Showing 432001 words to 432432 words out of 432432 words
Chapter 145 - Abban Sojoji Book 2 Hausa Novel Complete
ace zan iya mayar da ciwonshi jikina da nayi hakan,junaid bai ta6a shan wahala rayuwarba,Sae wannan karan da ƙaddara ta rutsa shi....."
"Mu gode ma Allah junaid yana raye,duk yarda suka so su cutar dashi,basu ci nasara akanshi ba,domin kuwa junaid kainuwa ne dashen Allah,badai mutun ba,lokacin da muka kawo shi asibitin nan,jinin jikinshi Yayi ƙanƙanta,cikin sa'a likita ya gwada jinina,kuma aka dace yayi dai dai da nashi,gashi nan ana ƙara mashi,Amma yana bukatar jini sosai,"
*ƙarin Bayani*
Abunda ya faru lokacin da Sehrish ta tura saƙonnin nan cike da saran Ya mu'allim zai gani,malaman da ta tura ma saƙon daga ciki akwai numbar Ya mu'alim,Yaga Saƙonta saƙonta sai kuma Aka kirashi a waya ana sanar dashi cewa ɗalibarsa na nemanshi,Sauran malaman data tura ma sakone suka sanar dashi,An turo masu saƙo ana nemanshi,Wannan dalilin ne yasa Ya mu'alimm Ya shirya zuwa gidan,tun lokacin baya ya ta6a zuwa gidan security guards ɗin gidan suka hanashi wuce wa,baisamu shiga ba a wannan lokacin,Sai yau daya samu saƙonnin nemanshi da sehrish keyi,Shi ne ya yanke shawarar Ya fara zuwa gidansu Amrish don tayi mashi jagora zuwa gidansu sehrish ɗin su tafi atare,Da yake ya ta6a zuwa gidansu Amrish lokacin da tayi jinya,kuma cikin sa'a ya zo adaidai lokacin da suke buƙatar taimako,Kunji yarda akai Allah ya hadasu dashi Har ya ɗauke su,
Saboda halin da Abban junaid ke ciki,Ya mu'allim Ya basu shawarar su ɗauki junaid su koma dashi Can Sgr hospital ɗin,Don A haɗashi da mahaifinshi in yaso sai acigaba da jinyarshi acan asibitin,Sai da suka tsaya Jinin ya ƙare sannan Likita ya sallamesu,Suka ɗauke shi a back seat ɗin motar Ya mu'alim Aka shigar da junaid,Sehrish ta shiga ta ruƙoshi ajikinta,bawan Allah ya zama tamkar lagwanin filita jikin sae kerma Yake yi sam baya acikin hayyacinshi,Mazaunin driver Ya mu'allim Ya shiga,Amrish ta zauna gefenshi,Ya tashi motar,a tsanake yake driving ɗinsu,Amrish sae faman zabga murmushi take yi,burinta Ya cika,junaid zai koma wurin ƴan uwanshi,Sehrish kuwa ba'a magana,Bakinta yaƙi rufuwa,Kamar wadda akayi ma Albishir da gidan Aljanna,Tsabar farin ciki ne kawai,Ta ƙankame junaid ajikinta kamar ta mayar dashi cikin cikinta,Saboda tsabar ƙaunar da take yi ma ɗan uwanta,A ranta tana ayyana irin farin cikin dasu Babban Yaya zasu yi idan suka ga junaid bai mutu ba,
Slowly motarsu ta ƙaraso cikin katafaren asibitin SGR................
*dakwai yiyuwar littafin Abban Sojoji yakai farkon march,Ba kamar yarda nace ba ƙarshen February,Amma idan kuna son ayi maku after 3 years,kuyi mun magana,sai mu katse shi,ra'ayinku nakeson ji,littafin yazo ƙarshe masu tunanin zai kai azumi,Aniyarku tabi ku😂*
*masu son karanta Littafin Abban Sojoji su tuntu6i layina,Message za'a tura mun ta whatsapp banda phone call*