Showing 387001 words to 390000 words out of 432432 words

Chapter 130 - Abban Sojoji Book 2 Hausa Novel Complete

mun da sha'awata,tunda nake ma ni ban ta6a jin sha'awar mace ba,Sai da nayi tozali da kyakkyawar surar ƙirjinki,Nayi mamakin yadda kika Cika ta ko'ina,ba kamar yadda na sanki ba,Kai gaskiya Abusufyan ya iya raino,Naira ta zauna maki shiyasa kika canza,"
A ruɗe Sehrish take furta"Allahumma ajirni fil masibati wa'aklifni khairan minha,tsananin tsoro ne ya kamata,ganin ya sanya hannu yana ƙokarin tattare jallabiyar dake ajikinshi,Tashin hankali!
..girgiza kai ta shiga yi tana fadin"karka kuskura kace zaka kusanto ni,Ni matar aure ce,"a ruɗe tayi maganar tana ƙoƙarin saukkowa daga saman gadon'..
   "Oh ashe ke matar aure ce,wannan ae ba wani abu bane dan naci amfanin gonar wani,"
   Durowa tayi daga saman gadon tare da nufar ƙopar fita daga ɗakin,Aikuwa a zafafe Ya sayyadi ya biyo bayanta,kafin tayi wani yunkuri ya damƙi rigar baccin dake ajikinta,nan take rigar ta zame har izuwa mid back ɗinta,Fashewa ta kuma yi da matsanancin kuka tana ambaton Sunan Daddynsu,ƙoƙarin kwale mata rigar yakeyi gaba dayanta amma ta hana hakan,Ba zato ba tsammani taji yana goga mata abun gabanshi ta bayanta,Wa'iyazu billah,Daddagewa tayi da iya karfinta na ƙarshe,Ta kai mashi naushi a tsakiyar cikinshi,Amma wani abun mamaki ko gezau baiyi ba,Kamar ta naushi ƙarfe,kiciniyar ƙwace kanta ta shiga yi daga hannunshi,Ji take kamar ta haɗiyi zuciya ta mutu saboda takaici,
  Saukar harshenshi taji asaman fatar bayanta,kamar wani maye haka ya dinga lashe shi,
  "Wayyo Allah na Oumma!na shiga ukku nabani na lalace!"cikin fitar hayyaci Sehrish ta samu hannunshi daya zagayo dashi ta gabanta,Ta daddage ta gartsa mashi cizo har saida ta fasa fatar hannunshi,raɗaɗin da yaji ne yasa shi yin saurin sakinta,A hanzarce ta sanya hannunta tana ƙoƙarin buɗe ƙopar ɗakin,Sayyadi ya taɗiyo ƙafarta gaba daya ta kife ƙasa,kanta ya bugu sosai,fashewa tayi da matsanancin kuka tana bugun floor ɗin da hannunta,Ta rasa ina zata tsoma ranta,jin motsinshi yasata yin saurin miƙewa zaune tana ja da baya,
  Cikin Shesshekar kuka take Ambaton sunan Daddynsu da sunan Oummansu don su kawo mata ɗauki,
  Hannayenshi ya sanya tare da tattaro jallabiyar jikinshi ya ɗage ta sama har izuwa saman cikinshi ya naɗe ta,tsikar jikinta ce ta fara tashi,ganin uban cunkoson gashin jikinshi mara kyan gani,hannu yasa ya kwale gajeran wandon nashi,Rasss taji mummunar faɗuwar gaba,
  Dariya ya dinga yi yana nuna mata abun nasa yayin da yake tunkararta tana ƙoƙarin ja da baya,
  Koke koken da sehrish keyi ne ya fara kai mata ziyara cikin kanta,lokaci guda Kwakwalwarta ta fara tariyo mata kukan ƴa'ƴanta yayin da suke ambaton Sunanta,Oumma Oumma aduk lokacin da suka shiga wani hali,Allah ne ya farfaɗo da ita,Hannu tasa tare da dafe kanta wani irin raɗaɗi ta dinga ji yanayi mata,tunkafin ta buɗe idanuwanta ta soma ambaton Sunayensu Sehrish Hosana Jahad,wani ihu da sehrish ta kurma ne yasa ta yin firgit ta mike zaune daga saman gadon,Zazzare idanuwanta tayi akan sayyadi daya duƙufa akan Sehrish,Ya sanya duka hannayenshi ya tallabo kanta yana ƙokarin Kafa bakinta agabanshi,Hasbunallah!
  Kukan kura abu tayi a fujajen ta diro daga saman gadon,a harzuƙe ta rarumi Side drawer ɗin gadon,gaba daya ta kinkimota ta ɗaga sama da gudun gaske,Bata sauketa a ko'ina ba sai akan sayyadi gaba ɗaya Ta rotsa mashi ita asaman kanshi,wani irin jiri ne ya ɗebe shi ya soma tangal tangal zai faɗi,Rawanin kanshi tuni ya yi tsalle ya fadi kasa,
  Tsabar raɗaɗin da yaji ne yasa shi sakin Wuyan sehrish,Jallabiyarshi ta sauko ƙasa daga naɗewar dayayi mata,Rawanin kanshi kuwa tuni ya wargaje aƙasa,wani irin jiri ya soma gani kafin ya dawo hayyacinshi,Ganin Abu yasa shi ɗaure fuskarshi tamau,idanuwannan sunyi jawur dasu babu ɗigon Imani akansu,Kallon kallo suka shiga yi,jinjina kanshi ya yi yana huci kamar wani mayunwacin zaki,gadan gadan ya tunkareta,gashin kanta ya damƙo tare da yin wurgi da ita,gaba ɗaya ta kife ƙasa,juyawa yayi ya koma kan Sehrish wadda ke yashe ƙasa a sume,naɗe jallabiyar jikinshi ya soma yi,zukunnawa yayi agabanta yana ƙoƙarin tallabo kanta,

Abu dake kwance a ƙasa,ta ɗaɗɗago da kanta,yayin da hawaye ke ta sharorowa akan fuskarta,karaf idanuwanta suka sauka akan Sirinjin Allurar da Likita yayi mata ɗazu da safe,Wani tunani ne yazo mata,matsawa tayi tare da miƙa hannunta,ta Damƙi sirinjin allurar,yunkurawa tayi ta miƙe,cikin sanɗa ta soma tafiya tana tunkararshi,motsin da ya ji abayanshi ne yasa yayi firgit,Juyowar nan da zaiyi don yaga me take ƙokarin yi mashi,Ba zato ba tsammani,Abu ta daddage ta burma mashi Allurar acikin ƙwayar idonshi,Zuruf ta nutse acikin ƙwayar idonshi,Wata irin ƙururuwa Sayyadi yayi,Gaba ɗaya yabi ya firgice ya gigice ya zauce,Wani irin raɗaɗin Azaba mara misaltuwa Yaji mai haɗe da zogi,Caccaka mashi allurar ta dinga yi,gaba daya ta tsiyaye mashi idanuwanshi duka biyun,sulalewa yayi kasa yana burgima,Wata irin ƙururuwa da ya soma yi gaba daya kwaratsin shi ya karaɗe ko'ina na cikin gidan,Abu ta shammace shi,ta naƙasa mashi idanuwanshi wanda ya kasance rauninsu ne,a ƙungiyarsu ta matsafa da zarar member ya rasa idonshi,duk wani sihiri na jikinshi zai rabu dashi ne,Ya dawo normal mutun kamar kowa,

Tsananin tsorone ya kama abu ganin yadda jikin ya sayyadi ke fitar da wani irin baƙin hayaki batare da wuta naci ajikinshi ba,kamar tsumma haka ya nannaɗe wuri guda,hannu tasa tare da toshe kunnuwanta,Saboda sautin kururuwar da yake yi tamkar  Ana buga ganga acikin kunnuwan nata haka take ji,sosai ta runtse idanuwanta,
Lokacin da ta buɗe su,Sai da ta tsorata,ya 6ace 6aat babu shi acikin ɗakin sai dai Tsummar jallabiyarshi tare da rawaninshi,da kuma sharba sharban Silifas ɗinshi,



*Boss Bature*


A hankali yake saukowa down stairs,jikinshi na sanye da Jeans tare da t.shirt fara,gaba ɗaya ya canza,komai nashi ya sauya,tamkar ba Sgr ba,kwata kwata babu annuri akan fuskarshi,ya ƙara haske sosai,ya kuma yi rama,

Jin takun tafiyarshi yasa suka ɗago suna kallonshi,Tsayawa yayi yana ƙare masu kallo one by One,Fuskarshi ɗauke da matsananciyar damuwa,kullum ne sai sun zauna Zaman jiran dawowar junaid,babu yadda baiyi dasu ba akan su daina hana idonsu bacci Amma sun ƙiya,koda zasu yi baccin to sai dai ya ɗaukesu anan falon,Yayin da suke zaune zaman jiran dawowar junaid,

Ƙarasa saukowa yayi daga Saman stairs ɗin Ya nufi wurinsu,tunkan ya isa yace'Bana hanaku zama anan ba"?
Shiru sukayi saboda basu da amsar da zasu bashi,
Fitowa azmee tayi daga kitchen ta tunkaro wurin da suke,ƙarasowa tayi tana faɗin"Yawwa Rafayet,Dan Allah kayi Masu magana,tun ɗazu nake fama dasu akan suci abinci amma sun ƙiya,narasa yadda zanyi dasu,
  Ɗaure fuska jahan yayi tare da cewa'Dan Allah abarmu muji da abunda ya Dame mu,Idan muna jin yunwa zamu taso ne muci,"
  Yana kai ƙarshen maganar Fawan yace"Ni wlh komai ya fita raina,Nasaba cin abinci tare da baby junaid ɗinmu,yanzu kuma babu shi,Taya ma zan iya Cin abinci?bayan bansan halin da junaid yake ciki ba,Shin yaci abinci ko bai ci ba,"ya ƙarasa maganar tamkar zai fashe da kuka,
   "Allah yasa basu cutar mana dashi ba,Junaid ya saba rayuwarshi acikin ƴan uwanshi,hakanan wasu mugaye marasa imani sun ɗauke mana shi,"Acewar Irfan,
  Guntun tsoki jabeer yaja kafin yace"Ni babban takaici na,Duk yawanmu nan,arasa wa za'ayi garkuwa dashi sai junaid,Saboda bakin Hali irin na mutanan nan,wlh duk ranar da sukayi kuskuren da Asirinsu ya tonu sai sun ɗanɗani kuɗarsu,"

Kasa kunne Sgr yayi yana sauraronsu,tsananin tausayinsu ne ya kamashi,Ita kanta azmee jikinta ba ƙaramin sanyi yayi ba jin maganganun da sukeyi,Banga laifinsu ba,dole ne suyi kukan rashin junaid,yaron ne akwai shiga rai,Ya damu da kowa,kowa nashi ne,
  "Wlh bazamu iya jure rashin junaid ba,Ya rafayet dan Allah idan sun ƙara kira,A sanar dasu cewa,Su dawo mana da junaid,Ni su ɗauke ni,In yaso ma su ruƙe ni na har abada,"Ayaan ne yayi maganar,yayin da yake share hawayenshi,
  "Yaya rafayet,dan Allah nima idan sun kira ace masu ga wani ƙarin ma,"khaleed ne yayi maganar idonshi arufe Kamar maijin bacci,
  "Wlh tun ranar da aka ɗauke mana junaid,ban ƙara yin wanka ba,na ƙuntata rayuwata ne saboda Nima in ɗanɗani irin raɗaɗin da junaid ke ji a hannun waɗancan Azzaluman mutanan"yana kai ƙarshen maganar ya sanya tafin hannunshi tare da rufe fuskarshi yana kuka,abun ya ta6a masu zuciyarsu sosai,

Juyawa azmee tayi da sauri ta koma kitchen saboda kukan daya ciyota,

Cike da takaici Jahan yace"wai sun ɗauke junaid saboda kuɗi..........

💋Boss Bature💋*



Join this link to follow my tiktok acct👇

https://www.tiktok.com/@boss_bature?_t=8WKx0lm4jaP&_r=1




قصة حب رومانسية بين سحريش والجراح العام رفايت💋💘❤🤍❤💕💖*

*Father of soldiers*

*🔥TAKUN ƘARSHE🔥*


Am sorry,


"Is Enough!"tsit su kayi basu ƙara cewa uffan ba,
  "Kafin nan da 3 minutes inaso inga kowa asaman dining chairs yana cin abinci"
Miƙewa suka yi ba don sun so ba suka nufi dining area,kowa yaja kujera ya zauna,wuri ya samu shima ya zauna,tare da ƙwalawa Azmee kira,

Fitowa tayi daga cikin kitchen ɗin fuskarta duk alamun hawaye,Serving ɗinsu ta shiga yi,daƙyar suke Cusa abincin abakinsu,
"Kunsan Allah!kaf sai kun cinye abincin nan,its better ku saki jikinku,"

Loma suka soma yi,Suna ci hawaye na zuba,kowa da abunda yake ayyanawa aransa,
  "Babban yaya,kaifa?ba zaka ci ba?" Fawan ne yayi maganar,
Ɗaga mashi kai kawai yayi batare da yace ƙala ba,

Takun takalmi suka jiyo kamar ana tunkarosu,ɗagowa sukayi da idanuwansu suna kallon mai shigowar,Mommy ce jikinta sanye da Sleeping dress,ƙarasowa tayi ta samu wuri gefen Sgr ta zauna,
  Hada baki su kayi wurin gaisar da ita Mommy barka da dare,
  "Yawwa Sons,"ataƙaice ta amsa masu tare da kallon Fuskar Sgr dake a gefenta,
  "My son,har Yanzu ba zaka daina sa damuwa aranka ba?ina fa sane da irin yarda kake rayuwa acikin gidan nan yanzu,Ba abinci ba bacci taya zaka samu natsuwar yin investigation akan Kidnappers ɗin da Suka ɗauke mun Romeo ɗina"idanuwanta cike tab da hawaye ta karasa maganar,
  Calmly ya furta"Mommy,don't worry about that,Addu'arki kawai nake buƙata,"
  "Kullum haka kake ce mun,why should i not worry?addu'a dama inayi maka,Ni so nake inga kana cin abinci kuma kana bacci",

  Bai amsa mata ba sai ma fawan da yayi ma magana"Fawan,Call Jahad for me,"miƙewa fawan yayi jiki ba ƙwari ya nufi bedroom ɗinsu Sehrish,
mayar da hankalinshi yayi kan Mommy
  "She needs ur caring,tana cikin wani hali na buƙatar uwa atare da ita,Fawan zai kira maki ita,pls ki bata kyakkyawar kulawa,"yana kai ƙarshen maganar ya miƙe da sauri yabar dining ɗin,sam baison anayi mashi magana akan halin da yake ciki,
Girgiza kai kawai tayi,ita kanta jurewa kawai takeyi,

A bakin ƙopar ɗakinsu Fawan ya tsaya tare da sanya hannu yana kwankwasawa,
"Wanene,"muryar hosana ce yaji ta amsa mashi,
 "Ya fawan ne,jahad ake kira,"
  bude mashi ƙopar Hosana tayi tare da ɗan leƙo da kanta tana kallonshi,
  "where is she"?
Nuna mashi cikin ɗakin tayi da hannunta,Jahad ya hango kwance saman Darduma,
  "Kamar bacci take yi ko"?
Jinjina mashi kai tayi"Eh,"
  "Ta ci abinci"
"A'a,bata ci komai ba,"
."Okey taso mun ita,"
Juyawa tayi ta koma cikin ɗakin zuƙunnawa tayi agaban jahad tare da sanya hannu tana bubbuga bayanta
  "Jahad!jahad!"mutsu mutsu ta fara yi kafin ta yunkura ta tashi zaune,ta rame sosai tun daga kan fuskarta zaka lura da hakan,idanuwanta sun ƙanƙance saboda kukan da take sha,
  "Hosana bana ce kada ki tashe ni ba,"
  "Yaya fawan ne ke kiranki ae,"ta ƙarasa maganar tare da miƙewa ta koma saman gadonsu,
jiki ba ƙwari ta miƙe ta nufi ƙopar ɗakin,Fawan na ganinta ya ɗan saki fuskarshi,
"Ya fawan,"ta ambaci sunanshi,
"Babban yaya ne yace in kira mashi ke,"
Hannunta ya ruƙo ya jata suka nufi dining area,
 Lokacin da suka ƙarasa dining area ɗin,kiranta Alex tayi"jahad,"Amsa mata tayi"na'am mommy,"da hannu Alex tayi mata nuni da tazo kusa da ita ta zauna,zagayawa tayi 6angaren da Alexandra take,taja kujera ta zauna,tana sauke ajiyar zuciya,
   "Ya jikin naki,"? jahad tace"Alhamdulillah da sauƙi,"
   "Good haka nake son ji,"
Da kanta tayi serving ɗin jahad,ta shiga bata abincin abaki,dole Jahad ta saki ciki taci Abinci sosai,


*Boss Bature*

Ajiyar zuciya ta soma saukewa tare da Ambaton"ALHAMDULILLAH"mayar da idanuwanta tayi kan Sehrish dake sume a ƙasa,da Sauri ta ƙarasa wurinta zama tayi daga gefenta sannan ta sanya hannunta tare da janyo Sehrish ta ɗaurata asaman cinyoyinta,lumshe idanuwanta tayi tare da buɗe su akan fuskar Sehrish,Slowly ta ɗaura tafin hannunta asaman fuskar Sehrish tana shafata,kafin ta yarfar da Sumar kanta gefe guda,tayi hakan ne don taga rubutun dake a bayan wuyanta,Wanda tun suna yara Maman Sadeeq ta bata shawarar tayi masu shaida,Sehrish ta sanya mata SB ma'anarshi Sehrish buzuwa,Hosana ma akwai nata rubutun wuyan HB haka ma jahad,kowaccensu tana da shi abayan wuyanta,
  "Ya Allah na gode maka,daka dawo dani cikin hayyacina,Adai dai lokacin da ƴata ke buƙatar taimako na,"tana magana hawaye ne shararowa akan fuskarta,waige waige ta soma yi tana kallon ɗakin da suke ciki,Allah sarki lokaci guda ta fashe da kuka Saboda ta gane ɗakinta ne na gidansu Abusufyan,Bazata ta6a mantawa da irin rayuwar farin cikin da tayi ba acikin gidan,Tunawa da mahaifinta Baba buzu mai gadi yasa ta ƙara sautin kukan nata,
  "Zainab!Zainabu abu,"haka yake ƙwala mata kira,idan yana nemanta,tayi matukar danasanin bijire mashi da tayi a lokacin da yake raye duk da ta auri za6inshi,bakowa tafi jin kunyar haɗuwa dashi ba,irin Abusufyan batasan da wani ido zata kalleshi ba,Ga kuma Hajiya Ameena,mutanen da suka yi mata halacci ta butulce masu,

Ruwan hawayen abu ne suka wanke mata fuskarta,wanda hakan yayi silar farfaɗowarta daga suman da tayi,Yunƙurin amai ta fara yi daga kwancen da take,da sauri abu ta ɗago da ita,nan take aman ya kwararo daga bakinta,tamkar ƴan hanjin cikinta zasu fito waje,hannu abu tasa tana ɗan bubbuga mata bayanta,Sosai ta dinga sharara aman anan ƙasa,ta galabaita sosai ga zazza6in da ya yi mata mugun kamu,
  Miƙewa abu tayi da sauri ta fito daga dakin ta shigo palour,fridge ta hango da sauri ta nufe shi,buɗewa tayi tare da zura hannu ta ɗaukko bottle water jiki na rawa ta koma cikin ɗakin,A gaban sehrish ta zuƙunna a lokacin ta kammala kwarara Aman,cire murfin robar tayi tare da tarba tafin hannunta ta debo ruwan tana zuba mata shi abakinta tana kuskurewa,bayan ta gama kuskure bakin Abu ta kafa mata robar ruwan abakinta,Sosai ta shiga kwankwadar ruwan tana sha,sai da ta ƙoshi sannan ta janye bakinta,Har lokacin Sehrish bata dawo hayyacinta ba,jikinta duk ya saki babu ƙwari,
    Ajiye robar ruwan abu tayi gefe tana kallon fuskarta,
  Gam ta runtse idanuwanta,tana faman ciccije la66anta,
  "RISHI"ta furta sunanta,
A hankali Sehrish ta ɗan ware idanuwanta akan fuskar abu,wani irin sanyi ne ya ratsa zuciyarta,ganin Oummansu agabanta,kuma da alama tadawo cikin Hayyacinta ne,
  "Oumma,"ta ambaci sunanta tare da fashewa da wani sabon kuka,
  Ita ma abun fashewa tayi da kuka,Cikin Shesshekar kuka take cewa"Laifina ne!komai ya faru arayuwarku ni ce sila,Ni naja maku...."
  "Oumma ba laifin ki bane,ki daina ɗaurawa kanki laifi,Allah ya rigada ya ƙaddara faruwar hakan"
  "Rishi bakisan irin raɗaɗin da nake ji acikin zuciyata ba,bansan tsawon lokacin dana ɗauka bana acikin hayyacina ba,bansan ya rayuwarku ta ƙare ba,Nasan dole kunsha Wahala"
  Sosai suke yin kukan babu mai lallashin wani acikinsu,
Sai da suka yi mai isarsu,Sannan suka tsagaita da yin kukan,
   "Ina Hosana take?ina Jahad?duk suna ina?meyasa kike zaune ke kadai acikin gidan nan?Babu kowa atare dake?
  ɗagowa Sehrish tayi daga kwancen da take saman ƙirjinta,cikin sanyin murya tace"Hosana da Jahad suna a Abuja wurin danginsu Daddy"
  Cike da Mamaki abu ta maimaita sunan Daddy,
  Sehrish tace"Eh,mahaifinmu nake nufi,Daddy Abusufyan atare muka zo kano,Tun da ya fita da marece bai dawo ba,kuma akwai security guards dake tsaron gidan,Amma bansan ya akai Ya sayyadi ya shigo ciki ba,"
  Tunda Sehrish ta ambaci sunan Abusufyan jikin abu ya kara yin sanyi lakwas,shiru tayi na wani lokaci kafin tace"Kina nufin Abusufyan yana atare daku"?
  ɗaga mata kai Sehrish tayi"Eh,"
Abun yayi matukar ɗaure mata kai,cike da mamaki tace"Taya akai kuka san cewa shi ne mahaifinku?Kuma ya akai kuka haɗu dashi"?har ya kai ku wurin danginshi"?daƙyar take magana saboda Ciwon kan da take ji yana ɗan takura mata,
  "Oumma,Labari ne mai dogon zango....,"kasa ƙarasa maganar tayi sakamakon tashin Zuciyar da take ji,
  "Sannu kinji,idan muka samu natsuwa sai ki sanar dani"
   ta ƙarasa maganar tare da ruƙo hannayen Sehrish Cikin nata,suka mike tsaye suna fuskantar junansu,haɗa ido sukayi lokaci guda suka sakarwa juna murmushi,
"Kin girma sosai,komai naki ya canza mun,"duƙar da kai kasa sehrish tayi tana dariya,
  "Allah sarki hosana,Ashe da rabon zata rayu"?
  "Sai ma kin ganta Oumma,Zaki sha Mamaki Allah,saboda hosana duk tafi mu girman jiki,"
 wani irin farin ciki ne ya lullu6eta mara misaltuwa,

Sun jima suna tattaunawa atsakaninsu,kafin daga bisani Sehrish ta shiga toilet don tayi wanka,tunda ta rufo ƙopar toilet ɗin,ta sulale ƙasa jikin ƙofar tana kuka ƙasa ƙasa,Abunda ya sayyadi yayi mata ya tsaya mata aranta,yadda ya dinga goga mata Abunshi ajikinta,Da kuma harshenshi da ya sanya yana lasar mata bayanta Ba ƙaramin ƙona mata rai yayi ba,runtse idanuwanta tayi sosai,wani irin ɗaci ta dinga ji acikin zuciyarta,lokaci guda ta fara jin ƙyanƙyamin jikinta,hada ƙaiƙayi miƙewa tayi ta soma tu6e kayan baccin dake ajikinta,

Lokacin da ta kammala wankan ta fito jikinta ɗaure da towel,bata samu kowa a ɗakin ba,Amma taga an gyara shi,komai ya koma yadda yake,hatta aman da tayi an kwashe shi da tarkacen Ya sayyadi,tasan cewa aikin Oummansu ne,

Jiki ba ƙwari ta wuce saman gado ta haye,tare jan bargo ta lullu6e jikinta,bakowa take jiran dawowarshi ba,fa ce Daddynsu,Tayi mamakin jimawarshi awaje,har wuraren 12,Allah yasa dai yana lafiya,

Kitchen ta shiga ta ɗauko Ashana,da sauri ta fito ta dawo harabar gidan,inda ta tattara Tsummokaran Ya sayyadi da ya bar masu,ba tare da taji komae ba ta Ƙyasta ashanar ta jefa ta asaman kayan nan take wuta ta soma ci ajikinsu,har sai da ta cinyesu abu na tsaye tana kallonsu,

Ajiyar Zuciya ta sauke tare da bin gidan da kallo,mutane ta hango a bakin gate ɗin gidan Sanye da kakin Sojoji,kowannansu a yashe ƙasa sai bacci sukeyi,Abun ba ƙaramin ɗaure mata kai yayi ba,ranta ne ya bata cewar Securities ne,Da alama Ya sayyadi ne yasa su yin baccin Dole,don ya samu hanyar shigowa cikin gidan,

Girgiza kai kawai tayi tare da komawa cikin falon,Bedroom ɗin ta shiga,tsayawa tayi abakin ƙopar ɗakin tana kallon Sehrish dake ƙumshe cikin bargo,jikinta sae kerma yake yi,
 Idasa shiga cikin ɗakin tayi har zuwa gefen gadon ta zauna,tare da Ambaton Sunanta"Sehrish,"
  Muryata na kerma tace"Na'am Oumma,"
   "Taya zan iya samun Daddynku?inaso nayi magana dashi,"
   "Ina da waya,nabarta a ɗaya daga cikin ɗakunan dake a upstairs,"
  Da sauri abu ta mike ta fuce daga ɗakin,Upstairs ta wuce,tana neman ɗakin da sehrish ta faɗa mata,Ɗaki ɗaya ta samu a buɗe,tun kafin ta shiga tajiyo ringing ɗin wayar tura ƙopar tayi ta shiga cikinsa,A saman gado ta samu wayar,hannu takai ta ɗauki wayar tare da duba screen ɗin
  "My Boss Man,"shi ne sunan daya bayyana akan Screen ɗin

Chapters

Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login