshi,
Runtse ido sehrish tayi daga 6oyen da take bayan labulen ɗakin,hada ƴan matan hawayenta saboda tsoran hukuncin da zata kar6a,
  Cikin sauri sgr ya aza eyes ɗinshi akan mayafin da Omar ya ruƙo a hannunshi just speechless,amace bakin shi ya mutu yama rasa bakin magana abun ya zarce tunaninshi,
  Omar ne yace"Abba tunda kaga yayi tsit ya gaza magana,to ya aikata ɗinne kasan mara gaskiya,ni fatan da nakeyi ma Allah yasa iya mayafi ya cire mata bai........'kasa ƙarasa maganar yayi saboda saukar pillow daya ji a saman fuskarshi,hannu yakai zai ƙara rarumar wani pillow abban nasu ya dakatar dashi da cewa"Wannan fa alamar rashin gaskiya ce,tun ɗazu kaƙi buɗe baki ka ce uffan,sai faman ƴan kame kame kakeyi mana,kaji tsoran Allah ka faɗa mana gaskiya,Rafayet yin hakan kuskure ne bai kamata don kana ra'ayin mace ka runƙa kawota har bedroom ɗinka ba asaman gadonka don ka rage zafi da ita ba,in kaga yarinya kanaso Ni zakayi ma magana sai aje masallaci ashafa fatiha kaga shikenan sai a kawo maka ita ɗakinka babu mai jin kanku,taka ce halak malak.....'
  Zare blue eyes ɗinshi yayi yana kallon Abban nashi,rai a6ace ya ciji la66ansa tare da ɗago pillown hannunshi ya ɗaga sama zai jefa ma Abban nasu a saman fuskarshi,sai kuma ya saki filon a saman katifar,
   Ganin ya dakata yasa Abban nasu cewa"ae fa kai yanzu komai ma zaka iya,saurayin da zai iya kawo mace ɗakinshi har saman gadonshi acikin gidan ubansa meke bazai iya ba Omar? Ya ƙarasa maganar yana kallon Omar dake ƙumshe da dariya yace"of course Abba,ina goyon bayan maganar ka,yanzu sai dai mu bishi da addu'a don na lura yarinyar ba ƙaramin zautar dashi tayi ba tunda gashi har ya gaza buɗe bakinshi yayi mana magana,rashin gaskiya dai baiyi ba,"
  gaba ɗaya sun gama hasala Sgr,yama rasa amsar da zai basu su dukansu,a ƙarshe ma daya rasa abunyi kawai sai ya fashe da dariya unexpected,tsananin mamaki ne ya kamasu ganin Sgr yana 6a66aka dariya yau shi da kanshi,yaushe rabon da suga sgr yayi dariya irin haka,white teeth ɗinsa sun fito rairasss,da wuya kaga yana dariya sai dai wannan murmushin nashi na gefen fuska shima kuma in kaga yayi wannan murmushin tofa zai bada horo ne,don ya iya murmushin mugunta,
   Hannu sehrish tasa a hankali ta ɗan yaye labulen tana leƙensu,ba ƙaramin bugun zuciya taji ba,kasa janye idonta tayi daga kallon kyakkyawar fuskar sgr da yake ta faman dariya kamar zautacce,gaba ɗaya dimples ɗin fuskarshi sun lotsa sosai abun ba'a magana sai wanda ya gani,suman tsaye sehrish tayi amace ta mace wurin kallon fuskarshi,aranta tana maimaita kalmar nan"tabarakallahu ahsanun khaliqin,"
   Har wani duƙar da kanshi yake yi ƙasa yana dariyar hakan yasa sumar kanshi ta ɗan yarfo ta gaban fuskarshi,
  Atare Omar da Abbansu suka haɗa baki wurin cewa"ikon Allah,abun mamaki abun al'ajabi,"
   Tsagaitawa yayi da dariyar lokaci guda ya ɗaure fuskarshi tamkar dariya bata ta6a wanzuwa a fuskarshi ba,takaici ne dama ya ishe shi shiyasa ya fashe da dariyar,
  Cikin sanyin murya yace"joking aside pls,abba nikaina bansan ya akai nasamu zanen lips ɗin nan asaman chest ɗina ba,sannan bansan ya akai mayafin nan yazo bedroom ɗina ba,na rasa ta yarda zansa kuyi understanding ɗina,gaba ɗaya kunyi confusing ɗina,kun tsareni da tambaya kamar wasu lauyoyi,that's why nayi shiru bance komai ba,"ya ƙarasa maganar a kasalance,
   Murmushi Abban su ya saki yana kallon face ɗinshi,bakomai ya faɗo mashi araiba face Mommynsu,komai na fuskarshi irin na mahaifiyarshi ne,yafi kama da ita amma akwai wasu abubuwan daya ɗauko na Abbansu,
   "Zan shiga toilet,"ya faɗi tare da saukowa daga saman gadon ya kama hanyar shiga toilet ɗin,
   Bin bayanshi su kayi da kallo har ya shige cikin toilet ɗin,
Sannan Suka janye idanunsu,cikin sauri Omar ya samu wuri tare da zaunawa yana fuskantar abbansu ya ruƙo hannunshi tare da cewa"Abba,dan Allah ka aurar damu tare, nida Rafayet,kayi mun wannan alfarmar"
  Murmushi Abbansu ya ɗanyi kafin yace"Omar bangane me kake nufi ba,har yanzu ɗan uwanka bai janye ra'ayin shi akan mace ba,ni kuma banson na takura mashi,duk da banda burin daya wuce wannan nima,inaso naga auran kowanne daga cikinku,musamman auran shi saboda ina tunanin cewa in soyayya ta shiga zuciyarshi zai rage wannan zafin kan nashi,zai sassauto ya zama tamkar kowa,idan har rafayet baiyi aure ba ya tsaya akan bakanshi,tabbas za'ayi asarar namiji har namiji Omar,bansan ya zanyi dashi ba,"yanayin da abban nasu yayi maganar zai tabbatar maka da cewa abun ba ƙaramin ciwo yake masa ba,
  "Abba kadaina cewa bakasan yarda zaka yi dashi ba,shifa ɗanka ne halak malak Allah ya mallaka maka,kuma kana da iko Akanshi,idan yau kaso Abba gaba ɗayanmu zaka iya yi mana aure batare da son ranmu ba ko batare da saninmu ba kuma dole muyi maka biyayya,"
   zuba mashi ido Abban yayi yana sauraran bayanin shi,
Ƙasa ƙasa da murya Omar yayi gudun kada Sgr yafito daga cikin toilet ɗin yaji abunda suke tattaunawa,
  Yasa shi yin hakan sannan yaci gaba da cewa"Abba,namiji irin rafayet,aure akeyi masu batare da saninsu ba,sai dai kawai suji an ɗaura auran...  "
  Katse shi abban nasu yayi da cewa"baka tunanin cewa zai iya sakin matar anan take,kasan shifa ba'ayi mashi dole,"?
    Murmushi Omar yayi tare da cewa"Abba ka fahimta mana,kaifa kake iko dashi,ka sama mashi mace ta gari wadda kasan cewa bazaiyi dana sanin zama da ita ba,ko kuma ni kaban za6i zan sama mashi macen data dace da rayuwarshi,ka aura mashi ita batare da sanin shi ba,sai bayan an ɗaura auran ka ware rana ɗaya ka sanar dashi cewa Umarnine ka bashi amatsayinka na mahaifinshi,in ya kuskure kuma yasan sauran,"
  dariya sosai Abbansu yayi yana sauraron omar dakyar

Chapters

Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login