Showing 177001 words to 180000 words out of 432432 words

Chapter 60 - Abban Sojoji Book 2 Hausa Novel Complete

goggon katsina ta faɗo cikin falon tana murna ganinsu yasa ta aza hannu akai tana cewa"La'haula masalli ila!acikin gidan nan ake wannan baɗalar?
A firgice suka ɗago suna kallonta hankali tashe,kamar yarda itama take kallonsu hankalinta atashe,
   sunnar dakai ƙasa sukayi suna ƴan kame kame,
   Jinjina kai tayi tare da cewa"munafukan Allah,yau asirinku ya tonu,dama abunda kuke aikatawa kenan duk in nashige cikin ɗaki ko?cike da tuhuma tayi masu maganar,. 
   buɗe baki saude tayi da niyar tayi magana,goggo tayi mata dakuwa da hannunta tace"Ungo nan,ja'ira dama kar nake kallonki,munafuka ashe shiyasa kullum nace zan maidaki rugarku sae kiyi mun narai narai da ido kamar na mujiya kina cewa bakison ki koma kiwon shanu,ashe kina nan kin kama wani shanun kina ta tatsa,ina nan sake da baki,Allah kaɗae yasan me kuke aikatawa,ni ban yarda daku bama Allah,ka fadamun gaskiya Harisu iya shinshine-shinshinen kuka tsaya ko kun zarce nan? Tayi maganar tana wurga mashi harara,duk kunya ta gama rufe shi,
  Cike da jin kunya suka sunnar dakai ƙasa atare suna sauraronta,sae da takai aya sannan Dr haris yace"Mommyna ni fa ba abunda ya shiga tsakanina da ita,wannan ma da Allah yasa kika gani sharrin shaiɗan ne, ba yin kanmu ba......'bai ƙarasa maganarba,goggo ta tsige kallabin dake kanta,ta wurga mashi shi kafin ya ƙarasa saman fuskarshi,cikin sauri saude ta tarbe kallabin goggon a hannunta,

  Baki asake goggo tace"Saude! don tsabar iya rashin kunya da tsageranci akan idona kike kare mashi don na jefe shi da kallabina?wato ya saba baki kina sha shiyasa kika raina ni ko"?
   Waro ido waje Saude tayi tana kallonta hankali atashe tace"nashiga uku goggo,me kike nufi daya saba bani ina sha"?
  Harara goggon katsina ta watsa mata tana murguɗa mata baki tace"nima bansani ba,nasan dae kina bashi kuma shima yana baki,Allah ya shiryeku in masu shiryuwa ne,sae yanzu nagane kuskuren danayi na barin ki acikin gidan nan,batare da an shafa fatihar Auranku ba,gashi yanzu kuna ƙokarin haifo min ɗan gaba da fatiha.....'fashewa tayi da kuka,cikin shesshekar kuka taci gaba da cewa"Allah sai kin bar gidan nan saude...bazan cigaba da zama dake ba,kina lalatamin yarona,kafin zuwanki gidan nan harisu ko kalmar kiss baisani ba,amma sae gashi yau na same shi yana ƙoƙarin manna maki kiss kamar wani maye,yabi ya kanenayeki don tsabar jaraba irinta ƴaran zamani,acikin gidajen iyayensu ma bazasu iya kame mutuncinsu ba,ni bandamu ba duk abunda zakuyi kuyi,amma ba agaban idona ba.....'
  Atare Dr da saude suka kalli juna cike da mamakin jin abunda goggo tace,wato komai zasuyi suyi amma ba'a gaban idonta ba,tashin sense,
   Miƙewa haris yayi tare da takawa inda take ya ruƙo hannunta,cikin lallashi yace"Goggo pls komai ya wuce,kuskure ne mun riga da munyi,kuma bazamu ƙara ba,kiyi haƙuri kinji mommyna"
   fisge hannunta tayi daga cikin nashi tace"kada ma Allah yasa ku daina,ni wannan ba damuwata bace,yanzu ni bani da sauran damuwa zan tattara nabar maku gidan,idan kunga dama kuyi aure,in baku ga dama ba ku cigaba da abunda kuka saba,Allah dae na kallon mutun,'
  Tayi maganar tana wurga ma saude harara,haushinta takeji kamar ta rufeta da duka,
   "Mommyna,ina zakije ne?naji kina cewa zaki bar mana gidan"?cike da damuwa yayi maganar
  Murguɗa mashi baki tayi tare da cewa"gidan Abba mana,zanje inga Abusufyan ɗina ne,yanzun nan zan shirya in tafi,'
   "Mommyna pls ki bari sae gobe zan kaiki da kaina har can ki ganshi,amma yanzu marece yayi fa,naji kamar ana kiran sallar magriba ma,dare zai yi mana a hanya,'cikin lallami yake yi mata magana,don yasan halinta bamai iya mata,
  Turo bakinta tayi tana gunguni kamar wata ƙaramar yarinya tace"Allah bamai hanani zuwa,sai naje naga Abusufyan dina tare da ƴa'ƴanshi,'
  ɗaure fuska babban likita yayi tare da cewa"Muddin kikasa ƙafa kika bar gidan nan,akwai karnukan layi na nan suna ran gadi acikin anguwar nan,da zarar sunyi arba dake hmmmmmm Allah kaɗae yasan mai zai biyo baya,
   tunda taji ya ambaci sunan karnuka,nan take jikinta ya shiga kerma,saboda mugun tsoransu take ji,bata ƙara tanka masu ba,jiki na rawa ta wuce bedroom ɗinta,
  Ajiyar zuciya Dr haris ya sauke tare da juyawa ya kalli saude dake ta faman sakin murmushi yace"wlh naji kunya sosai,mommyna bata da saiti,komai yazo bakinta faɗinshi takeyi,yadda kasan rakwa6a66iyar motar da burki ya kwace mata,'. 
  Fashewa da dariya sukayi,daga bisani Saude ta tsagaita da yin dariyar tace"babyna,addu'a yakamata muyi mata akan Allah ya bata lafiya,idan tadawo dai dai mu kanmu zamuji daɗi sosai,saboda goggo tana da kirki sosae,'
  Murmushi Dr haris ya kuma yi tare da cewa"insha Allah zamu cigaba dayi mata addu'a Akan Allah ya bata lafiya,'
 
_💋Boss Bature💋_
  

Wuraren ƙarfe 6:30 jirginsu Abusufyan yayi landing a Nnamdi Azikiwe International Airport Abuja,
gaba ɗaya su Abba sun gama hallara a airport ɗin suna jiran saukowarsu daga cikin jirgin,kowannansu a ƙagare yake daya ga fuskar Abusufyan da suka jima basu sanyashi a idanunsu ba,nikaina wlh amatse nake dana ga wannan Abusufyan ɗin da kowa yake ta ɗokin ganinshi,

Gaskiya namatsu,namatsu namtsu, inga wannan ɗan tahalikin,

daga cikin waɗanda suka hallara domin tarbar shi akwai Abbansu tare da junaid,kanal yousouf da kuma Irfan,jabeer,khaleed da kuma fawan,bayansu kuma akwai Twins suma duk suna zazzaune asaman waiting seats na airport din suna jiran ƙarasowarshi,suna zaune suka ji ana annoucement din ƙarasowar jirgin daya zo daga ƙasar turkey,

Tsantsar farin cikine ya bayyana a fuskokinsu,duk suka zuba ido suna jiran 6ullowarshi,


Passengers ne suke ta fitowa daga cikin jirgin kowannansu fuskarshi asake,sae bullowa sukeyi ta ko'ina,
Sannu a hankali ya aza kafarshi asaman matattakalar benen,masha Allah sae dae muce tabarakallahu ahsanul khaliqin,
  giant ne yana da tsayi da kuma cikakkiyar sura mai jan hankali,ta ko'ina Allah ya hore mashi,a launin fata kuwa chocolate colour ne,kala mai tsada,fatar nan tashi taji hutu ko a ido ka kalleta sae kasan cewa ba ƙaramin hutu taji ba,jikinshi na sanye da Suit maroon colour launin glass ɗin dake manne a fuskarshi,wani irin daddaɗan kamshi ne ke fesowa daga jikinshi,hannunshi na sanye da tsadaddan agogo na diamond,
  A hankali ya ɗaga hannunshi tare da kai shi saman fuskarshi ya zame glass ɗin da ke manne a fuskar,lumshe idanunshi yayi tare da waresu a hankali yana kallon mutanen dake shawagi a wurin,
  Yayi kewar ƙasar shi sosai,shekara kusan goma sha wani abu,bai taka ƙasar ba,sai yau Allah ya dawo dashi,
"Ƙaddara ta sake dawo dani wannan ƙasar" ya furta hakan yayin da yake ƙara ruƙe trolley ɗin hannunshi,jan shi ya shiga yi yayin da yake ci gaba da saukowa daga saman matattakalar jirgin,
  Dirar shi ke da wuya,yaji an ambaci sunan shi da wani irin sauti yaji ance"Uncle Abusufyan! "firgit yayi tare da kai idanunshi wurin da yaji an ambaci sunan,
  Waro ido yayi waje fuskar nan dauke da farin ciki ya ambaci sunan Junaid,
  Da gudun gaske junaid ya ƙarasa tare da faɗawa saman faffaɗan ƙirjinshi,ya kankame shi sosai kamar zai shige jikinshi,
  sosai Abusufyan ke sakin dariyar farin ciki yana ƙara bubbuga bayan junaid da hannunshi yana cewa"WOW MASHA ALLAH MY BABY BOY KAINE KA KOMA HAKA,GASKIYA NAYI MISSING ƊINKA SOSAI JUNAID,AM REALLY GLAD TO SEE U ........'
ya ƙarasa maganar tare dasa hannunshi ya ɗago junaid daga saman kirjinshi yana kallon fuskarshi,yayi mamakin girman yaron lokacin da daya tafi yana ɗan ƙaraminsa ya barshi,

ganin hawaye na sauka asaman fuskar junaid yasa shi cewa"meya faru junaid?kai da zan ga kana farin ciki sae kuma naga hawaye a idanun ka why?
  Cike da shagwa6a junaid yace"uncle bakaine ka tafi kabarmu ba,shekara da shekaru ka manta damu,ba ka damu da kazo ka ganmu ba,"
   ƙayataccen murmushi Abusufyan ya saki tare da cewa"Am really sorry my boy,nasan ni mai laifine ayimun afuwa pls,shiyasa nadawo nigeria don in goge laifina....'
  Yana cikin maganar tashi sai ga su Abba sun ƙaraso wurinsu tare dasu kanal yousouf,
  Gaba daya suka ƙarasa one by one suna rungume shi ajikinsu cike da nuna farin cikin ganinshi,
Sae da ya kammala rungumarsu,sannan ya ɗago yana kallon ɗan uwan nashi daya tsaya gefe guda,yana kallon shi fuskarshi aɗaure alamar fushi yake dashi,
Tunkarar shi yayi zai rungume shi,cikin sauri Abba ya dakatar dashi ta hanyar ɗaga mashi hannu yace"karka kuskura ka ƙaraso nan,bana son ganinka,ni banma san ya akai nazo airport ɗin nan ba,"
Hannu uncle abusufyan yasa tare da kama kunnan shi yana cewa"Am sorry my bro,ayi mun aikin gafara nasan nayi laifi,amma zan gyara kuskure na,yanzu dae ka barni in rungumeka kona ji sanyi araina,'
Buɗe mashi hannu Abba yayi alamar ya taho,faɗawa jikin shi abusufyan yayi sosai suka rungume junansu,tuni hawaye suka cicciko a idanuwan kowannansu
muryar abbansu junaid tamkar zaiyi kuka yace"Hakanan ka tafi ka barni batare da sani na ba,me yasa kayi mun haka abusufyan?duk irin son da nake maka,ka tafi ka barni da raɗaɗin rashin ka acikin zuciyata,abun ba ƙaramin ciwo yake yi mun ba,"
ya ƙarasa maganar a lokacin da yake ƙoƙarin raba jikinshi daga na Abusufyan,
Jikin shi yayi mashi sanyi,duk sai yaji ba daɗi,kuma bai kyauta masu ba,
daƙyar yace"Ka yafe mun ɗan uwana,na cutar dakaina,na raba kaina da ƴan uwana,bawai don bana son kasancewa atare da ku ba......'
Kasa ƙarasa maganar yayi saboda wani abu daya tuna a rayuwarshi daya ta6a faruwa dashi...,
Jinjina kai kawai Abbansu junaid yayi tare da ruƙo hannunshi yace"Komai ya wuce,tunda kadawo nigeria,kuma inaso ka sani bazan ƙara bari kabar ƙasar nan ba,komai kakeso ka faɗamun zanyi maka shi,in ma akwai wani abu dake damunka duk ka sanar mu,zanyi ƙoƙari wurin ganin na share maka hawayenka,dama ni sae da raina ya bani cewa bada son ranka kabar ƙasar nan ba,akwai wani abu dake faruwa wanda kaƙi sanarma kowa.....'
"Abba,uncle fa ya gaji sosai,ya kamata muyi hanzarin wucewa gida tare dashi,idan ya kwanta ya huta sae mu ƙara gaggaisawa dashi,"
Kanal yousouf ne ya katse mashi hanzarinshi,
murmushi abba yayi tare da janyo hannun abusufyan suka kama hanyar fitowa daga airport din,gaba dayansu suka ɗunguma izuwa wurin da suka ajiye motocinsu,murmushi kawai Abusufyan keta saki yana kallon ƴan uwan nashi kamar ya haɗiyesu haka yake ji,saboda tsabar son da yake yi masu.

Finally Uncle Abusufyan ya ƙaraso nigeria,saura mommynsu junaid da kuma Ammi,su muke jira,

Koda suka ƙaraso cikin gidan,anan main palour din suka zazzauna ana ƙara gaisawa da juna,a ƙarshe abba ya ruƙo hannun ɗan uwan nashi yakai shi izuwa cikin bedroom ɗin da aka tanadar mashi,katafaren ɗakinsa da zai zauna aciki,sae da abba ya tabbatar da cewa Abusufyan ya shige cikin ɗakin sannan yaja mashi ƙopar ya rufe,
Gaskiya zanso kuga irin farin cikin da ahalin nan suke yi na zuwan Uncle dinsu Abusufyan,

Wuraren ƙarfe 11 na dare lokacin komai ya lafa,junaid ya nufi bedroom ɗin sehrish yana nemanta ganin bata fito ba,lokacin daya je,ɗakin nata ya shiga wayam yaga babu kowa,jiki na rawa ya wuce ɗakin azmee yana tambayarta ina reesh take,azmee tace"tun ɗazu dana kai mata lunch ban ƙara sanyata a cikin idanuwana ba,"fitowa junaid yayi daga ɗakin azmee hankalinshi a matuƙar tashe,saƙo da lungu na gidan ya dinga bi yana dubawa bai ganta ba,lokacin daya tabbatar da cewa sehrish bata acikin gidan,jiki na rawa ya wuce ɗakin Abbansu anan ya same shi zaune shi da Uncle abusufyan suna ƙara tattaunawa a tsakaninsu,
Ganin yarda junaid ya faɗo masu ba sallama yasa suka shiga tambayarshi ko lafiya,hankali tashe yace"Abba,sehrish nake nema,na duba ko'ina acikin gidan nan bata nan,'
cike da mamaki abusufyan ya maimaita sunan Sehrish abakinshi,
Abba kuma yace"tun yaushe tabar gidan?baka je ɗaukota daga school bane"?
"Abba naje,dakaina na ɗaukota kuma na kawota acikin gidan nan,amma yanzu na duba ko'ina babu ita,"
Jin wannan maganar ta abba yasa shi miƙewa daga zaunen da yake gefen gadon ya nufi junaid yana cewa"muje wajen,"
Juyawa junaid yayi suka fuce atare,yayin da suka bar Abusufyan azaune cikin ɗakin,

Hankalin kowa fa ya tashi,abun sai ya baka mamaki,ashe ba ƙaramin so sukeyi ma yarinyar ba,duk wanda akace mashi Sehrish ta 6ace ba'a ganta ba,sae kaga ya fito daga bedroom dinshi yadawo falo cike da damuwa,gaba daya sae da kowannansu ya hallara banda Sgr,saboda tun ɗazu yabar cikin gidan,
Hankalin Marshal omar ba ƙaramin tashi yayi ba,jin ana neman Sehrish,sam ya manta da bata a cikin gidan,tunda junaid yayi musanyarta da jahad,ya tura sojojin nan don su nemo mashi jahad,su kayi arba da yarinyar saboda kamanceceniyar dake atsakaninsu yasa sukayi tsammanin Jahad ce,yayin da suka bi ta da nufin su kamata ita kuma ta watsa aguje,tabar masu school bag ɗinta a ƙasa,babu irin neman da basuyi mata ba,amma babu ita ba alamarta 6at ta 6ace masu.........Shin Ina sehrish ta shiga ina!?

"Abba wai meke faruwa ne naga kunyi curko-curko anan,kamar kuna cikin damuwa,"hajiya azeema ce ke tambayarshi a lokacin da take ƙarasowa inda suke tsaitsaye,duk sun hallara gaba dayansu kowa yana cike da zullumin abunda zai biyo baya game da yarinyar da ta 6ata,
"Yarinyar dake taya azmee aikice ta 6ace,an nemeta an rasa babu ita acikin gidan nan,"ya bata amsa fuskarshi cike da damuwa,
Fawan yace"Abba ita yarinyar bata da waya ne"?
junaid ne ya bashi amsa da cewa"akwai waya a hannunta,amma na kira layinta a kashe,tun ɗazu nake trying still switch off,
Hajiya azeema tace"gaskiya akwai matsala,yakamata ayi hanzarin binciko inda yarinyar take,"
Gaba daya duk sun shiga damuwa,musamman junaid hada ƴan hawayenshi,
Gyaran murya Marshal Omar yayi suka mayar da hankalinsu akanshi,sannan yace"kada ku damu,insha Allah za'a ganota,na zuba sojoji acikin garin nan suna nan suna bibiyarta,kuma insha Allah zasu gano mana ita,"
Abba yace"naji daɗi sosai Omar,Allah yasa su gano mana ita,hankalina bazai ta6a kwanciya ba in har yarinyar nan bata dawo cikin gidan nan ba,'
Ya ƙarasa maganar tare da kallon su fawan yace"kuje ku kwanta,insha Allah za'a gano ta,"
Har suna haɗa baki wurin cewa"Abba,ba zamu iya runtsawa ba,in har ba'a ganta ba,zamu zauna anan ne mu jira har Allah yasa ta bayyana,'
Abun ba ƙaramin mamaki ya ba Abbansu ba bai ta6a tunanin cewa sun damu da yarinyar ba,sae yau,abunda ke faruwa ita mace ce,kuma matashiya dole kowa yayi zullumin ina ta shiga,waya dauketa,sace ta akayi ko kuma cutar da ita akayi,?

*Sehrish*


*SANARWA SANARWA*💃💃💃💃


*ME TAKEN NA AMARYA HUTAA$$*

*MUNA FARIN CIKIN SANAR DAKU CEWA MUNA BADA HAYAR KAYAN AMARYA(WEDDING GOWN), KAYAN BRIDAL SHOWER, KAYAN BIRTHDAY PARTY, KAYAN FITAR SUNA, SANNAN MUNA BADA HEAD AND SHOULDER, MUNA DA POSS, MUNA ALKYABBAR KAI AMARYA KO TARON WALIMAR SAUKA, MUNA DA KAYAN FULANI FARARE NA YARA DANA MANYA MUNA DA NA AMARYA BLUE BLACK, SANNAN MUNA GYARAN JIKIN AMARYA DA UWARGIDA CIKIN KWANA UKU CAKAL ZAKIGA KIN KOMA TAURARUWA MAI WALWALI. MUNAYIN TURARUKAN WUTA DA HUMRA DA KOLACCAR, KOWANNE KALA KIKE BUKATA AKWAI CIKIN FARASHI MAI SAUKI.*


*LOCATION KANO*

08062073990
Ina kuke mata hamshakai wayanda suka amsa sunan su wajen mazajen su ina mata masu son qamshi shin ko kunsan tsafta bata tafiya seda qamshi ina masu son turare mai riqon gida tareda qamshin shi mai sanyaya zukata mardie collection tazo muku da dadadan turarukanta masu lasting riqon gida harma da jiki ku tuntube mu da nmb kamar haka 08136666994 inda zaku samu kaya kamar haka
Wadrobe balls
Madarar kulleccham
Vaseline kulleccham
Kajiji
Halut
Couscous
Khumrah
Da dai sauransu harda abin wanke toilet yayi tas komi dafe warshi wato BETHALEX METAL ku garzayo kar ayi baku


Ina kuke mata hamshakai wayanda suka amsa sunan su wajen mazajen su ina mata masu son qamshi shin ko kunsan tsafta bata tafiya seda qamshi ina masu son turare mai riqon gida tareda qamshin shi mai sanyaya zukata mardie collection tazo muku da dadadan turarukanta masu lasting riqon gida harma da jiki ku tuntube mu da nmb kamar haka 08136666994 inda zaku samu kaya kamar haka
Wadrobe balls
Madarar kulleccham
Vaseline kulleccham
Kajiji
Halut
Couscous
Khumrah
Da dai sauransu harda abin wanke toilet yayi tas komi dafe warshi wato BETHALEX METAL ku garzayo kar ayi baku

It's not just good ...it's finger linking good faster than fast food, better fine dining.
Snack
Awarah
Farah
Zobo
Samosa
Cup cake etc
Contact me 09063302182or 09012179727.
 
  *💋Boss Bature💋*



Join this link to follow my tiktok acct👇

https://www.tiktok.com/@boss_bature?_t=8WKx0lm4jaP&_r=1




قصة حب رومانسية بين سحريش والجراح العام رفايت💋💘❤🤍❤💕💖




Ga duk maison karanta littafin Abban sojoji,zai biya 300 ne,za'a tura mashi tundaga farko har inda muka tsaya,kuma zai cigaba da samun update dinshi akai akai,ga wanda ke buƙata zai tura mun message ta whatsapp ɗina (08103884440) kada ku bari abaku labari,




"Aunty azmee wai meke faruwa ne naga kowa ya hallara a falo fuskokinsu kuma da alamun damuwa atattare dasu,wani abu ya faru ne"?Hayamm ce tayi mata wannan tambayar,fitowarta kenan daga bedroom dinta,da alama tafara bacci,sae faman hamma takeyi,
Azmee dake tsaye daga wurin corridor ɗin shiga bedrooms ɗinsu,ta juya tare da kallonta tace"Ba dole ki ganmu a haka ba?Sehrish ce ta 6ata an nemeta an rasa,shiyasa kika ga kowa hankalinshi atashe,
  cike da mamaki hayaam tace"Wai don sehrish ta 6ata shine kowa ya tashi hankalinshi haka?suka hana idanunsu bacci saboda wannan yarinyar?sae kace dae wata ƙanwarsu ko ɗiyar Uncle ɗinsu?menene alaƙarsu da ita da har zasu sanya damuwa aransu don ta 6ace!ƴar aiki fa ce ba wata tsiya ba,"
   "Hayaam!Anya kina cikin hayyacin ki kuwa?mutun fa akace maki ya 6ace ba dabba ba!don me ba zasu tashi hankalinsu ba?don tana ƴar aiki?kamar kece fa ace kin 6ata acikin gidan nan!kina nufin kada kowa ya damu kenan tunda ke ma baki da irin alaƙar da kika ce dasu kamar dae ita din yarinyar!in fact sun ma fi sabawa da ita yarinyar,saboda hidimar da takeyi masu kullum tana cikin yi masu ɗawainiya acikin gidan nan,ta wuce ƴar aiki a wurinsu,tamkar ƴar uwarsu ta Jini suka ɗauke ta......'
  Tunda Azmee ta soma magana,Hayaam take kallonta Rai a matuƙar 6ace jin maganganun da take gaya mata,bata ta6a tunanin cewa azmee zata iya furta mata su ba,a tunaninta matsayinta yaci ace tayi respecting ɗinta amatsayin wadda yayyanta ke auran wasu daga cikin matasan gidan,
  "Aunty azmee yanzu saboda waccen ƙasƙantacciyar yarinyar kike gayamun magana!kin manta matsayina acikin gidan nan ne!ya kamata ki iya bakinki,ina girmamaki ne kawai saboda girma da darajar da kike dasu awurina,"
  Ƙarasa maganar tayi tana faman huci,saboda an 6ata mata rae,nace sannu ƴar masu gida,
  girgiza kai kawai Azmee tayi,dama tasan halin hayaam ciki da bai,bata da kunya futsararriya ce ta gidan gaba,tuna wannan yasa ta fasa mayar mata da martanin maganganunta,
  murmushi kawai tayi kafin tace"Hayaam

Chapters

Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login